Showing 12001 words to 15000 words out of 35486 words
gaba?"
Muktar ya sau?e numfashi, sannan ya ?ora hannayensa a kan table ?in da ya raba tsakiyarsu da Faruk ?in.
"Duk wani CCTV camera footage na hotel ?in an goge shi. Hakan ke nuna cewa wanda ya aikata kisan ya iya takunsa. Amma kuma duk da haka ya tafka wani kuskure da zai iya sawa mu kama shi cikin sau?i!"
Cike da za?uwa Faruk yace.
"Wani kuskure ya aikata?"
"Duk yanda mai laifi zai yi wurin binne laifinsa a ?ar?arshin ?asa yana kuskurewa ta wata hanyar. To haka shi ma wannan ya kuskure. Domin akwai ?aya daga cikin masu aiki a hotel ?in da muka tambaya, ta sanar mana da cewa ta ga sanda Munira ta fito daga ?akin da Mubarak ya kama. Amma kuma kafin ta kai ga sau?a ?asa ta tsaya a ?ofar ?aki me lamba 24. Sannan ita matar tana zargin cewa akwai abin da Munira ta ga a ?aki me lamba 24, wanda zai iya zama sanadiyyar mutuwarta!"
Girar Faruk na tattarewa wuri guda ya furta.
"Ban gane ba Muktar!"
Muktar ya jinjina kansa.
"A ranar da Munira suka ha?u da Mubarak aka kashe wani ba'indiye a cikin hotel ?in, me sunan Danesh Kumar. Danesh Kumar shi ne mutumin da ya kama ?aki me lamba 24. Idan har za ka iya zurfafa tunaninka. Za ka iya gane ala?ar zance na da kuma mutuwar Danesh!"
Faruk ya yi shiru. Can kuma yace.
"Idan na fahimta dai-dai, wata ?ila a sanda Munira ta baro ?akin da Mubarak ya kama ta ga sanda aka kashe Danesh, ko kuma ta ga masu kisan, ko kuma ta ma san wanda ya yi kisan, shi ya sa ita ma aka bita aka kasheta!"
"Wanna shi ne abin da bake so ka gane"
"Amma abin tambayar a nan shi ne. Me ya sa makashin ko makasan ba su kasheta a nan cikin hotel ?in ba, sai da suka bari ta fita, sannan kuma suka bita suka saceta. Sai kuma kirana da ta yi a waccan ranar, kafin su saceta!"
"Idan za ka iya tunawa tun farko na sanar maka da cewa masu gadin hotel ?in sun sanar mana da cewa Munira ta bar hotel ?in. Kuma a ?afa, sa?anin sanda ta shigo wurin da mota, ka ga wannan ma zai ?ara tabbatar mana da cewa lallai akwai abin da ta gani. Shi ya sa ta ru?e har ta manta da motarta da ta je wurin da ita. Kuma wata ?ila makashin yana ganin idan har ya kasheta a hotel ?in asirinsa zai iya tonuwa. Shi ya sa ya za?i ya barta ta fita daga hotel ?in, domin ya kauda tunanin jami'an tsaro kan ala?ar kisan Danesh da na Munira. Kuma ya za?i sace ma duk akan wannan dalilin. Batun kiranka kuma zai iya kasancewa ta gane makashin na bibiyarta, shi ya sa ta kiraka dan neman taimako!... Amma duk da haka akwai lauje cikin na?i! Sai dai na maka al?awarin gano shi nan ba da jimawa ba abokina!"
Faruk ya sa hannayensa duk biyu ya shafa fuskarsa zuwa ?eyarsa. Ya furzar da iska yana jin kansa na ?ara dulmiyewa cikin kogin matsaloli.
"Yanzu abin da za mu yi nagaba shi ne gano ainahin inda aka saceta. Kuma za mu iya gane hakan ta hanyar wayarta. Dan a lokacin da ta kiraka aka saceta!"
Faruk ya gya?a kansa. Kafin ya mi?e ya bawa Muktar hannu suka gaisa, haka ya bar headquartern da nauyin zuciya, ya nufi barrack.
MU'AZ POV.
"Shigo!"
Ya bada umarnin bayan da aka ?wan?wasa ?ofar office ?insa. Kansa ya ?aga ya kalli me shigowar.
"Sir!"
Sojan da ya shigo ya fa?i yana sara masa da hannunsa na hagu. Mu'az ya aje pen ?in dake ri?e a hannunsa yana kallonsa.
"Dismiss!"
Sojan ya sau?e hannunsa.
