Showing 90001 words to 93000 words out of 131968 words
amma hakanan tunda ta durqushe ta kasa tashi jin zuciyarta takeyi kamar zata faso qirjinta wai ita Umaimah ita zaayiwa kishiya kishiyar ma kusan saar yayarta Jameelah kuka ya kuma kwace mata wannan karon harda shshsheqa ashe da gaske ne da mata suke cewa ko labarin mutuwa baikai na kishiya ciwo ba “Allah ka kasheni na huta" abinda ta furta kenan jitayi an sanya hanu an dagota ta daga kanta ta dubeshi da sauri shima itadin yake kallo idanunsa sun kada sunyi jawur.
Har cikin ransa yakejin ciwon kukan Umaimah ya rasa meyasa kullum shine yake zama sanadin kukanta kullum shine sanadin baqin cikinta ya rasa yaushe ne zai zamewa Umaimah farin ciki a rayuwa yaji komai daya faru tun daga kwanciyar sa jinya har kawo yanzu a gurin Aunty Zarah yasani sarai ba raayinta bane sake rayuwar aure dashi tausayinta gareshi da sadaukarwarta da kuma gudun bacin ran iyayensu shine yasata aminta da sake auransa towai shi meyasa ma yakeson qara auren ne iyakar saninshi shi ba meson tara iyali bane kuma babu abinda yakeso a gurin mace wanda matarsa bata dashi to wai meyasa yakasa bijiirewa auran Salma ne?.........
_Kuyi hqr wutarmu ta lalace Ina fama da matsalar charge insha Allahu zaku jini anjima idan baku jini ba kuma kuyimin uzuri._
*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[1/26, 3:14 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *G.U*
Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:
Janye jikinta tayi daga nasa a hankali sai yanzu ta sami qwarin gwiwar bude baki a sanyaye cikin sarewa da sallamawa farin ciki tace “kishiya zakayimin Uncle me nayi maka meyasa bazaka bamu damar gyara aurenmu da tsarkakeshi ba sai ka zabi kawo wata cikin rayuwarmu a lkcn da mukafi buqatar kusanci da juna ko badon komai ba don rayuwar yarmu bazance maka kada kayi aure ba Uncle amma ka sani tunda na taso a zuri'ar mu banga gdan da ake zaune da mace sama da daya ba wayyoh ni Umaimatu meyasa qaddarorina suke da tsauri ne....”
Saurin rufe Mata baki yayi da nasa ta tureshi da sauri saboda jitayi kamar ya sanya mata garwashin wuta a lebanta ta qarasa gaban Shurafah da taketa wasan ruwa ta dauki sabu ta fara sabawa yarinyar batare da tana ganin komai ba saboda zuciyarta da tayi mata nauyi.
Da sauri ya qaraso ya janyeta saboda yaga neman kashe yarinyar takeyi ya qarasa mata wankan lkcn daya fito tana hada kayanta a trolly ya tsaya sake da baki yana kallonta bata dago ta kalleshi ba har saida ta gama ta miqa masa hanu domin ya bata yarinyar amma yaqi haushi ne yasata jan akwatinta zata fice yayi saurin riqeta yace “kina hauka ne Babyn Uncle Ina zaki da safennan"
Dagowa tayi da idanunta da suka dade da canza kala zuwa jajaye ta watsa masa wani mugun kallo tace “gda zani Abdulhameed idan naci gaba da zama dakai a qasar nan sai ka kasheni kayiwa Aunty Jameelah asara don na tabbata ita kadai keda asarar rashina" tana fadin haka ta figi jakar kayanta ya kuma fincikota jikinsa na rawa yace “kiyiwa girman Allah ki tsaya ki fahimceni Umaimah wlh nima bason auren nan nakeyi ba bansan meyasa nakasa cewa aa ba plz Umaimah ki yarda dani ki karbi aurannan a matsayin qaddara ki amince dani wlh bazan taba cutar dake.....”
