Showing 6001 words to 9000 words out of 34129 words

Chapter 3 - RAFEEQ COMPLETE HAUSA NOVEL

asmy   

08 Oct 2024

11288

tausayawa, yana jin mugun nauyinta akan yace ba itace a cikin wannan zuciyar ba. Maimoon gwarzo ta riga ta gama cika xuciyarsa da soyayyar ta"Kayi shiru baby kodai baka sona ne?" Ya kalleta da mayun idanunsa masu kama da madara farare tas dasu yake cewa. "Tun farkon haɗuwar mu dake nace ki daina yi min maganar aure saboda bana so kiyi tunanin zan aureki, Zee bana san yaudara a cikin tsari na shi yasa nake ce miki idan har kin samu wani wanda hankalinki ya kwanta dashi toh ki amince masa kiyi auranki. Zuciyata tana cikin wani irin yanayi wanda na rasa ta yadda zan ɓullo masa. Kiyi min addu'a kawai Allah ya cika min buri na." Hawaye suka fara zirarowa daga cikin idanunta, yana kallanta ta gefen ido haka kuma yana jin kukan nata har cikin jininsa saboda shi a rayuwarsa baya kaunar yaga ana kuka nan da nan yake jin tashin hankali. "Kana tunanin idanuwana zasu iya ganin wani bayan kai? Rafeeq idan wata ce a cikin zuciyarka ka gaya min hankalina zai fi kwanciya, idan kuma wani hali ne nawa da baka so ka sanar dani sai na gyara, wallahi zan gyara Rafeeq indai akan farin cikinka ne."wani irin karayewa xuciyar Rafeeq tayi lokaci ɗaya ya Xaiyi da Zainab idan ya fallasa mata sirrin dake cikin xuciyarsa xai iya karya xuciyarta.tun farko bai so wannan kusancin nasu ba,bai so tafiar su ta kawo nan ba duk laifin shaheed gwarzo ne da ya ta cusa masa ita alhalin ba itace aransa ba.haka kuma baya so ya cigaba da boye mata ,idan aka cigaba da tafia a haka xatayi wani tunani daban ne akan wanda ke ransa.
Damke hannunsa yayi yana kallonta da dukkan idanunsa,wani irin bugawa xuciyar zeey keyi a wannan lokacin tana jin bugawar da zuciyarta take har cikin tafin ƙafarta.A hankalin ya kamo hannunta abunda bai tabayi ba tsawon rayuwarsa riqa hannunta ,runtse idonta tayi xuciyarta na bugawa fisge hannunta tayi lokaci ɗaya ta fashe masa da kuka tana girgixa kai take faɗin"dan Allah karkace banice a ranka ba Rafeeq' xan iya mutuwa ka taimakeni karka fadamin dan Allah.
Ta fada tana kara sakin kukan da Rafeeq gwarzo keji har cikin xuciya da ruhi,Dukansu Abu ɗaya suke nema Amman kowane nasa ya banbanta da na dan uwansa,Zainab liman tana sonsa wanda ya lura a shirye take da ta sadaukar da farin cikinta saboda shi,shi kuma maimoon gwarzo ce acikin tashi xuciya shekaru goma sha takwas a baya ,wanda xuciya da gangar jiki basu taba gajia ba.banbancin shine yana son maimoon gwarzo Amman bata ma san yanayi ba,yasan xainab na tsananin sonsa da kaunarsa,sai dai shi kuma ba itace a tashi xuciyar ba dukan su suna cikin matsala.Hannu yasa yana squeezing sumar kansa gefe ɗaya kukan Zainab na hargitsa masa lissafi..Zainab goge hawayenki muyi magana,ya faɗa sounding so very cool cikin muryarsa, tissue ta fiddo acikin handbag nata tana goge hawayen idonta still wasu na kara fitowa...


#Hajja ce
#Asmy b Aliyu
#Rafeeq Gwarzo
#Zeey leeman
#Team tagwaye Novels
[5/4, 9:00 PM] Asmy B Aliyu😘: *RAFEEQ*

*PAID BOOK....*#400
NA
*_ASMY B ALIYU_*
DA
*_HAJJA CE_*


4....