"Barka da safiya sir"
"Barka. Eze me ya sa jiya baka je duty ba?"
Ya tambaya yana shafa fatar bakinsa. Sargent Chiku Eze ya washe baki, sannan ya yi taku biyu zuwa jikin table ?in Mu'az, ya aje masa containerr da ya shigo da ita. Mu'az ya kalli containerr, sannan ya kalli Eze. Da ido ya masa alama da wannan fa?. Eze ya sosa ?eya yana fa?in.
"Eh Sir. Grilled fish and potato ne matana ya girka maka!"
Mu'az ya yi murmushi. Wai shi za'a bawa cin hanci da abinci. Sai ya sau?e hannunsa a kan bakinsa, sannan ya kai hannu ya bu?e containern. Ba tare da tunanin komai ba ya fara cin abincin. Yau abinci ne fa, ai ba ya?i ci ba.
"Oh lord of mercy! Matarka ta iya girki Eze!"
Ya fa?i yana kai loma. Eze ya yi 'yar dariya, ganin dabarar kawowa oga cin hancin abinci ta yi aiki. Dan shi kam baka isa ka siye shi da ku?i ba. Ko da ace shi ba shi da ku?i kowa ya san irin arzi?in mahaifinsa. Kasancewar ?an kasuwa ne, kuma tsohon ministern ku?i a Nigeria.
Sai da Mu'az ya kusa cinyewa, sannan ya mi?e tsaye, hannunsa ri?e da containerr. Ya nufi Eze dake tsaye har zuwa lokacin. Sai ya dafa kafa?arsa suka fita zuwa wajen office ?in. Kuma har zuwa lokacin yana cin abincin.
"Eze me ya sa jiya baka zo aiki ba?"
Ya kuma dawo masa da tambayar ?azu. Lokaci guda yanayin fuskar Eze ya sauya daga fara'a zuwa mamaki da tsoro.
"Sir... Sir da ma. Matana ne ba shi da lafiya"
Mu'az ya kai loma yana gya?a kai.
"Na fahimta. Amma kuma ya aka yi matarka ta yi girki yau. Ita da bata da lafiya. Ko dan manta da wanan batun, ai lafiya ta Allah ce, haka ma jinya, zai iya ?orawa kowa ya kuma sau?e masa s sanda ya so, haka ne ba?"
Ya tambaya yana ?age masa gira. A tsorace Eze ya gya?a kansa.
"Eh haka ne. To amma me ya sa baka sanar ba. Ai ya kamata ace ka sanar da mu. Yanda matarka ta iya girki irin wannan ai ya kamata ace na je na dubata!"
Eze ya kuma ha?iye miyau. Sannan yace.
"Sir! Sir"
"Ya isa. Na san haka kawai ka ?i zuwa duty. Kuma wannan abincin bai isa ya hanani sakawa a maka hukunci ba. Dan haka ka je wurin lieutenant Bala, ka ce na ce a maka bulala hamsin!"
A take Eze ya fara rawar tsoro, hawaye suka zibo masa.
"Sir dan Allah ka yi ha?uri. Na tuba Sir, ba zan sake ba!"
"Hamsin ta yi yawa. Tun da ka ha?ani da Allah ka je a maka talatin. Idan ka kuskura ka sake magana kuma zan sa a ninka maka ita, daga talatin zuwa wasu masu kamarta sau uku. Na san ka iya lissafi!"
Eze ya ja bakinsa ya yi shiru. Ya sara masa a tsorace, sannan ya juya ya fita daga sashen office ?in nasa. Mu'az na tsaye a ?ofar office ?insa yana cin abinci Faruk ya shigo.
"Yanzu ba za ka iya ha?uri ka ci a zaune ba MJ?"
Mu'az ya kalle shi yana cusa loma a bakinsa. Kafin ya mi?a masa containern.
"Za ka ci ne?. Amma fa kayan haram ne, cin hancinsa aka kawo min!"
Faruk ya yi murmushi yana girgiza kai.
"A ci da?i lafiya. Ni ba na ci"
Ya fa?i yana shirin wucewa, amma sai Mu'az ya dakatar da shi.
"Daddy yace yau yana son ganinku a gida kai da Mariya!"
Cak Faruk ya tsaya. Sannan ya juyo ya kalle shi.
"Fatan dai ba wani abin ne ya faru ba?"
Mu'az ya girgiza kansa alamun bai sani ba.
