Showing 9001 words to 12000 words out of 34129 words
na gaya miki, tun wuri ki rabu dashi ki kama dahir, ga Salis nan babu irin nacin da baya yi akan ki bashi dama kinƙi. Last warning Zainab, kodai kice Rafeeq ya turo manyansa, ko kuma ki fita daga cikin rayuwarsa bana san sakarci." Tana kaiwa nan tabar wajan, Zee ta lumshe ido tana jin wani mugun tashin hankali. Ɗaki ta shiga da gudu ta isa wajan madubi jikinta yana wani irin rawa, kallan fuskarta tayi hawayen da take ɓoyewa suka shiga zirarowa saman fuskarta, kanta ta shiga kaɗawa side by side a fili take faɗin. "Wane cikas gareni da ba zaka iya aure na ba Rafeeq? Me yasa dole zuciyar ka sai Maimoon wacce ba ta san ma kana yi mata soyayya ba? Ina sanka Rafeeq domin ka riga da ka zama zuciya ta (Albi), ka so ni please Rafeeq kar ka barni cikin tashin hankalin rayuwa." Kamar daga sama taji ana cewa. "San maso wani ƙoshin wahala, kina cikin gararin rayuwa Zeeee" Da sauri ta waigo tana zare idanunta da suka yi jawur saboda kuka, ganin Sofia Yayar ta yasa ta juyawa ta fara ninke veil ɗin da ta ciro a kafaɗarta. Itama Yaya Sofia cikin rashin damuwa da ƙin kulawar da Zee ta bata yasa taci gaba da cewa. "Shi so dama haka yake idan bakai dace ba kamar dai yadda baki dace ba Zainab. Kina san Rafeeq amma shi bake ce a cikin tsarin sa ba, sai kiyi haƙuri ki kuma yi addu'a Allah ya kawo miki nagari mai sanki." Zee ta juyo kallan Yaya Sofia tayi cikin zafin rai take faɗin. "Kina so kice shi ba alkairi na bane? Yaya Sofia idan ba zaki min addu'a Allah ya bani Rafeeq Gwarzo ba kawai kiyi shiru kici gaba da zubamin ido." Sofia ta nufi wardrobe tana cewa. "Allah ya kyauta." Daga haka taci gaba da abinda ya shigo da ita ɗakin, yayin da Zee ta koma kan gado tana ci gaba da hawaye. Sai wajan karfe takwas na dare sannan ya iya fitowa daga side ɗinsu. Sanye yake cikin jallabiya hannunsa riƙe da wayarsa ya nufi cikin gidan. Dai-dai inda zaka shiga entrance ɗin gidan cikin baranda yaji muryarta da alama waya take yi da Abdul-Wahaab, ji ya yi gabaki ɗaya zuciyarsa ta wani hargitse saboda babu abinda ya tsana a duniyar nan irin yaga Maimoon tana waya da Abdul-Wahaab, gaba ɗaya sai ya waniji duk ya ruɗe. Tafiya yaci gaba da yi har ya isa wajan ƙofar shiga, yana ƙoƙarin murɗa handle yaji tayi masa magana abinda bai zata ba. "Yaya Rafeeq." Cak ya tsaya kafin ya ƙarasa buɗewa ya shige ciki dan idan ya tsaya tabbas zai iya yi mata abinda batayi tsammani ba. Maimoon ta rintsa ido Yaya Rafeeq akwai wulakanci ta rasa me yasa har ita wani lokacin baya saurarawa a cikin izzarsa. Kai tsaye kitchen ya shiga ya ɗauki electric kettle, kayan dafa black tea ya zuba a ciki ya jona sannan ya janyo kwai guda biyu yasa cikin tukunya yana dafawa kafin ya koma parlor ya zauna. Yana canza Channel zuwa ta resetlling ta shigo parlorn murmushi ɗauke a saman fuskarta. Wajan da yaje ta nufa, gabaki ɗaya ƙamshin khumran jikinta ya kusa hargitse masa kai, yai saurin miƙewa ya nufi kitchen. Bayansa tabi cikin shagwaɓe fuska tana masa magana. "Haba Yaya wai me nayi maka ne? Gabaki ɗaya ka canza min Allah zan gayawa Daddy, Yaya ku nake gani naji daɗi a rayuwa ta amma kai sai wani shareni kakeyi kuma bansan menayi maka ba." Maimoon ta ƙarasa maganar cikin yanayi na son fashewa da kuka. Sai da ya kashe kettle ɗin sannan ya dawo kusa da ita ya juya mata bayansa tare da durƙusawa alamar ta hau. Zaro ido Maimoon tayi tana ja da baya cike da mamakinsa take faɗin. "Yaya me zanyi haka?" Ɗan murmushi ya saki wanda iyakarshi saman leɓensa, ba tare da ya kalleta ba yace. "Goyaki zanyi yadda zaki gane cewa bana wulakantaki." Ya miƙe tsaya tare da matsawa dab da ita har numfashinsu yana bugar musu fuskar juna, ta