Showing 63001 words to 66000 words out of 214110 words

Chapter 22 - Bakar Ta'ada Complete hausa novel

24 Aug 2024

11099

tanadin ka Tijjani.
Sanin baka son nawa ne ya girmama ba'kin cikin da nake ciki. Domin ba a ha'da ni da kai ba, sai dan ana nufin kassara ni.
Ina da masoya birjik, amma aka hana ni aurensu, ake neman lika mini kai, tun bamu je ko ina ba ka fara fa'din baka ta'ba sona ba."
Ya watsa mini lalataccen kallo ya ce "Ko ina son ki ai dole son zai zagwanye.
Me zan yi da wacce zata zo har d'akin uwata ta tozarta ta?
A akan idon ta, da kunnen ta kika ce zan shafa miki S? Ashe ke din kin kere tunanina da nake miki kallon yarinya kankanuwa. Kin ringa kin san komai.
Dan haka ki janye tunanin zan cigaba da yi miki sassauci!
Wallahi sai kin biya wannan rashin kunyar da kika yi mata. Ki rubuta ki ajiye, matu'kar kaddara ta zargemu a matsayin ma'aurata sai kin yi tuba akan wadannan kalaman naki na raini da iyashege. Da ikon Allah sai kin ji kunya da nadama idan kika tuna wannan ta'asar da kika yi."
Na cuna baki ina fa'din "Ba ruwan ka da shirgina, kuma bana son ka so ni, dan Allah kada ka sake yi mini sassauci Tijjani".
Ya jijjiga kai yana fa'din "Yanzu ba ni da lokacin ki, sai kin zama mata ta zaki ga rashin sassauci, kuma ki ga karshen rashin kunya".
Na ja tsaki mai tsananin gaske tare da cewa "Dutse a tsakanina da auren ka. Ban da mugunta ta ya ya za'a yi wannan ha'din, kana nan tamkar Basumade! To na yi ya ya da kai?"
Ya sake girgiza kai ya ce "Za ki ga yadda zaki yi din. Watarana har kuka zaki yi akan son Basumaden".
Bansan ya aka yi ba, na tattaro yawun bakina na watsa masa a fuskar sa.
Tare da fa'din "Aniya bi Aniya! Har abada ba zan ga wannan bak'ar ranar ba".
Ransa ya b'aci k'warai da gaske.
Ba zato ya d'auke ni da marin da ya shige ni tamkar na saki sayi a wajen tsabar ki'dima.
Na k'walla k'arar da ya sanya Nasir fito wa a guje yana cewa "Mene ne Yabi?"
Ganin yayansa a tsaye a wajen ya sanya ya kasa magana. Sai kallommu yake yi.
Cikin fishi ya nuna ni da yatsa yana ce app lwa "Tashi ki dauko ragga ko tissue ki share mini wannan k'azantar da kika watsa mini, ko na nada miki na jaki".
Cikin kuka sosai na ce "Bazan share ba, ka kashe ni k'arewar duka irin na jaki.
Kuma wannan marin Wallahi baka ci bulus ba. Dan na zo gidanku ba shine dalilin da zaka dinga dukana ba."
Na fa'da ina matsanancin kuka.
Takaici ya kama shi ya dunfaro ni, ganin yanayinsa ya sanya na kankame jikina ina kare fuskata da dukkan hannayena.
A hanzarce Nasir ya ce "Rabu da ita Yaya ba k'arfinku daya ba".
Bai tanka ba, ganin yana shirin damkata ya sanya na sake canyara ihu fiye da na farko tare da rufe idanuwana.
Ba zato na ji ya ja hijabin jikina yana goge yawun fuskarsa da shi.
Daidai lokacin Babah da abokiyar zamanta suka shigo a matu'kar birkice saboda ihuna da ya cika kunnuwansu tun daga waje.