Kallon Rafeeq Gwarzo takeyi da dukkan natsuwarta, haka zuciyarta na wani irin harbawa tamkar zata fice daga cikin kirjinta dan jikinta yana bata ko menene zai fito daga cikin bakin Rafeeq Gwarzo toh ba alkhairi bane ba a gareta. Cikin husky voice ɗinsa dake sake narkar da duk wata jijiya a jikinta taji yana faɗin. "Tun farko ban so wannan tafiyar tamu ta kawo har nan ba Zainab, shi yasa kika ga ina ta baya-baya da lamarin mu. Nasan kuma idan har muka cigaba da tafiya a haka zan ta cutar dake ne alhalin kuma ba kece a cikin zuciyata ba. Kin san yadda qaddara take Zainab, ina jinki tamkar mun fito ciki ɗaya dake ne dan ban taɓa shawarar yin aure dake ba. Maimoon Gwarzo ce kawai a cikin zuciyata, wacce na fara sonta ne tun kafin tasan kanta, kuma nima na fara sonta ne tun kafin nasan menene ma soyayya. Na ɗauka soyayyar jini da kuma shakuwar dake tsakanin mu da ita shi nake yi mata, sai da shekaru suka fara ja na fahimci cewar soyayya ce irin ta son kasancewa matsayin inuwa ɗaya. Please Zainab dan Allah karki ɗauki wannan abun dana gaya miki da zafi, nasan Allah zai kawo maki wanda yafini acikin rayuwarki. But ina kaunar Maimoon kauna irin wacce baki da zuciya ba zasu iya bayyanawa ba, babban abin damuwar ma shine ni bata san ma inayi ba, gashi an saka ranar aurenta da wani bani ba, kuma saka wannan ranar auren nata dai-dai yake da tsayawar duk wani numfashina." Hawaye na zuba acikin fuskar Zainab wanda bata damu da ta gogesu ba, domin babu kalmar da bata fito daga bakin Rafeeq Gwarzo wanda bai taɓa mata zuciyarta ba. 'Shin da gaske ba soyayyar aure Rafeeq Gwarzo keyi mata ba tun tsayin lokacin da suke tare? Toh ita wace irin marar mai sa'a ce a cikin duniyar nan? Ya rabbi kasa mafarki nakeyi ba wai gaske ne ba.' Zuciyarta ta ayyana but still hawayen idonta sun kasa tsayawa, ga wani irin mugun sanyi mai kamar alamun zazzaɓi dataji yana rufeta wanda har haƙoranta suna karo da junansu. Ganin yanayinta ya tsorata Rafeeq, nan take ya ruɗe har bai san lokacin da ya ɗora hannayensa ya dafa kafaɗarta yana cewa. "Ki natsu dan Allah Zainab." Cikin wata irin murya da bai taɓa jinta ba tace. "Ka kaini gida Rafeeq... Please ka kaini gidan mu dan Allah." Ta faɗa da wani yanayi a cikin muryarta. Dakyar ta iya takawa zuwa wajen motarsa duk da yaso ya taimaketa ya riqata amman taki amince masa yayi hakan. Tunda suka ɗauki hanya babu wanda yayi magana kowanne da abinda yake sakawa a cikin zuciyarshi. Yadda Zee ɗin take ta share hawaye ne ya sanya Rafeeq kai hannu jikin radion motar ya kunna dala pm ya bari inda yaji sun saka wakar uwar gida ran gida. Suna ƙarasawa yai parking a ƙofar gidan su, bece komai ba dan yaga kamar bata san yana yi mata magana yanzu. Hannu tasa ta buɗe motar, a fusace ta kalleshi ganin yaki magana ta kura masa ido da wani yanayi a saman fuskarta. "Nagode Rafeeq, sai dai ina so kasan da cewa. Alaƙata da kai ba irin wacce za'a ce an rabu bace, zan kasance tare da kai har zuwa lokacin da naga ka samu abinda kake so. Ina fatan zaka kai min gaisuwa a wajan Maimoon?" Jinjina mata kai kawai ya yi dan ba zai iya cewa da ita komai ba dan yana jin duk wani furuci dake fitowa daga bakinta na