sake turo lips tana kuma haɗe rai. Kallanta yake yi da dukkan nutsuwarsa yana jin tamkar ya shigar da ita cikin kirjinsa sai dai basu saba irin wannan wasan ba. Yatsunsa biyu yasa tare da ɗago haɓarta sukai kallan cikin ido, ta sake turo baki cikin yanayin shagwaɓa da ta gama zame mata jiki. Yadda tayi ba ƙaramin sake tayarwa da Rafeeq hankali tayi ba, cikin sauri ya janye hannusa yana komawa ya buɗe tukunyar da yake dafa kwan yana faɗin. "Ban san me kike so a waje na ba Moon." Cikin kitchen ɗin ta sake binshi tana leƙa tukunyar da yake tsaye a wajan, yatsina fuska ta shiga yi tana taɓe baki take faɗin. "Yaya maimakon ka soya kawai sai ka wani dafa? Ni bana son dafaffan ƙwai, ko zanci sai dai gwaiduwa." Yana tsamewa yasa cikin ɗan bowl mai ɗauke da ruwan sanyi yake cewa. "Dama ni bake na dafawa ba." Maimoon ta ware idanu tana kallansa, a jikinsa yaji cewar shi take kallo dan haka ya ɗago a hankali ya zuba mata sexy idanunsa cikin nata da suke farare kal. Ganinta kawai cikin kitchen tare dashi yasa shi jin tamkar a cikin gidan auran su suke tare. Da sauri ya juya, kofi ya ɗaƙƙo yaje ya zuba tea ɗin ya suba zuma a ciki, bowl ɗin ƙwansa ya ɗauka ya nufi hanyar fita daga kitchen yana cewa ta taho masa da gishiri. Yana gaba tana bayansa ganin zai fita dan ta ɗauka a parlorn zai zauna tace. "Yaya Rafeeq." Maimakon ya amsa sai ya juya yana mika mata hannu alamar ta bashi robar gishirin. Bayanta ta mayar da hannunta tana sake kura masa ido. Tafiya yaci gaba da yi tana binsa har suka isa part ɗin su, gab da zai shiga nashi yace da ita. "Bani kije ki kwanta dare ya yi." Da wata murya tace "Magana fa zamu yi Yaya." Kamar yace ba zai yi ba sai kuma ya shiga ciki, akan soofa ta zauna tana janyo bowl ɗin kwan nashi ta fara ɓare masa. "Yaya magana zamu yi daku kai da Yaya Shaheed but kaine kawai nake samu free Ya Shaheed tunda kuka dawo ƙasar nan Allah ya zuba masa yawo.." Wayar sa ce ta shiga ruri Maimoon dake kusa da wayar tasa hannu ta janyota. 'My Zeeee Shine sunan da yake maƙale a wayar, haka kawai ta samu zuciyarta dajin babu daɗi kawai ta zubawa sunan ido. Tashi yayi yaje wajanta tare da karɓe wayarsa, ganin mai kiran yasa shi kallan Maimoon yana cewa. "Kije ki kwanta gobe sai muyi maganar idan Shaheed ɗin ya dawo." Jikinta na wani irin tsuma irin na takaicin nan taci gaba da ɓare masa, bata kalleshi ba tace. "Kayi wayarka ni ina ruwa na daku. Zan jira ka gama muyi maganar." Har wayar ta katse bai samu ya ɗaga ba, sake kira akai yaje ya karɓi bowl ɗin daga saman cinyarta yana cewa. "Kije kar Aunty taga bakya nan, idan na kammala uzuri na zanzo sai muyi maganar." Afusace ta miƙe ganin yadda yake ta wani korarta daga ɗakin. Zagaye shi tayi zata fice kawai taji ya riƙo mata hannunta, ta sake tsuke fuska tana san ƙwace hannunta ya wani janyota zuwa right side ɗinshi bayanta na jikin kirjinsa tana jin bugun numfashinsa a gefen wuyanta. Hakan yasa taji ta shiga cikin wani mugun yanayi, husky voice ɗinshi ta daki cikin kunnenta yana cewa. "Sorry." Yana kaiwa nan yaja hannunta ya zaunar da ita cikin soofa shi kuma ya daga kiran. "Hello." Zee ta lumshe ido lokacin da muryarsa ta ziyarci cikin kunnuwanta. "Ina Maimoon?" Yaji ta jeho masa wannan tambayar, inda Maimoon ɗin take ya kalla yaga tana ci gaba da ɓare masa ƙwan yace. "Lafiya lau." Zeee taji wani irin zafi a zuciyarta sai kace ba ita ta tambaya ba ya bata amsa. "Ance baka jin daɗi duk soyayyar Maimoon din ce?" Hannu yasa yana shafa kyakkyawar fuskarsa tare dajan dogon hancinsa da ya ƙarawa fuskar tashi mugun kyau yace da ita. "Yeah." Ya faɗa mata iya gaskiyarsa. Wani irin kishi ya tasowa Zee ta daure duk da yadda zuciyarta ke zafi tana faɗin........
