Showing 24001 words to 27000 words out of 34129 words

Chapter 9 - RAFEEQ COMPLETE HAUSA NOVEL

asmy   

08 Oct 2024

11281

titi na ɗauki microphone ina baiwa mutane labari ko? ai yin hakan da zanyi shine karshen surutu." Moobarak zai yi magana Rafeeq ya nuna masa kofa yana faɗin. "Ka fita... ka fita karka sakamin ciwon kai da yamman nan." Fita kawai Moobarak yayi yana rufo masa ƙofar. Hannyensa ya shiga kallo yana sakin murmushin da bai da alaka da farin ciki ko kaɗan, gashi a gabanta ya kasa bayyana abinda ke cikin zuciyarsa, bai san meyasa ganinta ke karya masa zuciya ba. Bai san meyasa ko ya buɗe baki da nufin yayi mata maganar ba sai yaji tayi masa wani irin kwarjini ba. Dariya yayi idan da wani ne ya faɗa masa Maimoon Gwarzo nayi masa kwarjini bazai yadda ba. A haka Zeeeee ta gama ganin lefen da murmushi a fuskarta take kallon Maimoon ɗin wacce tana fitowa wajen Rafeeq ɗakin ta shigo kai tsaye. "Allah ya sanya alkairi sis ya nuna mana lokaci lafiya." Da wide smile akan fuskar Maimoon take faɗawa Zeeeee ɗin ta gode, ta lura da yadda Zeeeee ɗin takeda saurin sabo da mutane, kuma a ɗan zaman da tayi na mintuna a tsakanin su ta lura Zeeeee ɗin bata da wata matsala, amman bata san meyasa wani ɓangaren na zuciyarta take jin sam batayi mata ba, haka kuma da gaske bata son Rafeeq Gwarzo ya aureta har aranta tafi hango soyayyarsa da Haneefa fiye da Zainab ɗin. Anan Zainab ɗin ta faɗa mata tana son ta shiga toilet. Batareda tunanin komai ba suka koma ɗakin Maimoon ta nuna mata ƙofar toilet ɗin, sai da Zainab ɗin ta shiga tayi tunanin kawo mata ruwan sha ganin tun da ta shigo basu bata koda ruwan sha ba ne bayan kuma wannan ba halayyar familyn Gwarzo bane na rashin daraja baki. Fita tayi dan kawo mata ruwan, koda ta fito ganin Maimoon bata cikin ɗakin yasa da sauri ta buɗe handbag ɗin ta, sannan zuciyarta ta riga ta faɗa mata nan ne ɗakin Maimoon ɗin ganin pictures ɗin ta manne a bangon ɗakin. Ƴar ƙaramar Camera ta fitar tana juyata a hannunta wannan shine plan ɗin ta na farko akan alaƙar dake tsakanin Rafeeq da Maimoon. A gaggauce take duba ko wace kusurwa ta cikin room ɗin wanda ta tabbata duk inda ta sakata zata riƙa ɗaukar mata record ɗin komai, Idan tunaninta yazo a lissafi yanzu baifi sauran sati biyu ba bikin Maimoon Gwarzo, ta wajen ac taje ta makala na'urar da sauri ta sauko jin ana ƙoƙarin buɗe ɗakin yasa ta zauna gefen bed gabanta na mugun faduwa. Da murmushi Maimoon ta aje mata ruwan sha da kuma Cup cake mai chocolate. Ruwan kawai Zainab tasha tace mata ta gode ta miƙe tsaye ta ɗauki handbag ɗinta, har ɓangaren Aunty Maimoon ta rakata tayi mata sai anjima anan kuma Zainab ta karbi lambar Maimoon ɗin tace mata ta turo mata da anko idan sun fitar. Tun lokacin da Aunty ta faɗawa Yakumbo Zainab budurwar Rafeeq ce komai dake cikin kan Haneefa ya kwance. Yakumbo taɓe baki tayi tana faɗin. "Oh matan yanzu sam babu kunya a tare da su, to yanzu meye na wani biyo shi har gidan? kunya tamkar Aunty zata nutse da sauri ta faɗawa Yakumbo ai ba wurinsa tazo ba, ana faɗar haka Haneefa ta shige toilet bata sake fitowa ba har sukabar ɗakin. Suna fitowa cikin compound Zainab ta kira wayar Rafeeq, yana ɗagawa ta faɗa masa gata ta fito, murya can ƙasa ya faɗa mata yana zuwa. Ba'a jima ba suka hango Rafeeq ɗin yana tahowa inda Zainab tayi parking