Showing 45001 words to 48000 words out of 214110 words
ba matu'kar tana da iko akansa.
Ya nemi sanin ba'asi ta ce ya saurare ta zuwa jibi.
Bai sanar da kowa ba, har sai ranar da ta ambata.
Dukkansu suna zaune a dakinta.
Cikin rashin damuwar komai ta ce "Alhaji! Yanzu ya kyautu ace an bar mai sunan manya yana gararanbar neman aure ana hana shi, alhalin akwai yara a gabanku?
Kullum da abin nake kwana, nake tashi, tare da zullumin kar'bar da zaka yiwa al'amarin.
Sai kuma na tuna ikon da shari'a ta bawa uwa ".
A sanyaye ya ce "Hakane".
To maganar auren Yabi da wannan ba'kin yaron ba shirayayya ba ce daga Allah.
Domin mai sunan manya za'a bawa ita."
Wani irin zullumi ya shige shi.
Murya a raunane ya ce "Dada ina ce Nasiba yake so?"
Nan da nan ta ce "Nasiba ai ubanta ne ya yi iko a kanta ya ce dan k'aninsa zai bawa."
Ya ce "Dada ina ro'kon arziki a ba shi wata cikin yaran Badamasi ko na Iliya tunda an riga an karbi komai na aurent a, akwai nauyi mai yawa a tsakaninmu da uban yaron nan ke ma shaida ce".
Ta kai kallon ta ga Baban Tsakiya ta ga ya murtuke fuska.
Nan da nan ta ce "Duk abin da yake tsakaninku da Tanimu ya kai da yar'uwar ka ne?"
Da sauri ya ce "Ba kai ba Dada! Sai dai haramun ne neman aure a cikin aure."
Baban kasuwa ya ce " Ai ba bisa son zuciya ba ne, biyayya ka yi, Allah kuma zai karrramaka tunda ka bi uwa. Idan ya so sai a bawa Nura Kaltume ba shike nan ba."
Baban Marina ya kalli kaninsa da wani irin duba.
Yana mamakin son zuciya irin tasa. Ya dauki y'arsa ya bawa Jabir yasan kuma saurayin Yabi ne. Yanzu kuma a kan idonsa yake fadin zai sake bawa Nura y'arsa tunda yasan akwai mamora a tare da yaron.
A hankali ya ce "To ko zaka lamince na bawa Tijjani Kaltumen kawai?"
Nan da nan ya ce "Ina! Ai ba ita Dada ta umarta ba, so ka ke na shiga fishin uwa?"
"Shike nan Allah ya amsa addu'ar ka, Allah ya sanya albarka a cikin wannan ha'din , ya amintar da lamarin. Na bawa Tijjani Yabi, da dukkan zuciyata"!
Baban Marina ya fa'da cikin wani irin yanayi mai ban tausayi.
Dada ta ce "Allah ya yi albarka".
Har ya yunkura zai tashi sai ya ce "Zan bawa shi Nuran kanwarta. Komai da suka kawo da sunan Yabi ya koma kan Ubaida".
Ya fita yana ha'da hanya.
A zaure suka yi kicibus da Bulkachuwa.
Baban Marina ya kalle shi cikin wani irin yanayi.
Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Dubi gashin kanka, kamar ba bahaushe ba, ka dubi wando jikinka, tamkar babu iyayenka a gidan, yaushe zaka zama cikakken mai kamala ne?"
Ya sunkuyar da kai ya ce "Za'a gyara Baba"
Domin kuwa da dukkan zuciyarsa yake ganin kimar Baban Marina fiye da su Baban Tsakiya.
A dakin Dada kuwa Baban Kasuwa ya dinga fa'din"Dada ai da kin ce a ba shi Kaltume kawai, ina ce ta fi Ubaidan a haife?"
A dan tsorace ta ce "Ga ni na yi zan takura da yawa, sannan dole hankalin mutane zai dawo kanmu".
Ba shakka ya ce "To ya dawo mana! Idan ka daka ta mutane ai ko sallah ba zaka yi ba, domin kana yi suna kallon ka, ba dan su gyara maka ba, sai dan su gano na'kasunka su yi zundenka
Bare kuma akan wani al'amarin duniya da bai zame komai a juya maka manufarka kyakkawa zuwa mummuna ba."