#ASMY B ALIYU
#HAJJA CE👈
#Rafeeq Gwarzo
#Maimoon Gwarzo
#Zee Leeman
#HANNU BIYU-BIYU
[5/4, 9:00 PM] Asmy B Aliyu😘: *RAFEEQ*
*PAID BOOK #400*
TEAM TAGWAYE NOVEL'S.
Na
_*ASMY B ALIYU*_
Da
_*HAJJA CE*_
7.....
"Mubishi a hankali har Allah ya kawo mishi wacce yake so tunda suma sauran duk sune suka kawo masoyan su da kansu." Da wani kallo Yakumbo ke kallan Daddy, cikin ɓacin rai take faɗin. "Sai kai ta wani cewa abishi a hankali, jaririne shi?" Daddy ya sake murmusawa yana wani kwantar da kai yake faɗin. "Kinsan maraya dole sai an bishi a sannu ba kamar yadda zaka tanƙwara sauran ba." Baki sake Yakumbo ke kallanshi wani haushi yana cika ta "Rafeeq ɗin ne maraya? Waye zai kalli yaron can yace yayi rashin uwa bare kuma uba?" Daddy ganin kamar ba zata fahimce shi ba yasa shi cewa. "Shikenan sai a tambayeshi aji idan yana da wacce yake so, idan babu sai a duba masa." Yakumbo ta sake taɓe baki tana cewa. "Ai ni wannan yaron ma idan ya yi auran bansani ba koshi zai zama matar, gaba ɗaya sullutu ne ga shegen faɗin ran jaraba." Girgiza kai kawai Daddy yai cikin san kawar da zancen Rafeeq yace da ita. "Gobe iyayen Abdul-Wahaab zasu kawo kayan lefe already Auntyn su ta bada aikin snacks, juice kuma gasu can a store tace za'a soya kaji ne ko naman rago oho dai sai kuma abinci da za a yi, toh a ganinki sai kuma meye za'a ƙara? Ko kuma meye ba'a yi ba?" Ta wani haɗe rai "Yo sai da matarka ta gama tsara komai sannan za'a nemi shawarata? Ai ta riga ta gama komai sai dai tukuici kawai da zaka ajiye musu." Ran Daddy ya ɗan ɓaci sai dai ko a fuskarsa bai nuna ba ya riga yasan Yakumbo da san girma da yasan maganar da yai zata canza mata manufa ba zai yi ba."Shikenan za a ɗora, kamar naira nawa kenan?" Ya faɗa yana san bata damar da take buƙata. Sai da ta kawar da fuska sannan tace ta wani hura hanci kafin tace. "Ahhh iya ƙarfin ka, sai ka duba kaga yanayin su dangin yaro, idan masu kwari ne sai ka basu da daraja, idan kuma gasu nan ne dai to sai ka basu ashirin ma tayi." Daddy ya jinjina kai daga nan sukaci gaba da hirar yadda abubuwan zasu kasance. Rafeeq na fita daga parlorn yaga Haneefa tsaye da alama shi take jira ya fito, sau ɗaya ya kalleta ya ɗauke kai yana nufar sashen su. "Yaya Rafeeq baka ganni bane ba?" Cewar Haneefa tana turo baki kamar zatai masa kuka. "Hanee na ganki mana me ya faru?" Ta wani matso kusa dashi har suna jin kusancin juna, wasa ta shiga yi da ƙasan rigar ta bata iya ce masa komai ba saboda wani mugun kwarjini da yake yi mata. Ganin kamar bata da alamar magana yasa shi tafiyarsa, ta wani buga ƙafafuwanta tana turo baki cikin muryar shagwaɓa yaji tace. "Yaya Rafeeq Maimoon." Ko jiran ƙarshen maganar beyi ba ya juyo da wani yanayi a fuskarsa yaga tana shagwaɓe fuska. "Bata nan ba abokin hira please Yaya nazo muyi hirar da kai?" Dawowa yai har gabanta yana wani haɗe rai tare da kai fuskarsa wajan ta ta kamar zai kai mata sumba, a gigice ta wani rintsa ido tana damƙe hannuwanta wani fitsari na taruwa a cikin mararta wanda ƙiris ya rage ya zuba kawai taji yace. "Jeki ki kwanta kafin kisa Yakumbo tayi min wata fassara akan ki." Da sauri ta kalleshi tana sake kallan kyakkyawan lips ɗin shi. Kafin tayi magana taga ya juya ya nufi side ɗin
