Showing 84001 words to 87000 words out of 131802 words

Chapter 29 - MATAR TAJ HAUSA NOVEL

27 Sep 2024

25370

ya soma karade wajen ''dan allah ki sakeni na tafi, wallahi nayi alkawari bazaku sake ganina anan kasar ba, garin mu zan koma, dan allah karku kasheni''

inda macen take mutumin ya nufa kai tsaye ya tsaya a gabanta ya sanya kafarshi ya shureta don a kwance take ta kasa motsawa, tsugunnawa yayi a gabanta inda ya sanya hannunshi daya ya dagota yana mai kallonta, nima dai maida dubana nayi gareta, gaba daya kamanninta ya sauya fuskarta duk an faffasa.
bakinta mutumin ya danqo babu imani ya matse fuskar ya soma magana ''babu wanda ya taba min aiki na barshi ya tafi da ranshi, koda kuwa aikin da yayi min anyi nasara, don bana barin abunda zai zamo min matsala nan gaba''

bakinta na karkarwa ga jini dankare daya bushe a lebenta data kwana kusan goma bata sanya mashi ruwa ba tace ''oga...na roke ka kamin rai, mamana bata da lafiya, gashi inada qanne har guda hudu, wallahi basu da kowa saini achan ghana,aikin da nake yi anan ne kawai nake amfani dashi wajen taimaka masu, dan allah karka kasheni, wallahi i promise babu wanda zai san nayi maka aiki, babu wanda zai san abunda ya kaini taheel family na rokeka sir dan allah karka kashe ni'' ta karashe tana hawaye, sai a lokacin danaji tayi maganar ghana na lura da ita da kyau, innalillahi ashe yar ghana ce, ita kuwa mai ya hadata da waennan???

wata iriyar dariya mutumin ya soma yi abun tsoro ba dadin sauraro mai sanya furgici, take jikinta ya soma tsuma, ''kin bani reason din da zaisa na kasheki dukda kasheki ba komai bane a wajena,bayan aikin dana turaki bakiyi min shi da kyau ba...hahahaha'' ya sake yin wata dariya irin ta tattattun mugaye marasa imani.
mikewa yayi tsaye yana mai daga hannunshi, mataimakin nashi ne ya karaso ya miqa mashi wata yar bindiga mai silencer, yana bashi ya jaa bullet din ya saita kanta, baiyi wata wata ba ya harbeta pauu, babu imani yana kallo ta sulale jini na bin tsakiyar kanta daya harba.

ihun da akayi ne yasa ya maida dubanshi ga dayan barin, wanda aka daure ne shima ya gama furgicewa don bai farka ba sai yanxu tun bayan azabar da aka gana mashi, cikin sauri ya miqe zaune yana rokon mutumin ''sir dan allah kamin rai, ka fada min duk abunda kake so zanyi maka, zan kashe maka kowa just tell me what to do, but na roki abarni da raina in exchange''
dariya mutumin ya sakeyi ''har kanada ikon yin yarjejeniya dani?, asking for something in exchange?,''

''oga dan allah kayi hakuri, wallahi zan iyayi maka komai as a reporter ka fada min zanyi komai, zan buga jarida da manya manya shaidu wanda ina tabbatar maka zai kawo downfall din taheels,''

wani abu mutumin ya soma yi da hakorinshi yana mai takowa inda mutumin yake ''kayi wasa da damarka reporter steve, ka fada min kan cewa jaridar daka buga akan taheel heir will work and zai dauka hankalin mutane zai zama scandal kuma zai kawo downfall din TG group daga baya kuma mai ya faru? abunda kayi ma ya zame masu cigaba a maimakon ya kashe masu kasuwa, tell me amfanin me kayi min?'' ya daka mashi tsawa, take reporter din ya saki futsari, yana roko da magiya,
''sir wallahi nayi duk kokarin da zanyi wajen ganin nayi attacking dinsu da waennan questions din saidai saidai...''
baima jira yaji wani ba asi ba ya harbeshi pauu shima babu imani, haka ya harbi kanshi da idanunshi harda cikinsa yanayi yana dariya gaba daya jini ya gama fallatsa akan fuskanshi da hannayeshi dukda ya saka gloves.

