Showing 9001 words to 12000 words out of 35486 words

Chapter 4 - ƘADDARA-CE_-By-Salma-Ahmad-Isah

05 Jul 2024

6333

tare da zaunawa. Sannan ya furta abin da Mima ke zaton zai fa?a ?in.

"?aramar mara kunya!"

Cike da mamakin halin yayan nata Mima ta yi serving Daddy. Ita ta rasa sai zuwa yaushe za ta girma a rashin kunyar nan. Kullum a ?arama take, daga ta masa abu zai ce mata ?aramar mara kunya, ko yace zai sauya mata kammani. Words ?insa ke nan.

"Daddy zan iya ganinka a falonka?"

Fa?in Mu'az yana mi?ewa tsaye. Bayan da ya tashi plate ?in da ya cika da boiled yam da kuma egg sauce daga aiki. Idan har abinci ya yi da?i ba za ka samu ragowarsa a plate ?in Oga me cika aiki ba. Daddy ya dube shi.

"Maganar na bu?atar privacy?"

"Yeah Daddy"

Ya amsa yana wanke hannunsa a sink. Kafin ya juyo yana kallon Mummy dake kallonsa.

"A kan mi ye?"

Mummy ta tambaya. Kafin ya kai ga bata amsa Daddy ya amsa mata.

"Ya ce maganar tana bu?atar sirri. Idan ba haka ba ai kin san da ya fa?eta a nan ko?"

Mummy ta yi wa Mu'az kallon ban yarda da kai ba!. Kafin takalli Daddy ta ta?e baki tana juya spoon a cikin teacup ?inta.

"Mu'azzam ka je falon ka jirani. Yanzu zan kammala na zo"

"Okay"

Ya fa?i yana nufar ?ofar falo. Fita ya yi, inda ya bi ta compound ya nufi sashin Daddy. A falon farko ya zauna yana jiran zuwan Daddy. Kuma Daddyn bai jima ba sai ga shi ya zo.

"Wace magana ce that needs privacy Mu'zzam?"

Daddy ya tambaya while sitting. Mu'az ya gyara zamansa yana fa?in.

"Daddy a kan Mariya da Faruk ne?"

Naman goshin Daddy ya tattare wuri guda cike da mamaki, sannan yace.

"Mariya da Faruk kuma? Me yake faruwa? Ko wata matsalar suka samu?"

"Ban sani ba Daddy. Amma na lura da kamar akwai matsala tsakaninsu. Na gane hakan ne ta hanyar halin damuwa da yawan tunani da Kaigama yake shiga. Kuma duk yanda na kai da bugun cikinsa dan ya fa?a min ya ?i fa?a. Saboda mugun zurfin ciki irin nasa. Amma ni na tabbatar akwai matsala a tsakaninsa da Mariya!"

Daddy ya yi shiru yana sosa ha?arsa dake ?auke da ?an gajeren gemunsa irin na masu rayuwa cikin hutun nan. Can kuma ya dubi Mu'az yace.

"In dai kuwa haka ne ya kamata a ji abin da yake faruwa"

"Haka ne Daddy. Sai ka kiransu su duka, dan su zo ka ji abin da ke faruwa a tsakaninsu, wata ?ila idan kai ka tambaya za su fa?a maka. Kuma ka ga sai a sasanta su!"

Daddy ya yi murmushi yana kallonsa.

"Shi yasa nake jin alfaharin cewa bayan na mutu kai ne za ka gajeni. Saboda a bayan bau??a??un ?abi'unka akwai halaye masu kyau. Ha?i?a ka yi tunani me kyau. Allah ya maka albarka, ya kuma baka ladan zama sannadiyyar gyara sunnar fiyayyen hallita. Tun da kai ka ?i raya sunnar!"

Mu'az ya yi murmushi yana shafa gajerar sumar kansa me ?arfi kamar ta sauran Africans. Amma da yake tana jin gyara kuma ba ya tarata sosai sai ta yi kyau abinta.

"Daddy! Zan yi aure fa. Kawai dai ni harkar 'yan matan ce bata gabana. Bana son raini Daddy, 'yan matan yanzu kuma sun iya raini!"

(MJ ne ya fa?a. Nii dai ba ruwana!)

Daddy ya dara.

"Allah ya baka mace ta gari, sannan ya baka wadda za ta yi ha?uri da kai, ya kuma baka wadda ba za ka zalunceta ba. Sannan ya baku zuri'a ta gari!"

Mu'az ya mi?e tsaye yana murmushi.

"Oh lord of mercy!. Irin wannan addu'a haka Daddy?"

