Showing 12001 words to 15000 words out of 34129 words
jin kawai Yakumbo zatayi maganar aurensu da Rafeeq Gwarzo. Zaune take a parlor ta kurawa ƙofar shigowa parlourn ido da alamar akwai wanda takeso ta gani ya shigo...
#ASMY B ALIYU
#HAJJA CE👈
#TEAM RAFEEQ
# ƳAN TAGWAYE BIYAR 2023
ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.
IYALINA (A'ILATY)
RAFEEQ
MUNƊO
ZAMANIN MU AYAU
FATHIYYA.
DOMIN SIYAR GUDA BIYAR N1500.
DOMIN SIYAR DAYA N400.
Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
Ga MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪
Tura ta Nita
Da sunan
Asma'u Buhari Aliyu
08086207764
SAI KI/KA TURA SHAIDAR BIYA TA DAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.
+234 808 620 7764
07065283730
+234 705 124 4211
+234 704 040 2435
[5/4, 9:00 PM] Asmy B Aliyu😘: *RAFEEQ*
*PAID BOOK #400*
TEAM TAGWAYE NOVEL'S
Na
_*ASMY B ALIYU*_
Da
_*HAJJA CE*👈_
6.....
Gabaki ɗaya taji ta kasa nutsuwa a cikin ɗakin, wayar da yake yi ta kasa barinta cikin nutsuwarta. A fusace Maimoon ta aje masa bowl ɗin akan center table ɗin dake tsakiyyar room ɗin cike da jin haushinsa ta nufi hanyar barin parlorn, lokaci ɗaya Rafeeq ya fisgota ta faɗo cikin jikinsa gabaki ɗaya. Jinta cikin jikinsa kawai yasa ta buɗe ido tana kallonsa cikin tashin hankali. Duk yadda take ƙoƙarin kwatar jikinta Rafeeq ya hana dan ya riƙeta sosai ta yadda ba zata iya ba, still yaki kashe wayar da yake yi da Zeee. Da wani yanayi cikin muryar Zeee ɗin haka tana jin wani abu na danne mata zuciya take faɗin. "Rafeeq hankalinka yana tare da kai kuwa?" Ta faɗa da rawar murya. Sai ƙoƙarin saita kansa yake ta yadda Zeee ba zata gane komai ba amma ya kasa, saboda jin kawai Maimoon Gwarzo acikin jikinsa baiki su dawwama a hakan ba har zuwa lokacin da Ubangiji zai dakatar da numfashinsu. "Yaya ka sakeni wallahi zan maka ihu." Maimoon ta faɗa ciki muryar kuka. Tamkar a mafarki Zeee taji muryar Maimoon ta cikin wayar, da mugun shock da mamaki take ayyana 'Kenan suna tare?' wata zuciyar ta faɗa mata tana jin hawaye na cika mata idonta. Kashe wayar tayi duka a hankali Rafeeq ya kalli gaban wayar yana cije leɓe kafin ya maida hankalinsa wajan Maimoon da ta wani haɗe rai, still tana zaune kan cinyoyinsa. "Ba kince zamuyi magana ba? meyasa zaki tafi? haka kurum kin sa budurwarta taji muryarki ta kashe wayar." Maimoon tana san fisge jikinta take faɗin. "Ni bana sonta wallahi ka canza wata tun wuri dan bazaka aureta ba indai wacce nagani agaban motar kace." Maimoon ta faɗa sounding so very serious cikin muryarta. Rafeeq ya zuba mata idanunsa zuciyarsa na mugun bugawa, zai yi magana da wata irin rigima tabar jikinsa. Kai tsaye ta fice daga parlorn kwantar da kansa yayi cikin soofa tare da lumshe fararen idanunsa da suka daɗe da canza launi. Hannu ya kai ya naɗe jallabiyar jikinsa yana jin wurin ya canza saboda kawai zaman Maimoon akan cinyoyinsa. Yana cikin wannan yanayin kira ya shigo wayarsa, dakyar ya ɗauki wayar ya katse tare da ajewa. Kai tsaye ɗakin baccinsa ya nufa riƙe da marasa yana sake cije baki. Duk da yasan illar da ruwan sanyi keyi masa haka ya tsaya cikin shower ruwa na sauka a kansa. Yafi minti ashirin