Showing 42001 words to 45000 words out of 131802 words

Chapter 15 - MATAR TAJ HAUSA NOVEL

27 Sep 2024

25353

room, kan kace me parlorn ya karade da ihun su da hirarrakin sun a yan mata,
''go and frenshen up mana kafin su karaso its about to go down today'' kloe ta fada tana kallon maya

''ku jira ni yanxu zan sauko please'' maya ta fada tana wucewa sama.

Orders din da sukayi aka soma deliverying, kayan ciye ciye daban daban kamar waenda zasuyi house party.

Within few minutes saigata ta sauko cikin riga da wando wanda suka amsheta pink sai gashinta datayi packing dinshi a tsakiya, duk da bata da wani qiba da shape hakan baisa kayan sunyi mata kyau ba.

Tana shugowa parlor suka miqe gaba dayansu suna Shewa, ''ouu let the party begins''
''oh yess'' ta amsa su
Katuwar speaker dake nan parlorn su ta kunna masu suka fara rawa, kidan gaba daya ya gama karade wajen block dinsu kamar gidan party, nanny bee dai babu yanda batayi ba akan su rage saboda mutanen neighbourhood din basa son kara bayan wannan ma throwing noisy party a neighbourhood din is prohibited, haka suka wuni suna sha'anin su kwata kwata babu wanda yaji knocking din da aka dunga yi.

Sai wajen karfe biyar wutar gidan ta dauke gaba daya, rai a bace maya tace ''what the hell is going on?, kodai electricity bill din ne ya kare''

''gaskia call your parents, kofa gamawa bamuyi ba gashi su tom basu zo ba''

Knocking din da akayi yasa suka tsagaita da surutan da suka fara, ''who's knocking kuma, daddy baya nan mummy kuma sai wajen midnight zata dawo''
''let me check'' kloe ta fada tana nufar hanyar kofar entrance din.
Saurin yin baya tayi ganin police a bakin kofar, ''who's the owner of this property''
Cikin saurin kloe tace ''maya, come over''
Tasowa maya tayi ta karaso inda police din suke, ''are you the owner of the property?'' suka sake tambayarta
''yes, I'm the daughter of the owners''

''you're under arrest for violating the regulations of this compound''
Hankali a tashe maya ta kallesu tace ''what have I done, who reported me? For what?''

Bai amsata ba yasa sauran officer din suka shigo suka saka su a gaba zuwa cikin moto, nannybee bata san me ake ciki ba saida ta fto lokacin ana shirin saka su cikin motar, turawa fa basu daukan wargi, dan report kawai neighbourhood din suka kai kusan guda biyar wanda haka yasa dole police suka zo suka tafi dasu.

Hankali a tashe nannybee ta soma kiran line din mummy, kiran duniya ta dunga mata bata sameta ba saboda suna cikin operation room, dan dole haka ta soma dialing number daddy, kiran farko kuwa ya daga wayan, lokacin yana kokarin barin san francisco zuwa ga los angeles daman tafiyar 30mins ce gaba daya, saboda akwai wani case da yake handling dole saiya bar garin zuwa wani garin ya samo concrete evidence.
Yana ganin call dinta kuwa ya tabbatar da ba lafiya ba, cikin sauri ya dauka call din.
Hankali a tashe ya ajiye wayar, ga ranshi yayi mugun mugun baci sosai, haka nan duk importance din aikin nan nasa ya barshi ya juya zuwa san diego.
A gurguje ya nema flight zuwa san diego allah ya taimaka akwai jirgin da zai tashi don haka ya nemi ticket a gurguje.
Bashi ya iso ba sai wajen karfe shida lokacin garin ya soma duhu, daga airport zuwa police station dinma akwai traffic sosai, ba karamin bacin rai ne kunshe a ranshi ba, allah kadai yasan me zaiyi ma maya, abubuwanta gaba suke karayi kusan kullum.

