Showing 54001 words to 57000 words out of 131802 words

Chapter 19 - MATAR TAJ HAUSA NOVEL

27 Sep 2024

25363

bayanin komai after an yi mashi running test din kwakwalwarshi.

Sallama yayi masu ya tafi, gaba daya kasa motsawa sukayi anan suka kwana harda hidaya, sai wani nan nan take da taj din, jamid dai kallonta kawai, yanxu tunaninshi baya kanta sai taj ya farfado tukunna.

Washe gari doctor ya sake dawowa, har zuwa lokacin bai farfado ba, jamid harya fita ya dawo, nan ya tadda hidaya, shifa lamarin tsoro yake bashi saidai ta bashi tausayi ganin yanda kamar ta damu sosai saidai sanin halinta yasa ya kauda tunaninta aranshi kawai.

Koda suka gaba gwaje gwajen su doctor ya soma masu bayani.
maida dubansa yayi ga hidaya hannunshi na rike da file din taj din. "madam this is a not a good sign"

" dalilin dayasa nace wannan is not a good sign shine, daman na fada maki, ba tun yanxu ba, kanshi ya soma tabuwa, ba komai ya kawo mashi haka ba sai maybe akwai abunda ke triggering dinshi, is there any sabon activity da yake yi?"
"Babu" ta amsa shi, "shiyasa na hana kowa muamala dashi saboda abunda ka fada min" ta sake bashi amsa yanda kasan sun tsara yanda suke maganar, yana fada tana bashi amsa, "hold on a second!" Jamid ya dakatar dasu,
"Kuyi min elaborating yanda zan gane da kyau? Menene dalilin dayasa kika hana kowa mua'amalar dashi"

Ajiyar zuciya doctor ya sauke kafin ya soma jero masa bayani, "sir, maganar gaskia stage din da yake yakai traumatic, wannan yasa mukayi blocking duk wani abu da zaisa ya tuna rayuwarshi a baya saboda wannan zai iya leading to trauma kuma wannan shine babban risk din condition dinshi yanxu ma haka we should be thankful akwai wani a kusa da shi don da babu kowa da zai tsayar dashi zai iya kashe kanshi don abun na triggering dinshi"

Hankalin majeed ba karamin tashi yayi ba, hidaya dai na daga zaune ta rike hannunshi taj din tana sauraronsu harda dan hawayenta.
"So what's happening to him doctor?"

"A gaskia for now dole haka zamu hakura har ya wuce stage din,ma'ana dole abar wani a kusa dashi kuma abun da ya faru jiya kan iya faruwa
Koda yaushe anytime, sannan i must say, who ever is staying with him should be someone who knows him so well and knows how to calm him down"
Jamid ne ya kalli hidaya yace "as far as i know yafi yarda da hidaya akan kowa"

"No sir" doctor ya katse shi, hidaya dai cije leve kawai tayi jin abunda jamid ya fada
"Sir, i will advice kar madam ta Zauna dashi, zamanta dashi is the biggest risk, saboda ita kadai ce bai mance ba, saboda tana da matsayi babba a zuciyarshi da gangar jikinshi, ganinta koda yaushe kan iya jawo wata matsalar daban"

Charab hidaya ta chapke, "wannan dalilin yasa na hana kowa kusantar shi ciki kuwa harda kai da khaal harma dani kaina, I'm doing all of this for him,"
Jamid dai bai kalleta ba saidai yana sauraronsu daga ita gar doctor din.
"So what do you suggest?"
"Ina ganin wannan yarinyar dake zaune dashi, why not ita ta zauna dashi koda yaushe, she's the only person da bai taba sani ba a rayuwarshi achan baya, and ina ganin keeping her around will help him in someway"

Tunani jamid ya soma yi, "but kace leaving her around him will be risk, and you advise a barta tare dashi how those that make sense?"

"Majid please, kamar yanda doctor yace lets do whats best for him, ... " ta katseshi.
Maido da dubanta ga doctor tayi tace "doctor please what else? Please let us know abunda ya kamata ayi?"

