Showing 66001 words to 69000 words out of 214110 words

Chapter 23 - Bakar Ta'ada Complete hausa novel

24 Aug 2024

11098

Ba ya sauke hakkin da shari'a ta wajabta masa.
Duk k'uncin da take ciki yau shekaru kusan takwas da aurenta, bata ta'ba zuwa gabana da nufin wata matsala ko da zummar na taimake ta ba.
Na sani kuma tana bu'katar a taimake ta, amma da yake ta dauko ha'kurin uwarsu ta shanye komai tana zaune da y'ay'anta, sai kuma ta yi tabarar koyon sana'a cikin cire girman kai da buri.
Shiyasa ni kuma ban ta'ba yin sallah ban roka mata sassauci a wajen Ubangiji ba.
Duk kuma wanda Allah ya ba shi nisan kwana zai ga yadda Allah zai albarka ci zuri'arta. Allah sai ya yi mata tukuicin hakuri da biyayyar da ta yi da ikon Allah".
Da k'yar na tokara na tashi zuwa daki na tarar da Gwaggo tana share hawaye.
A sanyaye na ce "Gwaggo baki huce da ni ba ne?"
Ta girgiza kai sai kuma ta ce "Ina mamakin duk alherin da mace zata yiwa namiji na ha'kuri da juriya akan al'amarinsa ko na ahalinsa. Amma idan d'anta ya yi laifin da ita kanta bata sani ba sai ya shafeta.
Ko sai yaushe uwa zata kubuta daga irin wannan kalubalen a k'asar hausa?
Duk lalacewar uwa ba zata so d'anta ya zama marar tarbiya ba. Na sani akwai uwayen da basa son laifin ya'yansu, amma me yasa aka fi yiwa masu hakuri da kawaici raddi?
Yanzu duk laifinki a kaina ya k'are. Yana wahalar gaske Babanku ya yaba ha'kurin da nake yi a gabana sai dai a bayan idona. Shikenan ita mace ba za'a yabe ta a kurzanta ta ba?
Ba za'a yayata alherinta ba, amma kuskuren da ba ita ta yi shi ba ma sai an yi mata tuya a kai".
Ta fa'da hawaye na sake k'wace mata.
Na taya ta kukan da take yi domin na sani sanadin tafiyar da na yi ne.
Da rawar murya na ce "Ki k'ara hakuri Gwaggo! Idan kika yi sa'a Ubangiji ya yabi ha'kurinki shikenan kin gama dace wa."
Ta zuba mini ido sosai ta ce "Kema na hore ki, ki yi hakuri, ki yi juriya, ko bana raye shine tsanin da zaki ri'ke, ki tsallake dukkan k'alubale a wannan duniyar".
Jikina ya sake sanyi. Domin kalmar ko bata raye ta yi matu'kar dukana.
Na ha'diye kukan na tayar da sallah.
Sai dai hawaye bai yanke mini ba, na idar da sallar ina zaune ina lazimin Ya ladifu da fatan na samu sau'kin halin da nake ciki.
Washagari sassafe Babah ta koma Bulkachuwa.
Ala dole na ha'kura na zuba ido aka cigaba da shirin aure, wanda yake sake k'arantowa.
Duk da na ha'kura amma wata irin rama nake yi mai tayar da hakankalin masu kallona.
Na sake zama wata yar sumoli da ni.
Ba annuri a fuskata.
Na kasa yiwa jama'a kitso bare kuma lalle.
Idan ba k'ure wa ta yi ba yana wahalar gaske na yi magana. Na zama very silent.
Makarantar boko ma na daina zuwa duk da a shekarar k'arshe muke.
Kwatsam sai ga Yaya J ya dawo daga Bauchi.
Bai samu labarin aurena da Bulkachuwa ba sai a jiya.