Marin data daukeshi dashine yasashi hadiye mgnrsa bata damu da yanayinsa ba ta dora da cewa “ ya isa haka Abdulhameed qaryar nan taka ta isheni so nawa ka cuceni cuta ta nawa kakeson yimin Hameed ka lalatamin quruciya ta wajan jarabarka ka yaudareni da kalamanka na qarya na sabawa ubangijina kayimin cikin zina na haifa ina kallon Shurafah a matsayin ciwon da bazai taba warkewa a rayuwata ba sannan yanzu kazomin da mgnr aure auren ma bana yarinya me qarancin shekaru kamar ni ba na guzuma sa'arka saar yayata sannan guzumar ma ka rasa wadda zaka hadani da ita sai Salmah Hameed Salman da babu wanda baisan tambari da kirarin gdansu ba ba kishiya ba dan miji babu uwar miji wannan shine kirarin da akewa uwarta Hameed tun ina qanqanuwata nasan da wannan kirarin sannan yanzu kazo saboda tsabar kai dan akuya ne qaramin mara kunya kacemin wai mutuniyar arziki ce ok na yarda a gurinka tunda idanunka sun rufe Salmah mutuniyar arziki ce amma ni a gurina bata isa na hada miji da ita ba wlh na hqr dakai Hameed nabar mata kai....”
Kamata yayi da sauri ya rufe bakinta a duniya babu kalmar daya tsana kamar yaji tana furucin ta hqr dashi.
Girgiza mata kai yayi yace “na...naji duk naji Umaimah amma ya zanyi wlh jinake kamar idan ban auri Salmah ba mutuwa zanyi kamar yanda nakejin idan na rabu dake zan mutu don Allah ki bani hadin kai Umaimah..." Kokowa suka rinqayi sosai ta akan saita fita inda shikuma ya dage akan bazata fita ba daga qarshe cillata yayi saman gadon ya fice ya kulleta ta waje.
Kifa kanta tayi a saman pillow ta rinqa kuka kamar ranta zai fita tanajin dama mutuwa tayi ta huta indai mutuwar hutu ce a gareta Shurafah ce ta rarrafo ta kwanta a jikinta itama tasa kukan miqewa tayi ta dauki yarinyar tana kuka tasa mata kaya ta bata nono tasha ta sake komawa ta kwanta tanajin zuciyarta kamar tayi tsalle ta fito.
Abin na Hameed kamar wasa saida suka qara kwanaki goma a Saudi babu wata mgn dake shiga tsakaninsu saidai kawai idan zai fita da safe ya kulle qofar parlourn idan ya dawo ya bude ya shiga yayi abinda yaga dama duk yanda yaso yaga ya shawo kanta taqi shawuwa takai ta kawo ma basa hada daki indai yananan to ita kuma zata kulle kanta a daki ta yini bata fito ba yasha tashi cikin dare yana buqatarta yayita dukan qofar yanayi mata magiya amma kamar batama san yanayi ba.
Hakanan a daddafe sukayi kwanaki goman suka dauki hanyar 9ja taso batace masa qala ba har suka isa katafaran gdan daya gina a tudun yola me part biyu har ciki dan taxi din ya shiga dasu suka fita ya sallameshi ya nufi wata qofa ya bude suka shiga tabi parlourn da kallo yayi kyau sosai sai qafar benen ya nufa tana riqe a hannunsa Shurafah tana daya hannun ya bude wata qofa yajata suka shiga ya sauke Shurafah dake bacci a wani qaramin gado dake gefe ya mayar da qofar ya danna Mata key ya tako zuwa gabanta yakai hanu zai ruqota ta zille da sauri yayi murmushi ya fara balle bottle din rigarsa ya balle belt din wandonsa ya zare Shortnicker din jikinsa ya nufota jikinsa na rawa ta janye ya cafkota da qarfi yace.