Ganinsa a tsaye a kaina ga hijabina a hannunsa.
Ya sanya ta fusata, ta dinga zaginsa irin na tsamar nama.
Ya kasa cewa kala kanzil bare ya kare kansa.
Ta juya ta kalli Nasiru ta tambaye shi ba'asin ihuna.
A sanyaye ya ce "Rashin kunya ta yi masa ta tofa masa yawu a fuska shine ya mareta, ya ce ta goge masa, ita kuma ta k'i shine ya goge da hijabinta."
Cikin kuka sosai na ce "Allah ya hana hubbul ra'as Yaya Nasir. A Ina na yi masa rashin kunyar?
Ba shine ya zo ya same ni ina zaune yake ta yi mini sababin wai na yi miki rashin kunya ba. Kuma har yana kirarin idan an kai masa ni sai ya kusan kashe ni tunda na zo gabanki na ce bana sonsa.
Dan na ce "Ai ke din uwata ce shikenan ya rufe ni da duka, wai ta ina kika zama uwata?"
Na fa'da ina jan majina.
Ta juya kuwa tana masa ba'kin kallo ta ce "Ta zo ta fa'da mini din shasha da baya girma! Idan ka ji haushi ka gyara munanan ta'adodin da ake k'yamarka saboda su.
Sannan ita din y'a ta ce har a kiyama kuwa! Zuwan data yi wajena ba k'aramin kara mata daraja ya yi a idona ba.
Ta karrama ni, daga nan har k'asa ta rufe mini ido kuma zan yi ta karrama ta ina yiwa kuruciyarta adalci".
Umma kishiyarta ta ce "To daina yi masa zagin yara a idonta. Wannan ba sharia kike yi ta gaskiya ba. Bangaranci kawai kike yi".
Da takaici Babah ta ce "Ban da shasha ne yana ganin halin da take ciki, maimakon ya dinga rarrashi da hila har ya samu ta sauko a samu daidaito a tsakaninsu sai kuma ya tisata a gaba da cin zali da alwashin razanar wa iri iri?"
Na sake fasa kuka ina cewa "Babah dazu kin ce za'a fasa auren, yanzu kuma kin ce ya rarrashe ni?
Ni Wallahi ba zan karbi rarrashinsa ba.w
Ya cire hular sanyin da ya kifa a kansa ki ga yadda sumarsa take.
Sannan ya dauki wannan tafkeken hannun nasa ya mare ni, gaskiya ni dai ki rama mini kawai".
Umma ta mini dakuwa tana fa'din "ungo na ki, ja'irar yarinya, Tijjani za'a doka?"
Na kara fashe wa da kuka.
Yayin da shi kuma ya koma gefe ya sunkuyar da kai.
A yau ka'dai na fahimci nauyin juna, Babah suke ji ita da Tijjani.
Bata kula shi a dalilin shine d'an fari.
Shima kuma baya iya katabus idan tana wajen.
Wata irin nutsuwa yake yi a gabanta.
Wadda ni ban fahimci hakan ba sai yau.
Kafin wayewar gari na fahimci Babah irin iyaye ne da basa sakarwa yaransu fuskar da zasu rainasu .
Haka nan yaranta maza ma suna aikin gida ba sai iya mace ba.
Kullum cikin jaddada musu, idan basu saba da jin k'ai da tallafa wa mace tun yanzu ba, sai yaushe zasu fara?
A wannan zaman na gane ita ce ta mayar da Tijjani Toro dan lalacewarsa da zata fi muni a gabansu tunda ubansa baya son damuwarsa.
Wannan rashin fuskar da bata ba shi tun yana yaro ya sake yin tasiri a mua'amalarsu.
Sannan na fahimci ita din wata irin uwa ce da son y'ay'anta bai hana ta yi musu sahihiyar tarbiya ba.
Ma'ana bata ta'ba dora ra'ayinsu akan nata, dole sune zasu bi tsarinta ko da basa so kuwa.