"To ai baka ce amin ba"

"Amin Daddy"

Ya amsa yana fita daga falon. Kai tsaye ya nufi sashensa dake can wani gefe da ban na gidan. Falo ?aya ne da ?aki sai bathroom. Tun daga falo ya cire rigar jikinsa. Dan shi da riga kamar ma?iya haka suke. Idan ka ga ya saka riga fita zai yi.

Amma muddin zai zauna a sashensa to fa ba zai sakata ba, a cewarsa wai takura shi take. Yana shiga ?aki ya aje rigar a kan bed. Sannan ya kunna ki?a ya yi zamansa a ?akin.

Saboda yawan jin ki?a ?abi'ar sojoji ce. Bai haura mintina biyar da shigowa ?akin ba aka kira wayarsa. Hakan ya sa ya rage sautin ki?an. Ya ?aga wayar yana wani ha?e rai, kamar wanda aka cewa ya sha magani ba ruwa. Kuma hakan ya samo asali ne daga ganin sunan me kiran.

Yasmin. Wata yarinya ?aya tilo da ta nace a duniya kan shi take so. Kuma cikin wani ikon Allah sai aka yi rashin sa'a shi babu sonta a tsarin rayuwarsa. Dan yace shi bata masa ba, saboda ta cika naci da yawa.

"Yanzu abin da kake min ka kyauta Mu'az?"

Muryarta me sanyi ta fito daga cikin wayar. Ya lumshe idonsa yana murza goshinsa.

"Me na yi kuma?. Ko da yake, ai ba'a rasa nono a ruga. Da ma ni kullum me laifi ne!"

Daga ?ayan ?angaren, Yasmin ta girgiza kanta.

"Ko ka?an Mu'az ba haka ba ne. Ni dai kawai abu ?aya nake so daga gareka. Kuma shi ne na kasa samunsa har yanzu. Kulawa ita ce abin da nake bu?ata Mu'az. Ya kamata ka ri?a nuna cewa ina da muhimmanci a cikin rayuwarka!"

"Me ya sa zan miki ?arya?"

Cikin rashin fahimta Yasmin tace.

"?arya kuma? What do you mean?"

"Yes, ?arya. Did you want me to be saying that i love you?. Bayan kuma a zahiri ba haka ba ne"

?walla ta zubo daga idon Yasmin.

"Mu'az!"

Ta kira cikin sanyin murya.

"Na'am"

Ya amsa.

"Ina so na tambayeka abu ?aya"

"Fa?i, ina ji"

"Mu'az kana sona, ko a'a?"

Kai tsaye yace.

"Bana sonki Yasmin. Ban ta?a sonki ba, kuma bana tunanin fara sonki ko da a nan gaba"

Cike da ba?in ciki Yasmin ta kashe wayarta. Yana jin ta sau?a a layi ya cilla wayar kan gado. Sannan ya ?ure Volume ?in wa?ar da yake ji hankalinsa kwance kamar tsumma a randa. Kamar ba shi ne ya gama tarwatsa zuciyar wata yanzu ba.

_Share fi sabillilah??_

------------------------

_I have told you that KADDARA CE! Isn't free!_
_If you want to subscribe pay ?300 to._

5487270431
Salma Isah
Monie point

And send the evidence of payment via 08130172792.

*Daga al?alamin Salma Ahmad Isah??.*
*CANDY CE??.*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*?ADDARA CE!*


*(c)SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY??*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_


*04*


*Unguwar Fantai, Ha?ejia local government, Jigawa state.*

MAIMUNA POV.

Su uku ne jere a bakin titi. Kuma ko wacce a cikinsu kayan siyarwarta ne a gabanta. ?aya tana suyar awara, ?aya tana soya wainar fulawa, sai kuma ita da bokitin kununta ke aje a gabanta.

Tun daga nesa ta hangi kawunta, ?anin mahaifinta wato Kawu Barau. Duk da duhun magariba da ya fara sau?a bai sa ta kasa gane shi ba. Baki ta washe ta mi?e tsaye tun kafin ya iso inda suke. Kuma shi ma har ya iso inda suke murmushi yake.

"Kawu ina wuni!"

"Lafiya ?alau me sunan Hajja"

Kawu Barau ya amsa yana kallon tilon 'yar ?an uwansa. A lokacin ya lura da hannunta na dama dake ?auke da tabon ?una. Lokaci guda fara'ar kan fuskarsa ta yi balaguro.

"Me sunan Hajja ya aka yi kika ?one?"

Maimuna ta kalli hannunta, sannan ta kalli kawu tana fa?in.

