Showing 123001 words to 126000 words out of 214110 words

Chapter 42 - Bakar Ta'ada Complete hausa novel

24 Aug 2024

11120

tunanin me ya faru. Amma na kasa gano ko na yi masa wani abu.
Na gama, na tafasa shayi. Na ha'da komai na kai falon.
Muka fara karyawa amma babu doguwar hira yadda ya saba mini.
Muna zaune, jigum jigum yaro ya yi sallamah daga ba'kin k'ofa ya ce "Wai ana sallama da Tijjani".
Na zabura na ce "Kai shigo". Ya shigo na kare masa kallo, gaba'daya ba zai wuce shekaru takwas ba.
Na zare masa ido a dalilin na ji haushin gatsa sunan da ya yi. Na ce "Ba zaka ce ana sallama da maigidan ba sai ka wani gatsa sunasa tamkar sa'an ka. Zaka iya fa'din sunan Babanku gatsal?"
Yaron ya yi shiru yana kallona da alamu ma tsorata ya yi kada na rufe shi da duka.
Sai lokacin Bulkachuwa ya ce "Kai je ka ce "Ina zuwa".
Ya mik'e ya bar ni.
Tunda ya fita sai yamma ya dawo. Bai ce mini ga inda ya je ba, nima ban tambaya ba. Na gabatar masa da ruwa da abinci na yi tafiyata wajen k'unshina. Domin na fara jin haushin daddaurewar da yake yi mini haka siddan.
Haka da daddare ma ya sake matse wa bai ta'ba ni ba.
Kwanaki uku ke nan, muna haka, na fara k'osawa domin gaskiya ya riga ya yi mini sabo a harkar, tun ina turjiya, ina raki har na zama yar hannu da al'amarin nasa. Sannan na fahimci nima irin halittarsa ce da ni. Ina son harkar, ina jin da'din ta.
Ban sani ba ko ya fahimci hakan ne shi yasa zai fara yi mini gayya.
Sai na yun'kura zan tambaye shi dalilin sauyinsa sai na yi maza na fasa. Ina jaddada wa zuciyata na ja ajina. Shi da yake namiji ma ya yi jarumtar runtsi idonsa daga gare ni, sai ni mace ce zan k'osa?.
Dan haka na yi hakuri, na zuba masa ido, amma gaba'daya bana cikin nutsuwa. Mussaman idan ya shek'a kwalliya ya baza turare sai na ji tamkar na yi tsalle na mak'ale shi.
Sai ya fita nake samun damar na yi kukana. Ina ayyana wai ni Tijjani yake yiwa wannan wula'kancin haka siddan dan ya fahimci na fara sonsa.
Na fara zargin akwai abin da yake yi a waje da ya sanya yake iya kawar da kansa a kaina.
Gaba'daya na rasa sukuni. Na yi wani iri.
Ranar da muka yi kwana hudu a cikin wannan halin. Gaba'daya ya juye mini, tamkar ba shine mai rawar jiki da tsoron ganin fishina ba. Tamkar ba shine mai kulafacina kamar me ba.
Ranar da wuri ya shigo. Na yi wanka na sanya riga da wando silky. Wando iya guiwa rigar ma iya tsayinta kenan wando kawai ta rufe.
Na taje gashina da yake a tsefe na mulke shi da man gashi na kwakwa da asalain man alaiyadi. Na dauko turarena na mai maiko na oudi na murtsike hannayena da jikina har ma da gashin. Na sake dauko turaren active woman da Tijjani ya canja mini na bi jikina na feshe. Na saka hula marar nauyi kalar kayan barcin nawa.
Na fita na same shi yana kallon labaran NTA Bauchi.
Na zauna ya dago ya kalle ni. Domin na tabbatar kamshina ya kai masa caffa mai yawa.
Na sassauta na ce "Wai mun b'ata ne?"
Cikin nutsuwa ya ce "Da yaushe?"
Na yi sakare ina kallonsa. Na numfasa na ce"Ai tambayar ka na yi."
Ya girgiza kai ya ce "To ke mun b'ata ne?"
Na rasa me zan ce masa ma. Na nisa na ce "Nasan bamu b'ata ba. Amma na ga ka sauya ne".
