Showing 21001 words to 24000 words out of 131802 words
shima aikin kula yara ne da raino aka bata, abu dai na tafiya tiryan tiryan aka sake korarta a gidan don ko wata bata cika ba, shima nan gidan yaran gidan ne suka nuna masa son ta don haka aka koreta.
Koda aka dawo da ita agency with same complain hakan yasa suka fara bincikarta don sanin dalilin korarta da akayi cikin wata biyu da zuwanta.
Nan suka gano facial appearance dinta ne ke jawowa a koreta, wannan dalilin yasa suka yanke shawarar turata gida Nigeria kawai dukda da wuya ake samun waenda ke yin irin aikin da information dinta ya nuna ta iya kuma ta kware which is mai kula da mara lafiya ko raino(caregiver/nanny) don shine aikin da yafi wahala sosai kuma ba kowa ke karban irin wannan aikin ba, baiwar allah ita bata ma san mijin Jamila aikin daya rubuta ta iya ba Kenan.
Nan suka fara preparation din turata Nigeria don basa son abunda zai shafi imagine business agency dinsu.
Taheel group of company
Wani mahaukacin building ne mai shegen girma da haduwa, fadin irin tsaruwar building din daga waje ma bata lokaci ne don ya gaji da haduwa gashi yana da tsayi sosai yakai international standard, tsagaye yake da mirror glass, daga gaban company din a rubuta Taheel group of company da manyan harufa tare da logo din companyn, mutane sai shige da fuce sukeyi.
Wasu manyan motoci ne suke shugowa cikin company inda aka rubuta factory asset a jikin motar, cikin gaggawa matukan motocin suka fito bayan sunyi parking, cikin motar cike yake da mutane, daya bayan daya suka fara fitowa gaba dayansu da kwalaye a hannunsu da alamu protest zasuyi, guards din bakin entrance dinne suka tsaya don hana su shiga cikin premises din, mutane ma'aikata kuwa haka suka dunga lekowa don ganin ikon allah, su kuwa protesters dinnan mai zasuyi banda ihun dole a kara masu kudin aiki saboda yanxu sun kwashe wata biyu Kenan sunayin wani project na wasu kaya da sukeyi a factory, babu dare babu rana haka suke aikin nan saboda pressuring dinsu da akeyi wanda sunsan daga wajen acting ceo ne wato Hajiyar da kanta gashi anqi kara masu kudin albashi wannan dalilin yasa suma suka fito protest.
Daga chan saman last floor kuwa, office daya ne na acting ceo wato wadda ke rike da mukamin ceo temporary kafin heir din company ya karba responsibility dinshi, daga kofar shiga office dinma kasan irin haduwar da zaiyi daga ciki, kamar wani A class hotel saboda da girma, katon table dinta ya cika bari guda na cikin office din inda akan table din documents ne sai katuwar desktop da laptop na brand din apple sai landline daga gefe, tsakiyar table din kuwa wani katon glass name plate ne akai inda aka rubuta chief executive officer Hidaya Talal Taheel.
Office din nata tsit baka jin komai sai karar ac dake tashi,a tsaye take daidai wajen glass mirror wall din office din wanda daga ciki zaka iya hango na waje, hannunta rike da cup of coffee, tana sanye da wata riga daidai gwaiwanta plain burnt orange color sai wandon rigar wanda yazo mata har kasa, kafarta kuwa sanye take wani hill baki sai kanta data nade shi da wani silk black veil, fuskan nan nata babu digon fara a, she looks so so serious, saida ta kare masu kallo sosai daga nan wajen wall din kafin ta juya cikin isa da aji ta soma takowa wajen desk din office dinta, zama tayi tare da janyo file din gabanta, budewa tayi ta karanta file din tass kafin ta danna wasu number dake jikin lanline din, nan take tasa ayi mata connecting da securities din entrance, lokacin da call din ya shigo cikin gaggawa security din ya daga saboda security call box dinsu na kusa da inda mutanen keyin protest, a gaggauce ya amsata kafin ya fito waje ya soma Magana ''we have a call for abdullah head of factory service''
Abdullah dake tsaye hannunshi da rike da board yana jin an kira sunanshi ya tako inda securities din suke, atare suka shiga cikin landline box din, inda daya daga cikin securities din ya bashi landline din, mutanen dake waje dai zuba masu idanu sukayi don jin dalilin kiran head dinsu.
