Showing 51001 words to 54000 words out of 214110 words

Chapter 18 - Bakar Ta'ada Complete hausa novel

24 Aug 2024

11086

mane min nata kuma ubansu ya ba shi Ubaida".
Ya sandare a zaune. Tunani iri iri suka dinga zarya a tsakanin zuciyarsa zuwa kwanyarsa.
Ya sani ko da wasa bai ta'ba furta yana son Yabi ba.
Amma me yasa duk mutanan kirki da suka zo neman aurenta ba'a basu ba, me yasa sai shi? Alhalin babu kyakkawar alaka a tsakaninsu bare kuma alaka ta soyayya.
A karan kansa ya fahimci so ake kawai a kassara rayuwarta saboda ana ganin mai tsiwa ce, kuma ubanta ba shi da yadda zai yi.
Karon farko da takaicin kansa ya kama shi.
Ya tabbatar an yi wannan ha'din ne dan ta tabbata a garari da wahalar rayuwa.
Wani irin bacin rai ya ziyar ce shi, wato ana masa kallon lallatacce marar amfani.
Ya mike ya kalle ta cikin ido ya ce "Amma kuwa Dada zan yi rikicin da kowa zai gane an taba ni. Ban ce ina son ta ba, ba'a taba ganin kankanuwar alamar ina sonta ba, bare k'atuwa. Akan me za'a hana ta wadanda suka bayyana da nufin soyayyarta sai kuma ace za'a yi mana dole gaba'daya?"
Ta sassauta ta ce "Mai sunan manya kada ka k'wari kanka. Yabi bata da makusa, irinsu ne matan da ko shekaru hamsin suka yi jikinsu baya nuna wa. Kalle ni mana yadda jikina ya boye shekaruna da suka tura ainun. Baya ga hakan kai ne muke da yakinin zaka tankwara ta ka yi maganin shak'iyancinta. Muna cike da tsoron kada ta je a sako mana ita bayan ta gama karya darajar gidan nan, kai kuwa ai zaka yi hakuri da ita, kamar yadda zata ha'diye dukkan dabi'unka marasa kyau".
Ya sake tunzura ya ce "To idan na kasa jurewar na sako ta fa?"
Cike da rashin damuwa ta ce "Ai dai ka yanke mata budirci, ba za'a yi ta mata kallon an aurar da sa'aninta har an zo kan kannenta ba".
Ya jijjiga kai ya ce "Zan je na samu wadanda suka kitsa wannan ha'din, basu isa ba, akan me zasu yi iko da ni irin haka alhalin basu dauki dawainyata ta zame musu dole kamar yadda ta y'ay'ansu ta zame musu ba?
Baban kasuwa bai aurar da Jabir ba, sai da ya bashi fili ya tallafa masa ya gina gida.
Amma D'an Baban Marina a gidan haya yake, sannan nima ba wanda ya mini irin wannan taimakon sai kawai ace za'a bani aure, abin ciwon ma ba da kyakkawar manufa aka shirya ba. Ita suna mata kallon tantiriya fitananniya, sai suka ga ba wanda ya dace da ita sai dan-iskan da yake tumbele a gari saboda ya rasa mafad'a idan yaso ni da ita mu tabbata a cikin bala'i.
Me yasa Baban kasuwa ba zai bani Kaltume ba?
Me yasa ya dauki Maijidda ya bawa Jabir?
Me yasa Baban Tsakiya ba zai bani Saratu na aura ba?
Me yasa autarki ta hana ni Nasiba, amma dukkanku kuka zuba ido alhalin kunsan ita take sona nake son ta?"
Jikin Dada ya mutu k'warai da gaske.
Ta kasa kalubalantarsa. Tsawon lokaci ya ce "Na sani matu'kar Allah za'a duba baki da bakin magana. Dada ki yi kokarin gyara wannan matsalolin da suka dabaibaye ahalinki tun kina da sauran dama.
Kuma komai za'a yi bazan auri Yabi ba. Ita din y'a ce ba baiwa ba. Tana da damar ta kawo duk wanda take so a aura mata, ban ta'ba ganin wadanda ake yiwa auren dole a gidan nan ba, sai yaran Baban Marina. Suma ba dai yaran dakin Mama ba. Sai na Gwaggo, sai kuma na Inna da za'a fara daga kan Ubaida. Ita kuwa auren Nura ai tsintar dami ta yi a kala".