A sanyaye Dada ta ce "Hakane".
Suka tashi ba tare da sun so a bawa Nura Ubaida ba.
Washagari sassafe Baban Marina ya zaunar da matansa ya shaida musu juyin da aka sake yi, da kuma hukuncin da ya yanke akan yin madadi da Ubaida.
Daga Inna har Gwaggo abin bai musu da'di ba. Mussaman Gwaggo da take gani ita ce zata fi shiga cikin tashin hankali, domin matu'kar Yabi bata samu dacen aure ba, to komai ma zai kwace mata ne. Ga Ummi ita ma fama take a nata gidan.
Shike nan a hakan zasu kare ita da y'ay'anta?.
Shirun da suka yi gaba'daya shi ya sake sanyaya masa guiwa.
Ya ce "Kun yi mini zuru?"
Mama cikin walwala ta ce "To me zasu ce Alhaji? Y'ay'anka ne fa ka yi iko da su, sannan ba shawara ka nema ba, tunda an riga da an zartar to wace ce zata yi inkarin hukuncin Dada matu'kar tana son ka rabauta?".
Maganar Mama ita ta sanya wa Gwaggo k'warin guiwa domin ta sani so take ta ganta cikin rashin sukuni da tashin hankali.
Nan da nan ta ha'diye damuwarta, ta murmusa tare da ce wa"Allah ya sanya alheri da albarka, ina fatan Allah ya sa ace gara da aka yi".
Wata irin nutsuwa ta zo wa Baba domin dama uwar Yabi yake ji. Ya sani borin da Yabi zata yi ba zai yi tasiri ba tunda an yi sa'a ita din mai jin maganarsu ce mai kuma kishin kada su kunyata ne.
Ya dinga yaba mata tare da sanya mata albarka.
Ya juya ga amaryarsa Inna uwar Ubaida.
Ya ce "Ke kuma fa?"
Murya babu amo ta ce ", Allah ya sanya albarka".
Ya sake numfasa wa tare da cewa"Yadda kuka kwantar mini da hankali a lokacin da aka jefa ni cikin matsanancin hali, ina rokon Ubangiji ya kewaye y'ay'anku da farin ciki da kwanciyar hankali a wannan aure.
Allah ya sanya alheri mai yawa ya biyo baya. Allah ina rokon a azurtasu ta inda muka zata da
ta inda bamu zata ba".
Suka amsa da ameen cikin juriya. Amma Mama bata ce uffan ba.
Ha'din kai da ya samu daga wajen matansa ya taimaka kwarai wajen kwantar da hankalinsa.
Har dare muna namu yi, ban samu labarin komai ba. Sai dai na lura da rud'anin da Gwaggo take ciki, gaba'daya ta zama wata iri, ta yi zuruzuru.
Na tambaye ta ta ce mini gudawa take yi. Take na gasgata na tura Anas ya siyo mata filagil.
Da daddare bayan dare ya d'an fara tura wa Baba ya kiramu ni da Ubaida.
Na cika da mamakin ha'damu da ya yi.
Muna durkushe a gabansa, shi kuma yana kan kujerar ba'kin karfe irin ta da, da take dakinsa.
Ya kalle ni ya ce "ku zauna sosai. Ina bu'katar hankalinku da nutsuwarku".
"Muka nutsu kuwa, amma gaba'daya zuciyata ta shiga rud'ani sosai.
"Shi da kansa ya jima bai iya yin maganar ba. Ya jima yana juya maganar yana tunanin ta yadda zai iya fa'dawa Yabi a karo na biyu za'a bawa wata saurayinta. Babban damuwarsa irin yadda ya ga ta sanya Nura a ranta.
Ransa ya baci fiye da jiya. Ba'kin cikin y'anuwansa ya mamaye shi. Wai me ya tsare musu a wannan duniyar ne?
Da k'yar ya yi k'arfin halin cewa "Yabi kinsan ce wa a duniya ba wanda zai so ki, ya so cigaban ki irin ni da gyatumarki ko?"
Ba haufi na ce " "Eh Baba".