"For now, zamu cigaba da monitoring dinshi saidai kawai wannan yarinyar ta kasance tana tare dashi kawai"

Godiya hidaya tayi mashi shima jamid ya mashi kafin ya fuce daga dakin, yana futa jamid ya kalli hidaya "ki je ki huta, i will take it from here"

Kamar jira kuwa take tace "okay kafin ta miqe"
Kissing kumatun big baby tayi kafij ta fuce daga dakin, jamid dai har zuwa lokacin mamaki yake.

Hidaya na fita ta wuce bedroom dinta,wayarta ta zaro ta soma dialing wata number, ana dagawa ta soma magana "good job,"
Tana fadin haka ta kashe wayan ta danyi yan danne dannen ta kafin ta ajiye wayar ta wuce bathroom.
Doctor na fita ya shiga motarshi daman baizo da health team dinshi ba, yau shi kadai yazo, yana shiga motarshi ya soma waya,
"successfully......" yana fadin haka ya kashe wayar ya fice daga compound din.
...




Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 27-28

Update!!!

Da sallama ta shugo dakin, tsakanin jiya da yau harta fada, wajen wuyanta yayi jaa sosai sanadiyar shaqeta dayayi, babu wanda ya lura da hakan, "good morning sir"
Ta gaishesa cikin ladabi, "morning" ya amsa ta

Yana son tambayarta abu saidai kuma baya son yasa ta fara tunanin wani abu dakyar dai ya soma mata magana cikin dabara, "did he do that?" Nuni yayi da wuyanta, ashe ya lura, sunkuyar da kanta tayi kasa ta kasa bashi amsa, sai hawayen dake shirin zuwan mata.
"I'm sorry about that but why didn't you call me?"
Nan ma shuru tayi ta kasa ce masa komai, saida ya sake maimaita tambayar "karkiji komai tell me why?,"
Harga allah tsoro take ji saidai yanda taga ya damu yasa take jin kodai ta fada mashi, amma ta ina zata fara? Me zata ce mashi, madam ce ta hanata kira ko me? Zaima yarda da hakan kuwa? yatsun hannunta ta soma murzawa yawanci haka take idan tana tsoron fadin abu, ita kanta ta kasa gane alamuran dake gudana a gaban idanunta, komai is questionable daga wunin jiya zuwa daren jiya,
Tattaro sauran maganar data rage mata a baki tayi ta soma magana "sir i couldn't leave him, sabod aina tsoron inna tafi wani abu zai sameshi"
Badan ya gamsu ba ya girgiza mata, sun dauki kusan yan mintuna a haka kafin ya kalleta yace "shekarun ki nawa?"
"I'm 19 sir" ta amsa shi.

Girgiza kai yayi yana tunani, Haka kawai he just feel like explaing to her about the condition, bayani ya soma yi mata da avunda doctor yace, to his surprise sai yaji ta amince, dukda yaga abunda taj din ya mata a wuyanta, she's willing to stand by him.

Ba karamin mamakin haka jamid yayi ba, toh kodai dan kudi take yin duka wannan? Ya tambayi kanshi tunawa da yanda take kula dashi da nuna damuwa dashi ya tabbatar mashi kudi bazaisa tayi hakan ba maybe haka take kuma zuciyarta ce mai kyau.

Fita yayi ya barsu a daki, koda ya fito bai wuce ko'ina ba sai gidan khaal don ya mashi bayanin al'amarin taj din.

Da daddare taj ya farfado, kamar koda yaushe hidaya ya sake tambaya, saida sabeeha ta lallaba shi kafij ya hakura.

Cikin dare wajen karfe daya kamar jiya da daddare haka yauma ya tashi ya soma dube dube,sabeeha baiwar allah tuni ta farka daga gyangyadin data soma, yau allah ya taimaka bai tashi ya dunga bugun kanshi ba sai kukan daya dunga yi yana marin fuskanshi, kuka sosai ya dunga yi babu yanda batayi dashi ba yaqi dainawa, karshe ma dai itama kukan ta somayi tana hadashi da allah ya bari, saida ya jigata dan kanshi ya hakura har safiya idanunshi a bude, sunyi jaa har wani baqi baqi dukayi daga wajen fatar eyelid dinshi.

Sabeeha dai ta maidashi kamar tv, sai kallonshi take gwanin ban tausayi.

