Showing 57001 words to 60000 words out of 131802 words

Chapter 20 - MATAR TAJ HAUSA NOVEL

27 Sep 2024

25387

ce, kuma ita ce zata zama MATAR TAJ"
Maido da dubansu sukayi ga hidaya, khaal ne yayi saurin cewa "a maid?"
"Yes" ta amsa shi kai tsaye,

Su fadwa dai kallon khaal sukayi suna jiran jin abunda zai ce,
"Ba opinion dinku nake nema ba its a decision dana yanke as big babys guardian and next if kin,kuma I believe hakan ne daidai kuka nasan koda ace baida mental issues bazai bijire decision dina ba"

Rai a bace khaal ya runtse idanunshi kafin ya bude, ranshi yayi mugun baci, wato hidaya ta maida taj kamar wani object din da zatayi abund ataga dama dashi abu har ya kaiga ta qasqantar tashi, yasan she's the one who made the whole world for him, kuma ita ce number one dinshi saidai bai taba tsammanin abun nata yakai ga haka ba, he's still confuse akan alamarin hidaya trying so hard to understand her da intentions dinta saidai yanxu komai ya baiyyana a fili.

Ba zato ba tsammani sukaji amsar khaal "okay!, ba damuwa, she will be taj legal wife and i approve it but inason na san meysa ita?"

"Saboda ita ke kula dashi kuma ita kadai ce ta dade dashi ba tare da wani problem ba"


Wani irin murmushi hidaya tayi kafin ta sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya, ta dauka zata samu matsala da khaal sai gashi komai yazo gidan sauqi.
Jamid dai runtse idanunshi yayi kafin ya bude, ya kalli hidaya, idanunshi sunyi jaa sosai,
"Amma inason naji daga bakin wannan maid din,"
Khal ya fada yana kallon sabeeha datayi sukan tsaye,kallonta khaal yayi kafin yace "what's your full name?" Khal ya tambayetaq
"Sa..bee..ha dalhatu"
Ta amsa shi muryarta na breaking, "sabeeha cire mask din fuskanki"
Tabe baki hidaya tayi don tasan me zasu tarar bayan ta cire kuma bata damu ba.

Kanta na kasa ta soma laluben fuskanta hannunta na karkarwa, mask din ta soma zamewa ahankali har tayi nasarar cireshi gaba daya, tana cirewa suka zuba mata idanu, afiya ce ta furta "what the fuck.." bata ma san tabfurta ba, dagowa ahankali sabeeha tayi ta zuba masu idanu suma kallonta sukeyi kamar sunga tv, afiya sai tashi tayi rai a bace tabar sitting room din.

Kallonta khaal yayi yana mamakin hallita iri irin a fadin duniya daban daban.
Idanunta dake rufe ta bude, yarinya ce danya shaf, wallahi tsarin fuskanta ya masifar haduwa kamar an kerata daga wajn girarta zuwa idanunta, ga hancinta mai tsayi wanda ya kara ma fuskan nata kyau, bakinta...
Lallai dan adam tara yake bai cika goma ba, duk kyawun da allah yayi maka sai an samu wani bangaren akasin hakan,halittar da allah yayi mata wadda ta fita daban shine bakinta, bakinta yayi wani zumbutu dalilin hakoranta da sukafi karfin fuskan nata, saida ta sakin bakin hakoran suka baiyya guda takwas reras kafa kafa kamar kacha,(gatso) ta gaban hakorin har wani kore kore yayi alamun hakoran marasa lafiya ne.
Wannan part of hallittarta ta aje mana wani baqin fenti a cikin tarihin rayuwarta tun tasowarta.

