Showing 30001 words to 33000 words out of 131802 words
time table din abuncin da zatayi yana nan an mannashi jikin fridge sai wani dan box din medication da date harda time a jiki, saidan karamin timer dake reading time komai dai cikin sauqi.
Neman abun shara ta soma yi da mopper, tana ganin komai ta kwaso ta koma parlor ta soma gyara, allah ya taimaka ta iya gyaran ma sosai saboda gidan data baro bayan aikin kula datayi har da gyaran daki tana yi, agidan wannan tsohon kuwa har abunci tana dafawa irin nashi wanda matar gidan ta koya mata musammam idan ita bata gidan.
A gurguje ta gama komai saboda babu datti ko digo sai yar kurar da baza a rasa ba, dakin activity room ta shiga, nan ma saida ta gyara ko'ina ta goge kafin ta fito, duk wannan abubuwan da takeyi cikin natsuwa takeyi gudun kartayi wani kwakwara motsin.
Mamakin kayayakin wasa dake dakin activity ta soma yi, wasu abubuwan wasan ma tun tasowarta bata taba ganin su ba, yaran larabawa dai suna shan gata.
Kitchen ta koma ta soma preparing abunda ke rubuce a timetable din, duban date ta fara yi a jikin time table din, yau Wednesday, abunda ke rubuce ne a wajen ya dan bata mamaki don ruwan zafi kawai ta gani da just 1 apple for breakfast, wakeyin Karin kumallo da ruwan zafi zalla bama ruwan shayi ba sai kuma slice of apple, sanin bata da hurumi a cikin dokokin da aka bata yasa ta bude fridge din, babu wani abun kirki a cikin fridge din na ci saidai fruits da chcolate sai vegetables... Apple din ta zaro guda daya ta soma slicing kafin ta jona ruwan zafi a heater kettle lokacin wajen karfe takwas tana gamawa ta samu waje anan kasan kitchen din ta zauna ta tankware kafafunta.
Duk bayan yan mintuna qalilan haka zata dubi time gudun kartayi kuskure har barci ya soma dibanta a nan zaune, haka nan ta hana kanta barcin nan har wajen karfe takwas rabi daidai.
8 dinma nayi alarm din kan timer dinnan yayi ringing, a furgice ta miqe tsaye jikinta na bari ta nufi wajen kettle din ta sake reboiling ruwan, tunawa da saiyasha magani a cewar matar nan yasa ta bude wannan box din ta zaro pack din magungunan ranar kafin ta dauka ruwan dake jere a wajen ta fuce daga kitchn din.
Daidai bakin kofar dakin ta tsaya, sai a lokacin taji wani sabon tashin hankali ya tunkarota, she's just so anxious haka kawai.
Kai tsaye ta bude ahankali gabanta na bugawa kafin ta shige cikin dakin, dakin duhu babu wani haske kwata kwata daga inda take tsaye, dagowa tayi ta fuskanci cikin dakin, sai a lokacin ta dan hango hasken rana dake haskowa daga wajen labulen dakin.
Takowa ta soma yi anatse ba tare da tayi making any movement sound ba har ta karaso tsakiyan dakin, shuru ta danyi tana yin nazari nan take haske ya zagaye ko'ina ya gauraye dakin, duban ko'ina ta soma yi da kyau, daki ne babba sosai mai dauke da gado dayasha beddings sai carpet a tsakiya, ko tv babu sai gefe kuma wata kofa ce kamar wani dakin daban kuma.
Duban gadon tayi ganin babu kowa akai kuma babu alamun da akwai mutun a dakin yasa ta danji sauqin fargabar da take ciki, ''toh ay babu kowa nan'' ta fada aranta
''kila yaron yana bandaki'' ta sake fada aranta, don daga yanda wannan matar ta fada cewa karfe takwas yake tashi, shuru shuru dai tana tsaye har wajen minti goma babu wani motsin, hakan yasa ta tunanin anya lafiya kuwa.