Ya numfasa sosai
Ya kaurara murya ya ce "Dada na fa'da mikii ki dakatar da wannan ha'din. Matu'kar a gidan nan za'a bani aure bana so, ba zai yiwu a hana ni wadda take sona fiye da komai ba, a kuma dauki wadda bata saka ni cikin mutane masu daraja a bani ba.
Bani da sana'ar da zan ri'ke Asiya Toro. Tun tasowar ta masu wadata suke zuwa neman auren ta akan me za'a hana su a ba ni, me nake da shi da zan burge ta Dada?"
Cikin rarrashi ta ce "Ita rayuwar gaba'daya tana tafiya ne akan *Lak'ad anan, laja'a anan, lak'as anam*. Aci, a rufe tsaraici, a kuma yi alheri, arziki na Allah ne mai sunan manya".
Duk rud'anin da yake ciki sai da ya yi dariya ya ce "wannan karatun kuma yaushe kika yi sabuwar k'awa makauniya?"
Ta tunzura ta ce "shekarar da nake goyon uwa ka".
Ya juya ya fice yana fa'din kome zaki ce, ina kan batuna".
Kai tsaye dakinsa da yake zaure ya shiga. Ya jangwabu kan katifarsa. Ya shiga zurfaffen tunani, zuciyarsa ta dinga hakaito masa Yabi. Tabbas bata da makusa, mai kyau ce, amma shi kuma yafi son mace mai manyan halittu. Yafi son wacce take tsananin sonsa, yafi son wacce idan ya yi mata mazurai zata shiga taitayinta. Amma ya sani Yabi ba zata ji tsoronsa ba, tunda ita ma k'walluwar kanta ce kuma bata sonsa.
Ya lumshe ido yana ganin ta cikin k'ahon zuciyarsa, bai san ya aka yi ba wani irin tausayinta da soyayyarta suka shige shi da wani irin k'arfi tamkar wadda aka yi masa turensu a lokaci guda.
Ya juya yana jin wani irin al'amarin da bai ta'ba jinsa akan ko wacce mace ba.
Cikin jarumta yake koka wa da abin da yake ji din, yafi son ya danne shi ya hana shi tasiri, baya son a ha'da kai da shi ayi zalunci, zunubin kansa ma ya ishe shi ba sai ya ha'da da zaluntar wata halittar ba.
Amma da yake ikon sarrafa zuciyarsa ba a hannunsa take ba. Ubangiji ne mai juya al'amura yadda ya so, ko da kai baka so ba.
A wannan kwanciyar da ya yi wata irin soyayyar Yabi ta yi masa d'auri fiye da daurin huhun goro.
Jikinsa ya mutu murus. Ido na lumshe sai ji yake ina ma, ina ma?
Ya sake tuno dan tsut din bakinta da ya iya rashin kunya da zaro bak'ar magana.
Ya saki gauron numfashi ya ce "Anan zamu yi ta samun sa'bani da ita matu'kar k'addara ta tabbatar da al'amarinmu. Domin ita marar kunya ce, ni kuma mai son girma ne, mai kuma k'iyayyar rainin wayo ne."
Sai ya tsinci kansa da fa'din "Allah idan da gare ka ne, ka tabbatar da wannan ha'din, ka sanya alheri da albarka, ka bani k'arfin zuciya. Idan kuwa rud'ani ne na shaidan Ubangiji ka sassauta mini wannan soyayyar da ta shiga dukkan zuciyata da gangar jikina, Allah ka ha'da kowa da rabonsa na alheri".
Ya mik'e da k'yar. Ya fita waje tafiya yake yi amma shi da kansa bai san inda za shi ba.
Ya sha kwana ke nan suka yi kicibus da Baban Marina.
Bai san ya aka yi ba sai ya ji kunyarsa ta rufar masa. Sannan bai so ya gan shi cikin wadannan kayan da kuma yadda kansa yake kuma babu hula.
Karon farko da Bulkachuwa ya ji nauyin a gan shi cikin wannan yanayin, domin shi a ganinsa ba wai ya saba wa sharia ba ne al'adar bahaushe ya bata wa, to shi bafulatani ne ba shi ke nan ba?
