Showing 15001 words to 18000 words out of 34129 words
wacce bata ma san yanayi mata wata kalar soyayya ba? Anya babu bakin ciki a cikin wannan lamarin? Ita ya kamata Rafeeq Gwarzo yaiwa wannan kulawar da nuna tsantsar soyayya tunda tana sonshi ta kuma damu dashi ya sani, sai dai ya kasa bata muhimmancin da take buƙatar samu a wajansa bare har ya mallaka mata komai nashi kamar yadda ya miƙawa wacce take shirin fara yin rayuwa mai daɗi tare da wani ba shi ba. "Lafiya dai ko?" Zee ta daure tare da jefa masa wannan tambayar wacce tasan ita kaɗai ce zata raba shirun da sukai na ɗan lokaci. Kuma damƙe sitiyarin yayi zuciyarsa na sake hasaso masa Maimoon Gwarzo a cikin idanunsa. "Zanje na kaiwa Moon wani saƙo ne, kuma kinsan menene Zee?" Bai jira tayi magana ba yaci gaba da cewa. "Yau za a kawo kayan lefenta ina cikin damuwa bansan wanda zan gayawa yadda nake jin zuciya ta ba. Please pray for me ko zan samu sassaucin yadda nake jin raina." Wani irin kishi ya tasowa Zee tana jin duk wata kalma dake fitowa daga bakin Rafeeq nayi mata nauyi cikin zuciyarta. Ita kam yanzu me zata cewa Rafeeq Gwarzo ya gane cewa ya hakura da Maimoon tunda tayi masa nisa? Tasan yanzu idan ta nuna bata bayanshi kila ya dena kulata abinda ita kuma ba zata iya jurewa ba. Cikin dauriya hannunta dafe saman kirjinta take faɗin. "Ka gaya mata sirrin zuciyarka kawai mana Rafeeq, dan wannan shirun da kake yi babu abinda zai ƙara maka sai damuwa tunda kaga dai wani yana shirin mallaketa gaba ɗaya." Ɗan shiru yayi yana cije leɓansa na sama, haka kawai bai san meyasa ba sai yaji maganganun Zee ɗin suna yi masa rashin daɗi a cikin ranshi. Ya sake jan ajiyar zuciya kamar tana gabansa yake cewa. "Zainab ki gaida mutanen gidan idan na dawo zamu yi waya." Ya faɗa yana datse kiran ba tare da ya jira me zata faɗa ba. Tuki ya cigaba da yi cikin natsuwa yana son kuma ya samu hanyar da zai fallasawa Maimoon Gwarzo cewa yana tsananin kaunarta a yau ɗin nan, sannan ya tabbatar mata da cewa dan shi kawai aka halicceta. Amma wani ɓangaren na zuciyarsa tamabayarsa takeyi shin ta ya ya zai gaya mata? Ya manta ne tana da zaɓin zuciyarta? anya kuwa Rafeeq bakayi zurfi dayawa ba a lamarinka da Maimoon? ji yayi zuciyarsa na qaryewa a hankali, haka kuma yaji tamkar ya juya kan motar ya koma gida ba sai yaje gurinta ba, sai dai yasan idan ya koma gidan damuwace zata qara cika masa zuciya, gara ya lallaɓa yaje ya ganta, fatansa Allah ya buɗe bakinsa a yau ya faɗa mata sirrin dake ransa watakila zata amince ta karbi soyayyarsa fiye da wancan baren dake gefe yana wasa da zuciyarta.
Tana jin yadda Ayshaa ke ɗan buga pillown da tayi matashi dashi, a hankali ta soma buɗe fararen idanunta wanda basu gaji da yin baccin ba, ta kalli Ayshaa tana ware mata ido tana faɗin. "Kina kallon agogo kuwa? Toh ko tashi dan bai wuce minti talatin ba mu shiga test ɗin kin san kuma halinshi ba kirki ne dashi ba kar ya sa muyi missing wannan gwajin." Miƙewa zaune Maimoon tayi tana ƙara murza idanunta take faɗin. "Kaina ciwo yake min Ayshaa, gashi ko'ina na jikina ciwo yake yi na rasa meke yi min daɗi yau." Ta ƙarasa maganar tana ɗaukar wayarta taga miss calls ɗin Abdul-waahab sai dai bata bi ta kansu ba saboda tasan idan ta kirashi zai tsareta da magana ne har su makara. Da sauri ta aje wayar kai tsaye toilet ta faɗa a gurguje tayi wanka ta shirya cikin ɗinkin doguwar rigar atamfar gillter wacce tayi matuqar yi mata kyau. Duk yadda Ayshaa taso ta tsaya tasha ko da tea ne ƙin tsayawa Maimoon tayi tana faɗin suje kawai idan suka fito sai ta samu abunda zataci.
