Showing 81001 words to 84000 words out of 131968 words

Chapter 28 - GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL BY UMMUH HAIRAN

10 Jul 2024

22484

matsawa kusa da yar uwar tata ta kamo hanunta tace “amma saboda tsabar rashin kunya da tsageranci da cin fuska kika iya duban tsabar idonsu kika iya furta musu bazaki qara zaman aure da dansu ba kuma kin tsaneshi hmn yarinya kiyi gaggawar sake tunaninki wlh mutanen nan basu cancanci wannan sakayyar daga gareki ba Umaimah kinsani Hameed yana sonki bazai iya rayuwa babu keba kamar yanda yasha fadamin, ko kinsan yasha zuwa ya fadamin irin wulaqancin da kikeyi masa da tsanar da kike nuna masa Umaimah Hameed yasha zuwa har Damaturu yasani a gaba ya rinqa yimin kuka yana fadamin zuciyarsa zafi take masa a duk lkcn da yaso ganinki ko yaso jin muryarki yazo gdan kikaqi yarda ku hadu ko ya kiraki a waya kikaqi amsawa Umaimah ko kinsan Hameed yasha fadamin sonki shine zai kasheshi ko kinsan a ranar da abin ya faru yana fitowa daga gdan Daddy ya daga waya ya kirani yake fadamin zuciyarsa fashewa zatayi Ina bashi hqr naji ya saki wata qara tare da kiran sunanki shikenan har yau tsayin sati biyu da kwanaki uku baisan kansa ba"....



Ajiyar zuciya ta kumayi kana ta dora da cewa “bakiyi kuka ba Umaimah sai ranar da kika daura aure da wani ba Hameed ba aka kaiki gdansa dare yayi ya shigo yayi mu'amalar aure dake minti biyu ya sauka ya bingire ya fara bacci bai farka ya sake nemanki ba saida safe ki nemeshi yace kin cika karuwanci da takura shi ya gaji to a sannan ne zaki fara kukan nadamar gujewa namiji daya tamkar da dubu namijin da mace da yawa take burin mallakar irinsa kuma namijin da bazaki qara samun irinsa ba a duniya ke bari nayi miki kalmar qarshe Umaimah wallahi tallahi billahillazi La'ilaha illah huwa bazaki iya zama da kowanne namiji ba sai Hameed shine ya fara saninki dashi kika saba kuma shine daidai dake saboda danshi kadai aka halicceki kamar yanda yasha fadamin"......



_Kuyi manege da wannan_ 🙈






*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[1/22, 8:35 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *GIDAN UNCLE*



Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:



*PAGE FOURTY TWO*




Kuka ta sake saki me ciwo tana girgizawa Aunty Jameelah kai, sake Mata hanu tayi tace “bazanyi miki dole ba kamar yanda Daddy yayi alqawarin bazaiyi miki dole ki yarda ki auri Hameed ba amma ina tausayawa rayuwarki a gdan wani ba Hameed ba domin shine mahadinki shine abokin rayuwarki kuma shine qaddararki ko ki yarda ko kada ki yarda Hameed nakine kema tasace kamar yanda yasha fadamin danshi kadai aka halicceki saboda haka kiyi gaggawar dawowa hayyacinki kafin kiyi abinda zai zame miki ciwo har qarshen rayuwarki”



Tana fadin haka ta dauke Shurafah a jikin Umaimah ta cire mata Pampers tayi mata tsarki karbarta Umaimah tayi ta fita zuwa dakin Hajiya ta bude ta shiga da sallamarta tasa kai ta shiga turus taja ta tsaya ganin Hajiya zaune gefen gado ta hada kai da gwiwa tanata gursheqen kuka.
Jiki a matuqar sanyaye ta qarasa ta tsugunna a gabanta ta kwantar da kanta a cinyar Hajiya kawai itama ta saki kukan da sauri Hajiya dago tace.



“Ke meye hakan Umaimah?" Cikin kuka tace “kiyi hqr don Allah Hajiya insha Allahu Uncle zai samu lfy zai warke kuma zaici gaba da rayuwa cikin farin ciki kamar baya don Allah Hajiya ki daina kukannan banaso ya kikeso muyi keda zaki rarrashemu" shafa bayanta Hajiya tayi tace “na fidda rai da rayuwar yaronnan Umaimah koda ya farfado idan yaji hukuncin da kika yanke na bazaki qara rayuwa dashi ba zaiyi mutuwar dungurungum saboda nasani kece zuciyarsa Umaimah bazai iya rayuwa babu keba..."



