Showing 30001 words to 33000 words out of 35486 words

Chapter 11 - ニ連DDARA-CE_-By-Salma-Ahmad-Isah

05 Jul 2024

6334

ma ya taka motar da gudun bala'i.

Kuma ba'a je ko ina ba ya buge Muktar da motar. Ya fa?i ?asa, hatta da?aran da ya yi sun ji shi da Mariya. Kuma ya na buge shi sai ya tsayar da motar. Mariya ta dube shi.

"Ka taka shi ka bi ta kansa mana"

Ya kuwa taka motar, har sai da suka ji motar ta taka shi. Sannan suka ja motar da gudu suka bar unguwar, sun ?auka cewa shikenan kuma, matsala ta mutu tare da mutuwar Muktar.

Sai da motasu ta bar unguwar, Sannan Muktar da ya kaucewa motar tasu ya tashi zaune da ?yar. Dan a sanda suka bige shi bai kwanta a wurin ba. ?arfin hali ya yi ya murgina gefe. Su kuma suka taka dutse, har suna tunanin cewa shi suka taka.

Hannunsa da yake da tabbacin ya karye ya ri?e yana jin ra?a?in azaba. Sannan ya yi ?arfin halin ?aukar wayarsa, ya kira Ali ya sanar masa da halin da yake ciki, sannan ya kira ?aninsa Walid.

"Walid kana gida?"

Ya fa?i da ?yar yana rsinte idonsa. Saboda yanda yake jin ko ina na jikinsa na ciwo, gaba ?aya ma ya rasa takamemen ina ne yake masa ciwo. Daga ?ayan ?angaren Walid yace.

"Eh Ya Mukhy. Ina nan, lafiya?"

"Ka fito ka zo kwanar gidan Alhaji Sadam. Ina wurin, na ?an samu wani ha?ari ne?"

Walid dake zaune a falo ya mi?e zumbur yana tambayarsa.

"Ha?ari? Yaushe? A ina?"

"Stop asking just come and help me!"

"Okay"

Ya kashe wayar, sannan ya nufi ?ofar falo da gudu.

"Kai Walid! Ina za ka je?"

Mamansu da ta fito daga kitchen ta tambaya. Sai ya dakata, sannan ya juyo.

"Ya Mukhy ne ya kirani yace ya samu ha?ari a kan kwanar gidan Alhaji Sadam. Shi ne zan je na duba"

"Ha?ari?"

Mama ta tambaya a hargitse.

"Eh Mama. Bari in je na duba shi"

"To ka kula. Allah ya sa ba wani mummunan abin ne ya same shi ba."

"Amin"

Ya amsa yana fita daga falon. Da yake shi ya fi kusa da Muktar ?in sai ya riga Ali isa. Dan gidan Alhaji Sadam ?in ?an gaba ka?an ne da nasu. Sai da Ali ya zo, tukkuna suka ?auke shi zuwa asibiti.

-------------------

_Na lura da bana letter (M) ce ke zamani_

_Rabin 'yan wasanmu duka sunansu da 'M' ya fara_

_To gaba ?aya babin yau ma a kan M ?in ya ?are. Ga Mariya fa Muktar._

_Sannan kun ji abin da ya faru tsakanin Munira da Mubarak_

_Kun kuma ji yanda aka yi Munira ta mutu_

_Mu je zuwa. Saboda yanzu muka fara sharar hanya??_

_Share fi sabillilah??_

*Daga al?alamin Salma Ahmad Isah??.*
*CANDY CE??.*

--------------------
_Kada a manta da biyan ku?in littafi. Dan free page zai ?are daga gobe in Allah ya kaimu. To subscribe pay ?300 to._

5487270431
Salma Isah
Monie point.

And send the evidence of payment via.

08130172702

#Candy
#SalmaAhmadIsah
ーーーーーーーーーーーーーーーーーー

*?ADDARA CE!*


*(c)SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY??*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_


*10*


MU'AZ POV.

Zaune suke a falo shi da, Mummy, Mima da Na'im. Abinci yake ci yana latsa wayarsa. A jima ka?an sai ya yi murmushi. Kuma ba komai ke janyo hakan ba face cry cry baby Leemat da yake tunowa.

A duk sanda zai tuno ha?uwarsa da ita a yau sai ya yi murmushi me fa?i. Bai san me ya sa ba, amma haka kawai yanayin shagwa?arta ke burge shi, da yanda take magana, da yanda kuka ba ya mata wuya. Kuma hakan ke nuna masa cewar shagwa?a ?abi'arta ce.

