Showing 78001 words to 81000 words out of 214110 words

Chapter 27 - Bakar Ta'ada Complete hausa novel

24 Aug 2024

11108

wannan tagomashin".
Fuskarsa ta yamutse kadan. Ya ce "To na biyayya fa?"
Nan da nan idona ya ciko da hawayen takaici. Na yi k'asa da kaina na kasa ce wa komai.
Murya babu amo ya ce "Abokina da muka yi karatu a Gad'au gobe zai zo.
Ya dame ni akan na ba shi lambar amarya ko na kawarta dan ya ji irin yadda ake sallamar amarya da kwayenta a nan, da kuma abubuwan da kike bu'kata".
Na ja tsaki tare da ce wa "Komai zai fito ta hannun ka ko ta sanadin ka bana sonsa ba kuma zan kalle shi ba."
Ya zuba mini ido sosai cikin damuwa mai yawa.
Cikin wani irin yanayi ya ce "Asiya Toro alfarma d'aya nake so ki mini, ko da kuwa ita ka'dai ce alherin da zaki yi mini. Ki taimake ni kada ki tsinka ni, ki yi mini wannan arzikin dan Allah".
Ban san ya aka yi ba, jikina ya yi sanyi, mussaman yadda na ga ya yi kalar tausayi tamkar ba Bulkachuwa ba.
Na yi shiru amma fuskata a cukune sosai.
Ya sake ce wa "ki bani lambar wacce zai yi magana da ita Asiya. Sannan idan sun zo mini ranar daurin aure kada ki wula'kanta ni a gabansu. Na yarda bayan sun tafi ko menene ki yi mini, zan jure".
Na sake gallah masa harara tamkar idona zasu fa'do k'asa. Tare da ce wa ban iya Yaudara ba, ba kuma zan fara yanzu ba. Ai na sha jin kana fa'dawa abokan naka ba macen da zaka aureta alhalin kasan bata sonka. Ba ayi macen da zata ce baka yi mata ba, sannan ka nace sai ka aure ta, duk wanda ya sanka yasan wannan alwashin na ka. To me yasa yanzu ka yarda zaka aure ni alhalin kasan bana son ka, bana farin-ciki da al'amarinka gaba'daya?"
Kuka ya k'wace mini sosai.
Murya babu amo ya ce"Kaddara ta ce a hakan Asiya! Ni kaina na kasa gane kaina.
Wata'kila cika bakin da na yi ta yi ne, ya sanya aka jarrabe ni da son auren wacce ta washe ni, wata'kila kuma Ubangiji ne zai mini wani alherin ta sanadin ki shiyasa ya jingina mini sonki mai yawa."
Na sake jan tsaki na ce "Ba wani alheri domin da zan ga sadda zai tunkare ka zan karkatar da shi na bawa wanda suka fika mutunci da so na".
Ya girgiza kai ya kasa magana domin ransa ya baci idanuwansa har canja wa suka yi.
Tsawon sakwanni bai iya ce wa uffan ba.
Ni kuma sai fama nake da kuncin zuciya. Sannan sai yanayinsa ya sanya na ji babu da'di, domin duk yadda na tsane shi. Sai na ji ya d'an ba ni tausayi ka'dan.
Muna haka Baban Marina ya dawo, ya zo wuce wa ta babban zaure ya hango mu a zauren Dada.
Ina kallon yadda yake murmushi yana amsa gaisuwar Bulkachuwa da walwala.
Ni kaina a wannan lokacin ya sace da fishin da yake yi mini. Domin da murmushi a fuskarsa ya amsa barka da zuwan da na yi masa.
Har yana fa'din "Sannunku Yabi"
Kunya ta saka na yi nufin shige wa wajen Dada. Sai ce wa ya yi "Dawo ku cigaba da tattaunawarku. Allah ya yi muku albarka. Allah ya sa ku zamo abin alfahari, Allah ya shiga al'amarinku".