cikin toilet haka ya fito daure da towel ɗin a kugunsa yana jin sanyi na shiga cikin jikinsa sosai dan har wani kaɗawa jikinsa yake yi. Mayukkan da yake using ya shiga shafawa yana gamawa ya buɗe closet ɗinsa ya fiddo pyjamas ɗinsa ya saka sannan ya kashe ac dan yasan idan Shaheed Gwarzo ya leƙo ɗakinsa yaji da ac zai canyesa da faɗa. Kai tsaye bed ya nufa ya kwanta ya jawo duvert ya rufe jikinsa. Kiran wayar Maimoon yayi amma ya jita busy, nan take yaji wani irin bakin ciki ya rufe masa zuciya kuma yasan da Abdul-wahab take wayar. Saƙo ya tura mata akan ta ɗauki wayarsa magana zasu yi, amma har kusan minti talatin yana jiranta sannan Maimoon ta kirashi. A fusace Rafeeq ke mata magana. "Saboda kin gama raina min hankali shine sai yanzu zaki wani kirani ko?" Za tayi magana ya kashe wayarsa duka. Tabbas Maimoon tana kona masa zuciya tun kafin ta tafasa. Rasa inda zai tsoma ransa yayi gashi ya kira Zainab ya kai sau biyar bata ɗauka ba. Har kusan karfe 12 idonsa biyu ya kasa bacci, kwan da ya dafa ma ya barshi a parlor baici ba. Washe gari suna breakfast dukan su a cikin dinning area, Aunty ta kalli Daddy da murmushi cikin fuskarta take faɗin. "Daddy jibi ne fa za'a kawo lefen Maimoon, shin wani shirye-shirye ya dace ayi? Saboda bamu san wane tsari kayi ba ta ɓangarenka." Da murmushi cikin fuskar Daddy ya wani kalli Maimoon yace. "Eyeeeh yarinyata zata girma kwanan nan." Da wata irin kunyar daddy Maimoon ta wani ɓoye fuskarta a bayan Rafeeq daman tana kusa dashi. Wani irin fat-fat ƙirjin Rafeeq ɗin ya shiga yi, Daddy ya kalli Aunty yana faɗin. "Gobe insha Allahu Yakumbo zata zo sai ku tsara komai tare, da dai har tace bazata zoba sai an fara bikin na dai samu na lallaɓata ta yadda, gobe driver zaije ya ɗakko ta." Da murmushi cikin fuskar Aunty take faɗin. "Allah ya kaimu ya kuma kawota lafiya." Daddy ya amsa da "Ameen." Sannan ya kalli Shaheed da Rafeeq yana faɗin. "Ku kuma banji kunce komai ba, me zaku bawa auta ta a matsayin gifts na aurenta? Dan something very speacial mukeso ko Auta?" Daddy ya faɗa sounding so very happy cikin muryarsa. Ɗagawa Daddyn kai kawai tayi cike da jin kunya. Da sauri Shaheed ke faɗin. "Toh wai mu mezamu bata Daddy? duk abinda zata buƙata kayi mata me kuma ya rage?" Da sauri Maimoon tace. "Wallahi sai kun bayar ban yadda ba." Wani irin kallo Rafeeq keyi mata da sauri ta matsa daga bayansa ta turo baki tana faɗin. "Daddy ka ganshi ko? Jifa yadda yake wani hararata." Miƙewa Rafeeq ya yi fuska babu walwala ya bar cikin parlorn ba tare da yace komai ba. Duk suka bishi da kallo, Maimoon ta buɗe hannunwa tana faɗin. "Sarkin zuciya sai kaga wanda zai wani bika ya lallasheka." Aunty tayi murmushi tana faɗin. "Ba'a shiga tsakanin ku ai." Da sauri shaheed ya karɓe zancen yana faɗin. "Wanda ya shiga ma zaiji kunya." Tana zaune a ɗaki tana duba handout saboda za su yi test gobe, dan haka gobe tunda safe zata koma Zaria, can kuma sai ta tuna da Rafeeq bai yi lunch ba har wurin 3 na rana Miƙewa tayi tsaye ƙananun kaya ne ajikinta ta ɗora rigar kimono a saman kayan ta fito. Babu kowa a parlorn daman kuma Aunty ta fita wata kawarta ta haihu shine taje yi mata