Dada ce dama take yawan yi masa fa'dan ya gyara, ita kuwa kai tsaye yake fa'da mata bai saba wa ka'ida ba ta bar shi ya yi yadda yake so. Sai kuwa Baban Marina da shi ma yake yawan yi masa nasiha. A gabansa zai nuna zai gyara, sai dai ba dan zai gyara din ba.
Amma a yau sai ya ji tamkar ya ruga da gudu dan tsananin kunyar da ya tsinci kansa a ciki.
Da walwala sosai Baban Marina ya amsa gaisuwar da yake yi masa.
Ya zarce da fa'din "Dama ina neman ka, mu je, idan babu inda zaka je".
Da nauyi sosai ya ce "Dada ce ta aike ni, amma da zarar na dawo zan zo Baba".
Baban ya k'ada kai ya ce "To hanzarta ka tafi, ka bari sai na dawo bayan isha sai ka zo".
"To Baba"
Bulkachuwa ya amsa da ladabi fiye da na kullum.
Ya tafi yana ayyana ashe surukuta gaskiya ce?
A da beken abokansa yake gani idan suna sun sun da kai idan sun ga iyayen matansu mussaman abokinsa Salisu yayansu Yabi.
Har da kansa ya ji yana mamakin kansa me yasa baya jin kunyar iyayen yan matansa, me yasa baya jin kunyar Baba Maryo uwar Nasiba?
Zuciyarsa ta harba domin ya gasgata su din ba sonsu yake yi ba sha'awa ce tunda ya sani shi din yana cikin jerin mazan da suke tsananin son kasance wa da mace.
Amma a yanzu ya fahimci son Yabi yake da dukkan na'kasunta domin shi yafi son cikakkun mata ba kwailaye ba, bugu da kari bai son mai tsiwa sannan kuma bai son auren zumunci.
Amma a yadda yake jin Yabi tana bin ilaihirin jikinsa da zuciyarsa tana sake yin kane kane a cikin ko wanne dakika ba zai iya tankwabar da al'amarinta ba. Duk da bata zo a yadda yake son ace ta zo masa ba.
Yana tafe yana murmushi a dalilin har ya fara hango ta dauke da cikinsa.
*
Har na iso gida ina tufka da warwara, ina ta tunanin inda zan tafi.
Gaba'daya tunanina ya tsaya a waje guda domin na fi gamsuwa na je wajen Baba ta Bulkachuwa.
Ana magariba na iso gida.
Da daddare duk ana zaune akan katuwar tabarma a dalilin d'an zafin da ake yi.
Baba ya gama cin tuwo yana jin radio.
Ni kad'ai ce a daki. Amma ina jin duk abin da suke yi. Kwatsam sai jin muryar Bulkachuwa aka yi yana kwada sallama. Bansan dalili ba, zuciyata ta harba da tsananin gaske.
Da sakakkiyar murya Baba da su Gwaggo suka amshe shi.
Ya gaishe su cikin nutsuwa ina hango shi sai da ya zauna sannan ya gaishesu sabanin da da yake gaida matan a tsaye kerere, kai duk gidan ma Baban Marina kawai yake dukawa har kasa, amma ko su Baban Tsakiya dan risinar da kai yake yi ka'dan.
Amma a yau hatta Inna ma sai da ya duka mata bare kuma ace Gwaggo ce da kanta.
Wani irin takaici ya shake ni wato dai a wannan duniyar samun mai kaifi daya ma'ana mai magana daya sai an tona sosai.
Daga dan ambata ha'di a tsakaninmu shine ya tattaro siffar mutanen kirki ya yaba a jikinsa?
Tamkar dai ba shine ya gama fa'din zai tsaya mini na auri wanda nake so tamkar ko wacce y'a ba?.
Na sake kad'uwa a dalilin kayan da suke jikinsa.
Wata farar shadda ce tar a wanke a goge. Ni da kaina duk adawar da nake da shi na sani shi din mai kyau ne, sannan halittarsa a cike take ga shi ingarma ne.
Ba k'aramin karbarsa shaddar nan ta yi ba. Ga kamala ya shinfida a dukkan jikinsa.
Matan gidan suka tashi suka basu guri.
Gwaggo bata shigo daki ba, sai ta nufi baya inda take tatar koko, ta kira Iklima tana taya ta.
