Showing 33001 words to 36000 words out of 131802 words
yana murmushi, kitchen din ta nufa ta duako mashi apple dinnan da warm water kafin ta dawo dakin.
Da sallama ta shigo, bin idanunta ya soma yi da kallo yana karantar abunda take fada, saida ta karaso har inda yake kafin shima ya maimaita abunda tace, kallonshi ta tsaya yi confusedly, kamar mai koyon abubuwa haka yake, wani irin tausayinshi ne ta sake ji kamar tayi kuka haka kawai taji she's so emotional.
''friend sit'' tana fada kuwa ya zauna,
Miqa mashi apple din tayi tace ''bismillah''
''bismillah?'' ya sake fada yana kallonta confusedly,
''ína nufin ka karba kaci'' nan ma kallonta ya dunga yi saida tace ''eat'' tukunna ya karba.
Abunda ta lura dashi kamar yana koyon abubuwa ne yanxu, ko kuma maybe saboda lalurar tashi ne yasa shi haka oho.
Yana kokarin cin apple din tace ''ga ruwan''
Karba ya sakeyi yana murmushi yace ''thank you''
Tsayawa tayi daga gefe tana kallonshi, kwata kwata bata yarda ta dauke idanunta daga ganinshi ba har y agama cin apple din a natse kamar wani hamshakin babban mutun, ita dai har yanxu wanna abu mamaki yake bata sosai, yana gamawa ya miqa mata glass din ruwan daya sha.
Juyawa tayi ta sake futa daga dakin kafin ta sake dawowa, lokacin data dawo ya cire rigar jikinshi gaban dayanta, yana kokarin zame dogon wandon jikinshi, tana arba dashi kuwa tayi saurin runtse idanun ta ''na shiga uku ni fatima'' juyowa yayi a tsorace ya kalleta, mazugin wandon na hannunshi bai kaiga saukewa kasa ba, takowa ya somayi don ya dan tsorata sosai saboda baya son ihu ko hayani ko sound ko kadan, hakan na furgitashi sosai, yana karasowa baiyi wata wata ba ta riko rigar jikinta kamar zai shige jikinta, take ta damke bakinta kuwa don kiris ya rage ta doka wata uwar kara jinshi a bayanta.
Karjarwar da jikinta ya soma yi ne yasa shi sake rikota sosai, ''friend friend, I'm scared''
Wannan furucin nashi ne ya sata jin wani irin,sai a lokacin ta tuna fa bashi da lafiyar kai, kuma yana abune kamar yaro don haka ta dan dake ta juyo ba tare da ta sake kallon jikin shi ba tace ''sorry friend don't be scared, me zakayi?''
''I want to shower and play friend'
Sai a lokacin ta tuna dole ita zata taimaka mashi yyi freshen up don haka ta soma kokarin zame rigar ta daya qanqame ba tare da ta sake kallonshi ba, hannunta ya sake rike wa don har lokacin a furgice yake, bata hanashi ba haka ta nufi hanyar kofar data gani a dakin, cikin ta shiga yana biye da ita, koda ta shiga kofofi biyu ne a wajen, daya daga cikin kofofin ta bude kafin su shige a tare.
Duk wani abunda tasan zai buqata wajen wanka saida ta hada mashi, yana tsaye daga gefe ya rike gefen rigarta, saida ta gama ta nuna mashi wajen wanka ''bismillah''
Kallonta ya sakeyi sai maida mata abunda tace nan take tace mashi ''you can freshen up now'' tana kaiwa nan ta soma cire hannunshi daga rigarta, yana ganin haka kuwa ya sake damqe rigar, ''wait for me friend''
Waro idanu sabeeha tayi jin abunda ya fada, ganin yana shirin janta zuwa wajen bathube din hakan ya sata kallonshi don dole badan taso ba ''no, zan jiraka a waje''
Haba wa tana fadin haka ya soma bubuga kafarshi a kasa kamar yaro, tashin hankalin da ba a saka mashi rana, yanda kasan tayi kuka haka take ji, anya zata iya wannan abun kuwa.