A ki'dime ya iso gidan Marina. Ya gurfana gabana Dada yana fa'din "Dada wanne irin abu ne haka?
Ta ya ya za'a dauki Yabi a bawa Bulkachuwa! Saboda Allah Dada wannan daidai ne?
Me yasa aka hana shi Nasiba baki tsawatar ba?
Me yasa aka tirsasa ni na auri Maijidda?
Akan me ita kuma za'a yi mata hakan? Ciwon abin ba shi ya yana sonta ba.
Idan saboda kada na sameta ne kuka k'ulla wannan al'amarin, na sadaukar da soyayyar da nake yi mata, na janye, bazan sake furta sonta, ko a bani aurenta ba. Amma ki yiwa Àllah Dada kada ki kassara mata rayuwarta.
Waye bai san BAK'AK'EN TA'ADODIN da yake yi ba?
Ta ko ina basu dace da juna ba.
Yabi mai son sana'a ce, yayin da Tijjani bai damu da ya gina kansa ba, irin mazan da suke barwa mace hidimar da shari'a bata dora musu ba ne.
Tijjani manemin mata ne, yayin da Yabi ta kasance mai tsananin kishin gaske.
Tijjani fari ne, Yabi bak'i take so.
Tijjani mai zafi ne. Yabi mai tsiwa ce.
Ta ina zasu ji da'din zama?
Ta ina suka dace?"
Kafin Dada ta ce wani abu Bulkachuwa da yake tsaye a bakin k'ofar Dada ya ce "Bamu dace da juna ba Jabir. Sai dai ka sani Ubangiji ne yake jujjuya al'amura, yake kuma k'addara afkuwar komai ko da bamu tsara faruwarsa ba.
Maganganunka sun yi matu'kar ta'ba zuciyata. Tabbas gaskiya ka fa'da, duk da na ji na muzanta. Da a ce son Yabi bai yi mini kamun kazar kuku ba.
Dana tirje wa aurenta. Sai dai an jarrabe ni akan ta cikin kankanin lokaci."
Ya numfasa ya sake fa'din " Na gode da ka ankarar da ni, duk inda sana'ar da zan gina kaina take zan nemota zan kuma yi duk wahalar ta.
Laifin da ka jingina mini kuma na neman mata wannan kai da Allah! Domin baka ta'ba ganina na yi ba.
Allah ne shaidar na yi tuba, Allah ne shaidar tunda na yarda aka zartar da hukuncin da ya yi a kaina ban sake yi ba.
Amma kun rike abu kuna ta faman jifana da shi."

*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
Ya fa'da cikin wani irin yanayi na bacin rai mai tsananin gaske.
Dada ta zuba masa ido cikin son ta nazarce shi.
Ta k'asa ha'diye abin da ta fahimta akan sa cikin dak'ik'a.
Ta nisa ta ce "Mai sunan manya, shin ka fa'da komar Yabi ne har haka?"
Takaicin ta ya k'ume shi.
Bata ce da Jabir komai ba, da yake faman sakin maganganun da suke nufin tozarci a gare shi.
Amma tana neman shiriritar da maganar. Bai ce mata k'ala ba ya juya tamkar ya tafi, sai kuma ya toge a jikin bishiyar zogalen da take gefen dakunan ka'dan. Cikin bacin rai na sosai.
Yayin da jikin Jabir ya yi sanyi domin ya fahimci ba k'aramin son Yabi Tijjani ya afka ba. Sannan ya ji kunyar maganganun da ya ji yana yi a kansa.
Dada ta kalli Jabiru ta ce "gara ma da baka auri Yabi ba Jabir. Na fahimci irinsu ne matan jaraba. A kansu ba abin da namiji ba zai yi ba. Mafi yawa haka zaka gansu yan firit amma suna murza mazaje ingarmai. Yadda kake sanyi k'alau din nan ba zaka sarrafa ta ba. Ko mai sunan manyan da yake a tsaye, tun komai bai gitta a tsakaninsu ba, ga shi nan yanayinsa ya nuna ta riga da ta shiga ransa ta yi kane kane".
Cikin jin nauyin maganarta Jabir ya ce "wacce irin magana ce haka Dada da girman ki?"
Ta nisa ta ce "Gaskiya ne mana! Kawai murnar da nake yi masa d'aya ce. Ta iya sana'ar samun ku'di, dolenta ta fito da ku'di su ci abinci. Idan ku'din da suke saka ta yiwa iyayenta raini basa zama mata ai ta nutsu ta girmama manya".
Tana rufe baki Jabir ya ce "Haka su Baban suka fa'da miki shiyasa kika tirsasa aka yi wannan bahagon hadin?"
Ta yi dan tari kafin ta ce "Gaskiyarsu ne ai! Sannan shi mai sunan manya tunda ba shi da sana'a asirinsa zai rufu".
Jabir ya ce "Gaskiya kun kassara rayuwarta, amma akwai Allah. Ina fatan alheri ya biyo baya, sai dai har yau din nan ban hakura ba. Na sani *Hannu daya* baya daukar jinga. Bazan ha'kura da ita ba har sai na ga ranar da aka shafa fatiharta da wanina. Daga ranar na zubar da makaman nemanta. Amma matu'kar ban mutu ba idan an kaddara mini cikar burina zai zama gaskiya. Idan da rabona zata dawo mini, ni kuwa zan aureta komin tsufanta, domin ita nake so ba wani abu a tare da ita ba".
Dada ta kyabe baki ta ce "Idan k'asa ta rufe mini ido komai ma sai ku yi tunda ban ga ni ba".
Tijjani da yake jinsu zuciyarsa ta dinga bugawa da k'arfin da ya zarce ka'ida.