"Auwwa ce ta ?onani rannan. Amma ai ya fara warkewa, saboda Mummynsu Maryam ta kaini asibiti, kuma har magunguna ta sai min"

Cike da tausayawa Kawu ya girgiza kansa yana fa?in.

"Wa cece kuma Mummyn su Maryam?"

"Wannan ?awar tawa, jikar tsohon Kaigama"

"To to. Na gane, 'yar gidan Bara'atu ko?. 'Yar Alhaji Haruna Kaigama me rasuwa, ?anwar Alhaji Bello Kaigama na yanzu!"

Maimuna ta gya?a masa kai.

"Amma ko ta kyauta. Allah ya biyata da gidan aljanna... Amma baki fa?awa Hajja ba?"

Ta yi saurin gya?a masa kai. Dan bata fa?awa kakar tata ba. Saboda a tsakanin kwanakin ba ta je gidanta ba. Kuma ko ta je ma ballale ta fa?a ba idan har ba tambaya Hajjan ta yi ba.

"To Allah ya kyauta. Ya saka miki da abin da Auwwa take miki. Ki ci gaba da ha?uri kin ji ko me sunan Hajja?. Allah na sane da ke, kuma zai kawo miki ?arshen wannan wahalar taki. Ki ci gaba da addu'a. Kan Allah ya baki ikon cinye wannan jarabawar da yake miki"

Fa?in Kawu Barau yana lissafo 'yan ku?a?en da suka sa aljihunsa yin nauyi a safiyar yau. Cike da damuwa Maimuna ta gya?a masa kai.

"To Kawu. Inshallah zan yi"

"Kar?i wannan ba yawa. Na san magungunanki sun ?are, dan wallahi suna raina, shi ya sa na kasa sukuni har sai da na samo ku?in siyansu, dan na san a yanzu lokacin sanyi kin fi bu?atarsu"

Maimuna ta yi murmushi tana girgiza masa kai.

"Ai duka Mummy ta siya min har da folic acid da palludrine"

Cike da mamaki Kawu ya kalli ku?in hannunsa, sannan ya ?ara mi?a mata.

"Duk da haka dai ki kar?a, ba zaki rasa amfanin da za su miki ba. Ko sabulu kika siya kika wanke kayanki ai kin rage"

Maimuna ta kar?i ku?in hanu biyu, tana kallon kawunta da yalayen idanuwanta.

"Na gode Kawu. Allah ya ?ara bu?i"

Kawu ya yi murmushi. Sannan ya mata sallama ya ?ale kekensa ya nufi gida. Kasancewar tun bayan rasuwar matarsa bai sake yin wani auren ba ya sa yake zaune tare da mahaifiyarsu. A soro ya jingine kekensa, sannan ya yi sallama ya shigo cikin gidan. Inda ya iske mahaifiyarsu Hajja, zaune a tsakar gida, da alamun alwala ta yi, dan ga buta nan aje a gabanta.

"Barau an dawo?"

"Eh Hajja. Na dawo"

Hajja ta mi?e tana fa?in.

"To sannu da hanya"

"Yauwwa Hajja"

Daga haka ta shiga rumfar dake gidan, ta ?auki hijabinta dake aje a kan sallaya. Ta saka ta tayar da sallah. Yayin da Kawu ya kama ruwa, sannan ya yi alwala ya fita masallaci.

Sanda ya dawo Hajja na zaune a nan rumfar tsakar gidan tana jan carbi. Zama ya yi a kan kujera 'yar tsugguno yana jiran ta kammala. Kuma sai da ta kammala ?in ya fa?i abin da ke bakinsa.

"Hajja magana nake so mu yi a kan Me sunanki!"

Hajja ta aje carbin hannunta tana tattara hankalinta gare shi, jin batun magana a kan tilon jikarta.

"Me ya samu Maimunatun?"

Cikin damuwa Kawu ya tsara mata abin da Auwwa ta yi wa Maimuna, sannan ya ?ara da.

"... Ni Wallahi dan de kin ?i ta tawa ne, tun yarinyar nan tana ?arama na so ta dawo wurinki da zama, amma kika ce can shi ne dolenta, dan haka ba za ta dawo nan ta zauna ba, yanzu bayan talla da Auwwa ke ?ora mata har da su hukunci da wuta take mata, ya kamata mu yi wani abin a kan lamarin me sunanki Hajja. Ko da wannan cutar dake damunta aka barta ya isheta ?addara, ballantana a ?ara mata da izayar matar uba!"

Hajja ta ci gaba da kallonsa har ya kai aya, sannan tace.