Wata dabara ce tazo mata ranta ''friend zan jiraka a waje kaji?, idan k agama sai muyi wasa tare''
Tana fadin haka kuwa ya saketa yana murmshi, tana ganin haka kuwa tayi saurin fucewa daga bathroom din tana haki.
Dayan dakin ta bude, wanda take tunanin nanne closet dinshi,kayan dake wajen kusan duk iri daya ne, fararen riga da wando, ko color daya babu, agurguje dai ta kwaso kayan ta ajiye mashi akan gado kafin ta fuce daga dakin.
Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Free page
Chapter 17-18
Update!!
Koda ya fito bai ganta ba sai yaji babu dadi aranshi,shiryawa yayi yanda hidaya ta nuna mashi don yana jin maganarta sosai yana gamawa ya zauna bakin gadon.
Tunda ya zauna ya zubama kofar shugowa dakin idanu ko zai ganta, sabeeha kuwa bata koma dakin ba saboda an gindaya mata sharudan shiga dakin, daman zata bashi maganin shi ne saita bashi breakfast daganan kuma saita taimaka mashi yayi wanka daga nan kuma bazata sake shiga dakin ba sai da yamma idan tazo bashi second dose.
Bayan Futar sabeeha daga dakin batayi gigin komawa dakinba saboda koba komai namiji ne kuma yana buqatar privacy bayan wannan ma bata son ta gane ma kanta abunda bai kamata ta gani ba saboda baya cikin hayyacinshi, don tundaga yanda ya soma kokari zame wandoshi kuma ya ganta ta tabbatar akwai gyara sosai a al'amarin.
kasa ta koma bayan ta kakkashe komai yanda head ta fada mata, harta sauko kasa yana ranta, saitaji kamar ta koma don ganin ko ya futo daga toilet din ko bai futo ba ko yana buqatar wani abun.
Jiki a mace ta shiga dakinsu, gaba daya tama manta da cikinta don ko karyawa batayi ba kuma it's past 10, yar Ghana da tsegumi ashe tana ankare da ita don ta jiyo lokacin da sauran maids ke gulman ta.
Abuncinta ma itace ta karbi nata ta ajiye mata don a pack pack ake basu kullum safe rana da dinner.
Koda ta shiga ko zama batayi ba saiga yar Ghana ta shugo itama da pack din abuncinta a hannunta,''new comer''
Yar Ghana ta kirata,juyowa sabeeha dake shirin zama bakin gadon tayi tana mai kallonta, cikin sassarfa yar Ghana ta karaso inda take kafin ta miqa mata pack din data shugo dashi, ''ga break dinky na karba maki''
Murmushi sabeeha ta yi duk da ba a ganin fuskanta kafin ta sanya hannu biyu ta karba pack din tace ''nagode.''
Murmushi yar Ghana tayi kafin ta soma rage murya ''ina aka kaiki?''
Shuru sabeeha tayi tana kallonta kafin ta sauke kanta kasa tace ''sama wajen madam''
Shuru yar Ghana tayi tana kallonta cikin nuna rashin yarda da abunda tace, chan kuma sai tayi murmushi tace ''na dauka wannan wajen aka kaiki, thank god ba nan bane, bari na koma wajen aikina bye''
Girgiza mata kai kawai sabeeha tayi kafin ta zauna nan bakin gadonta,pack din nata ta bude, fries ne sai kwai da aka soya yasha albasa.
Bismillah tayi kafin ta soma turawa cikin natsuwa, duk sanda zata kai bakinta haka zata dan janye mask din ta tura kafin ta maida shi.
Bayan ta gama zamanta tayi anan dakin ta doka uban tagumi, tunanin wannan mara lafiyan ne ya fado mata arai.
Taheels groups.....
Zaune take cikin kayataccen office dinta, the most trusted secretary dinta na gabanta, ga kuma wasu file dake ajiye akan table din office din, gaba daya yau ranta a mugun bace yake tun daga gida, ga kuma abunda ta riska anan office.
