Showing 72001 words to 75000 words out of 214110 words

Chapter 25 - Bakar Ta'ada Complete hausa novel

24 Aug 2024

11089

ta share.
Kamar ba zata tanka ba sai kuma ta zabura ta ce "Mandiya hamshakiya! Wai ke tabbataciyar marar kunya, kuma marar kirki. Idon ki babu kunya ko ka'dan, har ke ce zaki tafi wajen Hauwa ki fa'da mata ba kya son auren mai sunan manya?
Da me kika fi shi?
Sanin kan ki ne ban da ya mayar da kansa abin da ya zama ba, da ke baki isa ko kallon ki ya yi da sunan soyayya ba."
Na zum'bura baki ainun na ce "To kawai a bar shi ya auri wacce take son sa ta kuma dace da shi din.
Ni ma a bar ni da masoyana".
Ta kawo mini duka da mafici, ban goce ba, domin na riga na kai makurar fusata da al'amarinta.
Ba dan idon Babah da take zaune ba, da na zage na fa'dawa Dada gaskiyar magana. Amma ido mashi ne, mussaman da yake muna cikin zamanin da inka cika fa'din gaskiya sai ya zama rashin kunya a idon manya.
Mun jima a wajen Dada sannan muka isa k'ofarmu.
Muka tarar da Baban Marina yana gida ya dawo cin abinci.
Da walwala ya marabci k'anwarsa yana fa'din "Lale da mutanan Bulkachuwa". Ta zauna kusa da shi cikin nutsuwa da murmushi sosai.
Ta gaishe shi a ladabce.
Ya amsa mata da sakakkiyar fuska.
Ina gefe a takure tamkar mujiya cikin tsuntsaye.
Na gaishe shi kaina a kasa.
Ya share tamkar yadda Dada ta yi mini.
Na sake yi a karo na biyu.
Ya sake dauke kai tare da daure fuska.
Nan da nan na fara kuka sosai, ina ba shi ha'kuri.
A dan tsorace Babah ta ce "Ka yi ha'kuri! Da kanta ta ce na rakota ta baka ha'kurin fitar da ta yi baka sani ba."
Ya girgiza kai ya ce "To mai gaisuwarta zata yi mini?
Me zata fa'da mini?
Na zuba mata ido ta yi duk abin da ta ga dama tunda ni ban isa da ita ba.
Sannan ni ba tafiyar da ta yi ba ne ya bak'anta raina ba, wajen ki da ta dosa ne ya b'ata mini. Akan me zata je wajen dangina tunda ni din da zata ci arzikina a wajen ki, ta nuna mini iyaka ta?
Ban da hauka da kuma idonta babu ruwa a ciki ta ya ya zata doshe ki?
A sanyaye Babah ta ce "Yaya dan Asiya ta zo waje na sai ya zama aibu?
Akan wannan yaron ne kake ganin rashin kunya ne ta zo waje na?
Ni bana raba tsakanin yarana da naka.
Sannan na gode mata ta zo wajevna, da wani wajen ta yi fa?"
Ya murmusa ya ce "Da kuwa da kanta za ta dawo domin ai duniya ta ishi kowa darasi, a lokacin da za ta dawo daga gudun ni kuma a lokacin zan guje ta da ni da dukkan ahalina".
Kukana ya tsananta domin a lafuzzan Babanmu na fahimci girman bacin ran da na sanya shi.
Ina kuka, ina bavshi hakuri tare da ce wa "Na yi kuskure Babanmu".
Ya yi shiru bai ce k'ala ba.
Babah ta ce "Ka huce! Ka yi mata afuwa dan girman Allah. Ta ci arzikin rakota da na yi."
Ya saki gauron numfashi ya ce "Na yi mata afuwa, amma bazan huce da ita ba, sai an yi auren ta kwantar da hankalinta, ta kwantar da hankalin mijinta. Yardata tana d'amfare da yardar mijinta akan sha'aninta.
Ban da ke Hauwa, da ko kallonta ba zan yi ba. Domin ai ga Ubaida nan k'anwarta ce ta sosai, bata son auren da zan yi mata amma ta ha'diye komai. Amma ita Yabi da yake ta isa, kuma uwarta bata k'wabarta ai kin ga d'anyen hukuncin da ta dauka na guduwa ta kai k'arata. Ban da k'arfin addu'ar da kullum nake yiwa iyalinmu ai da duniya ta yi niyyar shiga".
