Showing 18001 words to 21000 words out of 131802 words

Chapter 7 - MATAR TAJ HAUSA NOVEL

27 Sep 2024

25347

dakin yasa wuce tsakar gida don daura dumamen da za akai asibiti.
Bata ma kaiga dora tukunyar ba maman nata ta futo daga daki, sanye da hijab.

''ajiye tukunyar nan kizo mu wuce''
Ajiye tukunyar tayi ta nufi inda maman nata take, daman already da silifas dinta a kafarta.

Lokacin da suka fito haske ya bayyana don gari ya soma washe wa,
Gidan Jamila suka wuce direct, da sallama suka shiga,Jamila ce a tsakar gidan tana hidimar abuncin yan makarnta.

Sama sama suka gaisa da hadiza kafin su wuce cikin daki, wasu yan maganganu sukayi sabeeha dai na daga tsaye ta raqube a gefe har suka fito, kallon inda take hadizar tayi kafin tace ''ki zauna anan''
Cikin girmamawa ta amsa da toh kafin hadiza ta fuce.

Anan tsakar gidan ta samu waje ta zauna, har gari ya washe sosai, karfe takwas daidai mijin Jamila ya futo tare da jamilar suka wuce.

Sabeeha dai binsu take da idanu duk ta soma tsorota har suka zo wani waje inda aka rubuta Aj agency service, cikin wajen suka shiga, wajen cike yake da mutane ga wasu yan mata da maza kamar ta harda wasu manyan mata dukkansu da irin kayan jikin da mamanta ta bata,idanu ta soma zaro wa tana tunanin ko menene dalilin kawo ta da akayi nan, mijin Jamila shima anan yake aiki so yana zuwa already yayi masu bayani daman sunsan da zuwanta, nan wani mutumi yayi mata nuni da inda sauran yaran suke don ta zauna.
Shikuma mijin Jamila da ita jamilar suka shiga wani office,wani mutumi ne a zaune, gaisawa suka farayi kafin mijin Jamila ya soma Magana ''alhaji mun taho da yarinyar, zaku iya ajiyeta na shekara goma ma idan kunaso babu matsala saidai kudin da aka bamu ne, shine nace tunda ita ba'a yanke mata lokacin dawowa ba ko za a kara mana''

''kaifa masinja kasan yanayin aikin nan, dubu dari fa muka baka, gaskia bazan iya kara wani abunba''

Jamila ce tayi saurin tsomo baki ''haba alhajin allah, mu fa bamuda matsala, ce maka akayi ku riketa, idan ma shekaru dari zatayi tana aiki karkashin ku mu bamuda matsala, ko dan wannan ya kamata a kara mana wani abun mana''
'
''ah toh mu gaba ta kaimu, zan kara maku dubu goma''
Godiya sukayi mashi kafin ya irga kudaden ya basu suka fuce daga wajen.

Samun waje tayi daga gefe chan ta zauna gaba daya ta fara furgicewa da tsoro, don bata taba shiga cikin hayaniyar mutane haka ba.
Su kuwa Jamila da mijinta suna amsar kudin su suka kara gaba abunsu suka barta tana zare idanu.

Tana nan zaune cikin yaran har wajen karfe goma kafin a fiddo dasu waje inda akayi parking wata katuwar bus.
Daga nan aka basu umarnin shiga cikin bus din, sai a lokacin sabeeha ta tabbatar da something is wrong? Ina ne nan ta tambayi kanta, ina za a kaita, nan take ta soma hawaye.
Har suka shiga cikin bus din bata bar hawaye ba.

Shin ina za akai sabeeha?
Ku biyoni don sanin wata duniyar sabeeha zata shiga, Siyar da ita su Jamila sukayi? Da sanin mahaifiyarta kuma? Ko kuwa Da gaske aikatau din za a kaita wata kasar daban? Inda bata san kowa ba? Gashi bata iya mu'amala da mutane ba.


Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Free page
Chapter 9-10

Texas high class restaurant Abuja.
Mota ce kirar range rover rr2023 fara tass tayi parking a cikin parking lot din dake cikin restaurant din, manyan manyan motoci masu class ne parke a wajen aqalla bazasu wuje guda biyar ba.