*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*MASU BUKATAR YON RIGISTA DA G.H.T. KAKARKU TA YANKUE SAKA DOMIN KUWA FASEELAT ZATA MUKU JAGORA HAR KU FAHIMCI KOMAI CIKIN KYAKKWAR MU'AMALA DA KYAUTATAWA*.
*07039269802*
Washagari sassafe muka dauki hanyar Toro.
Muna kusantar garin zullumin da nake ciki na sake tsananta.
Nadamar gudun da na yi, na yi ya fi sau dubu.
Kafatalin ahalin gidan Marina mu yaran Gwaggo ne muke guduwa idan za'a aurar da mu.
Duk da cewa mu ka'dai ake yiwa auren dole a gidan.
Na tuna daren shekaranjiya inda take fa'da mini tsananin da ta fuskanta a auren Yaya Ummi.
Komai sai ace ita ce ta saka ta.
Ta ro'ke ni na daure na kwantar da hankalina, domin tunda aka ambata aurena da shi bata sake kwanta ta yi barci mai nauyi ba.
Idan kuwa har addu'ar uwa tana tasiri akan ya'yanta ta tabbatar ba za'a juyar da addu'ar da take yi mini ba.
Na sake tuna rarrashin da Baban Marina yake yi mini a kullum, duk abin da zai yi dan ya sanya farin ciki a zuciyata shi yake yi mini a tsukun nan.
Amma shekaranjiya sai da ya zane ni dan ya tabbatar mini babu fashi akan al'amarin Bulkachuwa.
Amma washagari na saka kafa na fice na barsu.
Na kuma yi imani duk inda zan je ba zan sami daya bisa darin soyayyarsu ba.
Daga jiya zuwa yau Àllah ka'dai yasan ba'kin cikin da suke ciki, dan ma Babah ta yi hikimar skaa Bulkachuwa ya juya da yamma dan ya sanar da mutan Gidanmu ina wajen ta.
Tunda ta kasa fa'da musu ta waya.
Na dinga kuka ina shessheka. Ita kuma tana ta rarrashi da yi mini nasiha.
A motar na bata hakuri, na kuma roki alfarmar kada ta ce da Baban Marina komai, na ha'kura zan yi biyayya".
Ta dinga yi mini addu'a da fatan alheri a dukkan sha'anina.
Har muka iso Toro misalai iri iri ta dinga yi mini na irin aurena.
Da kuma dabarun ri'ke namiji a hannu. Har na dinga jin nauyi da kunyarta.
A k'ofar Dada muka fara sauka.
Ta amsa gaisuwar Babah, amma tawa gaisuwar ta share.
Kamar ba zata tanka ba sai kuma ta zabura ta ce "Mandiya hamshakiya! Wai ke tabbataciyar marar kunya, kuma marar kirki. Idon ki babu kunya ko ka'dan, har ke ce zaki tafi wajen Hauwa ki fa'da mata ba kya son auren mai sunan manya?
Da me kika fi shi?
Sanin kan ki ne ban da ya mayar da kansa abin da ya zama ba, da ke baki isa ko kallon ki ya yi da sunan soyayya ba."
Na zum'bura baki ainun na ce "To kawai a bar shi ya auri wacce take son sa ta kuma dace da shi din.
Ni ma a bar ni da masoyana".
Ta kawo mini duka da mafici, ban goce ba, domin na riga na kai makurar fusata da al'amarinta.
Ba dan idon Babah da take zaune ba, da na zage na fa'dawa Dada gaskiyar magana. Amma ido mashi ne, mussaman da yake muna cikin zamanin da inka cika fa'din gaskiya sai ya zama rashin kunya a idon manya.
Mun jima a wajen Dada sannan muka isa k'ofarmu.
Muka tarar da Baban Marina yana gida ya dawo cin abinci.
Da walwala ya marabci k'anwarsa yana fa'din "Lale da mutanan Bulkachuwa". Ta zauna kusa da shi cikin nutsuwa da murmushi sosai.
Ta gaishe shi a ladabce.
Ya amsa mata da sakakkiyar fuska.