Mima da tun ?azu take satar kallonsa ta gyara zama tana le?a cikin wayarsa. Wai ko za ta ga abin da yake saka shi murmushi. Amma ba ta ga ba, dan chat kawai yake. Sai ta ?ara matsawa kusa da shi tana fa?in.

"Ya Mu'az!"

Kallonta ya yi ba tare da ya amsa ba.

"Ko dai da Yasmin kake chat?"

Nan da nan ya murtuke fuska ya soma harararta.

"Saboda Yasmin ce ka?ai mace a duniya ko?. Ko kuma saboda an fa?a miki cewar ba ni da wani aiki sai na chat da Yasmin?... Wallahi Mima idan ba ki daina shiga min hanci ba zan fatoki. Kuma a ranar da zan fato ki idan kika duba fuskarki a madubi ba lalle ki gane kanki ba!"

Sai ta sosa kai tana zare ido.

"Shugaban masifaffu!"

Ta fa?i a ?asan ma?oshi. Mu'az ya kalleta.

"Kin yi magana ne?"

Sai ta yi saurin girgiza kanta.

"Ni kaza?... A'a, komai ban ce ba!"

Ya wurga mata harara yana fa?in.

"?aramar mara kunya!"

Mima ta ?auki wayarta ta nufi stairs tana fa?in.

"Allah ya nuna min ranar da ni ma zan zama babbar mara kunyar nan, matsayina ya ?aru a idon ya Mu'az!"

Kasancewar a hankali ta yi maganar ya sa bai jita ba.

"Mummy!"

Ya kira Mummy. Mummy ta dube shi tana amsawa.

"?azu na je gidan Anti Farida. Kuma tace tana gaisheki"

Mummy ta ja tsaki tana mayar da dubanta kan tv. Can kuma tace.

"To ina ruwana?"

Mu'az ya yi murmushi me sauti.

"Mummy! Mummy! Mummy!..."

"Kai ni kar ka ?arar min da suna!"

Mummy ta katse shi.

"Wai ni Mummy me Anti Farida ta miki ne?"

Mummy ta galla masa harara.

"Babu abin da ta min... Babana Mu'az"

Tana ?arashewa ita ma ta mi?e ta bar falon. Ya rage daga shi sai Na'im. Shi ma mi?ewa ya yi ya kama hanyar fita.

"Ya Mu'az wai yaushe za ka siyo min sweatern?"

Na'im ya tambaya. Lokaci guda ya saki murmushi. Sannan ya juyo.

"Kada ka damu oga tulele. Zan siyo maka gobe. Akwai chocolate a wurinka?"

Ya tambaya yana murmushi. Saboda har ya fara hasaso ha?uwarsa da Halima a gobe.

"Akwai. Amma sai kinder delice. Kuma ai kai baka shan kinder"

"Ba ni zan sha ba, kyautarta zan bawa wata Baby. Ka kawo min guda goma idan akwai m&m's cookies ka ?auko min guda biyar"

Na'im ya mi?e yana fa?in.

"Babyn waye?"

Mu'az ya kalle shi.

"Wata kyakkyawar baby girl ce... Me saurin kuka da fitina"

Na'im ya yi dariya kawai. Sannan ya nufi sama. ?akinsa ya shiga ya bu?e wardrobe. Ya ?ebo chocolate da cookies ?insa, sannan ya saka a cikin wata bag me kyau. Ya sau?o ?asa ya iske Mu'az a inda ya barshi. Ya mi?a masa jakar da ya saka chocolate ?in.

"Yauwwa oga tulele. Ka kyauta. Insha'allah gobe zan kawo maka sweaternka. Sannan zan sake siyo maka wasu chocolate ?in"

Mu'az ya fa?a yana kar?ar jakar. Na'im ya yi dariya.

"A'a. Ba sai ka siyo min wasu ba, ina da wasu kalar da Daddy ya sai min last week"

"To Baby ta gode. Yayan baby ma ya gode"

Ya fa?a yana juyawa. Fuskarsa ?auke da murmushi.

"Baby!"

Ya furta sunan yana nufar part ?insa. Kuma har ya shige bai bar murmushin ba.


FARUK POV.

Zaune suke a falo shi da Hilal da ya yi bacci tun wuraren ?arfe 8. Kwance Hilal ?in yake a kan cikinsa. Yayin da shi kuma yake zaune a kan kujera, yana jiran dawowar Mariya gidan.

