Showing 21001 words to 24000 words out of 131968 words

Chapter 8 - GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL BY UMMUH HAIRAN

10 Jul 2024

22464

ukuna Uncle ka cuceni ka cutar da rayuwata kamarni ace wai inada cikin shege a jikina Ina wlh saina zubar dashi bazai taba yuwuwa ba...” haka taketa surutai kamar wata zararriya ta riqe masa qwalar riga qamqam.


Daqyar ya samu ya banbare hanunta daga wuyansa ya fara qoqarin janyota jikinsa ta kuma janyewa tare da fashewa da kuka tace “wai kai wanne irin azzalumi ne ka cuceni ka rabani da mutuncina sannan harda guzurin ciki ya kakeso nayi Uncle wanne irin zagi kakeso duniya tayimin...”kamota yayi ya hadata da jikinsa sosai cikin tsananin kaduwa da yanda ta haukace masa yace “kiyi hqr Babyn Uncle wannan cikin shine matakin nasarar mu ta kasancewa tare saboda haka kada ki zubar min dashi ki taimakeni ki barshi muci gana da rainonsa wlh tallahi Baby dana ba shege bane halattacen dane kamar kowanne nasha fada miki niba mazinaci bane kedin matata ce ki bani lkc kadan zanyi miki bayanin komai kuma zan tabbatar miki da komai” duk yanda yaso lallashinta taqi lallasuwa ganin batada niyyar daina kukanne yasashi komawa ya kwanta yace “duk sanda kika gama batawa kanki lkcn kizo ki bani haqqina da kika danne min tsayin kwanaki”


Kallonsa tayi a tsorace ta maqalqale jikinta tana sake rushewa da kuka blanket yaja ya rufe jikinsa tare da kashe light din dake dakin ya lalubo ya janyota da qarfi ya mannata da jikinsa yana sakin wata sansanyar ajiyar zuciya ya sanya hanunsa ya dafe kanta tare da dora bakinsa a nata yana lasar lips dinta haqoranta har rawa suke saboda tashin hankali da tsoro hanunsa daya yasa yana shafa cikinta yana wani lumshe ido kafin daga baya ya gangara qasan mararta yana shafawa a hankali yana tsotse lips din nata kamar zai tsinkesu har yanzu kuka takeyi masa tana ta tureshi tana wani irin kakarin amai saboda bata qaunar turaren jikinsa tayar mata da zuciya yakeyi sosai jin yanda take yunqurin amanne yasashi janyewa daga jikin nata ta miqe da gudu ta shiga bathroom din ta fara kakarin aman amma babu komai a cikinta yaqi zuwa sai azabar tashin zuciya miqewa tayi ta kuskure bakinta tare da daukan sabon brush din da yake gurin ta bare ta wanke bakinta ta juyo zata fito a qofar toilet din ta ganshi tsaye dagashi sai boxes yacire duk wata sutura dake jikinsa gabanta ya fadi sosai ganin ya ruqo hanunta yana qoqarin hadata da jikinsa kawar dakai tayi cikin galabaitacciyar murya tace.


“Don Allah ka qyaleni banason turaren nan na jikinka tayarmin da zuciya yakeyi” murmushi yayi me sauti yace “oh turare nane matsalar?” kawar da kanta tayi ya cafkota yana shafa cikinta yace “sorry yarona daga yau bazan qara sawa ba tunda bakaso amma yau daya ayimin uzuri rashin sani ne”yana fadin haka ya dagata cak ya dorata a gadon ya fara qoqarin zare mata rigar jikinta ta riqe ta hanunta tasa sabon kuka me taba zuciya tace “ka taimakeni ka rabu dani Uncle banaso wlh banaso Uncle Hameed pl...” kallon da yake matane yasata hadiye mgnr ya balle bottle din gaban rigar ya cire mata ita ya kama twince dinta ya fara wasa dasu tare da qura musu ido yanda suke wani sheqi.