Zamowa Hajiya tayi tayi knilling a gaban Umaimah ta ruqo hanunta tace “Don Allah badon niba Umaimah ki taimakeni ki yarda ki rayu da dana kece cikon farin cikinsa Umaimah zan rasashi idan kikaqishi don....." Saurin rufewa Hajiya baki tayi cikin kuka tace.



“Kada ki qara hadani da Allah Hajiya ko baki hadani da Allah ba nasani kuma na amince Yayana Abdulhameed mahadin rayuwata ne bazan iya rayuwa babu shiba bansan inason Uncle ba kuma bansan ciwonsa nawa ne ba sai yau dana ganshi Hajiya na shirya sake komawa qarqashin inuwar auran Uncle Hameed indai wannan shine zaisa yaci gaba da wanzuwa cikin farin ciki...."



Wata runguma Hajiya tayi mata tana kukan dariya tace “na gde miki yata Allah yayi muku albarka Allah yabawa dan'uwanki lfy kuci gaba da qawatamu da salon qaunarku mai ban sha'awa" murmushi tayi tace “ina Daddy Hajiya?" Ajiyar zuciya tayi tace “yana Riyadh gurin Hameed shida Yusuf"



Sunkuyar da kanta tayi tare da qurawa Shurafah idon har yanzu idan ta kalli Shurafah sai taji tsanar Hameed a ranta amma tayi alqawarin kankareta a zuciyarta saboda cikar farin cikin iyayensu miqewa tayi a salube ta kwantar da Shurafah tace “na kawo miki ita ta tayaki hira inason zuwa harami ne Hajiya" murmushi tayi ta matsa kusa da Shurafah tace “ja'ira mekan qwanqwalati bata da aiki sai bacci kamar kasa nidai bansan ina kika debo ragwanta ba iyayenki duk ba ragwaye bane" murmushi Umaimah tayi tace “kun daifi kusa ta kwana tana maki waqa” itama dariya Hajiya tayi tace “to ya zanyi hausawa sunce abin cikin qwai yafi qwai dadi ai Allah ya taimaka saikun dawo”



Amsawa tayi da amin sannan ta fice taje ta tarar da Aunty Jameelah har ta shirya suka fito da qafa suka tattaka har masallacin harami suka fara gabatar da ibadarsu kamar kowanne musulmi itadai Umaimah rasa abin da zata roqi Allah tayi banda abu uku yafiya, samun lfyr yayanta da kuma shiriyar yarta Shurafah basu sukabar harami ba saida sukayi sallar asuba da yake tun kwanaki sha biyar da haihuwarta ta tsarkaka sai ciwon dinkin da tasha da har yanzu bai warkeba har zuwa wannan lkcn dingisa qafarta takeyi bata taketa sosai ba.



Haka sukaci gaba da gabatar da ibadarsu cikin rashin nutsuwar zuciya saboda itadai Umaimah hankalin ta yaqi kwantawa saboda rashin sanin halin da Hameed din yake ciki ranar da sukayi sati biyu a qasar Saudia ne ranar Daddy ya samu Umaimah a dakinsu shida Hajiya ya dubeta yace.



“Uwar masu gida Hajiya ta sameni da wata mgn a baya kinyi furucin bazaki sake rayuwar aure da Hameed ba kuma yanzu naji kince kin janye hakane?"



Jinjina masa kai tayi cikin kunya yayi murmushi yace “amma dai ina fatan ba wanine ya takuraki ya canza miki raayi ba?" Sake daga masa kai tayi yayi ajiyar zuciya yace “naji dadin hakan kuma nayi farin ciki da faruwar hakan Umaimah Allah yayi muku albarka ya shiga cikin lamarinku a gobe idan Allah ya kaimu zanje harami a mayar muku da auranku jibi saiku wucce Istanbul zuwa lkcn da zaku dawo komai yayi Normal da izinin Allah"



Dagowa tayi da sauri tace “aa Daddy nikam na fasa zuwa Istanbul dinnan ba" kallonta yayi da sauri yace “meyasa?" Qasa tayi da kanta tace “Daddy hankalina bazai kwanta ba ana zuwa yawon shaqatawa ne saboda nishadi toni nawa farin cikin yana asibiti baisan wake akansa ba wlh Daddy koda na tafi hankalina bazai taba kwanciya ba kayimin hqr bazan iya tafiya bansan halin da Abdulhameed yake ciki ba"........