Saida khaal ya gama kallonta kafin ya sake jefo mata tambaya, "zaki iya auren sa?"
"Khal??? Why are you even asking" hidaya ta fada
"Ay ba a aure sai an samu yardar both parties, tunda shi hes not in right sense ita ay tana da hankali so dole musan idan ta amince"

Sabeeha dai shuru tayi tana tuna maganar mutumin nan da sukayi waya dazu, "duk wani abu da za a tambayeki akai ko za a nemi amincewar ki karkiyi gardama, just say yes inva haka ba komai zai iya faru da ke harma dashi wannan mahaukacin"
Cikin ta ne ya duri ruwa sosai, batama tsaya wani dogon tunani ba kawai tace "na amince"

Wani irin disgusting kallo hidaya tayi mata kafin ta maida dubanta ga khaal, "ina son aurensu a yau"
Bai musa ba yace mata "okay amma inada sharuda uku,"
Gyara zamanta tayi tana sauraronsa "na farko wannan yarinyar you'll allow her do her duties as his wife not his caregiver cinshi shan sa, when it comes to time for decision akanshi da komai nasa, sannan duk abunda taga ya dace akanshi tayi deciding babu ruwanki a ciki"
"What??"

"Yes sannan na biyu daga ranar da any of them ya nuna bayason wannan auren za a raba shi, and lastly hiding and grounding him has to come to an end"
Shuru tayi na yan seconds, badan batada wani option ba babu abunda zaisa ta yanke wannan mummunar shawarar,
Da mamaki yaji tace "okay"

Wani irin murmushi kawai khaal yayi ya girgiza kanshi, tabbas akwai abunda hidaya ke shiryawa, kuma akwai kwakwaran dalili dayasata yanke wannan shawarar, the last thing da zasuga hidaya tayi shine wannan, jinjina rashin tunani da rashin mutunci irin nata kawai yake yi....

Saida suka gama magana ta fuce daga sitting room din, sabeeha na tsaye saida jamid yace ta tafi tukunna kafin ta tafi, likita kuwa already shima ya fita ya rage daga khaal sai jamid.
"Khaal maysa ka amince bayan kasan kudirinta"
"Jamid I'm still giving her benefit of doubt, i still dont want to believe intentions dinta,"

"Then why did you agree" jamid ya sake tambayarshi don ya bi ya damu

"Because i trust my instincts, mu zuba mata idanu"

"Yanxu khaal aurar dashi za kayi? What if ya dawo hayyacinshi? Kana ganin bazai jawo matsala ba? Bamusan yarinyar nan ba? Bamusan ya rayuwarsu da gidansu yake ba? What if akwai problem"

"Kaga hidaya? Bazata taba yin komaiba ba tare da tayi dogon bincike da tunani ba, tasan komai game da yarinyar nan, her family and all, jamid dont worry kaji, allah zai shige mana gaba, i have a feeling that the outcome of this will be good"

"Shikenan khaal yaushe za ayi auren"
"Anjima after dhur, a masallacin nan tahilia"
Khaal ya amsa shi.
***
Bayan salat dhuhur jamid ya miqa auren SABEEHA dalhatu ga Khaal wanda ke wakiltar TAJUDEEN taheel.
Babu mutane da yawa cikin masjid din, su shida ne kachal according to yanda sunnah ta qai'dar, mutun uku shedu, sai biyu dake wakiltar wanda zasu aurar sai malamin dake jan sallah a masallacin.
Harda certificate khaal yayi sighning na aurensu bayan an daura da sadakin ta har riyal dubu ashirin.

Tunda aka daura auren Jikin jamid yayi sanyi, he's having weird feelings about this, yana jin wannan auren da akayi ba dan alkairi akayi shi ba don yasan hidaya sarai, saidai ya kasa gane dalilin dayasa tayi suggesting hakan, kamar yanda khaal yace, yayi fatan alkhairi kawai, hakan yayi.

sallama khaal yayi mashi bayan ya bashi copy of the halal marriage certificate din kafin ya tafi shi kuma ya wuce gidan.
Koda ya shigo sama ya wuce direct, neman hidaya ya soma yi a saman bai ganta ba, kwata kwata bai kawo tana part din taj ba.

Zama yayi ya dafe kanshi tunani kala kala
Na yawo a kwakwalwar shi,tunawa da wani abu yasa ya wuce part dij taj.

Anatse bude kofar da mamaki ya ganta zaune gefen taj wanda murna ta gama lullubeshi saboda ya ganta a kusa dashu, hakoranshi sun kasa rufuwa tsabar murna, karasowa jamid yayi har inda suke kafin ya kalleta, murmushi tayi mashi tace "kun dawo ashe?"
"Yea mun dawo, fito ina son muyi magana"

Daman tasan hakan zata kasance don haka ta miqe ta rada ma big baby abu a kunne nan take ya qalqale da dariya yace "first love ina jiranki please ki dawo"
"Okay big baby"

Shi ya fara fitowa tana biye dashi a baya saida suka zo daidai bedroom din nasu ya janyo hannunta ya tura ta cikin part din ya rufo kofar.

