Showing 117001 words to 120000 words out of 131968 words
yanke shawara shine na siya miki ita a matsayin gift din first night dinmu Allah yasa banyi laifi ba?"
Ya fada yana rausayar dakai wani tsalle tayi ta rungume tana dariya tace “wow mijina Allah yayi maka albarka na gde sosai Allah ya barni tare dakai komai ka hada My D.S wlh kayi a rayuwa...” rufe mata baki yayi da sauri yace “nine me gdy da gimbiyar mata ta yarda zata rakani a cikin rayuwata ta amince dani a matsayin miji harta yabawa qwazona bayan an kusheni wasu ma suna cewa bazan iyaba saboda tayi rayuwa da kharijin namiji...." Rufe masa baki tayi tana girgiza masa kai tace “muyi abinda ya shafemu D.S banason tuna abinda ya wucce nidai kayimin kuma zan rayu dakai da zuciya daya wlh Sulaiman bantaba sanin asalin sex yanada dadi ba sai a gurinka ni a rayuwata dadin romance kawai na sani amma duk da haka idan nace maka banason dan'uwana nayi maka qarya saboda haka kadaina kawo min mgnrsa plz tayar min da hankali zaka keyi"
Share hawayen fuskarsa yayi da sauri matarsa tana iqirarin tanason wani ajiyar zuciya yayi yace “zan rabaki da son nasa ma ki tsaya a iyakae tausayinsa kadai" murmushi tayi masa shima yayi sukasa kayansu wayarsa tayi ring ya dauka Mommy yagani yayi murmushi ya kara a kunnensa yace “Allah yaja kwanan Mommy na fatan kin tashi lfy cikin aminci" murmushi tayi tace “lfy qlau babana ya kwanan amarya" kallonta yayi ya janyota jikinsa yace “Alhmdllh Mommy amarya tayi sosai saidai fatan dorewar zaman lfy da zuri'a ta gari” murmushi Momy tayi tace “masha Allah naji dadi bata mu gaisa" kara mata wayar yayi cikin in...Ina tayi sallama Hajiya Sa'adatu ta amsa da cewa.
“Yata kin tashi lfy ya kwanan baqunta" a kunyace tace “lfy qlau Mommy ya gajiyarku?" Amsawa tayi da “gajiya ta biya ai tunda burin babana ya cika Umaimatu naji dadin samunki a matsayin suruka kin samu yabo da shaida me kyau babu abinda da yake boyayye a gurinmu iyayenki sun sanar damu komai tun kafin munafukai su fada mana kuma munji mun gani mun yarda saboda munsani komai yana faruwa ne bisa turbar qaddara ko badon komai ba don maraicinki munyi alqawarin riqeki amana insha Allahu bazaki taba nadamar shigowa cikin zuri'ar Alh Kabir Yola ba Umaimah ga babana nan Sulaiman bawai donna haifeshi ba aa iyakar gsky ta nake fada miki Sulaiman bashida matsala kuma yana sonki qaddarar ku hadu ce tasashi zuwa course Skyline University so alhmdllh ko yanzu mu skyline ta biyamu Umaimah ki riqemin amanar babana yanada sanyin hali hqr da kawaici kuma yanason farin cikin duk wanda yake tare dashi bai yarda ya cutar da wanda yake qarqashinsa ba gara shi ya cutu yana da rauni akanki Umaimah ki tausaya masa ki zauna dashi da tsarkakkakiyar niyyah insha Allahu zakiyi alfahari dashi ki huta sosai yata kuma ki kula da mijinki masoyinki ne Umaimah bashi kadai na haifaba su hudune maza sai mata biyu shine dana na uku amma nafi jinsa a raina saboda rauninsa da hqrnsa tunda nake da Sulaiman tsayin shekaru 33 baa taba kawomin qararsa ba"
Tunda Hajiya ta fara mgnr take hawaye shikuma yana share mata a ranta tace “wadannan wadanne irin mutane ne karamci da sanyin halin D.S na mahaifiyarsa ne" ajiyar zuciya tayi tace “na gde Mommy insha Allahu bazan baku kunya ba" fadada fara'arta tayi tace “na gde yata Allah yayi muku albarka yabaku zuri'a ta qwarai" sukayi sallama ta miqa mass wayar ta kuma cewa dashi “kar naji karna gani babana ka riqe amanar daka dauka aure badon dadinsa kawai akeyinsa ba kuma kazama jagora na gari a gdanka ka zamo adalin shugaba wanda iyalinka zatayi alfahari dashi a koda yaushe Allah ya kade muku fitina kace mata nace ta huta zan turo driver ya kawo muku breakfast yanzu”