Suna cikin rubutu text ɗin saqo ya shigo wayarta amma babu halin ta duba saboda kar ai mata magana ko a korata ma. Dole ta hakura sai da suka gama suka fito suna ɗan maida maganar yadda gwajin yai musu, ta buɗe jakar ta ɗakko wayar daman ta sakata a silent ne shi yasa ma ba'a lura ba sai ita kadai. Da mamaki take duba saƙon tana kuma ware ido. Rafeeq ne ya mata sakon akan cewa yana cikin makarantar su ta fito, sai kuma ga kiransa kusan kira 5 wanda har ta fara hango yanayin fuskar Rafeeq ɗin a wannan lokacin, tasan tabbas yana can ya cika ya yi fam kiris yake jira a taɓoshi. Ta kalli Ayshaa tana faɗin. "Zo muje ku gaisa da Yaya Rafeeq shine yazo tun dazun." Ta sake kallan Ayshaa da fuskar tausayi take faɗin. "Idan muka je dan Allah kiyi masa bayani idan ba haka ba wallahi canyeni zai yi da faɗa saboda ya kira ban ɗauka ba, komai zan faɗa masa ba ganewa zai ba zai yadda ba." Ta faɗa tana mai da hannayenta baya. Murmushi Ayshaa tayi tana faɗin. "Da gaske wannan Yayan naki sonki yake yi sosai, Allah Maimoon soyayya ta musamman yake yi miki ko ki yadda ko karki yadda idan ba haka ba meye na biyoki har Zaria yau? baga waya nan ba me yasa ba zai kiraki ya gaya miki koma meye ba? Yaushe kika baro gida da har za a zo miki ziyara? Idan har kinga irin wannan tana faruwa toh tsantsar kauna ke janyowa wallahi. Gaskiyyar Abdul-Waahab ne da yace Yayanki Rafeeq yana da wata manufa tsakanin ku." Lokaci ɗaya fara'ar dake cikin fuskar Maimoon Gwarzo ta ɗauke gaba ɗaya, cikin yanayi na ɓacin rai take cewa. "Meyasa kika kasa yadda Yaya Rafeeq baya min soyayyar aure Ayshaa? sai dai yana min soyayya ne irin ta ƴan uwantaka kawai, karki manta matsayinsu ɗaya ne da na Yaya Shaheed a wajena. So ki daina ma wannan tunanin naki ki daina biyewa Wahaab kuna ƙoƙarin rugurguza kyakkyawar fahimtar dake tsakanina da Yaya, shima idan munyi aure zai daina zargi ya gane. Shakuwace kawai kuke ganin kamar Yaya Rafeeq yana sona. Karki manta yasan ina da wanda nake so, karewarta ma yau ne za a kai lefen Wahaab gidan mu, please mu tafi karki ɓatamin rai da sanyin safiyar nan." Maimoon taja hannun Ayshaa tana wani haɗe rai dan karma ta ƙara jan maganar, da ita da Abdul-Wahaab ta rasa me yasa suke hango cewar kamar Rafeeq Gwarzo yana yi mata soyayyar aure ba soyayyar Yaya da ƙanwarsa ba. Abun yana bata mamaki tare da ɗaure mata kai, da gaske ita kam bata yiwa Rafeeq Gwarzo soyayyar aure, tana jin matsayinsu ɗaya a zuciyarta kamar yadda takejin matsayin Yayanta Shaheed da Yayanta Moobarak..
#ASMY B ALIYU
#HAJJA Ce
#Rafeeq gwarzo
#maimoon gwarzo
ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.
IYALINA (A'ILATY)
RAFEEQ
MUNƊO
ZAMANIN MU AYAU
FATHIYYA.
DOMIN SIYAR GUDA BIYAR N1500.
DOMIN SIYAR DAYA N400.
Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
Ga MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪
Tura ta Nita
Da sunan
Asma'u Buhari Aliyu
08086207764
SAI KI/KA IS TURA SHAIDAR BIYA TA DAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.
+234 808 620 7764
07065283730
+234 705 124 4211
+234 704 040 2435
[5/4, 9:00 PM] Asmy B Aliyu😘: *RAFEEQ*
*PAID BOOK#400*
Na
_*ASMY B ALIYU*_
DA
_*HAJJA CE*_👈
9...
