Showing 75001 words to 78000 words out of 131968 words

Chapter 26 - GIDAN UNCLE COMPLETE HAUSA NOVEL BY UMMUH HAIRAN

10 Jul 2024

22474

qaramin cikinta daya fara turawa suna cewa “aunty Uncle yace kin kusa ki haifa mana qani mune zamu rinqa rainonshi muna goyashi muna tafiya mkrnta dashi" itadai saidai tayi yaqe wanda akace yafi kuka ciwo saboda Allah ya sani tana cike da nadama da danasanin abubuwan da shaidan yasasu aikatawa a baya qashi tunda cikin ya shiga wata na bakwai take fama da rashin lfy ciwon ciki da ciwon mara sunje asibiti da Hajiya aka tabbatar musu da kwanciyar yarinyar ne ba daidai ba saboda haka tana buqatar kulawa sosai kallon Dr Saleem tayi tace “to amma Dr ya lfyr abinda ke cikinta?"



Murmushi yayi yace “lfyr baby qlau Hajiya amma dai a qara kulawa" da wannan kalamin suka dawo gda Hajiya tanajin so da qaunar cikin jikin Umaimah wanda tasani bata tabajin haka akan yayan Sadiya ba kodan Umaimah jininta ce oho.



Ita kuwa Umaimah a ranta ji takeyi dama ace cikin ya lalace idan taji motsin cikin ji takeyi kamar ta bigeshi daga jikinta haushi da tsanar Hameed na nunkuwa a zuciyarta saboda badan shiba da rayuwarta bata shiga wannan gararin ba.



A kuma wannan dan taqin ne Sadiya tayi aure saboda ta bibiyi Hameed yana wulaqanta ta harta gaji ta hqr ta saduda ta auri wani abokin aikinta me Mata biyu saboda takurawar da babanta yayi Mata akan cewa saidai tabar masa gda bazai iya zama da ita suna hada kafada da matansa ba kasancewar babanta matansa uku.
Hakanan ta auri Alh Salisu badon tanasonsa ba saidon gudun korar karen da babansu yakewa duk wata yarsa bazawara da taqi aure yazo kanta musamman ita da kowa yasan ita ta kashewa kanta aure da masifa da zafin kishinta da kuma qin karbar qaddara ga uwa uba rashin daukan miji a bakin komai.



*************************



Tun farkon dawowar Umaimah gda Hajiya tayima Daddy mgn akan cigaba da karatunta to lkcn semester tayi nisa saboda haka ya biya mata Jamb ta zana ya Allah ya taimaketa ta samu abinda ake buqata ta zauna jiran lkcn da zaa koma hutu saboda komai na mkrntar an gama mata Skyline University ce Daddy ya biya mata.



Tun cikinta nada wata bakwai Hajiya tayima Hameed mgnr siyayyar kayan haihuwa yace Mata shi ya gama siyan komai da ake buqata Aunty Zarah zata kawo.
A cikin satin Aunty Zarah ta kawo kayan daya gigita tunanin kowa Kaka kam sallallami ta hau yi tana cewa “wannan yaro wanne irin mahaukaci ne ina zaakai kayannan haka saikace wanda zaa haifama yaya goma”



A haka kwanaki suka rinqa turawa ranar wata laraba da yamma Umaimah tana kitchen ita da Hajiya da titsetsan cikinta a gaba suna girki taji bayanta ya bada wata qara qass tare da riqewa tayi qasa da sauri tana dafe cikinta da bayanta tana fadin “way...yohhh uwata wayyoh ub...ana wayyoh Hajiya bay...ana cikina shikenan mutuwa tazo Hajiya ki yafeni🤣......


*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[1/20, 3:00 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *GIDAN UNCLE*



Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:



*PAGE THIRTY-SEVEN*




Kamota Hajiya tayi da sauri na hadata da jikinta tace “subhanallahi haihuwar tazo Umah bari mu tafi Asibiti" riqota tayi a jikinta suka fito parlourn inda Kaka take zaune tana duba jarida miqewa tayi da sauri daidai lkcn da Hameed din ya shigo parlourn ganin yanda Umaiman take yatsina ana rirriqeta ai baisan sanda yayi watsi da ledar shop din dake hanunsa ba ya nufi Umaiman da gudu ya ruqota Hajiya tace “yawwa maza sata a mota haihuwa ce..."