kallon yaronshi yayi yana mai miqa mashi bundigar hannunsa da gloves din ''clean this mess up''
''okay sir''
''i need more information akan wannan yarinyar dake gidan da duk wani movement dinta,sannan check those useless dogs dake bamu rahoton gidan, makesure that basu kawo mana wata matsala ba, any small mistake daya sake afkuwa you will be responsible for it''
yana kaiwa nan ya futo daga warehouse din zuwa wajen motarshi, zame wannan shades din nashi yayi take fuskanshi ta bayyana ''Abdul basit kenan, shugaban kamfani Bulgari kuma babban dan adawar kamfanin TG groups''

toh!! fa!! wace yarinya ake magana akai? badai sabeeha ba? daman waennan ne suka turo ta? indai haka ne to tabbas rayuwarta na cikin hadari, ku biyo ni don sanin amsar curiosity dinku da tambayoyinku acikin littafin matar taj...
Nagode.


Taheel's resident..
Bayan tafiyar khaal jamid ya zabarma sabeeha daki daga cikin guest rooms din dake kasa,sannan ya umarci head rubuta mashi list din abubuwan da mace zata buqata a cikin bedroom.
bayan tayi mashi list din yayi order wasu daga cikin abubuwan wasu kuma ya futa da kanshi don yaje ya sayo mata su.
kan kace me gaba daya bangaren ma'akata ya kachame da surutai, kowa na tofa albarkacin bakinsa don zanje yaje kunnensu saidai head ta umarci duk wanda ya futar da zancen sai an hukuntashi hukunshi mai tsauri sosai,wanda jamid ne ya umarci hakan bisa ga umarnin khaal.
sabeeha kuwa bayan jamid ya umarceta data koma part dinsu na yan aiki don ta tattara duk wani belongings dinta, jiki a mace ta shugo head maid na biye da ita don ta taimaka mata, har wani girma take bata na musamman abun ya gama daurema sabeeha kai sosai, da taimakon head ta tattara abubuwanta dukda basuda wani yawa ta ajiyesu gefe kafin jamid din ya dawo.
shiko jamid bayan fitarshi baiyi branching ko'ina ba sai wajen sayyyan abubuwa, haka ya dunga jido mata sabulai, mayuka, kayan kamshi harda few kayan sawa da dai sauransu wanda zata buqata immediately duk wani abu dayasan zata buqata saida ya sayo, ya dade sosai kafin ya dawo gida ya bama head ta shishirya komai daman already an kawo waennda yayi order har an gyagyara mata.

shugowa part dinsu na yan aiki head tayi donta shaida mata an gama shishirya guest part din.
''hello ma'am, the room is ready'' head ta fada cikin ladabi yanda take ma sauran yan gida,
kasa kallonta sabeeha tayi don saita ji wani irin da yanda head din ke bata respect, miqewa tayi head tayi saurin karbar jakar kayanta ''let em help you ma'am'' ta karashe tana mai karban jakar sabeeha, gaba maid tayi sabeeha na biye da ita a baya har suka karasa part din daidai nan fadwa ta sauko kasa tana mai kallon inda head ta nufi sabeeha, har suka shige cikin part, wani irin murmushi fadwa tayi tana mai tuna maganganun da sukayi da ita,
"I pity you" ta fada beneth her breath, kafin tabar wajen tana mai nufar part dinta, daman na sabeehan yana daga chan sako sosai don wajen na baqi ne kawai idan anyi baqi.

tunda shugo cikin dakin sabeeha ke faman kalle kallen dakin, dakine mai girman gaske ga katon english bed mai kyau yasha beddings masu laushi, gefen gadon kuma harda bedside lamp mai kyau, samun kanta tayi da bin dakin da kallo har head tayi mata sallama ta fuce bayan ta tambayeta idan tana buqatar wani abu.

har zuwa lokacin mamaki baibar sabeeha ba da abubuwan dake faruwa a cikin rayuwarta, komai is moving so fast, gaba daya it's so hard for her to accept and go with all of this, sai take ganin abun kamar a mafarki.