A hankali Tijjani yake amsa wa yayin da ni kuma ban amsa ba ko da a zuci ne.
Yana shige wa ya kalle ni a sanyaye ya ce "Asiya Toro Baban Marina bai dauki auren nan namu da wasa ba fa. Mu ha'da kanmu, kada mu ba shi kunya dan Allah".
Na ja tsaki tare da ce wa "Ni Malam na gaji tafiya zan yi".
A sanyaye ya mik'o mini wayarsa ya ce "Saka mini lambar"
A tunzure na ce "Ba ni da k'awa".
Da sigar lallashi ya ce "Yanzu duk ro'kon da na yi miki?
Farin cikin da Baban Marina ya yi a dalilin ganinmu bai sa zuciyarki ta rusuna ba?"
Na murguda baki na ce "To ai dai kasan ba ni da k'awaye, Adda Nazira ce kuma ta yi aure, sai kuwa Nasiba ita ma kuma ai auren ta za'a yi ko?"
Ya girgiza kai ya ce "Hakane! To Ina wannan fara mai dan jikin nan da yanzu kuke dawowa daga boko tare? Sannan tare nake ganinku a wajen koyon kwalliya".
Na zuba masa harara na ce "Tsabar sawa mata ido har ka gane halittar ta?
Har abada ba zaka burge ni ba Tijjani. Ba kuma zan baka lambar ba, domin dai da bakin ka ka tabbatar mini nema cikin nema haramun ne. Bari na shaida maka tuni an kai ku'din aurenta. Dan nasan kana iya lallabawa wajen ta".
Ya yi sororo sai kuma b'acin ran fuskarsa ya ragu.
Ya ce "Bana ma son lambar, na fasa, zan ba shi lambarki sai ki fa'da masa ta yadda zai turo miki ku'din kunshi da na kitso, ya damu akan a sallame ki ke da kawayen ki ne".
Na yi shiru ban ce komai ba.
A hankali ya ce "ya yi miki hakan?"
Na sake yi masa banza.
Ya sassauta ya ce "please mana Asiya Toro".
Na harzuka na ce "Gaskiyar magana baka yi mini adalci, idan ina kaunar yadda kake gatsa sunana ha'de da na garina Allah ya tsine mini!.
Ya dan murmusa ya ce "Da sannnu idan kin kwantar da hankalinki zan daina fa'da, na samo miki sunaye masu da'di da tsuma zuciya".
Ba'kin ciki ya sake turknike ni. Na ce zuciyar waye din zata tsumu?"
Ya make kafa'da ya ce ta "Asiya Toro".
Na yi kwafa na ce "Ai na gane zuciyarka babu alheri ne shi yasa kake k'yashin ce mini Yabi. Da'din abin ma dubun ka suna fa'da mini cikin girma da arziki".
Ya ce"Nan da lokaci ka'dan komai zai zama tarihi. Kin ga dai na nemi arzikin ki, ban kuma mayar miki da martanin bakaken maganganun da kika yi ta yab'a mini ba. Ina sake ro'kon ki idan abokina ya kira ki, ki taimake ni kada ki bayar da ni."
Ban amsa ba. Ya sake cewa dan Allah Asiya Toro".
Cikin fishi na ce "Na ji".
Da'di ya kama shi ya dinga fa'din "Na gode sosai. Ina fatan na ga ranar da zaki fahimci irin tarin alkhairorin da suke zuciyata mussaman akan lamarin ki".
A hanzarce na ce "Ai kuwa dai ba zaka ga ranar ba".
Ya girgiza kai tare da ce wa "Babu damuwa time will tell".
Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ina son na tambaye ki, zaki iya zama a wanccan daya bangaren na Dada?"
Maimakon na yi masa magana da baki, ai sai kawai na d'ora hannu aka na fashe da wani irin kuka na tashin hankali.
