Showing 21001 words to 24000 words out of 35486 words
take ?aukan albashinta ba ta ga dalilin da zai sa ta ci wannan abincin ba.
Amma ita ko da wu?a za'a ?ora a wuyanta ace nawa ne albashinta ba ta sani ba. Ko kalarsu ba ta gani, daga an yi albashi Kawu Sani yake zuwa ya kar?a da kansa. Tsakaninta da shi kawai shi ne ku?in abin hawa.
Gaba ?aya yau zuciyarta ta fi ko yaushe jagulewa. Na farko abin da Wannan ko??a?en mugun sojan ya mata. Na biyu ga kumatunta da take jinsa kamar ba a jikinta yake ba. Sai kuma wannan tuwon da take cinsa a dole. Dan cusawa kawai take. Amma sam bakinta babu wani ?an?ano.
*Efab metropolis Estate, Gwarinfa, Abuja.*
*10:18 na dare.*
MUKTAR POV.
Motar Ali ce ta yi parking a ?ofar gidan. Sannan a hankali ?ofar dake gefen driver ta bu?e. Ya fito daga cikin motar, sannan ya rage tsayinsa ya le?a kansa ?asan windown. Yana kallon Ali dake cikin motar.
"Gobe ka zo ka ?aukeni da misalin karfe takwas!"
"Okay sir!"
Ali ya amsa.
"Sai da safe!"
"Sai da safe sir"
Daga haka ya mi?e, sanna ya juya ya nufi gate ?in gidansu. Motarsa da Ali ke ja na barin wurin aka haske shi da fitilar babur. Hakan ya sa ya kare fuskarsa da hannunsa ?aya. Sannan ya juyo yana son ganin mashin ?in. Amma kuma yanda me mashin ?in ya haske shi ya sa bai iya ganin mashin ?in ballantana me shi.
A lokaci guda tunaninsa ya hasko masa lokacin da ya lura da wani me mashin da yake bibiyarsu. Sai ya yi murmushi, sannan ya juya bayansa yana sau?e hannunsa da ya rufe fuskarsa da shi. Sannan hankali kwance ya ?wan?wasa ?aramar ?ofar shiga gidansu.
Ganin haka ya sa me mashin ?in ya tako mashin ?in nasa da gudu. Ya iyo kan Muktar da shi. Sai dai kafin ya kai ga isa inda yake har me gadin gidan ya bu?e ?ofar, shi kuma Muktar sai ya yi amfani da wannan damar ya fa?a cikin gidan da sauri. Sanna ya datse ?ofar gidan.
"Yalla?ai lafiya?"
Me gadin da ya bu?e masa ?ofar ya tambaya. Amma Muktar bai amsa shi ba. Sai wayarsa da ya zaro ya aikawa da Ali kira.
"Hello Ali. Idan baka yi nisa ba ina so ka dawo da gaggawa. Wannan mutumin na kan mashin ne ya biyoni har gida ina so ka dawo ka tare min shi!"
Ya fa?i bayan da Ali ya ?aga kiran.
"Okay sir"
Ali ya amsa daga cikin wayar. Muktar ya kashe wayar, sannan ya sau?eta daga kunnensa. Ya ?ara matsawa jikin gate ?in ya le?a. Sai ya ga har yanzu mashin ?in na nan. Ya dawo baya yana kaikawo. Shi ko me gadi ya sa shi a gaba yana kallo, dan ya kasa gane abin da yake faruwa.
Yana tsaye a wurin ya ji dirin motarsa da Ali ya dawo da ita. Hakan ya sa ya bu?e ?ofar da sauri ya fita. Amma sai ya ga me mashin ?in ya tayar da shi ya ja shi da gudu. Kuma shi ma Alin sai ya bi bayansa da mota. Yana tsaye a wurin Ali ya dawo. Kuma tun da ya ga Alin ya dawo shi ka?ai ya san cewa bai samu damar kama shi ba.
"Sir ya kufce mana"
Fa?in Ali da ya fito daga mota. Ba tare da yace komai ba ya gya?a kansa. Sannan ya sallami Ali ya koma cikin gidan. Ya tsaya a wurin me gadi tare da fa?a masa cewar.
"Duk wanda ya zo kada ka kuskura ka bu?e masa gate ?in nan.!"