Saida aka dauka kusan minti biyu kafin abude kofar motar, cikin natsuwa ta fito daga cikin motar gaba daya, sanyayan murmushi ne kwance a fuskar mata, daga ganin ta babbar macece data manyanta,sanye take da jan lace na manyan mata masu aji da bakin mayafi wanda ya haskata sosai, hannunta rike da hermes hand bag baka, wuyanta zagaye yake da Sarkar gwal, haka zalika hannayenta, daga gani yar gayu ce don tasan fashion sense , bata da qiba kwata kwata saidai kana ganin fuskanta kasan ta manyanta, idanunta kuwa wani dan siriri glass ne akai,tana da wani irin calm appearance.

Rufe motar ta fara yi kafin ta soma takowa zuwa cikin restaurant din, saida tazo bakin kofar ta sauke wani murmushi wanda ke bayyanar da hakoran.
Fuskar data hango daga cikin restaurant din ne kawai yasa ta sauke wannan murmushi, guards din dake wajen ne ya bude mata kofa kafin ta sanya kafafunta cikin restaurant din, daga ciki kuwa mutane ne a zaune kan wani dogon table,akalla zasu kai su goma a zaune, kowannensu hankalinsa nakan plate din dake gaban su, kamar daga sama sukaji daya daga cikin yaran na fadin ''nanna, nanna''

Da sauri duk suka juyo don ganin ko da gaske ne nanna dince, suna tabbatar da ita dince kuwa duk suka miqe tsaye cikin farin ciki da murna, qananun yaran ne suka taho a guje, suka rungumeta, yaran sunsha cute kaya masu kyau, iyayensu kuwa duk miqewa sukayi suma cikin farin ciki suna kallonta.

Tun daga nesa ta soma Magana ''wai wai Anne ashe haka muka tara iyali masha Allah''
Dariya duk suka fara yi har ta karaso wajen tables din, samarin dake tsaye ne suka fara duqawa zasu gaisheta rungumosu ta fara yi daya bayan daya cikin farin ciki.
''barka da sauka nanna''
''barka dai sufyan, Abal din anne yaushe kuka dawo daga school ya uk''
Abal ne ya amsata ''alhamdullah, munzo holidays su ya sufyan kuma sun gama ay''
''Ahh masha allah, abun babu wuya''
Sunkuyar dakai sukayi gaba dayansu suna murmushi atare.

Iyayensu ne mata suka fara gaisheta suna duqawa suma don bata girma ''barka da zuwa nanna''
Kallon wadda ta fara gaishe ta tayi ''ah ah matar babban yaya, na sameku lpy?''
''lafiya lau nanna'' ta amsata cikin ladabi, sauran matan ma haka suka dunga gaisheta tana amsa su.


Gyaran murya da akayi ne yasa ta dago kafin ta sauke wani qayataccen murmushi, cikin hanzari ta tako har inda dattijuwar datayi gyaran murya take, kamannnin su sak babu makusa, kana ganin su kasan jini jini ne aduk inda yake,kamannin harta baci sosai banbancinsu kawai daya ta fi daya manyanta.
''yaya...'' ta fada tana mai rungumeta tsam,
Rungumeta itama dattijuwar tayi tana mai farin cikin ganin yar uwarta
Saida suka dauki kusan minti biyu a haka kafin su saki juna, wadda yaran nan suka kira da nanna ne tace ''happy 60th birthday yaya, allah ya karo shekaru masu albarka da nisan kwana''
Atare duk suka amsa da ameen, sai alokacin ta samu suka gaggaisa da sauran da basu gaisa ba, gaba daya an taru full family gwanin birgewa, surukai da matan surukai duka, harda jikoki.

Lokaci guda wajen ya kachame da hira sosai inda nanna ta zauna kusa da yar uwarta anne suma suka fara hira.

Hannun anne na cikin na yar uwarta don murna, nanna da anne yan uwa ne, ciki daya suka fito,anne ce babba sai nanna mabiyarta dukda ta girmeta sosai.