Yana son ya je ya fa'da wa Dada duk lalacewarsa bata kai mace ta ciyar da shi ba, bai yi mutuwar zuciyar da macen aurensa zata dauki nauyin kanta da nasa ba. Sannan ta fahimtar da y'ay'anta hakan.
Amma sai ya daure ya ha'diye. Ya ja jikinsa ya fa'da dakinsa ya fa'da kan katifarsa.
Wani irin yanayi na shigar sa na tsananin bacin rai da ya sababa masa k'arfin zuciya.
Domin gaba'daya ji ya yi hatta dako na daukar buhun gero da na su wake zai iya yi, dan ya ciyar da Yabi da guminsa ba wai ta ciyar da su ba.
Idonsa ya ciko da hawayen tausayinta domin ya gane k'iyayyar da ake yi mata ne ya sanya aka bashi aurenta.
Ya yi shiru yana nazari wato saboda ana ganin shi din lalatacce ne. Ana ganin shi ba zai amfana wa kansa komai ba, bare ita ta amfana da shi. Ana kuma fatan ya dauwama cikin lalace wa da mutuwar zuciya.
Sai ya tsinci kansa da tambayar shi da Yabi wa aka fi tsana ne a gidan Marina?"
Take ya muskuta ya janyo wani kwali.


*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*
*Lame fa garin su Yabi ne*