Shi ya rasa wannan wata kalar rayuwa suke shi da Mariya. Matar aurensa ta sunna ce za ta sa ?afa ta bar gidan aurenta ba tare da ta nemi izinin mijinta ba?. Ba kuma hakan ne ya sa shi mamaki ba. Saboda ta saba fita ba tare da ta tambaye shi ba. Mamakinsa shi ne barin ?aramin yaro da ta yi a gida shi ka?ai.

Idan bai ?ata a ?irgen watan haihuwar Hilal ba, dudu yanzu ba zai wuce wata goma sha ?aya ba. Amma har ta kan iya tafiya ta bar shi a gida shi ka?ai. Ko da gidan Hajiya za ta je bai kamata ta tafi ta bar shi a gidan shi ka?ai ba.

Kuma halin da ya zo ya same shi a ciki ne ya ?ara ba?anta masa rai. Ya zo ya same shi cikin yunwa. Ga kuma diapers ?in dake jikinsa ta cika da bayan gari da kuma fitsari. Da alama tun safe da aka saka masa ba'a sauya masa ba.

Tsaki ya ja yana kaiwa dubansa kan agogon dake bango. Ganin goma ta haura ya sa ya sake jan wani tsakin. Sannan ya sa hannunsa a kan ?ansa yana shafawa a hankali.

Lokaci guda ya ji Hilal ya zabura, sannan ya kuma canyara kuka yana ?ara zabura. Saurin kaiwa hannu ya yi ya gyara masa kwanciya a tsakiyar hannunsa. Yana karantowa ayatul kursi, tare da tofa masa.

A hankali a hankali kuma sai kukan nasa ya ragu, har ya yi shiru, ya dawo yana jan zuciya, kuma duk wannan abin da ya faru idonsa a kulle yake gam. Sai ya ?ata fuska yana turowa le?ensa na ?asa. Yanayin fuskar tasa ya bawa Faruk dariya. Dan haka ya yi murmushi. Ya shafa kansa, sannan ya sumbaci goshinsa. Ya rungume ?ansa yana fa?in.

"Allah ya raya min kai babana!"

Shiru ya yi ya ?aga kai ya kalli ?ofar falo da aka bu?e. Mariya ta shigo tana kallonsa. Kuma ba tare da tace masa komai ba ta wuce shi ta nufi stairs. Kamar daga sama ta tsinkayo muryarsa, da amon da bata ta?a sanin cewa yana da shi ba.

"Daga ina kike?"

Sai ta tsaya cak. Sannan ta juyo. Sai ta gan shi a tsaye, Hilal ?in da ta shigo ta same shi rungume da shi kuma ya kwantar da shi a kan sofa.

"Tambayarki nake Mariya!"

Ya sake magana yana tsareta da ido. Sai ta dawo cikin falon, ta tsaya a gabansa ba tare da ta masa ko tari ba.

"Ina kika je ba tare da izinina ba? Kuma kika fita kika bar min ?ana a cikin gida shi ka?ai kamar maye!?"

Sai ta yi murmushin da ta saba.

"In da ka aike ni na je!"

Lokaci guda wannan murmushin da take, da kuma yanda ta masa maganar a sigar dake nuna bata damu da ?acin ransa ba suka fara hasalla zuciyarsa. Ya ji ya kawo wuya. Duk da shi bai cika saurin fushi da saurin kai hannu ba irin na Mu'az ba. Amma yau dai kam yana jin Mariya ta kai shi bango.

"Na farko kin aikata min laifin fita daga gidana ba tare da izinina ba. Na biyu kin fita kin bar min ?a a gida shi..."

Bai kai aya ba Mariya ta katse shi.

"Wai ni a kanka aka fara haihuwa? Magana ?aya biyu sai ka sako ta ?anka a ciki? Ai ni ma ?ana ne, ba shegensa na yo a waje ba!..."

Ba ta rufe bakinta ba ta ji sau?ar mari a kuncinta na dama. Lalle yau ta ?ure Faruk har wuya, tun da yake bai ta?a ?aga hannunsa a kan wata mace ba, ballantana matarsa ta auren sunnu, matar tasa ma Mariya, wadda yake jin sonta har cikin ransa.

Amma abin da ta aikata yau ya sa ba zai iya yafe mata ba kamar sauran kura-kurenta na baya. Ita ce da laifi, amma ji yanda take ?aga masa murya kamar ita ce mijin, shi kuma matar.

"Ba ki isa ba Wallahi... Mary ba ki yi wannan tasirin a zuciyata ba da zai sa ki aikata min laifi, sannan ki zo kina ?aga min murya na ?yaleki..."