Kallon agogon dake maqale a hannunsa yayi kafin ya maida dubansa ga madam din nasa, ''ma'am lokaci yayi fa''
Tafin Hannayenta data rufe fuskanta dashi ta sauke kasa, sai kuma fuskanta data dago ta zuba mashi waennan idanuwan nata masu firgitawa, karantar facial expression dinta is so hard don gaba daya bazaka iya tantance a wani yanayi take ciki ba.
Mikewa tayi tsaye tare da ture kujeran dake bayanta kafin ta sagayo ''lets go''
Tana kaiwa nan ta nufi hanyar futa, shikuwa da hanzari ya bi bayanta da wannan files din, cikin takun isa ta fito daga cikin office din nata ma'aikata duk wanda ya ganta saiya tsaya yadan duqa mata cikin respect dukda bata bi ta kansu ma kwata kwata.
Bata tsaya ko'ina ba sai shareholders hall, secretary yana biye da ita a baya, koda tazo bakin kofar hall din shine ya bude mata kofar kafin ta shige ciki.
Mutanen dake zaune cikin hall dinne wanda akalla zasu kai su kusan guda goma sha biyar ne sukayi saurin mikewa don girmamata, bata tsaya wani amsar gaisuwarsu ba ta nufi hanyar wajen zamanta na musamman a tsakiyan dogon table din.
Zama tayi kafin kowannen su ya zauna suma, shuru ne ya biyo baya baka jin komai sai saukar nunfashin manyan mutanen dake zaune.
Secretary ne yayi opening meeting din kafin ya fara koro masu bayanin progress din da aka samu a wannan shekarar, hidaya dai binsu take da kallo daya bayan daya tana jiran taji wanda zai fara Magana, cikin waenda ke zaune kuwa harda uncle khal don shima shareholder ne sai sauran mutane da sukayi investing kudadednsu da waenda sukeyi partnership dashi.
Daya daga cikin manyan mutanen ne ya katse secretary, mutumin kowa yasanshi he's so bold kuma shi baya wani rufa rufa, don haka ya soma Magana ''wannan bashine purpose din meeting dinnan ba, munyi''
Sai a lokacin hidaya ta dago ta kalleshi, babban ne sosai don a haife zai haife ta kuma yana cikin waenda suka dade sosai suna investing a cikin company ma'ana sune waenda suka dade a cikin company kuma suna bada gudumawa sosai don ganin cigaban company tun marigayi taheel na raye.
Yanda take kallonshi haka yake kallonta, babu wani conering ya cigaba da Magana ''dalilin wannan meeting din shine, munason sanin dalilin dayasa wanda ya kamata ya karbi ragamar wannan company dinnan baiyi presenting kanshi ba har yanxu, yau kusan wata takwas Kenan, a yanda ka'idar business dinnan take da kowane company shine dole heir din owner of the company ne zai gaji wannan company ko next person In line'',
Hidaya najin haka ta maida dubanta ga uncle da ya hade hannayenshi a kirjinshi yana kallon wannan show din,
''madam munason sanin dalilin presenting dinshi bayan kowa yasan yanxu he's 30 kuma wannan ne ka''idar company, we understand your help and contribution in making this company standing on it's on, but...''
At this point idanunta sunyi jaa sosai, shi kuwa bai tsagaita bay a cigaba, ''but you're not enough madam, you can't run the company ko badan ka'ida ba, babu inda aka yarje mace ta rike company anan kasar, a woman can't rule the company, that's a disgrace to the taheel family and the company reputation as well''
Yana kaiwa aya gaba daya office din suka karade da cewa ''yes, that the fact''
Kan kace me nan take hall din ya kacame, wannan yace kaza wannan yace kaza, saida hidaya ta bari suka gama tass har lokacin kallon uncle take dake mata wani irin kallo,irin na barki dazu,
Runtse idanunta tayi kafin ta bude su ta daga hannunta biyu ta daki table din dake gabanta, nan take duk sukayi tsit bakajin komai.
