Showing 138001 words to 141000 words out of 214110 words
yi kuka Asiya da ikon Ubangiji ba zaki sake kuka akan irin wannan al'amarin ba. Ki yi ha'kuri, wannan rufin asirin da kika yi mini, ni ka'dai nasan yadda na sake jin ki a raina. Ni ka'dai nasan yadda girman ki da nauyin ki suka yi mini rubdugu. Ke yarinya ce k'arama amma hankalin ki na manya ne. Kin yi k'ank'anta kin tsunduma cikin irin wannan bak'in-cikin. Ina ro'kon Ubangiji ya sanya wannan ne kukanki na karshe akan wannan matsalar a dukkan rayuwarmu gaba'daya".
Na amsa da"Ameen" a hankali.
Murya babu amo na ce "Bana son wannan gidan, ba zan yi farin-ciki a cikinsa ba. Ka samo mini wani ko daki daya ne zan zauna".
A hankali ya ce "Da ikon Allah zan samo miki, amma ki d'aure zuwa lokaci ka'dan kin ji".
Na ce "To shike nan".
Ya dinga fa'din Na gode sosai my little. Allah ya bani dama da zan jiyar da ke da'di mai yawa".
Na ce ni "Ka tsare mini mutuncina da naka da kuma soyayya da tattali nake so fiye da komai".
Ya ce "zan miki Asiya, zan yi kokarin kiyaye ko wacce irin BAK'AR TA'ADAR da zata sanya ki kuka. Yanzu yaushe zaki fara yin k'unshin dan na tabbatar kin huce kin kuma yafe mini?"
Na shagwaba na ce "Sai ka yi al'kawarin ba zaka dinga yi mini sababi akan k'aramin abu ba. Bana son shouting".
Ya numfasa ya ce "Zan dinga k'ok'arin ina yin fa'dan a hankali. Amma bazan yi al'kawari ba, kin san wani lokacin ha'kurinmu k'wace wa yake yi, abin da zaki fahimta shine sab'awa a zamantakewar aure ba k'iyayya ba ce, matu'kar kuskure ne irin na zaman yau da kullum ko kuma sab'anin ra'ayi".
Na ce "Tom shike nan jibi zan fara yi In sha Allah"
Ya tsananta rik'on da ya yi mini yana fa'din"Thank you my little girl".
Daga hakan kuma ya shiga bai baye ni da zafaffar soyayya mai goge dukkan tsatsar zuciya.
Washagari muka yini cikin nutsuwa da walwala mai yawa. Tun safe kuma na yi status da cewar gobe idan Allah ya kai mu zan fara k'unshi.
Shike nan na ha'kurkurtar da zuciyata na manta komai.
Na rungumi mijina da sana'a ta. Illah iyaka na yanke mua'amala da Rafi'a. Mahaifiyarta kuwa ban fasa gaishe ta ba, ban fasa mutuntata ba. Illah iyaka shiga ne bana yi. Ita ma kuma Rafi'a din ta daina shigo mini.
Wata biyu da faruwar hakan na fara wani irin zazzabi mai zafin gaske. Domin kwana nake yi mutsutsukun ciwon jiki. Gaba'daya ji nake tamkar ana kwankwatsa mini kasusuwan jikina. Ga bana iya cin abinci.
Haka nake kwana ina yini cikin wannan halin. Sa'armu d'aya akwai kayan abinci tare da mu. Sannan yana k'ulla lallen da siyar da ruwa. Babu matsalar babu sosai a tare da mu. Kwana biyu ina ta shan maganin zazzabi da na rage rad'ad'in ciwo. Amma babu sau'ki kullum gaba ciwo yake yi.
Hakan ya sanya shi fita ya yi buga bugarsa ya samo ku'di ya ha'da da wanda muke da shi, ya kai ni asibiti.
Yini muka yi domin sai da aka k'ara mini ruwa. Aka yi mini gwaje gwaje.
Da yamma aka sallame mu bayan sun tabbatar ina da ciki na wata daya har da sati biyu.
Duk yadda nake jin rashin kwarin jiki amma sosai na yi murna. Ni da Tijjani ban san wanda yafi murna da zumudi ba.
Muna isa gida na dauki waya na k'ira layin Gwaggo.
Tana dauka ta ce "Yabi ya jikin dai?"
Da azarbabi na ce "Hmmm Gwaggo ashe duk wannan wahalar da murkususun da nake yi ciki ne da ni!"