dauriya ne kawai. Da gudu yaga ta shiga gidan ya samu kanshi da ɗora goshinsa jikin sityarin motar yana faman furta kalmar Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun dan baya kaunar yaga ya zama silar rashin farin cikin kowane ɗan Adam. Jikinsa babu wani kuzari haka ya tayar da motar, kai tsaye gida ya wuce yana mamakin yadda suka rabu da Zainab. Tunda ya doshi wajan parking yake jin wani irin faduwar gaba yana jin kamar ana matse masa zuciya waje ɗaya, yaci gaba da hailala a cikin ransa. Yana gama parking ɗin ya fito, har zai wuce apartment ɗinsu yaji yana san zuwa cikin gidan. Yana zuwa ya murɗa handle na entrance ɗin babban parlorn idanunsa suka sauka akan Maimoon, tana tsaye kusa da Aunty tana kara wasu weeding gown a jikinta. Da wani irin farin ciki ta kalli hanyar ganin shi yasa ta saurin sakin murmushi tana faɗin. "Yaya Rafeeq tayani zaɓe da white ɗin nan da gold wacce zan ɗauka?" Kallanta yake da dukan nutsuwarsa, duk da ba wai sanyawa tayi a jikinta ba sosai yaga tayi masa kyau. Rigar ya karɓa yana sake karawa a jikinta, cike da murmushi Aunty tace. "Ayya wallahi daman Abdul-wahaab ɗaukarki ya yi kukaje wajan rigunan ki ka zabi wacce kike so, dan dai kince bazaki bishi bane ba." Cak Rafeeq ya tsaya jin cewa rigunan Wahaab ne ya aiko ta ɗauka, cikin wani yanayi yayi cilli da rigar gefe kafin ya juya zai fita. "Yaya karka tafi please ka tsaya ka zabar min." Maimoon tayi maganar cikin shagwaɓa wacce tasa Rafeeq jin wani irin yanayi a jikinsa. Cikin yatsina fuska ya juyo tare da kallan kayan yace. "Gaskiya basu min ba shi yasa ban ɗauka miki ba." Zaro ido sukayi Auntyn tace. "Haba Yaya Rafeeq aikuwa bridals gowns ɗin nan sunyi mugun kyau, kuma masu tsada ne." Dawowa ya yi yana nuna rigunan cikin nuna fushi yake cewa. "Yanzu dan Allah wannan rigar zaki saka a gaban mutane kiyi yawo a ciki? Na tabbar a wajan Party ɗin harda kattan maza zaku gayyato, dubi rigar fa kamar ta arna, gata nan irin ta turawa ce kirji a waje, shima wanda zai aurekin bashi da kishi da har zai kawo miki irin wannan rigunan yace kisa." Duka mamaki ya kusa kashe su, ya sake juyawa ya fice daga parlorn, cike da tashin hankali ya koma sashen su tare da yin wurgi da hular kansa. Lallai akwai babbar matsala, Maimoon shirye-shiryen bikin ta kawai takeyi hankali kwance, yayin da shi kuma yake ta faman dako na muguwar kaunarta. Taya zai bayyana mata sirrinsa? Kodai yaje ya sanar da Daddy ayi wacce za'a yi tunda shi na gida ne yasan dole a bashi auranta. Kansa yaji yana wani irin sarawa, ya shiga cire kayan jikinsa da suka fara jiƙewa da gumi, dole ya samarwa zuciyarsa mafita ta hanyar samun Maimoon tun kafin ya rasa ta duka. Bathroom ya shiga, jikinsa ya sakarwa ruwa yana jin zuciyarsa tana yi masa ciwo. Yana fitowa ya tarar da wayarsa tana ringing, a hankali ya kai hannunsa ya janyota yana dubawa. Zeee ce besan me yasa take kiransa ba bayan yanzu suka rabu, shi yanzu gaba ɗaya baya san duk wani abinda zai sashi yin magana ta fatar baki dan haka ya maida wayar kan mirror yaci gaba da goge jikinsa yana jin wani bakin ciki a ransa. Fridge ya nufa ya ɗakko bottle water mai sanyi, ji yake idan besha ba zuciyarsa