Showing 45001 words to 48000 words out of 131802 words

Chapter 16 - MATAR TAJ HAUSA NOVEL

27 Sep 2024

25355

shima friend dinshi ce, don babu abunda hidaya zata fada ko ta nuna tanaso shi kuma yaqi wannan abun.

Yau weekends duk kowa na gida ana hutawa, hidaya na part dinta while su fadwa na wajen garden ita da afiya.

Zuwan doctorn big baby da hidaya tayi hiring yasa ta futowa zuwa part din nashi, yau sati guda Kenan rabonta da zuwa part din wanda hakan ba karamin dadi ya mat aba don ya bata damar concentrating akan abubuwan dake gabanta da ayyukanta, sai a lokacin take jin data kori sabeeha datayi dana sani don wannan ce first caregiver din data dade har warhaka tana handling situation din taj, don da kansu suke guduwa saboda idan abun nashi ya tashi tsorata su yake yi don handling mai irin lalurar shi ba abu bane mai sauqi,

daddyn barad ne ya shigo da doctor din sai wasu maza kamar ma'aikatan dake karkashin sa ne, saman ya jagorance su har zuwa part din, daidai nan hidaya ta fito daga nata part din, gaisawa sukayi da doctor kafun su nufi part din nashi, itace ta bude masu kafar kafun su shige daga ciki.

Ko'ina fess fess babu qazanta as always don part dinshi kwata kwata ba a barin shi unhygienic.
Daidai nan sabeeha ta futo don bashi maganinshi na yamma, tana sanye da uniform dinta kalar ruwan kasa sai face mask data rufe fuskanta dashi, ''step out''
Hidaya ta bata umarni, hakan kuwa yasa ta tattara abubuwanta ta fuce daga dakin gaba daya.
Cikin bedroom dinshi suka shiga, hidaya ce ta fara shugowa, yana zaune ya kafa ma kofar idanu yana jiran ganin sabeeha, cikin murna da farin ciki kuwa ya miqe tsaye har zai tunkaro inda yake ta daga mashi hannu hakan yasa suka karaso, wani iri dadyn barad yaji ganin yanda tayi mashi shima kanshi taj din saida yaji babu dadi, don he was so happy ganinta kawai da yayi, yanda yake wage baki kamar an mashi albishir da wani abu mai muhimmaci.

Su doctor na biye dasu a baya har zuwa inda yake, zama hidaya tayi baking ado inda ayke zaune kafin ta riko hannunshi, saida doctor suka karaso ya soma zaro ido, har jijiyoyin kanshi sun soma firfitowa rado rado alamun yana neman furgita.
''big baby'' ta kira sunanshi, gaba daya attention dinshi ya tattara ya bata dukda tsoron ganin doctor dinnan da yayi, daman normally idan zasu zo kuka yake yi saboda allurer da suke mashi duk wata, baya so kwata kwata, ga wani abu da suke zuwa dashi kamar inji wanda suke saqala mashi a kanshi, wannan abun yana tayar mashi da hankali sosai.
''look at mee, your're a good boy ko?''
Girgiza mata kai yayi alamun eh kafin ta sake cewa ''bana son wannan kukan naka, ka natsu, im by your side kaji?''

Saida ta tabbatar tayi capturing mind dinshi kafin ta dubi doctors din,babban dake cikin su ne yace ''sir ko zaka dan bamu waje''
Ya fada yana kallon daddyn barad, wani irin kallon hidaya jamid yayi, tana ganin haka ta kauda kanta gefe kafin tace ''ba damuwa, you say anything a gabanshi''
Gyaran murya doctor yayi kafin ya karaso inda taj din ke zaune ''hello handsome how are you, na kawo ma cholate''
Cikin murna kuwa yace ''da gaske''
''yes amma saika tsaya mun gama dubaka saina baka ka yarda''

Girgiza mashi kawai taj yayi kamar wani dolo kafin yace ''no injection please uncle''
''babu injection I promise''
Sauran yaran doctor ne suka karaso da abun gwajin kwakwal war tashi, abun is handy ana connecting dinshi da computer, inda sauran igigiyoyin kuma kamar hula haka zaka nada su akanshi.

