Showing 24001 words to 27000 words out of 35486 words

Chapter 9 - ニ連DDARA-CE_-By-Salma-Ahmad-Isah

05 Jul 2024

6331

hannun Maimuna. Haka Maimun ta yi ta ?walla ?arar azaba tana kuka tana ro?on Auwwa. Amma ko a jikinta. Ga shi su ba ma?ota garesu ba bare a ji a kawo mata agaji.

"Shegiya matsiyaciya. Allah ya sa gobe ma idan na hukunta ki da abinci ki sake zuwa can ki ci!"

Maimuna ta ?arawa kukanta sauti. Sannan ta dur?ushe a wurin tana kuka me ban tausayi. Haka Auwwa ta mi?e tsaye ta tsallaketa ta wuce ?akinta. Maimuna ta ci kukanta ta godewa Allah. Da ?yar ta iya tashi ta shiga ?akinta da babu bulb.

Da akwai, amma kwana nan Auwwa ta cire shi, wai za'a bawa Gambo. Saboda ?akin da yake kwana nasu ya mutu. Haka ta zauna a cikin sauron da take iya jin kukansu a kunnenta. Da ?yar ta janyo ledar magungunan da Mummy ta sai mata. Ta sha tana hawaye har zuwa lokacin.

Saboda wannan ?unan da Auwwa ta mata a yau ya fi na ko yaushe. Da ?yar ta lalla?a ta shiga net ?in. Tana jin yanda ?ashin bayanta yake amsawa. Saboda a kullum rana idan ta zo kwanciya sai bayanta ya amsa. Shi ya sa bata kwanciya kai tsaye, sai a daddafe.

Zaninta ta ja ta lullu?e jikinta. Duk da yanzu sanyin ya fara ja baya, ba kamar na kwanakin baya ba. Amma da ma ita ko da sanyi ko babu sicklernta tashi take a ko wani lokaci. Har ?arawo ya saceta ba ta daina zubar da hawaye ba.


HALIMA POV.

Kamar kullum, yau ma haka suka tashi a gidan babu ruwa ko na yin sallah ballantana na yin wanka ko girki. Tana ji tana ganin ?ananan yaran gidan zaune suna harkarsu aka sakata aikin ?iban ruwa. Kuma ba ta isa ta musa ba, dan ya zame mata dole.

Da zun?ure-zum?uren bakinta da komai ta fita daga gidan ?auke da bokiti. Tana tafe tana hawayen da suka zame mata farilla. Gidan dake kusa da nasu ta shiga, sannan ta ro?i matar kan dan tana so a mata lamunin ?iban ruwa a somon gidan. Matar bata hanata ba. Dan sun ?an saba a zamanta a unguwar.

Sai da ta cika babbar randar gidan, sannan Mama Zulai tace ta je ta ?ebowa Jidda ruwan wanka. Wai akwai inda take son zuwa yau. Cike da ba?in ciki ta fita daga gidan. Amma ?iwarta ta hanata ?arasawa gidan da take shiga ?iban ruwan. Sai ta tsaya a ?ofar gida. Jim ka?an ta koma cikin gidan tace ai matar gidan tace ruwan ya ?are.

"Ke ma?iwaciya ko? Ai ko za ki ga ?iwa ganin idonki... Jidda! Jidda!"

Mama Zulai ta ?arashe tana kiran Jidda. Jidda dake ?akinta na ita ka?ai ta fito tana amsawa.

"Zo ki ?ibi ruwa a randa ki yi wankanki... Ke kuma idan kin ?ibi ruwan nan sai dai idan na mutu!"

A take idon Halima ya ciko da ?walla. Da ma kukan a kusa yake. Dan haka ta sake shi takaici na cika ranta. Tana ji tana gani 'ya'yan Mama Zulai suka dinga ?iban ruwan suna ?atawa. Kuma ba ta isa tace uffan ba.

Sai Mama Sadiya ce ta sa ?aya daga cikin yaranta ?anana ya je ya ?ibowa Halima ruwa dan ta yi wanka. Da haka Mama Sadiya ta kashe wutar kukan nata. Tana zaune yaron ya kawo mata ruwan. Sannan ta yi wanka ta shirya domin tafiya wurin aikinta.

Ko abinci bata zauna ci ba. Saboda ita yanzu ba ta jin za ta iya cin wannan busasshen ?umamen nasu me kama da dutse. Babur ta hau, wanda ya sau?eta a Ummul Banat boutique. Kuma shigarta cikin boutique ?in ba wuya ta hango shi yana shigowa.