motarta har lokacin suna tsaye da Maimoon, daga Zainab har Maimoon kallonsa suke har ya qaraso wajensu, batareda ya kalli Maimoon ba ya buɗewa Zeeeee ɓangaren driver, ɗan sanyi taji aranta ganin yadda ya girmamata a gaban Maimoon Gwarzo. Tana kallonsa take faɗin. "Da yamma ka shigo muyi magana." Ɗaga mata kai yayi ta kalli Maimoon tana yi mata godiya. Murmushi kurum Maimoon ɗin tayi mata dukansu suna a tsaye har motarta ta fita daga gidan. Juyawa Rafeeq yayi ya nufi ɓangarensu batareda ya kalli Maimoon ba. Shi kuwa har addu'a ya rinqayi Allah yasa ta biyoshi sai dai har yayi nisa baiji ta biyo shi ɗin ba tamkar yadda yake tsammani. Batayi mamakin ganin Haneefa a ɗakin ta ba sai dai yadda taga idanunta sunyi ja alamar tayi kuka yasa ta karaso da tashin hankali a muryarta take faɗin. "Hanee meya faru? keda waye?" Cikin rawar murya Haneefa ke faɗin. "Ki faɗa min gaskiya Maimoon da gaske Zainab budurwar Rafeeq ce?" Ɗagawa Haneefa kai kurum tayi alamar ehhhh. Wani irin kuka mai ciwo Haneefa ta fashe dashi tana jin yadda wutar kishi ke rura cikin zuciyarta, Maimoon kam bata da zabi illah na jawo ƴar uwartata jikinta bata san kalmomin da zatayi amfani dasu wajen rarrashinta ba. "Nima a haka na tarar dasu tare Hanee, kuma wallahi nima ba son Zainab ɗin nan nake ba, Amman na kula daga Aunty har Yaya Shaheed duka suna son Zainab ɗin tareda Yaya Rafeeq. Ni dai bana sonta ganin farko bata yi min ba ko kaɗan dan ba kalarsa ba ce, duk da har yanzu na kasa yadda dashi ɗin yana sonta kin san halinsa wani irin bahagon mutum ne. Ki cigaba kawai da lallaɓashi kina haɗashi da Allah wata kila hankalinsa ya dawo kanki nima ban san ya zanyi da Yaya Rafeeq ba Haneefa idan nace miki halinsa baya damuna nayi maki karya. Zan tayaki neman soyayyarsa." Dakyar ta samu ta lallaɓa Haneefa ɗin. Da magrib tana zaune a ɗakin ta kan sallaya tana azkar taji shigowar sako wayarta, tana dubawa taga Abdul-wahaab ne. Da sauri ta shiga dubawa dan ba ƙaramin kewarsa tayi ba. "Ki fito gani cikin compound." Wani irin sanyi taji har acikin ranta, a parlor suka haɗu da Aunty wacce ke kai da kawo daga kitchen zuwa parlor dan har lokacin daddy bai shigo ba, ta faɗa mata Abdul-wahaab ne yazo zataje wajan shi, Aunty tace ta gaishe shi. Farin yadi ne ajikiinsa fari sol wanda baida zane ko kaɗan, kansa babu hula tun kafin ta isa wajensa taji ƙamshin Collections ɗinsa na cika mata hanci. Da murmushi a fuskarta ta gaishesa tana kallon yanayinsa, ya amsa batareda ya kalleta ba, tasan har yanzu fushi yake da ita. Cikin sanyin murya take faɗa masa su qarasa parlon baki, ya girgiza kai yana kallon agogon dake kwance acikin damtsen hannunsa yake faɗin. "Nan ma is okay ba jimawa zanyi ba wucewa zanyi." Yadda yayi maganar sai taji duk babu daɗi da alamar har lokacin ransa a ɓace yake. Ta shagwaɓe fuska cike da rigima take faɗin. "Kawai kace baka da lokaci na shine kawai, gashi nan tun kafin ayi auren ka fara yi min wulakanci, ka fara nuna min halinku na maza." Ta karasa maganar da rikici a muryarta. Runtse ido yayi yana jin kalamanta na taɓa sa, ya buɗe ido yana kallon kyakkyawar fuskarta. "Kin san kinyi min laifi ko? meyasa Maimoon?" Ya faɗa da damuwa a saman fuskarshi. Ta girgiza kai tana faɗin. "Motar haya na shigo ba tare muka zo Kano ba." Yanayin yadda take maganar ya gano gaskiya take faɗa masa. "Muje daga ciki muyi magana kafafuna sun fara yin sanyi kasan kuma bana iya jure tsayuwa.