Babah ta dinga fa'din "Da Ikon Ubangiji ba zamu ga haka akan ahalinmu ba! A yi ha'kuri Allah ya shirya mana su.
Ta dinga godiya da addu'a, akan alheri mai yawa ya biyo bayan auren.
Sai kuma ta fashe da kuka wanda ni dai bansan na menene ba.
Na dai ji Baban Marina yana ce wa "Yo Hauwa ban da dai muna cikin wani irin zamani da dan-uwanka yake zama tamkar makiyinka menene abin godiya? Komai zan yi miki ai kaina na yiwa. Tijjani d'a ne ko yafi hakan lalacebwa idan duniya da adalci bai kamata mu din mu hana shi aure ba.
Tunda mune muke zuwa nemo masa auren y'ar wasu. Kebnan idan da adalci sai mu ba shi tamu.
Fatana dai ki tsananta yi masa addu'ar shiriya, bakinki yafi na kowa tasiri a kansa."
Tana goge hawayen idonta tana fa'din "Ina yi Yaya, zan cigaba da yi. Allah ya shirye shi, ya sanya wannan auren ya zame masa sanadin shiriya da albarka a rayuwarsa gaba'daya.
Yabi kuma Allah ya bata hakuri da juriya."
Ya kalle ni ya ce "Tashi ki bamu waje. Na mike sum sum Babu nauyi. Domin hakan da Babanmu ya yi mini ya tabbatar bai huce da ni ba.
Ina shiga d'akin Gwaggo na tarar da ita tamkar wacce take fama da tsi da ha. Gaba'daya ta rafke, gata fara ce amma ta yi wani irin baki sosai.
Na zauna na gaishe ta ta amsa ba tare da ta kalle ni ba.
Nan da nan kukan da nake yi ya dawo sabo.
A fusace ta ce "ki rufe mini baki tun baki tunzira ni, na yi miki mummuna baki ba. Ai hakan kike so
Shike nan ni kuma duk sadda aurenku ya zo a lokacin watan bakin-cikina ya kama.
Kin ji da'di da ubanku ya jingina guduwar ki da ce wa ni na saki.
Allah shine shaidata, ban isa da ke ba ne, domin da na isa ko k'ofar gida zaki je sai kin fa'da mini.
Amma saboda ki jefa ni cikin kunya da ba'kin ciki shine kika gudu! Har kin yi girman da zaki gudu ki bar iyayen ki saboda sun miki laifi?
Ta share hawaye ta ce "
Da nasan hakan zaki yi mini Wallahi da ban kawo haka a cikin gidanku ba. Da na dauke Ikilima tun shekarun baya na yi tafiyata na bar wannan k'addararren zaman".
Na dinga kuka ina bata hakuri, domin fishinta da kukanta yafi d'aga mini hankali fiye da fishin Babanmu.
Murya na rawa take fa'din "da yake ita Innarku ta iya haihuwa, ai ga shi nan Ubaida bata kunyata ta ba, bata janyo mata ba'kin jini a wajen Babanku ba".
Tsigar jikina ta tashi sosai. Na dinga ganin wautata.
Da muryar kuka na ce "Dan Allah ki yi ha'kuri Gwaggo! Kaina ne ya kulle ainun. Na shiga rud'u mai girma. Amma da ikon Ubangiji komai zai daidaita, zan iyakacin bakin kokarina na ga ban sake janyo miki bacin rai ba. Ki sake ninka addu'ar da kike yi mini. Kullum ina sake jin tsana da k'yamar Tijjani a zuciyata".
Kuka na sosai ya k'wace mini.
A wannan karon sai ta kasa ce wa komai illa ido da ta zuba mini sosai.
Wata'kila rauni ne irin na uwa, wata'kila kuma tausayi na bata sosai.
Ta aro jarumta ta ce "Sau tari alheri yana zuwa mana ta inda bama so. Sai ka k'i abu tare da hasashen bai cancanta ba, sai kuma ya zame maka alheri. Sai ka so abu tare da hasashen za'a dace sai kuma ya zame maka fitina.
Ina fatan komai zai dunfaromu Ubangiji ya juyar da shi zuwa alheri.
Tashi ki d'oro alwallah, ni na yi tun dazu".