Karfe biyar daidai saiga jamid yazo, babu yanda baiyi dashi ba akan ya kwanta yaqi, saima kuka daya cigaba yana kiran first love first love dinshi.

Lokacin sallah nayi jamid ya tafi ya barsu shida sabeeha, mikewa tayi ta dauro alwala anan bathroom din kafin ta futo ta tada sallah, ta dade sosai tana mashi addua, tana idarwa ta juyo ta kalleshi.
Ya rame sosai ya chanza kamar bashi ba, he was so lively cikin kwanakin da suke wuce amma tsakanin jiya da yau ya chanza gaba daya.

After 1 week
Yau cikon sati guda kenan da wannan situation din na taj, saidai abun ya dan lafa ba kamar ranar da doctor yazi ya dubashi ba da next day.

Sabeeha na kula dashi sosai haka zalika jamid, shima kullum yana tare dasu don shi baya futa office zuwa caffeee dinshi, shi ke da companying caffe mocha, dan karanin kamdani ne dake producing traditional coffee, hidaya kuwa kullum tana hanyar office kullum, ba laifi tana shugowa dakin tana dubashi saidai yawanci lokacin da take zuwa yaja barci.

Su afiya da fadwa kuwa rayuwar su sukeyi hankali kwnace ba tare da sun damu ba, basu ma damu dasu san meke wakana da rayuwar dan uwan nasu ba. Tunda ba a saka su a ciki ba suma basu kai kansu ba don babu abunda zasu iya mashi.

Saturday morning....
Karfe bakwai daidai sabeeha ta samu ya koma barci, saida tabbatar yayi nisa kafin ta fito daga bedroom din tayi gyare gyaren ta, tana gamawa ta sauka kasa, don kullum saita sauka ta sauya kayanta.

Tunda ta sauko maids dinnan suke kallonta suna tsegumi, batabi ta kansu ba don basu ne damuwarta ba, abu daya daya dan dameta shine rabonta dataga yar ghana tun ranar data sauko kasa neman head, harta kamata tana labe, tundaga ranar bata sake ganin ta ba, gashi bata shiga al'amarin sauran maids din balle ta tambayesu inda take.

Wanka tayi tana gamawa ta koma kitchen, inda ake ajiya masu abuncinsu na maid ta nufa, daya daga cikin pack din ta dauka ta koma daki.
Saida taci tayi nak ta dauki hijab dinta data wanke a toilet ta futa dashi donta shanya.


Wajen shanyan nasu yana daga baya wajen garden, babu kowaa wajen sai birds din dake kara a wajen da sauran kananun dabbobi da aka ajiye don kawata wajen.

Tana gama shanyar ta juyo, a razane tayi baya ganin daya daga cikin maida din gidan, kallonshi tayi shima ya kalleta, duban wajen ya soma yi ganin babu kowa yasa ya fidda wayan dake hannunshi ya zura mata a aljihun gaban rigarta kafin yace "incoming call for you"
Yana kaiwa nan kamar iska yabar wajen, gaba daya sabeeha ta gama tsorata, tama rasa me zatayi tana nan tsaye wayar ta soma ruri, cikin sauri ta zaro wayar daga aljihun nata, number ce ke kira, wani irin tsoro ne ya durar mata "meyzaisa wannan maid din da bata taba ganinshi ba dukda ba futowa take compound ba balle ta sansu don maza ke kula da compound din, meysa ya bata waya? Gashi kuma ana kiran wayan gashi kuma ya tafi"

Daukan wayan tayi tasa a kunenta ba tare da tace uffan ba, wata kausashshiyar murya ce ta daki dodon kunenta.