Hannunta ta nade a kirjinta tana kallonshi tana jiran abunda zai ce mata "hidaya, bana son wani boye boye, fadamin menene dalilinki na auren?"

"Saboda shi ne what is best for big baby?"

"In what aspect?" Ya sake doka mata tambaya
"Bakaji abunda doctor ya fada ba ko sai na maimaita maka?"

"Kina tunanin bansan abubuwan da kikeyi its for your own benefit bane? What do you want this time around?"

Wata iriyar dariya tayi kafin tace "jamid listen to me, i don't care what you think rn, all i know is, I'm doing what is best for him, so please stay out of this"

"Hidaya kiji tsoron allah"
"In banji tsoronsa ba kai zanji tsoro?" Ta gaya mashi magana kafin ta wuce bedroom, certificate din auren data gani kan coffee table ne ya tabbatar mata anyi auren, ba karamin dadin hakan taji ba dukda bata nuna masu a fili ba, saidai wannan ne kadai last option.

Bangaren sabeeha, ta kasa gasgata abunda kunenta ya jiyo mata a sitting room, tunda ta wuce bangaren su na maaikata ta zauna samun kanta tayi da zuba da hawaye mara dalili, gaba daya ta shiga confusion, na farko ta kasa gane menene kudirin wannan mutumin daya turota leqen asiri, sannan abunda yafi daga mata hankali sosai har taie tambayar kanta shine, wanene wannan mutumin, meysa yake controlling dinta, sannan ya akayi yasan da maganar aure? Tun kafin ayi maganar har ya umarceta akan ta amince, karta yi gardama, fatanta daya da takeyi shine allah yasa hakan ba anyi shi bake don ayi amfani da ita don a cutar da friend, don sai yanxu take ganin komai is revolve around him, tasan tana kula dashi amma meysa za a aura mata shi? Mey zata ce ma mahaifiyarta? Why the need of the aure? Waima wani irin aure? Basu san ta ba bata sansu ba? Anya babu cutarwa a cikin wannan abun?""innalillahi wa inna ialaihi rahiun" ta soma furtawa, take hankalinta ya sake tashi sosai, gashi shes confuse babu wanda zai bata amsa kawai saita fashe da kuka, yaj dakin su kuwa mey zasuyi banda kallonta babu wanda yayi attempting yaje wajenta don yaji meke damunta.
Ranar dai ko part din taj din bata sake komawa ba saboda wani matsanancin ciwon kai daya saka ta a gaba.
Bangaren su fadwa, afiya babu irin zage zagej da batayi ba har fadwa ta gaji da ita
"Ke wai mene ruwanki? Why would you care?" Fadwa ta tambayeta,
"Dole na damu mana, wallahi tallahi na tsani ukty, bana kaunar ganinta akan wannan mahaukaci, yanxu ta manta ta sanadiyarshi yanda komai ya sauya mana? Farin ciki mu? Jin dadin mu da komai? Yanxu harta manga yanda muka taso cikin kunci? Childhood dinmu babu walwala babu komai dukdan saboda shi?, wallahi idan har ku bakwa kishin ummuh to wallahi ni inayi, "
Kuka ta fashe dashi " why would she care? Maysa zata so shi fiye damu? Meysa zata damu dashi fiye damu? Why?"

"Shiyasa nace wani sa'in kanki wallahi kamar na kifi, you're so annoying, yanxu kukan na menene kikeyi? Ta rigada tayi deciding so sai me?"