Wannan farin mugun sojan da ya sau?e mata rabin fuska jiya. Tana ganinsa ta yi saurin ?uya a bayan wasu kaya da akajera a cikin boutique ?in. Dan ba ta ma son wani tsautsayi ya sake ha?ata da shi, bare har ta kai ga ya sake marinta.


MU'AZ POV.

Kamar yanda ya kwanta da tunaninta haka ya tashi da shi. Har ya gama shirinsa na fita bata fita daga tunaninsa ba, da ?yar ya iya samun sukunin cin abinci. Kuma yana gama cin abinci ya yi hanzarin fita daga gida. Kai tsaye ya nufi Ummul Banat boutique.

A sanda ya shiga wurin ya lura da cewar yanzu ma masu aikin wurin suke zuwa. Dan haka ya shiga raba idonsa a kansu, wai ko zai ga tauraruwa mai wutsiyar da ta hargitsa masa lissafi a iyaka jiya kawai. Amma bai ganta ba. Dan haka ya tsayar da ?aya daga cikin ma'aikatan wurin, ya tambayeta.

"Dan Allah ina neman wata... Wata farar yarinya haka... Fara ce... Eh fara!"

Ya tsaya kame-kamen kammaninta. Dan gaba ?aya ba yace ga yanda suffar jikinta take ba. Da ace yanayin idonta aka tambaye shi da ya zayyana komai game da shi, ba dan kar ya yi ?arya ba, zai iya cewa ya san adadin yawan gashin idonta na ?asa. Saboda su ne abin da ya fi kallo a fuskarta.

"Halima kake nema?"

Ma'aikaciyar ta tambaya. Sai ya kalleta yana tuna sanda wata ta kirata da Halima jiya. Kamar gaula, haka ya gya?a mata kai, sanna ya ?ara da.

"Eh, ita ce. Ya aka yi kika sani?"

Sai ya ga ta ?an yi murmushi.

"Cry-cry baby kenan. Ai na ga sanda ka mareta jiya!"

Kamar wanda ita ma ta ko?a masa marin haka ya ji sau?ar maganarta a tsakiyar kansa. Hakan ta sa ya rintse idonsa. Kafin ya bu?e yana cilla mata tambaya.

"A ina zan ganta?"

"Bata da?e da zuwa ba ai. Ka duba ta can, ba za ta wuce wurin ba"

Ya dubi inda ta nuna masa. Sannan ya mata godiya ya ra?ata ya wuce. A hankali yake duba kayyayakin dake wurin. Har ya wuce, sai ya tsaya cak, saboda wani hoto da idonsa ya ?auko masa. Ya dawo da baya, ya tsaya a inda ya ganta. Sannan a hankali ya kalli fusarta da ta ?oye a tsakiyar kayan.

Suna ha?a ido Halima ta zaro nata idon. Sannan ta turo baki gaba tana shirin fashewa da kuka. Ta mi?e tsaye tana shirin fita da gudu. Kuma a lokacin ya aikata abin da bai ta?a zaton zai aikata ba. Kuma ya aikata abin da ita kanta Halima ba ta zata ba. Dan ba ta yi taku uku ba ta ji ya ri?o tsintsiyar hannunta.

Cak Halima ta tsaya. ?irjinta na dokawa da mugun ?arfi. Saboda wani abu da ta ji ya sau?a a kan fatar hannunta me tsananin taushi. Bata kai ga tantance abin da yake faruwa da ita ba ta ji ya dawo da ita baya. Sannan ya shiga janta zuwa waje.

Bata san me ya zare mata laka ba har ta kasa musa masa. Dan haka ya yi ta jan hannunta tana biye da shi har parking lot. Kallonsa kawai take, bakinta sake, hawaye kuwa tuni suka wanke mata fuska. A jikin motarsa ya tsayar da ita, sannan ya bu?e front seat. Ya zaunar da ita a cikin motar, amma kuma ?afafunta duka biyu suna waje.

Har zuwa lokacin kallonsa kawai take tana sakewa, ashe ma jiya bata ?are masa kallo ba. Saboda sai a yau take ganin ainahin kammanin fuskarsa da ba su bayyana gareta ba a jiyan. Fari ne sosai, yana da tsayi, kuma yana da manyan idanu. Ga wasu dogayen gashi da suka ?awata mabu?ar idon nasa sama da ?asa.