"You're doing a good job,muna monitoring duk wani movement dinki,ive never taught you're this smart, abunda bamu taba tunani ba kuma hankalin mu baizo wajen ba kin nuna mana hanya, firstly to gain your target trust, wonderful for that, Secondly yanxu aikin naki zai fara,"

Jikin sabeeha ne ya soma rawa, dube dube ta soma yi hankali a tashe, babu abund atake sai innalillahi a zuciyarta, tabbas ta gane wannan muryar, muryar mutumin daya zo yace mata zatayi leqen asiri anan, gaba daya tama manta sai yanxu, ashe suna kallonta, tsoro ne ya durar mata, me mutanen nan suke so? Mene dalilin kawota da sukayi? Har yanxu kanta ya kasa daukan komai
Katse mata tunani yayi ta hanyar cewa


"Don't worry your self, aikinki mai sauqi ne, like i said yanxu ne ma zaki fara aikin naki, i don't want to say abunda zai biyo baya idan kika kuskura kika bata mana plan, by now kinsan dalilin dayasa muka kawo ki gidan, your part of work is so simple"

"Sir please meysa kuka kawo ni gidan nan mai zan maku?"
Sabeeha ta fada adan tsorace, gaba daya attention dinta ya koma ga wayar.
"Just do as i said, idan kikayi hakan rayuwar mamanki will be spared"

"Mamana?, sir dan Allah kuyi hakuri, ni wallahi bansan may zan maku ba"
"Its so simple, now listen..."
Ya dade sosai yana mata maganganu a wayar kafin ya kashe, confusely sabeeha ke kallon wayar, ta kasa gane meysa yace tayi abunda yace tayi, ta dade soaai tana tunani har tazo to a conclusion, tabbas akwai wata boyayyi a cikin wannan gidan, gidan nan cike yake da abubuwa da dama wanda kanta ya kasa warware mata.


Khaal....

Da mamaki Khaal ya tashi da kiran hidaya, rabonshi da ita tun lokacin daya zo akan maganar taj, tun daga ranar kawai ya zuba mata idanu.

Shiri yayi cikin kamala, kafin ya futo,"abuh!!! Abuh!!!"
Wasu yara suka taho a guje wajenshi, yaran suna kama dashi sosai, da mamaki yake kallon su, "karku buge fah"
Mamansu ce ta fito sanye da abaya da alamu futa zasuyi, kyakyawa ce Masha allah, a kalla zata kai shekaru talatin da yan kai, takowa tayi ta rungume shi kafin tace "ya habibi"
"Habibty, daga shopping sai ina?"
"Zan kaisu disney land daga nan zamu sawo gida my love"
Murmushi yayi mata kafin yace "nima zanje tahlia"
Shuru tayi jikinta yayi sanyi lokaci guda tace "allah yasa yau ka samu ka ganshi"
"Ameen" ya amsa ta
Kissing dinta a kumatu kafin ya futa.

Khaal is about 58years amma in ka ganshi zaka ce bazai wuce shekaru talatin ba, yayi aure very late hakan yasa bai da yara manya, ba kamar dan uwanshi ba taheel da yayi aure yana mid 20s dinshi.

Motarshi ya shiga ya fuce daga compound din yana zullumin kiranshi da hidaya tayi.

Gidan ya nufa direct, lokacin daya karaso doctor taj ya karaso shima, gaisawa sukayi da khaal kafin su shiga daga ciki,
Khaal tunda yaga doctorn taj din hankalinshi ya dan tashi, yasan dai jamid yazo mashi da bayanin situation din taj din don shike zuwa ya fada mashi abunda ke faruwa game da taj din.

A tare suka karaso cikin main sitting room, babu kowa a ciki don haka suka samu waje suka zauna, jamid ne ya fara saukowa da mamaki don baiyi tsammanin ganin khaal din ba, yanxun hakan ma ya fito ne don ya wuce gidanshi, gaisawa sukayi har kasa ya rusuna kuwa ya gaishesa kafin ya zauna "yanxu nake shirin zuwa chan gida ay"
Murmushi khaal yayi yace "zuwan ne nima i wasn't expecting it"
Da mamaki jamid ya bude baki zaiyi magana saiga hidaya ta sauko, afiya na gefenta da fadwa, karasowa sukayi suka gaishe da khaal, hakimar ma yau fiska a sake ta gaishesa, mamaki dai bai sa khaal da jamid rufe baki ba.

Shuru ne ya biyo baya kafin hidaya ta soma magana "akwai dalilin daya sa na taraku saboda decision din dana yanke akan big babu, which I believe kuma ga doctor dinshi, ya bani kwarib gwigwa akan hakan"

Gyara zama khaal yayi a zuciyarshi yana hamdala don tabbas kiran nan datayi mashi akan lafiyar taj dinne saidai yayi mamakin yanda akayi harta sauko haka kuma ta nemeshi? Wannan abun ya bashi mamaki sosai.