zata iya konewa duk kuwa da yasan illar da shan ruwan sanyin zai janyo masa, idan har yasha asthma ɗinshi zata iya tashi kuma Daddy yaja masa kunne kamar yadda likitoci suka ce ya dena amfani da duk wani abu mai sanyi. Jikinsa yana wani irin rawa ya buɗe zai sha yaji an buɗe ƙofar, da sauri ya kalli hanyar, Shaheed ne suka haɗa ido ya bi shi da wani kallo yana cewa. "Kamaka nayi ko kuma me?" Cikin basarwa Rafeeq ya ƙarasa buɗe murfin ruwan yana cewa. "Bafa sha zanyi ba." Shaheed ya yi murmushi tare da cewa. "Bansan me yasa aka bar fridge ɗin nan a wajanka ba, kuma bansan me yasa ake kunna maka shi ba. Anyway Zeeee ce tace tana ta kiranka baka daga ba shine nace bari nazo naga ko lafiya?" Rafeeq ya furzar da iska daga bakinsa yana dafe goshi yake cewa. "Ina wanka naji ringing, yanzu na fito ban duba ba."ganin Shaheed ya Xauna a dakin nasa ya fiddo wayarsa yana dannawa yasa ya dora bottle water
Kan fridge ta gefen ido shaheed ya kalli Rafeeq da ganga ya Xauna cikin dakin yasan ruwan yake so yasha,komawa yayi kan bed yayi ya zauna ya jawo pillow ya dora kansa sama.ka Kirata dan Allah tanata damuna, Shaheed gwarzo ya faɗa yana kallon Rafeeq."idan na Kirata nace mata me?"yanxu fa na baro wajenta duk ba kai ka jamin wannan matsalar ba,Rafeeq ya faɗa da dan daga murya .hoton yarda Maimoon gwarzo ke farin ciki tana daga gown din Aurenta na dawo masa,da mamaki Shaheed ke faɗin."ban san me kake faɗa ba kayi min da Yaren da xan gane, Please ka fita dan Allah bana son ganin kowa kusa Dani."Rafeeq ya faɗa sounding so very harsh cikin muryarsa baki Shaheed gwarzo ya buɗe yana kallonta.bai taba ganin Rafeeq haka ba."Toh Meya hadasa da Zainab,batareda Shaheed yayi magana ba yabar masa dakin.pillow ya dannawa fuskarsa sai da yaji Asmath dinsa tana kokarin tashi sannan ya cire pillow gamida wurgi dashi gefe ta hakan ma,
Kasa fisgo numfashinsa ya kasayi,dakin yaji yana juya masa,inheler dinsa yake kokarin daukowa kan mirror ya kasa anan kasa ya xube yana jin numfashinsa na wani irin fisga,Turo kofar room din akayi Shaheed ne ya manta car key dinsa ya dawo ya dauka ganin Rafeeq cikin wannan halin yayi mugun daga hankalinsa da gudu ya nufesa yana kiran sunansa da karfi...da sauri Shaheed ya tallabo kansa ya saka inheler din cikin hancinsa, kaja numfashi Rafeeq sunfi minti goma a haka kafin numfashinsa ya dawo sai dai duk ya gama galabaita, Shaheed ya dafe kansa yana kallon rafeeq wanda ke kwance kan bed idonsa a rufe suke Amman ba barci yake ba,wai menene damuwarka dan Allah?"kashe kanka xakayi tunda muka dawo kaxama haka.idan baxaka iya faɗamin ba ka fadawa daddy ko maimoon,bance dole sai ka faɗamin damuwarka ba mr.Rafeeq gwarzo,
Abu dayane bazan iya dauka ba shine Rasaka,
Da haka Shaheed ya fice daga room din ransa a bace da alamar Rafeeq'
Ya bata masa rai,yana fita ya daga waya ya kira Zainab yana da tabbacin xaiji damuwar Rafeeq a wajenta,tana dagawa yake faɗin."dan Allah xan iya zuwa gidanku akwai maganar da xamuyi,da tashin hankali Zainab ke faɗin."meya faru?"wani abu ya samu Rafeeq ne.
Babu ko daya Zainab sai nazo da haka ya kashe wayar mota ya dauka zuwa gidansu Zainab liman dake unguwar....