Cike da murnar hangoshi suka ƙarasa wajan da yake, sama-sama suka gaisa da Aysha kafin ta nufi hostel dama kuma can jininsu bai wani haɗu da Rafeeq ɗin ba. A tunanin Ayshaa yana cikin mutanen da suka kasance masu mugun ji da kai da wani irin faɗin ran tsiya, wanda idan aka gaisheshi ma dakyar yake iya amsawa mutane babu walwala acikin fuskarsa. Saɓanin Yaya Shaheed da suke wasa da dariya idan ya kawowa Maimoon ɗin ziyara a yawancin lokutta. Ayshaa na wucewa Maimoon ta buɗe gaban motar ta shiga tare da saka hannunta ta rufe motar, bata kalleshi ba tunda ta shiga, hannu kawai ta saka tare da rage sanyin ac motar sannan ta kallesa tana faɗin. "Yaya wannan sanyin ai ya yiwa jikin ka yawa sosai, wai bakaji me likita ya faɗa maka ba ne?" Rafeeq ya share yaki kula maganar da take yi masa, cikin takaici yake cewa. "Please Moon idan zaki zo wajena ki rinƙa zuwa ke ɗaya bana son wannan ƙawar taki tayi ta bin ko'ina na jikin mutum da ido tamkar wata mayya." Ya faɗa mata so pissed up a muryarsa. Maimoon ta langabe kai tana kallon cikin fuskarsa ganin yadda yake wani haɗe rai. A hankali ta kamo hannunsa batareda tunanin komai ba ta riqe cikin nata hannun. Wani irin shock yaji lokaci ɗaya tun daga tsakiyyar kansa har cikin tafin ƙafarsa. Muryarta mai sake rikita masa lissafi yaji tana masa magana. "Yaya ko dai ko dai?" Cewar Maimoon fuskarta ɗauke da fara'a tana son tabbatar da zargin zuciyarta. Da sauri ya kalleta yana wani ƙara haɗe rai tamkar ba'a taɓa halittar dariya acikin fuskarsa ba. Murmushi Maimoon tayi wanda ya kusan narkar da zuciyar Rafeeq Gwarzo. Hannunta ta saka taja gefen kuncinsa fuskantar ɗauke da murmushi tana son jin amsa lokaci ɗaya kuma ta ɗage masa gira, da farin ciki a muryar ta take magana. "Kodai kana son Ayshaa ne Yaya Rafeeq? Naga duk lokacin da kuka haɗu sai ka samu abunda ka kushe a tattare da ita. Kasanfa Yaya a wani ɓangaren ana fara soyayya da tsana da hantara kafin ta rikiɗe zuwa wata irin soyayya mai ban mamaki da burgewa, irin wannan soyayyar Yaya Rafeeq tana burgeni sosai, saboda na sha karanta irinta a novels ɗin Hausa da na Turanci. Kasan taya soyayyar mu nida Wahaab ta fa?" Saurin katseta ya yi tare da fisge hannunsa daga cikin nata, lokaci ɗaya ya kwantar da kansa cikin seat yana sauke wani irin numfashi mai matukar zafi. Haka kuma numfashinsa yaji yana wani irin sexing, gabaki ɗaya hirarta zafi take ƙara masa, wato ita bama soyayyarsa akanta take ganowa ba, wasu daban itace a ranta. Ganin haka yasa hankalin Maimoon ɗin ya ɗan tashi, hannunta duka biyu ta ɗora akan kirjinsa dake wani irin dokawa ta shiga dannawa tana faɗin. "Innalillahi Yaya breath! breath please." Haka take ta maimata masa kirjinta yana bugawa tana tsoran kar wani abun ya sameshi. Lumshe ido ya yi a hankali har na kusan minti biyu sannan ya samu numfashinsa ya dawo normal ya buɗe fararen idanunsa masu cike da kaunarta da suka fara canja kala suna kuma ƙanƙancewa yake faɗin. "Daga zuwa na babu wani gaisuwa kin fara min zancen da ban tambaye ki ba. Ya kike ya test ɗin? kun gama ne?" Sai da ta ɗan turo baki tana haɗe rai kafin tai magana. "Mun gama koda ka kirani muna class muna yi." Ta faɗa tana jan dogayen pingers ɗin ta. Satar kallonta yayi ta yadda ko ita ba zata gane yana kallanta ba. "Yaushe zaki