Ga kuma ba?in gashin girarsa da bai cika yawa ba. Kansa babu gashi sosai, sannan a fuskarsa babu gemu, sai dai ?an siririn gashin bakinsa da babu gashi da yawa, dan sai ka yi da gaske za ka gane cewa yana da gashin bakin.

Yanda yake kallonta da fararen idanuwansa ya sa ta ji kamar ba a zaune take a kan kujerar motarsa ba. Sai ta ji kamar tana zaune a kan wani abu me tsananin laushin da ya fi gajimare. Duk sai ta ji kamar za ta narke a wurin. Ba ta dawo hayyacinta ba sai da ya mi?a mata gorar ruwa, sannan yace.

"Kar?i ki sha"

Sai ta kalli gorar. Sannan ta kalli farin hannunsa da ya ri?e gorar. Wanda yake ?auke da fararen faratu, gakuma wani ba?in smart watch da ya saka a tsintsiyar hannunsa da ya sa farar fatar tasa ?ara haskawa da kyau a cikin safiyar.

Cikin wannan shagwa?ar da ta zame mata jiki ta ?aga hannu ta kar?i ruwan. Sannan takai bakinta ta sha tana hawaye har zuwa lokacin. Yayin da Mu'az ya ke tsaye a kanta yana ?are mata kallo. Shi kam ba zai ce jiya bai kalleta da kyau ba. Ya kalleta sosai, ta yanda ko da zana kammaninta za ayi idan aka tambaye shi zai iya wassafasu.

Amma wannan fuskar tata da ta shagwa?e ce ta fi ?aukar hankalinsa fiye da komai tattare da ita. Haka kawai ya ji ta burge shi. Yanda ta turo bakinta gaba, da yanda take ?if-?ifta idonta cike da zallar shagwa?a, da kuma yanda hawaye yake zuba a kan fusarta. Kuma a hakan ya ga shatin yatsunsa hu?u a gefen fuskarta.

'Lord have mercy!'

Ya fa?a a ranaa yana furzar da huci ka?an.Kansa ya kawar gefe yana rintse ido. Sannan a hankali ya furzar da iska daga bakinsa. Ya bu?e idonsa sannan ya juyo ya kalleta.

"Kin ga!..."

Cak maganar da yake son fitarwa daga bakinsa ta tsaya a ma?oshinsa, saboda yanda Halima ta kalleshi da fararen idanuwanta dake zubar da ?walla.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil!"

Ya furta a iyaka kan le?ensa. Shi yanzu gaba ?aya ma ya rasa me yake damunsa. Ko de yarinyar nan ta masa wani abin ne?... Sai ya girgiza kansa a fili yana ha?iye yawu. Ya yi gyaran murya, sannan ya ?auke idonsa a kanta yana fa?in.

"A... Abin da na miki jiya ban kyauta ba... Shi ya sa na dawo yau dan na baki ha?uri... Ki yi ha?uri!..."

'Kuma dan Allah kar ki sake shigo min cikin tunanina...' Ya ?arashe sauran maganar a zuciyarsa. Dan ba ya jin ta isa ya fa?a mata cewar jiya tunaninta ya hana shi bacci. Halima ta ci gaba da kallonsa da fararen idanuwanta da har zuwa lokacin ba su daina zubar da ?walla ba.

Mamakinta ?aya, dalilin da ya sa yake bata ha?uri. Ya san cewa zai zo ya yi nadama zai mareta tun farko?. Sai ta ?ara turowa le?enta na ?asa gaba. Tana wani ?if-?ifta ido. Sannan ta shafa gefen fuskarta.

"To me ya sa ma za ka mareni jiya?. Kuma ma fa ni ba da gangan na bigeka ba. Sai da na yi ?o?arin kauce maka, amma ka kai ka ?i ka kauce. Har ka san na bigeka na zuba maka ruwa a jikin rigarka... Wallahi jiya har na yi bacci ina kuka. Gefen fuskata sai zugi yake min, har ji nake kamar ba a jikina yake ba!..."

Mu'az ya yi shiru kawai yana kallon bakinta da take turowa gaba lokaci zuwa lokaci, da kuma yanda take maganar a shagwa?e. Kafin ya kalli idonta da take kallon ?asa da shi. Wato ita nan har damar yin ?orafi ta samu, saboda kawai ya bata ha?uri?...