Su. Bubbuga ƙafa tayi tana yatsina fuska, juyawa tayi zata koma ciki taji muryar Yaya Shaheed yana mata magana. "Menene Hanee?" Ta sake yatsina fuska cikin shagwaɓa wace gabaki ɗaya Yakumbo ce ta maida ita dan bata san ɓacin ran Haneefa ko kaɗan, sosai ta shagwaɓa ta. Cikin turo baki take faɗin. "Yaya Shaheed ba Ya Rafeeq ne ba ni bansan me yasa yake da shariya ba, ko magana fa sai yaga dama yake min." Dariya Shaheed yai shidai Rafeeq duk wanda zai zo gidan nan sai anyi korafi akan shariyarsa, sai dai fa mutum ne shi mai matukar mutunci da girmama mutane, uwa uba abun hannunsa baya rufe masa ido yana da kyauta sosai irin wacce ake so. "Toh Hanee sai ki hakura ai kinsan halin Yayan naku." Sake turo baki tayi. "Maimoon bata nan gidan ya sake yi min girma Yaya Shaheed." Bayan kansa ya shafa da murmushi a fuskarsa yake faɗin. "Ki kunna kallo mana sai ya ɗebe miki kewa, nima dan dai free call zanyi yau da na shigo na tayaki hirar." Haneefa ta rausayar da kai tana kallon wayar hannun Shaheed, kamar zatai magana sai kuma ta juya tare da shigewa masaukin su. Yakumbo ce ta shigo ɗakin, kallan Haneefa tayi wacce ke faman haɗe rai tana wani rufe ido Yakumbo tace. "Ke kuma meye hakan? Waye ya taɓaki?" Hafeefa ta shiga juya ido tana turo baki take faɗin. "Yaya Rafeeq ne." Ran Yakumbo ya ɓaci jin tace Rafeeq ne yasa ranta ɓaci. Da kulawa ta isa wajan Haneefa, kafaɗarta ta riƙo cike da soyayya take tambayarta. "Meyayi miki dan nasan da wannan shiru-shirun nashi yake yiwa mutane rashin mutuncin da yake so. Sanar min yanzu naje na sameshi har ɗaki." Da wani kallo Haneefa ke bin Yakumbo ta sake turo baki Yakumbo tasa hannu ta buge bakin cikin masifa take cewa. "Ina tambayarki zaki tsaya kina zumɓuro min baki, Toh ma wani shegen ne yace kije wajan Rafeeq ɗin da har yai miki abinda ya ɓata miki rai? Idan na sake ganinki tare da shi sai ranki yayi mugun ɓaci." Yakumbo na gama faɗa ta mike tana gyara wajan kwanciyarta wato kan rug dan bata san hawa gado ko a can gidan ta. "Kika ce na dena kulashi? Haba yakumbo dan uwana ne fa." Wani kallo Yakumbo ta sake wurgawa Haneefa tana faɗin. "Nafiki sanin hakan, kuma bawai mantawa nayi ba bare ki tuna min. Rafeeq ɗin ne bana son kina shige masa karki sake janyo min raini a wajan sa." Hawaye ne suka shiga yawo a saman fuskar Haneefa, da muryar kuka take cewa. "Yakumbo nida nake cewa zaku haɗa mu aure dashi? Ina son Yaya Rafeeq da ga...." Ai bata ƙarasa ba Yakumbo ta jefa mata pillow a fuskarta wanda yasa ta haɗiye sauran maganar da take yi. Kuka Haneefa ta saki tana faɗawa kan gado, Yakumbo taja tsaki tana sake gyara shimfiɗarta sai masifa take. "Kiyi kukan jini indai Rafeeq ne ina raye ba zaki aure shi ba, ko meye abin so a wajan mutum mai shigen faɗin rai? Kiyi kukan babu lallashinki da zanyi." Yakumbo