Rarraba idanu nanna(grandma) ta soma yi kafin ta maida dubanta ga matar Sameer ''ina babban yayan ne ban ganshi ba?''
Cikin ladabi da kunya matar ta dago ta kalleta ''ay ya tafi wani course a Europe yau wata guda kenan''
''Ayya shiyasa kennan'' nanne ta fada tana mata murmushi.
Sallamar da akayi ne yasa suka dago gaba dayansu, wadda ke gaba ce ta soma fada, ''wai ace mutun ya tsaya yangan banza da wofi, wallahi next time kika kara bata min lokacin bazan kara jiranki ba shirman banza kai, kai kuma hamad ka riqe package din da kyau karka yarda cake din''
Wanda ta kira da hamad kanshi na kasa ya rike wani package da hannu daya,dayan hannunshi kuma key din mota ne da wayanshi, saurayi kyakyawan gaske black beauty, bazai wuce 22 years ba gefenshi kuma wata yar budurwar yarinya ce akalla bazata wuce 18 years ba, sanye take da wata doguwar rigar material datayi mata kyau, baka ce kuma kamanninta daya da hamad din saidai shi yafita kyau, hannunta itama rike da wayaa latest iphone fuskanta tasha makeup a wadda ya amsheta, wadda ke gaba da alamu mamansu ce.

''sannu da zuwa anty fadila'' yaran suka fara fada suna gaisheta, sai alokacin ta dago don gaisheda anne, ganin nanna yasa ta sauri waro idanu tare da tahowa cikin sauri ta rungumeta ''nanna, saukan yaushe''
Dariya nanne tayi ta rungumeta tsam itama tana mai jin dadin ganinta tace ''my daughter, nayi missing dinku wallahi, how are you ya mai gidanki''
Murmushi tayi wanda yasa duk mutanen wajen suka zuba mata idanu, don da wuya murmushin anty fadila ya futo shiyasa kowa yafi son anty bahijja don ita tafi faran faran ga son mutane sosai, anty fadila kuwa akwai fada bata daukan nonsense, gashi ta iya dressing don ta iya buga naira a jikinta, to kudin ne ma gashi nan kamar zai kashesu.

''yana nan lafiya nanna, ya turkey,fatan kin dawo Kenan shekara kusan biyu fa rabonmu dake''
Murmushi nanna tayi kafin tace ''na dawo Kenan insha allah bazan koma ba,''
Yaranne suka soma cewa ''yay'' suna murna,

Sama sama fadila suka gaisa da matar Sameer kafin ta maida dubanta ga anne tare da taya ta murnar cika shekara sittin a duniya.
Hamad ne ya karaso ya tsugunna har kasa ya gaisheta kafin Laila itama ta rungumeta tana mai farin cikin ganinta.

Haka suka gama celebrating 60th birthday din anne cikin jin dadi da murna har mutanen US saida suka kirasu sukayi video call inda suka taya anne murnar cika shekara 60th a duniya kafin su wuto gida.

Saudi Arabia......
Karfe biyar daidai jirginsu ya sauka a international airport dake garin jedda, daya bayan daya suka fito, gaba daya suka sauko daga jirgin inda wanda ke jagorantarsu ya jagorance su zuwa wajen barrier din dake controlling shige da fuce na kasar, mazan na daga gaba while matan ba biye dasu har suka shigo cikin airport din, checking dinsu aka fara yi daya bayan daya don ganin information dinsu, basu wani samu matsala da immigration din ba don haka ana gamawa dasu suka fuce daga airport din.
Bayan sun fito daya bayan daya wanda ke jagorantarsu ya soma karbar passport dinsu kafin su shiga bus din da aka tanadar masu ta agency company don tabbatar da babu wanda ya gudu.

Sanyayyiyar ni'ima ce tare da fargaba ta saukar ma sabeeh lokacin data shaqi iskar qasa mai tsarki,harga allah hankalinta yana gida musamman mamanta da inna dake kwance asibiti.