Ya daure fuska ya ce "Tun yaushe na canja d'in?"
Na ce "Tun kwanaki hudu, tun ranar da ka kai ni gida".
Ya yi shiru tsawon lokaci kafin ya bu'de baki ya ce "Kuma sai yau kike bu'katar sanin dalilin sauyin nawa saboda baki d'auke ni a bakin komai ba?"
Ga mamakina sai na shiga rud'u na ce "To ai kai ne zaka fa'da mini."
Ya girgiza kai ya ce "Babu damuwa ki cigaba da zaman jiran na fa'da miki".
Idona ya ciko da k'walla. Na zuba masa ido sosai na nuna kaina da yatsana na ce "Ni kake wula'kantawa saboda kawai ka shiga ka fita kasa na saba da kai ko?.
Ai shike nan na gode".
Daga hakan na kifa kaina a hannun kujerar na fashe da kuka mai tsananin gaske.
Ya taso da azama ya zauna kusa da ni. Ya ru'ko ni na fizge tare da ce wa "Ba ruwanka da ni, komai kake yi na barwa Allah. Ka cigaba da yi mini wula'kanci komai lokaci ne ai, watarana ba zaka yi ba".
Ya sake tarairayo ni jikinsa yana kamo weak points dina. Jikina ya fara tsuma. Amma na sake k'wace wa na mike, cikin muryar kuka na ce "Bana so Tijjani, ka bari na fa'da maka".
Na fice na yi d'akina ina kuka sosai.
Sai da ya yi wanka sannan ya shigo d'akin har lokacin kuma ina dukunkune ina kuka sosai.
Sai da ya yi shafa'i da wutiri sannan ya tarar da ni a gadon.
Bai kwanta ba. Ya zauna ya kaurara murya ya ce "Asiya tashi mu yi magana."
Na share shi, na k'i na nuna ma na ji shi.
Ya saka hannunsa biyu ya d'aga ni ya zaunar da ni.
Na sake yun'kurin koma wa na kwanta dan na nuna masa ba ni da lokacinsa, sai kawai na ji ya bu'de murya sosai ya ce "Wallahi idan kika kwanta idan ranki sun kai dubu ki tabbatar sai na bisu d'aya bayan d'aya na b'ata su."
Jin ya rantse sai na zauna din. Amma na tattaro dukkan fishi na yab'a a fuskata.
Ya jima yana kallon yadda nake tunbatsa.
Shima ya d'aure tasa fuskar ya ce "Ki saurare ni da kunnen basira Asiya Toro".
Jin ya fadi wannan sunan na sake hassala ainun.
Ya furzar da iskar baki ya ce "Ranar da muka je gida kin wula'kanta ni, kin tozarta ni!
Watannin baya na fa'da miki, ba zai yiwu a gabana ki wula'kanta iyayenmu ba. Idan kin ture girmansu na k'annen mahaifinki ne, to ki sani baki isa ki ture nasabarsu da ni ba. Ina kuma da hak'kin ki mutunta iyayena. Dole ne, wajibi ne Asiya ki mutunta mini dangin uwata matu'kar kina son mu zauna lafiya. Ba zai yiwu ina aurenki kuma in zuba miki ido ki dinga yin rashin mutunci ba. Bilhiillazi wannan ne karon k'arshe da zaki ga wani cikin iyayenmu ki k'i gaishesu, ko ki yi musu gaisuwar je ka na yi ka".
Na fara kuka ina ce wa "To ina ruwanka ne kam. Kai baka ga irin k'iyayyar da suke yi mini ba? Saboda baka kishina, saboda kai sun yarda gyatumarka yar'uwarsu ce shiyasa kake ganin bekena. Duk abubuwan da suke yiwa ubanmu baku da kaico. Ai ka sani ba sai na fa'da ba, ko auren nan nawa sun yi sanadinsa ne dan kawai suna ganin bazan cigaba ba.
Amma da sun tabbatar zan samu nutsuwa a cikinsa a sai sun rugurguza shi. Yanzu ma kuwa nasan akwai lokacin da zai zo da zasu rabamu tunda zuciyarsu mai k'yashi ce."