"Barau! Ba wai na ?i amincewa da shawararka ba ne. A'a, ni akwai abin da nake hangowa. Yanda Auwwa take da masifar son abin duniya za ta iya cinyewa wannan gidan. Bayan kuma shi ne ka?ai gadon da mahaifinsu ya bar musu ita da Gambo. Ina da tabbacin idan har Maimuna ta bar gidan nan Auwwa da ?anta za su iya mallake mata gado. Kuma ko ba komai ?a a gidan ubansa ya fi daraja, idan tana can ?in ita kanta sai ta fi jin cewa a gidan ubanta take!"

Kawu ya yi shiru. Can kuma yace.

"A gaskiya Hajja ni na fara tunanin yi mata aure. Dan na lura da auren shi ka?ai ne zai ku?utar da ita daga wanna ba?ar azabar da take sha!"

Hajja ta girgiza kanta.

"Barau kenan! A auren yanzu masu lafiya ma ba auruwa suke da da?in rai ba. Ballantana ita da take da jinya. Jinyar da iyaye ma kan guji 'ya'yansu idan suna ?auke da ita, saboda gudun wahala, ballantana kuma miji. Kuma a irin auren yanzu ba na jin akwai wanda zai iya kula da Maimuna. Ka sani ba sai na nanata maka ba cewar cutar da Maimuna ke da ita na matu?ar bukatar kulawa. Kuma fa ni tun da nake da ita ban ta?a ji tace yau ga wani saurayi yace yana sonta ba, saboda kawai tana da sickler!"

Hajja ta ?arasa maganarta a raunane. Saboda tausayin jikarta dake ?ara kamata. Shi dai Kawu shiru ya yi kawai, dan a zahirin gaskiya ya fara gajiya da abubuwan da Auwwa takewa 'yar ?an uwansa. Kuma yana ganin kamar lokacin da zai ?auki mataki ya yi.



MARIYA POV.

Zaune take a kan kujerar falo. Ta saka Hilal dake wasa a cikin car toy ?insa a gaba tana kallo. Kamar ta samu tv, a hankali ta ciro yatsun hannunta biyu da ta cusa a cikin gashin kanta.

Sannan ta gyara zamanta tana kallon yaron, sai kuma ta kai hannunta saitin da motar wasan nasa take. Sannan ta motsa hanun nata. Na take motar ta iyo gabanta kamar yanda ta motsa hanun nata.

Kallon yaron ta ci gaba da yi, kamar yanda shi ma yake kallonta. Sannan a hankali ta ?aga hannunta na dama, ta saka a cikin sumar kansa me laushi, sannan ta ciro gashin kansa da mugun ?arfi. Amma kuma ko gezau yaron bai yi ba.

Ya yi shiru kawai yana kallonta, hannunsa ri?e da rattle yana karka?awa. Gashin ta ?aga tana kallo. A take ?wayar idonta ta sauya kala zuwa ja. Sannan ta kalli Hilal, ta bu?e baki da shirin yin magana, fi?o?in ha?waranta na sama suka ?an ?ara tsayi ka?an.

"Na gode Hilal. Saboda da ban haifeka ba da ba zan zama ta hannun daman shugaban bayin shai?an ba. Ina sonka!"

Ta ?arashe tana shafa gefen fuskarsa. Shi dai kallonta yake kawai, kamar me fahimtar abin da take fa?i. Mariya ta janye hannunta daga kansa, sannan ta yi amfani da ?arfin tsafinta ta tura car toy ?in nasa inda take da.

Ta mi?e ta fita daga falo, ta zagaya bayan gidan, sai ta tsaya ta waiga hagu da dama, sanna ta rufe idonta, ta ?ora hannunta a bayan wuyanta, inda tambarin ?ungiyarsu ta bayin shai?an ke zane a wurin. Sannan ta furta.

"Mishk baksh hushk!"

Bata kai ga rufe bakinta ba wani farin matashi ya bayyana a gabanta, sanye da jajayen kaya. Idonta ta bu?e ta kalle shi, sannan ta mi?a masa gashin Hilal.

"Sa?o ne zuwa wurin Wahash!"

Matashin ya kar?i silin gashin guda ?aya. Sannan ya kalleta.

"Sa?o zai isa ga shugaban bayin sha?an!"

Yana gama fa?in hakan ya ?ace ?at kamar almara. Tunawa da cewar yanzu haka ta kusa zama ta hannun daman Wahash ya sa ta yi murmushi. Sannan ta saka yatsun hannunta biyu cikin bakinta, ta fito da reza sabuwa daga ?asan harshenta. Cike da nisha?i ta shiga juya rezar tana murmushi.