Babu tsoro babu fargaba ta daga ma secretary hannu, cikin hanzari kuwa ya miqa mata wannan file din, yana miqa mata ta bude cover din file din kafin ta watso masu shi gaba daya,
Daya bayan daya suka soma dauka papers din don karantawa, ''idan kun gama karantawa let me know''
Tana kaiwa nan ta hade hannayenta a kirjinta tana jiran su gama, nan take kuwa suka soma zuru zuru da idanu don kowa da sunanshi a jikin papers don da duk abubuwan da sukeyi ta bayan fage, sunan uncle ne kawai babu a ciki, wanda yayi Magana ta fara pointing babu tsoron komai ta soma Magana ''you!!! with due respect, inason ka fada min waye a cikinku ya kamata na miqa ma company dinnan?''
''you!!'' ta sake fada tana nuni da wani dake gefenta, shi har ya soma balle maballin buttons din suit dinshi tsabar tashin hankali.
''kai dake da record of molesting workers, da harassment tsakanin ni da kai waye yafi dacewa ya jagoranci wannan company?''
Mutumin najin haka ya sauke kanshi kasa, idanunshi sunyi jaa sosai, wannan shine babban embarrassment din da akayi mashi agaban bainar jama'a kuma manya kamarshi.
Wata iriyar dariya tayi mai bayyanar da hakoranta kafin ta tafa hannunta ta maida dubanta ga dayan dake gefenshi tace ''and you... kaida kake da record of homosexuality, gayzism, kana nufi kaine ya kamata yayi ruling wannan company din?, how are you all better than a woman ku fada min''
Daya daga cikinsu ne ya dake, daga gani zaiyi kafiya yace ''mu bamuce muna son amsar legacy din family dinku ba, what we just want to know shine maysa har yanxu heir din wannan company din bazai karba muqaminshi ba''
Shuru hidaya tayi ta kasa cewa komai sai kuma chan ta saki wani murmushi, ''seems like you're are not understanding this language''
Jin haka ya tabbatar masu da abunda take shirinyi, wata bankadar zatayi masu gashi kowa yana tsoron kar ta fidda wani abun nashi don basu taba tsammanin hatsabibya bace ba sai yanxu,
''we're done for today''
Uncle ya fada yana miqewa, sauran mutane na jin haka kuwa suka mike kowannensu ya soma fita daga hall din, gaba dayan su tashin hankali ne karara a fuskansu, gashi a junan su ma baqin ciki suke ma juna kuma basa kaunar juna gashi lokaci guda wannan la'ananniyar ta tona ma kansu asiri a junansu.
Suna fita tayi ma secretary nuni da hannu akan ya basu waje, yana fita kuwa ta kalli khaal kafin ta soma tafa hannayenta tace ''wow, wow, wow, wonderful, that's a great attempt khaal, ni da kai kasan cewa idan mutanen nan suka san cewa wanda suke tambaya akai is not mentaly stable zasu iya komai don ganin sun karbi wannan company din daga hannu mu, kana tunanin zan bar haka ta faru?, no never, this is my parents legacy, my parents hard work, abuh and ummuh, so this is just the beginning khaal''
Tana kaiwa nan ta mike ta fuce daga office din ta barshi saqe a tsaye, hannunshi daya dungule yayi jaa sosai kamar gauta.
Hidaya kuwa na futa secretary ya mara mata baya zuwa office, wani irin sign of relief ta sauke kafin ta kalli secretary ''mun tsallake wannan, nasan bazasu hakura ba, zasu ta kawo hari with much questioning, inason kayi providing komai, da yanda mukayi planning komai''
''okay ma'am'' ya amsata kafin ya fuce yana murmushi.
Bayan futarshi Kenan ta, ta bude wata safe locker, wayoyi ne guda biyu sai wasu papers a cikin locker din, daya daga cikin karamar wayar ta zaro kafin ta soma dialing wata number, ana dagawa ta soma Magana anaste ''bana son dogon bayani, so guda nawa ne suka shigo hannu?''
Daga chan ne aka bata amsa kafin ta sake cewa ''okay!!''
Tana kaiwa nan ta kashe wayar ta maidata cikin locker din kafin ta maida dubanta ga papers din dake cikin safe locker, tunani ta soma yi chan kuma kawai sai ta rufe locker din ta cigaba da ayyukan dake gabanta.