Murya na rawa na ce "wato dai a cikin masifar gidan nan zan tabbata? Idan kuwa har a cikin gidan nan ake nufin na zauna da sunan zaman aure Allah ya dauki raina kafin hakan ya tabbata. Na shiga uku ni Yabi".
Ya rikice ya hau fa'din yi shirun ki dama na fa'da mata wajen ya miki local da yawa, sannan baki samu sauyin muhalli ba. Yau din nan duk inda gida yake zan nemo kafin dare. Da ku'di a hannuna.
Yi hakuri ki daina irin wannan kukan. Kin ga yadda kika koma kuwa Asiya?"
Da k'yar ya lallaba ni, na yi shiru.
Ya zura hannunsa a aljihu ya ciro cakulet manya masu da'di da tsada k'waya biyu ya mik'o mini.
Bansan ya aka yi ba na fashe da dariya ga kuma hawayen ba'kin ciki na ziraro mini.
Da yake d'an duniya ne sai kawai shima ya fashe da dariyar yana cewa "Ni nasan Ubangiji zai cusa miki soyayyata dan yasan yadda ya gina ki a tawa zuciyar. "
Da k'yar na samu dariyar ta tsaya.
Da hawaye a idona na ce "me zan yi da wannan abar?"
Ya zuba mini ido yana wani lumshe su ya ce "Wai fa dan kada na zo hannu na dukan cinya ya sanya na taho miki da su"
Na rasa me zance masa tsabar takaicinsa da ya d'ada makure ni.
Na ce "To ajiye idan ka ga Yarinya k'arama ka bata amma ba ni ba".
Ya waske ya ce "Asiya Toro maraina ka'dan fa barawo ne. Kowa ba iya karfinsa zai yi kyauta ba?
Kin san wahalar da na sha kafin na samo miki wannan cakulet din a garin nan? Saboda nasan kina son ta ne. Amma ban burge ki ba? Idan kin yi hakuri wataran katon zan siyo na ajiye miki."
Da sauri na ce "da dai ace ba hannun jinjirai ne da kai ba tsabar rowa."
Ya nuna kansa da yatsansa ya ce "Ni ne mai hannun jarirai? Lallai kuwa zan baki mamaki Asiya Toro local government. Bauchi state of Nigeria".
Ko kula shi ban yi ba na wuce shi na tafi na bar shi a tsaye. Tsabar takaicinsa da ya sake kular da ni.
Ya d'aga murya ya ce "Sai gobe zan dawo, ko da anjima ma na dawo?"
Da kansa ya bawa kansa amsa da ce wa "To zan dawo da daddaren ran ki ya da'de."
Har na isa k'ofarmu mamakin Bulkachuwa kawai nake yi. Ban da dai ya riga ya same ni a araha ya rasa me zai kawo mini sai cakulet k'waya biyu. Shi ko kunya bai ji ba? Amma da na tuna halin rowarsa sai kawai na janye mamakinsa. Na shiga tambayar kaina wanne irin zama zamu yi ne da shi?
Na tabbatar sassaucin da ya yi dan baya son na yarfa shi ne.
Amma da tuni ya baje mini kalolin rashin mutuncinsa.
Na zauna na fara kokarin cigaba da k'ullin sigan.
Zuciyata ta shiga hakaito mini kayan jikinsa.
Shadda ce a jikin sa kalar ganye wato kore sosai. Ya d'ora hular sanyi mai tambarin kungiyar Manchester United. Na sani kuma d'an ya boye wa Baba curarriyar sumarsa ne tunda zafi ake yi ba sanyi ba.
Daga ni tun farar safiya ya sanya kayan a hakan kuma shi ya k'ure malejin kwalliya ne.
Na ja tsaki tare da ce wa "Idona ya saba ganin samari ma'abota wanka da gayu. Irinsu Yaya J da Nuru Tanim. Ta ya ya Bulkachuwa zai burge ni?."