Ta yi shiru, sai kuma ta ce "Ni kika kira ki fa'da wa hakan Yabi? Wacce irin marar kunya ce ke haka?"
Na yi sakare domin ni ban ga wani laifin ba. Ita ce uwata bani da wacce ta fita a halin yanzu. Ita ce mafi kusa na tattauna dukkan farin-cikina da ita. Zan yi kokarin na boye fa'da mata damuwar da nake ciki domin na yi amanna damuwata zata tsayar mata da dukkan farin-cikinta ne.
Na sanyaya murya na ce "Gwaggo ki yi ha'kuri. Ina cikin murna ne. Kin san kwanaki a gidan nan aka fa'da mini ce wa Tijjani ya gama zubar da yaransa a titi ni bazan haihu ba. Sannan kuma ke da bakinki kika ce sai na haihu da ki zo ki ga muhallina".
Ta sassauta ta ce "To ba sai ki bari na fahimta ba, ko na ji a bakin yayarku ko kuma Nazira".
Na ce "To sake yin hakuri Gwaggo ai yanzu na fahimta. Idan zan yi ta biyu, bazan fa'da miki ba. Sai dai kawai a ce miki Yabi ta haihu"
Ta ja tsaki ta ce "Allah dai ya baki lafiya" tare da kashe wayarta.
Tijjani da yake gefe yana ta faman murmushi ya ce "Burinmu ya cika.
Yanzu fa'da mini sunan nawa?"
Na yi dariya na ce "Ai sai na haihu".
Ya girgiza kai ya ce "Kin ce da zarar kin samu ciki zaki fa'da mini fa".
Na ce "Haka ne".
Ya ce "To fa'da mini na ji".
Na murmusa ka'dan na ce "Abbanta".
Ya kwashe da dariya ya ce "Wanne irin suna ne wannan? Duk yadda kika kwadaita mini zakuwar samuwar cikin a iya wannan sunan zan k'are?
Abbanta kuma. Wace ce?"
Na jingina a jikin kujerar na ce "Bebin mana."
Ya sake fa'dada dariyarsa ya ce "To idan namiji ne fa?"
Na ce "Ai kuwa sunan da zan fa'da maka mai wuyar samu ne indai namiji na haifo tunda na fa'da maka mai kama da kai nake so".
Dadi ya kama shi ya ce "Allah ka kula mini da Asiya. Ka taya ni son ta, ka shiga dukkan kasafinta. Duk al'amarin da zai dunfaro ta, Ubangiji kada ka bar ta da iyawar ta.
Na ce "Ameen" a gajiye domin wai maganar da na yi har na gaji na fara haki.
Haka nake kwana da yini babu lafiya. Duk dare bama barci kwana muke muna fama. Domin gaba'daya ni dai babu sau'ki. Kwana nake magogo. Haka kuma Tijjani baya runtsawa. Tausa yake yi mini, da fifita idan babu wuta. Tin a lokacin muka fahimci zama iyaye ba karamin al'amari ba ne. Duk yadda na zaku na samu ciki sai da na fara sare wa. Murnata ta fara koma wa ciki dan tsananin wahalar da nake ciki.
Al'amura suka fara yi mana tsauri a dalilin ku'di ya fara yanke mana.
Haka da safe idan ya tallafa mini na yi wanka, ya shafe mini jiki da man zafi zai fita ya dan yawata. Idan an yi sa'a ya samu aiki ya samo ku'di, zai siyo mini 'dan abin kwadayi. Watarana kuma hakan zai dawo.
Baya kuma nisan kiwo, ko ya fita hankalinsa na kai na.
Sai na samu sau'ki, sai kuma jikin ya sake rikice wa.
Na fara gazawa. Rannan Baban Marina da ya zo duba ni, ya ga yadda na koma gaba'daya na yi yaushi.
Ya bashi umarnin ya kai ni gida, ko shima ya d'an huta.
Bai musa ba kuwa washagari da hantsi ya dauke ni da jakar kayana ya kai ni gida. Har da siya mini su maltina da madara da indomi da zan dan yi kwanaki ina ci. Wanda na tabbatar ya ha'da da bashi.
Da k'yar na shiga muka gaisa da Dada wacce bayyana farincikin da ta yi a dalilin samuwar cikin bata lokaci ne.