“Saboda zanyi aure Umaimah sai akace idan mijinki zai qara aure ki qaurace masa ki daina kulawa dashi ki daina sauraron kukansa da buqatarsa hakan shine zaisa yasoki ya fasa abinda Allah ya hukunta masa kada ki mayar da kanki jahila bayan nasani bakin gwargwado iyayenmu sun bamu ilimi kada ki biyewa son zuciya ki cutar damu Umaimah inasonki kina sona kada mu zalumci kanmu qarin aure bashine yake rusa zaman lfy da farin cikin gda ba rashin fahimtar junane ki yarda dani inasonki” yana fadin haka ya janyota jikinsa yaci gaba da famfata da kalamansa masu saurin canza mata tunani duk da haka kuka takeyi hakanan ya rinqa sarrafata tana kukanta tana komai ya rabata da komai na jikinta ya kwantar da ita ya rinqa aika mata da saqonsa yana tsotseta hakanan badon tanajin dadi ba yayi abinda zaiyi ya dagata yaje yayi wanka yana fitowa wayarsa tayi ring ya dauka da sauri jikinsa har rawa yakeyi ya kara a kunnensa yace “hello my love ganinan fitowa” kalmar ba qaramin girgiza nutsuwa da lfyr jikin Umaimah tayi ba ta zuba masa ido yanda yake ta sauri yanasa kayansa baiko bi takanta ba yayi ficewarsa ta miqe daqyar ta leqa ta window taga yanda yake wani gudu² ya shiga motarsa ya fice tana tsaye jikin windown wani malolo ya taso mata a zuciyarta yanzu duk wannan saurin da yakeyi saboda wata mace yakeyi yana ganin halin da take amma ya tsallake ya barta saboda buqatarsa ta biya.
Da wannan tunanin tayi wanka ta fito ta shiga kitchen ta dora tea ta dawo parlour ta zauna tana zama tajiyo kukan Shurafah ta miqe ta haura ta daukota ta dawo ta zauna har lkcn idonta bai daina zubar da ruwa ba daidai lkcn wayarta tayi Ring ta daga da sauri ganin number Aunty Jameelah tace “he... helo aunty yaushe zakizo?” yanda taji muryar yar uwar tata tasan ba lafiya ba tace “yadai meye ya faru Umaimah naji Daddy yace mijinki aure zaiyi saura kwana uku daurin auren hakane?" Ajiyar zuciya tayi tace “hakane Aunty Salman gdan Alh Musa zai aura....” katseta tayi da sauri tace “kutumar ubancan wannan tsinanniyar gantalalliyar yarinyar zai auro miki Umaimah kayyy Innanillahi wa innah ilaihir raji'un wannan wacce irin masifa ce ne Umaimah me kikayi masa haka?"
Cikin kukan da batasan yaushe ta fara ba tace “bansani ba Aunty wlh iyakar sanina banyiwa Abdulhameed komai ba Aunty meyasa rayuwa na zama karfa ne wacce batada rabon farin ciki meyasa kowacce masifa take fadowa kaina ne? Aunty meyasa su mama da Abba suka mutu suka barni Allah da nasan wannan muguwar rayuwar zan riska bayan mutuwarsu dana bisu mun tafi tare”........
*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[1/26, 8:07 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *G.U*
Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:
Daqyar Jameelah ta iya rarrashin Umaimah saboda yanda take kukan bilhaqqi da gsky tace “babu komai Umaimah ki kwantar da hankalinki kici gaba dayi masa biyayya kima kiyi hqr da duk abinda zakiji ko ki gani Umaimah da hqr da rashinsa taqinsu kadanne idan kuma kikayi hqr zaayi dake kuma shi zalinci baya tabbata indai Hameed yayi aurene ne saboda ya zalinceki da sannu zakiga sakayya batare da kinje ko inaba yauwa kuma nasan kinsan komai game da gdansu kishiyarki basu zama da kishiya balle ke da duk inda Hameed ya zauna bashi da zance sai naki bashida hira sai taki sannan ko badon wannan ba saboda kyawunki da quruciyarki Salma zata zafafa kishinta akanki to ke kiyi qasa da naki duk da kowa ma ya sani namu na gadone bama iya control dinsa idan ya motsa amma ki rinqa daurewa kina dagewa kina basarwa kada ki yarda mijinki da kishiyarki su gane raunin ki ta wajen kishi musamman kishiya Umaimah kada kiyi kuskuren nuna Mata ke raguwa ce sannan ki riqe Allah ki cire kasala ki rinqa tashin tsakar dare kina fadawa Allah damuwarki lkcn da kowa yake bacci da sannu Allah zai kawo miki mafita Umaimah wlh daga Daddy har Hajiya babu wanda yayi ammanna da auren nan kawai dai don babu yanda zasuyi dashi ne kinsan mijinki da murdadden hali akan raayinsa saboda haka ko kadan kada kiga laifinsu kuma kada kiga laifinsa shima ina zargin bayin kansa bane saboda nasan tarihin soyayyarsu da Salma tun zamanin quruciya ma baisota ba balle yanzu data zama abinda ta zama"