7 dot ya iso police bureu dake cikin san diego city, a gurguje ya bada sunanta ga officer din dake counter din wajen ''maya Majeed please, I'm her father''

Ciki suka shiga inda suka bashi waje ya zauna, officer daya kawosu ne ya soma mashi bayanin charges da report din da aka shigar da kudin damage din da zai biya ga electry line dinsu da aka kashe gaba daya dole saiya biya tax.
Yana daga zaune saida ya kashe over 4000 dollars akan minor mistake na maya, at that point ko ganinta baya son yi, bai taba saka tunanin dukan yaro a cikin rayuwar shi ba, saidai yau yana jin kamar ya mata duka sosai.
Saida ya biya komai suka rakashi har inda aka kullesu, koda suka karasa tana daga zaune idanunta yayi jaa sosai tasha kuka, gaba daya friends dinta sun kira iyayensu sunzo ita kadai ta rage.

Fito da ita sukayi suka wuce gida, taxi ya tsaida masu suka shiga don motarshi na gida saboda daga airport ya biyo nan din.
Suna isowa mummy ta iso itama gidan,already ta kirashi bayan taji daga wajen nanny bee, dady ne ya fara futowa kafin itama ta futo daga taxi din, da gudu ta karasa wajen mummy dake tsaye hankali a tashe tana jiran fitowarsu, rungumeta tayi tsam tana hawaye, ''mummy I'm sorry please''
Ko kallon inda suke majid baiyi ba ya wuce cikin gidan daman tunda suka shiga cikin motar bai ce mata tak ba har suka iso, babu abunda take kuwa sai kuka kuma yana jinta yayi banza da ita don har zuwa lokacin yana processing irin hukuncin da zaiyi mata daidai da ita.

Kallon fuskanta da tayi gaja gaja mummy tayi kafin ta kamota zuwa cikin gidan, gaba daya ranta a dagule yake da alamarin, tasan wannan karan kam bazasu kwashe ta dadi ba da daddy don ta hango tsantsan bacin rai akan fuskanshi.
Koda suka shiga nanny bee na tsaye hankali a tashe, gaba daya laifin kanta take gani na qin hana maya, son da takeyi mata ne ke sawa take hana ta yin wasu abubuwan saboda tausayinta da takeji, iyayenta are very busy parents, basuda time din ta saboda aiki, wannan yasa ta taso da kadaici da rashin kusanci da iyayen nata musammam daddy.

Har cikin bedroom dinta mummy ta rakata tayi wanka nanybee ta kawo mata abunci taci kafin mummy ta bata maganin ciwon kai.
Saida ta tabbatar ta natsu kafin ta kashe mata wutar dakin nata ta koma zuwa bedroom dinsu.

Da sallama ta shiga dakin, a zaune ta taddashi har zuwa lokacin ranshi a bace yake,karasowa tayi inda yake bakin gado ta zauna gefenshi kafin ta soma Magana cikin hikima ''daddy!!''
Dagowa yayi ya kalleta idanunshi yayi jaa sosai, ''majeed dan allah kayi hakuri, yarinta ke damun maya,''

''yarinta? Bahijja yarinta fa kikace? Are you listening to your self kuwa, where's she?''
''na sata barci, ''
Ta bashi amsa kai tsaye.

Wani irin mugun kallo yayi mata kafin yace ''barci? Bahijja wani sa'in kina bani mamaki?,kinsan asarar da yarinyar nan ta jawo mana? Kin san me zatayi nan gaba, after all she has done kin sata barci?wallahi kinji na rantse bahijja wallahi this time around I'm going to deal with maya, duk abubuwan da takeyi ina Kauda idanu this time around bazanyi ba, and don't even think of saying a word kinji na fada maki''
Yana kaiwa ya miqe ya fuce daga dakin, tana ganin futarshi tabi bayansa, dakin maya ya nufa kai tsaye ya bude kofar ya kunna lights din dakin, barcinta take hankali kwance kamar ba itace tayi aika aikar nan ba, ''maya!!!'' ya doka mata uwar tsawa, tashin farko ta mike zaune zumbur,
'wani irin furgici ne ya durar mata ganin daddy nata a tsaye, daidai nan mummy ta karaso cikin bedroom din, ''step out now''

''daddy please I'm sorry bazan sake ba please''
''shut up your dirty mouth, I said out to, don't make me repeat my self, ''

Ya karshe hannunshi har karkarwa yake tsabar bacin rai,
''mummy please talk to dad dan allah, wallahi banason zuwa displine room dan allah''

Tana kaiwa nan ta karaso inda mummyn take ta boye a bayanta, ''daddy please, for god sake laifi tayi kuma tayi nadama, maya is not a kid fa da za a kulleta a daki, she will be 18 in a month''

''bahijjaaaaa!!!!,''
''majid please....''
At that point ranshi ya gama baci sosai, ba maya ba hatta mummyn ma ta gama bata mashi rai sosai.