Me gadi ya gya?a kai cike da bin umarni. Dan tun da ya ji haka to akwai matsala. Daga wannan umarnin Muktar ya juya ya nufi cikin gidan. A ?ofar shiga falo ya cire takalman ?afarsa, sannan ya bu?e ?ofar falon ya sa kai, bakinsa ?auke da sallama. Mahaifiyarsa da kuma ?aninsa dake zaune a falon ne suka amsa masa. Kuma a tare suka dube shi.
"Ya Mukhy sannu da zuwa"
Ya yi murmushi yana kallon ?aninsa.
"Sannu Walid... Karatu ake ne?"
Ya tambaya yana kallon littatafan dake gaban Walid ?in. A lokaci guda kuma yana zama kusa da mahaifyarsa.
"Eh, muna da test on monday"
"To Allah ya taimaka... Mama ina wuni"
Ya ?arashe yana gaida mahaifiyarsu. Mama ta amsa da murmushi.
"Lafiya Muktar. An dawo ke nan?"
"Eh Wallahi... Bari na je na ?an watsa ruwa na zo na ci abinci"
Ya fa?a yana mi?ewa tsaye.
"To sai ka fito"
Ya gya?a kansa. Sannan ya nufi corridorn dake ?unshe da ?akunansu shi da Walid. ?akinsa ya shiga. Kuma ya na shiga ya kulle ?ofar ?akin. Sannan ya zaro wayarsa ya aikawa Kaigama ?ira. Bugu uku ya ?aga da sallama.
"Wa alaikassalam. Kaigama!"
Daga ?ayan ?angaren Faruk ya amsa.
"Na'am Mukhy... Fatan dai lafiya?"
"Lafiya, amma ba lau ba..."
Nan ya kwashe kaf abin da ya faru tun daga ranar da ya je BB hotel domin bincike har zuwa kan wanda ya faru yau. Ya zauna a bakin gadonsa yana ?arawa da.
"... Duk yanda aka yi wannan mai laifin ba mutum ?aya ba ne. Wata ?ila su biyu ne, ko uku, ko hu?u. Ko kuma ?ungiya garesu. Kuma ina da tabbacin suna da ?arfin ikon yin duk abinda suke so. Saboda idan ba haka ba babu ta inda za ayi su shigo unguwarmu. Ka san yanda matakan tsaro suke da tsauri a nan. Ammz abin yana bani mamaki!"
Faruk ya sau?e numfashi. Sannan yace.
"Mukhy! Idan har kana ganin wannan case ?in zai iya shafar personal life ?inka zai fi kyau ka aje shi. Ni da MJ za mu iya ?arasa shi!"
Muktar ya girgiza kansa.
"Kaigama. A baya ban sanka ba, amma wannan binciken shi ne ya ha?ani da kai. Kuma tun da na fara wannan binciken ba na jin zan aje shi ba tare da na kai ?arshensa ba. Idan har zan ji tsoron abin da zai same ni ko ahalina a kan aikina to me ya sa zan fara?. Da ma can na riga na saba da irin wannan abin... So dan haka ba na so ka saka kanka a cikin damuwa, zan ci gaba da bincike a kan wannan case ?in har sai na kama me laifin nan!..."
Faruk ya yi murmushi.
"Na gode sosai Muktar. Allah ya saka da alkairi"
"Kada ka damu. Da yardar Allah mun kusa kaiwa ?arshen wannan binciken. Duk wani ci gaban da aka samu i will give you a touch!"
"Na gode sosai. Sai da safe"
"Okay sai da safe"
Muktar ya aje wayar, sannan ya shafa kansa. Ya yi shiru yana nazari, bisa ga dukkan alamu wanna case ?in ba ?arami ba ne kamar yanda suke tunani. Dan haka yana bu?atar fa?a?a tunaninsa domin kaiwa ?arshensa. Daga haka ya mi?e tsaye, sannan ya shiga barthroom dan ya watsa ruwa a jikinsa.
*No.53, off Justice Clara Ogunbiyi street, Asokoro, Abuja.*
MIMA POV.
Ita da wata cousin sisternsu ne zaune a falo suna gulmar Mu'az. Mima ta dage tana shararowa budurwar me suna Zulaihat labarin kalar cin abinci irin na Mu'az.
"... Kin ga fa waccan layyar haka bawan Allahnan ya cinye rabin ragon da ya yanka tun a ranar farko!"
Zulaihat ta zare ido cikin fa?in.
"Rabin rago fa Mima? Ban da sharri dai!"