Ya kira Ikilima ta ri'ke ni zuwa cikin gida. Na sani kuma dan ya mutunta iyayenmu ne ya sanya bai ri'ke ni da kansa ba.
Yadda Tijjani ya ha'do ni da shirgi da maganganuwana. Sai ka rantse har cikin zuciyarsa yake nufin na zo na yi goyon ciki a gida.
Kwana na biyu a gida na fara samun sau'ki tamkar a gidana ciwon yake. Domin ina barci, da safe kuma ina shan koko na ci dumame.
Sannan Gwaggo da kanta take daddana mini jikina. Har gasa mini jiki take yi da tawul. Ga shi duk abubuwan da nake son ci na gargajiya ina samu.
Kwatsam ranar da na yi kwana uku sai ga shi ya ce shi ya gaji da rashina sai dai mu koma gida.
Na tubure akan sai na ji k'warin jikina.
Shima ya kafe. Kuma wai ni ce zan ce ina son komawa gidana.
Nan da nan na rantse akan bazan fa'da ba.
Ya jijjiga kai ya ce "Shike nan tunda babu taimako da fahimta a tsakaninmu. Ni zan fa'da wa Baban akan na gaji ina son ki koma dakinki. Dama kunya da nauyinsa ne suka sanya na kawo ki."
Da yamma ya dawo akan na taimake shi mu koma gida. Ya kasa fa'dawa Baban zai tafi da ni. Na ce "Ni dai na fi son zaman nan".
Nan da nan ya tunzura ya ce "Saboda bani da ku'di ko Asiya?"
Na kalle shi a razane. Ya ce "Haka ne mana. Inba hakan ba wace ce ta taba zuwa gida dan bata da lafiya a gidan nan?"
Na ce "Ubaida bata dawo ba?"
Da hanzari ya ce "Amma duk jinyar da ta yi da ciki ai bata dawo ba. Sai da ta haihu. Ke kuwa ai ba haihuwa kika yi ba. Idan ba gazawa ta aka ga ni ba. Mene ne zai sa ayi mini wannan umarnin?"
Na sake kallonsa cikin tu'ajjibi na ce "Baban Marina kake fa'dawa hakan ko kuwa wa?"
A tunzure ya ce "Asiya na ke fa'dawa saboda ita ce zata ce masa ta samu sau'ki."
Idona ya ciko da hawayen takaici na ce "To".
Daga hakan na k'ulle bakina ban ce masa komai ba.
Ganin hakan sai jikinsa ya yi sanyi. Ya ce "Ya muke ciki?"
Ko kallonsa ban yi ba.
Ya gama zamansa ban sake kula shi ba.
Da daddare ma ya dawo, ban yarda na kula shi ba. Domin idan akwai abin da yake b'ata mini rai da shi idan muna magana ya dinga sako babun shi ne. Na kuma lura idan ban taka masa birki ba, ba wanye wa k'alau zamu yi ba. Tunda yana nema ya mayar da ita sara.
Washagari sassafe sai ga Babah ta Bulkachuwa ta dira a gidan. Ina daga daki na ji suna gaisawa da Baba. Ya ce " Hauwa kamar ba kwanaki ka'dan da suka shud'e kika zo duba y'arki ba. Me ya sake dawo da ke kuma yanzu? Mata kuna da son sabgar yawo.
Ta ce "Ba hakan ba ne Yaya. Shi ne ya mini waya wai jikin Yabi ya yi tsananin da ka ce ya dawo da ita gida. Sai ya ro'ki na zo na zauna masa da ita. Ni kaina hankalina ba kwanciya zai yi ba idan ba zuwa na yi na ganta ba."
Baba ya numfasa ya ce "Ai shi Tijjani bai gamsu zan kular masa da iyali dan karan kansa ba, sai ya zargi na yi masa fin k'arfi saboda y'ata ce?".
Ta diriri ce ta ce "Haba Yaya ni Wallahi har kasa na ji babu da'di."
Ya ce "To ki ji mana. Ban da dai ke ma kin banbanta ta ya ya zaki zo ki ce mini "Zaki dauki matar Tijjani a gaba na?"
✍️
[10/4, 5:26 PM] +234 806 878 8989: *Dandano*
*DAGA Littafin BAK'AR TA'ADA*
*NA SURAYYA DEE*
*MARUBUCIYAR HALIN YAU DA SABO DA KAZA*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GICSrs9TfxG1Q6FUXiu1Qg
*Ina tallata muku make up artist din Guduyo*
*Aisha Lame mai kayan kwalliyar yan gayu*.