ta faɗa so pissed up ta nufi makunnin fitilar ɗakin ta kashe ta duka tayi kwanciyarta tabar Haneefa cikin kunnar zucci dan har ta fara tunanin da gaske Yakumbo ta daina sonta tunda har zata iya yi mata iyaka da soyayyar Rafeeq Gwarzo. A hankali shesshekar kukan Haneefa ke tashi a dakin, shiru Yakumbo tayi duk da ba baccin take ba, a hankali kukan autarta tata ke wani taɓata, ko kaɗan bata son ɓacin ran Haneefa. Kai tsaye ta miƙe tsaye ta lalubi makunnin fitilar haske ya gama gauraye ko'ina, kai tsaye Yakumbo ta zauna gefen bed ganin haka yasa Haneefa ta wani kwantar da kanta kan cinyar Yakumbon hawaye na rolling cikin fuskarta tana sauke ajiyar zuciya a hankali. Yakumbo na shafa kanta a hankali cikin sanyi murya ta kira sunanta ba tare da Haneefa ta amsawa Yakumbo ba kawai runtse ido tayi. A hankali Yakumbo ta nisa kafin tace. "Nifa ba wai ƙinki nake da Rafeeq ba, a'a Haneefa idan ke kina sonsa ke kin san wacece a tasa zuciyar? Ko kina tunanin bashi da wacce yake so?" Da sauri Haneefa ta miƙe zaune ta wani rike hannayen Yakumbo tana faɗin. "Yakumbo bayan auren ni nasan zai soni, da gaske ina sonsa Yakumbo idan ban aureshi ba zan iya mutuwa. Nidai kiyiwa daddy magana idan ba haka ba zan iya mutuwa ko na shiga duniya kowa ma ya huta." Da sauri Yakumbo ta rufe mata baki da hannunta tana wani zaro ido take faɗin. "Duk zuri'ar Gwarzo babu mai yawan bariki karma na ƙara jin wannan maganar ta sake fitowa daga bakin ki Haneefa. Ki goge hawayenki zanyi magana da shi baban nashi nasan zaiyi farin ciki da hakan. Shi kuma Rafeeq dole ya yadda ya aureki inhar yana son albarkar mu." Wani irin murmushi Haneefa tayi ta wani rungume Yakumbo jikinta, cikin jin daɗi take faɗin. "Dan haka nake matukar kaunarki Yakumbo, Allah yasa tare dake zamu mutu ga kabarina ga naki." Murmushi Yakumbo tayi tana faɗin. "Ki kwanta kiyi bacci mai daɗi gobe zamuyi magana da Baban ku Insha Allahu." Sai da yakumbo ta tabbatar Haneefa ta koma ta kwanta sa'annan itama ta koma makwancinta, amman a can ƙasan ranta damuwa ce fal aranta, ko kaɗan bata son Haneefa ta shiga cikin damuwa zata tsaya da kafafunta har sai ta tabbatar da auren Rafeeq da Haneefa ya tabbata. Ya kirata yakai sau goma amma har lokacin waya takeyi, nan take zuciyarsa ta bashi amsar waya takeyi kuma da Abdul-wahab. Haɗa kansa yayi a bango yana jin zuciyarsa na wani irin tafasa, a daren bai samu yin wani bacci ba. Suna dawowa Shaheed kawai ya faɗawa cewa zaije Zaria amma yace kar ya faɗawa kowa dan a yau zai dawo. Fatan sauka lafiya ya yi masa ko cikin gida bai shiga ba kusan ƙarfe 7:00am motarsa tabar cikin harabar gidansu dan ko kaɗan bai son haɗuwa da Yakumbo ta cika sakawa mutum ido da magana akan abunda bai shafeta ba, ga kuma ƴarta a gefe da ya lura tana ƙoƙarin shiga rayuwarsa karfi da yaji wanda shi kuma baya buƙatar hakan. Yau tunda safe ta tashi da wata irin murna cikin fuskarta
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book
14, February 2025
Hasina Ayuba Adam
I like to read the book