Ya ce "Madallah! Sannan kuma ba wani abin kaico da zai dunfaro d'a mahaifi ya zuba ido ya cimmasa, sai idan abin ya gagare shi.
Ina son ki fahimce ni, ki mini adalci, ki kuma ninka biyayyar da zaki mini a wannan karon.".
Jikina ya fara tsuma, zuciyata ta shiga zullumi, idanuwa suka cika da ruwa.
Na kasa bu'de baki na ce komai dan tsananin bugun da zuciyata take yi.
Ya numfasa sosai ya ce "Ina son na fa'da miki auren ki da Nura ba zai yiwu ba, ba kuma na son ki kalli hakan a matsayin shirina ko shirin wani, ki yarda shirin Allah ne, shi kuwa idan Ubangiji ya jarrabe ka, ka yi ha'kuri a farkon al'amarin kana da lada da sakamako mai girma".
Take ruwan da ya cika a gurbin idona ya tumbatsa ya fara zuba.
Ina jin nauyin da zuciyata ta yi ba zai kwatantu ba.
Wacce irin Bak'ar kaddara ce nake gudu take bina da gudu shigen na fanfalaki?
Na kasa bu'de baki na ce uffan domin sai na fara hasashen mafarkin da nake yawan yi ne akan aurena da Nura zai iya ruguje wa.
Jin shiruna ya sanya ya ce "Na sani kina sona, son da yake sanya ki son duk abin dana haifa, ko nake so.
Ina ro'ko ki taimake ni, na yiwa mahaifiyata biyayya, ni kuma zan dauwama ina miki addu'ar wanye wa lafiya da kuma rufin asirin duniya."
Cikin rishin kuka na ce "To Babanmu".
Ganin irin rudin data shiga sai wata dabara ta zo masa.
Sai ya ce "Babanku Iliya ya bu'kaci na bawa Nura Kaltume a madadinki".
Na d'ago a matu'kar birkice na ce "Wai me na yi muku ne Baba?
Yan'uwanka suna azabtar da ni, kai kuma ka zuba ido kana kallo, ka kasa kare mini darajata! Ko dai da gaske karayar arzikinka tana damfare da zuwana duniyar nan mai cike da ba'kin ciki mai tsanani?"
Na fa'da ina kuka sosai.
*Auzubillahi! Na yafe miki Yabi! Na sani kina cikin ki'dima ne, ni kaina da na haife ki kiris ya rage ban zautu ba a dalilin wannan al'amarin.
Allah ka sassauta, Allah ka kawo mafita. Allah kada ka jarribi Yabi da jarrabawar da zata bijire mini. Bare ta haifi wanda zai bijire mata."
Na yi kasa da kaina ina kuka kasa kasa.
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
Tsawon lokaci kafin na ce "Na ha'kura da shi Baba. Amma Wallahi indai aka ba shi Kaltume to zan roki Ubangiji ya matso mini da ajalina kusa, domin na sani bazan sake farin ciki ba.
Indai kunyar Babansa kake ji, to ka bashi Ubaida tunda dama saboda kai ya turo d'ansa ya neme ni, ka bashi ita, zai fi mini sauki a maimakon ka rasa suruki nagari irinsa".
Ina rufe baki kawai Babanmu ya fara hawayen da ya daskarar damu.
Wanda na tabbatar na zallar ba'kin ciki da kuma farin cikin yadda nake tsananin son y'anuwana.
Ai ko murya na rawa ya ce "Irin yadda kike son yan'uwanki haka nake son nawa, amma shaidan da son zuciya sun shiga cikin al'amarinmu sun yi kane kane."
Ya daga kai ya ce "Allah kada ka jarrabi ya'yana da rugujewar zumunta".
Jikinmu ya sake yin mugun sanyi ya ce "Ubaida kin ji me yayarki ta ce shin zaki bi bayanta wajen sadaukar da burinki, ki mini biyayyar da ke ma zan dauwama ina yi miki farar addu'a?"
A sanyaye ta ce "Zan yi Baba! Na amince, da ikon Ubangiji ba zan kunyataku ba, komai zan zama kuma a duniya a sanadin auren nan, na sani arzikin Adda Yabi na ci, ba kuma zan juya wa al'amarinta baya ba".
