Showing 126001 words to 129000 words out of 131802 words

Chapter 43 - MATAR TAJ HAUSA NOVEL

27 Sep 2024

25364

lura baima san taqamaimain abunda sukeyi ba daxun, dole tayi protecting dinshi daga wannan yar iskar tsohuwar budurwa tashi, tunawa da hakan yasa ranta ya kara baci, "ko wace iriyar rayuwa kukayi a baya oho, banda iskanci tsotsoj bakin fa takeyi? allah na tuba me zakayi da wannan mai kama da kosan oho, gaba dayanta kamar wata sandar rake mteww"
Da harshen hausa ta karashe maganar shiko confusely yake kallonta, "ka daina kallo na da wannan idanun naka, ni fushi nake dakai"
Still bai gane me take cewa ba "bibi what are you saying?"
"Never mind me, sleep good night"
Kwanciyar yayi ya jawo duvet dinshi yana kallonta yace "Okay night"
Inda ta saba kwanciya itama ta kwanta ta juya mashi baya, "bibi what language did you use daxu? Can you teach me"
Da batayi biyar kulashi ba chan kuka saita juyo gefen bangaren sa yake tace "its called hausa, from nothern nigeria, kasan nigeria?"
"Nigeriya? Wheres nigeriya?"
Yanda ya fada yasa ta dan murmusa tace "ba nigeriya ba its nigeria, zan koya maka gobe okay?kayi adduar barci"
Excitedly yace "okay thank you bibi"
Rufe idanunshi yayi ganin haka yasata kashe masu bedside lamp suka kwanta.

Next morning...
Yaudai sonata bata zoba kamar yanda take zuwan sassafiyar nan, kamar kullum as usual wanka yayi ta taimaka mashi da kayan sawa, tana kokarin gyaran gadon daya kwanta akai, hidaya ta shugo part din, lokacin yana cikin bathroom yana sauya kaya

Tana shugowa tabi dakin nasu da kallo, har idanunta ya sauka kan sabeeha, rabon data shugo part din harta manta,sabeeha na ganinta gabanta ya fadi, harga allah ita duk sanda taga hidaya sai gabanta ya fadi don komai nata babu alkairi a ciki sai sharri,
"Sabahal khair" sabeeha ta gaisheta kanta a qasa ko da wasa bata bari sun hada idanu ba,
Kamar yanda bata saka ran amsa gaisuwar tata ba hakan ta kasance ba don ko kallonta batayi ba.
Daidia nan ya futo daga bathroom bayan ya shirya yana ganin hidaya ya karaso cikin hanzari excitedly yanda ya saba ya kwala mata kira
"First love!!!!!" tare da karasowa inda take ya rungumeta tsam a jikinshi,fuskanshi dauke da murmushin farin cikin ganinta yace "good morning first love!"
Fiddoshi tayi daga jikinta ta zuba mashi idanu kamar yau ta fara ganinshi, "how can i believe he's not pretending? Ya warke ne already ban sani ba?I cant trust him neither can I trust kowa, harma da doctor din daya shiada min hes mentally ill, zai iya yuwu ya hada baki da khaal? Dole nayi wani abu akan haka"
kallonta yayi fuskanshi dauke da murmushi ganin tayi shuru,katse shurun tayi tace
"Kayi breakfast?" Ta tambayeshi kai tsaye tana kallon cikin idanunshi.

Girgiza mata kai yayi hannunshi na cikin nata "no ukty"
Jin haka yasa Hidaya sauke wani murmushi ta dubi inda sabeeha ke tsaye tace "join us"
Da mamaki sabeeha ke kallonta, bugun zuciyarta na ninkuwa, tun lokacin datayi threatening dinta da taj hankalinta ya tashi da hidayar, gashi babu damar fadama jamid, jikinta babu laka haka tabi bayansu zuwa kasa, anan kasan kuwa already duk sun fara karin kumallo, jamid ne kawai baya cikin su, ganin shugowar su yasa suka bisu da kallo, sonata na ganin sabeeha ta bita da wani irin kallon tsana, tareeq ma nayin arba da fuskar sabeeha ya hade rai sosai, fadwa da afiya kuwa tunda suka shigo suke kallon taj suna jinjina lamarin shi, yanxu shine T-ford? One of the young billionaires?