''first love'' furucin data faraji Kenan, tabbas taji anyi magana saidai ta kasa gane daga ina ne tajiyo wannan sound din dake futa ahankali, dube dube ta soma yi har idanunta ya sauka wajen labulen nan dake facing dakin, chan kuma ta hango tudun abu ta wajen labulen wide glass din dakin ahankali ta soma takawa zuwa wajen,
tsugunnawa tayi daidai wajen curtains din sannan ta fara yaye labulen, tundaga yatsun hannunshi daya ajiye agefenshi zuwa bayanshi that is so wide zuwa sumar kanshi da take akwance kamar gashin jariri da alamu an aske mashi gashin ne ma amma ya fara fitowa,zaune yake ya tankware kafafunshi ya hade su waje guda ya zuba ma windown fararen idanu babu ko kiftawa.
Afirgice ta koma da baya, hankalinta atashe azuciyar ta fara karanto addu'oin tsari kamar an kira sunan shi kuwa ya juyo ya kalleta, shima saida yadan razana.
Lafiyayyan saurayi ne zankadede a zaune, fari tass dashi, yana da yalwan gashin jiki da gashin baki daya cika mashi round innocent face dinshi, akalla zai kai shekaru talatin da yan kai a doran duniya, yana da wani irin kyawu da cikar haiba masha ALLAH gashi da girman jiki na mazan taka(masculine) dukda a zaune yake.
Kallon juna suka soma yi tsakanin shi da ita,sabeeha dai kasa dauke idanunta tayi akanshi, saboda kamar anyi magneting idanunsu waje guda babu abunda take tambayar kanta sai wannan ne sir din? Shi wannan din mutun ne? tsabar furgici ma kallon shi take kamar aljani saboda kyawun shi ya wuce musali.
Shikuwa ganin tana kallonshi yasa ya zuba mata idanu shima, jikinshi harya soma jaa, take yanayin fuskanshi ya sauya zuwa na furgici har jijiyoyin kanshi sun bayyana rado rado, sanye yake da wata farar riga mai dogon hannu sai wando shima fari tass masu laushi,, zumbur ya mike tsaye wanda yasa ta dago da kanta sosai kamar tana kallon sama don yana da tsayi sosai, saita zama kamar wata yar dwarf a gabanshi, bakinshi ya soma juyawa kamar wanda ke son yin Magana ''who are you?'' ya fada a hasale, wannan kalmomi sune kalma ta biyu daya furta da kunnenta ya jiyo mata,
Inda take ya soma dosowa kamar wani zaki, ''who are you?'' ya sake fada yana binta daf da daf, tana ganin haka ta koma baya cikin sassarfa har tana harde kafafunta, saida suka karaso tsakiyar dakin ya fara dube dube da alamu yana neman abunda zai dauka ya buga ne a kasa, ganin babu komai a kusa yasa shi kwala uwar kara wanda yasa sabeeha burkicewa sosai, take ta saki maganin da ruwan duka a kasa, ''na shiga uku''ta furta bakinta na karkarwa,
wata uwar tsawa daya sake doko mata yasa ta zubewa a kasa sai hawaye wiwi, tata ta kare, wannan mai kama da aljanun ko mahaukaci ne? shiyasa ake ta tsoron hawa sama kenan,abunda yazo ranta Kenan.
''dan..dan allah kayi hakuri, karka min komai dan allah'' ta karashe tana mai hade hannenta waje daya tana rokonshi, hwayenta kuwa basu bar tsayawa ba kuma daga gani ta torota sosai.
Wannan kukan nata ya sashi sarewa anan take kawai, sai yaji wani irin tausayin ta ya mamaye zuciyarshi kamar an zuba mashi ruwan sanyi a kirjinshi, he was never soft towards kowa sai first love dinshi, baitaba yarda da kowa ba sai first love dinshi don duk wanda aka kawo don kula dashi tsoronsu yake ji kuma baya son ganin su kwata kwata, shi a ganin shi saboda su ne first love bata zuwa wajen shi kuma bata kulashi, sai gashi a karo na farko yaji wani iri game da wannan din.