Zan yi zumunci da ita a cikin ko wanne hali da rayuwa zata wullamu".
Daga hakan kuma ta fashe da kuka sosai.
Wanda ita kanta bata san dalilinsa ba, amma dai tana jin na tausayin Yabi ne.
Da ya rasa yadda zai fadi Tijjani ne mijin da aka zaba mata sai ya ce "Yabi ki tsananta addu'ar shiriya ga Tijjani! Ki kuma rage tsananta al'amarinsa ta yadda zaki fahimce shi da kyau, Annabi ya ce "Addu'ar miji akan matarsa karbabbiya ce, haka addu'ar mata akan mijinta karbabbiya ce.
Dan haka ki tsananta yi masa addu'ar shiriya, da kuma a cika kirjjnsa da soyayyar ki da tausayin ki, sannan a buda masa kofofin arziki"
A ki'dime na ce "Baba dan Allah warware mini wannan curarren bayanin, d'an yi mini gwari gwari".
Da matu'kar rauni ya ce "Tijjani zan aura wa ke".
Ai kuwa na dage na zunduma ihu ina birgima, ina fa'din "Wayyo Allah mutuwar tsaye ta samu Yabi! Wayyo Allah nakasa ta zo mini. Yabi zata zama iyalin mai *BAK'AR TA'ADAH*
*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. Domin kuwa asalin *Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*.
*08032773332*
[9/25, 3:39 PM] Hauwa Galadima: *WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
Da dukkan k'arfina nake ihu, domin na tabbatar an zartar mini da wananan hukuncin ne dan na tabbata a cikin garari, a kuma jefa mahaifana cikin ba'kin ciki mai dagargaza lafiyar d'an adam.
Babu zato na ji saukar duka ta ko ina a jikina.
Da k'yar Baba ya k'wace ni a hannun Gwaggo yana fa'din "Akan idona zaki dake ta?
Ai abin sai ya yi mata yawa ga mari ga tsinka jaka!"
Da rawar murya ta ce "A wannan daren da ko allura ce ta fa'di za'a iya ji ne zata yi ta mana kururuwa?
Ba ga k'anwarta nan Ubaida ba, da aka zartar mata da hukuncin aure babu zato, bata yi hakan ba sai ita?"
Ya girgiza kai ya ce "Tana cikin rud'ani, rarrashinmu take bu'kata ba fishi da juya baya ba.
Baba ya ri'ke ni a jikinsa yana ce wa "Yi tafiyarki ki bar ni da su ai ban kira ki ba".
Haka kuwa ta fita, ba tare da ta sake ce wa komai ba.
Ya ce "Uwarki mai biyayya ce, mai ha'kuri ce, daure ki gaje ta, da sannu Ubangiji zai yi muku tukuicin alheri.
Allah baya kunya ta masu ha'kuri duk lalace war zamani".
Ya dinga rarrashi da ban baki har ya samo kaina na tsagaita kukan da nake yi mai gigitar wa.
Ubaida kuwa ita ma taya ni kukan take yi.
Da kansa ya raka ni har dakin Gwaggo tare da jan kunnen ta kada ta sake ko murya ta d'aga mini.
Sannan ya raka Ubaida yana ta faman sanya mana albarka.
Wannan dare ni dai duk yadda ake fadin barci barawo ne bai iya sace ni ba.
Kwana na yi ina kukan zuci da na ido.
Wata irin kiyayyar Bulkachuwa ta mamaye ni, har na ji ashe ma da ban washe shi ba.
Yanzu ne nake jin asalin k'insa da k'yamarsa.
Yadda na kwana ban runtsa ba hakan ma Gwaggo.
Sai dai ita kwana ta yi akan abin sallar ta.
Tana ta addu'ar idan wannan al'amarin daga gare shine, to ya amintar da mu akansa, ya kuma sanya alheri da albarka a zamantake war aurenmu, ya shirye shi, ya ha'da zuciyoyinmu, ya kuma saukar mana da arziki.
Idan kuma ba daga shi ba ne, to ya ruguza al'amarin cikin kwanciyar hankali.
Ba addu'ar da nake jin da'dinta irin idan tana fa'di "Allah ya ruguza al'amarin.
Domin har cikin zuciyata na tsani ta ce Idan alheri ne Allah ya tabbatar din nan.
