Showing 15001 words to 18000 words out of 35486 words

Chapter 6 - ƘADDARA-CE_-By-Salma-Ahmad-Isah

05 Jul 2024

6332

orange ta bala'in dacewa da fatar jikinta da take wani abu tsakani fari da ba?i.

Ta yafa wani orange gyale, fuskarta babu wata kwalliya ta a zo a gani. Amma she looks perfect. Murmushi ya yi yana binta da kallo har ta shiga cikin motar. Har ga Allah shi kam yana son matarsa. Kuma duk abin da take masa yana dannewa saboda darajar yayanta da ta mahaifinta, da kuma son da yake mata. Da ma an ce so hana ganin laifi.

"Mu je?"

Ta fa?i ganin bai ja motar ba har bayan da ta shiga. Idonsa ya ?auke daga kanta, sannan ya tayar da motar ya fita daga gidan, gidan Hajiyarsu suka fara zuwa, kafin su nufi gidan su Mariyar.

A falo suka iske Hajiyarsa zaune tana cin abincin dare. A falon suka zauna, suka gaisheta cike da girmamawa. Har ta kar?i Hilal tana masa wasa. Kafin suka mata sallama suka fita a kan za su je gidan su Mariya ne.

Sai da suka fita daga falo ta janye idonta a kansu. Ta girgiza kai, halin damuwar auren ?an nata na bata mamaki. Ba sai an fa?a ba, ta san cewa Faruk ba ya jin da?in zama da Mariya.

Duk kuwa da bai ta?a fa?a mata ba, saboda ta san halin zurfin ciki irin nasa. Amma ko makaho ya shafa zai gane hakan. Sai dai kuma ita a matsayinta na uwa bai kamata ta saka musu baki a cikin al'amarin aurensu ba tare da sun sakota a ciki ba.

"Wa alaikassalam!"

Ta amsa sallamar ?anta Adamu, yayan Faruk, kuma ?anin Bara'atu 'yarta ta fari dake aure a mahaifarsu wato Ha?ejia. Asalin mahaifinsu Alhaji Haruna haifaffen garin Hadejia ne. Wanda ya gaji sarautar Kaigaman Ha?ejia tun daga kakkaninsa.

Kuma yana da mata biyu. Hajiya Ru?ayya ita ce matarsa ta fako, wadda ta haifa masa yara uku maza, wanda a yanzu babbansu Muhammad Bello shi ne yake ri?e da sarautar ta Kaigama. Hajiya Aisha, wato mahaifiyar su Faruk ita ce matarsa ta biyu. Wadda ta haifa masa yara uku, Bara'atu ita ce ta farko, sai kuma Adamu, sannan Faruk.

Kasancewar harkokin kasuwancinsa yana yinsu ne a garin Abuja ya sa ita Hajiya Aisha ya dawo da ita nan garin Abuja. Yayin da matarsa ta farko da yaranta ke gidansa na garin Ha?ejia. Karatu ne ya sa Bara'atu ta koma Ha?ejia. Kuma da Allah ya sa rabonta a can yake sai Allah ya ha?ata da mijinta a can ?in.

Wanda suka yi aure har suka hayyayafa, kafin Allah ya masa rasuwa, amma duk da haka bata bar garin Ha?ejia ba, saboda aikinta da kuma yaranta da 'yan uwanta da suke can. Adamu kuma yana da mata ?aya. Wadda yake zaune da ita a nan garin Abuja da yaransa biyu.


MARIYA POV.

Dur?ushe suke ita da Faruk a gaban Daddy. Wanda ke musu nasihar hannunka me sanda. A nasihar tasa bai fito yace akwai ?aya daga cikinsu da ya zo ya kawo ?arar ?an uwansa ba. Kuma bai nuna cewa ya san akwai matsala a tsakaninsu ba.

Ya yi amfani da hikima irin tasu ta manya. Wurin ganin ya nusar da su kurakuransu cikin ruwan sanyi. Tun da babu wanda ya san abin da ke tsakaninsu. Ko da Daddy ya kai ?arshe sai Faruk yace inshallah za'a kiyaye. Mariya kuwa bata ce komai ba. Kuma da ma ba za ta ce ?in ba.

Da Daddy ya sallame su ma ta riga shi fita daga falon na Daddy. Ta wuce sashin Mummy, yayin da shi kuma ya tsaya a wurin Mu'az dake compound. Sun da?e a gidan. Kafin suka yiwa kowa sallama suka tafi.