Amsawa yayi da “to mun gode Mommy Allah ya qara girma" yana kashe wayar ya dorata kan bedset drower ya dagata cak ya fita da ita zuwa parlourn ya bude qofar parlourn suka fita saida yakaita filin motsa jikin da aka tanada a gidan aka zuba masa kayan motsa jiki kala² sannan ya sauketa ya fara tsallen tsalensa na motsa jiki tana kallonsa sun dauki minti ashirin sannan driven yazo yaje ya karbi kwandon da aka jero musu abincin ya sallameshi ya tafi ya shigar dasu parlourn ya jera a dinning sannan ya dawo ya kama hanunta suka shiga ciki suka zauna sukayi breakfast dinsu duk wani motsinta akan idonsa yaqi yarda ya dauke idonsa akanta saidai idan suka hada ido yayi mata murmushi tare suka shiga kitchen suka wanke kayan da suka bata sannan yajata suka koma daki suka yaci gaba da lalubeta sunata bawa flowers dinsu ruwa a ranar saida D.S ya kusanceta sau hudu amma babu wanda ta jigata saboda yana amfani da dabarun da bazataji a jikinta ba kuma baya dadewar da zata wahala baya wucce awa daya da rabi zuwa biyu kuma idan yanayi ya rinqa tausarta da dadadan kalaman da dole ta sallama masa.
*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/2, 12:52 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_GU_*
Haka rayuwa taci gaba da tafiya tsakanin ma'auratan cikin so kulawa da tattalin juna D.S ya shardantawa kansa kullum zai kira Daddy a waya ya tambayeshi jikin Hameed itama tana kiran Daddy sosai ta tambayeshi yakanyi mata nasiha da riqe mijinta amana yakan nuna mata sa'ar mijin da tayi nutsuwa hankali da dattako so tari yakance “uwata yanzu kikayi auren da hankalina ya kwanta Umaimah Hameed danane amma zuciyata taqi nutsuwa da aurenki dashi saboda nasani yafi qarfinki cutar dake yake a mu'amala irinta aure amma ke kinkasa gani kiyi hqr ki cireshi a ranki ki zauna da mijinki lfy kuma kiyi hqr"
Idan ya fada mata haka takan yini tana kuka amma takanyi iyakar qoqarinta ta boye damuwarta a gurin d.s saboda tasani idan yaganta cikin damuwa yakan fita shiga damuwar haka rayuwar taci gaba da tafiya cikin so da tattalin farin cikin juna.
*************************
A bangaren Hameed kuwa saida yayi wata biyar a asibitin yana karbar magani sannan ya farfado Daddy ba qaramin farin ciki yayi ba da samuwar lfyr dan nasa haka yaci gaba da samun kulawa har saida ya warware sosai a wannan lkcn ne kuma suke hira da Dr Ammar likitan dake kula dashi yake fada masa matsalarsa ta sex abuse ya tausaya masa sosai yace masa dama ana samun haka idan mutum mabuqaci ne kuma ya kasa samun kulawa tun farko ya rasa macen da zata iya daukansa akwai wani sinadari da yake sauka cikin jininsu ya rinqa bawa jijiyar mazakutarsu matsalar da zasuke fita daga hayyacinsu idan suka buqaci mace wasu sukan rasa rayuwarsu saboda ciwon cikin da zasu rinqa fuskanta ko wanne lkc wasu kuma hakanne yake sanyasu su kasa control din kansu idan sukaga mace kawai su afka mata wannan dalilin yana haifar da afkuwar fyade sosai a cikin al'ummah masu dama dama kuma sukan fada neman matan banza baji ba gani saboda kiyaye kansu daga hallaka.