"Base on yanda doctor shi yayi mana explaining situation din da yake ciki yanxu which I believe duk kun sani, I've come to conclusion which I believe zai taimaka mashi sosai kuma its a step that maybe or may not lead to his recovery but I'm trying to believe it will"

Sabeeha ce ta sauko kasan, kanta a kasa, yau gaba daya bata jin dadin jikinta kwata kwata, da head taci karo tana shirin fitowa daga kitchen da maids a bayanta kowannensu hannunta riqe da baverages, saida ta bari suka wuce kafin ta nufi hanyar shiga kitcehn din.


Karo suka kusa yo da maid din data fito, cikin sauri sabeeha tayi baya, "sorry about that" sabeeha ta fada, dayar maid din da suka kusa gwarawa kuwa kasata zube da alamu ko rashin lafiya take yi, kallonta sabeeha tayi tace "are you okay?"
"No, I'm burning up, please help me with this"
Taimaka mata sabeeha tayi ta miqe kafin tace "you can go and have a rest, zan gyara maki"
Godiya maid din tayi mata kafin ta fuce daga dakin, tana futa sabeeha ta kwashe abubuwan da suka zubar kafin ta sauya wasu, daman savate ne, tana gamawa ta juya ta futa daga kitcehn din, kalle kalle ta somayi don neman inda head sukabi, rasa hanya tayi don haka harta juya kuma ta tsaya, ganin head yasa ta tsaya har suka karaso, "what are you doing standing here?
"Sorry head, batajin dadi ne shine na karba"
"Jeki ajiye ki fito" head tayi commanding dinga.

Takawa ta somayi, bugun zuciyarta na tsananta, harta shugo ciki, lokacin data shugo doctor nayi masu bayanin situation din da tak ke ciki, sannan ya dora da kanshi ya soma tabuwa, tana jin wannan ta saki savage box din batama san tayi ba, juyowa sukayi gaba daya su suka kalleta, dakata doctor yayi yana jiran ta futa kafin ya cigaba don dukda ya ganeta,

Statement din da hidaya ta jefo masu yasa duk suka juyo suna kallonta, babu ins atake kallo sai inda sabeeha ke tsaye don tana kallonta saboda opposite inda take sabeeha ta tsaya, "you come here"

Kafafunta ne suka soma kyarma, kamar munafuka haka ta karaso wajen, sauran duk suka bita da idanu, daga chan gefw sabeeha ta tsaya kafin hidaya ta maida dubanta gare su.

Jamid ne yayi dakewar cewa "what did you just say?"
Maido da dubanta tayi garesa tace "i said zanyi ma big baby aure!!!!!!"

"Aure?" Fadwa ta fada tana kallon hidaya surprisingly
"Ukty you must be joking, wa kike ganin zai auri mahaukaci? Good for nothing man? Mai kwakwalwar yara wow this is too much gaskia ukty you're doing too much," Afiya ta fada a gatsale.

Wata uwar tsawa hidaya ta daka mata "don't you dare say that again, and yes, aure zanyi ma taj because I believe shine best decision.

Jamid ne ya sake kallonta rai a bace yace "hidaya are you sure kinsan me kike fada kuwa?"

"Yes i do," ta bashi amsa kai tsaye, yana kokarin sake magana khaal ya daga mashi hannu,

"Waye zaki aura ma TAJ din?" Khaal ya tambayeta yana mai kallonta, lallai bai taba tunanin haka hidaya take so heartless ba, jamid dai kasa komai yayi ranshi yayi mugun baci, lallai yau ya tabbatar hidaya bazata taba chanzawa ba, shi yasan definitely akwai wata a kasa.

"Her!!!!!"
Dammm gaban sabeeha ya bada ganin ana nunata, saurin sauke kanta tayi kasa furgici bayyane a idanunta, kallonta suka komawa yi daga kan khaal zuwa su afiya da fadwa, "maid??? Wow" fadwa ta fada a ranta

"Wannan personal caregiver din taj

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login