Showing 27001 words to 30000 words out of 34129 words
wani. Sai dai a kwanakin nan ya kula ba ƙaramar azaba yake sha ba na rashinta a kusa dashi. Gabaki ɗaya duniyar ta hargitse masa baya jin daɗinta kwata-kwata.
Zeeee Liman ta kirashi a waya tace masa Maimoon zata bashi anko ɗinta ya kawo mata dan Allah. Bai ce komai ba ya sauke wayar, tasan haushi yaji, murmushi kurum tayi a lokacin saboda tasan yana cikin tashin hankali. Ana sauran sati ɗaya biki Rafeeq yayi wani irin fita daga hayacinsa, ya sake zama shiru babu inda yake fita yana ɗaki yayi karatu ya shiga media yaga abubuwa duk dan ya samu sassaucin zuciyarsa. Da sassafe sai gashi a ɓangaren daddy lokacin daddy yana zaune a parlornsa yana duba littafin addu'oi ya daga kai yana kallon Rafeeq ɗin kafin ya amsa masa sallamar da ya yi masa, sai da gaban daddy ya faɗi a lokacin ganin irin ramar da Rafeeq ɗin yayi lokaci ɗaya ta ban mamaki. Har kusa da Daddy ya isa ya zauna akan rug gamida tankwashe kafafunsa waje ɗaya. Zuba masa ido daddy yayi batareda ya ce masa komai ba shima, addu'a kurum daddy keyi Allah yasa Rafeeq ɗin ya faɗa masa damuwarsa. Sun kai minti biyu a haka babu wanda yace komai, shi kuma zurciyarsa wani irin bugawa take yana jin yadda yake kokuwa da numfashinsa. Kusan sau uku yana buɗe baki dan ya yiwa daddy magana amman sai ya kasa. muryar Daddyn yaji akansa ya kira sunan sa a hankali. Dagowa yayi yana kallon daddy kafin ya ɗauke idonsa daga cikin na daddy da sauri dan baya iya jure kallon kwayar idon daddy da fuskarsa ma baki ɗayan ta dan wani irin kwarjini daddyn keyi masa. "Akwai abunda kake bukata ne Rafeeq?" Ɗan sosa kai yayi cike da karfin hali yake faɗin. "Daman daddy maganar business ɗinkane dake ƙasar Chaina ko zaka yi min izini na koma companyn ka dake can sai na ci gaba da kulawa dashi." Tun da ya fara magana daddy ke kallonsa, ɗan murmushi daddy yayi yana faɗin ya tashi ya tafi zai yi tunani akai. Duk da RAFEEQ ɗin so yayi a ce a kwanaki biyu ma masu zuwa ya tattara ya tafi, haka yabi umarnin Daddy ya tashi ya bar wajan yana neman hanyar da zai zillewa ganin auran Maimoon da Wahaab Bammali. Ana sauran kwana biyar a sakata a lalle Moobarak Gwarzo ya iso Nigeria. Lokacin Rafeeq na a gida wanda sai yaga dama yake zuwa office, shi ya kira a waya yaje ya ɗakko shi daga air port. "Ka rame da gaske Yaya wata cuta ke damunka haka ne? Amma shine daddy da Yaya Shaheed basu kai ka asibiti aka duba lafiyarka ba? muje gida na dubaka tunda na dawo." Yayi maganar sounding so very serious a muryarsa, daman kuma shi kaɗai ne ya karanci fannin likitanci. Jin surutun Moobarak Gwarzo na saka kanshi na ɗaukar wani irin dumi yasa ya kalli Moobarak ɗin yana faɗin. "Zoka karbi tukin nan ka daina yi min magana haka." Murmushi Moobarak ɗin yayi ya karbi car key ɗin hannun Rafeeq yana jinjina miskilanci irin na Yayan nasu wato Rafeeq Gwarzo. Akai-akai Moobarak na driver yana kallon gefen Rafeeq ɗin wanda ya kwantar da kansa cikin seat ya lumshe ido har suka isa gida. Jin Moobarak yana biyo shi a baya ba tare da ya nufi cikin gidan ba dan gaishe da su Yakumbo yasa ya ɗan juya da mamaki yana kallon Moobarak ɗin. "Nasan meye aranka Yaya, Zan fara duba lafiyarka tukuna sai naje mugaisa." Wannan qaron da mamaki cikin fuskar Rafeeq ɗin yake faɗin. "Wai meke damunka haka? waya faɗa maka bani da lafiya ne? Toh lafiya ta kalau Moobarak karka sakamin wani ciwon kai kaje kayi abinda yake gabaka." Bai san Moobarak da gaske yake ba sai da yaga ya bishi har ɗakin baccinsa. "Ka zauna zamuyi magana Yaya kafin nasan meke damunka." Moobarak Gwarzo ya faɗa