Ganin yanda yake maqale da hidaya da yanda yake acting kamar wani yaro yasa suka jinjina kai, yanxu idan duk pretending hakan yakeyi akwai matsala, dolema su san yanda zasuyi wajen tabbatarda da gaske yanada amnesia din ko kuma pretending yakeyi.
"Hello big baby" afiya ta daga mashi hannu fuskansta dauke da murmushi, dariya yayi mata yace "hello ukty"
"Zoka zauna kusa dani yau ni zan baka abunci a baki"
Turo mata baki yayi yace "nop kusa da first love zan zauna"
Yana kaiwa nan ya karasa kusa da kujerar hidaya ya zauna,kallon sabeeha hidaya tayi tace "serve him"
Ta umarceta, jiki a mace sabeeha ta karaso wajen ta dauka dinner set ta zuba mashi abuncin dake wajen, Tosted bread ne sai baked beans da chip, a jikin toast din ta shafa mashi peanut butter tana gamawa ta faki idanunsu tayi tasting abunci a bakinta, hidaya ce kawai ta lura da ita saidai batace komai ba, gabanshi ta tura mashi abunci yace "thank you bibi"
Nuni da kujera chan nesa hidaya tayi mata tace "seat"
Jiki a mace sabeeha ta zauna a chan gefen ta danyi serving kanta

Spoon ya dauka ya soma cin baked beans din da chips yana gamawa ya dauki bread din har yakai bakinsa ya dan dakata saboda kamshin dayaji yakai mashi ziyara, hidaya dake lura dashi tana ganin ya daka ta dan murmusa aranta tace ,"let's see idan zaka ci abunda kasan zai iya kasheka lokaci guda"

Murmusawa tayi tana mai kallonshi, cikin ranta ta fara tunani, he's allergic to peanut tun yana karami, akwai ranar da mistakenly yaci peanut take jikinshi ya karade yayi jaa sosai, sai wasu kuraje da suka soma feso mashi kamar an hankado su, take ya soma kakari kamar zai mutu, saida aka kaishi ER urgently aka mashi emergency allergy shot, kafin ya samu sauqi ranar kamar zai mutu saboda yanda jininshi ya kasa functioning a jikinshi saboda jininshi baya son peanuts ko kamshin yaji sai ya samu reation, ranar ne suka gane yanada Anaphylaxis ( severe potentially life-threatening allergic reaction ) da zarar yaci koma menene indai yanada hadaka da peanut, ba komai ke zama a cikinshi ba,Abu qalilan ke tada allergy dinshi specifically peanut din dai kuma tasan har yabar saudi ya koma london he's still allergic to it, shiyasa koda yaushe yake yawo da allergic shot a jikinshi, duk inda yaga peanut kuwa hankalinshi Tashi keyi.
Ganin har zuwa lokacin baikai bakinshi ba yasa tace "kaci mana"

Dagowa yayi ya kalleta tare da kaiwa bakinsa yayi one bite, da gefen ido duk suke binshi da kallo, babu abunda suke sai murmushin mugunta, shiko bawan allah baisan kudirinsu akanshi ba haka ya dunga turama cikinshi harya cinye tass, tun kafin ya gama ya soma kakarewa, dagowa sukayi gaba dayansu suna kallon, sonata na ganin yana nuni da ruwan tayi seizing chance din ta miqe tare da diban ruwa daga dispenser dake wajen ta miqa mashi,tana mai cewa "sorry babe"
sabeeha dake zaune a gefe ko dagowa batayi ba balle ta ga kayan takaici, su fadwa kuwa daman haka sukeso.