koma Kano? ba yau bako?" Ta girgiza kai tana faɗin. "Eh ba yau ba Yaya saboda akwai abinda zan ƙarasa zuwa anjima, sai dai zuwa gobe idan Allah ya kaimu." Ɗan shiru ya yi yana faɗin. "Okay zan jiraki zuwa goben sai mu wuce, yanzu zanje na kama hotel Dan ko breakfast ban yi ba yunwa nake ji." Ya faɗa yana kallonta da idanuwanshi da suke ɗauke da wasu sinadarai da kowace mace zata so ganin hubby ɗinta dashi. Wani abu taji yana tsaya mata arai, wani haushi ne ya kamata, akan me Yaya Rafeeq zai jirata har zuwa gobe? Yanzu ya zata yi da Abdul-Wahaab wanda sun riga sun gama tsara cewa gobe zasu tafi tare? yanzu ma haka yana Kaduna gobe zai zo ya ɗauke ta, me zata faɗa masa? Idan kuma ta faɗa masa cewa Rafeeq Gwarzo ne yazo ya ɗauke ta Allah kaɗai yasan irin rikicin da zata ɓallo. Idan kuma ta faɗawa Yaya Rafeeq cewa zata koma tare da Wahaab tasan halin zuciyarsa kuma ciwonsa ma na iya tashi akan hakan saboda abu kaɗan zai ɓata masa rai ciwonsa ya tashi, shi yasa duk familyn Gwarzo ke lallaɓasa, babu wanda baya lallaɓashi kan lalurarsa. "Nima yunwa nake ji Yaya." Ya taɓe baki yana faɗin. "Muje ki rakani na kama ɗaki daga nan sai nayi mana ordern abincin da zamuci." Yai maganar yana ɗagowa daga seat da ya jingina bayansa. "Okay tom ka jirani naje na yiwa Ayshaa sallama sai na nazo mu tafi." Bai ce komai ba amma yanayin fuskarsa ya sake canzawa ta fice daga motar tana murmushi ƙasa-ƙasa dan tasan sunan Ayshaa da ta kira ne ya canza shi. Baki Ayshaa ta buɗe tana kallon Maimoon Gwarzo tana ganin yadda take sakewa Rafeeq Gwarzo jiki tamkar abun ya yi yawa. Aysha ta zauna bakin bed tana kallon Maimoon ɗin da ta ɗauki handbag ɗinta tana cewa. "Wai da gaske binsa zaki yi har hotel? Haba Maimoon ke bakya jin wani iri a ce kinje hotel? Rafeeq bafa muharamminki bane kamar su Yaya Shaheed ya kamata ki dinga tunawa da wannan." Da wani irin mamaki cikin fuskar Maimoon take kallon Ayshaa ɗin tamkar bata fahimci me take faɗa ba. Ɗan murmushi Maimoon ɗin tayi tana faɗin. "Har yau da sauranki baki gama sanin waye Yaya Rafeeq Gwarzo a wajena ba, da gaske babu abunda zai faru ko ɗaki ɗaya zan iya kwana tare dashi saboda Yayana ne babu abunda zai faru da mu na rashin da cewa. Ke baki san har wanka ya yi min lokacin da ina ƙarama ba Ayshaa? So ki daina yi masa irin wannan fassarar dan Allah bana jin daɗi, sannan yana da tsantseni shigewa mace ba ɗabi'arsa ba ce ba." Daga haka Maimoon ɗin ta fice daga room ɗin ba tare da ta yiwa Ayshaa sallama ba. Baki a sake Ayshaa take kallon Maimoon ɗin har ta fice. Kai tsaye mota ta buɗe ta shiga zuciyarta na ɗan yi mata zafi saboda maganganun Ayshaa akan wannan fitar da zata yi da Rafeeq mutumin da har a jikinsa zata iya yin bacci ba tare da fargabar zai cutar da ita ko kanshi ba. Duk da yaga a yanayin da ta dawo hakan baisa ya tambayeta dalilin sauyawar fuskarta ba yaja mota suka tafi. Cikin gari suka shiga ya kama hotel anan ya yi musu order breakfast, tare sukaci abincin anan kuma ta ɗakko masa hirar Haneefa wacce ta kirata tace sun shigo Kano amma bata gari kuma ni nasan ba saboda kawo lefe na Haneefa ta wanko ƙafa tazo gidan ba, Yaya Rafeeq saboda kai tazo." Cikin rashin damuwa yana sipping tea ɗinsa yake magana. "Oh ai nima saboda ita na bar Kano nazo nan." Dariya Maimoon tayi