"Malama karki fada min maganar banza, ba tun yanxu ba ke ma nasan kina bin bayanta mteww, duk abunda takeyi akanshi baki taba complain ba kamarma ke baki damu ba kwata kwata, i need fresh air i cant with all of your nonsense" tana kaiwa nan ta fuce daga dakin


****
Zaune suke cikin wani parlor babba, daya na zaune wajen masaukin baki, daga gefe kuma wani saurayi ne a tsaye, suna nan zaune saiga wani mutumi ya fito, babba ne mutumin don ga furfura ne ta mamaye fuskanshi gaba daya, yana da qiba sosai, sanye yake da farar jallabiya sai rawani da yayi a kanshi, wata baqar jaka ce a hannunshi, yana karasowa parlorn wanda ke tsaye yayi saurin matsowa ya karbi jakar.

Na zaunen ne yayi saurin miqewa yana girmama shi, kallonsa babban mutumin yayi kafin ya zauna, dariya ya soma yi "great job doctor!"

"Thank you sir"
Kallonshi mutumin ya sakeyi kafin yace, "kana da kaso mai tsoka saboda wannan labari daka bamu, akwai ticket dinka to bangkok, your new job awaits you from there"
Da sauri ya miqe ya karbi jakar "thank you sir thank you sir"
"You can go now"
Fucewa doctor yayi yana murna, don wannan ba karamin kaso ya samu ba, yayi mamaki sosai kuma akan just dan information din daya basu,wannan abu yayi mashi dadi sosai.
Yana fita mutumin ya kalli yaronshi yace "prepare babban kamfanin gidan yada labari, gobe inason a tashi da latest labari kai rikitarwa kan dan taheel kuma heir of the company is mentally unstable, zanga ta yanda za ayi wannan kamfanin ya cigaba da bunkasa, over this years sai yanxu zamu samu damar kawar dasu daga industry dinnan hahahahaha"
"But sir ya zamuyi da wannan likitan?"
"Wipe him off,kasan duk wanda yamin aiki yana gamawa bana barin shi da rai saboda threat so just finish him"
"Okay sir"
Yaron ya amsa shi kafin ya futa daga parlor, wata iriyar dariya babban mutumin yayi kafin yace "its high time" hahah

Abdullah ibn basit kenan, babban competitor kuma tantirin dan kasuwa, yana cikin Manya manyan masu kudin tahlia district sannan yana kasuwanci daban daban, duk wani harkar business da taheel sukeyi shima yanayi, yana da baban campany saidai baikai taheelz ba don shi bai dade da shiga kasuwancin ba, ba kamar taheels ba da su kasuwancin su suka gaje sa daga wajen iyayensu har yayi accending to yayansu.

Abdullah ibn basit shine babban dan adawar taheel, tun kafin marigayi taheel ya rasu har zuwa bayan mutuwarsa, bayan mutuwarsa ya dauka kamfanin zai durkushe sai kuka yazo yafi da ma habaka, babu irin bibiya da harin da abdullah baya yi ma taheel company, amma abun yaci tura shekara da shekaru ya kasa samun abu guda daya dazai kama wanda zai sashi ya danqwafar da kamfanin a bayan fage kenan, a gaban duniya kuwa an shaida abdullah as aminin taheel kuka na hannun damanshi don shine wanda ya maida abdullah mutun a yanxu, ya dauke shi ya bashi aiki a companyn shi lokacin da bashi da kowa har ya maidashi mutun ya ajiye shi a kusa dashi.


ABUJA...
Kallon maqudan kudin dake gabansu jamila tayi kafin ta kalli mijinta, "jamila, anya wannan abun kuwa babu wata matsala? Wannan uban kudade ki duba fa ki gani?"

"Mai gida mai kake nufi kenan? Waye zai sani? Kaga ni wallahi babu abund aya shafeni, kudi kuma wallahi kashesu zamuyi muma mu shigo gari, wannan miliyan biyun ka ajiyesu kason mu ne sauran miliyan daya dake account dinka kuma zamu dinga bawa hadiza da kadan kadan karta fuskanci wani abun"

"Amma hadiza bamusan fah wani hali yarinyar nan ke ciki ba, an kira mu ne kawai an bamu kudi kuma ance saboda ita, Basu fada mana mene kudinrinsu ba fah? Da dalilin turo kudin? nidai tsoro nake ji wallahi"

"Kai matsalar ka kenan in kasan haka ne meysa kayi karyar kaine mariqin ta kuma maisa kayi karyar iyayenta duk sun mutu ? Ay naga son kudin ne kaima yasa kayi karyar, saida muka karba kuma zakace wani tsoro kake ji?, amma dai tsaya yanxu da gaske daga chan kasar saudiyyan aka aiko? To saboda me? Kai koma dai saboda menen oho chan ta matse masu, koma mey ya sameta achan ko sayar da ita akayi wannan ba damuwata bace ba, ita kanta uwarta ba damuwa zatayi da hakan ba dukda bazan fada mata ba"
"Toh shikenan" mijin jamila ya amsa ta.




Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 29-30

Saudi Arabia.....
Monday morning!!!

Washe gari ta kama monday, wannan rana ta kasance rana wadda mutane da dama suke jiran zuwanta, hidaya tun wajen karfe bakwai ta bar gida don ko breakfast batayi ba.

Jamid ne ya kai barad school kafin ya dawo, lokacin daya dawo wajen karfe takwas na safe, abubuwan da suke faruwa tsakanin jiya da yau sun tsaya mashi arai ga fargaba da yake ji, anan compound din soma jin hayaniyar ma aikata sun hade waje daga, da mamaki yake kallonsu don sunbar ayyukan da sukeyi.

Kauda kanshi yayi daga kansu kawai ya wuce cikin gidan, bai tsaya ko ina ba sai hanyar dazai sadashi da stairs zuwa sama daidai nan fadwa ta fito daga bangaren ta, batama lura da jamid ba ta nufi wajen tv ta kunna news wayanta na hannunta, daman kiranta mijinta yayi ya shiada mata abunda ke faruwa.
Rasa ma wace tasha zata shiga tayi .

Headline din da jamid yaji ne yasa ya tsaya chak bai sake daga kafarshi da niyar tafiya ya yayi saurin maida dubanshi ga tv din, ga headline nan a kasa anyi rubutu da manyan harufa, " reported news; heir of taheel groups has been grounded and hidden to the world because of amnesia"

Saurin chanzawa fadwa ta sakeyi ta shiga wani news channel din, nan ma cece kuce akeyi akan wannan breaking news din, akan company taheel, da gudu jamid ya sauko kasan baima san sanda ya warce remote din hannunta ba ya soma kara volume don jin abunda ake cewa,

Nan take kuma aka sauya headline din zuwa sabo, inda aka hasko hidaya a zaune zatayi press conference, dabas jamid ya zauna akan kukera yana kallon tv babu ko kiftawa,
Intoduction ta farayi kafin reporter din suka fara mata tambayoyi, " madam shin da gaske ne heir din kamfanin taheel group kuma qani a wajenki yana fama da ciwon hauka? Madam meysa kuka boye wannan? Munason musan dalilin da yasa duniya bata san da haka ba?"

Saida ta gama jin tambayoyin su wasu ma sukarta sukeyi da tambayar, suna gamawa ta soma magana.
"Na farko wannan official announcement zanyi Tabbas heir din kamfanin taheel group yana fama da critical traumatic amnesia wanda yasa bayyanashi ya zame mana babban threat a gareshi da mental illness dinshi"

"Does that mean grounding dinshi kukayi for your benefit ko saboda kada tattalin arzikin kamfanin ku sauka?"

"Noo, i can't publicly explain why but saboda health dinshi ne"

Wani reporter ne daya rufe fuskanshi da mask yace "does that mean situation dinshi is critical kenan meaning hauka yakeyi kenan?"

Shuru tayi suka zuba mata idanu sai faman haskata ake da cameras, jamid dai kasa dauke idanunshi yayi akanta yana jiran jin abunda zata ce, to his surprise sai yaji tace " yes, situation dinshi is critical, i dont want to use the word hauka but i can say something similar cause he's like good for nothing"

Wannan statement datayi ba karamin hargitsa komai tayi ba mutane sunyi mamaki sosai don kamar tayi destroying komai,

Wani ne cikin reporters yace "yanxu a wani mataki taheel group yake ciki? Zaku sayar da kamfanin ne? Ko zaku bari wannan ya zama downfall din legacy din? As we all know babu yanda za ayi companying yayi running without the heir"

Murmushi hidaya tayi kafin ta kalli wanda yayi magana tace "bazamu bari gumin iyayenmu da a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login