Nan take ya tsugunna a gabanta kamar wani dan yaro dan shekara goma, musculine hannunshi ya dago ya dora shi akan fuskanta dake cikin mask, nan take ta bude idanunta data runtse ta sauke shi akan fuskanshi, ''í'm so..rry don't cry''
Mamakin yanda yake yi da fuskanshi da yanda yake goge hawayen idanunta take yi, wasu abubuwa yake yi kamar wani dan karamin yaro, hawayen fuskanta kuwa basu bar kwaranya ba dukda yana goge su don kamar tunzurata yake yi dayin hakan,
''don't cry for me please''
Ya sake fada yana mai hade fuskanshi abun tausayi kamar zaiyi kuka shima, ai kuwa kan kace me shima yayi zaman dirshen a gabanta ya soma kuka wiwi kamar karamin yaro, mamakin hakan ya sata dan tsagaitawa nan take kuwa ya soma bugun kasan tiles din da kafafunshi har yana zungurinta, tashin hankali, nan take itama ta zabura sai kuka jikinta har rawa yake yi tsabar furgici, ita abun da ya tayar mata da hankali shine, ya za ayi ace dingiqin zabgege mutun dinnan ne yake kuka kamar yaro, haka suka dunga kuka daga shi har ita kamar kananun yara suna nan zaune aka budo kofar dakin kamar za a balla kofar, maido da dubansa yayi ga kofar nan take kuwa ya miqe cikin sassarfa ya nufi wajen kofar baiyi wata wata ba ya rungume hidaya data shigo dakin hankali a tashe kamar an wullota.
Kankameta yayi sosai jikinshi na rawa, yanda ya rungumeta kamar wani dan karamin yaro, itama dai sai ta zama wata yar kif a gabanshi, hidaya dai kasa motsawa tayi tana mamakin wannan al'amarin, bubuga bayanshi ta soma yi don ya saqalo hannayenshi a arms dinta tana mai duban maid din ranta a mugun bace.,
Yana nan a jikinta ta soma jan shi zuwa bakin gadonsa ta zaunar dashi, sabeeha dai tunda ta dago sau daya ta kallesu bata sake dagowa ba haka zalika kukan nan nata bata dainayin shi ba.
Hidaya na zaunar dashi ya matso kusa da ita ya kwantar da kanshi kan kafadarta, ''first love, she's crying, for me tell her to stop crying''
Ya karashe yana nuna sabeeha dake zaune dabas a kasa, kallon inda take hidaya tayi kafin ta maida dubanta gareshi, ''clean those tears'' ta bashi umarni nan take, shi kuwa yana gama sauraronta ya goge fuskan tass, yana mai kallon ta yana murmushi sosai saboda dadin ganinta, shidai idan kaganshi yayi murmushi to sai idan yaga first love dinshi.
Miqewa hidaya tayi tsaye, kamo hannunta yayi da sauri kamar zaiyi kuka irin yanda kananun yara keyi, ''sit down and let go of my hands'' ta bashi command, ay kuwa tana karashewa ya koma ya zauna ba tare da ya sake koda motsawa ba.
Tana ganin haka ta nufi hanyar futa tana mai kallon inda sabeeha ke zaune, ''ke kuma fito''
Tana kaiwa nan ta futa daga dakin, miqewa sabeeha tayi tana mai kallonshi, yanda kasan baya fidda nunfashi yanda ya zauna ya natsu sosai, futa itama tayi daga dakin kafin ta janyo kofar.
A sitting room ta tadda hidaya dake zaune cikin shiri da alama office zataje, ta daura kafa daya kan daya fuskannan babu annuri, karasowa sabeeha tayi dan nesa da matar kafin ta tsugunna anan wajen har kasa.
''ke are you stupid? Bakida hankali ne kema aka kawoki ko kina da mentality, where are you from? Wani agency ne suka kawo ki?'' abunda hidaya taso fada mata Kenan, saidai ta hana kanta da fadin hakan don yanxu dole ta hakura da duk maid din data dauka don kula dashi saboda bazaiyiyu a barshi shi kadai ba koda yaushe gashi ita kadaice a gidan ya yarda da ita sosai,wannan yasa ta hadiye duk wani abun dake bakinta ta soma Magana with so much class.