Haka suka fara sassaka mashi wannan wireing din akanshi, saida suka tabbatar sun saka ta ko'ina kafin daya daga cikinsu ya dauko wani dan syringe mai shegen tsayi kamar allurer doki, shidai daddyn barad na daga tsaye yana kallonsu.

Sai da suka shanmace shi dayan ya tsira mashi wannan doguwar allurer, idanunshi har sun soma jaa don saida aka soma zuba ruwan allurer ya tabbatar allurer dai akayi mashi, nan take ya fashe da kuka kuwa, hidaya dai idanu kawai ta zuba mashi, saida kukan ya isheta tace ''shut up, kai karamin yaro ne kake kuka''
''madam ayi hakuri karamin yaron ne ay ayanxu,'' doctor ya fada,
Jin haka yasa ta hade rai sosai, taj kuwa tunda tace yayi shuru dinnan haka ya gume baki yana hawaye idanunshi sunyi jaa sosai ya kafa mata idanu dasu ko gajiya da kallonta baya yi, dadyn barad dai kasa kallonshi yayi don ba karamin tausaya mashi yake ba, yau wata takwas Kenan da faruwar wannan mummunan hadarin daya sauya mashi rayuwarshi lokaci guda, Taj was a definition of a perfect young innocent man, he's the sweetest yet the most controlling duk da he's tough musamman ga waenda bashida kusanshi dashi, daga danginsa sai danginsa gaba da baya, da wuya mutun ya shiga rayuwar cikin sauqi don he's very tough with his lifestyle.

Bayan an gama mashi wannan allurer kawai sai ya soma jijiga, hidaya dai miqewa tayi sauran yaran doctor nan suka zauna inda ta tashi suka ririke shi, wannan jijigar tashi effect din allurar ne, saida suka tabbatar ya futa hayyacinshi kafin doctor ya soma duba kwakwalwarshi da emotions dinshi don komai yana reading ta cikin laptop din, ya dauka kusan minti goma yana dube duben shi kafin ya sa yaran suka cire mashi wannan wiring din daga kanshi, a daidai wannan lokacin kuma jijigar ta lafa, kwantar dashi sukayi kafin likitan ya duba pulse dinshi, ganin komai normal yasa suka dan tsaya nay an mintuna, don allurar cikin minti ashirin take sakin mutun gaba daya.
Ai kuwa lokacin na cika sai gashi ya bude idanunshi ya zuba masu idanu daya bayan daya harya sauke akan hidaya, cikin sauri kuwa ya miqe zaune ya riko hannunta, ''first love, yaushe kikazo, I missed you please karki tafi!!''

Ba tare da ta kalleshi ba tace''doctor, whats his progress?''
Nunfasawa doctor yayi kafin ya soma koro mata bayani, ''gaskia babu wani changes, saidai he's stable kawai, brain dinshi na functioning saidai babu wani alamun change a tattare dashi.''

Daddyn barad ne yayi saurin katse shi, ''wannan barcin da yake yi all the time fah?''
''effect din magungunan shi, idan baisha sub a brain dinshi bazat huta ba, saboda zata dunga confusing dinshi da wasu flash memories dinshi na baya''

''ya za ayi yayi recovering idan bamu barshi ya samu wannan flash memories dinba? Stopping him from having wannan memories din bazaisa a samu any progress ba, are you kunsan yanayin aikin ku kuwa?''

Doctor ne ya kalli daddyn barad don baima son koshi waye ba, ''sir are you a doctor ne?''
''no I'm not, but dis is a common sense, babu aynda za ayi yayi regaining memory dinshi idan har aka hanashi hakan''

Sai a lokacin hidaya ta soma Magana ''jamid please, are you going to teach him how to work ne?''