Ai bata I rufe bakinta ba ya sunkuceta yayi waje har yana tuntube yanakiran sunanta, sata yayi a sit din baya yashiga ya tada motar bai jira fitowar su Hajiyan ba saboda gani yake zata bata masa lkcn yaja motar a mugun guje ya fice daga gdan.



Suna fitowa sukaga tashin qurar motarsa suka shiga wata driver yaja suka rufa masa baya bai iya hqrn kaita asibitin nassarawan ba saboda nisansa yake gani daga unguwar tasu wani asibitin kudi ya nufa aka karbeta aka shiga da ita larbour room sai bayan an shiga da ita sannan su Hajiya suka qaraso Hajiya ce tabada katinta tare da fada musu matsalarta shikam gogan sai safa da marwa yake yana hada gumi kamar shine yake naqudar duk sanda ya juyo nishinta shima sai yayi kamar shine me haihuwar lamarin ba duk da halin tararrabin dasu Hajiya suke ciki basu kasa yimasa dariya ba amma shi ko a jikinsa bin likitocin kawai yakeyi da suketa kaiwa da komowa idan kuwa yajisu shiru ya rinqa leqe kenan ta window.



Cikin ikon Allah baa bata wani dogon lkc ba Allah ya sauki Umaimah lfy ta haifo kyakkyawar yarta mace me kama da ubanta da uwarta dake dama kamar tasu dayace kowanne ka kalla sai kace yarinyar tana kama dashi tsakanin Hameed din da Umaimah.



Kukan jaririyar ne ya ankarar dashi aikuwa tun kafin a bashi izinin shiga ya danna kai dakin ya hango Babyn tanata wutsil² a hanun wata nurse ko takan Babyn baibi ba ya nufi inda Umaiman take ya tsugunna yace “wayyohhh Allah Babyn Uncle sannu kinsha wahala ko da wahala haihuwa ko? Ni nama yafe kawai wannan kadai ta ishemu”



Wani kallo da takeyi masa ne yasashi miqewa a sanyaye ya matsa inda nurse din take riqe da Babyn take shiryata ya tsaya ya zubawa yarinyar ido kawai sai yaji wasu hawaye sun zubo masa Allah kenan duk cikin yayansa babu wacce take tsananin kama dashi kamar jaririyar ajiyar zuciya yayi ya miqa hanu ya karbeta daidai lkcn dasu Hajiya suka shigo dakin.
Da sauri Hajiya ta nufi Umaimah ta dagota ta nufi toilet din da taga wata nurse ta fito tace “akwai ruwan da zata gyara jikinta?"


Amsawa tayi da “eh nama hada mata gashi can a ciki" shiga sukayi Hajiyan ta gasa mata jikinta sannan suka fito ta zaunar da ita a gefen gadon dagyar saboda ta dunku kamar qwarya sai a lkcn Hajiya ta samu damar daukar jikar tata da taketa wawuran abinci ta zuba mata ido kamarta da ubanta lkcn yana jariri har tayi yawa.



Hakanan suka yini a asibitin Hameed yana liqe dasu suna zuwa Hajiya dakinta takai Umaimah tana mata sannu har yanzu tana maqale da jikarta saida ta bawa Umaimah abinci da tea tasha sannan ta dora mata babyn a cinyarta tayi murmushi tace “yarinya kyakkyawa amma kun bata mata nasaba saboda son zuciyarku"



Hameed ne ya dago ya kalleta ya kalli Umaimah da kanta yake qasa yace “muma ba muso hakan ba Hajiya komai yana faruwa ne bisa buwaya da ikon ubangiji ku daina zargina wlh ba haka nakeba rabon wannan yarinyar zatazo a hakane yasa kika takura saina saki matata a halin inasonta tanasona kuma mun riga mun zama abu daya bazata iya rayuwa babu niba nima bazan iya rayuwa babu ita ba Hajiya ku taimaka ku dawomin da matata tunda ta haifemin abinda ke cikinta"








*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[1/20, 7:57 PM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *GIDAN UNCLE*



Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:




*PAGE THIRTY-EIGHT*




Miqewa Hajiya tayi ta zugewa Umaimah rigar jikinta ta sanya hanunta ta ciro nononta ta dago yarinyar ta sanya mata a bakinta yarinyar ta kama tana tsotsa ya zubawa nonon nata ido yanajin wani shauqi da feeling na bijiro masa da sauri ya miqe ya fita daga dakin don ya fahimci zamansa zai iya haifae da matsala ko wanne lkc zai iya kai hanunsa ya cafki nonon ya taya yartasa sha.