Tun kafin ya karba ruwan, jikinshi ya soma yin jaa sosai, daga fuskanshi zuwa idanunshi ya karade, hanunshi na karkarwa ga kakarin tarin daya soma tunkudo mashi, ruwan ya karba ya kwankwanda kadan
A maimakon ya lafa saiya sake burkicewa ya miqe zumbur, kiftawar idanu saigashi wasu kananun kurajji sun feso mashi fesss kamar yaqi, jikinshi na tsuma, sonata dake patting bayanshi take ta lura da yanayin da yake ciki,"hey whats wrong?"
Take ya soma kuka, nunfashinsa na seizing, fuskanshi tayi jaa sosai, sai a lokacin sabeeha ta dago ta kalleshi,cikin hanzari itama ta miqe tsaye ta soma ambaton Allah, hidaya na kallonshi tayi fuska tana mai cin abuncin gabanta, ganin yana neman burkicewa yasa ta kallesu, kamar batasan meke faruwa ba ta miqe tsaye tace "menene? What's going on?"
Yanajin hannun hidaya yayi saurin kamata hankalinshi a tashe yama kasa magana, ganin haka yasa hidaya ta kalli sabeeha, "me kika bashi? What did you do"
"Wallahi ban bashi komai ba,"
Kallon plate dinshi sonata tayi ganin sauran bread din dayaci gashi an shafa peanut a jiki yasa tace "peanut?????His allergies" da mamaki suke kallonta su fadwa na mamakin yanda akayi ta san yana reacting to peanut.

Bin plate din da kallon sabeeha tayi tabbas ta saka mashi a cikin bread dinshi kuma suna kallo amma babu wanda yace mata hes allergic to peanut, take ta soma furta innalillahi, idan ta lura kudirinsu har yanxu yana nan akanta kenan? Sharri sukeson kulla mata.
Kakarin daya sakeyi ne yasa ta ajiye tunanin nata a gefe ta tunkaro inda yake tsaye, tana zuwa sonata ta ingizata gefe, "how dare you feed him peanut? Are you insane Kinsan me kikayi kuwa? This can cause him his life"
Rai a bace sonata ke magana, su fadwa me zasuyi banda nade hannayensu a kirjinsu,suna kallo, tareeq kuwa ko gizau baiyi ba yana daga zaune,sabeeha bata kulata ba ta sake tunkarar inda yake ganin yanda yayi jaa gaba daya ga kakarin da yakeyi, daga nan afiya tayi stepping up ta kama hannunta tayi baya da ita, "don't even think of taking a step, so kike ki kasheshi? How do you call your self his caregiver or so called wife?idan wani abu ya sameshi bazamu barki ba"
Jikin sabeeha gaba daya yayi sanyi sosai, kokari take sosai wajen hana kanta hawaye, Yau ga ranar jamid, gashi baya nan, gaba daya haka sukayi ganging dinta up a wajen, ita bama tasu take ba ta taj din take daketa faman kakari.

Dubansu hidaya tayi, sai yanxu ta lura sunyi amfani da wannan opportunity dinne don su qala ma sabeeha, ita wannan maid din yanxu ba itace matsalar ta ba taj dinne matsalarta da zargin da take akanshi da.

Futa hidaya tayi daga wajen, cikin yan mintuna kalilan sai gata ta dawo da allergies shot dinshi a hannunta, tana karasowa ta chaka mashi a hannunshi, Cikin abunda baifi minti biyu ba komai ya baje, hatta kakarin da yakema ya tsaya chaak sai jaa da jikinsa yayi ya soma bajewa, ajiyar zuciya ya soma saukewa akai akai kamar wanda yayi tsere,

Ganin komai ya lafa yasa hidaya cewa "take him to his room"
Miqewa sonata tayi dashi suka wuce bedroom dinshi, sabeeha na kallo ta fuce dashi har zata bi bayansu, afiya ta dakatar da ita, "you have the guts to? After what you did?"

"Let her go"
Hidaya ta fada ba tare da ta kallesu ba, juyowa afiya tayi ta kalli hidayar ranta a bace, meysa zata barta haka nan, zasu iya amfani da wannan damar din ganin su korata gidan, sabeeha kuwa najin haka tabi bayan su ta haura sama sai a lokacin hawaye kan fuskanta ya soma saukowa.
"Ukty meysa zaki barta ta tafi haka, meysa wai bazaki kori yarinyar nan ba"
Kallonta hidaya tayi tace "bana aikin gaggawa, lokacin da zan koreta daga gidan nan baiyi ba, zanyi amfani da ita don tabbatar da abunda nake zargi"
"Toh me kike tunani kenan? " fadwa ta tambayeta, kallon inda tareeq ke zaune hidaya tayi kafin ta maida dubanta ga fadwa, gaba daya sunma manta yana zaune a wajen har sun fara sakin layi, karar notification din wayarta dake hannunta yasa ta dubi screen din na yan sakanni, kafin ta fuce daga dining area din, tana fita afiya tabi bayanta.

