Showing 66001 words to 69000 words out of 131802 words

Chapter 23 - MATAR TAJ HAUSA NOVEL

27 Sep 2024

25360

ranar da taj ya cika shekaru ashirin da tara khaal ya samu hidaya da maganar dawowan shi, Lokacin daya fara maganar dawowan nashi bata nuna mashi komai ba Saima shaida mashi datayi zai dawo idan ya kammala second degree dinshi da yakeyi, wannan excuse din data bayar yasa khaal yyi shuru bai sake cewa komai ba, ana nan har shekara ta sake zagayowa inda taj ya cika shekara talatin cir a duniya, nan ne fa khal ya miqe tsaye shima akan dole sai taj ya dawo saboda ya karbi responsibility dinshi a matsayin shine da namiji a Cikin familyn, babu irin matsalar da khaal bai samu ba daga hidaya, inda ta nuna mashi cewa babu wanda ya isa ya fada mata yanda taj zaiyi rayuwarshi, she's doing what is best for him, kuma karatun da yakeyi shi zai amfana, duk wannan excuses din data dunga bayarwa are not valid to khaal, don ya kasa gane wannan wani irin karatu ne, taj yabar saudi yana da shekaru sha bakwai a duniya and now it's over 13 years.
sai a lokacin ya fara ganin true intentions dinta saidai har zuwa lokacin yaqi aminta da hakan ne, kwata kwata bata ganin girmanshi kamar ba kanin mahaifinta ba, har tazo ta kaiga bashida ta cewa akan alamuran family din, wannnan abu yayi mashi zafi sosai har ya fara tunanin rabuwa da ita da qannen nata suyi abunda sukaga dama don su afiya ma sun kangare, sai abunda sukaga dama sukeyi, saidai tunawa da dan uwansa da amanar daya bar mashi yasa kawai ya danne duk abunda ke mashi zafi ya cigaba da hakura da abunda takeyi.
Da taimakon jamid da shareholders khaal ya samu yayi forcing dinta dole ta sashi dawowa, ranta yayi mugun baci ganin harda jamid a cikin waenda suke jayyaya da ita akan taj, babu irin isa da bata nuna masu ba akanshi saidai tasan tunda shareholders suka shugo alamarin dole ta hakura kuma babu yanda zatayi ta sauya yanda rules din suke, saidai har zuwa lokacin bata nuna masu taqa maiman dalilin daya sa ta hanashi dawowan ba saima nuna masu shine baya son dawowa da takeyi.

Hidaya dai tsara ma taj rayuwar da zaiyi tayi, tun achan england ta chusa mashi qiyayyar dawowa kasar, saida ta tabbatar ya saba da nan din sosai har yaji baya son barin kasar.

England
Wayarshi dake cikin aljihunshi ce ta soma ruri, daga kwancen da yake ya ajiye dumbells dake rike da hannyenshi guda biyu, dagowa yayi zaune ya gyara zamanshi kan weight bench, greyish idanunshi da gashin ido suka kwata luff luff akai ya soma budewa, bin wajen yayi da kallo mutane maza da mata jajayen fata kowa na hada hadarshi, daman yawanci anfi zuwa during weekends.
Kyakyawan saurayi ne ajin farko, gashi fari tass shima, zufa ta gama wanke shi sanadiyar workout din da yakeyi incoming call din ya katseshi, Sanye yake da fitness hoodie mai gajeran hannu da ta dan kamashi don ana iya hango shatin 6packs din dake a shafe wajen cikinshi, gefen damtsen hannunshi wani dan baqin zane ne kamar tattoo dan karamin, sai wani short da leggings daya saka daga ciki, kayan sunyi masifar amsar jikinshi dayake maintaining physique dinshi, he's so fit and huge.

Wayar dake ta faman ruri ya zaro yana mai kallon screen, ganin wadda ke kiranshi, ya sashi saurin cije lebenshi da sukayi jaa kafin ya sauke wani irin sanyayyan murmushi mai melting zuciyar mata.
Daga wayar yayi cikin hanzari ya soma magana yana mai lumshe idanunshi ya sauke ajiyar zuciya sound of relief
Puffy lips dinshi ya soma motsawa ahankali
"First love!!!" Ya furta cikin muryarshi wadda bata futa sosai at the same time yana lumshe ido jin muryarta kadai.