Dakatar da ita doctor yayi ta hanyar cewa ''first of all, you need to understand the psychological and medical reasons din daya sa yake shan wannan medication din, first of all, ayanxu his brain works like a child, sannan kwakwalwarshin ita ke controlling mind dinshi, kaga yanxu both 2 are connected, dalilin dayasa muka hanashi ya samu wannan flash memory din kuwa shine, any flash daya zo mashi zaiyi confusing mind dinshi dake controlling brain dinshi wanda hakan zai iya jawo mana wata matsalar, brain din itace center of universe din komai nashi, zata iya saka zuciyarshi ta buga ma tunda ayanxu ma he's not normal, ina fatan wannan bayanin yayi maka''

Nunfasawa jamid kawai yayi ba tare da ya sake cewa komai ba, wasu yan bayanai hidaya tayi mashi game da abubuwan daya shafesu kafin suyi mata sallama, suna gab da futa taj ya soma Magana ''first love ina friend, I was waiting for her yanxu ta futa, kin ganta? Yau munyi wasa nida ita'' washe baki yayi excitedly yana bata labarin

Tsayawa doc din yayi yana sauraron bayanan nasa da mamaki, na farko abunda ya bashi mamaki shine ya akayi ya tuna event din dazun na futar yarinyar don bai kamata ace ya tuna ba saboda allurar tana da karfi sosai wanda karfinta kesa wanda akayi ma ya manta da duk abunda ya faru dashi a ranar, da wannan tunanin ya futa daga part din da yaranshi, daddyn barad kuma yayi masu rakiya don shifa yana jin kamar bai yarda dasu ba kwata kwata.

Suna fita suka tadda sabeeha tsaye bakin kofar part din hankalinta a tashe , da mamaki duk suke kallonta ganin haka ya sata cewa ''sir baisha maganin shi na yamma ba''
Daddyn barad ne ya amsata ''don't worry about it kije''
Tana wucewa doctor ya bita da idanu kafin ya sauke wani murmushi ta gefen baki.

Bayan tafiyarsu doctor hidaya ma bata wani dade ba ta futo daga part din big baby ba ta wuce nasu, bata dade da shiga ciki ba kuwa saiga daddyn barad, tasan maganganun daya saba zai mata don haka ta zauna ta daura kafa daya kan daya.
''hidaya, kina ganin wannan...''
Daga mashi hannu tayi alaman ya dakata ''jamid please not today, na fada maka koma menene indai akan batun big baby ne don't ever question me, wannan tambayoyin da kake ma doctors din shi na menene? I trust them so please''

Saida ya bari ta kai aya, kafin yayi wani murmushi mai kama da na taqaici kafin yace ''at this point ke nake tsoro HIDAYA!!!!!!!''
Yana fadin haka ya fuce daga bedroom din, harya fuce bata bar kallonshi ba tana mamakin abunda ya fada, ''me yake nufi Kenan da wannan furucin nashi?, itafa har yanxu tana jin akwai abunda yake boye mata wanda bata sani ba, shike sashi questioning dinta koda yaushe, yanda yake kallonta anya kuwa bai gano......
Saurin kauda tunanin tayi "no that's impossible'' ta bama kanta amsa, nan take wani irin fargaba ta durar mata,.....



Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 23-24

Update!!!!

Washe gari da safe tun kafin alarm dinsu yayi ringing ta tashi, don yanxu ta fara gane komai na gidan da yanda alamuran gidan ke tafiya, wanka ta fara yi ta saka uniform dinta kafin ta fara nafilfilu, ta dade sosai kanta a kasa tana kiran sunan allah har alarm dinsu yayi kara.

Karfe biyar daidai ta fito daga part din nasu na ma'aikata kafin ta wuce sama, kamar kullum yauma ko'ina shuru babu motsi saima haske daya bade ko'ina, saman ta wuce cikin natsuwa kanta a kasa, daidai nan daddyn barad ya futo don zuwa sallah, gaishesa tayi kafin ta wuce part din taj.

Koda ta shiga part din batayi gigin shiga bangarensa ba saida ta gama gyaran parlorn kafin ta nufi bedroom din.

Lokacin data shiga yana daga zaune kamar kuwa jiran ta yake yi, murmushi yayi mata wanda ya sata sauke ajiyar zuciya mai nauyi, yau bata shugo ta taddashi yana kuka ba kamar kullum, "friend!!!"
"Naam friend good morning"
Ta amsa shi, murmushi kawai yayi mata kafin yace "first love batazo ba?"