Bai yi musu ba suka jera suka nufi entrance ɗin shiga gidan. Suna tareda Abdul-wahaab sako ya shigo wayarta kuma saqon daga Rageeq ne. "Ki haɗo min coffee, idan kinzo ki ajemin a parlor karki shigo min ɗaki." Murmushi ta tsinci kanta da yi, saqo itama ta turawa Haneefa akan ta haɗawa Yaya Rafeeq coffee kuma kar ta saka sugar da yawa dan tasan baya shiri da zaki. Kiranta tayi tace ta duba wayarta ta turo mata saƙo yanzu dan batason tayi maganar Rafeeq ɗin a gaban Abdul-wahaab dan bata son ƙara ɓata ransa. Tamkar a mafarki ta shiga duba saqon Maimoon ɗin. Kan gado take a kwance amma bata san lokacin da ta sauko da kafafunta kasa ba, wani iri farin ciki ta tsinci kanta aciki ba tareda dogon tunani ba kai tsaye kitchen ta nufa cikin mintinan da basu gaza goma ba ta haɗa masa coffee ɗin, doguwar riga ce ajikinta da ɗan ƙaramin mayafin da tayi rolling kanta dashi. Babu kowa a parlorn nasu sai karar Ac. Kai tsaye stairs ta nufa zuwa ɗakunan baccinsu. Kai tsaye ɗakin Rafeeq ɗin ta nufa, aje tray ɗin hannunta tayi ta tura ƙofar, jin ƙarar buɗe ƙofa yasa ya ɗago yana kallon ƙofar duk a tunaninsa Shaheed ne. Tun da ya dawo daga sallar magrib yake kwance a ɗakin, ido biyu yayi da Haneefa dake yi masa wani irin murmushi lokaci ɗaya gabansa ya faɗi aransa yake faɗin Moon ta raina masa wayo. Wato yasa ta kawo masa abu Shine zata bawa wata aikin saboda shi bai isa da ita ba ko? lallai ta raina shi da yawa, wai a hakan ma bai fallasa mata sirrin zuciyarsa ba yasan kila da rainin da zata yi masa ya yi yawa. Haneefa kuwa tunda ta kalleshi taji gabaki ɗaya tana neman rasa nutsuwarta, kirjinta ya shiga bugawa wata irin soyayyarsa tana sake mannewa a cikin ranta. Addu'a ta farayi Allah ubangiji ya bata Rafeeq koda kuwa baya santa ita zata iya zama dashi a duk yadda yake. Laptop ɗinsa ya sake janyowa yana cewa. "Ita wacce nasa aikin tafi karfin tayi min sai ta saki? Ko ban isa da ita ba?" Yai maganar da murya marar sauti wacce ke nuni da ɓacin ran abinda Maimoon tayi masa. Haneefa ta kalleshi karo na biyu da dara-daran idanunta bakinta yana ɗan rawa take cewa. "Ba haka bane Yaya Rafeeq, bako tayi shine dalilin da yasa tace na kawo maka." A firgice ya tashi zaune yana kallon Haneefa zuciyarsa na bugawa yake cewa. "Waye bakon?" Tayi mamakin yadda taji muryarsa a kaurare, tsawa ya daka mata yana sake tambayarta. "Bakya ji ne?" Cikin firgici tace. "Wanda zata aura." Kamar zai fashe saboda bakin ciki ya buga mata wata tsawar. "Get out." Haneefa ta fara murza idanuwa zata saki kuka ya kalleta ganin bata tafi ba, ganin yanayinta yasa shi tunowa da Yakumbo yasan idan ya bari ta fita a haka yanzu zata zo ta sauke masa kwandon rashin mutunci, duk da zuciyarsa na wajan Maimoon da Abdul-Wahaab hakan bai hanashi controlling nutsuwarsa ba yace. "Ku me yasa idan kuna tare da wasu bakwa bawae mutanen da suke tare daku muhimmanci? Ke a ganinki abinda tayi min ta kyauta? Ta nunawa wani banza can cewa ni ban isa da ita ba ko? Yayi kyau tafi sai da safe." Haneefa ta buɗe baki zatai magana taga ya sakko daga bed ɗin ya shige toilet da alama baya san wani surutu. Babu yadda zatayi dole ta juya tana jin kamar laifin nata ne ita kadai tunda itace ta kawo coffee ɗin......