Saurin miqewa yayi, wayar har zuwa lokacin tana hannunshi don akwai airpod a kunneshi, dagowa nayi don kallon asalin height dinshi, yana da tsayi da jiki mai kyau, masha allah kawai za ace.
Magana akayi daga chan wadda ya sashi sakin wani irin murmushi kawai.
Wayar ya zura cikin aljihunsa kafin ya duki katon bottle dinshi ya nufi hanyar futa daga gym din.
Toilet din gym din ya fara shiga ya cire hoodie din tashi yayi wanka kafin ya sauya kaya zuwa waenda yazo dasu wasu arnayen english wears designers.
Sense of dressing dinshi is just different, daga gani yasan irin shigar dake mashi kyau.
A gurguje ya gama ya saqala agogoshin sannan ya saka wani shade baqi ya futo da back pack dinshi.

Daidai inda motarshi take ya nufa ya danna keys din, cikin arniyar sport car din tashi ya shiga, yana shiga ya kunnata kafin yayi reverse yabar wajen.

Anatse yake driving cikin kwarewa, fuskanshi har zuwa lokacin dauke da murmushi, hannunshi daya na kan steering yana murzawa cikin kwarewa ga sound din cool music na tashi.

Tafiyar minti goma ta kawoshi airport, yana parking ya fito bayan ya rufe motar tashi.
Cikin airport din ya nufa bai tsaya ko ina ba sai private lounge na arrivals,yana zuwa ya soma dube dube ko zai ganta, daga chan nesa kuwa ya hangota a tsaye tana waya, tana sanye da abaya sai baggage dinta dake gefenta.

Ganin fuskanta kawai ya sashi sauke wani irin murmushi mai wuyar fassara.
Takowa ya soma yi har zuwa inda take, sai a lokacin ta lura dashi, sanin abunda zaiyi yasa ta daga mashi hannu alamun ya dakata, chak kuwa ya tsaya yana murmushi yana kallon fuskanta ba tare da ya damu da gwale shin datayi ba don harya bude hannunshi yana shirin rungumeta, kallo daya ta mashi ta dauke kanta daga kanshi, saida ta gama wayan kafin ta maido da dubanta gareshi, fuskanshi kawai ta zuba ma idanu, ya kara kyau ba kafan ba compare to last zuwan da tayi, shi kamar ma kullum kara kyau yakeyi da cikar ido.
Cikin british accent dinshi a shagwabe yace "first love" kafin ya rumgumeta gaba daya, "i missed you so much first love"
Shuru kawai hidaya tayi tana mai sauraronshi harya gama kafin ya saketa, "daga ina kake? I've been waiting"
"Sorry for keeping you waiting first love"

Ba tare da ta kalleshi ba fuskanta na nan yanda take ba yabo ba fallasa, duban agogon hannunta tayi kafij tace "next flight dina zai tashi in the next 10 mins, seat let's have a chat"
Zama sukayi yana kallonta da mamaki, ganin haka ya sata cewa "ba zama nazo yi ba, i had to stop by saboda inason muyi magana."

Attention dinshi gaba daya ya bata ya natsu sosai cikin ladabi yace "okay first love"

"Get ready by monday inason ka dawo saudi"
Cikin sauri ya dago yana kallonta, girgiza mashi kai tayi alamun yes kaji abunda na fada,
"No but" ta katseshi don tasan abunda zai fada kenan,
Sunkuyar da kanshi kawai yayi yace "okay, i will" ya amsa ta cikin ladabi.

"You're going back for good," ta sake fada ba tare da ta kalli fuskanshi ba, fuskanta a hade kamar hadari babu digon murmushi ko dariya

Gabanshi ne ya fadi, meysa first love zatace haka, ayyukanshi na nan fa? Tech Business company dinshi da yake running fah? yana son ya tambayeta dalilin hakan saidai bazai iya ba don hakan kamar jayyaya ne da ita.
Sama sama suka danyi discussion kafin time flight dinta ya gabato har lokacij ya cika kafin ya mata sallama, har cikin wajen check in ya rakata kafin suyi sallama.