Cafka yayi ya fara wasa dasu cikin wani irin yanayi da yake nuna tsananin feeling dinsa duk yanda take masa kuka da magiya yaqi sakinta saboda bazai iya qyaleta a matuqar matse yake hakanan ya biya buqatarsa da ita yanajin wani mugun farin ciki dadin Babyn Uncle dabanne a cikin mata duk yanda ya debo sha'awar sa da ya kusanceta zaiji ya gamsu rungumeta yayi yana bubbuga bayanta cikin sigar lallashi yana busa mata iska a kunnenta baccine ya dauketa ya janye jikinsa a hankali saboda tsoron kada ta tashi ya shiga toilet yayi wanka ya dawo yayi sallar isha ya fita restaurant din cikin hotel din ya nemo musu abinci ya dawo yaci saboda yunwa yakeji sosai yau feeling din da yakeji bai bashi damar iyacin abinci ba sai yanzu a dole yakecin abincin saboda tsarinsa bayacin abincin waje idan ba dole ba.


Bata farka ba sai sha biyu na dare ta bude idonta jinta qamqam a jikinshi ne yasata janye jikinta ta miqe ta nufi bathroom din tayi wanka ta fito a zaune tayi sallar isha saboda jirin da takeji yana kallonta harta gama ya bude idonsa ya kafeta da idonsa ganin yanda ta hade kai da gwiwa tana shassheqa kuka miqewa yayi ya sauko kusa da ita ya kamo hanunta ta dago kanta yayi murmushi yace “duk kukannan akan cikina dake jikinki ne to don Allah kiyi hqr nayi laifi amma inason baby na ki kulamin dashi” wani mugun kallo ta rinqa watsa masa bai kulata ba ya dauki abincin ya rinqa bata a baki da farko qinci tayi saboda tasan ba zama zaiyi ba amma ys dage saida ya bata ta rinqacin sakwarar daqyar saida yaga ta fara qoqarin mai sannan ya qyaleta ta miqe da sauri ta nufi bathroom din duk abinda taci saida ta dawo dashi hankalinsa ya tashi sosai da ganin yanda ta galabaita tana gama aman ya daukota ya dawo da ita ya rufe mata jiki da bargo ya saboda rawar sanyin da zazzabin daje jikinta yasata wayarsa ya dauka ya kira likitansa ya sanar dashi inda yake da abinda ke faruwa cikin saa kuwa a asibitin Abdullahi Wase din yake dutyn dare saboda haka yace gashinan zuwa.


Number Sadiya ya kira bugu biyu ta daga tace “tun dazu nake kiran wayarka bata shiga saboda matsalar network" a gajarce yace mata “eh bayan nakai Babyn Uncle gdanmu na fito aka kirani meeting din gaggawa yanzu haka uzuri na karba na fito dazun kashe wayar nayi bazan dawi ba may be sai gobe zan dawo” haka kawai taji zuciyarta bata gasqata mgnrshi ba cikin tsoro tace “anya Uncle meeting ka shiga kuwa?" Cikin son ta gasqatashi yace “to me kike tunani sabon gari na tafi gurin karuwai kome?" “Koma ma zai iya” faruwa abinda ta fada kenan takaici yasashi cewa “ok ai kin kasa dani baki saukemin haqqina dake kanki dole kiyi tunanin haka toni ba haka nakeba banacin itaciyar da Allah ya haramta ta gareni" yana fadin haka ya kashe wayarsa daidai lkcn likitan ya qaraso ya tashi ya bude masa sukayi musabiha ya qarasa gadon ya nuna masa Umaimah yace “sati guda kenan da lkcn period dinta ya wucce Ina tunanin tanada shigar ciki amma Dr komai taci saiya dawo gashi naji jikinta da zazzabi” dubata likitan yayi sosai ya tabbatar da shigar cikin sannan ya rubuta mata magunguna tare da shawarar ta daina aikin wahala ta rinqa samun hutu sosai, gdy yayi masa tare da yi masa transfer kudi masu kauri ya rakashi har gurin motarsa ya dawo har yanzu bacci takeyi ya kwanta kusa da ita shima tare dayi musu addu'a bacci ya daukesu.