"To Allah ya kaimu an jima ?in. Zamu zo"
"Sai kun zo"
Mu'az ya fa?i yana shiga office ?insa. A kan table ya aje containern da ya cinye abin ciki tas. Sannan ya shiga ban?aki ya wanke hannunsa da bakinsa. A sanda ya dawo cikin office ?in ya ja ya tsaya yana kallon Yasmin da bai ji shigowarta ba. Yasmin na ganinsa ta mi?e tsaye.
"We need to talk MJ!"
"Bani da wannan lokacin Yamin. Na sha fa?a miki cewar kada ki sake zuwa office ?ina. Bana tattauna abubuwan da suka shafi rayuwata a office, ki bari idan na koma gida sai ki zo mu yi magana!"
Ya kai ?arshe yana zaunawa a kan kujera. Takaici ya sa Yasmin cewa.
"A nan nake so mu yi maganar, saboda bana jin za mu sake ha?uwa bayan yau!"
"Mutuwa za ki yi ke nan?. Yasmin bai kamata ki kashe kanki a kan wanda bai damu da ke ba!"
Yasmin ta kai hannu ta goge ?wallar da ta zubo mata.
"Ko ka?an ban ta?a tunanin kashe kaina ba, domin kuwa da ace zan yi hakan da na yi tuntuni. Nan da next week zan tafi Cairo, zan je na ?arasa makarantar da soyyayarka ta hanani ?arasaww!"
Mu'az ya yi dariya.
"Da kuwa kin taimaki kanki"
Yasmin ta kuma goge ?walla.
"Mu'az ya kamata ka ji tsoron Allah. Ko da ka?an ne ya kamata ka nuna kulawa ga wanda yake sonka..."
Ya nuna kansa yana fa?in.
"Ni? Ni kuma me na yi bawan Allah?"
"A'a, ba ka yi komai ba, ni ce wadda ta yi kuskuren fara sonka, har ina zaton cewa wata rana kai ma za ka fara sona. Ashe na aikata babban kuskure. Mu'az ina maka addu'ar Allah ya ?ora maka son da zai wahalar da kai. Allah ya sakawa zuciyarka son da zai sa ka yi ?o?arin kashe kanka. Allah ya sa maka son wadda za ta hana rayuwarka sukuni, Allah ya saka maka son da zai gana maka kwatankwacin azabar da ka bani. Allah ya ?ora maka son da zai sa ka ga fari ka ce ba?i ne. Wata ?ila a lokacin za ka fahimci irin abin da nake ji. Bana maka addu'ar fara son wadda ba ta sonka, dan nasan yanda ra?a?in son ma so wani yake. Na barka lafiya!"
Ta ?arashe tana ?aukan jakarta da ta aje a kan table sanda ta shigo office ?in. Kuma har ta fice Mu'az bai ce mata ?ala ba. Dan shi yana farin cikin ficewa daga rayuwarsa da za ta yi. Kuma ko ka?an bai sa a ransa cewa addu'o'inta za su bishi ba. Tun da ya san shi bai zalunceta ba.
_Share fi sabillilah??_
*Daga al?alamin Salma Ahmad Isah??.*
*CANDY CE??.*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*?ADDARA CE!*
*(c)SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY??*
_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_
*05*
MAIMUNA POV.
Yau ba kamar kullum da ta saba siyar da kunu duka ba. An samu ragowar wanda ba'a siya ba. Kuma ga shi har ?arfe goma kunun bai ?are ba. Dan haka ta kamo hanyar gida tana hasaso yanda za su kwashe da Auwwa.
"Maimuna!"
Ta ji an kira daga bayanta. Hakan ya sa ta juya dan ganin me kiran kafin ta kai ga amsawa. Ganin Abba ne, ?aya daga cikin abokan Gambo ya sa ta amsa.
"Na'am"
Ta tsaya tana kallonsa. Har ya ?araso inda take. Duk da ba haske sosai a inda suke tana iya ganin fara'ar da yake ta yi.
"Har an dawo daga tallar ne?"
Ta gya?a kai tana son sanin dalilin da ya sa yake mata magana. Bayan da ba ya mata magana.
"Kin siyar da kunun duka?"
Ta girgiza kai.
"To yanzu ya za ki yi da wannan muguwar matar?. Na ga idan ba ki siyar ba dukanki take"
Sai ta yi shiru tana ?are masa kallo.
"Ko ba za ta dakeki ba?"
Ta kuma girgiza kanta. Sai ya sa hannu a aljihun wandon jikinsa, ya zaro ku?in da ya kai dubu biyu, ya mi?a mata.
"Ga shi idan kin je ki bata. Na san wannan zai hana ta dakeki!"