Jiki a mace ya dawo, bai tsaya ko ina ba sai tech company dinshi, wajen kamar repair shop ne da harkar kere keren abunda ya shafi karfe da motoci technically, babban elegant tech shop ne sosai mai girma ba kadan ba, yana da employers sunkai su goma kowanne yana aikinsa da bangaren da yake ma aiki, tsayawa yayi yana kallon wajen, "Autofix,"
Nan take ya fara tunanin yanda ya fara wajen, tun tasowarshi yake son harkar motoci, he's so into automotive technology, wannan yasa yayi karatun engineering, koda ya fada ma hidaya bata musa mashi ba ta amince akan yayi abunda yake so wanda hakan ya mashi dadi sosai don a ganinshi tayi supporting abunda yake so, wanda hakan yasa yake jinta sosai aranta,
Wajen ya kasance one of his happy place kuma its like his dream he build it da kanshi tun wajen bai zama abunda ya zama ayanxu ba, daman yana da passion din wannan.
Wannan autofix din nashi ya samu recognition a England city, don ba karamin waje bane, yana harka da manyan company's inda suke kawo mashi ayyukansu daya shafi kere keren abubuwan fannin electronical technology.
Yana cikin top members na desiging team din hyundai,wannan yasa ya zama popular sosai achan.

Wajen ya zama popular for both maza da mata masu zuwa da motocin su, matan ma dai zuwa suke saidai su zuwansu saboda owner din wajen ne, saboda he's resistable, babu wanda ya taba tunanin shi ba citizen kasar bane don yana da connections sosai.

Wannan nasarorin daya samu hidaya bata sani ba kwata kwata, don bashi ne a gabanta itadai duk a ganinta wannan part din daya zaba shine daidai dashi as long as baya tunanin dawowa.



*****
Tsaye suke a wajen parking space din arrival,hidaya na daga tsaye tana receiving call while su fadwa da afiya suna daga tsaye bakin mota,cikin yan mintuna kalilan saiga mutane sun fara fitowa daga gate din international arrival, kallon gate din fadwa da afiya suka soma yi, yau ce rana ta farko da zasu sanya shi a idanunsu tun bayan tafiyar shi, saida aka gama fitowa gaba daya basuga alamun shi ba.
"ni zan koma cikin moto na nikam..." fadwa ta fada

Kasa karasa maganar dataso yi tayi inda idanunta sukayi capturing dinshi yana fitowa majestically, saurin tabo afiya fadwa tayi,

A natse yake tafiya yana tunkaro inda suke hannunshi rike da baggage dinshi sai dayan kuma ya rike jacket dinshi, fuskanshi sai walqi takeyi don ya tara beard wanda ya qara ma fuskanshi kyau sosai, dukda yana jin wani irin fargaba hakan baisa ya sauya yanayinshi ba, gaba dayansu sakin baki sukayi banda hidaya da ta bama bangaren da yake futowa baya tana amsa waya.

fadwa ce ta kasa boye expression dinta beneath her breath tace "wowwwww"
afiya dai tabe baki kawai tayi tana kallon ikon Allah don ya chanza gaba daya kamar bashi ba, shekara goma sha uku kenan.

TAJ kenan, the charismatic handsome young man, he's a definition of perfection tafiya yake majestically cikin kananun kaya, fuskanshi yasha wani baqin glass daya haska fuskanshi.

waige ya soma yi kafun idanunshi su sauka kan hidaya data juya baya, dukda baiga fuskanta ba jikinshi ya bashi itace saboda kaunar da yake mata koya makance zai iya sensing intana waje.

gaba daya baima gane su fadwa ba don tun bayan tafiyar shi bai Kara ganinsu ba don basa zuwa duba shi chan england.