*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[1/23, 4:34 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *G.U*


Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:










Ajiyar numfashi Daddy yayi cike da jin dadi ya miqe yace “shikenan ki zauna Baby bazan miki dole ba amma kinsan bazaku zauna anan ba tunda kun gama umararku zaku koma gda duk halin da ake ciki ma rinqa waya saboda makarantar ki kuma ma jikin Hameed da sauqi tunda yanzu numfashin sa yana fita sosai kuma wasu bangarori na jikinsa suna motsawa ba kamar baya ba"



Ficewa yayi ita kuma ta miqe ta haye gado ta kwanta inda Hajiya ta dauki Shurafah suka fice.
A washe garin ranar aka sake daura auranta da Hameed itadai a ranar yini tayi zuciyarta babu dadi hakanan bata farin ciki da auran nasu duk da ita kanta tasani yaudarar kanta ta rinqayi a baya da takejin kamar zata iya cireshi a ranta, kwana hudu suka qara a qasar Saudia suka dauko hanyar 9ja badan tanaso ba saidon batason yin musu da iyayen nasu musamman Daddy daya matsa akan sai sun tafi kwana uku ta huta Aunty Jameelah ta kama hanyar gdanta ita kuma ta shirya domin fara halattar makaranta micro biology take karanta kuma tanajin dadin course din sosai da yake Umaimah bamai hayaniya bace yasa ko qawa batayi a skul din ba daga ita sai Shurafah dinta suke harkokinsu yarinyar tayi qiba sosai tayi wayo cikin wata biyun idan ka ganta zaka dauka tayi wata hudu yarinya kyakkyawa abarso ga kowa ga Umaimah da sanin darajar kwalliya wa yaro kullum cikin ado Shurafah take hakan yaja Mata farin jini gurin yammatan department din nasu kowa Shurafah hakan yanasa Umaimah taji dadi aranta Saudat Alfah itama sabuwar daluba ce matashiya meji da gayu da tsayuwar naira a jikinta tunda ta shigo makarantar Allah ya hada jininta da Umaimah itama sanadin Shurafah Saudat Alfah itama matar aure ce da yaranta biyu tana auran wani custom tun Umaimah na janyewa abotar tasu harta saki jiki suka zama abokai sosai ita Saudat namiji take goyo Sudais kusan saanni ne da Shurafah.




Semester ta fara nisa sosai su Umaimah yan makaranta itadai karatun kawai tasa a gabanta amma rabin hankalinta yana wajen su Daddy da kullum sukayi waya saidai yace musu jiki yana kyau sosai a haka har suka cinye semester sukayi hutu a cikin hutun ta takurawa Daddy kan cewa tanaso taje ta gano jikin Hameed Daddy yaso hanata zuwan amma yanda yaga ta damune yashi dole ya qyaleta dake ya dawo dazai tafi suka tafi tare.



Kai tsaye asibitin da yake suka nufa suka shiga dakin tana rungume da Shurafah tunda suka shigo ya Hameed dake zaune jingine da matashin kai ya ya zubawa Umaimah ido ya kasa ko qiftawa sai yawo yake da idanunshi akanta kamar wanda ya warke daga ciwon makanta ajiyar zuciya ya sauke ta dago kanta da tayi qasa dashi tun kallon farko da sukayima juna idonsu ya qara sarqewa da juna a hankali ya daga hanunsa ya miqa mata alamun yana buqatar tabashi wani abu.



Cikin sassarfa ta qarasa gabansa ta dora masa Shurafah a jikinsa ya qurawa yarinyar da itama shidin take kallo ta qura masa ido sai bangale masa baki takeyi shima murmushin shima yayi mata tare da dagowa ya dubi Umaimah da taketa kallonsa ya rame sosai hancine kawai da ido sai dan qaramin bakinsa da yake motsawa a hankali alamun magana yakeson yi mata amma muryarsa bata fita sosai.
Shigowar Daddy da likitocin ne yasata neman guri kusa dashi ta zauna a sanyaye taji ya ruqo hanunta ta dago da sauri suka hada ido ya lumshe nasa a hankali ya bude tare da cewa “Kina kulamin da Shurafah yanda ya kamata kuwa?"