da wani irin tone a muryarsa wanda zaka ɗauka shine babba ba Rafeeq ba. "Da gaske akwai abinda ke damunka kana avoiding ɗinsa ne tamkar baka son kowa ya sani, but jikin ka fuskarka komai naka ya nuna haka Yaya tell me meke faruwa da zuciyarka?" Girgiza kai Rafeeq Gwarzo yayi yana kallon Moobarak ɗin, duk cikin su yasan shine mai naci da bin diddigi, zai yi wuya ya barshi muddin baiji damuwarsa ba. Saɓanin Maimoon da Shaheed idan yace baya so zasu barshi ne bazasu takura masa ba. "Kaje kayi wanka ka huta da daddare zamuyi magana." Yadda Moobarak ya tsareshi da ido ne yasa ya wani yamutse fuska ganin kallon da yake masa ya tabbatar alkawari yake so yayi masa. Rafeeq ya mike tsaye da car key a hannunsa yana faɗin. "Fita zanyi idan kana bukatar wani abu ka kirani." Ya faɗa yana nufar kofa. Hakan yasa Moobarak ɗin binsa da ido, yasan yayi haka ne dan ya zille masa. Sai da ya isa kofar gidansu sannan ya ɗaga waya ya kirata, cikin mintunan da basu wuce goma ba sai gashi ta fito, wannan karon babu hijab ajikinta mayafi ne ta yafa sai dai tayi masa kyau sosai cikin shigar atamfar da tayi. Fitowa yayi daga motar ta jingina bayanta da motar tana kallon yadda ya zama wani iri lokaci ɗaya, addu'a take akan Allah yasa shawarar da zata kawo tayi mata amfani itama. Murmushi mai ciwo tayi tana kallonsa tana qara jin wani sabon sonsa fiye da ko yaushe, tana hango irin ramar da yayi duk kuwa akan Maimoon Gwarzo ne da kwata-kwata bata ma san yanayi ba. Ɗan zaman da tayi da Maimoon cikin hidimar bikin nan ta kula da tana matuqar son Abdul-Wahaab wanda zai yi wuya tabarshi. "Maimoon ce koh?" Ta faɗa cikin qaryewar murya tana kallon Rafeeq ɗin yana kallonta da idanunsa da suka faɗa lokaci ɗaya. Ɗan guntun murmushi ya yi. "Na yiwa daddy magana Allah yasa ya amince, Zainab wannan qaron zanyi nisa da gida wanda zai yi wuya na waiwayo, bani da tabbas akan ko zan warke akan zazzafar soyayyar da nake yiwa Moon. Zee akwai ciwo sosai akan abinda kake so amma ka kasa furtawa, kila yin shirun shine mafi alkairi a gareni, but is so painful Zee." Hankali a tashe cikin rawar baki Zeeee tayi saurin katseshi ta hanyar cewa. "Mai kake tunanin zakayi Rafeeq? karka fara gwada min wannan wasan dan Allah. Zaka sameta cikin sauqi ni nayi maka wannan alkawarin. Amman ban sani ba ko zaka bi shawarar da zan baka. Da sauri Rafeeq ke faɗin. "Kwana biyar ya rage ta zama tashi taya zan sameta Zainab?" Ya faɗa da rawar murya. Murmushi samun nasara tayi kafin ta tattaro dukkanin jarumtarta tana faɗin. "Hanya ɗaya ce idan zaka yi." Cikin zumudin son jin hanyar yake cewa. "Faɗa min Zainab kai tsaye dan Allah." With full confidence take cewa. "Ta hanyar yi mata fyade..!" Ai gabaki ɗaya ji yayi kalmar fyaɗe na zauna masa ta wurare daban-daban acikin zuciyarsa. Kallon tabin hankali yake yiwa Zainab ɗin a wannan lokacin, zuciyarsa na zafi yake cewa. "Ƙanwar tawa zan yiwa wannan mummunan aikin? Tabbas ban taɓa tunanin baki da hankali ba sai yau. Toh wallahi da na yi wannan abun ƙara na jure rasata akan na jefa rayuwarta cikin mummunan haɗarin da zai yi wuya ta warke. Tsarkakakkiyar soyayya nake yiwa Moon ba wai wani son zuciya ba. Zainab zan koma gida." Ya faɗa yana kama murfin motar ya buɗe ya shiga ya yiwa motar key. Zainab tana kallonsa yabar gate ɗin gidansu haushi da takaici suka isheta lokaci ɗaya. Tabbas dole ma ta samu taje gidansu Beeba tun da gashi nan bai qarbi shawarar taba sai kallon marar hankali yake yi mata. Jiki sanyaye ta koma gida a gefe tana tunanin ƙaryar da zata yiwa Ammi dan ta samu fita taje gidan Beeba su sake wani plan ɗin....