Yana karasowa ya rungume hidaya "first Love"
Katse wayar datakeyi tayi tare da hadiye wani mugun miyau, lokaci guda wani irin baqin ciki ya turniketa, ta dauka kusan second talatin a haka kafin ta daidaita natsuwar ta tare da sauya fuska kamar ba ita ba ta juyo inda yake fuskanta dauke da murmushi

"welcome back big baby, finally Ka dawo Zan samu peace of mind"
Murmushi yayi wanda ya fadada fuskanshi ya Kara mashi kyau ya sake kallonta yace "I'm so happy to see you,meysa kika tsaya a cikin rana? Banason kina wahalar da kanki first love"
Hannunshi ta dan saki ta kauda kanta gefe tace "dole nazo Ay na tarbeka my baby brother"

Gyaran murya ta danyi kafin ta kalli inda su fadwa ke tsaye kamar gumaka suna kallonsu, kowacce da irin abunda take ayyanawa a ranta

"Bakaga sisters dinka bane?" Hidaya ta tambayeshi tana kallon inda su afiya ke tsaye
Maido da kallonshi yayi ga inda take mashi nuni, daya bayan daya ya kallesu, yanayin fuskanshi ya dan sauya kafin ya karasa inda suke ya rungumesu ba tare da yace masu komai ba.

Fadwa ce kawai ta iya ce mashi "welcome" afiya kuwa cikin motar ta koma tana takaicin dalilin da zaisa hidaya ta tilasta sai sunzo daukan shi.

Bangaren hidaya bazaka taba iya tantance a wani irin yanayi take ciki ba saidai deep down tana jin wani irin tashin hankali da bacin rai a zuciyarta da wannan dawowar tashi.

Wannan rana ta kasance mafarin da zai sauya rayuwar shi da kaddarar shi, ranar da rayuwar shi zata sauya daga rayuwar daya saba, ranar da farkon babin rayuwarshi mai dauke da sarqaqiya zai bude.



Cigaban labari....


Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 34-35

Cigaban labari.....

Bayan futar hidaya daga bedroom din fadwa ta kalli afiya daketa faman zubda hawaye, itama ranta ba karamin baci yayi ba ta soma magana ''ay daman saida na fada maki, kanki kamar na kifi,how could you even think about that?''
Saurin kamo hannunta afiya tayi ''haba fadwa, meysa baki fada min tun wuri ba, wallahi bansan haka abun yeke ba' na dauka duk wadannan abubuwan da ukty keyi saboda tana sonshi ne''
''Ke baki da Ido ne saina fada maki? Saurin fuzge hannunta tayi daga na afiya tare da yi mata kallon kin bani mamaki kafin ta fuce daga bedroom din rai a bace itama.

Tana fita afiya tayı saurin share hawayenta, nan take kuma ta sauke wani murmushi mai wuyan fassara akan fuskanta.

Bangaren hidaya daga bedroom din afiya direct ta wuce study room dinta dake sama, idanunta yayi jaa sosai, fadin yanayinta a wannan lokacin bashi misaltuwa, tana shiga ta rufo kofar daidai nan jamid ya fito daga bedroom dinsu, kallon study room din nata yayi kafin ya kauda kanshi ya fuce daga part din nasu.


sabeeha dai tunda ta shiga dakin su bata fito ba, gaba daya ta gama shiga confusion da wannan ala'amarin dake faruwa da ita, tsoro fargaba babu wanda baya yawo a cikin ranta, har zuwa lokacin ta kasa gasgata abunda ke faruwa, aure dai data sani, yau itace keda aure akai, kuma auren wanda baima san ina kanshi yake ba, kuma aurenda babu sanayyar iyayenta akai sannan itama an yi conering dinta, don harga allah bada saninta haka abun zai juye ba, haka ta kwana tana hawaye, ta rasa dalilin dayasa ita rayuwar tazo a haka, mey zata cema mahaifiyarta?.yanxu idan aka kamata fa a matsayin yar leqen asiri?, bama wannan ba, ayanxu dai ta tabbatar ana son ayi amfani da ita ne wajen cutarda wannan mara lafiyan, abunda ta Kasa ganewa shine meysa za a turota nan gidan, kuma maysa ka aura mata shi? da wannan tunanin barci barawo ya fusgeta

washe gari ta kama talata, shirinta ta fara yi yanda ta saba koda yaushe cikin uniform dinta, gaba daya jikinta a mace daga yanayin yanda take shirin ma, tana gamawa ta fuce daga bangarensu na yan aiki.