barka. Ɗibar masa abincin tayi ta jera komai akan tray ta nufi ɓangaren su. Babu kowa a parlorn sai karar ac wani irin sanyi ke fitowa daga cikin parlor, ta aje abincin ta girgiza kai ta ɗauki remote ta kashe ac ɗin duka. Wallahi ko kaɗan Yaya Rafeeq baya jin magana. Ɗan tsaki taja tana nufar hanyar bedroom ɗinsa, knocking tayi kusan minti ɗaya jin shiru yasa ta tura kai ta shiga. Kallo ɗaya ya yi mata ya wani ɗauke kai tare mai da hankalinsa kan wayarsa. "Yaya ga abincinka na kawo maka ka taso kaci." idonsa na kan waya ya wani taɓe baki yana faɗin. "Aka ce maki ina jin yunwa ne?" Ta wani harareshi ba tare da ya ganta ba take faɗin. "Tun karin safe fa baka zo kaci komai ba, wai meyasa kake wasa da lafiyar ka ne?" Jin yaki cewa komai ne yasa ta juya tabar ƙofar, bata jimaba ta shigo da tray ɗin ta ɗauki plate ta zuba shinkafa da miya sai kuma naman rago da coslow ta wani haɗe rai ta saka spoon ta jujjuwa gefe ɗaya ta nufi bakinsa da ita, kallon idonta ya shiga yi sai kuma ya wani ɗauke kai. "Yaya ka karbi abincin nan kaci tun kafin na tara maka jama'a." Ta faɗa babu alamar wasa cikin fuskarta. Saboda baya son magana yasa shi buɗe bakin ta shiga feeding ɗinsa tamkar wani ƙaramin yaro. Shi kanshi bai san yana jin yunwa ba sai da ta fara basshi abincin, sai da ya kusa canyewa sannan ya kauda kai yace mata ya koshi. Plate ɗin ta aje agefe ya jawo tissue ya shiga goge bakinsa ba tare da ya kalleta ba yake faɗin. "Me kikeso a matsayin gifts ɗin da zan bayar na aurenki dan naga har wani daɗi ke shiga cikin kanki wai ke zaki bar rayuwarmu ko?" Ya faɗa yana wani haɗe fuska. Lokaci ɗaya Maimoon gwarzo ta saƙalo hannayenta ta wuyansa tana leƙen fuskarshi take faɗin. "Yaya zan tambaye ka, wai meyasa baka son Abdul-wahab? meyayi maka? kowa na gidan nan yana sonshi banda kai why?." Ji ya yi zuciyarsa na masa zafi jin kalamanta kafin yace. "Kawai dai beyi min ba, kuma ina jin har abada ba zai yi min ba." Ya faɗa yana kallon cikin idanunta. Idan tace maganar Rafeeq Gwarzo bata taɓa ta ba tayi karya. Ba tare da ta ƙara magana ba ta ɗauki tray ɗin tabar masa ɗakin. Ɗan tsaki yaja ya koma yayi kwanciyyarsa. Har washegari da zata koma Zaria bata nemi Rafeeq ba daman tayi sallama da kowa ban dashi, shima da yaji a bakin Shaheed cewar ta wuce yasha mamaki dan bai taɓa tunanin zata iya tafiya ba tare da tayi masa sallama ba. Sai kusan la'asar Yakumbo ta iso tare da driver da kuma ƴarta Haneefa. Kowa yazo ya yiwa Yakumbo sannu da zuwa amma ban da Rafeeq, ita kuma Haneefa burinta kawai ta sanya Rafeeq Gwarzo a cikin idanunta, saboda shi tazo garin Kano saboda shi ta biyo Yakumbo suka zo. Kasa daurewa Haneefa tayi ta kalli Aunty dake serving ɗinsu cikin dinning area tana faɗin. "Aunty wai Yaya Rafeeq fa?" Da murmushi Aunty ke faɗin. "Tun safe bamu haɗu ba, maybe yana ɗaki ko kuma baya gidan." Yakumbo ta taɓe baki tana faɗin. "Oh har yau bakin halin nashi yana nan? Allah ya kyauta." Murmushi kawai Aunty tayi. Sai kusan magrib ya shigo gidan duk yau bai zauna cikin gidan ba saboda wani irin faɗi da gidan yayi masa ganin babu Maimoon a cikin sa. Koda ta sauka ta turo masa sako akan sun isa lafiya har