Yanda yayi maganar abun tausayi, saida ta karaso ta gane yanayin da yake ciki, he looks so pale, bakinshi ya vushe sosai yayi fariii tarr kamar wadda ke jinya, ga idanunshi sunyi jaa sosai.
Haka kawai taji kamar he doesn't sound like yanda yake koda yaushe, "friend kayi brush?, ga breakfast na kawo maka"
Daidai nan ta karaso bakin gado ta dan duqa don ajiye tray din gefen bedside table.

Kallon corn soup din yayi, take ya soma jin wani abu ya soma zuwan mashi maqogaron shi kamar amai, batama lura dashi ba ta dauka bowl ta miko mashi, daidai nan kuwa ya soma kakarin amai, lokaci guda ya burkice, amai yake son saidai cikin nashi babu wani abun arziki a cikinsa da zai amayar, ganin yanda yake struggle tare da riqe maqogaron shi yasa ta saurin ajiye bowl din hankali atashe.

"Subhanallah!! Menene? Wani abun ke damunka"
Nuni yayi mata da bowl din kafin ya kauda kanshi gefe, "bana so"
Sai a lokacin ta lura da abuncin ne baya so, gashi batasan ya zata ya ba, abunda aka rubuta kenan a breakfast timetable dinshi kenan, gashi dole saiyaci abunci zaisha magani.
"Baka son wannan?"
Ta karashe tana nuna mashi bowl din, girgiza mata kai yayi abun tausayi, "meysa baka so?"
"I hate it" ya sake fada
"Kayi hakuri kasha kaji friend saboda ka samu kasha magani Okay?"

Juya mata baya yayi a shagwabe tare da nade hannayenshi a kirjinshi "no noo banaso"
Ya karashe kamar zaiyi kuka.

"Friend dan Allah ko kadan ne kaji? Kaga maganinka ma baka sha ba kar lokaci ya kure"

"I don't want to"
"Idan baka sha ba first love zatayi fushi dakai" sabeeha ta fada hoping hakan zaisa ya sha, ai kuwa bata gama karashe maganr bama ya juyo ya zuba mata idanunshi, idanunshi da sukayi jaa ya zaro mata shi "zatayi fushi sosai?"
"Eh zatayi fushi dakai sosai"

Sauke idanunshi yayi kasa irin yanda yara keyi kamar bazaice komai chan kuma ya hadiye wani irin miyau mai daci a bakinsa
Hannunsa ya miqo mata, hakan yasa ta ajiye mashi bowl din a akan lap dinshi.
Kallon bowl din yayi kafin ya runtse idanunshi ya soma diban soup din yana kaiwa baki daga yanda yake sha zaka gane baya so kwata kwata kuma baya mashi dadi a baki, saida yasha kusan rabi kafin ya maido da dubanshi gareta yace "friend ya isheni"
"Saura kadan friend ka shanye please kaji? Bana son first love tayi fushi okay?"

Haka nan ya cigaba da sha harya shanye tas da kyar, sabeeha na ganin haka tayi saurin karban bowl din tace "yauwa friend,"
"Friend zanje toilet please i what to pee"
"Okay tohm" sabeeha ta amsa shi tana dan yin baya don ta bashi hanya ya wuce.

Kafafunshi ya soma saukewa kasa kafin ya miqe, taku daya yayi ya soma yin baya kamar zai fadi, cikin hanzari sabeeha ta karaso ta kama hannunshi, wani irin zafi taji dayasa ta sakin hannun ta kalli fuskanshi, layi taga ya soma yi wanda ya sata tsorata lokaci guda ta sake taba hannun nashi, yanda kasan daman neman makafa yake gaba daya ya sakar mata jikinshi, wani irin wahalallen nunfashi ta sauke " wayyo allah na, zaka karyani"
Tururin da jikinsa ke fitarwa yasa hankalinta ya koma kanshi gaba daya "friend are you okay?, jikinka akwai zafi,"
Baya jin abunda take fada ma gaba daya saboda yanda gaba daya yaji wani irin dummm a kunenshi lokacin daya miqe
"Zanyi pee"

Da taimakonta suka karasa cikin bathroom din, hannunshi har zuwa lokacin yana cikin nata, koda yazo yin pee din ita ta taimaka ta zare mashi mazugin tana kauda ido kafin ta fuce daga bathroom din.