Mariya da mamaki ya sa ta sandare ta ci gaba da kallon fuskarsa da ta sauya mata lokaci guda. Ko dai ba Faruk ?inta ba ne?. An yama kuwa wannan mijinta ne?... Har ya gama fa?ansa ya ?auki Hilal ya bar mata falon ba ta iya yin ko da tari ba.

Cike da jin haushin da bai gama washewa a ransa ba Faruk ya kwantar da Hilal a kan gado. Ya lullu?e shi yana jin wani abu na ba?in ciki na tokare masa ma?oshi. Gaba ?aya ma ya rasa yanda zai yi ya huta.


MAIMUNA POV.

Yau da matsanancin ciwon baya ta tashi. Amma duk da haka sai da ta yi duk ayyukan da suka zame mata wajibi a gidan. Tana yi tana kuka, saboda yau ciwon da take ji ya fi na kullum. Ta yi doyar safe. Ta je ta siyar, sanan ta fara ha?a kunun dare. Tana tsaka da tatar hatsin da ta kar?o a wurin ni?a Auwwa ta kirata.

"Ke Maimuna!"

Da ?yar ta iya ?aga yalayen idonta irin na masu sickler ta kalli Auwwan. Sannan ta amsa.

"Na'am"

"Zo!"

Da ?yar ta iya mi?ewa tsaye. Tana dafe da bayanta da yake matsanancin ciwo. Ta nufi inda Auwwa ke tsaye. Auwwa ta mi?a mata dubu uku, ta kai hannu ta kar?a.

"Kasuwa za ki zo ki tafi ki siyo min doya. Na ga sauran guda ?aya!"

A take Maimuna ta ji ruwan dake zuba a idonta ya ?ara gudu. Dan haka ta ?aga kai ta kalli Auwwa. Yanzu idan ba'a rage mata aikin dake kanta ba ai ba a ?ara mata ba. A yanayin jinyarta kwata-kwata ba'a son su shiga damuwa ko tashin hankali, dan hakan kan iya ta?a zuciyarsu kai tsaye. Amma a gidansu sam ba'a damu da hakan ba. ?acin rai kullum sai Auwwa ta kasa mata a fai-fai ta ?auka.

"Ko ba za ki je ba ne?"

Ganin Auwwan na shirin ?aukan madoki ya sa ta yi saurin girgiza kai.

"A'a zan je"

Ta rufe le?enta ?walla na ?ara sau?o mata. Ba tare da tace komai ba ta ja siraran ?afafunta da ba su cika ?wari da lafiya ba ta ?auki hijabinta. Ta saka. Sannan ta fita waje tana kallon yanda rana ta baza duniya.

Da ace tana da gata da a mashin za ta je kasuwar. Amma a halin da take ciki na magen ma?ota ma ta fita muhimmanci ba za ta samu wannan gatan ba. Ba komai take hasasowa ba face nisan dake tsakanin gidansu da kasuwa.

A abin hawa ma tafiyar ba ka?an ba ce, ballantana kuma a ?afa. Ga kuma yanda rana ta ?walle a sama, kamar ba lokacin hunturu ba, duk da sanyin ya fara ja baya. Ga ciwon baya ga na ?afa, ga kuma na jiki da na zuci.

Haka ta ci gaba da daurewa tana tafiya. Idan ta gaji sai ta samu gefen hanya ta zauna ta huta, kafin ta tashi ta ci gaba da tafiya. Da haka har ta iso titin ?ofar fada. A nan ?in ma sai da ta zauna ta huta. Tana ta haki, ga bayanta da take jin kamar zai karye.

Kuma idan aka raba tafiyarta biyu, ba ta ?auki kashen ?aya ba, sai dai a kirata da kwata. Hawaye ne ya zubo mata. Ta kai hannu ta share, sannan ta raba kanta da wannan hutun na jaki kaya a ka. Ta ci gaba da jan ?afarta da ?yar... Har ta hau kan titi a ?o?arinta na tsallakawa...

A dai-dai lokacin kuma wani mummunan ha?ari ya faru, a tsakiyar titin, a tsakiyar gari, a tsakiyar jama'a da ma duk wani me wucewa.

*. *. *.

Gambo ne da uban gidansa, wato me napep ?in da yake ba shi sojan haya. Suka ?ebo wasu fasinjoji mutum biyu. Gambo ya juya ya kalli ogansa yana fa?in.