drivern da ya kawota ya taho, shareta yayi ba tare da ya mayar mata da reply ba. Da fara'a sosai cikin fuskar Haneefa ta nufi Rafeeq Gwarzo tamkar zata rungumeshi sai kuma ta fasa ta mai da hannunta baya, da murmushi a fuskarta take faɗin. "Yaya Rafeeq sannu da zuwa." Da ɗan murmushi Rafeeq ke faɗin. "Sannu Haneefa saukar yaushe?" Tace, "Tun dazu muka shigo baka gidan." Daga haka ya nufi Yakumbo ya zauna kan rug yana gaisheta, wani kallo ta riƙa yi masa tana cewa. "Nidai ka rainani Rafeeq idan Mustapha ne yazo zakaki zuwa ka gaisheshi?" Lokaci ɗaya ya haɗe rai abunda ke hadashi da Yakumbo kenan zagi, shi kuma daman can jininsa bai haɗu da ita ba. Hakuri kawai ya bata ya miƙe yabar musu parlorn, tamkar Haneefa zatayi kuka take faɗin. "Meyasa zaki yi masa haka? Kinga kin sa ya tafi bancin kin san ya tsani hayaniya." Haneefa ta faɗa cike da takaici, wani mugun kallo Yakumbon keyi mata tana faɗin. "Sannu uwata, nace sannu kinji? Toh shi ubana ne da zan riƙa wani lallaɓashi? daman duk Mustapha ya sangartashi shi yasa yake kallon mutane a sama-sama." Ganin Yakumbo zata juyewa Haneefa tamkar ita tayi mata laifin yasa tabar wajen tamkar zata yi kuka. Da daddare Daddy ya samu Yakumbo suka gaisa anan kuma take faɗa masa irin kallon hadarin kajin da Rafeeq keyi mata. Murmushi Daddy yayi duk dan a zauna lafiya ya fiddo waya ya shiga kiran layin Rafeeq sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗauka, muryarsa tamkar mai mura haka Daddy yaji muryar dan haka yace "Lafiyarka kuwa? anya babu mura a tare da kai Rafeeq?" Da sauri Rafeeq yace "No daddy." "Owk ka sameni a parlor." Daga haka ya kashe wayar Ita dai baki Yakumbo ta buɗe tana kallon Daddy take faɗin. "Dole Rafeeq ya sangarce haba, yanzu saboda Allah dan yana mura zaka wani damu sai kace ƙaramin yaro ne yake murar?" Murmushi Daddy ya yi yana kallon Yayar tashi yake faɗin. "Kin san fa matsalarsa Yakumbo dole sai ana lallaɓa shi." Da sallama ya shigo parlorn Daddy ya samu wuri ya zauna yana gaishe da Daddyn da respect hakama ya sake gaida Yakumbo. Da kulawa Daddyn ke faɗin. "Meya haɗaka da Yakumbo?" Ya wani haɗe rai yana faɗin. "Daddy kafa san halinta." Dakuwa Yakumbo ta shiga yi masa, murmushi yayi yana kallon Rafeeq da kulawa cikin harshen turanci yake ce dashi ya riƙa lallaɓa ta haka take sai hakuri baya ganin tana zaune dasu Shaheed lafiya lau. Rafeeq zai yi magana Daddy yayi saurin dakatar dashi. "Oya tell her sorry." Tamkar Rafeeq bayaso ya wani dawo gaban Yakumbo ya wani riƙe hannunta da murmushi acikin fuskarsa yake bata hakuri. Taɓe baki kawai tayi ta maida kallonta wurin daddy tana faɗin. "Nidai ga shawara ka haɗe yaran nan duka kayi masu aure, Shaheed yana da wacce zai aura dama, shi kuma wannan banga mai yake jira ba." Da sauri Rafeeq ya miƙe yabar musu parlorn, cikin ɗaga murya Yakumbo ke faɗin. "Sai mun tashi tsaye akan yaron na kilama aljana ce ta aureshi bamu sani ba." Murmushi kawai Daddy ya yi yana cewa....
#ASMY B ALIYU
#HAJJA CE👈
#Rafeeq Gwarzo
#Zeee Liman
#Maimoon Gwarzo
#Haneefa
#HANNU BIYU-BIYU....
[5/4, 9:00 PM] Asmy B Aliyu😘: *RAFEEQ*
*PAID BOOK #400*
Na
_*ASMY B ALIYU*_
Da
_*HAJJA CE*_
8.....