hanyar bathroom ta nufa, shima babba ne sosai babu abunda babu a ciki, an jera mata abubuwan wanka harda bathrob, fitowa tayi jiki a mace tana mai kallon wall closet dake facing bathroom din na glass, daga nan tsaye tana hango yan few kayayyakin dake cikin wajen ga gefen dresser an saka turaruka suma basu da wani yawa, danshi danshin data soma ji ne kan fuskanta ta yasa ta sanya hannu a wajen, hawaye ne ya soma sauko mata tama rasa dalilin hawayen, na farin ciki ne ko na bakin ciki ko na tsoro da fargaba.
yau itace a cikin daki na alfarma harda gado da katifa ga kayan sawa na mutane, abunda bata taba samu ba kaff rayuwarta kuma tana tsaye a matsayin matar wani, wanin ma mai arziki da girma da zati dukda yana da matsalar kai, wanda ko a mafarki bata taba tunanin zata iya hada hanya dashi ba,ita da ba kowan kowa ba, kaskantacciya kamarta? mara gata kamarta?, ga kuma sarqaqiya dake cikin rayuwarta sai takejin abun kamar a mafarki ga wata masifa dake tukarota wadda takeji a jikinta koda ba'a fada mata ba she can sense it,
''ya Allah kaine gatana, kaine jigona, ya allah ya karfafamin, ka dafamin, ka bani ikon taimaka wa wannan bawa naka, karka bari na karaya ya Allah,'' ta karashe tana mai kuka mai tsuma zuciya mai ban tausayi, hawayenta masu dumi na saukowa kan tafin hannunta.

Allah sarki sabeeha!!
Akwai aiki jaa agabanki😭


Matar Taj (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️

Free page
Chapter 45-46

Update!!!
washe gari da safe tayi wankanta tun karfe biyar ta tashi don ta saba already, sallah ta farayi tana idarwa ta shiga wanka, tana gama wankan ta fito da hijab dinta ajikinta.
gaban closet ta tsaya tana mai kallon kayan dake wajen, wata doguwar riga ta zaro mai mayafi blue ta ajiye a gefe kafin ta dan shafa mai datagani a wajen tana gamawa ta zura rigar, ciff kuwa kayan yayi mata masha allah ita kanta saida ta kalli kanta ta sake kallon kanta, gashinta dake daure da wani kyalle ta warware, take jelar da tayi kitso daya ya sauko har gadon bayanta, gashin ya dankare yayi due sosai saboda rashin mai da kulawa ta musamman, saurin maida kyallen tayi ta nade gashin kafin ta nado mayafin rigar akanta sannan ta zagayo dashi wajen bakinta ta rufe.

knocking da akayi ne yasa ta maida dubanta ga kofar, head ce ta shugo tare da gaisheta respectfully, ''good morning ma'am, sir jamid yace ki fito zakuyi breakfast''
shuru sabeeha tayi tana nazari ga fargaba, hakanan badan taso ba tabi bayan headmaid suka fito tare tana daga bayanta har suka karso dining din, kasa dagowa tayi ta kalli mutanen dake dining kanta na kasa, su kuwa juyowa sukayi suka zuba mata idanu banda hidaya data sdauke kanta daga ganin sabeehar.
gaba daya a tsorace take tama rasa me zatayi, sai kawai ta nemi dukawa don gaishesu jamid ya tsaidata,
''good morning sister inlaw''
jamid ya gaisheta, wata iriyar kunya ce ta lulubeta sai taji wani irin, cikin sauri ta karasa dukawa kasan ''no please ....get up, come and have a sit, bismillah'' ya mata nuni da kujerar dake gefe wajen da taj ke yawan zama.
jikinta kamar babu laka haka ta zagayo wajen kamar munafuka ta nemi zama a kujerar, sai a lokacin hidaya tayi magana, ''stop...'' ta dakatar da sabeeha,
tsayawa chak sabeeha tayi ba tare data kalleta ba kanta a kasa, ''joining us here doesnt mean nayi accepting dinki, and you have no right to sit and have breakfast before your husband, go and call him''
saurin kallon hidaya afiya da fadwa sukayi jin abunda ta fada har afiya zatayi magana fadwa ta zungureta da kafa tayi shuru.