Ya buge mini baki ya ce "Kada ki kuskura ki fa'di maganar banza a kansu a gabana. Dole fa ki mutunta su a matsayin surakanki tunda ke kin yanke nasabar da ta hada ku".
Cikin gigita na ce "To ka sake ni, bana son yin surukuta da su. Kai ma bana sonka Tijjani".
Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*

Jikinsa ya yi sanyi domin ya ga matsanancin fishi a tare da ni.
Ya numfasa ya ce "Na sani ai ba kya sona Asiya. Ban manta ba, amma na sakankace a d'an zaman da muka yi, zaki iya mini kawaici da alkunya akan abin da kika san zai musguna mini tunda kin sani sarai an jarrabe ni akan son ki. Amma yanzu na gane da gaske ba kya sona tunda akan idona kika k'i gaida Baban Tsakiya cikin mutunci duk da kashedin da nake yi miki da ido. Sannan kika gaida Jabir cikin falli har kina kiransa Yaya alhalin kin kankare zumuntar da ubansa."
Na yi shiru domin kam jikina ya yi tub'us.
Ya cigaba da ce wa "Saboda shi kina sonsa, kuma yafi ni ku'di shi yasa kike ce masa Yaya ni kuma ki gatsa Tijjani gatsal duk da na girme shi kuma ni ne mijin ki. Asiya ba zamu tab'a daidaita wa da ke ba alhalin kin ri'ke BAK'AK'EN TA'ADODI. Yanzu duk k'uruciyar ki ai k'iris ya rage ki yi sha bakwai. Kin san kuma hukuncin wacce ta bu'de baki ta ce mijinta ya sake ta ba tare da gamshasshen dalili ba. Sannan kina da ra'ayin ruk'au na k'ullaci. Hakan kuma ba siffar mace ta gari ba ce. Kamata ya yi zuciyar mace ta zama mai taushi da sassauci ba mai tauri da tsanani ba."
Na ji kunyar kalamansa mussaman akan J.
Na tabbatar shi ba na ce masa Yaya. Amma ban da yau ai nafi wata ban kama sunansa ba, sai dai na yi masa magana kawai. Domin na da'de da daina fa'da a dalilin kunya na kama ni tare da nauyin gatsa sunan nasa.
Na tura baki na juya baya. Cikin k'unk'uni na ce "To ai kai ma kana da Bak'ar Ta'ada din, akan me tun a ranar ba zaka fa'da mini laifina ba, sai kawai ka k'ulla ce ni, ka tsiri fishi. Ni ba Allan musuru ba, ta ina zan san kuskurena?"
Ya matso jikina ya ce "Da kina sona ai tun a lokacin zaki fahimci sauyin nawa, sai ki shawo kaina ki ririta ni, ki mantar da ni b'acin ran da nake ciki. Amma saboda am nothing to you ai share ni kika yi. Kika tattara kika yi wurgi da ni".
Na cuna baki na yi shiru. Ya mik'e dukkan k'afafuwan sa. Ya janyo ni ya kwantar a kai. Ya shiga wasa da gyararren gashina. Murya a dak'ushe tabbacin yana cikin kewa ya ce "Bana son abubuwan da kike yi a gabansu. Su din iyaye ne. Ta ko wacce fuska sune a sama da ke.
Zan yi hakuri da komai akan sha'anin ki, amma ban da na fito na fito da iyaye, bana so, ki bari."
Na yi shiru ban amsa ba.
Ya sassauta murya ya ce "kin yi shiru."
Na sake yin shiru still.
Ya zame ni daga jikinsa ya juya baya ya yi kwanciyarsa.
Ina ganin hakan ai kuwa na tak'ark'are na zunduma masa fallashasshen kukan da baya so.
Ina ce wa "Tunda juninka k'ullaci ne ka mayar da ni gidanmu kawai".
Ya juyo da azama ya ce "Asiya ki cigaba da wula'kanta ni. Amma ki sani komai zaki yi ni ba zan mayar da ke ba, domin ina son ki, ke da ba kya sona sai ki tafiyar ki, hakan kuma ba shine k'arshe farin-ciki a gare ni ba."
Na sassauta kukana domin na ga ya hassala sosai.