Kukanta take qoqarin tsayarwa tace “amma Aunty haka zanci gaba da zama dashi banida wani amfani a gurinsa sai lkcn biyan buqatarsa idan naqi ya gwadamin qarfi babu ruwansa da halin da zan shiga kawai shidai buqatarsa ta biya anya Hameed yana sona kuwa Aunty kamar yanda kike tunani?" Ajiyar numfashi Jameelah tayi tace “karki damu da wannan Umaimah nidai alfarma daya zan nema a gurinki duk rintsi kada ki yarda karatunki ya salwanta ki tsaya kaida fata wajen ganin kin gama karatunki ki fitar dashi daga zuciyarki Umaimah inada tabbacin duk ma inda yaje zai dawo gareki saboda kedin is naturally kinada qualities din da baduk mace ba”
Da wadannan kalaman ta rinqa rarrashin qanwar tata harta tursasa ta akan taje tayi masa girki batayi musu ba tana ajiye wayar ta tashi ta shiga kitchen ta fara shirya masa dinner tare da kunna karatun qur'ani saboda ragewa kanta quncin zuciyar da take ciki bayan ta gama ta shiga wani daki a qasan abin yaso bata dariya dakin guda kayan wasan Shurafah ne ajiyeta tayi a ciki ta nufi sama tayi wankanta tayi kwalliyarta me kyau tsari ta dawo parlourn ta zauna tare da daukowa Shurafah motar wasanta taci gaba da zagayawa a parlourn tanata debewa uwarta kewa sunata dariyarsu saidai idan lkcn sallah yayi ta tashi tayi ta dawo ta zauna haka har lkc yaja ta tashi ta shiga dakinta ta sake shiryawa cikin kayan baccinta tana tsaka da fesa turare ya shigo gdan yaga yanda ta gyara ko ina sai abin ya burgeshi Umaimah akwai tsafta komai nata kaf-kaf cikin tsari yunwa yakeji sosai saboda shi iya wuya bai yarda yaci abinci a waje ba indai ba qasar ya bari ba.
Dinning table ya nufa ya zauna yana bude abincin qamshi ya dakeshi ya lumshe idonsa ya bude tare da fara zuba abincin daidai lkcn ita kuma ta gama lallaba Shurafah ta sauko da gudu²n ta domin daukar wayarta tun tana saman ya qura mata ido yanajin wata muguwar faduwar gaba yarinyar komai nata daukar hankalinsa yake towai shi mene ma yaja raayinsa ga Salma har yake sha'awar aurenta ita ba kyau na azo a gani ba ita ba diri ba nagarta ba ita ba komai ba amma yanajin kamar zai zauce akanta amma dai ya sani koma me yakeji akan Salma baikai wanda yakeji akan Umaimah ba saboda duk inda yake a fadin duniya indai a cikin hayyacinsa yake to ita kadai yake tunawa.
Baiji qarasowarta ba saida yaji sautin sassanyar muryarta tace “sannu da zuwa" firgigit ya dawo hayyacinsa ya sakar mata murmushin sa me tsada ya lumshe idonsa tare da budewa daidai lkcn data bar gurin ta matsa kusada center table din ta dauki wayarta ta juya zata wucce ta tsinkayo muryarsa yana fadin “Hearty” tsayawa tayi cak ya taso a hankali ya sanya hanunsa ya tallafo faffadan hips dinta daya baje cikin blue din rigar baccin jikinta iya gwiwa yaja numfashi me qarfi yace “bazaki tambayeni meyasa naje nakai dare ban dawo ba” wani mugun yawu me zafi ta hadiye tare da kada kai tayi gaba zata tafi saboda batajin zata iya furta masa kalma daya me dadi a yanda takejin zuciyarta na tafasa idan ta ganshi sake ruqota yayi yace “naje gurin Salma ne akan tsare²n yanda bikin zai kasance so abin yazo unexpected babu wani shiri bazan samu damar yimata lefe ba shine tace na bata million daya da rabi tasai kayan fitar biki so naje na cira na bata shine nakeson kema ki fadamin abinda kikeso nayi miki?”