Maimuna ta kalli ku?in, sannan ta kalli fuskarsa.
"Idan har ka bani wannan ku?in ne dan Allah. Allah ya baka kadan niyya, kuma na gode. Idan kuma ka bani ne da wata manufa mummuna. Allah ya mayar maka da kayarka kanka. Kuma ina so ka san cewa duka ba ya kisa!"
Tana gama fa?in hakan ta ja siraran ?afafunta ta yi gaba. Abin da Abba ya yi bai bata mamaki ba. Saboda Allah ne ka?ai ya san adadin samarin da suka so lalata rayuwarta. Samari da dama sun sha cewa suna sonta, amma ita ta san ba soyyayar gaskiya ba ce.
?awayenta na makaranta sun fa?a mata cewar a halin rayuwar yanzu babu namijin da zai iya aureta, saboda tana da sickler. Duk wanda zai zo yace yana sonta raina mata hankali kawai zai yi. Kuma ita ma ta yarda da wannan batun nasu, shi ya sa bata sa a ka ba, in ji ?arawon tagiya.
Bata takurawa kanta cewar sai ta yi aure ba. Tun da ta kammala secondary school bata sake sakawa kanta wani buri ba. Saboda ita ma secondary school ?in da ?yar da fama Auwwa ta barta ta ?arasa. Shi ya sa ta ture ko wani irin buri da ta san tana da shi. Ta fawallawa sarkin sammai da ?assai duka lamuranta. Kuma ta san zai kawo mata ?arshen wahalar nan da take sha.
"Salamu alaikum"
Ta yi sallama daga soron gidan. Jin muryoyi uku sun amsa sallamar ya sa ta fahimci cewa ba Auwwa ba ce ka?ai a gidan. Ilai kuwa, kusan su hu?u ta samu a tsakar gida. Kuma ta san su waye, ?annen Auwwan ne daga cikin gari.
"Anti Kubura ina wuninku!"
Ta gaishe su tana tsuggunawa. Ciki-ciki suka amsa. Kuma ita bata damu ba, dan idan da sabo ta saba. Tana shirin mi?ewa Auwwa ta dakatar a ita da fa?in.
"In ji dai kunu bai ?are ba?"
Ta sau?e ajiyar zuciyar kwanciyar hankali. Dan ta san tun da su Kubura suka zo su za'a bawa sauran kunun. Da ace ba su zo ba kuwa yau da ta yabawa aya za?inta a hannun Auwwa. Da sauri ta gya?a kai tana aje bokitin.
"Akwai saura"
"Shiga kitchen ki ?auko kofuna ki zubawa su Kubura!"
"To"
Maimuna ta amsa da sauri. Sannan ta mi?e ta shiga ?an ?aramin kitchen ?in gidan. Ta ?auko kofuna hu?u. Ta zube kunun da ya yi saura a bokitinta, ta mi?awa ?annen Auwwa.
Daga nan ta shiga ban?aki ta ?auro alwala. Sannan ta shiga ?akinta ta yi sallah. Ta fito ta zauna tana jin yunwa, a gefe guda kuma tana jin tsoron tambayar Auwwa abinci.
"Ub*n miye za ki zo ki zauna ki samu a gaba kina jin zancen da muke?"
Auwwa ta fa?i cike da hantara. Maimuna ta sinne kai tana fa?in.
"Yun... Yunwa nake ji!"
"Saboda ub*nki ne yake kawowa abincin da zan girka ai dole ki ce min kina jin yunwa. To na yi na bawa 'yan uwana sun cinye... Sai a tashi a kaini gaba"
Ta sunkuyar da kanta, ?walla na taruwa mata a cikin ido. Kafin ta mi?e ta fita daga gidan. Da ta rasa inda za ta je sai ta nufi unguwar Chadi a cikin wannan daren. Dan ba ta son ta cika kaiwa Mummyn su Maryam matsalolinta. Jiki da jini, wata rana za ta iya gajiyawa da ita. Dan haka gwanda ta je wurin dolenta, wato gidan kakarta.
Da yake tsakanin unguwar Fantai da Chadi ba nisa sai bata sha wahala wurin isa ba. Tun daga soro ta fara shagwa?e fuska, dan ta san ta zo inda za'a share mata hawaye. Sallamar ma a shagwa?e ta yi, ta shiga cikin gidan tana wani bubbuga ?afa a ?asa.
"Wani irin iskanci ne kuma wannan Maimuna?"
Hajja dake zaune a cikin ?akinta ta tambaya. Maimuna ta ?arasa cikin ?akin tana turo baki gaba.