Na dinga yinsa kasa kasa irin mai cin rai din nan.
Da ya gaji da jin kukan nawa ya saka hannunsa ya ja ni jikinsa ya ce "Yi shiru Asiyata, amma ba zamu shirya ba sai kin ba ni hakuri dole".
Duk yadda na k'agu mu shirya fuska na yi da ce wa "Ai ban maka laifi ba. Sannan ba dan komai nake ce wa Jabir Yaya ba sai dan yana ce mini Yabi ne. Amma kai sai ka dinga ce mini Asiya Toro babu ko sha'awa ma".
Ina rufe baki ya ce "Har abada ba zan ce Yabi ba, idan ya so ba Tijjani kawai ba, ki fa'di cikakken sunan nawa Tijjani Yusuf Bulkachuwa! Marar kunya. Shine rannan kika yiwa yaro sababi akan ya k'ira ni da Tijjani to ke d'in kin saya ne bare ki ji ciwon wani bai saya ba. Kuma ni ban damu sai kin saya d'in ba".
Na nisa na saki ajiyar zuciya irin wacce ake yi idan an ci kuka sosai. Na ce "Ni fa tuni na samo maka sunan da zan fa'da maka, amma sai na haihu".
Maganar ta zo masa a bazata. Ya ru'ko ni ya ce "Kina son haihuwa ne Asiya?"
Da sauri na ce "Ina so sosai, domin duk wanda muka taso ko wacce ta haihu. Wadanda aka yi aurenmu tare Nasiba da Ubaida dukkansu ciki ne da su, ni ce kawai ba ni da shi".
Na fa'da da karyayyar murya.
Ya sassauta ya ce "Asiya haihuwa lokaci ne da sannu ke ma wataran zaki gan ki da naki cikin. Tunda kin daina guduna, sannan nima ina iyakacin k'ok'ari, kawai mu dinga addu'a".
Na ce "To. Ka ga Gwaggo ma ta ce ba zata zo gidan nan ba sai na haihu".
Ya rungume ni sosai ya ce "In sha Allah zaki haihu Asiyata. Mace kike so ko namiji?"
Kai tsaye na ce "Ni dai na samu cikin nafi so. Ko mai na haifa ina so ba ni da za'bi."
Ya yi dariya ya ce "Tom shike nan Allah zai bamu In sha Allah! Kawai ki kara zama jaruma, ko sau nawa za'a yi kada ki yi musu ko ki ce kin gaji".
Na ce "Da gaske idan na yi haka zan samu cikin ko dai wayo zaka yi mini?"
Ya k'yal-k'yale da dariya ya ce "Ba wani wayo gaskiya nake fa'da miki Asiyata".
Daga hakan kuma ya shiga kissing d'ina tare da zafafan sakonni masu rikita ni. Sai da ya tabbatar ya rura mini jiki. Sannan ya sake ni ya kwanta tare da ce wa "Au ashe baki ba ni ha'kuri ba fa, bamu shirya ba".
A hankali na ce ", Mun shirya mana, ba har ka yi dariya ba yanzu".
Ya ce "Ai ba ki bani hakurin da na ce ki ba ni ba".
Na fara kukan shagwaba, ya juyo ya ce "To fa'da mini a kunne na ji".
Cikin kuka kuka na ce "Allah ya baka hakuri".
Ina fa'din hakan ya rungume ni yana cewa"Ameen little girl na ha'kura na huce gaba'daya".
Daga hakan kuma ya dinga b'arin jiki a kaina, komai ha'dama ha'dama yake yinsa har na gamsu k'arfin hali ya yi a kwanakin amma ba samu yake yi a waje ba. Domin duk kulafacina sai da na k'osa amma shi bai k'osa din ba".
Haka muka cigaba da gurgurawa ciikin rufin asiri. Dai-dai gwargwadon k'arfinsa yana yi mini komai.
Matsalar da ta fara damuna har cikin zuciyata rashin samun cikina gashi watanmu goma da aure Nasiba jiya ta haihu Ubaida kuwa har an saka ranar da za'a yi mata tiyata(c.s).
Da aka sanar mini da haihuwar yini na yi cikin sanyin jiki.