saman part dinshi ta wuce direct, kamar kullum saida ta fara gyaran part din cikin natsuwa kafin ta nufi dakinsa lokacin wajen karfe takwas na safe.
koda ta bude kofar dakin sanyin ac ya bugeta take taji wani irin yanayin mai wuyar fassara ya risketa, haka kawai taji wani irin sauyi a tattare da ita, kallon inda yake kwance tayi, ganin bashi kwance sannan bedside lamp dinshi a kunne ya tabbatar mata da ya tashi, a gurguje ta gyara mashi beddings din gadon kafin ta shige closet room dinshi ta debo mashi kaya riga da wanda masu laushi farare tass wanda ya saba sakawa.
tana kokarin ajiye mashi su a bakin gado taji yo ihu daga toilet din.
cikin saurin ta ajiye kayan ta nufi wajen toilet din ta soma knocking ''friend are you okay?''
yana jin muryarta ya fashe da kuka, ba tare da tunanin komai ba sabeeha ta bude kofar tana mai kokarin rufe idanunta don bata san a wani yanayin zata taddashi ba, kasa rufe idanun nata tayi ganinshi jikin bangon bathroom din jikinshi har bari yake ya tamke idanunshi baima ga sabeeha ba, kallon bathroom din sabeeha ta soma yi don ganin abun da ya tsorata shi haka, idanunta ne ya sauka kan dan karamin kenkeson dake crawling a wajen, maido da dubanta tayi gareshi inda yake pointing abun,kasa dauke idanunta tayi daga kanshi, yana daure da towel a waist dinshi, take taji wani irin tausayinsa ya mamayeta, ya za ayi ace wannan katon ne ke tsoron dan wannan mininin abun, baifi ya takeshi da kafarshi ba.

hannunshi ta kamo cikin sauri ya waro idanunshi don ya tsorata sosai, ganin sabeeha ya sashi saurin rungumeta gaba dayanta ya rufe ta ruff, cikin sauri ta rufe idanunta, yauce rana ta farko data taba jinta jikin namiji kaff duniyar nan, abun yazo mata a bazata, saurin hankadashi tayi ya koma baya, kokarin dawowa ya soma yi zai rungumeta tayi saurin dakatar dashi,
''kaga na dauke abun bazai maka komai ba''
kallon tiles din yayi ganin babu kyankyason yasa ya sauke wani murmushi har kumatunshi na lobawa, fuskanshi har wani walqi takeyi saboda annuri, bata san lokacin da itama ta sauke wani murmushi ba, ''thank you bibi''
da mamaki sabeeha ke kallonshi jin sunan daya kirata dashi, ''waye bibi?''
da yatsan shi yayi nuni da ita tare da dungure mata goshi, ''you!! you're my bibi my hero, you save me''

samun kanta tayi da kallon lebenshi dake furta sunan, ''yanxu wannan ne aka yima aure jiya? aure dai na mata da miji?, saboda me? why? what's the reason?'' haka ta dunga saqe saqe cikin zuciyarta, motsin data ji daga bedroom din ne yasata saurin juyawa ta futo daga bathroom din shima ya biyo bayanta.

kallonsu jamid dake tsaye yayi, saurin gaishesa sabeeha tayi kafin ta fuce daga bedroom din, kallonta jamid yayi harta fuce kafin ya maida dubansa ga taj dake tsaye da towel rike a kugunshi don bai iya kullewa ba sosai.

excitedly ya soma magana fuskanshi dauke da murmushi ''good morning uncle''
''morning big baby'' jamid ya amsa shi yana kallon fuskanshi, hannunshi jamid ya kama suka zauna bakin gado
''how are you today?'' jamid ya sake tambayarshi yana mai kokarin janshi a jiki sosai
''i'm fine uncle, i slept well''
kallonshi jamid ya soma yi yana wani tunani, kwata kwata babu wani improvement a tattare da rashin lafiyar taj, wannan abu yana damunshi sosai.

''taj'' ya kira sunan shi
''yes uncle''
''zanje england zaka bini?''
shuru taj yayi kamar mai nazarin wani abu harda sanya dan yatsa a gefen bakinshi, ''uncle england? ina ne england?''

''bakasan england ba? achan fa ka taso har kayi karatu ka manta?''
confusely yake kallon jamid, ganin haka yasa jiki a mace jamid

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login