Ya dauko memo da biro, ya yi rubutun magananun Jabir, da wanda su Baban Tsakiya suka yi da ya ji a harshen Dada.
Da irin manufar ba shi Yabi. Da yadda ake fatan ta tabbata cikin halin ni 'ya su.
Sai kuma ya je shafi na gaba sosai ya rubuta "Zan yi komai na halal dan na sauke nauyin da yake kaina.!
Allah ka sani ban sake aikata zina ba! Allah ka taimake ni ka cigaba da tsare ni.
Allah ka fahimtar da ni sarrafa mace ta yadda Yabi zata rayu cikin farin-ciki a hannuna.
Allah ka hore mini kofofin arziki ta yadda zan sauke nauyinta ba tare da tallafinta ba.
Na sani al'kawarin ka baya tashi, da kanka ka yi al'kawarin taimakon wanda ya k'udire niyyar aure saboda kai. Ga ni bawanka, Ibnu bawanka cikin kankan da kai, ka taimake ni, ka kubutar da ni kunyata a idonta da na dangimu. Allah ka hore mini lafiya, ka sanya mini hakuri akan sha'anin ta, sannan a mallaka mini zuciyarta da tunaninta." Sannan ya rubuta kwanan wata.
Ya rufe yana jin girman k'alubalen da yake gabansa.
Wani irin son ta da tausayinta yana sake bin dukkan jikinsa yana kutsawa.
Har yake jin anya akwai wanda ya so mace kamar yadda yake jin son Yabi ya sake shak'e shi a yanzu?
Domin shi son ta yake yi babu wani dalili na sha'awa ko na burge wa.
Na farko yafi son manyan mata masu manyan halittu. Yabi kuma yar mitsil mai k'ananun halittu, maimakon ya ga ba hakan yake so ta zo ba. Sai yake jin ko bata da komai na cikar mace yana sonta a hakan.
Na biyu yafi son mace mai sanyin hali, mai kawaici.
Amma daga ranar da aka jefa masa sonta shikenan ya ji da tsiwarta zai yi amfani wajen kutsawa dan ya sami kusanci a zuciyarta.
Ya sani ba zai yarda da rashin kunyar da ta wuce ka'ida ba.
Amma yana fatan a cikin rashin kunyarta ya dinga isar mata da sakwanni masu girma.
Na uku akan abin da aka yi mata na tirsasa Jabir auren Maijidda, da kuma yadda uwar Nasiba ta ture komai na zumunci ta fadi maganganu marasa dad'i a gaban mahaifiyarsa! Shike nan ya k'yamaci auren zumunci.
Amma a yanzu yadda yake jin Yabi zai iya yin komai dan ya same ta.
Ya gamsu tausayi da sonta sun masa rubdugu.
Ya rufe littafin ya mayar da shi ma'adaninsa.
Ya jima a zaune yana ta tunanin sana'ar da zai fara.
Ya saki gauron numfashi! A fili kuma sai ya ce "Allah ka hana Tijjani sanya Yabi kuka! Allah ka hana ni zaluntar ta. A hore mini ita ya Ubangiji".
Ya zabura ya mik'e yana ganin lokaci ya yi da zai daina buga buga ya samu tartibiyar sana'ar da zai dogara da ita tunda nauyi mai yawa ne zai hau kansa, wata'kila ma badi war hakan yana shirin zama Abba.
Murmushi da kunya suka subuce masa ya dinga sosa k'eyarsa tamkar yana gaban manya ne.
A fili ya furta wa ya ga "Yabi as uwa?"
Sai dariya ta sosai ta kama shi, har bacin ran da Jabir da Dada suka cusa masa ya yi sauki.
Ya fito ya nufi wajen Alh Tsoho magini dan ya ji ko zai masa hanyar samun aikin ginin.
Yana tafe sanye da yadi na wando da riga bata kai guiwar sa ba.
Kamar kullum a wanke suke amma fa babu guga.
Sannan ya saka hular sanyi ya rufe gashin kansa.
Domin tunda aka furta za'a bashi auren Yabi. Bai sake yarda an ganshi da gashin kansa ba, duk da ya ki aske wa.
Ba wanda yake jin kunyar ya ganshi da sumar irin Baban Marina. Domin ya sani baya so, ya sha tisa shi a gaba ya saka a masa askin akan dole.
A yanzu kuwa wata irin kunyarsa yake ji ta sosai domin bayan kawunsa ne da yake yi masa adalci, yanzu shirin zama surukinsa yake yi.
Bulkachuwa da kansa ya yi amannar ba dan zuciyar Baban Marina irin ta daddako ba ce da ba za'a yi masa wannan k'arfin akan diyarsa ba. Ba dan alherinsa mai yawa ba ne, da ba zai ba shi aure ba, komai za'a yi kuwa.
Amma ya yi shahadar ba shi, babu dogon turanci. Yana tafe yana fa'din "Allah ka fitar da Tijjani kunyar Baban Marina".
Ya sha kwanar shiga cikin wani kwararo sai kawai ya fara jin k'amshin turaren da yake ji a jikin Yabi da kuma wanda yake shaka a jikin Jabir.
Ya shiga sai kuwa ya hangosu kowannensu jingine a garu.
Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi.
Kishi mai tsananin gaske ya dabaibaye shi.
Tamkar ya juya sai kuma ya tsinci kansa da tunkararsu.
Ya zuba musu ido. Yabi na kuka sosai yayin da Jabir idonsa ya kad'a ainun.
Sau d'aya za'a kallesu a gane suna cikin tsananin soyayya da kuma halin cankacakare.
Ya kalli Jabir da yake tsab da shi cikin shadda ruwan toka ta sha guga. Farin gilass ya mak'ala.
Ga k'amshi mai da'di na tashi a jikinsa domin komin hassada baka isa ka ga wani abu na rashin tsabta ko gayu a tare da Jabir ba.
Yayin da Yabi take sanye da hijabanta har k'asa sai dai duk ya b'aci da hawaye har da ba'kin kwalli.
Kishi sosai ya turnike Bulkachuwa.
Har ji ya yi zukar numfashi na neman yi masa turjiya.
Amma a hakan ya motsa k'wanjinsa ta hanyar cewa "Jabir na tabbatar babu jahilci a tare da kai tunda ka yi zurfi a ilimummuka daban daban. Sai dai abin mamaki sanin naka bai amfana maka komai ba, tunda zaka iya tsayawa da wacce kwanaki kadan ya rage a daura mata aure a cikin lungu inda babu sawu.
Ni ba zan yi maka rashin adalci na yi maka kazafi irin yadda ka yi mini ba.
Sai dai na sha fa'da kai din azzalumi ne, ba masoyi ba. Ta ya ya an baka aure ka karba, dan kwadayin albarkar iyaye ita kuma ka dinga hure mata kunne da ga yiwa nata tsohon biyayya? Ban da ita din sakara ce har wanne kalami ne a bakinka da zaka tsara mata da yafi na ubanta da kannensa tasiri?".
Jabir ya sandare ya zuba wa Bulkachuwa ido, yana jin wata irin fargaba from no where tana shigarsa.
Yayin da ni kuma na dago ido jage jage da hawaye na watsa masa kallon kiyayya da raini na ce "Ba ruwan ka da ni Tijjani! Na saurare shi din, domin shi nake so, nake fatan kasance wa da shi".
Ga mamakina sai kawai ya ja kakkuran tsaki tare da ce wa "Ai ke din shasha ce! Kuma kin ji na saka maganata da ke?
Da shi na ke wanda na gamsu da hankalinsa da iliminsa, kawai adalcinsa ne bai gamshe ni ba. Amma ke da baki da hankali ina ruwana da ke?
Jiyan nan na gan shi da matarsa a asibiti yana ri'ke da ita. Yana faman tattalinta. Wai matar da ya aure ta ba dan yana so ba yake yiwa irin wannan son da adalcin, amma ke kullum yana cikin dama miki lissafi. Da yake ya mayar da ke shargalle marar tunani."
Ai kuwa yana rufe baki kuka ya k'wace mini sosai.
Jabir ya kasa magana domin ya tabbatar Bulkachuwa ya gansu a asibiti ba k'arya ya yi masa ba.
Bulkachuwa ya sake yin k'uta tare da nuna Jabir da yatsa ya ce "Neman aure cikin aure haram ne in ji ma'aiki (S.A.W).
Da ku'din aurena akan ta, ko ba zaka yi mini kawaici irin na zumunci ba, to ka yiwa ka'idojin shari'a biyayya. Ka fita mini a harkar Asiya! Ubangiji ya baka Maijidda wacce ita ce mafi alheri a gare ka. Amma bar mini Asiya Toro domin ina da yakinin akwai babban al'amari a tsakanina da ita. Daga ranar da aka tabbatar mini an ba ni ita, na fara addu'ar na yi nisan kwana mai yawa dan na tabbatar ni kad'ai na mallake ta".
Still Jabir ya kasa magana domin gaba'daya almarin ba k'aramin bugunsa yake yi ba.
Kishin Bulkachuwa ya shak'e shi k'warai da gaske. Domin idan gaskiya zai fa'da ya ga son Yabi a idonsa irin wanda bai yi zaton Tijjani zai yi mata ba. Mussaman yadda bai dauki soyayya da muhimmanci ba. Mace tana bata masa rai zai juya mata baya duk yarda yake da ita kuwa.
Ina kuka, ina kallon Yaya J. Na sani dan na yi ba'kin ciki ya sanya Bulkachuwa sako maganar Maijidda. Ban da haka mene ne dan ya nuna kulawa akan matarsa ta aure?
Nan da nan zuciyata ta hassala cikin rawar murya na ce "Mene ne dan ya kula da lafiyar Iyalinsa? Tabbacin nima zai kula da ni ke nan tunda har ya yiwa wacce baya so adalci to ina kuma a ce ni ce da yake so? Kai sau nawa ana ganinka da tambadaddun matan banza?"
Take jikin Yaya J ya yi k'wari domin yasan yadda nake da kishi na gaske, maganar Bulkachuwa na iya tunzura ni na yi masa fishi. Dan haka ya dan murmusa. Sannan ya ce "Ko yanzu na mutu a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login