ƳAN TAGWAYE BIYAR 2023
ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.
IYALINA (A'ILATY)
RAFEEQ
MUNƊO
ZAMANIN MU AYAU
FATHIYYA.
DOMIN SIYAR GUDA BIYAR N1500.
DOMIN SIYAR DAYA N400.
Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
Ga MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪
Tura ta Nita
Da sunan
Asma'u Buhari Aliyu
08086207764
SAI KI/KA IS TURA SHAIDAR BIYA TA DAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.
+234 808 620 7764
07065283730
+234 705 124 4211
+234 704 040 2435
#ASMY B ALIYU
#HAJJA CE
#Rafeeq
[5/4, 9:00 PM] Asmy B Aliyu😘: *RAFEEQ*
*PAID BOOK#400*
LAST FREE PAGES#
NA
*_ASMY B ALIYU_*
DA
*_HAJJA CE_*
15....
Zaune yake akan rug gafda ƙafafun Daddy ya saukar da kansa ƙasa, tun kafin ma yaji me daddy zai faɗa masa yaji zuciyarsa na wani irin rawa, da gaske yasan ko menene zai fito daga bakin Daddyn babu alkhairi acikinsa, hakan yasa duk yadda yaso samun natsuwa kasawa yayi hatta da yatsan kafarsa zufa yakeyi duk kuwa da sanyi ac dake jikin kowace kussurwa ta cikin parlorn. Rafeeq zufa kawai yake haɗawa tun kafin ma yaji me Daddy ya kirawo shi dan ya faɗa masa. "Rafeeq meke damunka haka ne?" Daddy yayi maganar cike da lallashi da kalamai irin na kowanne uba a wajan ɗansa." Dagowa yayi yana kallon Daddyn da idanunsa da suka juye saboda tsabar damuwa. "Soyayyar Maimoon Gwarzo ce Daddy." Rafeeq ɗin ya faɗa acan qasan ransa. Kusan sau uku yana buɗe baki dan ya faɗawa daddy gaskiyar abinda yake damunsa amman ga mamakinsa kalma ko guda ɗaya ta kasa fitowa daga bakinsa. Shiru daddy yayi yana nazarin yaron nasa. Kusan minti biyar babu wanda ya kuma cewa komai a tsakaninsu kafin yaji Daddy na faɗin. "Idan bazaka iya gaya min ba shikenan, sannan kuma Yakumbo tayi maganar a haɗa aurenka da Haneefa sai dai ban sani ba ko a ɓangarenka kana da wacce kakeso, zan baka ɗan lokaci saboda hakkinka ne, na baka nan da sati ɗaya kaje kayi tunanin magana ta, idan kuma kana da wacce kakeso kayi min magana nan da wata biyu masu zuwa zan haɗe aurenka dana ɗan uwanka Shaheed, idan yaso bayan auren sai ka fara shirye-shiryen komawa ƙasar Chaina tareda iyalinka saboda bana so kayi nisa ba tare da muharrama ba, nima haka nafi samun natsuwa Rafeeq idan har kana da iyali a tare dakai." Habawa tunda Daddy ya fara magana yaji dai maganar aurensa da Haneefa, daga nan kuma ya daina fahimtar komai da daddy ke fada masa. Sai da Daddyn ya kira sunan sa da ɗan karfi, a firgice ya ɗaga ido yana kallon Daddy zuciyarsa na sake hargitsewa. "Zaka iya tafiya." Daddy ya faɗa yana kallon Rafeeq ɗin da yanayin da yake hangowa acikin fuskarsa wanda ko kaɗan baya masa daɗi. Tunda ya fito daga parlorn daddy ya kasa fahimtar komai da kowa a cikin duniyar nan. Kai tsaye wajen motarsa ya nufa ga mamakinsa Zeeeee ya samu a wajen tana tsaye tana jiransa. Tunda tasan Rafeeq har kawo yanzu bata taɓa ganinsa a haka ba sai yanzu, wani abu take hangowa a cikin idanunsa wanda bata taɓa ganin kalarsa ba. Matsawa tayi daga jikin motar tana jin yadda kafafunta ke wani irin rawa, gabaki ɗaya tsoro lamarin Rafeeq ya bata, da gaske tsoron lamarinsa takeyi a wannan lokacin. Yau bata fito da motar gidansu ba, da sauri ta nufi gate tamkar zata faɗi ƙasa. Addu'a takeyi Allah ya bata abun hawa da wuri dan bata son ta wuce wannan damar da take da ita. Wani mai napep ne ya sauke wasu a kofar gidan Alhaji Mustapha Gwarzo, suna fita ta shige napep ɗin da sauri tana faɗa masa dan Allah yabi bayan wannan farar motar saboda tasan Rafeeq ba gudu yake da mota ba zai yi wuya ya ɓace musu.