jiki a mace ta juya ta futa daga dining area din, saitaji wani irin aranta, maima take tunani ne da har zata zauna kusa dasu, sunfi karfinta ita ba kowan kowa ba, tana wannan tunanin ta karaso saman ta bude kofar shiga, tana shiga ta nufi bedroom dinshi ta sanya hannu domin bude, bamm taji kofar a rufe a, da mamaki ta sake danna kofar shuru a rufe, kocking ta soma yi har wajen sau biyar shuru ba a bude ba, muryanta yayi sanyi ta soma magana ''friend, are you okay? open the door bibi ce''

bangaren taj yana zaune tsakiyar gado yayi wanka ya shirya hidaya ta kawo mashi breakfast yaci ya koshi abunshi, yana jin sabeeha na knocking amma ko gizau baiyi ba, karshe ma dai puzzle dinshi ya cigaba da wasa dashi.

30mins later shuru, babu irin knocking din da sabeeha batayi ba yaqi budewa harta soma tunanin kodai wani abun ne ya sameshi, tunanin sauka ta soma yi saidai tsoron abunda hidaya zatace yasa ta kasa samun kuzarin sauka din, haka ta hakura ta zauna bakin kofar abun tausayi.

shuru shuru babu sabeeha babu taj wannan yasa jamid haurowa saman, yana shugowa part din kuwa ya ganta a zaune a bakin kofa, da mamaki ya soma tambayr lafiya take zaune, ''sir na knocking ba a budeba, ban sani ba ko wani abu ne ya sameshi''
''meysa baki sauko kin fada min ba'' jamid ya tambayeta yana kama handle din kofar
''taj, are you there? are you okay''
ya sake tambayarshi shuru babu response, tuni hankali jamid ya tashi ya sake knocking, ''Big...''
bude kofar da akayi ne yasa jamid ya shigewa cikin bedroom din da gaggawa, karasawa inda taj din yake yayi bakin gado ya zauna gefensa inda sabeeha itama ta shugo bedroom din,
''hey dear are you okay maysa ka rufe kofa kaki budewa''
nuni yayi da sabeeha tare da miqewa yana ''futa min a daki na, leave my room i hate you''
da mamaki suke kallonshi ganin yanda ya rufe ido yana nuni da sabeeha ta futar mashi daga daki, ''calm down, tell me meysa kake so ta fitar maka daga daki''
jamid ya tambayeshi, ''i hate her uncle, i hate her,itace tasa first love take fushi dani, she's wicked....fita min a dakina na fita i hate you''

''taj, stop this okay, she's not wicked, ka manta friend dinka ce fa''
jamid ya tambayeshi cikin lallami, ''no uncle, she's not my friend anymore, muguwace, fitaaaa'', ya daka mata tsawa yana mai turata,
''TAJ!!'' jamid ya daka mashi tsawa, tuni ya saki kuka kamar karamin yaro, turo kofar da akayi ne yasa suka juyo don ganin wanda ya shugo, hidaya ce afiya da fdwa na gefenta, yana ganinta kuwa ya tafi wajenta a guje ya rungumeta, itama rungumeshi tayi tsam a jikinta tana mai kallon jamid da sabeeha rai a bace ta soma magana
''what's going on here, me kukayi mashi yake kuka?''

''first love please kice ta fita min a daki na bana son ganinta, i hate her''
kallon inda sabeeha take hidaya tayi, ''bakiji me yace bane?, get out!!''
jiki na bari sabeeha tabar dakin tana hawaye, gaba daya ta kasa gane meke faruwa, yau taj ke korarta daga dakinshi?, meysa toh? me tayi mashi haka? ko kallonta baya sonyi ma kwata kwata.