Gidansa ya nufa yayi wanka sannan ya fara sanar da abokan arzikin sa anyi masa haihuwa matarsa ta haihu harda hotunan da yayi da bebyn ya dora a status dinsa na WhatsApp da Facebook aikuwa ya samu addu'a sosai zama yayi dirshen yana kallon bebyn da yayima huduba da sunan Hajiyansa Zulaiha yana kallon hoton yana hawaye yana Istigifari nadama yake da zuciya me tsarki tabbas ya aminta so masifa ne saboda sone umul aba'isin faruwar komai tsakaninsa da qanwar tasa amma meye ya sabbaba hakan? “Hajiya” ya fada a fili tare da cewa “itace taja mana komai amma yanzu laifina suke gani saboda nine mara gata”



Wayarsa ya dauka a karo na ba adadi ya kira layin Umaimah amma a kashe yasani koda a kunne take ba dagawa zatayi ba saboda ta dade da ajiyeshi da rayuwarsa a gefe gashi shikuma sai yanzune ma yake qara gasqata cewa soyayyarta itace take sarrafa rayuwarsa komawa yayi ya kwanta a kujera ya zubawa hotonsu ido lkcn farin cikinsu nanan bai gusheba shi abin ar mamaki yake bashi yanda yake hangen tsantsar qiyayyarsa a idon Umaimah Umaimah da a baya yake sarrafata da zuciyarta yanda yake so.



Da wadannan tunane² ya kwana da safe ya tashi ya shirya domin tafiya aiki saida ya fara zuwa yaga lfyr Umaimah da bebynsa daya laqabawa Shurafah sannan ya haura sama gurin Daddy daya dawo daga tafiya jiya da dare suka gaisa yayi masa barka kamar abin arziqi sannan yace.



“Alhmdllh babana Ina tayaka murnar samun qaruwar da kayi taya mace naji karar da kayiwa mahaifiyarku ka kyauta daka sanya sunanta wa baiwar Allan nan Shurafah so kamar yanda na fada maka lissafin da mukayi a baya zai canza ne bayan haihuwar Umaimah to alhmdllh ta sauka lfy saboda haka yanzu zabi biyu gareka kodai ka karbi yarka ka nemi wacce zata shayar maka da ita ko kuma ka rinqa biyan uwarta take shayar maka da ita"




Mamaki ne ya kusan kashe Hameed wannan fah shine tsugunu bata qareba ansai da biri ansai mage.
A sanyaye ya dago yace “amma Daddy na dauka cewa Umaimah koba itace ta haifi Shurafah ba ita me riqemin itace ta shayarmin da ita batare data nemi ko qwandala daga gurina ba...."


Daga masa hanu Daddy yayi yace “ai wai da take uwar tata shiyasa muka fada maka haka dama da ace ba ita ta haifaba ma aida mu da kanmu zamu bata ta shayar maka da ita saboda haka zabi ya rage naka idan ka yarda zaka rinqa biyane to wajibine duk wata ka kawo min 5 million na ciyarwa"



A matuqar mamakance ya dago yace “5 million fah Daddy me Shurafah zataci da har zata cinye 5 million a duk wata Daddy duk mutanen dake gdannan ma bazasuci 2 millions a wata ba balle jaririyar da aka haifa jiya?"



Shiru Daddy yayi ya dauki wayarsa ya fara latse² bayan yan sakanni aka daga yace “kuzo dukkanku inason ganinku a parlourn sama" yana fadin haka ya kashe wayar yaci gaba da duba wayarsa yana murmushi irin nasu na manya,
Shigowa sukayi suka hada ido ita dashi gabanta ya fadi sosai saboda wani kyau da taga yayi mata duk da ramar da yayi.



Daqyar ta iya samun guri ta zauna saman tumtum saida Daddy ya gama danne²nsa yace “Hajiya bashi yarsa" dagowa sukayi da sauri musamman Umaimah da taji mgnr kamar dirar kwarankwatsa a kanta.
Miqawa Hameed yarinyar Hajiya tayi jikinta a sanyaye hanunsa na rawa ya karba yana cije lebe wasu hawaye masu zafi suka zubo masa ya kwantar da yarinyar da taketa sharar baccinta a cinyarsa ya dago ya kalli Daddy yace.