Fuskar Rafeeq Gwarzo ke yi mata yawo a cikin idanunta tana jin yadda kirijinta ke wani irin bugawa, komai zai faru a yau bazata bari wannan damar ya wuce ta ba. (TAHIR GUEST PLACE) nan motar Rafeeq ɗin ta shiga, da sauri Zee Liman ta ciro 1k daga cikin handbag ɗinta ta miqawa ɗan sahun dake faɗa mata ta tsaya ta karɓi canjinta amma ko saurarensa bata tsaya yi ba.
Ko wane taku ɗaya da take yana tafiya ne tareda bugun zuciyarta, wannan qaron bata san ya Rafeeq Gwarzo zai qarbi zancenta ba. Sai da ya nufi entrance ɗin shiga wajen sannan tabi bayansa wanda akwai tazara a tsakaninsu. Rafeeq kuwa har ajikiinsa yana jin yadda ake binsa a baya, amman bai da natsuwar tsayawa yaga ko waye saboda bashi da case da mai bibiyar tashi. Key ya ciro ya shiga buɗe hotel room ɗin yana jin yadda jikinsa ke wani irin kaɗawa. Shiga yayi hannu yasa zai rufe ƙofar kawai Zeee ta riqe ƙofar itama tana kallonsa, girgiza masa kai ta shiga yi, mamaki yake taya akayi tazo nan wajan? "Zainab.!" Ya faɗa cike da gajiya a muryarsa. "Na sani Rafeeq baka so na biyo ka ba but magana zamuyi." Ta faɗa tana kallonsa. Sakar mata ƙofar yayi a hankali ko takalmin ƙafarsa bai cire ba, anan ya zube kan Rug bai san kalar tashin hankali irin wannan ba sai yanzu da zai rasa Maimoon Gwarzo dukanta. Wata dariya ce ta kwace masa wacce bata da alaƙa da farin ciki ko kaɗan. Girgiza kai ya shiga yi tamkar wanda ya sami tabin hankali. Wai kamar shi Daddy aure zai yi masa kuma batareda ma Maimoon Gwarzo da soyayyarta take niyar haukatarwa, da wata daban zai masa auran, meyasa Daddy zai masa hakan?" Ya faɗa yana yarfe hannayensa. Dogayen yatsun hannunsa ya shiga ja. "Banda wurin kowa a zuciyata Daddy karka ɗora min nauyin da bazan iya yi maka alkawarin zan cikashi da farin ciki ba. Da gaske Maimoon Gwarzo ce kawai a zuciyata." Maganganun Rafeeq ɗin ke zauna mata a cikin zuciyarta da wani irin ciwo marar misiltuwa, tana jin yadda hawayen idonta suka kasa tsayawa. Wace irin marar sa'a ce ita? Ganin kamar Rafeeq ɗin baya cikin hankalinsa yasa ta isa gareshi, zube gwiwonta kasa tayi tana ganin yadda hawaye ke gudu akan fuskarsa tamkar an kunna ruwan famfo kuma wai duk adalilin soyayyar da yake yiwa Maimoon Gwarzo yake kukan, ita kam tayama za'a yi taso Maimoon Gwarzo a rayuwarta? yarinyar da ta hanata jin daɗin rayuwarta, yarinyar da ta shigo kai tsaye cikin rayuwarta ba tare da ta sani ba kuma tana juyata yadda taga dama. Wata irin runguma ya yiwa Zeeeee liman a lokacin abunda bai taɓa faruwa ba a tsakanin su. Wani irin shock Zainab ɗin keji a ko'ina na cikin jikinta, tana jin wani irin mugun feeling na soyayyar Rafeeq Gwarzon tana taɓa ko'ina dake cikin jikinta tana jin wani qalar dumi da jikinsa ya ɗauka. Murya a shake jikinsa na mugun rawa yake faɗin. "Zainab bazan iya rasata ba da gaske bazan iya rasata ba, zan iya mutuwa akan hakan." A hankalin take shafa sumar kansa tana faman rintsa ido, wani irin tausayinsu yana qara cika mata zuciya. Sunfi minti biyar a haka tana riqe dashi jin ya dawo dai-dai