Kasa cewa komai yayi kawai ya fuce daga dakin cikin bacin rai sosai, shi kadai yasan meke cikin ranshi da matakin dazai dauka akan sus u duka ma.
He's trying so hard to understand bahijja, wani sa'in yana kauda ido sosai akan rashin jin da maya keyi saboda maya kadai ce yarsu, kuma bazasu sake haihuwa ba saboda matsalar mahaifa da bahijja ta samu bayan haihuwar maya.

Wannan rana dai cikin bacin rai sukayi gaba dayansu daga daddy har mummy, haka suka kwashi wajen sati guda babu wanda ya kula wani cikin su, maya kuwa harkarta ta cigaba ba tare da damuwa ba, ita dadinta daya mummy ta bi bayanta, saidai ta gindaya mata sharuda sosai tare da warnings akan cewa idan ta sake ta sake maimaita abunda tayi bazatabi bayanta ba.



Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 21-22

Update
NIGERIA ABUJA
Santuraki family...
Yau family an tashi da jimamin mutuwar babban aunty amarya (matar uncle sameer), gaba daya cikin shiri suka fito inda zasu je gidan gaisuwa, already uncle Sameer ya wuce da aunty amarya chan gidan gaisuwar don tunda asuba aka kirashi aka shaida mashi, lokacin ma ba'a bangarenta yake ba yana bangaren anty Laila don kwananta ne ya zagayo a ranar, anne ce da nanna suka fito cikin shiga ta mutunci da alfarma sai sauran matan gidan, anty fadila da yaranta mazan, hamad da laily karama sai sufyan da abil, kananun ne kawai aka bari a gida wajen nannies dinsu.

Gaba daya suna tsaye a compound din har kowa ya futo gaba dayansu banda anty Laila,
Anty fadila ce tayi saurin cewa
''mamanku fah''
Anty fadila ta fada tana mai duban su abil,kallon juna suka fara yi shida sufyan, ''tace driver zai taho da ita''
Tabe baki antie fadila tayi kafin ta shige cikin katuwar lexus inda hamad ke driving motar while sufyan ke driving dayar motar dasu anne ke ciki.

Cikin anguwar GRA dake cikin maitama suka nufa, anguwar ta masu shi ne don anguwar dai ta hadu sosai, daidai wani babban gida suka karaso, daga wajen gidan mutane ne burjik.
Parking sukayi kafin su firfito, uncle Sameer ne yayi masu iso zuwa cikin gidan inda mahaifiyar aunty amarya ke karbar gaisuwa.

Gidan kana shiga kasan anyi rashi babba don ko'ina shuru mutane ana zazzaune,Allah ya jiqan musulmai baki daya wanda suka rigamu gidan gaskiya, muma idan tamu tazo allah kasa mu shika da Imani Ameen.

Har cikin babban parlor hajiya babba suka nufa da sallama inda suka fara gaggaisawa da mutanen dake parlor, anne ce ta farayi ma hajiya babba gaisuwa kafin su nanna dasu anty fadila, ba karamin dadi hajiya babba taji ba ganin dangin mijin diyar tata.

Anty fadila ce tayi saurin cewa ''ina aunty mubina''
''tana ciki, bari a kirawo ta'' hajiya babba ta fada
''ah ah bari na shiga daga ciki'' anty fadila ta fada.

Cikin dakin ta shiga nan ma dai akwai mutane amma basu kai na parlorn ba, mubina na daga zaune bakin gado, ta dafe kanta da alamu kuka take kanyi har zuwa yanxu, ga mubin a gefenta yana ta barcinshi hankali kwance.