Faruk ya ?auka cewa Mariya ta ji nasihar Daddy, ta kuma ?auketa kamar yanda Daddyn ke fata, amma sai ya ga sa?anin haka. Dan suna komawa gida ta wuce ?akinta ?auke da Hilal a hanunta, wanda ya yi bacci. A mamakance ya bita da kallo har ta shige ?akin. Ji ya yi yau ba zai iya turewa ba kamar yanda ya saba, dan haka ya bita ?akin dan ya mata magana. A bakin gado ya sameta tana kwantar da Hilal.

"Mariya"

Ya kira sunanta. Ta juyo ta kalleshi.

"Na ?auka cewar ko da laifi na miki, za ki yafe min saboda nasihar da Daddy ya mana ?azu. Na ?auka cewar ko da kina jin haushina ne za ki sau?o saboda maganar Daddy... Amma kuma kin tabbatar min da ba haka ba ne, tun da har kika dawo ?akinki a maimakon nawa."

Mariya ta yi shiru tana kallonsa. Wai da shi haka yake zaton tana da sau?in kai?. Ai ko ya yaudari kansa da zuciyarsa. A ta waje ne jama'a ke mata kallon me sau?in kai, amma a ta ciki sam Mariya bata da taushin zuciya.

"Faruk! A gaskiya ba na jin zan sake ha?a ?aki da kai. Ballantana har na ha?a shimfi?a da kai... Wannan a baya ne, ban da yanzu!"

Ta yi maganar tana juya masa baya, tare da nufar barthroom. Amma sai ya ri?o hannunta ya dawo da ita baya. Ta kalli hannunta da ya ri?e, sannan ya kalli fuskarsa.

"Faruk! Are you trying to hurt me?"

Ta tambaya a mamakance. Faruk ya kalli hannunta da ya matse. Da sauri ya saki hannun nata, sannan yace.

"Mariya, look, I don't want to hurt you or cause you any harm. I just want to know if you've stopped loving me. Just be honest with me!... A farkon aurenmu ba haka muke zaune ba. There is love and care. Me ya sa komai ya sauya yanzu? Could you explain to me why?"

Ko gezau ba ta yi ba ballantana ta ba shi amsa. Jin haka ya sa Faruk ya ?ora yatsun hannunsa biyu a kan karan hancinsa ya rintse ido. Sannan ya bu?e idonsa.

"Mariya!. Idan sona kika daina ya kamata ki fa?a min. Ni kuma a shirye nake domin sawwa?e miki, da ace mun ci gaba da yin irin wannan zaman da za mu ri?a cutar da junanmu!..."

Jin yana batun rabuwa ya sa Mariya ta saka ?wayar idonta cikin nasa. Sannan a hankali bakinta ya motsa cikin fa?in wata kalma. A take ?wayar idonta ta sauya kala zuwa ja.

Wani irin jiri Faruk ya ji ya kwashe shi. Hakan ya sa ya yi saurin dafe kansa yana yin baya. Idonsa ya rintse gam, sannan ya bu?e yana jin wani irin juyawa da kansa yake. Juyowa ya yi ya kalli Mariya dake tsaye. A take ya ji tunaninsa ya birki ce. Sai ya kasa tuna sanda ya shigo ?akinta. Ya kasa tuna maganar da yake, kamar kuma wani abu yake nema a wurin wani.

"Mary!"

Ya kira yana kallonta.

"Papi lafiyarka ?alau?"

Sai ya sau?e hannunsa daga kansa yana kallon ?akin kamar ba?onsa. Gaba ?aya ya kasa tuna abin da ya faru a ?akin.

"Me nake yi a nan?"

Wani irin makirin murmushi ta yi na gefen baki. Sana ta nufe shi, ta tsaya a gabansa ta yanda har suna musayar numfashi.

"Baka da lafiya Papi. Mu je na kaika ?akinka"

Ta fa?i tana kama hannunsa na dama. Sannan ta shiga jansa zuwa waje. Kuma bai musa mata ba. Ya bi bayanta yana son tuna abin da ya kai shi ?akinta. Amma ya kasa tunawa. Har ?akinsa ta kai shi. Sannan ta zaunar da shi a bakin gado. Ta ?auki ruwa ta bashi ya sha, har zuwa lokacin bai fita daga cikin ru?anin da ya shiga ba.