''whats your name''
''sabeeha'' ta bata amsa
''I'm sorry for that, patient ne,wannan da kike gani brother nane, he's battling with amnesia caused by brain damage, nasan kin tsorata da shi, he's not harmful at all sannan baya yin anything weird or strange, he's just mentally unstable''
Tunda ta fara Magana kan sabeeha na kasa bata dago ba haka zalika itama hidayan ita take kallo dukda bata ganin fuskanta saidai kwayar idanunta,
''brain dinshi ke controlling mind dinshi, shiyasa yake acting kamar 13 year old child, which was the neurological effect of the amnesia, ba wani abun zakiyi mashi ba fa ce kula dashi da maganinshi sai movement dinshi that's all''
Sai a lokacin sabeeha ta dago don da farko bata gane bayanan matar ba sai a yanxu,ko ba a fada mata ba tasan wannan itace madam din da head tace bazata samu ganinta ba, nan take taji wani iri aranta, a nata tunanin da farko ta dauka mahaukaci ne ganin yanda shima ya dunga kuka saida wannan matar ta mata bayani ta gane cewa ashe ba mahaukaci bane, larura ce dashi.
Nunfasawa madam din tayi don this is the first time ta zaunar da wata kaskantacciyar caregiver tayi ma bayanin shi, shima hakan ya zama dole ne don bazai yuwu ace ita zata kula dashi koda yaushe ba tunda maa''aikatan guduwa suke yi, ita kuma bazai yuwu tabar ayyukan gabanta ba saboda situation dinshi, shiyasa ta zaunar da sabeeha tayi gaslighting dinta yanda bazata yi kokarin barin aikin ba dukda tasan yana da hot temper musamman idan abun kan nashi ya motsa ko idan ya furgita.
''zaki iya kula dashi ko bazaki iya ba babu wanda zai maki dole '' hidaya ta tambayeta
Shuru sabeeha tayi tana nazari, yau ita ake bama zabi? Tunawa da wani abu yasa ta kawai tace mata eh don bata da wani zabi, da sauqi ma dai tunda matar tace bazai mata komai ba
Katse mata tunani hidaya ''ina fatan zakiyi aikin ki daya kamata?''
Samun kanta tayi da amsata ''yes madam''
''great decision, I hope you know that your job is confidential, wannan maganar no one is allowed to know about this, so be careful''
Cije lebe tayi don taso ta danyi threatning dinta saidai kuma bzatayi hakan ba saboda plans din da take dashi.
Wasu yan maganganu ta fada mata game dashi kafin ta miqe tsaye, dakin suka nufa atare, yana nan zaune yanda tabarshi kmar statue, tana karasowa kusa dashi ta kama hannunshi, nan take kuwa ya sauke mata wani murmushi mai sanyaya zuciya, he looks so innocent.
''big baby, wannan ce new friend dinka kaji'' ta nuna sabeeha dake bayanta kamar munafuka, ''she will play with you okay? She's my frind as well bazatayi maka komai ba, nasan you will be friends with my frend ko''
Kallonshi hidaya tayi gashi nan dai a haka saika rantse lafiyarshi kalau, gashi da wani irin kwarjini da cikar haiba,kuma kamar lafiyayyan mutun,
Hannunta ya sake rikewa cikin nashi hakan ya sata zamakusa dashi kan gado, fuskanta ya shafa cikin so da kaunar ta yace ''yes first love, if she's your friend then we are friends'', murmushi tayi mashi tare da zame hannunta daga nashi ta mike,
''I love you first love'', ya fada ahankali kamar helpless child,batace mashi komai ba ta juya inda sabeeha ke tsaye a bayanta
''if there's any issue zaki iya kiran line dina direct daga landline'' tana kaiwa nan ta fuce tana mai yima sabeeha murmushi don ta dago da fuskanta.
''okay ma'am''
Hidaya na futa ta dubi agogon hannunta tana mai yin tsaki rai adan bace, saboda tayi latti sosai gashi yau din is a very important day saboda suna da share holders meeting.