*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
*Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*.
*08032773332*
[9/25, 9:06 PM] Hauwa Galadima: *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*

*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers*
*08089965176*
*07084653262*


*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*



Ina alwallah ina kuka. Ba abin da ya sake karya mini zuciya irin yadda na jiyo Baban Marina yana cewa Baba "Ni fa ki daina ro'ko na Hauwa! Tuni na yafe mata, amma walwalata ce ba zata ga ni ba, har sai ta kwantar da hankalinta an yi hidimar nan lafiya lafiya. Sannan kuma ta zauna lafiya da mijinta kamar yadda y'anuwanta suke zaune lafiya.
Ina ce Ummi gidan mai iyali aka kai ta? Ga kuma mijin ya d'orawa ransa masifar son abin duniya. Ba ya sauke hakkin da shari'a ta wajabta masa.
Duk k'uncin da take ciki yau shekaru kusan takwas da aurenta, bata ta'ba zuwa gabana da nufin wata matsala ko da zummar na taimake ta ba.
Na sani kuma tana bu'katar a taimake ta, amma da yake ta dauko ha'kurin uwarsu ta shanye komai tana zaune da y'ay'anta, sai kuma ta yi tabarar koyon sana'a cikin cire girman kai da buri.
Shiyasa ni kuma ban ta'ba yin sallah ban roka mata sassauci a wajen Ubangiji ba.
Duk kuma wanda Allah ya ba shi nisan kwana zai ga yadda Allah zai albarka ci zuri'arta. Allah sai ya yi mata tukuicin hakuri da biyayyar da ta yi da ikon Allah".
Da k'yar na tokara na tashi zuwa daki na tarar da Gwaggo tana share hawaye.
A sanyaye na ce "Gwaggo baki huce da ni ba ne?"
Ta girgiza kai sai kuma ta ce "Ina mamakin duk alherin da mace zata yiwa namiji na ha'kuri da juriya akan al'amarinsa ko na ahalinsa. Amma idan d'anta ya yi laifin da ita kanta bata sani ba sai ya shafeta.
Ko sai yaushe uwa zata kubuta daga irin wannan kalubalen a k'asar hausa?
Duk lalacewar uwa ba zata so d'anta ya zama marar tarbiya ba. Na sani akwai uwayen da basa son laifin ya'yansu, amma me yasa aka fi yiwa masu hakuri da kawaici raddi?
Yanzu duk laifinki a kaina ya k'are. Yana wahalar gaske Babanku ya yaba ha'kurin da nake yi a gabana sai dai a bayan idona. Shikenan ita mace ba za'a yabe ta a kurzanta ta ba?
Ba za'a yayata alherinta ba, amma kuskuren da ba ita ta yi shi ba ma sai an yi mata tuya a kai".
Ta fa'da hawaye na sake k'wace mata.
Na taya ta kukan da take yi domin na sani sanadin tafiyar da na yi ne.
Da rawar murya na ce "Ki k'ara hakuri Gwaggo! Idan kika yi sa'a Ubangiji ya yabi ha'kurinki shikenan kin gama dace wa."
Ta zuba mini ido sosai ta ce "Kema na hore ki, ki yi hakuri, ki yi juriya, ko bana raye shine tsanin da zaki ri'ke, ki tsallake dukkan k'alubale a wannan duniyar".
Jikina ya sake sanyi. Domin kalmar ko bata raye ta yi matu'kar dukana.
Na ha'diye kukan na tayar da sallah.
Sai dai hawaye bai yanke mini ba, na idar da sallar ina zaune ina lazimin Ya ladifu da fatan na samu sau'kin halin da nake ciki.
Washagari sassafe Babah ta koma Bulkachuwa.
Ala dole na ha'kura na zuba ido aka cigaba da shirin aure, wanda yake sake k'arantowa.
Duk da na ha'kura amma wata irin rama nake yi mai tayar da hakankalin masu kallona.
Na sake zama wata yar sumoli da ni.
Ba annuri a fuskata.
Na kasa yiwa jama'a kitso bare kuma lalle.
Idan ba k'ure wa ta yi ba yana wahalar gaske na yi magana. Na zama very silent.
Makarantar boko ma na daina zuwa duk da a shekarar k'arshe muke.
Kwatsam sai ga Yaya J ya dawo daga Bauchi.
Bai samu labarin aurena da Bulkachuwa ba sai a jiya.