Da asuba da salonsa ya tasheta daqyar ta bude idonta yayi kissing tounger dinta ya miqe yace “a tashi ayi sallah Uncle yanason gaisawa da Babyn sa” bata kulashi ba har yayi alwala ya fito itama tayo shine yajasu sukayi jam'i suna idarwa ta miqe ta koma ta kwanta shima kwanciya yayi ya matseta a jikinsa yana shafa cikinta da haka bacci ya sake daukesu 11:00am ta farko ta zame jikinta ta shiga bathroom tayi wanka ta fito tasa kayanta daidai lkcn yayi miqa tare dakai hanu zai damqota tayi baya da sauri tayi raurau da ido zatayi kuka murmushi yayi ya miqe ya matsa kusa da ita ya dora habarsa a kafadarta yayi mata mgn cikin rada yace “inason gaisawa da yarona ne fah yasan Daddynsa ya tashi lfy" shassheqar kukan data farane yasashi dariya yace “matsoraciya na qyaleki badon halinki ba” wanka ya tashi yayi yana fitowa ya danna number restaurant din ya fada musu abinda suke buqata yanzunma kusan dura yayi mata ta sakeyin amansa babu yanda ya iya hakanan ya miqe ya bata magungunan tasha sannan yace ta tashi su tafi kallonsa tayi tace “Gdan Daddyn fah kace shine yakeson ganina" murmushi yayi yace “bazaki ba" abinda yace kenan ya dauki wayarsa ya fice itama bin bayansa tayi yana shiga gdan yayi parking abin mamaki sai yaga motar Sadiya bata fita ba murmushi yayi don yasan saboda su taqi fita bude qofar yayi ya fito ya budewa Umaimah ta bisa da kallo daga Mata gira yayi tare da ruqo hannunta ta fito gaba daya batajin dadin jikinta jirine ya dauketa tayi luuuu zata fadi ya riqota da sauri ya mannata a qirjinsa daidai lkcn Sadiya ta fito daga cikin gdan karaf idonta ya fada cikin na Hameed daya qanqame Umaiman a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya, laptop da takardun hanunta ta saki a qasa tare da quduma wata uwar ashar tayo kansu a guje......






*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*




*🅱RILLIANT WRITERS* *ASSOCIATION* 🖊
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers)_



*GIDAN UNCLE*
( _Love and romantic story_)


*SHORT AND TRUE LIFE STORY*



*MALLAKAR*
👇🏻
*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
*®FAUZAH*



Wattpad👉🏻 realfauzah



www.fauzahtasiu41@gmail.com




*PAGE TEN*



Da sauri Umaimah ta fara qoqarin janye jikinta daga nasa amma yaqi sakinta cafka Sadiya takai mata yayi wani juyi da Umaiman yamai da ita bayansa qanaamesa tayi ta saki kuka jikinta yana rawa saboda tasani yau kashinta ya gama bushewa sake kaiwa Umaimah wawura tayi ya riqe hanunta tare dayi mata wani murmushi yace “kada ki tabamin qanwa Sadiya batada wani laifi jirine yake daukanta shine na riqeta..." Hanu ta daga ta daukeshi da mari cikin bala'i tace “qarya kake Abdulhameed dama na dade Ina zarginka da Umaimah yaudai Allah ya tona maka asiri ashe abinda kukeyi kenan cin amanata kukeyi Hameed ka rasa dawa zakayi lalata saida Umaimah yarinyar dana raineta naci wahalarta Hameed menayi maka mena rageka dashi da zakake lalata da Umaimah yarinya qarama me hakan yake nufi? Ashe gsky abinda Nihal ta fadamin taganka kanashawa Umaimah nono nace qarya ne ashe cinyeta kakeyi Hameed yarinyar daka Raina tun batasan kantaba yanzun ita kake zina da ita ita kake qwaqwulewa meye hakan Hameed ni dama nasan ba wani meeting daka tafi kanacan kana iskancin kane...."


Allah ne ya bata saa ta cafko hijjab din Umaimah ta fincikota da qarfi ta wani wujijjigata tayi jifa da ita cikin rashin saa ta kifa saman wani dutse da aka ajiye a gurin ta qwallah wata razannanniyar qara da gudu ya nufota ja yayi da baya da sauri yace “na shiga uku Sadiya kin kasheni jini Sadiya jini take zubarwa a tsorace ta juyo daidai lkcn ya dago Umaiman da tayi doguwar suma yabi jikinta da kallo jini take zubarwa sosai ya qara qanqameta ya saki kuka yana jijjigata yana cewa “kada ki mutu Baby don Allah kada ki bari muyi asarar babyn mu kada cikin nan ya zube inasonsa Baby plz.."