"Ba na so ka cika zurfafawa a tunani. Dan haka ka kwanta ka huta"

Ta fa?a tana shafa sumar kansa. Yanzu ma bai musa mata ba. Kansa kawai ya gya?a sannan ya kwanta a kan gadon ba tare da ya sauya kayan da ya fita da su ba. Ba ta bar ?akin ba sai da ta tabbatar da ya yi bacci. Sannan ta sumbaci goshinsa, ta mi?e ta fita.

A yanzu ba ta shirya rabuwa da Faruk ba, saboda har yanzu tana sonsa, kuma bata jin za ta iya rabuwa da shi, sai dai idan har shugaban bayin shai?an ya bu?aci ta sadaukar da shi ne. To a nan fa ba makawa za ta bayar da shi. Amma yanzu dai kama bata shirya ba.

(Aikin ?irr! In ji tusa??)

*Daga al?alamin Salma Ahmad Isah??.*
*CANDY CE??.*

_Share fi sabillilah??_

------------------------
_A halin yanzu mun yi rabin free pages, dan haka sai ku shirya domin fara biyan ku?in littafi, tun da idan baku manta ba na ce muku isn't free._

_Ga duk wanda ya shirya biya, sai ya biya ?300 to_

5487270431
Salma Isah
Monie point FCMB

Shaidar biya kuma ta wannan numbern wayar.

08130172702.

Ku tabbatar wannan tafiyar bata wuce ku ba, dan har yanzu ba ayi komai ba a tafiyar.

#Candy
°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*?ADDARA CE!*


*(c)SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY??*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_


*06*


*BB paradise hotel.*

MUKTAR POV.

Muktar da abokin aikinsa ne tsaye a gaban ginin hotel ?in 'BB paradise'. Binciken hanyar da Munira ta bi a sanda ta fito daga ginin hotel ?in shi ne ya sa suka buga uban sammako.

"Sir!"

Muktar ya juyo ya kalli Ali, abokin aikin nasa da ya kirashi.

"Me zai hana mu binciki CCTV camera footage ?in wancan super market ?in?. Ina ga kamar za mu iya samun wani abu"

Muktar ya ?aga kai ya kalli super market ?in dake opposite da hotel ?in. Kafin ya duba CCTV cameras ?insu dake sa?ale a gaban ginin. Ba tare da yace komai ba ya nufi titi da nufin tsallakawa. Ali ya bi bayansa har zuwa cikin super market ?in. Ko da suka shiga sai suka iske cewa babu ma'aikata sai masu aikin share wurin.

"Barkanku da aiki"

Mutum biyun dake aiki a wurin suka amsa.

"Dan Allah zan iya ganin ma'aikatan wurin nan?"

Suka dubi juna a tare. Kafin suka kuma dubansu.

"Eh Abubakar manager ne ka?ai ya zo"

Muktar ya gya?a kansa.

"To ko zan iya ganin shi managern?"

Suka kuma diban juna. Alamun dai basu yarda da su ba. Kuma su Muktar ?in sun gane hakan.

"Mu jami'an 'yan sanda ne... Za ku iya yarda da mu"

Muktar ya fa?a yana nuna musu ID card ?insa. Sai a lokacin suka ?an yarda da su ka?an. Kuma da haka ?aya daga cikinsu ya juya ya nufi ?ofar wani office. Jim ka?an ya dawo tare da wani mutum, wanda da alama shi ne Abubakar managern.

"Salamu alaikum"

Fa?in Muktar yana mi?a masa hannu alamun su gaisa. Abubakar ya amsa yana mi?a masa nasa hannun suka gaisa, kafin suka gaisa da Ali. Sai ya ci gaba da kallonsu cikin rashin sani.

"Ko zan iya sanin dalilinku na son ganina?"

Ya tambayi tambayar dake rubuce a kan fuskarsa. Muktar ya yi murmushi.

"Mu jami'an 'yan sanda ne. Kuma muna bincike a kan wani kisa da aka yi wata ?aya da ya wuce. Binciken mu ne ya biyo ta kan super market ?inku. Amma fa ba wai abin ?aga hankali ba ne, taimakonku kawai muke bu?ata!"

"Allah ya sa za mu iya"

"Da yardar Allah ma za ku iya. A ranar da aka rasa victim ?in kafin a tsinci gawarta ta ziyarci wannan hotel ?in dake opposite da super market ?inku. Kuma da muka duba footage na ranar da ta ?ata ba mu samu komai ba. Hasali ma an goge duk wani footage na ranar. Dan haka muke bu?atar taimakonku. Ta hanyar nuna mana footage ?in ranar da ta ?ata daga CCTV Cameras ?inku!"