A ki'dime ya iso gidan Marina. Ya gurfana gabana Dada yana fa'din "Dada wanne irin abu ne haka?
Ta ya ya za'a dauki Yabi a bawa Bulkachuwa! Saboda Allah Dada wannan daidai ne?
Me yasa aka hana shi Nasiba baki tsawatar ba?
Me yasa aka tirsasa ni na auri Maijidda?
Akan me ita kuma za'a yi mata hakan? Ciwon abin ba shi ya yana sonta ba.
Idan saboda kada na sameta ne kuka k'ulla wannan al'amarin, na sadaukar da soyayyar da nake yi mata, na janye, bazan sake furta sonta, ko a bani aurenta ba. Amma ki yiwa Àllah Dada kada ki kassara mata rayuwarta.
Waye bai san BAK'AK'EN TA'ADODIN da yake yi ba?
Ta ko ina basu dace da juna ba.
Yabi mai son sana'a ce, yayin da Tijjani bai damu da ya gina kansa ba, irin mazan da suke barwa mace hidimar da shari'a bata dora musu ba ne.
Tijjani manemin mata ne, yayin da Yabi ta kasance mai tsananin kishin gaske.
Tijjani fari ne, Yabi bak'i take so.
Tijjani mai zafi ne. Yabi mai tsiwa ce.
Ta ina zasu ji da'din zama?
Ta ina suka dace?"
Kafin Dada ta ce wani abu Bulkachuwa da yake tsaye a bakin k'ofar Dada ya ce "Bamu dace da juna ba Jabir. Sai dai ka sani Ubangiji ne yake jujjuya al'amura, yake kuma k'addara afkuwar komai ko da bamu tsara faruwarsa ba.
Maganganunka sun yi matu'kar ta'ba zuciyata. Tabbas gaskiya ka fa'da, duk da na ji na muzanta. Da a ce son Yabi bai yi mini kamun kazar kuku ba.
Dana tirje wa aurenta. Sai dai an jarrabe ni akan ta cikin kankanin lokaci."
Ya numfasa ya sake fa'din " Na gode da ka ankarar da ni, duk inda sana'ar da zan gina kaina take zan nemota zan kuma yi duk wahalar ta.
Laifin da ka jingina mini kuma na neman mata wannan kai da Allah! Domin baka ta'ba ganina na yi ba.
Allah ne shaidar na yi tuba, Allah ne shaidar tunda na yarda aka zartar da hukuncin da ya yi a kaina ban sake yi ba.
Amma kun rike abu kuna ta faman jifana da shi."