“Na yarda zan rinqa badawa Daddy ka taimakeni kabar yarinyar nan a gurin mahaifiyarta idan na tafi da ita bansan ya zanyi da ita ba ko kuma ka mayar mana da aurenmu mu raini yarinyar nan cikin kulawar da duk wani da me gata yake samu a gurin iyayensa....” daukeshi da mari Daddy yayi yace “zaka tashi ka barmin gurin nan da shegiyar yarka kosai naci mutuncinka"



Miqewa yayi a matuqar sanyaye ya matsa gaban Umaimah da take kallon Daddyn tana mamakin furucinsa kalmar shegiyar daya Kira Shurafah da ita tafi komai dukanta ya dora mata babyn a cinyarta cikin kuka me ban tausayi yace “Koda kowa na duniya zaiqi Shurafah bai kamata ta rasa gata biyu ba nawa da naki Umaimah ni namiji ne banida nonon dazan bawa Shurafah ta rayu dashi kada kibada qofar rabaki da yarki da qaddara ta qadarta mata zamowa me rangwamen gata duk da nasani a gurin gama garin mutane take me rangwamen gata amma a gurina me cikakken gatace saboda na yarda itadin qaddara tace Umaimah babu wanda ya isa yayi maka wannan kyautar bayan Allah kuma bakida tabbacin sake samun wani bayan ita ta yuwu ita kadaice rabon dake tsakanina dake karki manta Umaimah kinsani komai yana faruwa ne bisa buwayar buwayi gagara misali badon hakaba dasai kice ya zaayi muna matsayin ma'aurata mu samu yarda bata sunnah ba to wannan kadai ya isheki misali ganin damarsa ne hakan ta faru Umaimah na roqeki kada kibada qofar banzatar da rayuwar yarinyar da bataji ba bata gani ba laifi nawane naji ayimin hukunci a kankin kaina amma kada ya shafi Shurafah dan Allah Umaimah....."



Wata tsawa Daddy ya sake doka masa yace “wlh tallahi Hameed idan baka bacemin da yarinyar nan a gurin nan ba sainayi maka abinda baka taba tunani ba” jikinsa har bari yake ya miqe ya dauki yarinyar ya rungume a qirjinsa yana wani kuka mecin zuciya ya juya ya kalli Daddy yace “hakan ma na gde daka bari aka raini cikinta a gidanka amma kasani Daddy wannan zata zama rana ta qarshe da zaka rasani nima zanbar maka gdanka kuma Shurafah zatabar maka gdanka bari na har abada"



Yana fadin haka ya juya zai fice Umaimah tayi saurin riqo qafarsa cikin kukan tashin hankalin abu biyu rabuwa da yarta qwaya daya tak a duniya tace ““Ina neman alfarma daya Daddy baa matsayina na mahaifiyar Shurafah ba a matsayina na yar'uwar mahaifinta ta jini wacce zan iya fansar rayuwata da tasa ina neman izinin shayar masa da yarsa batare dako sisin sa ba Daddy na roqeka kayimin wannan alfarm....."



Daka mata tsawa Daddy yayi yace “wlh baki isaba Umaimah saidai ki tashi kibishi tunda kin zabi farin cikinsa akan nawa kin fifita darajarsa da matsayinsa akan nawa to kitashi maza ki hada kayanki kibisa bana buqatar ganin shegiyar yarinyar nan a gdannan" bata iyajin kalmarsa ta qarsheba ta toshe kunnenta tare da sakinsa ta fashe da wani gigitaccen kuka me firgita zuciyar me imani tanaji tana gani ya juyo ya kalleta shima yana kuka daidai lkcn yarinyar itama tasa kuka da alamun nono take buqata amma ya juya ya fice da sauri ta miqe tana hada hanya zata bishi Daddy ya ruqo hanunta ta kuma rushewa da kuka tace.



“Tun safe Daddy Shurafah batasha nono ba ka taimakeni kabarni nabata koda shine na qarshe da zatasha daga jikina......" Dauketa yayi da wani gigitaccen mari tayi qasa ta zube yaraf ta qara dora hanunta a kanta ta rushe da kuka tace “shikenan Daddy ka rabani da yata qwaya daya tak a duniya...." Miqewa ta sakeyi da gudu ta nufi window daidai lkcn da Hameed ya kwantar da yarinyar a kujerar me zaman banza ya shiga ya tashi motar a guje yabar gdan har lkcn kuka yakeyi.