Manager ya yi shiru kawai. Kamar ya yarda kamar kar ya yarda, kuma ba komai ya sa ya ji kamar kada ya yarda ba face jin batun ?ata da kisan kai.

"Kaga Abubakar Sadik. Taimakon da za ka mana a wannan case ?in shi zai sa mu iya kama mai laifin da ya kasheta. Idan har baka taimaka mana ba. Makashin zai ci gaba da yawo a cikin gari, kuma cikin kwanciyar hankali, tunanin cewa ya aikata wani kisa ba tare da an kamashi ba zai ?ara ba shi access na ?ara kashe wani. Kaga hakan ya bawa aikinsa damar ci gaba... Babu wanda ya san gobe, wata ?ila sai ka ga har ya fa?i kan wani naka!"

Jikin manager ya yi sanyi. Kuma kalaman Muktar na hikima sun ta?a zuciyarsa. Dan haka ya gya?a kansa. Sannan yace su biyo shi zuwa CCTV control room.

Shi da kansa ya binciko musu footage ?in ranar da aka yi kisan. Kuma cikin taimakon Allah sai suka samu abin da suke so. Dan tun daga kan zuwan Mubarak hotel ?in, da zuwan Munira duk sun gani. Kuma har fitar Munira daga hotel ?in sun gani. Sannan a cikin footage ?in suka ga wata ba?ar mota ta fito daga hotel ?in, ta bi bayan Munira. Footage ?in na zuwa nan ya tsaya...

"Daga wannan camerar ta 08 babu wata a gaba?"

Muktar ya tambaya. Manager ya gya?a kai.

"Eh, daga wannan babu wata camera!"

Muktar ya gya?a kansa. Sannan suka yi wa Abubakar godiya suka fita daga super market ?in. Jikin motarsu suka koma. Inda Muktar ya tsaya a jikin motar yana nazari. Ganin ya yi shiru ya sa Ali fa?in.

"Sir! Yanzu mi ye abin yi na gaba?"

"Dole muna bu?atar sanin mutanen cikin motar nan. Sannan bayanai a kan motar, da kuma wuri na gaba da Munira ta je bayan hotel ?in nan..."

Ya ja fasali yana saka hannayensa cikin aljihun wandonsa. Sannan ya juya ya kalli hanyar da suka ga Munira ta bi a footage ?in da suka kalla.

"Wata ?ila waccan kwanar ta kusa da me lemon can ta shiga. Wata ?ila kuma ta mi?e hayar nan ne har zuwa wurin da suka saceta. Wata ?ila kuma tun a sanda ta fito daga hotel ?in nan suka saceta. Zargin ya taru ya min yawa Ali. Komai zai iya faru"

Ya dakata yana rage girman idonsa. A lokacin da wata mata ta tsaya kusa da mai lemon da yake kan wata kwana.

"Ali! Mu je"

Yana fa?in hakan ya soma tafiya. Ali ya bi bayansa ba tare da neman ba'asi ba. A gaban rumfar me lemon suka tsaya. Sai da suka gaisa da shi sannan Muktar yace.

"Baba akwai wani abu da ya faru wata ?aya da ya wuce. Ban sani ba ko idan na maka tambaya a kai za ka iya tunawa!"

Tsoho me lemo yace.

"Eh to yaro. Yi tambayarka, idan na iya tunawa in amsa maka, idan kuma na gaza sai a ?au ha?uri"

"Allah ya baka ikon tunawa Baba. Wata ?aya da ya wuce. A wata ranar asabat, da misalin ?arfe shida na yammaci. Akwai wata matashiya, fara me ?an siririn jiki, da ta zo wucewa ta nan hanyar!?"

Baba mai lemo ya yi shiru yana son ya tuna. Can kuma sai yace.

"Wani kalar kaya ne a jikinta?"

"Baba tana sanye da abaya ruwan goro!"

Ali ya amsa masa. Baba ya kuma yin shiru, can kuma sai ya gya?a kai.

"?warai kuwa da gaske, na gano, lokacin da ta zo ta wuce ina zaune a nan. Har nake cewa wata ?ila wani mugun abin ne ya biyota..."

Muktar ya yi murmushi.