Yanda yake mgnr kadai zai tabbatar maka da lallai baa cikin hayyacinsa yakeba kuka yake sosai yana jijjigata yana kiran “ki tashi Umaimah ki tashi don Allah kada ki mutu ban fadawa duniya matsayinki a gurina ba kada ki mutu kina kallona a matsayin mazinaci Umaimah kada ki mutu bamu cika burin kakanmu da iyayenmu ba Abba ya mutu da burin ganin zuri'ar mu ya mutu yana fatan zamanki a wannan matsayin yabada wasiyyar ko bayan ransa kaka ya tabbatar da dauruwar aurena dake kakanmu ya cika masa burinsa kafin yabar duniya Umaimah don Allah kada ki mutu saimun haifi danda zamusa masa sunan mahaifin ki aurena dake hadin Allah ne shine ya hada”


Tsoro ne ko tashin hankali yasa Sadiya yanke jiki ta fadi oho faduwar tatace ta fargar da mai gyaran fulawar ya nufo gurin da sauri ganin Hameed din rungume da Umaimah wacce take kamar matacciya ga jini sai malala yake ta qasanta yanata gursheqen kuka kamar wani mace ne ya tashi hankalinsa ya matso da sauri yace “ya salam maigida jininta zai iya qarewa akaita asibiti” sai yanzu hankalinsa ya fara dawowa jikinsa ya miqe ya dauketa cak kamar wata yar jaririya yasata a mota har yaja motar Sadiya tasha gabansa tana layi tace wlh baka isa ka fita da ita daga gdannan ba yau saidai koni ko kai ko ita na rantse da Allah baku isa kuci amanata ku fita lfy ba aure tab billahillazi baka isaba Allah ya tsine uban Wanda ya fasa wlh dagaku har danginku sai kunsan kunci amanata" tana fadin haka ta nufi cikin gdan a guje kamar mahaukaciya.



Hakanne yabashi damar figar motar a guje ya nufi Abdullahi Wase specialist hospital yana zuwa aka karbeta aka shiga da ita emergency duk inda sukayi binsu yake kamar wani zautacce daqyar Dr Saleem ya lallasheshi ya zauna a reception din ya hadakai da gwiwa cike da tashin hankali ji yayi an tabashi ya miqe da sauri yace “na shiga uku ta kasheta ko Dr?" Murmushi Dr Saleem yayi yace “ka kwantar da hankalinka bata mutuba munsamu nasarar tsayar da jini amma akwai buqatar wani jinin da gaggawa saboda ta zubar da jini sosai” ajiyar zuciya yace “alhmdllh cikin jikinta fah?" Girgiza kai Dr Saleem yayi yace “saidai muyi hqr wannan ya lalace muyi addu'ar Allah ya kawo wani me albarka” wasu hawayene suka zubo masa yace “shikenan tayimin sanadinsa ya zube” dafa kafadarsa yayi yace “karka damu zaa samu wani da wuri bamuda lkcn wannan yanzu jini muke buqata” hanunsa ya miqa masa yace “ka diba wanda zai isheku” janshi yayi suka nufi Lab din cikin saa jinin nasu iri dayane zama yayi aka dabe leda biyu sannan suka nemi daya aka siya suka fita har dakin yabisu har yanzu tana kwance kamar gawa Dr Saleem ya daura mata jinin nurse din dake kula da ita ce ta kalli Umaimah ta kalli Hameed tace “yallabai qanwarka ce ko matarka?" Dr Saleem yace “nima abinda ke raina kenan wannan aikin mijine yallabai samada shekara ashirin nake aikin kula da lfyr iyalan Alh Adamu Hameed Shuwa a tsayin shekarun nan Umaimah autar Hajiya ce qanwa a gurinka amma kuma naga wani baqon lamari tsakanin jiya da yau"



Lumshe idonsa yayi ya kwanta a gadon dake facing din na Umaiman ya zuba mata ido yace “qanwata ce kuma matatace iyakar abinda zan iya fada muku kenan" murmushi nurse din tayi tace “kamar ku kadai ta Isa ta bayyana hakan..." banko qofar da akayi ne yasasu miqewa da sauri a tsorace ya nufi gadon da Umaimah ke kwance ya nuna Sadiya dake shigowa da hanu yace “kada ki qaraso nan ki tsaya anan wlh idan kika bari na waiwayoki zakisha mamaki idanma baki sani ba ina qara sanar dake Umaimah matata ce ta sunnah wacce take iya dauke lalurata Sadiya kiyi a hankali kada ki dauki haqqin marainiyar Allah batajiba bata gani ba wlh batada laifi saboda itama batasan da aurena akanta ba....”