Rarraba idanu ta dunga yi har suka shiga cikin bus din, at that point ta hakura kawai ta barma allah komai, don babu abunda yayi saura kuma,baiwar allah saita zama wata iri, kuka dai tasha kuka kamar babu gobe, tsoron da take ji ya wuce musali, matar da suka taho tare ma bata ganta ba don bata shugo cikin bus dinba, abunda yafi bata mamaki atare duk suka fito juyawar da zatayi kuma ta nemeta ta rasa ta.
Sauran yan matan ma rarraba idanu suka dunga yi, wasu daga cikin su murna suka dungayi gashi a saudia wasu kuwa hankalinsu tashi yayi don basu san ya rayuwar kasar take ba.
Tafiyar minti talatin sukayi suka karaso company, dukda garin bai soma washe ba amma inkaga yanda mutane ke hada hadarsu kamar da rana.
Fitowa sukayi daga cikin motar kafin a wuce dasu cikin agency din, mazauni aka basu da ruwa da apple kafin gari ya waye.

Wanda ya jagorancesu ne ya nuna masu inda bandaki yake da wajen yin sallah na musulmai, mazan dai mikewa sukayi suka wuce wajen sallah while matan kuwa suka kasa miqewa saboda tsoron karsu bata, sabeeha ce kawai ta iya dannewa ta miqe ta wuce bandakin, saida ta biya buqantunta ta dauro alwala har tayi sallah a wajen sallah kafin sauran su shiga wajen suma.

Suna nan zaune har wajen karfe goma har aka kawo wasu daga wata kasashe daban kafin a tattara su waje guda, wata agreement paper aka basu kowanne don yayi sighing kafin a rarraba masu wani tag mai dauke da sunayensu a jiki tare da sunan agency kafin kowannensu ya saqala tag din a wuyanshi.


Sorting dinsu masu agency din suka fara yi base on shekarunsu da abunda suka fi kwazo wajen yi kafin a fara futar dasu, don tun daga kasashensu ake masu training kafin a kawo su, agency din data kawo sabeeha ma AA agency Kenan itama tana karkarshin waenda ke kawo masu aiki dukda basa bin dokokin daukan yan aikin saboda su basa yin wani training suke aiko wa, wasu daga cikin yaranma basu san inda za a kaisu ba ake daukosu kamar su sabeeha Kenan, don saida suka shiga jirgin matar nan take mata bayanin komai.

Wasu daga cikinsu manyan company za a kaisu wasu kuma gidajen da sukayi requesting maids za a kaisu, wasu daga cikinsu ma har asibiti za a kaisu shara da dai sauransu, wasu gidan abunci, wasu har makka ana kaisu suyi aiki a masallaci.

Sabeeha dai bata san inda aka wullata ba, haka aka tasata da wasu a gaba acikin motar agency su kusan biyar.

Tunda ta zauna cikin motar take bin titin garin da kallo dukda sunyi zaman kasar waje da maman ta kafin su dawo rayuwar talaucin da suke ciki hakan baisa ta danyi kauyanci ba da mamakin wai yau itace a kasa daban, gaba daya tunaninta yayi nisa ya tafi wani wajen har suka karaso wani gida, sunanta da balaraben daya dauko su ya kira ne yasa ta saukowa daga cikin motar, wata jakar goyo ya bata kafin su shiga cikin gidan.

Gidan bashi da wani girma sosai, irin tsoffin ginin nan ne wanda ya dan kwana biyu, ciki suka shiga inda mutumin ya jagorance ta, hannunshi rike da wata paper.
Koda suka kwankwasa kofa wata balarabiya ce ta bude kofar, daga ganinta ta dan manyanta, mutumin ne yayi mata bayani cikin harshe larabci kafin ta karbi paper din tayi sighning, tana signing ya wuce ba tare da ya kalli sabeeha ba.
Matar kuwa ganin ta tsaya a tsaye kamar wadda za a sace,sai faman zare manyan idanuwanta take, hakan ya sata ta mata nuni da hanyar cikin gidan.
Ciki matar ta shige sabeeha na biye da ita, gida ne gidan bene bashi da wani girma sosai.
Anan kasan matar tayi mata nuni da wani dakin kafin ta mata bayani da turanci kan cewa ta shiga tayi washing up.
Dan turanci da take ji ne yasa ta gane abunda take nufi, duk da karatunta baiyi zurfi ba, kanta kawai ta sauke kasa kafin ta shiga ciki,hawayen da take kokarin hana kanta yi ne ya sauko mata lokacin data shiga cikin dakin, dakin shake yake da abubuwan da sun kai kusan shekara ba ayi amfani dasu ba, hardasu tsohon keken dinky da wasu robobi, duk kura ta gama bade dakin gashi dakin bashi da wani girma sosai.
Jefa idanunta tayi wajen wata kofa, kusa da kofar akwai wani dan karamin gado, anyi laying gadon da zanin gado kamar anan ake kwana don harda pillow da abun luluba a wajen.
Takowa tayi har bakin wajen kafin ta ajiye yar jakar da mutumin nan ya bata akan gadon, bakin kofar tabi ta leka ganin bandaki ne a wajen yasa ta dawo ta zauna akan gado.