rai a bace jamid ya fice shima daga bedroom din yana fita hidaya ta jawo taj din bakin gadonsa ta zaunar dashi, ''sorry big baby na, sun bata maka rai ko?, don't worry bazata kara shugowa bedroom dinka ba, ka tuna abunda na fada maka ko?, karka bari ta sake zuwa inda kake, zata cutar dakai okay? kaga abunda ya faru jiya saboda ita, tana son ta raba mu, and i will not allow that okay?''

girgiza mata kai yayi ''i love you first love''
''and i love you more my big baby, yanxu ka zama big boy and i'm proud of you okay? murmushi afiya da fadwa sukayi tare kai kafin su fice daga dakin,
suna fita afiya tace ''wato nayi underestimating ukty da yawa, ya akayi cikin overnight ta sa ya tsani yarinyarnan? how''

''yanxu kin soma gane game din kenan? wannan ake kira da manipulation, kinata mita akan taqi yin komai akan common maid dinnan, yanxu tunda khaal ya shiga lamarin dole saida plan komai zai tafi, nasan ukty gaba da baya, kuma i believe in her shiyasa ban damu da lamarin nan ba, kinsan flies? wannan yarinyar kamar flies haka take a wajen ukty, kawar da ita ba komai bane a wajenta its just like dumping trash in a can''
fadwa ta karashe tana murmusawa, ''hmm ay na shaida hakan'' afiya ta amsa ta suna dariyar keta.

bangaren sabeeha daga nan saman kasa ta wuce zuwa dakinta, tana shiga ta zauna sai hawaye,watan ta biyu zuwa uku a gidan nan taj bai taba korarta ba ko ya nuna baya son ganinta sai yau, ko ranar data fara haduwa dashi baiyi mata haka ba sai aynxu, maisa? haka ta dunga tambayar kanta abunci da bataci ba kenan sai yamma.
da rana haka ta sake komawa dakin nashi, lokacin kofar na bude don haka tasa kai ta shiga, baya cikin dakin don haka ta dan jinkirta tunaninta ko yana cikin bathroom, shuru shuru bai fito ba haka ta karasa toilet din ta kwankwasa jin shuru yasa ta bude wayam babu kowa haka ta hakura tabar dakin ta fito jiki a mace.

washe gari haka jamid ya sake aikawa a kirata don yin breakfast, saman ta fara hawa dan duba taj din, dakin na bude don haka ta shiga yauma ba kowa cikin dakin don haka ta fito ciki a mace ta sauko kasan ta nufi dining area, yana nan zaune cikin yan uwanshi, yana daga gefen hidaya, dadi ya gama lulubeshi saboda yanda take bashi abunci a baki yana murna,jamid dai mamaki bai sashi ya maida dubanshi garesu ba,,sallamar sabeeha yasa suka dago harda taj din, tuni ya hade rai, gaishesu tayi jameed ne kawai ya amsa ta kafin ya mata nuni da wajen zama, tana nufo wajen taj ya miqe tsaye da cup din hot chocolate hannunshi, tana zuwa daidai wajenshi don inda zata zauna na kusa dashi ya saki cup din akan kafarta, take zafin hot chocolate din ya ratsa ta tuni tayi baya, ''oupss sorry'' taj ya fada yana mai komawa ya zauna, afiya mai zatayi banda dariya don abunma abun dariya don yanda ya dauka cup din da gangan ya zuba mata is so obvious, 'jameed da bai lura da abunda ya faru ba saida yaji dariyar afiya da yar karar da sabeeha tayi ya dago.,''subhanalla garin yaya!!'' ya miqe yana janyo paper towel ya karaso inda sabeeha ke tsugunne tana faman sharce kafarta da hannu har kafar ta danyi jaa don har turiri hot chcolate din yake,tissue din ya miqa mata yana mai yi mata sannu, ''sir banji ciwo''
saida yaga taj yana dariya ya fuskanshi abunda ya faru,
''Taj, kaga abunda kayi kuwa....?''
''jamid please,'' hidaya ta katse shi ''bai lura da mutun a wajen bane, and besides bakaji abunda tace ba? bataji ciwo ba so please dont be over reactive''
hidaya ta karashe tana mai wullama sabeeha wani irin kallo mai wuyar fassara.


afusace jamid ya futa daga wajen ya dauko first aid box ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login