#Hajja ce
#Asmy b Aliyu
#Rafeeq Gwarzo
#Zeey leeman
#maimoon Gwarzo
#Shaheed Gwarzo
[5/4, 9:00 PM] Asmy B Aliyu😘: *RAFEEQ....*
*PAID BOOK...* #400


_*ASMY B ALIYU*_
Da
_*HAJJA CE👈*_


5......

Unguwar sharaɗa dake ja'in can ya nufa. Tun kafin ya gama yin parking ya kirata yace gashi a bakin gate. Sanye cikin doguwar riga ta atamfa orange da ratsin coffee brown a jiki, ta yafa ɗan karamin vail wanda ya dace da shigar jikinta. A hankali ta isa inda yake tsaye jikin mota ya zuba hannayensa duka cikin aljihun gefe da gefe na rigar. "Shaheed Allah yasa dai lafiya dan gabaki ɗaya hankali na ya tashi." Kallanta ya yi yana tsuke baki, gyara tsayuwar yai tare da shafa kyakkyawan gemunsa da yake ta faman sheƙi. Sai da ya ja numfashi ya sauke kafin yace. "Ba gaisuwa?" Zee ta ɗan janyo murmushi wanda iyakarsa zaman leɓenta tace. "Sorry Shaheed ina yini..?" Amsa mata yai yana lasar lips ɗinshi da ya fara bushewa yake faɗin. "Ko ke fa, daman tambayarki nake so nayi, dan Allah Zee ki gaya min gaskiya meke damun Rafeeq? Yace min ɗazu kuka rabu but na ganshi cikin tsananin damuwa dan har asthma ɗinshi sai da ta tashi." Wani irin zaro ido Zee tayi tana dafe kirjinta da taji ya buga da wani irin mugun karfi. Cike da tashin hankali take kallan Shaheed tana faɗin. "Shi me yace maka?" Shaheed yai mata wani kallo yana cewa. "Da ya yi min bayani bazan zo wajan ki na tambayeki ba, just tell me Zee meke damun ɗan uwana?" Ruwan hawaye ne ya fara taruwa cikin idanunta, sai dai bata bari sun sakko ba gashi bata san a gane halin da zuciyar ta ke ciki. "Kinyi shiru Zee ko ba zaki gaya min ba?" Ta wani rintsa ido tana jin zuciyarta na bugawa, bazata iya cewa Rafeeq baya santa ba. Haka kuma ba zata iya tona asirin zuciyar Rafeeq ba tunda shi be bayyana ba, ita kawai ya sanarwa cewa yana son Maimoon. "Bansan menene damuwarsa ba, nima naga baya cikin walwala da jin daɗi lokacin da muna tare. Koda muka rabu ma yana cikin damuwa shi yasa na kirashi dan naji amma yaki ɗagawa shine dalilin kiran da kaga nayi maka ina tambayarka ko yana gida? Kace bari kaje ka duba." Shaheed ya shafa sumar kansa yake faɗin . "We have to figure out Zee, Ina tausayin Rafeeq abubuwa sun masa yawa, wallahi bana son kuma yazo ya dinga ganin ko dan iyayensa basa raye ne yasa duka waɗannan problem ɗin sukai masa yawa. Yana da heart problem ga ulcer sannan uwa uba asthma ɗin nan. Dan Allah Zee kiyi iya yinki wajan ganin kin cire masa tunani da kuma yawan shiga damuwa. Ya kamata ma ku fara maganar aure dashi, ko ke baki shirya ba?" Wani irin murmushi Zee ta saki wanda bayada alaka da farin ciki.tamka anyi mata dukan kawo wuƙa dan yadda zuciyarta takeyi kaɗai azaba ce. Taya zata sanar da Shaheed cewar ba ita Rafeeq yake so ba? Ya zata sanar dashi cewar ba ita Rafeeq yake so ya aura ba? Taya zata gaya masa cewar Maimoon ƙanwarsa, jininsa ita Rafeeq ke so yake kuma san ya aure ta? Yarinyar da kwarjininta kaɗai ya hanashi bayyana mata sirrin dake ransa. "Idan kina yin shiru Zee zuciyata babu abinda bata rayawa. Ki fito ki gaya min menene abinda yake faruwa? Dan naga alamar kinsan wani abu game dashi." Kallanshi tayi da sauri kuma ta janye ganin idanunsa na neman sanya ta fallasa abinda ba huruminta ba. "Sai dai idan kana ganin babu damuwa ka tafi dani wajansa ƙila ya iya gaya min." Wani irin buɗe idanu Shaheed yai yana faɗin. "Kai a'a Zee Daddy na nan, idan yaga kinje wajan Rafeeq har ya tabbatar da cewa ke budurwarsa ce zai iya fassaraki ko ya saki a wani matsayi marar daɗi. Kawai dai zanyi ƙoƙarin ganin kunyi waya dashi a yau. Sai ki bugi cikinsa da irin salonku na masoya." Ran Zee ya fara ɓaci da murya marar daɗi tace. "Mubar wannan maganar please." Ya jinjina kai tare da cewa. "Shikenan ni zan wuce." Ta ɗan matsa baya daga wajan motar tana cewa. "Agaida Maimoon." Yana murmushi jin an faɗi ƴar uwarsa yace zataji, ya shiga motar ya bar gurin. Juyawa itama tayi jiki babu kwari ta shiga gida. Tana shiga parlor ta tarar da Ammie ɗinsu ta fito daga ɗaki, harara ta zabga mata cikin ɓacin rai take cewa. "Kin fita wajan Rafeeq ɗin ne? Wai ni Zainab yaushe zaki yi hankali ne? Duk samarinki masu son auranki kinƙi basu fuska kin biyewa wancan yaron da ba shiryawa yayi ba ko? Toh bari kiji

14, February 2025
Hasina Ayuba Adam

I like to read the book

14, February 2025
Hasina Ayuba Adam

I like to read the book

14, February 2025
Hasina Ayuba Adam

I like to read the book

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login