Dafashi yayi yace “kayi hqr Abdulhameed kuskure ne na rashin fahimta da kuma qaddara yasa komai yaita faruwa a rashin sani amma komai ya kusan zuwa qarshe zakayi aure ka sadu da iyalinka kaji dadi ba wahala ba don s baya ba dadin sex kasani ba wahalarsa ka sani tunda zaka kwana kana kusantar mace batare da tana tayaka ba tama fita daga hayyacinta zan doraka akan wasu magunguna kuma zan hadaka da wani kakana likitan gargajiya ne akwai wani mutum da yataba zuwa da irin wannan matsalar shekaru uku da suka wucce yayi masa magani ya samu sauqi amma zaka zauna a gurinsa harsai komai ya zama normal"
Baiyi musu ba saboda a yanda yakeji jiyake dama zaa iya kashe masa sha'awar gaba daya ya huta idan ya tuna bloody dinsa tanacan tana rayuwa da wani namijin kawai sai yaji zuciyarsa tana tafasa hawaye nabin kuncinsa damma ya dage wajan addu'a da neman zabi da sauqi gurin ubangiji yana kuwa samun sauqin sosai duk da yasani son Umaimah bazai taba barin jininsa ba domin dashi aka halicceshi.
Hakan kuwa akayi ana sallamarsa daga asibiti yayima Daddy bayanin komai ya bashi goyan baya har dashi suka tafi qauyen Ghabriel garin da kakan Dr Ammar yake suka samu karamci sosai sukayi masa bayani ya cajeshi tsaf sannan ya dorashi akan magani ya fada masa zaiyi wata biyu anan baija ba saboda bama ya buqatar zaman 9ja din kwata² yana karbar maganinsa yana warwarewa sosai.
Watan auren Umaimah da D.S bakwai lkcn tanada cikin wata biyar sosai d.s ya dauki so da qaunar duniya ya dorawa cikin jikinta bashi da mgn sai tasa a lkcn kuma tana 300 level a jami'a tare suke fitowa kullum kowa yana yabawa soyayyarsu da kulawar da yake bata a lkcn ne kuma wata qaddarar ta fado rayuwar Ahlin Hameed Shuwa ranar wata juma'a Hajiya tana kitchen tana girki Nihal da Shurafah suna kitchen din suna wasansu saboda Maliha da Shuraif suna gdan Aunty Zarah kawai sai aka kira Hajiya a waya bisa tsautsayi ta fita tabar yaran a kitchen fitarta keda wuya Gas din yayi wata bindaga gobara ta tashi ta kama wani bangare na gdan ihu Hajiya ta rinqayi tana salati daqyar yan kwanakwana suka kashe gobarar amma abubuwa da yawa sun qone a gdan harda asarar rayuka biyu Nihal da Shurafah.
Wannan mutuwa ta girgiza mutane sosai Daddy ne ya hana a fadawa Hameed ita kuwa Umaimah sai Mijinta aka fadawa shine yaje ya daukota ya kawota gdan tun daga qofar gdan tasan wani abu ya faru gabanta ya yanke ya fadi tayi baya luuuuuu zata fadi yayi saurin tarota amma ta suma nan fa hankali ya dawo kanta ya dauketa shida Hajiyansa da aunty Zarah suka tafi Asibiti bayan wani dan lkc ta farfado tana tashi ta riqe hanunsa ta fashe da kuka tace “don Allah Sulaiman kada kacemin Abdulhameed ya mutu zuciyata bugawa zatayi..." Rufe mata baki yayi yace “ai dama na sani nasan tunaninki kenan to ki kwantar da hankalinki bashine ya mutu ba..." katseshi tayi da cewa “to waye waye ya mutu D.S?" Share hawayen idonsa yayi yace “Nihal ce da..." Saikuma yayi shiru daya tuna irin son da takewa Shurafah kullum burinta akan Shurafah ya qare katse masa tunanin tayi da cewa “dawa kuma D. S?"
Janye hanunsa yayi daga nata ya fice daga dakin da sauri Aunty Jameelah tace “kunyi Mata shuru ai dolene ta sani Umaimah hqr zamuyi Allah ya karbi rayuwar Nihal da Shurafah jiya da magaruba sakamakon gobara da sukayi a kitchen kiyi hqr Allah zai mayar miki da wadda tafita” ajiyar zuciya tayi tana kallon Aunty Jameelah tana furta “Innanillahi wa innah ilaihir raji'un” iyakar abinda take furtawa kenan har zuwa yamma da D.S ya dawo likitan ya sallameta suka tafi gdan rasuwar ta wucce akayi zaman uku da ita taso tayi kwana bakwai amma ya hanata yace ta dawo ana gobe bakwai din.