Magan daya biyu tayi mashi kafin ya sauke wayan, yana saukewa ya fito wajen mutanen ya tsaya tare da daga hannunshi don su bashi attention.
''na samu Magana da madam, and ta buqaci ganina yanxu, inason ku natsu zanje muyi negotiating yanxu.''
Ihu duk suka farayi cikin murna kafin su zazzauna anan kasan gaban company don jiran dawowanshi.
Daga cikin company executive secretary ya jagoranceshi don ba kowa ne yake zuwa ganin madam ba balle a shiga office dinta sai manyan shareholders da mutanen da suke partnership dasu don ceo ba karamin muqamin ba ne dukda ita acting ceo ce.
Cikin lift suka shiga inda secretary ya danna floor din da zasu tsaya,daman floor goma ne, inda madam take kuma 9th floor ne.
Button din floor dinma na office dinta ya fita daban don duk wanda ya shiga cikin lift din zai tabbatar da wajen na daban ne.
Suna karasowa kofar lift din ta bude, secretary n agama Abdullah na biye dashi abaya, saida suka wuce office din excutive secretary tukunna suka kaiga nata offce din.
Saida secretary yayi knocking kafin ta basu access wanda nutton din access door din na jikin table dinta.
Ciki suka wuce Abdullah sai rarraba idanu yake yi yana kallon ikon allah, ay inbanda ya gani da idanunshi zai iya karyata akwai waje kamar haka a doran kasa, yasha ayyuka a companys daban daban dukda yafi dade anan saboda sune yan farko farko da marigayi taheel mutun mai nagarta ya daukesu aiki.
Wata kujerar baqi dake facing din table dinta secretary ya nuna mashi, zama yayi yana washe bakin kafin ya soma gaisheta, wato kudi duniya ne duk girmanka shekarunka dole saika girmama wand aka kusan haifa ma.
Bata amsashi ba haka zalika bata dago ba saida ta gama abunda take kafin ta dubeshi da kyau, wannan file din ta mikama secretary ya miqa mashi, karba Abdullah yayi yana mai sauraron dalilin miqa mashi da akayi.
Cikin muryarta mai dauke da iza da isa ta soma Magana ''abdullah Muhammad right?
Dagowa yayi ya kalleta yace ''yes madam''
''why are you trying to tarnish my image?, shin kasan idan nakai karar ka zan iya charging dinka for defame of reputation''
Wani irin kallo ya mata kafin ya soma Magana ''cikin book of record na rules din companying nan ya bamu daman yin protest akan abunda ba ayi mana daidai ba''
''and who said your part of the company? Youre fired 10mins ego''
Hankali atashe ya dago zaiyi Magana ta dakatar dashi ta hanyar daga mashi hannu ''ouff no need for that, check that profile first then I have 2 reasonable options for you''
Jin haka ya sashi bude file din, fadin irin tashi hankali daya garzayo mashi ma bata lokaci ne, sunanshi ne baro baro a cikin file din inda takardunci suka tabbatar bashida qualification din shigowa company din ya shugo, daman requirement din dole sai kana da background ma'ana babu any criminality record da good education qualification, shi kuwa an taba kamashi lokacin about 20 years ago shi kanshi bazai iya tuna dalilin kamashin da akayi ba saidai yasan tabbas lokacin da yarinta akanshi, yanxu kuwa komai has been buried danko matarshi bata sani ba balle yayanshi, cikin sauri ya dago ya kalleta idanunshi sunyi jaa sosai, bamanashi kadai ba harda wasu abubuwan da babu dadin ji daya dangance shi da iyalanshi tayi digging and shes using it against him ko ince take threathning dinshi akai.