yasa ta raba jikinta da nashi a hankali. Tana kallon yadda fuskarsa ta zama lokaci ɗaya. "Kana ji kana gani zaka rasata Rafeeq tunda ga shawara na kawo maka cikin sauqi ta hanyar da zaka sameta babu mai tuhumarka amma kaƙi. Babu wanda zai san wannan sirrin fa dagani sai kai Rafeeq bana san wani abun ya sameke dan ba zan yafewa kaina na. Ta faɗa tana riqe da hannunsa. Gabanta na mugun faɗuwa saboda wannan karon idan bai yadda ba batasan me zai faru ba. Tana so ya amince da hakan, dan ta hakan ne zata samu ta ruguza duk wata alaƙa dake tsakaninsa da Maimoon Gwarzo ta hanyar mallakarsa ita kaɗai. Bata da damuwa koda duka familyn Gwarzo zasu san wannan sirrin, koda duka zasu juya masa baya tayi alƙawarin tana tare dashi a duk inda rayuwa zata kaisu. Tasan koda can Rafeeq ba wani damuwa yayi da arzikin mahaifin su Maimoon ba, saboda shima yana da nashi arzikin, yana da qaddarorin da mahaifinsa ya bar masa a matsayin gadonsa, tasan rayuwa bazata yi musu wahala ba koda basa cikin zuri'ar Gwarzo. "Zaka sameta Rafeeq idan kayi yadda na faɗa maka tun farko. Kasan Allah da tuni yanzu ta zama taka kai kaɗai. sauran kwana biyu a ɗaura mata aure zata zama mallakin wani bakai ba saboda zurfin ciki irin naka." Runtse ido yayi wani kishi na cika masa zuciya, yana da kishi sosai har addu'a yake Allah ya rage masa wannan kishin nasa saboda daga ranar da wani ya kai hannu jikin Moon ɗinsa yasan mutuwa kawai zai yi. "Tayaya zan sameta Zainab? kina ganin yadda security suke cike da gidan mu? tsoro nakeji da gaske Zeee kawai mu canza wata hanyar banda wannan." Da wata irin damuwa take masa magana. "Nasani zan taimakeka Rafeeq saboda jin daɗin ka kawai, zaka sameta ka bani dama kawai." Kallon cikin idanunta yake yana son ya yadda da abunda take faɗa masa, da ya bari ya rasata gara ya nemeta ta wannan haramtacciyar hanyar. Miqewa yayi har lokacin zuciyarsa na rawa yake faɗin. "Ki tafi Zainab zanzo gidanku da daddare muyi magana." Wani daɗi ne ya cika zuciyar Zeee ɗin, lokaci ɗaya ta miqe tsaye. Ɗan murmushi tayi tana kallonsa ta saukar da murya tana faɗin. "Da gaske zaka zo na jiraka?" Ɗaga mata kai kurum yayi batareda ya kalleta ba. Acan ƙasan ranta wani mummunan kishi ne ke danne mata zuciya, wai itace zata baiwa Rafeeq Gwarzo damar yayi tarayya da wata ba ita ba, wannan ranar kawai Zainab tasan komai zai zame mata dai-dai. Wata zuciyar ta faɗa mata hakan. Har bakin ƙofa ya rakata. "Ka kula da kanka dan Allah." Ta faɗa cikin rawar murya dan har lokacin bai gama dawowa dai-dai ba. murmushi kurum yayi harta fice. Anan bakin ƙofa ya zube yana jin yadda kirjinsa ke wani irin harbawa, idan kuma ya tuna da maganganun Daddy sai yaji komai ya kwace masa yana neman rasa kwarin gwiwarsa. Shikam da ya auri Haneefa a wannan yanayin ai ƙara ya auri Zeeee liman yayi maneji da ita a haka, da dai ya auri ƴar wajen Yakumbo. Yana gama parking motarsa acikin Gwarzo mantion ya fitar da wayarsa ya kirata, Haneefa ce ta miqo
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book