ƳAN TAGWAYE BIYAR 2023

ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.

IYALINA (A'ILATY)
RAFEEQ
MUNƊO
ZAMANIN MU AYAU
FATHIYYA.

DOMIN SIYAR GUDA BIYAR N1500.

DOMIN SIYAR DAYA N400.


Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis

Ga MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪

Tura ta Nita
Da sunan

Asma'u Buhari Aliyu
08086207764

SAI KI/KA IS TURA SHAIDAR BIYA TA DAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.

+234 808 620 7764
07065283730
+234 705 124 4211
+234 704 040 2435


#ASMY B ALIYU
#HAJJA CE
#Rafeeq gwarzo
#Abdul-wahaab
#Haneefa
#Zeee
#maimoon gwarzo
[5/4, 9:00 PM] Asmy B Aliyu😘: *RAFEEQ*
*PAID BOOK #400*

NA

*_ASMY B ALIYU_*
DA
*_HAJJA CE_*

TEAM TAGWAYE.....


13...


Sai da ya tabbatar da ta fita sannan ya buɗe ƙofar ya fito yana jin wani irin ɓacin rai. Da gaske Maimoon tafi bawa Wahaab muhimmanci akansa, yanzu kenan haka zai zauna ya zuba ido yanaji yana gani ta auri wani ba shi ba? Maimoon ba Alkhairi bace a gareshi? Rintsa ido yayi yana fatan cireta daga ransa ko zai samu sassaucin kishin da yakeji yana shirin kasheshi. Turo baki tayi tana maƙe kafaɗa ɗaya, murmushi yake yana sake hango lokacin da za a ce ta zama mallakinsa gaba ɗaya, ya ɗan shafi kanshi yana kallanta da idanunsa da suke cike da tsantsar bukatarta yace. "Na ƙagu ranar ɗaurin auran nan tazo nifa, wannan shagwaɓar ina jin haushin barinta babu lallashi na musamman." Buɗe idanuwa tayi cike da mamakin kalamansa, ganin yana ɗage mata gira yasa ta saurin kauda fuska da rigima a muryarta take faɗin. "Nifa bana shagwaɓa sai kace wata baby girl." Wahaab ya sake narkewa da salon yadda take masa, gyara zama yayi yana ciro wayarsa ya hau yi mata video yana cewa. "Bari nayi miki video saboda nasan idan na koma dole zanyi missing shagwaɓar nan." Da saurin ta cusa fuskarta cikin kujera tana sake buga ƙafa tare da cewa ita dai gaskiya ya dena. "Zan so ace wannan rigimar akan bed ɗin mu ake yinta." Ya faɗa yana mikewa tsaye. "Yar rikici na zan wuce tunda nazo da wayo da wayo an lallasheni." Maimoon ta mike tsaye kamar zatai kuka. "Ni bana so ka tafi." Ware ido ya yi, "Toh ya kike so ayi tunda naga yau da gaske rigima za'ai min?" Hannu tasa tare da holding ɗinsu a kirjinta tace. "Ka kwana anan please." Wata iri dariya ce ta kwacewa Abdul-Wahaab ya yi ta yin ta sosai dan ba ƙaramin dariya maganar ta bashi ba. "Hayati a nan zan kwana? So kike a kaini ana yaɗawa a social media. Ko kuma so kike wannan ɗan uwan naku ya sake tsanata?" Duk da tasan da Rafeeq yake amman sai da tace. "Ba wanda zai yi magana, Daddy kuwa murna zai taya ni." Tafiya ya farayi yana zura wayarsa cikin aljihu yake cewa. "Zan kwana wata rana, yanzu dai ki bari mu zama mata da miji komai ma zai zo mana da sauki." Har wajan mota ta rakashi ya buɗe passinger seat, wata leda ya ɗakko yar madaidaiciya ya mika mata tayi masa godiya cike da soyayyarsa. Har ya fice daga gidan tana tsaye sai da mai gadi ya rufe gate sannan ta juya zuwa cikin gidan.sai lokacin ta tuna da Aunty ta faɗa mata ya shigo su gaisa da Yakumbo. Tamkar zatayi kuka haka take ji dan tasan mitar Yakumbo sai tafi kwana biyu tana korafi, duk da a wani ɓangaren taji daɗin yadda ta manta ɗin, dan tasan yakumbo zuba zatayi kamar mai ruɓaɓɓan baki a gaban Abdul-Wahaab ɗin har ta kai ga sakata jin kunyar wata maganar da zata fito daga bakinta. Addu'a take Allah yasa babu Yakumbo a parlon kuma Allah yasa babu wanda ya faɗa mata zuwan Abdul-Wahaab ɗin. Kai tsaye kitchen ta nufa