Har ta koma falon ta zauna. Bata da?e da zama ba wayarta ta shiga ringing, ganin Daddy ne me kiran ya sa ta ?aga tana saita nustuwarta.

"Barka da safiya Daddy. Ina kwana!"

Ta gaida shi cikin sanyinta. Kuma cikin kamalarta dake burge kowa da ita. Daga ?ayan bangaren Daddy ya amsa sallamar, sannan ya fa?i abin da ya sa ya kirata.

"Yau da daddare ina son ganinku ke da mijinki!"

Ta tatare girarta wuri guda. Zuciyarta na raya mata ko dai Faruk ne ya je ya kai ?ararta?. Sanin zurfin ciki irin nasa ya sa ta kore wanna zargin, dan tana da ya?inin cewa ba lalle ace ko Hajiyarsa ta sani ba ballantana Mu'az ya sani, har a je ga kan Daddy.

"To Daddy, bari na sanar da shi"

"A'a, ba sai kin yi hakan ba. Dan na fa?awa Mu'az ya sanar masa"

Ta gya?a kanta. Daga haka suka yi salama. Tunani barkatai a ranta. Dan ta kasa hasaso dalilin da ya sa Daddy ke son ganinta ita da Faruk.

*FCID (Force Criminal Investigation Department), Moshood Abiola Road, Garki, Abuja.*

MUKTAR POV.

"Wallahil azim da gaske nake muku yalla?ai!. Wallahi ba ni na kashe Munira ba!"

Fa?in Mubarak saurayin Munira. Yayin da yake zaune a cikin ?akin tuhuma na headquartern. Muktar da ya sa shi a gaba da tambayoyi, ya har?e hannayensa a ?irji, yana daga tsaye a kan Mubarak ?in da tsoro ya sauyawa kamanni.

"Ni ma ban ce ka kasheta ba. Amma me ya kaika hotel ?in a waccan ranar, da har ka tura mata sa?o ta wata lambar da ba taka ba?"

Mubarak ya ha?iye miyau. Sanna yace.

"Eh, na... Na tura mata da sa?o ne saboda ina so mu tattauna wata magana ni da ita!"

"Amma me ya sa ka tura nata sa?o da ba?uwar lamba, sa?anin wadda ka saba amfani da ita!"

A tsorace yace.

"Sati biyu kafin lokacin aka sace min wayata a Almart farm. Kasancewar ba ni ne wanda ya yi rigistern waccan layin nawa ba ya sa na jinkirta yin welcome back. A maimakon na zauna haka sai na siyi wani sabo na fara amfani da shi!"

"Me ya sa ka za?i ha?uwa da ita a hotel. Sa?anin gidansu ko wani wurin da ban"

"Da... Dama... Da dama!"

Suna ha?a ido da Muktar ya ji cikinsa ya saki ?arar tsoro. Ganin yana kame-kame ya sa Muktar ya saki hannayensa. Sannan ya ?ora su a kan table ?in dake wurin.

"Zai fi maka kyau ka sanar da ni komai. Tun kafin nasa a kaika ?akin horo. Dan wallahi ka ji na rantse idan ka je can ba za ka fito da kammaninka na asali ba!"

A take Mubarak ya soma hawaye, ya ha?iye miyau ya fi sau ?irgen yatsunsa. Ganin babu sarki sai Allah ya sa ya bu?e baki ya fa?i gaskiya.

"?warai. Na kirata hotel ne saboda ina so mu sasanta wata matsala da ta shiga tsakanina da ita. Bayan ta zo sai na nemi da ta bani kanta. Hakan ya sa muka yi wani sabon fa?an da ita. Har ta bar hotel ?in ranta a ?ace yake. Amma daga wannan ban san komai ba yalla?ai..."

Ya kai ?arshe yana fashewa da kuka me sauti.

*

"Duk abubuwan da ya fa?a gaskiya ne. Saboda na sa an yi bincike a Almart farm, inda yace an sace masa wayar, kuma masu gadin wurin sun tabbatar da hakan. Dan sun ce a lokacin da aka rasa wayar su ya fara sanarwa... Shi ya sa tun farko ni ban yi zarginsa da kashe Munira ba. Tun bayan sanda muka gano cewa shi ne wanda ya aiko mata da sa?o kan ta zo ta same shi a hotel ?in!"

Muktar ya korowa Faruk dake jiransa a office tun ?azu bayanin, bayan da ya baro ?akin tuhuma. Faruk ya sau?e numfashi. Yana jin ko ina na duniyarsa na ?ara cika da hargitsi. A gida Mariya da matsalolinta, a waje kuma damuwar mutuwar Munira.

"So yanzu me nene mataki na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login