Yau shekara goma sha biyar Kenan yana aiki da taheel group, tun lokacin ubanta na raye, kuma shi ya daukeshi aiki ma, mutumin kwarai wanda yasan darajar mutane dukda yana da arziki mai tarin yawa hakan bai rufe mashi idanu bay au gashi lokaci yazo da yayanshi suke wulaqanta waennda suka taimaka masu suka daukaka company, don idan babu mutanen nan babu yanda za ayi companying ya dunga moving dukda kudi suke basu, acikin employee din company din masu kula da harkar factory suna da amfani sosai, shiyasa ake basu mahimmanci sosai don da gumunsu suke yin komai.
Kaste mashi tunaninshi tayi har lokacin coffee dinta na hannunta tayi relaxing bayanta akan kujerar ''I know wat you're thinking right now but ina tunanin ba wannan ya kamata kayi ba, don't be corny,''
Ajiye cup din coffee din tayi ta mike tare da takowa har wajen masaukin baqi kafin ta zauna opposite dinshi fuskanta babu alamun digon rahama ta soma Magana ''inada option biyu da zan baka masu sauqi, na farko ka sauka kasa ka tattara workers dinnan ku koma bakin aikin ku, maganar qarin kudin salary ku cire shi daga aggender dinku don ko penny bazan kara ba, you don't owe me an explanation for that, na biyu zaka iya miqewa ka fuce min daga office like I said''
Ta dan dakata kafin ta duba agogon danyen gold din dake hannunta ''like I said this is 25mins Kenan da sallamarka, sannan ka jirayi charges din da zanyi pressing su kuma waenchan nasan how I will deal with them, anyways ko ban fada maka ba kasan how I will deal with them just how I did with you, and lastly I want to give you a sounding warning wallahi wallahi babu wanda ya isa yayi tarninshing image dina ya zauna lafiya, I'm going to sue yall and rot you in jail mark my words, this is how I do my business, yanxu zabi ya rage naka''
Tana kaiwa nan ta miqe ta wuce wajen sit dinta, Abdullah kuwa kasa motsawa yayi tsabar tashin hankali, bai taba tunanin matarnan bata da Imani ba sai yau, bai taba tunanin zaka haifi da yaqi gadar ubansa ba, shes completely opposite din mahaifinta.
Turkashi, wani irin zufa ne ya wanke mashi fuska anan zaune, yama rasa irin tunanin da zaiyi saida secretary yace yazo ya futa kafin ya dawo daga tunanin daya fada, koda ya fito daga office din saida yayi kwalla don wannan ba karamin cin mutunci tayi mashi ba da girmanshi da shekarunshi, gashi yanxu ta bashi zabin da dole saiya dauki daya, na farko idan yace zai dau gaskiyar daya fito protesting to fa abin zaiyi affecting dinshi da iyalanshi don da wannan aikin ya dogara, na biyu kuma ta bangaren mutanen dake karkashinsa a matsayin san a head, sun bashi amanar su akan ya karbo masu encin su da halaliyar su sai gashi yanxu ya rufa dashi.
Kwallar data zubo mashi ya sharce yana mai jin wani irin nauyi a zuciyarci, matar nan ko shekarun da yayi yana masu bauta dukda suna biyanshi bata gani.
Haka ya fito premises din company jiki a mace, suna ganin shi kuwa duk suka mike daga zaune suna mai farin cikin jin ko anyi dace, gaba daya zagaye shi sukayi suna jiran jin furucin da zaiyi, abunda ya fada masu ba karamin tayar masu da hankali yayi ba nan suka tabbatar ba ayi dace ba, suna kokarin cigaba da protest din ya roke su akan su bari saboda madam tace duk wanda yake son barin aiki to zai iya cigaba da protest din wanda kuma yake son aikinsa ya koma factory.