Yayi mgnr da murya me rauni a salube ta jinjina masa kai ya janye hanunsa daga nata tare da cigaba da kallon yarinyar yanajin qaunar da baitabaji akan sauran yayansa ba game da yarinyar dagata yayi a hankali ya dorata a qirjinsa.













*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[1/23, 8:05 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *G.U*


Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:















Likitan ne ya dubi Daddy sukayi larabcinsu ya miqawa Hameed hanu sukayi musabiha suka juya suka fita Daddy ya dubesu yace “zuwa sati idan ka qara warwarewa saimu tafi gda ko babana?" Lumshe idonsa yayi ya bude Daddy yayi murmushi yace “gadai Umaimah tazo ta kawo maka Shurafah nima hankalina ya kwanta yanzu zamu iya tafiya"



Daddy ne ya taimaka masa ya miqe kasancewar komai a asibitin ake masa babu abinda suka dauka sai kayansa yana rungume da Shurafah Daddy yana riqe dashi haka suka fita motar asibitin ta daukesu zuwa masaukinsu dakin da Daddy ya kamawa Umaimah nan yakaiwa Hameed kayansa ya juya ya fita ya barsu su biyu zama yayi a gefen gadon yana binta da shu'umin kallonsa me kashe mata jiki bata iya ce masa komai ba sai neman guri da tayi ta zauna a saman resting chair din dake gefen gadon ajiyar zuciya ya sauke tare da kawar da kansa daga kanta yace.



“Ina buqatar zan kwanta na huta” da sauri ta dubeshi ya sake kawar dakai yace “ina nufin Ina buqatar privacy zaki iya fita kice da Daddy ya kama maki wani dakin" dagowa tayi zatayi mgn yayi saurin daga mata hanu yace “banason surutu kuma banason takura kitashi kije ki kwanta dare yayi"



Jikinta a mugun sanyaye ta miqe ta nufi gadon idanunta ya ciko da hawaye ta sunkuya zata dauki Shurafah ya daka mata wata tsawa data sata saurin yin baya yace “get out for my room" da sauri ta juya ta nufi qofar dakin ta bude a tsorace ta fice daga dakin.



Miqewa yayi ya kwantar da Shurafah dake bacci yasha magungunansa ya kwanta tare da janyo yartasa a jikinsa da haka bacci ya daukesa.
Umaimah kam a tsayawa tayi jikin qofar dakin zuciyarta nayi mata wani zafi da ciwon irin korar da yayi mata takeji wai ta fice masa daga dakin wasu hawaye ne masu zafi suka ziraro mata ta zauna a parlourn saman carpet zuciyarta nayi mata suya wannan ko wanne sabon wulaqancin rashin lfyr tasa tazo masa da ita oho.



Da wannan tunanin ta kwanta saman carpet din bacci ya dauketa da asuba ya farka yayi alwala yayi sallah yana zaune saman sallaya ta bude qofar ta shigo ta saida gabanta ya fadi data ganshi zaune yana lazumi kamar wacce qwai ya fashewa a ciki ta nufi bathroom din ta dauro alwala ta juya ta fita zuwa parlourn ta tayar da sallah tana idarwa yana fitowa yana cilla Shurafah sama yana cafewa ya zauna saman kujerar yana yima yarinyar wasa cikin faduwar gaba tace masa.



“Ina kwana" kallonta yayi kallo irin na rainin wayo yaci gaba da yima yarsa wasa shiru tayi masa taci gaba da azkar dinta kamar daga sama taji muryarsa yana cewa “wato da nace kije ki fadawa Daddy bana buqatarki a kusa dani ya nema miki dakin da zaki zauna kafin mu koma gda shine saboda ban isa ba kika kwana anan ko? To bazan hanaki kwana anan ba tunda haka kika zaba amma kisani kada ki kuskura ki shigomin daki da dare ranki baci zaiyi"



Harya gama mgnr batace masa qala ba sai hawayen da take zubarwa a rayuwarta babu abinda yake mata ciwo irin jizgi da wulaqanci bata jurewa hakan ko kadan.
Bai sake bi ta kanta ba ya tashi ya miqa mata Shurafah yace “yarinyata me hqr ya kamata a bata abincinta taci" yana fadin haka yasa hanunsa ya zare hijjab din jikinta ya zuge zif din ya sanya hanunsa ya dago qosasshen breast din nata yayi ajiyar zuciya tare da hadiye wani yawu ya saita bakin Shurafah yasa mata ta kuwa kama da sauri harda sanya hanunta ta dafe.