Saman hidaya ta wuce zuwa part dinta ta sauya kaya kafin ta fito zuwa kasa ta fuce daga gidan, yau ko driver ta ma bata dauka ba tabar gidan.

A chan daki kuwa tareeq na shigowa ya tadda fadwa na shirin shiga wanka daure da towel, tundaga sama yake kallonta har kasa,shidai kwata kwata he don't find hwr attractive at all, badna kudinta ba bayajin zai iya zama da ita din jin dadin moriyar aure tsakanin ma'aurata.
Rugumeta yayi ta baya wanda hakan yasa ta taagaita nade gashinta dake nade a taakiyar kanta
"Habibty, it looks like we have a same goal da sisters dinki"
Dakatawa tayi tare da juyowa ta kalleshi tana mai daga mashi gira daya, "if you need my assistant just tell me anything, zan iya maki komai"
Dariya sosai sannan tace "basai ka fada ba, lokacin da zan buqace ka yana nan tafe"

Tana kaiwa nan ta bar wajen zuwa bathroom ta barshi tsaye yana nanata maganganunta akanshi.
Bangaren su sabeeha tana hawa saman ta tadda sonata a kan gadonshi, kanshi na kan cinyarta shi kuma yana kwance a gefe barci harya kwashesa, saurin futa tayi ta rufo kofar sonata ta bita da mugun kallo, ita kuwa baiwar allah bama ta yanda ta taddasu take ba, tausayinshi kawai takeji, dazun ta furgita sosai ganin yanda ya sauya lokaci guda, saita tuna da lokacin da akayi poisoning dinshi, maisa rayuwarshi ta kasance koda yaushe cikin masifa iri iri? Guilt din bashi peanut dinnan ya tsaya mata arai sosai, kwata kwata bata fatan ta zama silar da zaisa ya cutu, haka ta wuni a kitchen tana blaming kanta.

Sonata bata bar bedroom dinba sai wajen karfe sha biyu, karfe daya nayi sabeeha ta dawo bedroom din zatayi alwala, har zuwa lokacin yana barci, takowa ga somayi ahankali gudun karya farka ta gyara mashi kwanciyarsa ganin kamar ya takure, gefen gadon ta zauna tana kallon kyakyawar fuskanshi innocently,hannunta na dama ta daga kamar mai tsoron tabashi haka ta soma shafa fuskan nashi zuwa wajen jaw lid dinshi gemunshi dake kwance a wajen baki siddik, batasan lokacin da hawaye ya soma sauko mata ba, ayanxu batada burin daya wuce taga ya warke ya samu lafiya kamar kowa, yayi defending kanshi daga yan uwanshi da basa boye qiyayyarshi a fili, sannan ya koma rayuwarshi daya saba,ya zama namiji,

Batada burin daya wuce wannan ayanxu, ganin yana neman farkawa yasa ta zare hannunta tare da sauke ajiyar zuciya cikin ranta ta soma tunanin "ko yaushe zai samu sauqi? Allah ka dubi lamarin wannan bawa naka, ka tsareshi daga duk wani sharri"
Ta furta kafin ta juya ta miqe tsaye, karaf ya kamo hannunta ya rige gam, kafin ya bude idanunshi, yana ganin itace ya sauke mata murmushin daya sata jin wani irin, guilt din abunda ya faru dazu yana cinta sosai.
Kokarin zama yayi akan gadon ya fuskanceta Ganin tana kuka yasashi kamo fuskanta da hannayenshi biyu yace "bibi meysa kike kuka?"
Ay kanar ya zugata kawai saita fashe da kuka, ganin haka yasashi janyota jikinshi kamar yanda ta saba mashi idan taga yana kuka ko idan ya farka daga mumunan mafarki, ita kuwa tsulum ta shige faffadan kirjinshi, yauce rana ta farko data shige jikinshi sosai, sai taji wani peace of mind lokaci guda, hawayen nata na sun kasa tsagaita wa,kamshinsa da warmth presence dinshi yasa taji wani irin sanyi aranta, yanda ta shige mashi tana iya jiyo bugun zuciyarshi fatt fatt fatt kamar zuciyar zata futo har abun ya bata tsoro, saurin fitowa tayi daga jikinshi ta kalleshi tana mai taba kirjinshi wajen saitin zuciyarshi tace "didi, zuciyanka na buqawa sosai? Are you okay?"
Dariya yayi yana mai taba nata dake wajen kirjinta yace "bibi kema naki yana gudu sosai"
Kallon hannun nashi tayi dake kan kirjinshi sai kawai tayi dariya tace "naka yafi gudu sosai"
"Ban yarda ba Naki yafi gudu"
Haka suka wuni cikin nishadi shida ita.