*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
Ya fa'da cikin wani irin yanayi na bacin rai mai tsananin gaske.
Dada ta zuba masa ido cikin son ta nazarce shi.
Ta k'asa ha'diye abin da ta fahimta akan sa cikin dak'ik'a.
Ta nisa ta ce "Mai sunan manya, shin ka fa'da komar Yabi ne har haka?"
Takaicin ta ya k'ume shi.
Bata ce da Jabir komai ba, da yake faman sakin maganganun da suke nufin tozarci a gare shi.
Amma tana neman shiriritar da maganar. Bai ce mata k'ala ba ya juya tamkar ya tafi, sai kuma ya toge a jikin bishiyar zogalen da take gefen dakunan ka'dan. Cikin bacin rai na sosai.
Yayin da jikin Jabir ya yi sanyi domin ya fahimci ba k'aramin son Yabi Tijjani ya afka ba. Sannan ya ji kunyar maganganun da ya ji yana yi a kansa.
Dada ta kalli Jabiru ta ce "gara ma da baka auri Yabi ba Jabir. Na fahimci irinsu ne matan jaraba. A kansu ba abin da namiji ba zai yi ba. Mafi yawa haka zaka gansu yan firit amma suna murza mazaje ingarmai. Yadda kake sanyi k'alau din nan ba zaka sarrafa ta ba. Ko mai sunan manyan da yake a tsaye, tun komai bai gitta a tsakaninsu ba, ga shi nan yanayinsa ya nuna ta riga da ta shiga ransa ta yi kane kane".
Cikin jin nauyin maganarta Jabir ya ce "wacce irin magana ce haka Dada da girman ki?"
Ta nisa ta ce "Gaskiya ne mana! Kawai murnar da nake yi masa d'aya ce. Ta iya sana'ar samun ku'di, dolenta ta fito da ku'di su ci abinci. Idan ku'din da suke saka ta yiwa iyayenta raini basa zama mata ai ta nutsu ta girmama manya".
Tana rufe baki Jabir ya ce "Haka su Baban suka fa'da miki shiyasa kika tirsasa aka yi wannan bahagon hadin?"
Ta yi dan tari kafin ta ce "Gaskiyarsu ne ai! Sannan shi mai sunan manya tunda ba shi da sana'a asirinsa zai rufu".
Jabir ya ce "Gaskiya kun kassara rayuwarta, amma akwai Allah. Ina fatan alheri ya biyo baya, sai dai har yau din nan ban hakura ba. Na sani *Hannu daya* baya daukar jinga. Bazan ha'kura da ita ba har sai na ga ranar da aka shafa fatiharta da wanina. Daga ranar na zubar da makaman nemanta. Amma matu'kar ban mutu ba idan an kaddara mini cikar burina zai zama gaskiya. Idan da rabona zata dawo mini, ni kuwa zan aureta komin tsufanta, domin ita nake so ba wani abu a tare da ita ba".
Dada ta kyabe baki ta ce "Idan k'asa ta rufe mini ido komai ma sai ku yi tunda ban ga ni ba".
Tijjani da yake jinsu zuciyarsa ta dinga bugawa da k'arfin da ya zarce ka'ida.

Yana son ya je ya fa'da wa Dada duk lalacewarsa bata kai mace ta ciyar da shi ba, bai yi mutuwar zuciyar da macen aurensa zata dauki nauyin kanta da nasa ba. Sannan ta fahimtar da y'ay'anta hakan.
Amma sai ya daure ya ha'diye. Ya ja jikinsa ya fa'da dakinsa ya fa'da kan katifarsa.
Wani irin yanayi na shigar sa na tsananin bacin rai da ya sababa masa k'arfin zuciya.
Domin gaba'daya ji ya yi hatta dako na daukar buhun gero da na su wake zai iya yi, dan ya ciyar da Yabi da guminsa ba wai ta ciyar da su ba.
Idonsa ya ciko da hawayen tausayinta domin ya gane k'iyayyar da ake yi mata ne ya sanya aka bashi aurenta.
Ya yi shiru yana nazari wato saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login