“Ina ruwana Hameed kai wannan ta shafa cin amana ba ni zakuci amana saboda kai tsinanne ne mayaudari maci amana azzalumi ni zakaci amana ka fakemin da wata qaryarka wai matarka ce to na rantse da Allah ba matarka ba ko uwarka ce saina kasheta saidai Khadijah ta dawo duniya ta haifi wata kuma kaima saika tafi inda ta tafi..." Zabura tayi a guje ta nufi gadon Umaiman yayi wani tsalle ya tareta tare da riqeta ga dukkannin qarfinsa ya hankata baya ta fadi Tim a qasa kafin yayi wani yunquri ta kuma tasowa ta fakaceshi ta haye ruwan cikin Umaimah shima kanta yayi a guje ya tunkudata qasa ya zare belt din wandon jeans dinsa yace “wlh kika qara tabata sainayi miki abinda bantaba yimiki ba kashe yar mutane kikeson kiyi Sadiya me tayi miki wanne irin haukane wannan kawai don takasance matata to ki sani aurena da Umaimah hadin Allah ne haukanki bai isa ya rusheshi ba abinda yasa na boye aurannan kenan saboda nasan ke mahaukaciya ci shigowar Hajiyansa ne yasashi yin shiru da bakinsa gadan² tayo kansa kafin ya ankara yaji ta daukeshi da wani gigitaccen mari ya dafe gurin da sauri ya dago kansa yace “Hajiya...” sake zabga masa mari tayi tana kuka tace.



“dama abinda yasa ka dage sai anbaka ita kenan Hameed irin taka amanar kenan me yaja hankalinka harka lalata tarbiyya marainiyar Allah na tabbata Umaimah bazata taba banzatar da tarbiyyar da kayi mata ba saidai kai ka banzatar da taka itama ka lalata mata tata meye ribarka Hameed qanwarka ka lalata harda ciki Innanillahi wa innah ilaihir raji'un wannan wacce irin baqar rayuwace wacce irin qaddara ce Hameed da kanka da kanka ka ketama Umaimah haddi ka cucemu Hameed kaci amanar maraici bazanyi maka baki ba amma da sannu zaka girbi abinda ka shika” tunda ta fara mgnr kansa na qasa harta gama ta juya ta nufi gadon da Umaiman takekai ta ruqo hanunta cikin tausayawa tace “Allah ya isanki Umaimah Allah ya isar miki” miqewa Sadiya tayi ta kalleshi tace “zaka dawo ka iskeni har gda wlh saidai koni ko kai azzalumi”


Yanajinta amma bai iya tanka mataba harta fice zuciyarsa mugun tafasa takeyi yasan duk bayanin da zaiyiwa Hajiya bazata saurareshi ba saboda haka yaja jikinsa ya fita ya zauna a kujerar dake qofar dakin, daidai lkcn da Umaimah ta bude idonta ta saukeshi akan Hajiya ajiyar zuciya Hajiyan tayi tace “sannu kinji Umaimah” daga Mata kai tayi cikin sarqewar murya tace “Hajiya ki tafi dani gdanki Aunty Sadiya da Uncle zasu kasheni wlh Hajiya kasheni zasuyi” kama hanunta tayi tace “wa ai dama kin gama zaman tsinannen gdannan ni dama tun farko banso zamanki ba dandai wannan azzalumin ya nace ne kuma Daddyn ku ya goya masa baya yanzu ga abinda gari ya waya” kwallar dake zubo mata Hajiya ta share mata tace “kiyi hqr wlh saiya gane kuransa wannan ai zalumci ne shekaran jiya yaje yake fadamin wata shashashar mgn saboda Daddyn ku yace yabarki ki fitar da miji bayan Daddyn ku ya tashi yake cemin wai yayi miki miji ashe abinda yake nufi kenan Allah ma ya rufa mana asiri da cikin ya zube da munga ta kanmu don wannan me raayin riqau din ba bari zaiyi a zubar dashi ba macuci kawai”



Abinka da zuciyar mace duk saitaji babu dadi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login