"Hajja"
Ta kira tana zama kusa da kakarta. Hajja ta dubi jikar tata cike da tausayawa.
"Na'am mai sunana"
"Hajja yunwa nake ji. Rabona da abinci tun safe"
Ta fa?i a shagwa?e tana shafa cikinta. Hajja ta girgiza kanta.
"Jeki ki ?iba abincin a cikin cooler. Yana nan a rumfa"
"Da yawa fa zan ?iba"
"?ibi wanda zai isheki"
Ta mi?e ta fita da murnarta. Ta ?auki kwano ta zubo tuwon shinkafa da miyar taushen da Hajja ta girka. Ta bu?e ?an ?aramin fridge ?in Hajjan, ta ?auki pure water. Ta dawo ?akin ta zauna. Ta shiga ci tana bawa Hajja labarin abin da ya faru da ita yau, ciki har da ha?uwarta da Abba.
"To yanzu Maimuna. Da kika masa haka, idan kuma da gaske yake yana sonki fa?"
Maimuna ta dakata daga kai loma bakinta. Ta mayar da abincin da ta ?ebo cikin kwano. Sannan ta kalli Hajja.
"Hajja ban bari ya kai ga furta min hakan ba. Saboda na san ba zai min soyyaya tsakaninsa da Allah ba. A irin halin da nake ciki bana jin akwai namijin da zai soni"
Hajja ta girgiza kai.
"Ba komai Maimuna ?addara ce!. Ki ci gaba da ha?uri, Allah ya san da ke. Kuma zai kawo miki sauyin rayuwa"
Maimuna bata sake cewa komai ba. Har ta kamalla cin tuwonta. Ta fito da kwanon waje. Ta wanke hannunta ta dawo ta zauna kusa da Hajja.
"Ina Kawu ne? Tun da na shigo ban ji motsinsa ba"
"Ya tafi jajantawa Alhaji Babangida. Saboda asarar da ya yi a satin nan."
Maimuna ta gya?a kai.
"Ah, Maimuna. Duba cikin jakar can tawa, za ki ga leda ki ?auko"
Cewar Hajja. Maimuna ta mi?e ta nufi jakar. Sannan ta bu?e ta ?auko ledar dake ciki. Ta dawo kusa da Hajja ta zauna.
"Hajja ga ledar"
Hajja ta kar?a ta bu?e, sannan ta fito da hijabai biyu dake ciki, da abonaki, da kuma audugar mata.
"Gasu nan. Duka naki ne na sai miki a bakin asibiti. Na san yanzu sanyi ya shigo, kina bu?atar abonaki... Kuma idan za ki tafi zan baki kwaki da ?anzo. Ki ?oye a ?akinki idan kin koma. Duk ranar da Auwwa za ta hanaki abinci sai ki ?auka ki ci"
Maimuna ta yi murmushi ta kwanta a jikin kakarta.
"Ina sonki Hajja"
Hajja na murmushi ta shafa kan gudaliyar jikarta.
"Allah ya ji ?an Muhammadu da Asabe (iyayen Maimuna)."
"Amin Hajja"
Ta amsa tana jin kewarsu, duk kuwa da kaf cikinsu babu wanda ta sani. Sai dai a hoto ko ta ji labarinsu.
FARUK POV.
Tsaye ya yi a ?ofar ?akin Mariya yana kallonta. Yayin da take yafa mayafi a kanta. Alamun ta shirya tsaf domin ziyartar gidansu. Idonsa ya zarce kan Hilal dake zaune a kan gado. A hankali ya saki handle ?in ?ofar ya shiga ciki. Kallo ?aya Mariya ta masa ta ?auke kai. Shi kuma bai ma kalleta ba, Hilal kawai ya ?auka, sai a sannan ya kalleta.
"Kin gama shiryawa ne?"
"Umm"
Amsarta ta fito a ta?aice kamar kullum. Kansa kawai ya gya?a, sannan ya nufi ?ofa yana fa?in.
"Ina jiranki a mota"
Sannan ya fita daga ?akin. Kai tsaye ya sau?a ?asa, ya shige motarsa dake parking lot. Ya zauna a ciki, tare da zaunar da Hilal a kan cinyarsa. Yana jiran fitowar Mariya.
Ido kawai ya tsira mata a sanda ta fito daga ?ofar falo. Saboda kalar kwalliyar da ta yi. Wata kyakkyawar atamfa ce da ya sai mata a Khadeeja Candy store a jikinta. Atamfar me ratsin