*Jakadiyar oriflame, duk wani nauyin kayan oriflame tana kawo su cikin farashi mai sau'ki*.
*Ba iya kayan kwalliya masu daraja ba, ita din GWANAR sarrafa pop corn ce(gugguru), ni shaida ce ta hakika*.
*Sannan tana da spices kasaitatu. Masu mayar da girki ya zama na alfarma*
*07036662633*.
*INA SANAR MUKU ZAMU BUGA LITTAFIN KANA NAKA ZUWA HARD COPY*.
*MASU BU'KATAR MALLAKAR NASU SU TUNTU'BE NI, KO SU TUNTU'BI MARUBUCIYA JANAFTY*.
*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*.
Na gama komai na kai falo kamar yadda na saba. Shi kuma ya zama mutum mutumi.
Na fito na ce "Ga abinci ko sai ka dawo daga masallaci?"
Ya zuba mini ido ya rasa abin fa'da.
Ya tashi ya ce "Da sauran lokaci ai."
Na zuba mana kamar yadda na I'm. Amma gaba'daya mun kasa ci sai faman juya shi muke yi.
Gara ni na ci loma biyu na ji mak'oshina ya cushe na ajiye. Shi kuwa yama kasa kai wa ba'kin nasa.
Ya gaji ya kalle ni ya ce Dan Allah Yabi ki yi ha'kuri, ki yafe mini".
Ba ja in ja na ce "To".
Daga haka kuma ban sake ce wa komai ba. Ya yi maganganu na ban ha'kuri da nuna nadama masu yawa amma ban ko kalle shi ba. Aka kira sallah ban yarda na bu'de baki mun yi magana kamar yadda yake fata. Ya yi alwala ya tafi masallaci.
Har muka haramar kwanciya ban bu'de baki na ce k'ala ba. Duk jaye-jayen maganarsa kuwa. Da muka kwanta ya fara lalubata ban hana shi ba, amma ko kwakkwaran motsi ban yi ba. Ya yi duk abin da zai yi dan na motsa ko na mayar masa martani amma tamkar an shuka dusa.
Ya gaji ya koma ya kwanta yana fa'din "Innalillahi wa ilaihir rajiun" .
Ya ru'ko ni da rawar murya ya ce "Yabi ki yiwa Allah, ki bu'de baki mu yi magana".
Yana rufe baki na ce"To".
"Asiya ki yi ha'kuri, ki yafe mini, dan Allah, dan Annabi, ki yafe mini".
Na yi shiru. Ya sake ce wa Bansan me ya same ni ba Yabi. Dan Allah ki mini uzziri ki yi ha'kuri ki gafar ce ni".
Nan ma na ce "To".
Ya yi iya ban hakuri, amma ban yarda na ce komai ba.
Da gari ya waye da wuri ya dawo daga masallaci ya hau hidimar gyaran gida.
Ya yi abin karya wa. Har d'aki ya kawo mini amma ina ci sau daya ban sake kai wa na biyu ba, na ce na koshi. Ya yi shiru ya rasa yadda zai yi.
Bai fita ko ina ba. Yini aka yi ana zuwa lalle amma ban iya yiwa ko mutum daya ba. Sai ha'kuri nake basu tare da uzzirin cewa bani da lafiya ne.
Hakan da ya ga ni ya sake rib'anya tashin hankalinsa. Domin yasan yadda nake matu'kar son sana'ata. Bana son abin da zai hana ni yin lalle ko kitso.
Amma da bakina nake sallamar mutane yasan al'amarin da yake zuciyata ba k'ank'ani ba ne.
Kwanaki uku muna cikin wannan halin. Daga ni har shi, mun yi matu'kar rame wa tunda bama iya cin abinci ga rashin nutsuwar zuciya.
Ya yi juyin duniya mu yi magana na ki, domin har yau ban yarda na yi masa korafi ba. Komai kuma zai ce sai na amsa da "To". Kullum safiya zan gaishe shi, zan kuma amsa sallamar sa idan ya shigo. Daga hakan kuma bazan sake yarda na ce komai ba. Rashin yin lallen har zuwa lokacin ya fara ta'bamu tunda shi ma baya iya fita, ko ya fitan ma baya nisan kiwo zai dawo.