Haka kuwa akayi ana gobe bakwai da kansa ya kawota tunda ta shigo unguwar taji gabanta yana faduwa hakadai ta daure ta rinqa yi masa yaqe suka fito yana riqe da hanunta saboda cikinta yayi nauyi da girma sosai kamar yakai wata tara bayan yanzu ne ya shiga na takwas tana daga qafarta daqyar suka shiga parlourn yanata zuba mata sannu yana riqe da jakarta dagowa sukayi a tare idonsu ya sarqe da juna taja baya da sauri ta shige jikin D.S inda shikuma ya miqe da sauri yana nunata da yatsa yana kallon cikinta yace “Blo... bloody ciki......."
*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[2/2, 8:49 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *_GU_*
Yana fadin haka ya nufi qofa da sauri ya fice daga dakin ko hanun da D.S yake miqa masa bai kulaba wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata ya kamata ya zaunar da ita yace “to ya isa haka kinsan banason kuka ko?" qoqarin tsayar da kukan ta farayi daqyar ta tsayar da kukan yayi murmushi ya miqe yace “zanje gda ke sai yaushe?" Qasa tayi da kanta tace “jibi" kallonta yayi da sauri yace “aa gobe dai" batayi masa musu ba ya juya ya fice bayan sun gaisa da mutanen dake dakin sai lkcn ta samu damar gaisawa da kowa ta miqe da qyar ta shiga dakin Hajiya ta kwanta tana tunanin Uncle dinta zuciyarta na fada Mata ta tashi tabishi taje taga halin da yake ciki amma saita dake kawai tayi kwanciyarta har dare ya fara ta fita ta koma parlourn Aunty Zarah ce kawai saboda Aunty Jameelah tun uku ta tafi sai Hajiya Kaka da maqota dayake aikin abincin sadakar duk kwangila suka bayar suna zaune har sha daya sannan kowa yaje ya kwanta itama kwanciyar tayi amma zuciyarta taqi hutawa koda D.S ya kirata ma daqyar ta daga tace masa bacci takeji sukayi sallama ta aje wayar tanata karanta wasiqar jaki ranar daga ita har Hameed babu wanda ya rintsa shi gani yake Umaimah taci amanarsa data yarda wani ya kwanta da ita harma yayi mata ciki wannan ciki ya tsone masa ido da yasan mugun ganin da zaiyi kenan da bai dawo 9ja ba yanda yakejin ciwon abinda ya gani a jikin Umaimah bayajin ciwon mutuwar yaran nasa haka saboda yasan su lkcnsu ne yayi amma ita ta manta da halaccin da yayi mata taje ta bawa wani kanta yanzu abinda yakeji a jikinta shima Sulaiman abinda yakeji kenan?
Wani kishi ya taso masa daqyar ya rinqa danne zuciyarsa da qarfin addu'a.
Washe gari akayi sadakar bakwai basu hadu da Hameed ba harta gama zamanta a gdan D.S yazo daukarta ta hado shirginta ta fito yana yana riqe da hanunta yana zuba mata zance tana dariya Hameed din ya shigo a motarsa sabuwa dal yayi parking duk da batasan shi bane amma saida gabanta ya fadi ta kalli motar sosai jikinta yana bata na cikin motar ita yake kallo.
Ilai kuwa itadin ya zubawa ido yanajin wani abu yana tasowa qirjinsa zuciyarsa tana tafasa yanda suketa dariyarsu da Sulaiman din yana jamata karan hanci har kuma dan jaraba irin tasa ya kasa daina kallonsu yana qara tsinewa Salma data zama sanadin rabashi da farin cikinsa qiri² Umaimansa tafi qarfinsa yanason yaga ya cireta a ransa amma ya kasa hukunci ya yankewa zuciyarsa na barin qasar gaba daya dama ya samu aiki a World Bank of America da yace bazashi ba amma yanzu dole ya hada komatsansa ya tafi can qila ya samu sauqin rashinta saboda yasani Umaimah batada ta biyu a gurinsa har yau idan ya kwanta tunanota yakeyi da irin sadaukarwarta ga farin cikinsa.