"Oga ba na jin Auwwa za ta iya bada ku?in nan... Ba ka san Auwwa ba ne, masifar son ku?i gareta kamar me?"

Ogan ya yi murmushi.

"To ai shikenan. Sai ka yi ta zama a haka, kana hawa napep ?in sojan haya. Ka je ka sha ba?ar wahala, ka dawo a ?auki ku?in da bai taka kara ya karya ba a baka a matsayin sallama!"

Gambo ya mayar da hankalinsa kan tu?insa. Yana nazarin maganar ogansa. A ?alla yanzu an kai kusan shekaru biyu kenan da yake ta ?o?arin siyan napep tasa ta kansa. Amma babu hali, saboda yanda Auwwa ta kasa ta tsare a kan ku?inta.

"Me napep a Gagulmari fa za ka sau?e mu!"

?aya daga cikin fasinjojin ta fa?a. Hakan ya sa ya ?an juyo ya kalleta, sannan ya amsa.

"To Hajiya"

Ya fa?a yana juya kan napep ?in. Dan harsun ?an gota unguwar Gagulmarin. A kan titin ?ofar Arewa ya sau?e su. Suka biyasu ku?insu, sannan suka juya kan napep ?in zuwa ?ofar fada.

Haka suka ci gaba da hira shi da ogansa. A kan mallakar napep ?in da ya kamata ace ya yi, yana magana yana ?auke kai daga kan tu?in da yake. A haka har ya buge wata yarinya dake shirin tsallaka titin ?ofar fada ba tare da ya lura ba.

Duk da ya tsorata bai sai ya kasa guduwa ba, amma kuma cikin rashin sa'a sai jama'ar dake wurin suka yi caraf suka kamasu su biyu...


HALIMA POV.

Hannu ta kai ta ?auki jakarta. Ta rataya a kafa?arta, saboda lokacin tashinsu aiki ya yi.

"Kairat sai gobe"

Ta yi wa ?awarta sallama tana ?aga mata hannu. Ita ma Kairat ?in hannu ta ?aga mata. Tana shirin wucewa, hirar da cashier da wata ma'aikaciya suke yi ta ?auki hankalinta. Hakan ya sa ta tsaya tana sauraronsu.

"... Wallahi dai kam haka na ji manager ya fa?a. Wai za ayi ragin ma'aikata!"

Lokaci guda ta ji gabanta ya fa?i. Dan haka kawai zuciyarta ta raya mata cewar ita ma tana cikin wa?an da za'a sallama. Ita kuwa idan aka sallameta ina za ta je ta samu wani aikin?. Wannan ?in ma da ya aka same shi?. Ballantana kuma ace ta rasa shi... Gabanta bai tsananta fa?uwa ba sai da ta ji cashier na fa?in.

"Kuma a yanda Amina ke fa?a min wai wa?an da suka zo a ?arshe-?arshen nan za a kora!"

Ido ta zaro tana fa?in 'Inna lillahi wa inna ialaihi raji'un' a cikin zuciyarta. Sai ta kasa motsawa daga wurin da take. Ta ci gaba da baza ido har ta yi wani kyakkyawan gani.

Saboda a sanda idonta ya lula zuwa ?ofar shigowa ta ga sanda Mr. JJ ya shigo boutique ?in. Gabanta ne ya sake fa?uwa. Musamman da ta tuna rabuwarsu ta jiya. Hannunta na dama da ya ri?e ta kalla, tana jin kamar har yanzu hannayensa na kan wurin... Sai ta yi saurin goge ?wallar da ta zubo mata, sannan ta nufi hanyar fita a sace, wai duk dan kada ya ganta.


MU'AZ POV.

Tun da ya shigo boutique ?in yake ta dube-dube ko zai ganta. Amma har ya ?auki sweatern da ya zo dominta bai samu ganin nata ba. Har ya fara jin ba da?i na rashin ganinta, saboda ya fara tunanin ko dai ta tafi gida ne.

Yana shirin nufar wurin cashier ya ci karo da ita tana tafiya a sukwane. Tana ganinsa ta taka birki tana ?ata fuska. Lokaci guda kuma ta juya za ta gudu. Sai dai kamar jiya, haka yau ma ya ri?o hannunta. Kuma kamar dai jiyan, yau ma sai da ta ji kamar ta yi hauka da ya ri?o mata hannu. Da ?yar ta juyo suka ha?a ido. Sai kuma ta shiga bin kayan jikinsa da kallo.

Kamar dai yanda ta saba ganinsa ne, sanye da ba?ar T-shirt, da kuma wandon kakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login