Kwata kwata ba tsarina daya da shi ba, mun yi hannun riga, kyaunsa da farar fatarsa basa rud'ata.
Na tsani halaiyarsa, na tsani yadda nake ganinsa a kaca kaca.
Na tsani namiji fari sol ma gaba'daya.
Washagari duk yadda na so na ha'diye damuwata, kasa wa na yi. Sallah kawai na yi na sake kwanciya.
Ba'kin ciki har mak'oshina nake jin sa.
Na dinga jin wani irin azababben ciwo a kahon zuci.
Na hakaito yadda aka raba ni da Yaya J wanda ciwon hakan ba gushe wa ya yi a zuciyata ba.
Ubangiji ya ha'da ni da kwamishina nan ma aka ce bai cancanci a ba shi aure ba.
Allah ya sake kawo Nura an sake cewa a a.
Wanne irin zalunci da raini ne wannan?
Kuka na yi har idona suka kuje.
Farar fatar fuskata ta zama jawur. Idon sun yi luhu luhu.
Na zabge tamkar mai ciwon tsi da ha.
Kwanaki biyu ina cikin tsananin da ban yi zaton zai wuce a waje na ba.
Gaba'daya na takura kaina, na k'warzabi raina.
Har mafarki nake yi wai Bulkachuwa ya shafa mini S.
Ranar da Babanmu ya tara dukkan ya'yansa ya fa'da musu sauyin da aka yi.
Jikin kowa ya yi sanyi.
Mazan Cikinmu hankalinsu ya tashi da jin za'a ba ni Bulkachuwa.
Yayin da Nazira da Yaya Ummi suka fashe da kuka sosai.
Da k'yar Baba ya hakurkurtar da su yana fa'din da ikon Allah bazan wula'kanta ba.
Su Yaya Indo kuwa na kasa gane inda suka saka dosa. Gasu nan dai ba yabo babu fallasa.
Ba abin da Baba yake ta fa'da mana irin mu taimaki kanmu mu zauna da junanmu lafiya. Mu guji dabi'ar y'an ubanci babu ahalin da suke yin nasara a rayuwar nan alhalin suna da wanan *BAK'AR TA'ADAH*. Allah ne ya tsara namiji ya auri mace sama da guda, shi ya shirya ya haifi y'ay'a daga mata daban daban, ke nan ba laifi ba ne yin hakan. Akan me zamu k'i jininmu dan kawai an fito daga uwa daban daban.
Abin kaico sai yar'uwar ka da kuke uba dyaya ta yki fa'da maka sirrinta ko damuwar da take ciki, amma sai ta fa'da wa k'awar ta da basu had'a komai ta fuskar nasaba ba. Kuma abin ba'kinciki wannan k'awar sai ta fitar da zancen har ya iso kunnunwan wadanda ba kya fatan su ji."
Ya numfasa ya zarce da ce wa "Zaku daukaka ne idan na sama kun tsaya kun taimaki na kasanku, idan kun yi adalci a tsakanin kannenku shakikai da li-abbai, abin da zaku dinga kallo shine.
Gidanku daya, gadonku daya, haka nan nasabarku daya. Ba ruwanku da dauko matsalar iyayenku mata ku jefata cikin al'amarinku.
Ku manyan idan kuka jibanci al'amuran kannenku yau, gobe suma zasu jibanci naku lamuran da na y'ay'anku."
Ya yi shiru sannan ya numfasa ya ce "Mutuwa bata yi mana sallama, dan haka ya kamata mu zama cikin shiri da fa'din wasiyya ko da kuwa lafiyarmu kalau.
Zan nemi alfarmarku duk taku. Ko bayan raina ku yi ha'kuri da junanku, kada ku bar kananun cikinki da kawunansu, ku kuma ku bi manyanku, ku shawarce su. Ku zauna da yan'uwana lafiya, ku gaishe su. Ku mutuntasu.
Allah ya muku albarka, ya saukaka muku hanyar neman halal dinku. Allah ya daidaita muku al'amuranku gaba'daya. Allah ya jefa soyayyar junanku a zukatanku. Sannan dukkanku ku yawaita yiwa Yabi addu'a Allah