Zuba mashi idanu sukayi gaba daya suna mamakin furucinsa, kamar ba head Abdulla ba mai sn gaskia,lallai tabbas akwai matsala kuwa, ganin kamar basa sauraronsa yasa ya juya ya shiga cikin motar factory din, wasu daga ciki haka suka biyoshi a baya wasu kuwa qin bin bayanshi sukayi don gani suke kamar shima an saye shi ne.
Shiko tausayinsu ya dinga ji, karshe dai sai juya katuwar factory bus din yayi suka koma factory house, sauran kuwa suna nan tsaye secretary ya fito,hannunshi rike da papers dinsu ta sallama kusan guda ashirin, hidaya dake zaune a office tana hango duk abunda yake faruwa daga cikin laptop dinta saboda akwai cctv cameras ta kowani lungu da sako dake cikin company.
Tana kallo secretary ya watsa masu takardar sallamarsu inda ya umarci securities su fitar dasu.
Ranar dai ma'aikata sunga tashin hankali, gashi babu wanda ya isa yayi questioning dinta sai shareholders.
On top korar datayi masu saida tayi pressing charges akansu, wasu ma basu san hawa ba basu san sauka ba ake laqaba masu sharrin abunda basuyi ba, haka aka dunga kamasu ana kullesu.
A office kuwa haka aka dunga circulating magana saidai babu wanda ya isa yace uppan don itace oga kwata kata, familynsu sunfi kowa shares a companyn don ko share din gaba daya shareholders din bazai kai koda rabin nasu ba suke da 75% shares sauran 25% kuma na sauran shareholders dinne dukda ba a raba nasun ba ita da qannenta saboda ba ayi presenting heir din company ba har yanxu.
Bangaren hidaya kuwa hankali kwance ta cigaba da ayyukan dake gabanta ba tare da tsoro ko fargaban komai ba, yanda take jin kampanin nan ba a cewa komai, zata iya yin komai don kare martabar family business line dinsu, bangaren completion she's compatative kowa ya shaida haka, when it comes to business bata da sauqi kwata kwata.
Wayar hannunta ta kura ma idanu tana wani dogon tunani, cikin call log dinta ta shiga, wata special number ta kura ma idanu inda tayi saving da big baby T, ta dade idanunta akan wayar ta zurfafa cikin tunani kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye wayar kawai.
Tana ajiyewa karar message yayi popping, wayar ta dauka ta bude message din, ganin sunan khaal yasa ta ajiye wayar ba tare da ta bude message dinba.
Duban screen din laptop dinta tayi inda ta fara duban wani business proposal da Gucci brand suka tura masu, saida tazo daidai wani slide ta tsaya, rubutun slide din ta zuba ma idanu ina aka rubuta ''possession of control, authority, influence is power!!!''
Ta dade sosai tana kallon wannan rubutun ko kifta idanu ta kasa, saida ta dauka kusan minti biyar kafin ta sanya hannu tayi banging laptop din ta mike tsaye ba tare da ta dauki komai ba ta zari handbag dinta ta fuce daga office din tana dialing wasu numbers a wayanta.
Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Free page
Chapter 11-12
Update!!!!
Agency...
Zaune take har wajen karfe biyar a zaune,babu abunda ke miqar da ita sai shiga bayi ko sallah, gaba daya tayi laushi abun tausayawa,babu abunda take tunani sai rayuwarta, ba karamin tausayin kanta take ba, tun tasowarta sai yanda akayi da ita kamar kaya,tunda mutanen nan suka jinginar da ita anan basu sake waiwayonta ba, ita dai tasan cewa maidata gida zasuyi ayanda taji suna fada.
Tana nan zaune ogan agency din gaba daya da wasu yaranshi suka fito daga office din nasu, fuskarsu a washe suka karaso reception inda suke ajiye ma'aikata.