Bangaren sabeeha, karfe uku da rabi nayi ta koma dakin nashi, a hankali ta soma bude dakin kamar wata barauniya, dakin duhu dum yanda kasan dare yayi babu haske babu sound din komai kamar babu rai a cikin dakin, ahaka ta dunga rarrafawa ta karasa tsakiyar dakin, sai data karaso bakin gadon ta samu dan hasken bedside lamb,
Bin kan gadon ta soma yi da kallo, barcinsa yakeyi hankali kwance hanunshi rike da wani puzzle solver da ake jujuyawa, ya nado jikinshi da pillow ya rungume.
Tsugunnawa tayi agaban gadon ta zuba ma innocent kyakyawar fuskanshi idanu daga kan lashes dinshi da sukayi zaro zaro ga dogon siririn hancinsa a mike kamar pile zuwa ga lips dinshi da suke a cike sunyi jaa kamar ansa mashi filler ga sexy jaw line dinshi mai daukar hankali sosai, kasa dauke idanunta tayi daga jaw line din nashi don wajen is so attractive duk da bata san attracting dinta wajen yake ba,maido da dubanta tayi ga huge kirjinshi zuwa ga arms dinshi, ya zakalo hannunshi ya rungume pillow a kirjinshi, ya rike wannan puzzle box din da yatsunshi, daga ganinshi yana amfani da musles equipment saboda yanda ya damke pillow din kamar za a kwace mashi pillow din har jijiyoyin hannunsa sun bayyana.
Samun kanta tayi kawai da murmushi ganin yanda yayi wani irin juya bakinshi alamun kosawa da barcin, samun kanta tayi da qin tashinsa saima kallonshi data cigaba da yai harta sakankance lokaci ya kure.
Kokarin tashinsa ta soma yi saidai tsoron yanda zai tashin take don ance yana furgita, wata dabara ce tazo mata kai don haka ta daga dan karamin hannunta ta soma shafa karan hancinsa ba tare da tayi making sound movement ba ko hakan zaisa ya tashi, shuru dai babu motsi saima nunfashi da yake saukewa a hankali, ta dade tana hakan harta maida tafin hannunta kan bare fatar skin din fuskanshi mai laushi kamar na sabon jariri, shafa fuskan nashi ta soma yi ko hakan zaisa ya tashi har zuwa wajen silk gashin sajen fuskanshi daya zagaye fuskan nashi, dukda hakan ma datayi shuru ganin haka kawai yasa ta miqe ta futo daga dakin bayan ta tabbatar yana nunfashi.
Lokacin data futo karfe hudu yayi kowa ya sauka kasa gaba daya maids babu wanda ya tsaya anan saman don wannan dokar ba a tsallaketa.
Hidaya......
Bayan wannan shareholder meeting dinnan bata bar office dinba sai wajen yamma liss, school din barad ta fara zuwa suka daukeshi kafin ta dawo gida.
Akan hanyarsu ta dawowa gida ya soma nuna mata medal din da aka bashi na competition din da sukayi kuma yaci second position, kallon medal din kawai tayi kafin ta kalleshi, first tambayar datayi mashi is ''why would you take second position, ban haifi danda za a wuceshi a komai ba so buckle up and make me proud next time with a first position, not this rubbish okay''
Girgiza mata kai kawai yayi in response,
Bawan allah yana jinta ta gama kanshi a kasa, yau kwata kwata baya cikin jin dadi saboda koda yaushe shi mai faran faran ne, dalilin fushinshi kuwa shine kowanne student parents dinshi na zuwa suyi supporting din yayansu, but shi babu wanda yazo mashi, daman daddyn shi yafi bashi attention akan harkokin nan shiyasa yafi shaquwa da daddyn nashi akan mamanshi, wannan yasa koda yaushe yake missing dinshi sosai.
Koda suka karaso gida kamar koda yaushe maids na tsaye suna jiranta, daya na kula da harkar barad while dayar kuma tana daukan Jakarta da sauran files dinta da sun dawo.