Zamewa tayi ta zauna a qasa tama manta da dinki akayi Mata soyayyar da da mahaifi ta mantar da ita ciwon komai sai ciwon rabuwa da yarta, saboda tsabar kuka har muryarta ta dashe Daddy ya tsallake ta ya shige dakinsa inda ta miqe tana hada hanya ta fita daga dakin ta fara taka matattakalar benen amma bata iya sauka ba jiri ya debeta tayo qasa luuuuuu daga saman ji kake tim ta fado tsakiyar parlourn qasan kamar matacciya Hajiya dake zaune take gursheqen kuka ta taso da gudu hakan yayi daidai da fitowar Kaka dake baccin asara a daki......







*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[1/21, 9:52 AM] UMMUH HAIRAN CE...✍🏻: *GIDAN UNCLE*



Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:



*PAGE THIRTY-NINE*



Da gudu sukayo kanta cikin tashin hankali Hajiya taja da baya tace “mun shiga uku Kaka jini ta bakinta da hancinta kinga wani yana fita ta qasanta zata mutu Kaka anya Adamu bashida mental problem kuwa yaraba uwa da yarta a daidai wannan lkcn da kowacce uwa tafi buqata da tausayin danta Kaka ina Hameed zaikai Shurafah yanzu idan Umaimah ta mutu akan wannan dalilin me Adamu zaice da ubangiji?"



Riqeta Kaka tayi tace “me..mekike cewa Zulaiha maza ku tafi Asibiti ina zuwa nima" tana fadin haka tayi sama da gudu gurin Daddy ta fara buga qofar kamar zata balleta fitowa yayi ya bude ta cukuikuiyeshi tace “ina ka bari Hameed ya tafi da yarinyar nan to wlh ka fita da gaggawa ka nemoshi ka karbowa Umaimah yarta kafin fushina ya hau kanka ku baku da hankali da tunani kullum baku da aiki sai yanke hukunci cikin fushi"



Tana fadin haka ta sake juyowa ko mayafi babu a jikinta ta fito waje ta tsari taxi ta sanar dashi inda zai sauketa suna tafiya tana cewa dashi ya qara gudu cikin saa tana zuwa qofar gdan nashi dake FRW Layout ta hangi motarsa da wata motar a qofar gdan ta cillawa driven 1k tayi ta fada cikin gdan a guje amma me sai ta rinqa jiyo wani kakari yana fitowa daga parlourn da sauri tasakai ciki idonta kan Shurafah ya fara sauka dake dauke hanun Sarah tanata kukan neman uwa shikuma yana kwance a qasa sai fitar da dafara yakeyi mijin Sarah yanata bashi taimakon gaggawa tare da danna masa.



Cikin tashin hankali Kaka tace “mun shiga uku mukam wannan wacce irin masifa ce ta nufomu ne" daidai lkcn Daddy ya shigo don cika umarninta.



Dafe bango yayi da sauri tare da furta “Innanillahi wa innah ilaihir raji'un" mantuwa daya Daddy yakeyi a rayuwarsa shine matsalar zuciyar da aka haifi dannasa Hameed da ita.
Da sauri ya qarasa inda yake kwance yana fitar da wani wahalallan numfashi ya rungumoshi yana jijjigashi yana cewa “Abdulhameed! Abdulhameed!! Abdulhameed!!! Babana ka tashi kada ka fada a bakin mala'iku kada muyi irin wannan rabuwar dakai kada ka mutu kabarni babana ba qinka nakeyi ba wlh inasonka"



Kuka yakeyi sosai kamar qaramin yaro yana girgiza dannasa Kaka itama tana kuka tace “Shikenan ai kun kashesu kun huta saura yar itama gatanan Adamu kasa wuqa ka yankata sai ayi jana'izarsu gabadaya su ukun kukuma ku rayuwa a duniyar ku dawwama babu jarabawar ubangiji amma inaso ka sani nidai bazan yafe maka haqqi yarannan ba kuma Allah bazai yafe maka ba saboda shugabanci ba hauka bane Allah ma daya haliccemu munayi masa laifi ya yafe mana balle kai abin halitta Mai tarin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login