Buruka da yawa daya dauka akan rayuwarsa da bloody dinsa yanaji yana gani sunbi ruwa wai yau bloody dinsa ce da cikin wani a jikinta har tana ganinsa tana razana to meye ma ya razanata dashi? Tambaya ce da bashi da amsarta tashin motarsu ne ya dawo dashi hayyacinsa ya buga kansa a sitiyarin motar tare da dukan qirjinsa yana kiran “ya rabbih" yana hawaye masu zafi yace “Allah Kaine ka halicci zuciyata da son baiwar nan taka Allah kasani bani na dorawa kaina ba kaine ka jarrabeni Allah ka ciremin ita a raina Allah meyasa kullum ina roqonka kamar baka amsawa Allah banaso ka kamani dason matar wani kafi kowa sanin banida qarfin raba zuciyata da ita a jinina take yawo" bude qofar motar da akayi ne yasashi dagowa da idanunsa da har sun dafe saboda kunan zucci ya zubasu akan Yusuf yayi murmushi don yasan kukan me yake Hameed bashi da damuwar data wucce Umaimah a rayuwarsa gashi Umaimah tayi masa nisa.
Dafashi yayi yace “mutumin ya kamata ka cire bloody dinnan taka aranka ka nemi wata yar baby ks aura ka qarasa rayuwarka da ita" wani kallo ya watsa masa wanda ya tilasta masa rufe bakinsa jikinsa har tsuma yake saboda bala'i yace “waikai anyama kuwa kasan meye so a rayuwarka Yusuf to bari kaji idan baka sani ba ka sani inasonta kuma ina fatan na mutu da soyayyarta wlh nayiwa zuciyata alqawarin bazan sabawa farin cikinta ina sani ba Umaimah tana sona jiya nagano soyayya ta da tausayina har yanzu a cikin idonta Maliha ta fadamin tun jiya take tambayarta Ina Ina me nakeyi har turowa tayi tazo taga lfyta Umaimah tana kishin ganin nayi tarayyah da wata mace saboda haka bazanyi ba har abada zan hqr na rinqa azumi har zuwa lkcn da Allah zai yankemin ya kawomin mafita amma bata hanyar aure ba na hqr da aure har abada indai bada bloody bane kuma koda banda rabon sake aurenta inason na mutu da soyayyarta saboda itama nasan da tawa zata mutu wlh Yusuf na tsani mutumin nan da yake ganin kansa wai mijinta kayyy! kayyy!! kayyy!!! badai miji ba dan riqon qwarya wai harma ciki yayi mata kuma ma harta kusa haihuwa"
Ya mgnr yana dafe kansa yana jan zuciya yace “babu komai qaddara ce da kuma rabo wannan kadai ya isheni ishara" ajiyar zuciya Yusuf yayi cikin tausayin abokin nasa yace “kayita addu'a Allah yana sane dakai zai kawo maka mafita yawwa kaji kuwa cewa matarka tana gdan mahaukata?" Dagowa yayi da sauri yace “wa kenan?" Murmushi yayi yace “matarka data rabaka da kowa kaqiji kaqi gani matarka data rabaka da farin cikinka jiya nake samun lbrn ta haukace sai tonawa kanta asiri take har tana fadin yanda tayi ta rabaka da Umaimah da bayan ka daketa ka saketa komawar da tayi akan a haukata Umaimah yanda bakai ba wani ma bazaiyi sha'awar rayuwa da ita ba taje ta hado abinta tazo tayi ita kuma Umaimah tayi aure wannan dalilin da kuma addu'a sune suka mayar Mata da abinta kanta" qwafa yayi yace “narasa me muka tsarewa mutane kowa yake nufin mu da sharri Allah shine muka dogara dashi kuma shine abin dogaron bloody" yana mgnr yana dafe qirjinsa yace “bani maganina nasha qirjina ciwo yakeyi"
Haka sukayi sallama Yusuf ya tafi kwanaki biyar tsakani ya gama dukkan shirye²nsa ranar daya cika sati da dawowa daga India ya shirya sai birnin California na qasar amurka inda suka bashi katafaran gdan zama da zundumemiyar mota da matsayin me girma a world Bank.
*******
Sati hudu da rasuwar su Shurafah Umaimah ta haifo yaranta biyu mace