**
Jamid na zaune cikin office din abokinshi dayayi stepping out, cikin yan mintuna aka sake budo kofar office din, "i can see youre so nervous"
"Of course i am qalam, hankalina bazai taba kwanciya ba saina tabbatar an kama suspect din kidnap dinnan"
Zama abokin nashi yayi yana fuskantarshi yace "im sorry to say this, abunda zan fada maka ba lallai kaji dadinshi ba"
"Just tell me qalam, hankalina bazai taba kwanciya ba saina kama wanda yayi sanadiyar mutuwar khaal sannan yayi tarning image dinshi"
Nunfasawa abokin yayi sannan ya soma warware file din dake gabanshi ya fiddo da evidence din da sukayi gathering yana gamawa ya miqama jamid din kafin ya soma mashi bayani, "wanan ne babban suspect dinmu, tony antony, also known as black, serial killer ne yanada charges goma akanshi na murder, he's been declared wanted for over 2 years now, inda ya gudu wata kasar,bayan ya badda kama, yayi fuce sosai wajen kisa ta yanda baya barin lead din da za a gane shine, wannan confidential information ne nake fada maka, ssd organization bata yarda a fiddashi ba musamman ga waenda ba ma'aikatanta ba, i have to go this far just to get this for you, saidai inason ka sani, irin waennan gangs din ba a taba kamasu, countless of time idan munso kamasu bama iyawa saboda akwai waenda ke protecting dinsu saboda dirty work din da suke masu, gudun kar asirin su yafito yasa suke protecting dinsu, so duk aikin dakaga sunyi an basu kwangilar yi ne, kuma yanzu tunda mun tabbatar shine yayi wannan aiki, definitely akwai master mind behind, duba ga yanda kidnaping dinsu kawai yayi ya zubar dasu a desert ba tare da ya illata su ba hakan ya kara tabbartar min da hunch dina and I believe yanama wasu aiki ne, most importantly"
Ya jinkirta yana mai sauya papers din zuwa ga na kasan su ya fidda hoton da aka dauka inda aka dauko khaal yana musayar hannu dashi kafin yace "as i concluded, this is framing, its a brainwashing trick, someone most be against khaal, don komai has fallen into places, its possible an bashi aiki ne yayi tailing dinsu saida ya tabbatar kabar asibitin kafin yayi stepping har yayi badda kama da suffarka da motarka sannan yayi kidnapping dinsu after 24 hours saiya kirashi wanda zaiyi tricking wato khaal kenan a waya ya umarci yazo same exact location dinnan da akayi hoton don ya shaida mashi inda suke daga nan ne suka samu opportunity sukayi hoto daya fidda khaal a cikin hoton da motar da akayi kidnap din, duk wanda yaga wannan babu wanda bazai yarda da cewa khaal bashida hannu a ciki ta wannan damar suka samu sukayi framing dinshi wannan ne hunch dina da zargin danakeyi kenan, saidai inason ka sani bude case dinnan zai zame mana babban aiki saboda an rigada anyi declaring wanda yayi kidnapping nasu which is khaal, amma inason nasan ko you have someone in mind da kake tunanin zaiyi hakan? "
Take gaban jamid ya fadi babu wanda ya fadi mashi arai sai hidaya, saidai deep down yanajin bazata iya kashe khaal ba, jininta ne kamar mahaifi yake a wajenta, saidai tunawa da yanda suke rigima akan taj da maganar poisen yasa yaji kawai zuciyarshi gana wasi wasi da lamarin, what if she went that far? What if shes behind all of this? Take yaji wani irin faduwar gaba mai tsanani, Dole yasan yansa zaiyi, idan haka ta tabbata to fa hidaya is very dangerous, zata iya yin komai kenan,katse mashi tunani qalam yayi ta hanyar bugun table din gabansu yace "you have someone on mind?"
Bakinsa na karkarwa yace "I'm not sure gaskia i have no one on my mind, but waye zai yi haka?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login