Ina gefe a takure tamkar mujiya cikin tsuntsaye.
Na gaishe shi kaina a kasa.
Ya share tamkar yadda Dada ta yi mini.
Na sake yi a karo na biyu.
Ya sake dauke kai tare da daure fuska.
Nan da nan na fara kuka sosai, ina ba shi ha'kuri.
A dan tsorace Babah ta ce "Ka yi ha'kuri! Da kanta ta ce na rakota ta baka ha'kurin fitar da ta yi baka sani ba."
Ya girgiza kai ya ce "To mai gaisuwarta zata yi mini?
Me zata fa'da mini?
Na zuba mata ido ta yi duk abin da ta ga dama tunda ni ban isa da ita ba.
Sannan ni ba tafiyar da ta yi ba ne ya bak'anta raina ba, wajen ki da ta dosa ne ya b'ata mini. Akan me zata je wajen dangina tunda ni din da zata ci arzikina a wajen ki, ta nuna mini iyaka ta?
Ban da hauka da kuma idonta babu ruwa a ciki ta ya ya zata doshe ki?
A sanyaye Babah ta ce "Yaya dan Asiya ta zo waje na sai ya zama aibu?
Akan wannan yaron ne kake ganin rashin kunya ne ta zo waje na?
Ni bana raba tsakanin yarana da naka.
Sannan na gode mata ta zo wajevna, da wani wajen ta yi fa?"
Ya murmusa ya ce "Da kuwa da kanta za ta dawo domin ai duniya ta ishi kowa darasi, a lokacin da za ta dawo daga gudun ni kuma a lokacin zan guje ta da ni da dukkan ahalina".
Kukana ya tsananta domin a lafuzzan Babanmu na fahimci girman bacin ran da na sanya shi.
Ina kuka, ina bavshi hakuri tare da ce wa "Na yi kuskure Babanmu".
Ya yi shiru bai ce k'ala ba.
Babah ta ce "Ka huce! Ka yi mata afuwa dan girman Allah. Ta ci arzikin rakota da na yi."
Ya saki gauron numfashi ya ce "Na yi mata afuwa, amma bazan huce da ita ba, sai an yi auren ta kwantar da hankalinta, ta kwantar da hankalin mijinta. Yardata tana d'amfare da yardar mijinta akan sha'aninta.
Ban da ke Hauwa, da ko kallonta ba zan yi ba. Domin ai ga Ubaida nan k'anwarta ce ta sosai, bata son auren da zan yi mata amma ta ha'diye komai. Amma ita Yabi da yake ta isa, kuma uwarta bata k'wabarta ai kin ga d'anyen hukuncin da ta dauka na guduwa ta kai k'arata. Ban da k'arfin addu'ar da kullum nake yiwa iyalinmu ai da duniya ta yi niyyar shiga".
Babah ta dinga fa'din "Da Ikon Ubangiji ba zamu ga haka akan ahalinmu ba! A yi ha'kuri Allah ya shirya mana su.
Ta dinga godiya da addu'a, akan alheri mai yawa ya biyo bayan auren.
Sai kuma ta fashe da kuka wanda ni dai bansan na menene ba.
Na dai ji Baban Marina yana ce wa "Yo Hauwa ban da dai muna cikin wani irin zamani da dan-uwanka yake zama tamkar makiyinka menene abin godiya? Komai zan yi miki ai kaina na yiwa. Tijjani d'a ne ko yafi hakan lalacebwa idan duniya da adalci bai kamata mu din mu hana shi aure ba.
Tunda mune muke zuwa nemo masa auren y'ar wasu. Kebnan idan da adalci sai mu ba shi tamu.
Fatana dai ki tsananta yi masa addu'ar shiriya, bakinki yafi na kowa tasiri a kansa."
Tana goge hawayen idonta tana fa'din "Ina yi Yaya, zan cigaba da yi. Allah ya shirye shi, ya sanya wannan auren ya zame masa sanadin shiriya da albarka a rayuwarsa gaba'daya.
Yabi kuma Allah ya bata hakuri da juriya."