Wani irin barcin gajiya ne ke fuzgarta, ga tsoron daya addabeta na sabon waje.
Tana nan zaune barci ya dauke ta ba tare da saninta ba, saida ta shafe wajen awa biyu kafin ta tashi da kugin ciki saboda yunwa data addabi cikinta, tunawa da apple dinnan da aka basu yasa ta bude jakar, kaya ne kamar uniform kala uku a ciki riga da wando, gaban kowacce riga an rubuta sunan agency din a jiki harda phone number su a jiki.

Ajiye kayan tayi a gefe ta dauki apple din ta fara yi tana hawaye,saida ta cinye tass harda kwallon kafin ta shiga bandakin ta tara ruwa daga fanfon sink din tasha abunta tana kuka.

Satin sabeeha uku a cikin wannan gida, acikin kwana ukun nan abubuwa da dama sun faru wanda suka firgitata suka hargitsa mata tunani sosai, wato aikintaa gidan shine kula da wani tsoho, inda ita zata dunga kula da komai nashi don baya tafiya kullum yana kan kujera, tsohon yana da masifa sosai ga rikici, itake wanke kayan da yake kashi da futsari akai, itake zama ta bashi abunci dukda idan ta kawo watsa mata yake a jiki, wani sa'in har marinta yakeyi ko ya jefeta da objects, su uku ne kawai a gidan daga ita sai wannan tsohon sai matar wadda da alamu itace guardian din tsohon.
Zataci zata sha saidai kuma wannan rikicin tsohon ne ke tayar mata da hankali, data zauna babu abunda take sai kuka, gashi wannan yar tashi dataji ya fara kuka zatazo ta balbaleta da masifa wani sa'inma harda mari take hada mata.
Watan sabeeha guda a gidan wanda ya zame itace maid ta farko datakai har wannan lokacin, har zuwa wannan lokaci babu abunda ya sauya game da wannan tsoho da take kula dashi,kullum in zatayi aikinta kuwa zata saka uniform dinnan ta daura koren hijab din da aka basu tare da facemask dinnan kafin ta fara aikinta, mask dinma har ya fara tattogewa saboda tsufa don wankeshi takeyi.
Akwai wata ranar laraba, matar gidan bata nan daga sabeeha sai tsohon nan a gidan, bayan ta gama ayyukanta lokacin cin abuncinsa nayi ta zuba mashi ta wuce dakinsa don ta bashi, tana zuwa ya fara watsa mata abunci yanda ya saba yana masifa, yana cikin wannan masifar yana larabci ya cizge mask din nata, daidai nan yarsa ta dawo, jin ihunsa yasa ta taho aguje zuwa dakinsa, tana zuwa dakin ganin tsohon yashe a kasa duk yabi ya tsorata yasa ta juya don ganin inda yake kallo, sabeeha ce a tsaye itama tana kuka yanda yake kukan, ta janyo hijab ta rufe fuskanta, nuni tsohon ya dunga yi da sabeeha cikin furgici ya fara cewa ''shaytan shaytan,''

Ba matar kadai ba har itama sabiha saida hankalinta ya tashi sosai,ganin haka yasa matar ta korata akan tabar daki.
Da daddare kuwa saiga motar agency tazo don tafiya da ita, haka ta tattara kayan nan nata guda uku ta tura a jaka tabar gidan.

Agency aka maidata ko kwana batayi ba aka dungumeta aka kaita wani gidan daban, wannan gidan da aka kaita bata samu wani matsala ba da matar gidan dukda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login