"Kuka da ma ai ke gwanarsa ce... Tun da yanzu ma ga shi nan kina yi"

Ya fa?i yana kallonta. Sai ta kalle shi ita ma. Sannan ta ?auke kai tana ?ara tura baki gaba.

"Yanzu kin ha?ura?"

Ya tambaya. Shi kansa tambayar na ba shi mamaki. Ita ma sai ta kuma kallonsa, sannan ta mi?e tsaye, hannunta ri?e da gorar ruwan da ya bata.

"Na ha?ura amma ban ha?ura ba!"

Ya ?an ?ara girman idonsa cikin mamaki. Wai ta ha?ura amma bata ha?ura ba.

"Me ya sa kika ha?ura kuma at the same time ba ki ha?ura ba?"

Ta masa wani irin kallo da ya hautsina bugun zuciyarsa nan take. Sannan ta juya kanta tana kallon wani gefen... Sai tura baki take, kamar wadda aka wa dole kan sai ta yafe masa.

"Na ha?ura dai"

Ta fa?a tana kallon gorar dake hannunta. Mu'az bai san sanda murmushi ya su?uce daga kan le?ensa ba. Saboda shi haka kawai wannan abin da take yake burge shi. Yana jin ana cewa shagwa?a, bai ta?a ganin mace me shagwa?a ba sai yau...

A hankali ya sunkuya ya sa hannunsa a cikin motarsa ta saitin inda ta fito. Ya ?auki chocolate. Sannan ya mi?e ya mi?a mata.

"Kina so?"

Sai ta masa irin wannan kallon na ?azu. Sannan ya kalli chocolat ?in.

"Ai ban sanka ba. Na sani ma ko kai ?an yankan kai ne?"

Murmushi ya sake yi yana ?aga kansa sama ka?an. Sannan ya sau?e yana fa?in.

"Ba ki ga ni soja ba ne?"

Ta kalli wandon kakin sojojin dake jikinsa. Dan daga shi sai wata ba?ar T-shirt da ya sa. Ta kalli fuskarsa, wadda yanayinta ka?ai, da kuma askin kansa zai sa ta gane cewa shi sojan ne, amma sai ta girgiza kai.

"Ai akwai sojojin gona"

"Ni ba ?aya daga cikinsu ba ne"

"Me cece shaidarka?"

Ta tambaya tana kafe shi da ido. Ya kuma yin murmushi yana girgiza kansa, sanna ya sa hannunsa ya kamo nata da bata ri?e gorar ruwan da shi ba. Ya saka mata chocolat ?in a ciki, kuma ba tare da ya saki hannun nata ba ya kalleta yana fa?in.

"Ki daina jayyaya Leemat. Ba na son gardama na san kin yarda da ni, tun da har kika yarda kika sha ruwan da na baki. Dan haka ki kar?i wannan ma. Kyauta ce daga MJ zuwa Leemat! Sunana Mu'az... Wata ?ila hakan zai amfaneki wata rana"

Tun da ya ri?o hannunta Halima ke kellon fuskarsa. Saboda ita ta kasa gane wannan wani kalar mutum ne. Haka kawai sai ya yi ta ri?e mata hannu ba da son ranta ba?. Saboda ?arfin hali biyan ba shi da ?an kishiya?.

Kuma ita amfanin ne sunansa zai mata. Ai tun jiya take fatan kada Allah ya sa ta sake ha?uwa da shi, yanzun ma tsautsayi ne. Kuma tana fatan kada Allah ya sake nuna mata shi har ta koma gare shi. Hannunta dake kan nasa ta janye tana goge ?wallar idonta. Sannan ba tare da tace masa komai ba ta juya ta nufi hanyar shiga cikin boutique ?in.

Sai da ta shige ciki sannan Mu'az ya yi dariya. Haka kawai halinta na saurin kuka da langwami da kuma shagwa?a suka saka shi cikin nisha?i. Motarsa ya shiga ya tayar ya bar boutique ?in. Kuma har ya isa barrack bai daina dariyar abin da Halima ta yi masa ba.

Cike da farin ciki Halima ta bu?e ledar chocolate ?in da MJ ya bata. Saboda tun tana ?arama Allah ya ?ora mata ?aunar chocolate. Kuma iyayenta na sai mata chocolate ?in sosai. Yanzu kuma da ruwa ya ?arewa ?an kada ta manta rabonta da shan chocolate ?in.