Bayan futar hidaya wani irin sanyi sabeeha taji aranta, batayi tunanin haka madam din take so nice ba, gashi shikuma wannan dan uwan nata abun tausayi,maido da dubanta tayi gareshi ganin disappointed expression akan fuskanshi.
Takowa tayi inda ta zubda magungunan ta kwaso su da ruwa kafin ta komo inda yake,tsugunnawa tayi har kasa tana mai kallon fuskanshi, shiko da sauri ya dauke fuskanshi daga dubanta a shagwabe, ganin haka yasa ta cewa ''Hii''
Qin juyowa yayi saida ta sake cewa ''hii'' nan ba shuru, ganin haka ya sata cewa ''ka manta madam tace nima na zama friend dinka?''
Sai a lokacin ya juyo ya kalleta, dukda bai ganin fuskanta both yanayin yanda idanunta ke nuni da murmushi tayi mashi hakan yasa shima ya mata murmushi, baiyi wata wata ba ya sauko daga kan gadon ya zauna zaman dirshen a kasan ya kamo hannunta yana mata murmushi, ganin haka ya sata miqa mashi maganin hannunta, tabe baki yayi kamar yaga abun kyama,
''haba friend dina, kasha sai muyi wasa'' hakan data fada kuwa yasa shi washe mata baki ya bude bakin shi, zuba mashi maganin tayi kafin ta bude ruwan ta bashi a baki.
Yana gama sha ya tabe baki irin yanda yara keyin kafin yace mata ''thank you'' da mamaki ta dago ta kalleshi, yanda ya fada zaka rantse wani mai hankali ne ya fadi hakan.
''whats your name friend?'' ya tambayeta yana kura mata idanu alamun son jin abunda zata fada
''sa..bee..ha'' ta bashi amsa, dariya yayi ya maimaita abunda ta fada,
''zan iya kiranka da friend?''
Girgiza mata kai yayi shima yace ''nima zan kiraki da friend okay?''
Sun dan dade a zaune tana kallonshi shiko wasa yake da kananun yatsun hannunta don sai hannun nata ya zama dan karami a cikin tafin hannunshi.
Duk yanda sabeeha tayi ta karbi hannunta kin sakar mata yayi haka ta zauna tana kallonshi yanata faman jujuya yatsunta ita mamakin wai ace babba haka ne yake abubuwa kamar karamin yaro, daga yanda yake Magana da shagwaba da yanda yake murmushi kamar karamin yaro, yanayin yanda halittarshi take idan ba a fada maka ba zaka rantse lafiyar shi kalua kuma yasan inda kanshi yake, take taji wani irin tausayinshi aranta, ashe ita da take ganin bata samu jin dadin rayuwa ba kamar kowa har take questioning ko shin ita din ta daban ce ashe akwai mutanen ma da su they are helpless, basu san ma inda kansu yake ba, nan take ta yi godiya ga allah daya barta a yanda take, shi kuma wani irin tausayin shi ne ya fara yawo cikin jikinta, allah kadai yasan what he's going through.
Lokaci guda taji kawai she want's to help, don taimakon wanda ke neman taimako ba karamin lada mutun ke samu ba.
''friend?'' ta kira sunanshi
Kallonta yayi kamar wani mara wayo yana mata murmushi,
''kana son muyi wasa''
Da murnarshi kuwa ya girgiza mata kai, mikewa sabeeha tayi hannunta na cikin nashi, ganin haka ya sashi shima ya mike, koda ya mike a gabanta saida gabanta ya fadi, he's so huge, ga girma ga kyau, komai nashi ya fita daban, daga ganinshi kasan ba karamin mutun bane, saurayi ne mai jini a jika saidai lalura da take kan kowa wanda allah ya kaddara saita shafe shi babu makawa kuma kowa da irin kaddararsa.
Da kyar ta samu ta zame hannunta daga cikin nashi dukda yana kokari sake chapke hannun nata, ''bari na kawo maka breakfast sai muyi wasa okay?''
''okay friend'' ya amsata
Juyawa tayi ta nufi hanyar futa daga dakin, harta fuce yana kallonta