Yamutsa fuska tayi ta hadiye wani yawu me daci tace “na gde" daga haka bata kuma cemasa komai ba ta juya zata tafi ya sake ruqo hanunta yace “kamar kina sauri Babyn Uncle wai bakyason gani nane kome?” da sauri ta daga masa kai tace “eh hakane Abu Shurafah wlh banason ganinka jinake kamar na kashek....” da sauri ya hade bakinsu ya matseta a jikinsa sosai qirjinsa yana bugawa da sauri².
Sosai take kiciniyar qwacewa amma yawi qyaleta yaqi sakin mata baki saida yasha iya shansa sannan ya saki wasu hawaye masu zafi suka zubo masa yace “wannan kalmar ita Hajiya ta fadamin yanzun nan kema kuma kika sake maimaita min Umaimah nima wlh bansan meyasa nakeson auran nan ba nasani babu wata mace da nakeso da sha'awar kasancewa da ita a duk fadin duniya data wucceki ki yarda dani Umaimah aure na qaddara ce kuma kece kika jayo nasani badan kin gujeni ba da qila bazan hadu da Salma ba balle naji inason aurent....."
Daga masa hanu tayi tace “ya isa haka Abu Shurafah nasani kuma naji auranka qaddara ce kona yarda ko kar na yarda ba fasawa zakayi ba saboda haka yardata batada wani amfani amma nidai nidai nasan auranka ba qaddara bace son zuciyarka ne duk da haka inayi maka fatan alkhairi ka matsamin na wucce inada abinda yafi wannan surutun muhimmanci" tana gamawa ta fincike hanunta ta haura saman da gudu²nta bin bayanta yayi da kallo yana hadiyar yawu mace iyakar mace.
Daga murya yayi ya kira sunanta amma Ina ta shige dakinta ta datse yaja wani gwauron numfashi ya sauke ya koma gurin abincin ya rinqa turawa daqyar danma yanajin yunwa ne kawai Umaimah ta riga ta rikita masa lissafi ba dafaffan abinci yakeso ba danye yakeso kuma na jikinta, da wannan tunanin ya gama ya tashi ya shige dakinsa yayi wanka ya dauki remote control din qofar dakin nata ya fita ya nufi dakin ya bude ya shiga a saman sallaya ya sameta tayi sujjada tana kuka tana roqon Allah cikin larabcinsu na shuwa kuka takeyi sosai tana roqon Allah ya kawo mata dauki ya rabata da qaddararren auransa.
Miqewa yayi da sauri ya dagota zuciyarsa na tafasa baisan meyasa kowa ya juya masa baya akan auran Salma ne koda yake dama yasan haka zata faru amma baitaba tunanin zafin kishin Umaimah yakai haka ba baitaba tunanin zata nemi rabuwa dashi akan wannan qaramin dalilin ba..........
*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[1/27, 9:02 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *G.U*
Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan;09031307566:
Hadata ya fara qoqarin yi da jikinsa amma taqi yarda ta rinqa tureshi tana dukansa ta ko Ina tana mgn cikin yarensu tana fadin “ka sakeni Hameed ka sakeni na gaji da zalincinka Hameed nagaji dayi maka biyayya kana cutar dani Hameed ka sawwaqemin wannan masifaffen auren naka na tsaneka Hameed bazan iya cigaba da rayuwa dakai ba cikin wannan rayuwar da komai nayi maka ban iyaba baka yabawa bare na burgeka wlh Hameed nagaji da zama dakai ko ka sakeni ko kada ka sakeni sai nabar maka gdanka bazan yarda hqrna da kawaicina da kuma rashin gatana yasa ka debomin masifa ka kawomin ba Ina baka isa ba Hameed koda kuwa kai kadai ka saura namiji a duniya wlh yau saika sakeni idan ba hakaba zan baka mamaki mamakin da bazaka samu damar yinsa a duniya ba”
Sassauta murya tayi tayi qasa ta zame ta zauna tare da riqe qafafun sa ta dago ta kalli cikin idonsa daya kada yayi jajur saboda zafi da radadin kalamanta tace “Abdulhameed pls daivoce