"Yauwwa Baba. To ko za ka iya tunawa da inda ta yi bayan ta wuce ta nan ?in?"

"?warai zan iya tunawa. Dan har ta ?ulewa ganina idona na kanta. Saboda na ga kamar akwai wata ba?ar mota dake bibiyarta."

Tsabar jin da?i yasa Muktar zama kusa da baba. Sannan yace.

"Haka nake son ji Baba. To nuna min ta inda ta bi"

Baba ya juya bayansa, sannan ya nuna musu layin dake bayansa.

"Ta nan haka ta bi. Kuma har ta ?ace min ba?ar motar nan na binta"

Muktar ya gya?a kansa. Sannan ya mi?e tsaye. Ya mi?awa baba Hannu suka kuma gaisawa. Ya masa godiya. Suka juya zuwa wurin motocinsu. Yana shirin shiga motar ya tsinkayo muryar Ali cikin fa?in.

"Sir ya kamata mu shiga layin mu bincika ko akwai wanda ya ga sanda aka ?auketa"

Ba tare da ya juyo ba ya yi murmushi. Sannan yace.

"Ka ?an juya bayanka ta ?arin hagu. Akwai wani matashi a kan mashin da yake amsa wayar ?arya tun sanda motarmu ta tsaya a nan. ?a le?en asiri ne. Idan muka ce za mu shiga layin a yanzu akwai matsala. Ni da kai ne kawai, kuma mu duka ba mu da bindiga. So sarkin yawa ya fi sarkin ?arfi. Yanzu mu koma headquarter. Next time za mu ha?e da shi!"

Yana gama fa?in hakan ya bu?e motarsa ya shiga ciki. Ali ya juya ya kalli matashin dake waya yana satar kallonsu. Kuma ba tare da yace komai ba shi ma ya zagaya ta ?ayan ?angaren ya shiga motar ya ja suka bar wurin.

*No.42, Inuwa Wada crescent, Utako, Abuja.*

*08:32 na safe.*

FARUK POV.

Kasancewar yau an tashi da yayyafi ya sa dadda?ar iskar dake ha?e da sanyin ruwan saman a aka yi yake ka?a curtains ?in dake ?akin. Iskar da ta ?an ?ara ?arfi ce tasa windown ?akin ya bu?e. Sannan iskar ta ka?a labulen da yake a saitin inda gadon ?akin yake.

Sanyin iskar ya busa a kan fatar jikinsa. Hakan ya sa ya motsa ?afafunsa dake cikin takalmi. Kafin ya rintse idonsa dake rufe, saboda wani ciwo da kansa ya fara lokaci guda. Hannunsa na dama ya ?aga ya ?ora a kansa. Sannan ya ja iska ta bakinsa cike da jin zafin ciwon kan.

A hankali ya bu?e idonsa. Sannan ya rufe, ya kuma bu?ewa, ganin gari ya yi haske ya sa ya yi saurin mi?ewa zaune. Ya dafe kansa dake masa ?an karen ciwo. Da ?yar ya mi?e tsaye ya shiga ban?aki. Bayan wani lokaci ya fito. Ya yi sallahr asuba da ta wuce shi. Bayan ya idar bai mi?e daga kan dardumar ba sai da ya yi ta jero istigfar.

Saboda rashin yin sallahr a kan kari. Haka ya zauna a kan dardumar yana nazarin da bai san na miye ba. Har yanzu yana jin kamar akwai abin da ya manta, kamar akwai wani abu da aka goge daga cikin tunaninsa. Amma kuma ya kasa tuna miye. Jin an bu?e ?ofar ?akin ya sa ya ?aga kansa ya kalli Mariya da ta shigo. Ganinsa cikin wannan yanayin da ya kwana da shi a jiya ya sa ta yi miskilin murmushi.

"Sai yanzu ka farka?"

Ya kalleta. Amma bai ce mata komai ba. Dan ji ya yi bakinsa ya yi nauyi, ga kansa da yake sarawa.

"Ya Mu'az ya zo yana waje. Yace ya jika shiru ba ka je barrack ba, kuma ya kira wayarka baka ?aga ba, shi yasa ya zo!"

Da ?yar ya iya mi?ewa tsaye. Sannan ya sa hannu ya cire rigar jikinsa yana fa?in.

"Ki ce masa ina zuwa!"

Mariya ta juya kai, sannan ta fita daga ?akin. Ta dawo ?asa. Idan ta bar Mu'az da Hilal zaune suna wasa. Ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login