Ranar da aka yi kwanaki biyar da faruwar al'amarin, ya zauna ya bani hakuri tamkar yawun bakinsa zai k'afe. Har da k'wallarsa. Amma ban ce komai ba, sai ma murmushi mai ciwo da na yi na ce masa "To me ka yi ne?"
Duk da k'arancin shekaruna amma na fahimci shirun da na yi masa ba k'aramin dafa shi take yi ba. Ba abin da yake so irin na yarda mun yi magana ko da rashin kunya ne na yi masa. Amma ban yi hakan ba. Ni a karan kaina so nake na yi kuka, na caccaba masa maganganun da zasu gasa masa zuciya tamkar yadda ya yi dalilin da tawa zuciyar take gasuwa, amma na kasa.
Tsawon sati guda muna cikin wannan matsanancin halin, daga ni har shi mun zama wasu iri. Gidanmu ya koma tamkar na zaman makokin mutuwar uwa mahaifiya.
Sannan na k'i yin k'unshi har lokacin. Al'amarin da ya sake damalmala mana komai.
Shi kam kawai k'arfin halin da aka san maza da shi ne. Amma kana kallonsa kasan yana dandanar kudarsa da shiruna. Yadda bana cin abinci haka shi ma baya ci. Gara ma ni da daddare na kan yi barci, amma shi duk juyin da zan yi zan gan shi kan sallaya ko yana zaune ko kuma yana sallah.
Da asuba ya dawo ya tarar har na koma na kwanta.
Ya zauna a bakin gadon. A sanyaye ya ce "Yabi wai a haka zamu rayu ne? Bazan iya wannan rayuwar ba. Ki yiwa Allah da ma'aiki ki bu'de baki ki fa'di duk abin da kike so. Na ro'ke ki ba dan ni ba, da Allah nake ha'da ki."
Ko motsi ban yi ba. Bare na tanka masa.
Ya tsananta da magiya. Sai kawai ji na yi cak ya dauke ni ya yi nufin d'ora ni kan cinyoyinsa. Ai gaba'daya wani irin k'arfi mai tattare da matsanancin fishi ya taso mini. Da dukkan zuciyata na fisge na ingiza shi ya fadi k'asa warwas.
Na dinga huci mai zafi, amma na kasa bu'de baki na yi magana.
K'irjina sai harbawa yake yi da tsananin gaske.
Ya mik'e ya kafe ni da ido, cikin kad'uwa da tashin hankali. Ya ce "Dan Allah bu'de baki ki yi magana. Fadi me zaki ce, idan kuma na zauna ki mini duka zai fi mini akan irin halin da nake ganin ki, ki yafe wa mijinki, ki yafe wa masoyinki, ki yafe mini, kaddara ce ta hau kaina Asiya".
Na juya na kwanta ba tare da na ce uffan ba.
Kukan kuma bai zo ba.
Ya kasa hakuri ya sake biyo ni inda nake kwance ya hau lalubata, ban hana shi ba, ban kuma yi wani yun'kurin da zan tankwabar da shi ba. Ya yi abin da zai yi. Yana gamawa na lalubi zanina na daura na fice.
Wanka na yi, sannan na dawo na kwanta. Bayan na mulke jina da hadadden man oriflame. Wanda jakadiyar kamfani ce ta za'ba mini shi fa kanta, q cewarta shi zai fi dace wa ta tarar fatata.
*Kunsan dai Aisha Lame make up artist din Guduyo ce. Yanzu ma bata bata bar fatar Yabi babu gyara ba*.
*Kun tandadi fame wash din nan kuwa da na yi ta jaddada muku muhimmancinsa a wajenku?*
*Ku tuntu'be ta a wannan lambar dan samun sabbin kayanta masu kyau da farashi mai sau'ki da ya zarta na saura*.
*07036662633*.
Shi kuma yana kwance sai fa'din "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya ke yi da k'arfi.
Yau duk jarumtar sa kasa yin ayyukan gidan ya yi. Dan haka na yi abuna. Na yi abin karyawa har na gama yana kwance. Na d'aga labule na ce "Ka zo mu karya."
Yana daga kwancen ya ce "Ko na zo d'in ma ai ba ci muke yi ba. Ki yafici abin da zaki ya fita ki rufe".
Wasa wasa yana kwance har azahar, ko wanka bai fito ya yi ba. Abin da