Gaisawa ta farayi da matan wajen kafin ta karasa inda mubina ke zaune, jin an dafa ta yasa ta dago, ganin anty fadila yasa ta soma share hawayen fuskanta, idanunta sunyi jaa sosai, ''aunty fadila kunzo?''
''munzo mubina, ya hakurin mu allah yayi masa rahama, ai duk mun zo harda su anne duk suna parlor''
''ameen anty fadila nagode bari naje parlorn''
Atare suke wuce parlor inda su anne sukayi mata gaisuwa da sauran yaran harda samarin gida gaba daya.
Wayar aunty fadila ce tayi ringing, ganin wanda ke kiranta yasa tayi saurin picking call din, ''wa alaikum salam'' ta amsa sallamar da akayi daga chan bangaren kafin ta sake cewa ''tohm gani nan zuwa''
Ajiye wayar tayi kafin ta miqe ta fuce daga parlor, daidai tsakar gidan inda babu mutane sosai ta hangoshi daga chan nesa, cikin sassarfa ta karaso inda yake tsaye, babban mutun ne magidanci, kamanin su daya sosai don kamarma har ya fita kyau saidai girma dayazo mashi sosai, yana sanye da farauncle Sameer Kenan.
''gani yaya ya hakuri, allah ya jikan sa''
''ameen ya Allah'' ya amsa ta
''banga Laila ba ku kadai kuka zo?''
Tabe baki anty fadila tayi kafin tace ''mun barta a gida tace wai driver zai kawo ta''
Girgiza kai kawai yayi kafin yace ''shikenan, bari na koma gidan''
Sallama tayi mashi kafin ta koma ciki shi kuma ya shige motarsa zuwa chan zuwa gida.

Tafiyar minti ashirin ta kawoshi gidan, daidai apartment dinsu yayi parking kafin ya futo.

Da sallama ya shigo cikin gidan, babu kowa a kasan sai househelp din dake fama kwashe kayan wasan yara, ''barka da dawowa''
''barka dai,'' ya amsata kafin ya wuce saman, bai tsaya ko'ina ba sai bedroom dishi dake chan saman, da sallama ya shiga bedroom din, ko'ina tsaftsaf sai kamshin bakhoor dake tashi.
Wanka ya fara yi kafin ya shirya cikin manyan kasa, yana gamawa ya zari key ya wuce bedroom din anty Laila.
Da sallama ya bude dakin yasa kai ciki, dakin lum lum babu haske sai karar ac, hasken dakin ya kunna kafin yakai dubanshi ga tsakiyan gado, da mamaki ya hangota kwace hankali kwance, karasawa yayi har bakin gadon ya zuba mata idanu
''laila laila'' ya soma kiranta,
Saida ya taba kafadunta kafin ta farka, kallonshi tayi kafin ta kauda kanta gefe ta miqe zaune, daga ita sai wata doguwar rigar barci da alamu ko wanka ma batayi ba,
''sai yanxu ka dawo tun asuba?''
Ran shi ya dan soma baci, yanayin yanda take mashi maganar kamar bata san daga inda yake ba da kuma dalilin futar tashi, ''eh sai yanxu na dawo, maysa baki buyosu ba kunzo gaisuwa?''

A hasale ta amsashi, ''basu fada maka nace zanzo daga baya ba''

''kewai Laila yaushe zakiyi hankali ne? rasuwa fa akayi ma yar uwarki? Wannan wani irin shahsan ci ne, ke kullum sai kin jawo ma kanki abun Magana sannan kizo kina kuka kina cewa bana kyautata maki bana bin bayanki? Yanxu ke hakan ya dace? Duk gidan nan gaba daya sun tafi ke kina daga kwance''

''kaga Sameer karka qara hadani da matarka, ka taba ganin inda kishiyoyi suka zama yan uwa? ni ba yar uwata bace ba, sannan mutuwa allah na tuba wanda ya tafi ya tafi Kenan, zuwana bazai dawo dashi ba, kuma naga dai bance bazan zo ba, mutuwar nan fa kowa anyi mashi ita saboda ka daina wasu maganganu don ka nuna min matarka ta fini shiyasa yan uwanka ke min abunda sukaga dama suka raina ni basa ganin mutunci na''