Har suka karaso kanta na kasa ta lula duniyar tunani, saida daya daga cikinsu ya kira sunanta kafin ta dago, da mamaki take kallonsu su uku a tsaye akanta suna washe baki.
Sanin bata jin larabci yasa daya daga cikin su ya kalli ogan nasu yace ''sir kana ganin bazaamu samu wata matsala ba idan muka tura ta?''
Kallonshi ogan yayi kafin ya dan hade rai ''bana fatan haka, kai ni banma damu ba kasan irin kudin da zamu samu kuwa ta dalilin yarinyar nan?, ''
Daya daga cikin su ne ya sake Magana ''but sir, kasan dalilin da yasa ake korarta daga aiki, what if hakan ya jawo mana matsala''
''na rigada nasan da wannan kuma inada plan akan wannan, this girl is the only option we have dole mu turata''
''but sir yanda...'''
Katseshi ogan yayi da gaggawa kafin ya dubi sabeeha da tayi tsuru kanta a kasa.
Jin kalamanshi na karshe yasa hankalinta ya tashi sosai, ta shiga rudu, dukda bata gane wasu abubuwan da suka fada da larabci ba, abunda ya danfi tsaya mata arai shine abunda ogan ya fada, me suke nufi Kenan waennan mutanen kodai inda za a cutar da ita zasu kaita? Tambayoyin data dunga yima kanta Kenan saidai ta tabbatar koma menene daga yanda suke Magana akai ba alkhairi bane.
Wata takarda suka bata domin tayi signing kafin daya daga cikinsu ya jagoramceta zuwa motar da zata tafi da ita.
At that point ta gama saddaqarwa kuma, sai yanda allah yayi da rayuwarta.
Tafiyar minti ashirin ta kawosu wani waje wanda ta kasa tantance ko'ina ne, driver ne ya futo ya bude mata motar kafin yace ''fito''
Futowan tayi da Jakarta a hannu kamar za a kwace mata, shine yayi gaba kafin ta bishi a baya har suka shigo cikin wajen, har suka shiga wani daki bata tantance taqamaimai wajen don kamar dakuna ne burjik a bulding din.
Suna shiga ciki driver ya mata nuni da wajen zama kafin shima ya zauna a gefe.
Zaman minti goma sukayi kafin a bude kofar shugowa, mutane ne guda biyu suka shigo, daya nag aba dayan kuma na biye dashi a baya.
Miqewa driver yayi cikin ladabi ya gaishesu kafin ya basu waje.
Sabeeha na ganin haka ido ya raina fata, ko gigin dago da idanunta batayi ba don cike suke da tsoro da fargaba.
Zama daya daga cikinsu yayi while dayan na tsaye yana fuskantarta da kyau, gyaran muryar da akayi ne yasa ya maida dubansa ga ogan nasa.
''I'm sure kasan dalilin kawoka nan danayi ko?''
''yes sir'' ya amsa shi
''okay inason ka fada mata abunda zan fada yanxu da yarenku yanda zata fahimta sosai.
''okay sir'' wanda ke tsayen ya sake bashi amsa.
Magana wanda ke zaunen ya fara cikin harshe larabci har yakai aya kafin ya nunfasa ya maida dubanshi gareta don jin response din da zata bayar, shi kuwa dayan yana ganin haka ya soma fassara mata yanda zata gane cikin harshen hausa don daman shi interpreter ne, aikinsa Kenan anan kasar, kuma yana samun kudi sosai.
''zakiyi mamakin kawoki nan da akayi, ba komai bane yasa aka kawo sai dan wani aiki da zakiyi mana cikin sirri, bawai muna neman yardarki ko amincewarki bane, dole kiyi abunda zamu umarceki inba haka ba rayuwarki da rayuwar iyayenki zata salwanta''
Wani irin quuu cikin sabeeha ya bada lokaci