Na sake kasa kunne na ji dalilin zuwan nasa da kuma wannan sauyin da ya yi farat daya.
Cikin nutsuwa Baban Marina ya ce "Na kira ka ne dan na fa'da maka jiya su Alhaji Shehu sun zo nema maka auren Yabi.
Na kuma basu babu jayayya, har na ji ban ji da'din yadda aka taso su suka zo cikin gidan nan wai nema maka aure ba".
Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*.
*08032773332*

Zuciyata ta sake tsinke wa, hawaye ya b'alle mini. Shi ke nan dai da gaske wancan kazamin halittar ne mijina".
Kuka ya nemi subuce mini da karfi.
Na yi maza na danne bakin da filo.
Ina cikin kukan sai jin Bulkachuwa cikin rawar murya da alamu suka nuna gaf yake da rushe wa da kuka.
Yana fa'din "Madallah da kai Baba! Kafin wannan lokacin ban ta'ba sanin ina da gata har hakan a wajen ka ba. Ban yi zaton zaka iya mini irin wannan sadaukarwar ba.
Ban san ce wa zaka iya rintse ido daga dukkan nakasuna ba sai yanzu.
Hakika na sani dole aka yi maka akan ka ba ni aure, na kuma yi imani zaka iya bacni aure ko da ba'a yi maka tilas ba.
Ina da yakinin idan ba wanda ya riga ni son Ubaida da zaka bani babu haufi. Ni da kaina da aka zabe ni aka ce a bani ita, na kad'u matu'ka da aniya Baba.
Da dukkan zuciyata na karbi auren nan, ban karba akan dole ba sai dan ina so.
Al'kawarin da zan yi maka daya ne, zan ri'ke ta irin rikon da uba zai yiwa y'arsa, zan kuma ri'ke ta irin rikon da miji nagari zai rike matarsa.
Zan sassauta mata, zan yi dukkan iyawata na hana ta zubar da hawaye a dalilin ba'kin cikina.
Ina maka al'kawarin komin nisan zamani sai Yabi ta ce Madallah da aurena In sha Allah".
Ban san ya aka yi ba, na fita a guje na tsaya kusa da shi, cikin kuka sosai na ce "Har abada ba zan yi alfahari da auren ka ba Tijjani! Cuta dai an gama cuta ta, da ikon Allah kuma duk mugayen da suka kitsa wannan ha'din sai sun ga tozarcin duniya."
Ashe har Baba ya tashi ya samo tsabga ban ankara ba.
Sai kawai ji na yi ya wancakalar da ni, na zube k'asa, sannan ya saka k'afa ya take ni sosai, ya shiga shaud'a mini tsabgar nan babu tausayi.
Na kuwa dage dukkan murya ina canyara ihu, tare da shure shuren neman tsira.
Bulkachuwa sai fa'di yake "Bar ta Baba! Yarinya ce. Yi hakuri, yi mini hukuncin a madadin ta.
Yayin da Mama da Inna suka tsaya cirko cirko, suna fa'din Alhaji yi hakuri mana, yi hakuri, Gwaggo kuwa ko kusa da wajen bata zo ba.
Ganin ba zai bar ni ba.
Ya sanya Bulkachuwa yin rumfa a kaina Baban Marina kuwa ya shiga labta masa babu sassauci.
Amma abin mamaki ko gezau bai yi ba.
Illah fa'di yake "Ka yafe mana, ka huce, ka gafarcemu Baba".
Duk yadda ya yi mini rumfa dan ya hana dukan Baba samu na, ban ji kamshi a tare da shi ba. Haka nan kuma ban ji yana hamami ba.
Sabanin Yaya J idan yana waje sai an gane saboda yadda kamshi ya kama komai nasa.
Sai da ya mana lilis sannan ya yar da bulalar yana cewa "Gobe idan ina magana da na gaba da ke ki zo ki saka mini baki.
Idan kuma an yi auren ki ha'diye zuciya ki mutu, ai kin sani sarai ina da irin ki, sama da bakwai. To mene ne zai dame ni, akan idona kike zagin y'anuwana da fatan tsiya a garesu?
Ki bi a sannu Yabi.
To ina cikin wad'anda suka kitsa maganar sai ki hada har da ni a muguwar addu'ar ta ki!