Sai kuma matsalar Rafi'a. Wata guda da kammala karatunta na digiri ta tattaro ta dawo gida gaba'daya.
Kusan ko yaushe a k'ofata take. Idan ina k'unshi sai ta hakince a falo da sunan kallo. Ko Tijjani ne ya dawo ba zata tashi ba, sai ma ta yi ta jansa da zancen makaranta su yi ta hirarsu. Ko idan ta ga ya fita sai ita ma ta bi shi su fita tare.
Ranar da na yi masa k'orafi ya balbale ni da sababin wai na raina shi, ban yarda da shi ba.
Na kame baki na yi shiru, kuma sai da na ba shi hakuri akan hakan.
Tunda ya ja ya tsaya ba shine yake zuwa wajenta ba, ba shi yake kiranta ba, tunda bana so ta zo mini gida to na hanata zuwa kawai.
Na rasa ta yadda zan kore ta domin dai gaskiyar magana uwarta tana mini kirki da alheri mai yawa a matsayin ta na babba. Bayan haka ita kanta Rafi'a din kirki ne da ita. Bai zame mata komai ba ta yi mini gyaran gida ba. Kawai ni yadda take shige wa Tijjani ne bana so, domin na riga da nasan shi akan lutayen mata.
Wadannan matsaloli sai suke neman sauya zaman aurenmu. Domin ni a k'arancin shekaruna dauka na yi Tijjani ne ya ki yi mini cikin kawai. Sannan yana son Rafia.
A hankali na fara janye masa, abubuwa suka fara sauya wa a tsakaninmu.
Na daina sauraronsa ko na saurare shi ma to kuwa sau daya ne shima ba cikin da'din rai ba.
Ranar da na dawo daga sunan Nasiba kuwa. Kuka na zauna na yi masa mai d'aga hankali k'warai da gaske. Ina yi ina ce wa "Akan me zaka matsa mini sai ka ta'ba ni bayan bana so, na riga na gane ba cikin nan zaka yi mini ba, dan haka na gaji da nukurkusata da kake yi babu sassauci babu kuma wani abu da zan samu."
Ya zuba mata ido yana kallon yadda take kuka bilhakki. Ya tafi tunanin shekarunta. Watan da ya shud'e ta ciki shekaru sha bakwai.
Ke nan akwai k'uruciya mai yawa a tare da ita. Bai kamata kuma ya biye mata ba, domin ya fahimci da dukkan zuciyarta take ganin shine bai mata ciki ba.
Ya numfasa ya saki gauron numfashi kafin ya ce "Asiya Allah ne fa mai bayarwa, kuma ba mantawa ya yi damu ba. Kika san tanadin da yake yi mana?"
Cikin kuka na ce "Ba wani, ni kawai ciki nake so, ai ko wacce ta haihu saboda mazansu suna sonsu, sai ni ce kawai saboda baka sona, kowa wani gani gani yake yi mini ba'a yi mini ciki ba".
Dariya ta so subuce masa, amma ya maze ya ce "Asiya zai yi wahalar gaske a samu wacce ake takarta irin yadda nake yi miki a cikinsu. Kin san da yawan yi ne sanadin samun ciki da yanzu kin haihu sau uku.
Amma shi samuwar ciki ai ikon Allah ne."
Da rawar murya na ce"Ba wani kawai dai ni ce baka so na samu ba, ga Ubaida nan yarinya da ita jibi za'a ciro mata d'a ko y'arsu, kai ma da su Nasiba ka aura ai da tuni ka yi musu.
Ina goge idona na ce "Wallahi na baka nan da wata d'aya, idan ban samu ciki ba to ba zan zauna ba".
Ya sake zuba mini ido cikin mamaki mai yawa. Ni kuwa ko d'ar ban ji ba.
Ya ha'diye komai ya ce "Shike nan Allah ka taimaki Tijjani ya yiwa Asiya Toro cikin y'an-uku".
Na yi maza na ce y'an uku tashi guda? Y'an biyu ko daya ma ya isa."
Ya fara ta'ba ni, na bige hannun na ce "Ni fa yau na gaji Wallahi".
Ya ce "To shike nan Asiya Toro

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login