''laila kishi fa ba hauka bane ba, you better stop this nonsense, girma kikeyi ba rage maki shekaru ake ba''

''naji ka fadi duk abunda zaka fada, daman baka ganin laifin kowa sai nawa'' tana kaiwa nan ta fashe da kuka
''wallahi Sameer na gaji, na gaji da wannan wulaqancin da yan uwanka ke min''

''wake maki wulaqancin? Fada min particularly'' ya bata amsa
''kowa ma, kaga yanda fadila ke yi min, fisabilillahi kamar banice matar wanta ba, saboda tambarin agola da nake dashi a gidan nan, hatta anne ma ba sona take ba kuma na sani wallahi na gaji kaf danginka babu wanda ke sona, ita matar da aka auro maka ay ba a mata haka, sunfi janta a jiki ni kuwa da nake bare an kawo ni agola bani da qima da mutunci''
Mikewa tayi tsaye rai a bace tana share hawaye shiko babu abunda yake sai kallonta
''laila, duk maganganun da zakiyi ya tsaya akan su fadila amma karki sake sako anne a ciki, sannan kina maganar basa kaunarki basa janki a jiki, ya akayi kika san basa kaunarki bayan ke kike janye jikin ki daga wajen su, bakya kaunar kusanci dasu, ke gani kike kinfi karfin shiga cikinsu'' ya bata amsa shima ranshi ya dan soma baci.

''daman gaskia ce dai ba a son jinta,''

''bana son jin wata Magana daga bakinki, kije ki shirya kizo mu wuce''
Kai tsaye ta amsashi, ''bazani ba''
''saboda me?''
''banyi ra'ayi ba'' ta amsa shi kafin ta shige bathroom tayi ramming kofar bamm

Ranshi yakai kololuwar baci sosai, when it comes to Laila tasan yanda zatayi ta bata mashi rai, yau shekara nawa Kenan abunda takeyi kullum gaba yakeyi, ada abun nata ba komai bane ba saboda bata comparising yanxu kuwa tunda ya auri aunty mubina bata da Magana sai ba a sonta a tsane, which shi yasan ba haka bane kuma duk wani problem daga ita ne, a komai saita nuna ta isa.

Fucewa kawai yayi daga gidan ya koma gidan gaisuwa, basu suka bar gidan ba sai wajen karfe tara na dare, inda suka bar aunty mubina da Laila karama saboda zata zauna da ita.




Saudi Arabia.....
A yau sabeeha ta cika sati biyu ciff a gidan da aka turo ta liken asiri, gaba daya tama manta da wani batun leken asiri.
A cikin sati biyu nan wata iriyar shakuwa ce ta wanzu tsakaninta da TAJ sosai, ita ke mashi komai, ita ke kula da duk wani abunda ya shafe shi, a cikin kwanakin ta gano halayenshi da abubuwan da baya so da wanda yake so.
Ta bangarenta ba karamin tausaya mashi take ba, don gaba daya a yanda ta fuskance shi da yanda yake abubuwa da tunaninsa gaba daya na yara ne, don kamar an shafe gaba daya tarihin rayuwar na shekarun baya an sako mashi na lokacin da yake yaro, ko sallah ma bai iya ba idan yana yi kamar dan koyo, abunda yafi bata mamaki dashi shine he's very smart sosai, don duk abunda ta koya mashi ciikin lokacin qanqani yake dauka, gashi yana bala'in son yayar shi madam Kenan, wannan soyayya sabeeha ta shaida ta don bata taba ganin irin wannan ba, bashi da Magana sai first love first love, idan abunci zaici first love, idan barci zaiyi zaice yana son ganin first love, wani sa'in haka kawai zata taddashi yana kuka yana kiran first love indan ya kwana biyu bai ganta ba.

Ta bangarenshi kuwa, bashi da friend din data wuce sabeeha ita kadai ce friend din daya fara yi, kullum ita ke wasa dashi yanxu ita ke bashi abunci, yana ji da ita sosai saboda first love dinshi tace mashi friend dinta ce saboda haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login