Da mamaki Yakumbo ke mata wani irin kallo tana bin ƙofar da ta zubawa ido kamar mai nazarin wani abun, bata ga komai ba a hanyar hakan yasa ta kiran sunanta da kulawa. "Haneefa." Ba tare da ta ɗauke ido daga bakin ƙofar ba ta amsawa Yakumbo "Na'am." Mamaki ne ya kama Yakumbo, anya yarinyar nan lafiyarta ƙalau kuwa? Wannan fa duk ba ɗabi'unta bane amma taga tunda suka zo gidan nan ta fara canzawa komai nata juyewa yake yana komawa kalar mamaki. "Ki tashi daga parlorn nan kije kiyi kwanciyarki kin zauna kina tunani." Yakumbo ta faɗa tana ƙoƙarin shiga kitchen dan haɗo ruwan tea tasha.Haneefa ta shiga turo baki ita kam bazata iya kwanciya ba sai taga shigowar Rafeeq Gwarzo da take jin bugun zuciyarta yana sake canzawa saboda wata soyayyarsa da take shigar ta a hankali. Aunty ce ta fito daga wajan Daddy zata nufi kitchen taga Haneefa kamar gunki ta zubawa hanyar shigowa parlorn idanuwa, mamaki ya kama Aunty cike da kulawa take faɗin. "Haneefa tunanin me kike haka?" Haneefa ta ɗan juya gani take kamar an gano abinda yake damunta, rausayar da kai tayi gefe tana gaida Aunty ta amsa da kulawa kafin tace. "Gidan ne yayi min girma Aunty saboda rashin Maimoon." Aunty na wucewa kitchen take cewa. "Aikuwa bata nan wai test gareta shine ta koma makarantar." Bata jira me Haneefa zata faɗa ba tabar wajan. Yakumbo ta tarar tana zuba tea cike da girmamawa kamar yadda Daddy ke bawa Yakumbon girma itama ta gaishe da ita tana cewa. "Yakumbo maimakon ki kirani na haɗa miki? Kawo a ƙarasa kije parlor kiyi zamanki." Aunty ta fara ƙoƙarin karɓar mug ɗin Amma Yakumbo ta janye tana cewa. "A'a kibarshi ai na gama haɗawa, ga Lami can ma ta fara shirya kayan karin ni da yake kinsan ba jira nake yi ba da safe." Ta ƙarasa maganar tana buɗe fridge ta ɗakko bread kai tsaye ta dawo parlor tana sake kallon Haneefa da duk ta rasa nutsuwarta.
Yana tuƙi yana shafa haɓarsa dake ɗauke da wani ƙawataccen (beard) bakin gashi da ya sake ƙawata kyawun hlittar fuskarshi, tunani ne fal a cikin zuciyarshi na yadda zai kawo karshen alaƙar maganar auran Maimoon Gwarzo da Abdul-Wahaab wanda za a yi shi kwana nan, amma ya rasa mafitar da zata hana ayi shi gashi har yau za'a kawo kayan auranta yana ji kuma yana gani ba zai iya hanawa ba. Babbar damuwarsa a wannan lamarin itace Maimoon ɗin wani irin kallo takeyi mishi irin wanda take yiwa Shaheed Gwarzo da Moobarak Gwarzo, abin nufi da kallon anan shine babu aure a tsakanin su tana mishi kallon sun haramta wajan yin soyayya irin ta aure. Banda haka Rafeeq Gwarzo namiji ne da ba kowacce mace zata iya gani bace ta kyale saboda tsarin halitta da ubangiji ya bashi. Kai ya shiga juyawa yana jin zuciyarsa na wani irin nauyi, duk da cewa gudu yake yi mai cike da nutsuwa da babu wanda zai zageshi ko ya aibatashi, amma shi gani yake yi tamkar baya saurin. Ƙaguwa ce cike a zuciyarsa na san ganin Moon Yana ganin kamar sunyi watanni basu haɗu da juna ba. Wayarsa ce ta fara ringing ya ɗan ja ƙaramin tsaki dan shi a yanzu baya san ana damunsa, gani yake komai yai masa zafi a cikin duniyar. Gudun motar ya ɗan rage sannan ya zaro wayar daga cikin aljihun gaban rigarsa yana duba sunan mai kiran. Zeeeee ce, Rafeeq ya ɗan cije leɓe yana sake yatsina fuska, baya buƙatar kiran kowa idan ba na Maimoon ba kuma yasan ba kiranshi zatai ba sai dai ta kira Wahaab tunda shine zabin zuciyarta. Kamar anyi masa duka haka ya kara wayar jikin kunnansa yana riƙe da sitiyarin motar da ɗan karfi saboda wani irin nauyi da yaji kansa nayi, yaji muryarta tana cewa. "An tashi lafiya?" Yace, "Uhmmm na tashi." Zee ta sake jan pillow ta rungume a jikinta idanun ta a lumshe babu abinda take hangowa sai kyakkyawar fuskar Rafeeq, cikin nuna kulawa tace. "Naji kamar baka ma gida, kana ina da sassafe haka?" Sai da yaja numfashi yana wani lumshe idanuwa ya sauke sannan yace da ita. "Ina hanyar zuwa zaria." Gaban Zee ne ya wani irin bugawa dan tasan tabbas Rafeeq wajan Maimoon zaije a wannan lokacin duk da bata da tabbacin ta koma makaranta. Shin takoma ne dama ko kuwa dai ba wajanta zai je ba? Shin wai me yasa Rafeeq Gwarzo ya sadaukar da duk wani lokaci nashi da jin daɗinsa, walwalarsa duka a wajan
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book