Gwaggo ta shigo ta ce "me ya faru da kika je?"
Na yi kasa da kai na ce "Ba Dada ba ce ashe".
Ta ce "To waye?"
Na bata rai duk da kan nawa yana kasa na ce "Tijjani ne".
Daga hakan bata kara ce wa komai ba ta dauki abin da zata dauka ta fice tsakar gida.
Washa gari da azahar ina kwance a tsakar daki sai ga Nazira ta zo. Karon farko da ta zo gida tunda aka yi mata aure. Duk rud'anin da nake ciki sai da na tashi da azama na rungume ta.
Muka haye k'aramin gadon Gwaggo da muke kwana a kansa ni da ita tun fil'azal.
Da murmushi a fukskata na ce "Yau Adda Nazira ce a gidanmu?"
Ta d'aka mini duka tare da cewa"oh har kin cire ni a cikinsa, to kema kwana nawa ya rage miki mu yi kunnen doki?"
Na bata fuska sosai. Ta ce "daga wajen Dada nake suna can, suna artabu da Yaya Bulkachuwa akan inda zaku zauna.
Wai akan me zai je ya kama haya tamkar ba shi da kowa a Toro?
Shi kuma ya kafe ba zai zauna a cikin gidan nan ba.".
Na bata rai na ce "Ai Wallahi na fa'da masa indai ya yarda da tsarinsu to kuwa sai dai a tsine mini dan bazan zauna a gidan nan ba'kin ciki ya karasa ni tun ajalina bai zo ba"
Adda Nazira ta ce "Haba ashe tirjiya ya samu daga gare ki, kin ga yadda ya fitittike akan ba zai zauna a wajen ba?
Dada har da kukanta wai sai da ya bari su Baban Tsakiya sun gama gyara masa wajen sannan ya ce zai fita ya kama haya tamkar wanda bashi da galihu a Toro? Shi kuma kinsan shi ya ce "Salisu da yake hayar rashin galihu ne ke nan?
Ashe ashe Gimbiya Yabi ce ta saka ya rikice ya turje.
Ya kama miki gida mai kyau a bayan sakatariya. Ba ki ga gidan ba. Yanzu muka dawo a mashin dinsa ya goye ni muka je ya nuna mini gidan. Ni Wlh har na ji na daina k'insa. Kin ga rawar jikin da yake yi. Sai fa'di yake ya kika ga wajen Nazira? Nasan idan ya burge ki to zai burge kanwar ta ki ma.
Gaskiya Yabi ke d'in mai sa'a ce. Gaba'daya kin rikita namiji irin Yaya Bulkachuwa. Murna nake yi, da dukkan zuciyata nake jin addu'armu ta karbu. Da ikon Ubangiji sai kowa ya yi mamakin alherin da zai biyo bayan wannan auren."
Na tab'e baki na ce "Hmm ai ni dai an cuce ni kawai. D'azu muna maganar k'awayen amarya. Na ce masa ba ni da k'awaye, ke ce to kuma kin yi aure.
Yana bu'de baki da yake shi d'in bunsuru ne sai ce wa ya yi wai ina k'awata fara mai dan jiki. Kin san wa yake nufi?"
Kafin ta ce komai na zarce da ce wa "Shafa'atu yake nufi fa. Har ya k'yalla ya ga halittu a tare da ita shine zai silala me za'a yi da Tijjani ne. Na fa'da cikin kunan rai.
Ga mamakina sai ganin Nazira na yi ta k'yal-k'yale da dariya sosai. Sannan ta ce da wuri haka Yabi?"
Na bata rai na ce 'ban gane ba?"
Ai kuwa cikin ido ta ce" tun yanzu kin fara kishin Yaya Bulkachuwa ina kuma idan kin shiga hannunsa?"
Hawaye ya b'alle mini ina ce wa "Allah ya sauwake, ashe ba ki fahimce ni ba Adda Nazira?"