ta tarar da ƴan aiki nata gyaran wuri, ta kalli ɗaya daga cikin ƴan aikin nasu mai suna Suwaiba ta tambayeta Aunty fa? ta faɗa mata tana sashenta. Sanin Aunty a irin wannan yanayin da sun gama aiki wanka take shiga shi yasa bata nufi sashen nata ba, kai tsaye room ɗinta ta nufa, tana tura kofar sukayi ido biyu da Haneefa wacce ke zaune kan soofa gabaki ɗaya yanayinta ya canja. Maimoon ta ƙarasa ciki ta aje ledar da Abdul-Wahaab ya taho mata dashi, sannan ta cire hijab ɗin jikinta tana kallon Haneefa wacce da alamar tunani takeyi dan sai da ta ɗaga murya ta kira sunanta sannan ta ɗago a zabure. Haneefa ta kalli Maimoon, ƴar ajiyar zuciya Haneefa ta sauketa yamutse fuska tana faɗin. "Irin wannan kiran Maimoon Gwarzo ai sai ki fasawa mutum dodon kunne." Maimoon ta girgiza kai tana zama gefen bed take faɗin. "Kin kai masa coffee ɗin kuwa? Dan kin san bayason jira indai Yaya Rafeeq ne." Haneefa ta ɗaga kai da wani yanayi a tattare da muryarta take faɗin. "Na kai masa sai dai dakyar ma idan zaisha, ni kam ban san me zanyi Yaya Rafeeq ya soni ba wallahi. Maimoon ban san me zanyi ba wanda zai burgesa sam." Ta qarasa maganar a hankali cike da karaya. "Hakuri zaki kara yi Haneefa ki ɗauka har aranki cewa haka halinsa yake, da kin saba ba zaki kara wahala ba." Wani murmushi mai ciwo Haneefa tayi tana hango maza masu wani irin class dake binta suna rokon ta basu soyayyarta amman a makance take kallon su,
RAFEEQ Gwarzo ne kurum takeyiwa wani irin so da take tunanin ko kanta bata yiwa shi."Baya kulani fa taya zan iya jure ɗauke kan da yake min? Anya ba wata ce ta mallake mana zuciya da gangar jikinsa ba?" Maimoon dariya tayi har tana faɗawa kan bed. "Shi yasa nace miki idan kika jurewa halin Yaya Rafeeq tabbas zaki samu soyayyarsa, kawai dai dan ba tare kuke ba kullum shi yasa kike jin bazaki iya ba Hanee but, koma wacece ta shiga zuciyarsa sai ta fito tunda kina son shi. Muci gaba da addu'a Allah ya tabbatar mana da alkairi." Haneefa ta jinjina kai tana sake hasko yanayin yadda suka kare dashi. Washe gari drivern Daddy ya maida Yakumbo garin Gwarzo, acewarta nan da sati ɗaya zata dawo sai dai tabar Haneefa wacce itama already sun samu hutun makaranta. Shirye-shiryen biki akeyi gadan-gadan tun lokacin da Maimoon ta aiko Haneefa wurinsa ya rage mu'amala da Maimoon ɗin ya fara jan baya-baya da dukan lamurranta, a ganinshi hakan shine zai samu sauqin abunda yakeji aransa game da ita, ko cikin gidan ya rage zama. Iyakarsa da safe ya shiga ya gaishe da Daddy idan sun haɗu da Aunty ya gaisheta idan kuma basu haɗu ba shikenan bai takurawa kansa akan lallai-lallai sai ya gaisheta dan tana matar Daddy. Itama Maimoon hidima tayi mata yawa gabaki ɗaya ta rage zuwa dakinsa ta dubashi bare tasan halin da yake ciki. Sai dai kuma a rana tana yi masa kira fiye da goma ta tambayi lafiyarsa ko tace. "Yaya duk yau ban ganka ba. Me zakaci na saka a kawo maka?" Irin wannan tambayoyin take yi masa a waɗansu lokutta. Shi kuwa wataran da gangan yake ganin kiranta ya share, sai dai yasan ko ya shareta nacinta bazai barsa ya zauna lafiya ba dan zatai ta damunsa da waya har sai ya ɗaga taji muryarsa. Shi kuma avoiding ɗinta da yake ya zata shine zai sa ya daina jinta aransa musamman da yasan ta kusa zama matar

14, February 2025
Hasina Ayuba Adam

I like to read the book

14, February 2025
Hasina Ayuba Adam

I like to read the book

14, February 2025
Hasina Ayuba Adam

I like to read the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login