Ya kalle ni ya ce "Tashi ki bamu waje. Na mike sum sum Babu nauyi. Domin hakan da Babanmu ya yi mini ya tabbatar bai huce da ni ba.
Ina shiga d'akin Gwaggo na tarar da ita tamkar wacce take fama da tsi da ha. Gaba'daya ta rafke, gata fara ce amma ta yi wani irin baki sosai.
Na zauna na gaishe ta ta amsa ba tare da ta kalle ni ba.
Nan da nan kukan da nake yi ya dawo sabo.
A fusace ta ce "ki rufe mini baki tun baki tunzira ni, na yi miki mummuna baki ba. Ai hakan kike so
Shike nan ni kuma duk sadda aurenku ya zo a lokacin watan bakin-cikina ya kama.
Kin ji da'di da ubanku ya jingina guduwar ki da ce wa ni na saki.
Allah shine shaidata, ban isa da ke ba ne, domin da na isa ko k'ofar gida zaki je sai kin fa'da mini.
Amma saboda ki jefa ni cikin kunya da ba'kin ciki shine kika gudu! Har kin yi girman da zaki gudu ki bar iyayen ki saboda sun miki laifi?
Ta share hawaye ta ce "
Da nasan hakan zaki yi mini Wallahi da ban kawo haka a cikin gidanku ba. Da na dauke Ikilima tun shekarun baya na yi tafiyata na bar wannan k'addararren zaman".
Na dinga kuka ina bata hakuri, domin fishinta da kukanta yafi d'aga mini hankali fiye da fishin Babanmu.
Murya na rawa take fa'din "da yake ita Innarku ta iya haihuwa, ai ga shi nan Ubaida bata kunyata ta ba, bata janyo mata ba'kin jini a wajen Babanku ba".
Tsigar jikina ta tashi sosai. Na dinga ganin wautata.
Da muryar kuka na ce "Dan Allah ki yi ha'kuri Gwaggo! Kaina ne ya kulle ainun. Na shiga rud'u mai girma. Amma da ikon Ubangiji komai zai daidaita, zan iyakacin bakin kokarina na ga ban sake janyo miki bacin rai ba. Ki sake ninka addu'ar da kike yi mini. Kullum ina sake jin tsana da k'yamar Tijjani a zuciyata".
Kuka na sosai ya k'wace mini.
A wannan karon sai ta kasa ce wa komai illa ido da ta zuba mini sosai.
Wata'kila rauni ne irin na uwa, wata'kila kuma tausayi na bata sosai.
Ta aro jarumta ta ce "Sau tari alheri yana zuwa mana ta inda bama so. Sai ka k'i abu tare da hasashen bai cancanta ba, sai kuma ya zame maka alheri. Sai ka so abu tare da hasashen za'a dace sai kuma ya zame maka fitina.
Ina fatan komai zai dunfaromu Ubangiji ya juyar da shi zuwa alheri.
Tashi ki d'oro alwallah, ni na yi tun dazu".

*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
*Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*.
*08032773332*
[9/25, 9:06 PM] Hauwa Galadima: *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*

*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers*
*08089965176*
*07084653262*


*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*



Ina alwallah ina kuka. Ba abin da ya sake karya mini zuciya irin yadda na jiyo Baban Marina yana cewa Baba "Ni fa ki daina ro'ko na Hauwa! Tuni na yafe mata, amma walwalata ce ba zata ga ni ba, har sai ta kwantar da hankalinta an yi hidimar nan lafiya lafiya. Sannan kuma ta zauna lafiya da mijinta kamar yadda y'anuwanta suke zaune lafiya.
Ina ce Ummi gidan mai iyali aka kai ta? Ga kuma mijin ya d'orawa ransa masifar son abin duniya.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login