Miqewa yayi ya shige dakin saboda wani yar da yakeji a jikinsa ya fada bathroom da sauri ya sakarwa kansa ruwa ya fito ya dauki wani magani da Dr Maheelr ya bashi wanda yake taimaka masa wajan control din feelings dinsa sosai yasha ya koma ya kwanta tare da jan blanket sanyi Umaimah takeji sosai saboda weather din sanyin Saudi akwai shiga jiki amma tsoron ta tashi ta shiga dakin take ta dauko rigar sanyinta saboda ta lura ya qaro rashin mutunci sosai hakanan ta zauna data gaji ta dauki pillows din kujerar ta kwantar da Shurafah itama ta kwanta.



Ta jima tana baccin kafin ta tashi yana zaune a parlourn yana kallo miqewa tayi ta nufi dakin ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta tsaya jikin mirrow tana gyara jikinta daidai lkcn ya shigo dakin da Shurafah a hanunsa ya cire mata kayanta saurin dauke idonsa yayi daga kan Umaimah ya nufi bathroom ya fara yima yarinyar wanka lkcn daya fito itama ta gama har tasa kayanta ta koma parlourn ta soma hada tea bai fitoba saida ya shafama yarsa mai ya bude jakar kayansu ya dauki kayanta yasa mata ya shafa mata powder tare da taje mata sumarta baqa sidik mai yawa da tsayi yayi kissing lips dinta ya dauketa yace “ehhhh beautiful daughter kinfi kowacce ya kyau a duniya"




Suna fitowa Daddy yana nocking door din qarasawa yayi ya bude Daddy ya shigo ya dubi Shurafah da taketa hanqoron zuwa gurinsa yayi murmushi tare da daukanta ya cillata sama ya cafe yace “kin tashi lfy ayar Allah" kallonshi dukkansu sukayi yayi murmushi irin nasu na manya yace “sunanta kenan iznah ce Zulaiha" share zancen yayi da cewa.




Naso na bari sai nan da kwanaki shidda mu tafi so amma wani uzuri ya tasomin na gaggawa saboda haka yau da yamma nakesa ran zan tafi..." da sauri Umaimah ta tari numfashin sa da cewa “yawwa Daddy dama inason ce maka nima zan bika mu tafi saboda saura kwanaki uku hutunmu ya qare” wani malolon kishine ya tasowa Hameed yayi saurin kallon Daddy yace “hutun me Daddy?" Murmushi Daddy yayi yace “hutun makaranta ta fara degree dinta a Skyline University har sunyi semester guda”



Daure fuska yayi ya zabga mata wata uwar harara ya juyo ya kalli Daddy yace “kayi tafiyarka kawai Daddy idan na qarajin qwarin jikina zamu taho" dagowa tayi cikin tsoro saboda ita tunda taganshi jiya yayi Mata wani kwarjini sannan tsawar daya daka mata jiyan tasata jin wani mugun tsoronsa ya darsu a zuciyarta tace “amma don Allah Uncl...." hanunsa ya dora a lips dinsa alamun tayi masa shiru yace “ba dake nake mgn ba malama banason rashin kunya"




Kallonsa Daddy yayi da mamaki yaga yanda ya wani tsare gda shi a dole me iko yasan tabbas idan ya barta bazaa shuka abin arziqi ba ya miqe yace “debo kayanki kizo mu tafi Jidda mu jira lkc mu tafi" miqewa tayi zuciyarta fari tas ta shiga dakin ta fara hada shirginta saboda Allah ma ya sani bazata iya zama inuwa daya da wannan sabon Hameed din mara mutunci ba.
Baiyi mata mgn ba har saida ta gama hada kan kayanta ta goya yarta tabi bayan Daddy har Daddy yakai bakin qofa ya zai fita suka tsinkayo muryar Hameed

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login