Bite na fako da ta yi sai da ya sa ta ji ta kamar a wata duniya. Saboda ta yi matu?ar kewar chocolate fiye da yanda za'a iya kwatantawa. Lokaci guda ta yi murmushi. Saboda ta tuna da yanda mahaifinta yake yawan kawo mata chocolate.

"Allah ya ji ?anka Daddy"

Ta fa?a a fili. Tana tuna duk wani kyakkyawan abu da ya gabata a rayuwata.

"Ke Halima! Zaman me kike a nan da ba za ki zo ki kama aiki ba?"

Ta juyo muryar Boss ?insu a bayanta. Da sauri ta sau?a daga kan kujerar da take. Tana zare ido kamar wadda ta yi wa sarki ?arya.

"Ki zo ki fara aikinki. Ga wasu can sun zo siyan kaya suna neman wanda zai taya su za?a!"

Ta gya?a kai da sauri tana nufar hanyar wurin da Boss ?in ya nuna mata.

_________________

_Da?ina da gobe saurin zuwa??_

_Salmanians!_

_Da alama Sir MJ dodon abinci ya ha?u da gamonsa_

_Share fi sabillilah??_

*Daga al?alamin Salma Ahmad Isah??.*
*CANDY CE??.*

--------------------
_Kada a manta da biyan ku?in littafi. Coz free pages sun kusa ?arewa. To subscribe pay ?300 to._

5487270431
Salma Isah
Monie point.

And send the evidence of payment via.

08130172702

#Candy
#SalmaAhmadIsah
ーーーーーーーーーーーーーーーーーー

*?ADDARA CE!*


*(c)SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY??*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_


*09*

MUKTAR POV.

Kamar yanda suka yi al?awarin komawa bincike layin BB hotel sun koma ?in. Amma a wanan karon da shirinsu suka tafi, ta yanda ko da za'a kawo musu hari za su iya kare kansu. Amma kuma rasa makama ya sa shi da Ali yin cirko-cirko a cikin layin da Munira ta bi sanda motar nan ta biyota. Saboda tun da suka shigo ba su ga wani me tallah ko me abin siyarwa ba. Hatta da masu wucewa sai dai ka gansu jifa-jifa.

Shi ya sa ya fa?awa kansa cewar dole ne ma a sace mutum a wannan layin, saboda babu zirga-zirga a layin. Sai dai idan har Allah ya hukunta faruwar abu a lokaci, to ba makawa sai ya faru. Dan har sun riga sun cire rai da samun wani abu. Sai Allah ya jefo da dalilin tonuwar asirin da suka da?e da son ya tonu. Saboda a sanda suke da niyyar juyawa su koma inda suka fito. Muktar ya yi arba da wata mabaraciya ta shigo layin. Hakan ya sa ya yi wa Ali magana kan ya tsaya.

Tsayawar suka yi. Kuma a kan idonsu matar ta tsaya a jikin wata bishiya. Ta shimfi?a buhu, ta zauna a kai, sana ta aje wani kwano a gabanta ta fara barar da ta saba yi kullum a layin. Muktar bai san sanda murmushi ya su?uce masa ba.

"Ali mu je"

Yace kawai. Sannan ya nufi wurin matar. Ali ya bi bayansa kamar kullum, zuwa jikin bishiyar da matar ke zaune a ?arkashinta. Har ?asa suka dur?usa suka gaisheta. Sannan Muktar ya fara tambayarta.

"Iya. Mu jami'an 'yan sanda ne. Kuma muna bincike a kan ?atan wata matashiya. A cikin binciken mu mun yi karo da wani bayani da yace an ga sanda ita wadda aka sace ?in ta shigo layin nan. Dan haka muke so mu tambayeki ko kin ga sanda ta shigo!"

Iya me bara ta jinjina kai. Sannan tace.

"To yaro, fa?a min rana da kuma lokacin da aka ga ta biyo ta nan ?in. Idan zai iyu ma ku fa?a min har da kalar tufafin jikinta. Saboda idan har nan layin ta iyo to tabbas zan ganta. Dan ni nan da kuka ganni kullum nan nake zama ina bara, sai dai idan da magariba ko da sassafe ta shigo layin. To shi ne dai ba zan sani ba!"

"To Iya. Yanzu za'a iya kaiwa kimanin wata ?aya da kwanaki da faruwar abin. Kuma ranar asabat ne da yamma. Sannan tana sanye da jallabiya kalar ruwan goro. Haka fara ce, me ?an siririn jiki!"

Muktar na kaiwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login