wacce tayi mata matuqar kyau da yasa Rafeeq ɗauke kai tana buɗe hannuwa take faɗin. "Toh saboda me Yaya?" Ya yatsina fuska yana faɗin. "Tana sakani ciwon kai ne bata gajia da surutu, komai nata bata yinsa da aji ina son mace mai class." Maimoon ta juya ido tana faɗin. "Saboda kai kasan kana da class ba? Aini da Haneefa ta daina kulaka kana wani yarfa ta. Hmmm Yaya Rafeeq zanso naga matar aurenka wallahi dan nasan akwai kallo, za a ga iyayi. Zai buɗe baki yayi magana wayarta ta fara ringing, Abdul-wahab ne mai kiran ta manta ya kirata bata kira ba tun kafin su fito daga class. Wani zufa ta shiga haɗawa na rashin dalili tana jin yadda zuciyarta ke wani irin bugawa saboda rashin kyautawa da tayi. Rafeeq kuwa kallanta kawai yake yana ganin yadda take faman kallon screen ɗin wayar, ganin ta kasa ɗagawa yasa shi jan dogon hancinsa yana faɗin. "Wayake kiranki?" Cike da shagwaɓa tana turo baki tana haɗe girarta take cewa. "Wahaab ne." Nan da nan Rafeeq ya haɗe rai. "Toh me yasa bazaki ɗaga ba?" Maimoon ta ɗago tana kallansa sukai ido hudu, saurin janye nata tayi tana sake shagwaɓa fuska da wata irin murya take cewa "Laifi nayi masa kuma bansan me zance ba yanzun." Wayar ta katse aka sake kira. Rafeeq ya kasa cewa komai saboda takaicinsu, rai a haɗe yace. "Ki ɗaga wayar nan karar ta dameni kuma kisa a hands-free." Zaro masa dararan idanunta tayi masu kama da farin kindirmo wanda baƙar kwayar dake tsakiya wacce ta sake ƙawata idanuwanta suka ƙara ƙawata muhibbatar, ganin yadda yake wani haɗe rai ne yasa ta sunkuyar da kanta tana faɗin. "Yaya sirrin mu nida mijina zaka ji? Ni dai a'a uhm." Ta ƙarasa maganar cike da shagwaɓa har tana jujjuya kai side by side. A wani irin haukace ya kalleta jin ta ambaci Wahaab a matsayin mijinta, wani irin mugun kishi ya taso masa cike da tsawa yake cewa. "Ki ɗaga kona fasa wayar." Kamar zatai kuka dan ba ta gama shirya amsa tambatoyin da Wahaab ɗin zai mata ba, cike da rigima a muryarta take amsa masa bayan ta sanya hands-free ɗin. "Na'am... A'a Honey lokacin fa muna test..." Daga can Wahaab yake faɗin. "Amma da kuka fito me yasa baki kirani ba? Kinsan yadda hankali na ya tashi kuwa?" Kamar yana gabanta haka take buɗe idanuwa tana sake shagwaɓewa abin da yake ƙara hautsina Rafeeq kenan da yake ta faman danne zuciyarsa dan kar yaje ya yi a binda bai kamata ba. "Kayi hakuri abubuwa ne suka hau kaina na manta." Wahaab dake tuƙi yace. "Tun yanzu abubuwa sun fara yi miki yawa ina ga kuma an fara hidimar biki sweetie? kice wayar ma bazamu samu damar yin ta ba ko?" Murmushi ta saki wanda yasa Rafeeq saurin miƙewa tsaye, gurin ya bari dan idan yaci gaba da zama yana jin muryar ƙaton can zuciyarsa zata iya bugawa. Gurin motarsa ya nufa yana zuwa buɗewa yai ya zauna ba tare da ya rufe murfin ba, kansa ya ɗora a jikin sitiyari yana rintsa ido. "Anya ban yi wauta ba na ƙin sanarwa Maimoon halin da nake ciki a kanta ba?" Ya tambayi zuciyarsa dake yi masa wani zafi da raɗaɗi. Shin me yasa yake jin nauyin sanar da ita kaunar da yake mata? Duk lokacin da yazo gaya mata sai yaga kamar zai shiga haƙƙinta tunda tana da zaɓin ranta ya kuma san bashi bane, sosai Rafeeq ɗin yake jin rashin dacewar hanata san abinda take so. Ya shiga
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book