Sannan ki sani daga ranar da aka daura miki aure da Tijjani yafi kowa hakki akan ki har ni Uban ki.
Idan kin kwantar da hankalinki kin zauna lafiya, kin taimake shi, kin rufa masa asiri, kema da ikon Ubangiji Allah zai miki fiye da hakan.
Idan kuma kin tasa shi gaba da bala'i da cin mutunci da tashin hankali ke ma ba zaki samu kwanciyar hankali ba In sha Allahu"
Na sake rushe wa da kuka mai tsananin gaske.
A ki'dime Bulkachuwa ya yi maza ya rufe mini baki da hannunsa yana fa'din "Yi shiru Yabi kin ga Baban Marina baya son kuka irin wannan, kada ya sake cuda miki jiki".
Gaba'daya jikin kowa ya mutu ana tu'ajjibin irin soyayyata da aka ga ni a dukkan jikinsa da ayyukansa.
Gwaggo ta shige daki, yayin da Inna take fa'din "ki yi ha'kuri komai zai wuce kamar ba'a yi ba.
Mama kuwa ta wuce tana fa'din "Ikon Ubangiji! Wata'kila yanayin Tijjani ne ya sanyaya mata jiki.
Baban Marina kuwa ya ce ",Tashi ka tafi na sallame ka da alamun ka sullutun namiji ne kai".
Bai ce komai ba ya risina yana "Fa'din na gode sosai Baba Allah ya saka da alheri, ya shirya maka zuri'a. Allah ya hana ni kunyata a idon ka".
Baba bai amsa ba shi kuma ya tafi da sauri.
Bayan fitarsa Baba ya dinga yi mini fa'da tamkar harshensa zai tsinke.
Hakan ya sake rura wutar k'iyayyar Bulkachuwa a raina, domin a kansa mahaifina ya ta'ba duka na.
Na kwana ina juyi ina hawaye, yayin da Gwaggo ta kwana akan sallayarta, da ta fara gyangyadi zata zabura ta sake doro alwallah.
Na sani kuma ni take faman yiwa addu'ar zabin alheri.
Duk da ina cikin yanayin kunci, sai da kawata Rukayya ta fado mini da uwarsu ta rasu bara.
Ko waye zai musu addu'a irin wadda Gwaggo take yi mana?
Hawaye ya balle mini na tausayin Gwaggo da kuma duk wata macen da bata da uwa.
Hakika y'a mace bata ta'ba fita daga marairaicin rashin uwa duk girmanta kuwa.
Cikin Sa'a na doro alwallah na yi shimfida a gefenta, ba abin da nake roka irin Ubangiji ya yiwa Gwaggo alheri mai yawa a rayuwarta.
A fili nake fadin "Allah ka amsa addu'ar Gwaggo! Allah ka yarda da ita, ka bata aljannah.
Haka nake ta nanata wa, sai kuma na ce Allah ka jibanci al'amarin marayu, Ubangiji al'kawarinka baya tashi, Allah ka sanya farin-ciki a zuciyar duk wanda ya rasa uwa".
A karshe na ce "Allah ka yiwa Yabi zabin alheri".
Sai kuma na fashe da kuka sosai.
Kamar ba zata tanka mini ba, sai kuma ta ce "Ai kin gama magana, share hawayen ki tunda kin bar wa Allah ya yi miki za'bi.
Na ha'diye kukan amma nauyin kirjina bai sassauta mini ba.
Da safe na tashi da kuka. Baban Marina ko ta kaina bai bi ba, da k'yar ma ya amsa gaisuwar da na yi masa.
Hankalina ya sake tashi na dinga tsine wa Bulkachuwa domin dai a dalilinsa ubana ya yi fishi da ni irin wanda bai ta'ba yi mini ba.
Wato ko auren ma aka yi hakan zai dinga zuwa yana bata ni a wajensa?
Na diga kuka irin na sharbe.
Ai kuwa na shammace mutan gidan bayan Baba ya fita, nima na fice da ledar kayana da na zuba tun jiya.
Kai tsaye na yi bakin titi na shiga motar da zan sauka a Bulkachuwa.
Na isa da azahar.
Baba ta dinga marabta ta, cikin wata irin soyayya da farin ciki mai yawa.
Gaba'daya kaina ya kulle

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login