*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*



[9/27, 11:20 PM] Hauwa Galadima: *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*

*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.


*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBE TA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*

"Tunda Kika kasa gane abin da yake zuciyata ba wanda zai fahimce ni dai-dai".
Na fa'da cikin kuka sosai.
Ta maze ta ce "Ai kuwa dai kinsan na sanki tamkar yunwar cikina. Wata'kila kuma y'an watannin da muka yi ba tare ba ya sanya na soma mance ki. Amma tunda kin ji bacin rai a dalilin maganar ki yi hakuri da wasa nake yi shikenan?"
Da haka na fara goge hawayen idona.
Sai yamma lis ta tafi. Na rakata hanya ta hau abin hawa.
Ina kan hanyar dawowa sai ganin mutum na yi tamkar daga sama yana biye da ni.
Bai yi magana ba, bare ni kuma. Har muka iso gida sannan ya ce "Asiya Toro manyan mata. Na wuce shi na yi shigewa ta. Ina ayyana shi bai san ya kintsa kansa idan za shi wajen budurwa ba.
Ina shiga na tarar da Babanmu a zaune.
Ko hijabi ban cire ba, sai ga yarinya cikin yaran Baban kasuwa ta shigo ta ce "Adda Yabi Yaya Bulkachuwa ya ce "sauri yake yi ki je yanzu sakon zai fa'da miki".
Ba'kin ciki ya tokare ni, wai shi nan masharranci.
Na fito babu b'ata lokaci na fita ba dan komai ba sai dan Baban Marina yana zaune ba dan haka ba sai dai ya bushe a wajen.
Da fishi shinfide a fuskata na isa.
Ya kalle ni ya ce "Me kuma ya faru dan Allah. Dazun nan fa na ganki kina ta murmushi har na yi zaton ko labarin gidanki da Nazira ta gano miki take baki ya saukar miki da farin ciki mai yawa."
Na d'ago na kalle shi ina rasa ma ajin da zan ajiye Tijjani. Na lura kusan halin mahaifina ne da shi. Zaka yi musu abin takaici sai su waske su nuna basu gane ma me kake nufi ba, bare su nuna sun damu a karshe kuma sai su yi maka abin da kai ne zaka shaki takaici cikin salama.
Na wuce shi na yi tafiyata.
A hakan har kwanakin suka zo ya rage saura kwanaki biyu daurin aure.
A wannan ranar kuma aka yi mini jere.
Da yake Yaya Salisu ya na aiki bansan yadda aka yi ba an ce dai an yi mana gado da kujeru ni da Ubaida.
Na tuna irin yanayin damuwa da Nura ya shiga a dalilin rashina. Da hawaye a idonsa yake fa'din "Na tafka asara Yabi! Tijjani ya zama mai sa'a. Na yarda da kaddara. Na kuma karbi auren kanwarki da hannu biyu in sha Allah kuma zan yi mata adalci.
Allah ya sanya alheri. Allah ya sanyamu cikin masu biyayyar iyaye da ha'kuri saboda shi".
Da alhini mai yawa muka rabu.
Kimanin kwanakin sati kenan.
Na nisa ina sake hakaito wa ban da y'an kofarmu ba wanda ya yaba lefe ko kyaun gidana na rasa irin wannan masifar.
Har gara ma an dan yaba gidan Ubaida kadan duk da gidanta gida ne mai kyau sosai.
Amma da yake da ahalinmu aka fi adawa ba a wani yaba an zuzuta kamar yadda aka kurzanta na su Maijida da Firdausi ba.
Haka gidan Nasiba aka yaba aka kod'a lefenta tamkar me? Amma namu mukus kake ji.
A hakan har asabar din da ta yi daidai da 20 ga watan 5 ta zo aka daura aurena da Bulkachuwa, sannan aka daura na Ubaida da Nura.
Daga nan aka d'unguma gidansu Nasiba aka daura nata.
Fa'din halin da nake ciki na damuwa ba sai na fa'da ba.
Amma dai ji na yi tamkar na sheka barzaku.
Ina takure a dakin Gwaggo Nazira sai kai komo take yi cikin kwalliya. Ga cikin jikinta da ya fara tasawa ya kara mata kyau sosai.
Ihisan k'anwarsu Bulkachuwa ta shigo wai na je abokan ango na jirana.
Akan dole na yarda na bita bayan na ce sai dai ta tsaya ni idan mun je.
Haka na dinga yak'e ina gaisawa da su. Ala tilas na yarda aka yi hotuna. Shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login