Dakin ta koma ta kwashe bowl din kafin ta fuce zuwa kicin.
Ta dan dade kafin ta dawo cikin dakin saboda wanke bowl din datayi, da mamaki ta karasa bathroom din ganin kamar bai futo ba, knocking ta fara yi, jin shuru yasa ta cewa "ka gama?"
Nan ma shuru babu response, hankalinta ne ya soma tashi,bata tsaya wani dogon tunani ba kawai ta bude kofar ta sa kai ciki, ganinshi a kasa helplessly yasa ta karasowa cikin sauri, babu abunda yake sai kakarin amai gashi aman yaqi zuwa, da sauri ta karasa inda yake ta tsugunnawa, gaba daya ya gigice, babu abunda yake sai kuka, yana jinta a kusa dashi ya nanukota, jikinta har rawa yake.

Daburcewa sabeeha tayi hartama fi shi shiga tashin hankali ganin yanda yake faman tura jikinshi ga nata, aman dake maqale a moqogoron shi ne ya soma zubowa, gaba daya ya amayar da wannan soup din a jikinta wajen gaban rigarta, baiwar allah ko kyankyaminsa bata ji ba saima dabbing bayanshi data dunga yi, struggling sosai ya dunga yi wajen amayar da abunda ke cikinshi tass, ga jikinshi yayi wani irin zumm sosai.
Saida ya gama tass kafin komai ya dan lafa mashi ya kwantar da kanshi a kafadarta jiki a mace ,gaba daya ya gama batasu daga shi har ita, "friend i want to see first love please,"
Fashewa yayi da kuka don daman idan yana rashin lpy irin wannan indai ba hidaya ya gani ba sai yayi ta kuka.

Wani irin kuka ne ya zo ma sabeeha, allah ya bata wata iriyar raunaniyar zuciya mai rauni, tana da tausayi sosai, musamman idan taga mara lpy, lokacin da aka tafi da inna asibiti kwana tayi tana kuka, duk da zaman su da inna ba wani dadi yake ba hakan baisata tausaya mata ba lokacin da za a kaita asibiti, balle kuma wannnan daya gama shiga ranta saboda lalurar shi,
"I'm so sorry friend, wallahi bansan ranka baya so ba da bazan baka ba, i'm so sorry please kaji"

Sun jima anan zaune, gaba daya ta zama kamar wata yar tsana a zaune gashi ya rufeta ruff da girman jikinsa daman gata ba tsayin kirki ba ga dan jikin nan nata.
Saida taji ya daina kukan kafin itama ta tsagaita, miqewa ta soma yi ya ruko hannunta "don't leave me please, karki barni yanda first love ta barni, stay with me, i don't want to be alone"
Wannan furuci nashi ba karamin narkar mata da zuciya yayi ba don saika rantse mai hankali ne yayi maganar, tasan yana da rashin lpy amma kuma bata san dalilin dayasa kullum yake daki ba dukda ta yanke hakan saboda rashin lafiyarshi amma harga allah yana buqatar yan uwanshi a kusa dashi koba komai shima mutunne kuma yana da zuciya ta dan adam bai chan chanci wannnan ba, saidai tunawa da kaddarar sa kenan yasa ta jin wani irin.

Hannunshi da jijiyoyinsa da suka futo rado rado ta zuba ma idanu don fatarsa fara ce tass, samun kanta tayi ta komawa ta tsugunna a gabanshi ta riko hannunshi "bazan barka ba friend, i promise,"
Murmushi kawai yayi mata kafin ta taimaka mashi ya miqe zuwa wajen basin, wanke mashi baki tayi da kanta kafin ta rakashi har bedroom ya kwanta ta jawo mashi duvet ta rufe shi.

Toilet din ta koma ta gyara shi tsaf sannan ta gyara gaban rigarta daya bata mata kafin ta futo, lokacin data fito har ya soma barcin wahala, sai a lokacin ta tina baisha maganinsa ba, don dole badan taso ba sai dan tsoron kar abunda ya faru kwanaki yasa ta soma tashinsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login