Mima ta ta?e baki.
"Wallahi da gaske nake. Kin san ai ba zan miki ?arya ba. Kin san Anti Maryama ce ta zo ta tayamu suya waccan layyar. To in fa?a miki Ya Mu'az zuwa ya yi compound ya aje kujera, ya hau ya zauna yana aika Na'im ya je ya ?ebo masa idan an soya. Ana soyawa yana ci, kan ki ce me har naman ya fa?a. Haka Anti Maryama ta yi ta mamakin ?arewar naman. Da aka tambayi Gogan ina nama sai yace ai shi ya cinye kayansa. Anti Maryama har da cewa an yakuwa Mu'az mutum ne?"
Zulaihat ta kwashe da dariya Mima na tayata.
"Wallahi. Ai wannan mutumin da kika ganshi kura ma haka ta ga ta ?yale a kan cin nama. Ya Mu'az? Humm!"
Bata kai ga rufe bakinta ba, Mu'az ?in ya bu?e ?ofar falo ya shigo. Saurin gimtse bakinta ta yi. Ta shiga zara ido tana fa?in ta shiga uku a ranta. Dan ta ?auka cewa ya ji abin da tace, idan kuwa har ya ji ai yau sai ?an buzunta a gidan nan.
Amma kuma sai ta ga ko kallonta bai yi ba har ya zauna a kan sofa. Hakan ya sa ta gane cewa bai ji abin da tace ba. Ajiyar zuciya ta yi, dan ta san da ace ya ji babu abin da zai hana ya laka?a mata na jaki. Saboda Mu'az bai iya kauda kai a kan laifi ba. Daga zarar an masa yake mayar da martani.
Amma kuma ba shi da ru?o. Dan daga zarar ka masa laifi ya amayar da abinda ka masa zai manta, mintuna ka?an za ka ga ya dawo yana maka magana da kansa. Kuma da ma yawancin mutum mafa?aci haka yake.
A sace ta ci gaba da kallonsa. Har ta lura da kamar akwai abin da yake damunsa. Ta riga da ta san halin yayanta. Abu ne mawuyaci ya ganta zaune a falo bai mata magana ba. Ko da ko ita bata fara masa maganar ba, ko tsokanarta ne zai yi.
"Ya Mu'az ina wuni"
Zulaihat ta gaida shi. Sai ya juyo ya kallesu da mamaki. Dan shi a sanda ya shigo kwata-kwata tunaninsa bai ba shi cewar akwai wani ?an adam a falon ba.
Kuma ba komai ya ja hakan ba face wani halin damuwa da zuciyarsa ta shiga yau ka?ai. Gaba ?aya tun bayan abin da ya faru a Ummul Banat boutique ya rasa nutsuwarsa. Zuciyarsa da gangar jikinsa na fa?a masa cewar ya aikata ba dai-dai ba.
Amma kuma ?wa?walwarsa ta kasa yarda da hakan. Gaba ?aya shi ji yake cewar bai aikata ba dai-dai ba, tun farko wa yace ta buge shi, har ta zuba masa ruwa a jikinsa?. Sai dai kuma wani sashi na zuciyarsa na fa?a masa cewar ya aikata kuskuren marinta. Bai kamata ace tashin farko ya mareta ba, ya kamata ace sai da ya tambayi ba'asi tukkuna.
Amma ya zai yi?. Zuciyarsa ce a kusa, abu ka?an ke sawa ya harzu?a, kuma shi daga ya fusata yake mayar da martani. Ture wannan tunanin dake damun kansa ya yi, sana ya amsa gaisuwar Zulaihat.
"Lafiya Zulaihat... Ya gida?"
"Gida lafiya"
Ta amsa tana satar kallon idon Mima da har yanzu a tsorace take. Kuma ba ta ?ara razana ba sai da Mu'az ?in ya kalleta.
"Mima ina Mummy?"
Ta ha?iyi yawu, sannan ta amsa masa da sauri.
"Tana ?akinta"
"Me aka dafa yau?"
Ya kuma tambaya.
"Tuwo aka yi. Amma Mummy tasa na dafa maka jollof ?in couscous"
"Kin saka nama ko kifi?"
Ta ?an kalli Zulaihat, dariya na son kufce mata. Sannan ta kalle shi tana amsawa.
"Eh. Na saka maka catfish"
"Zuba min Please"
"To"
Ta fa?a tana mi?ewa, sannan ta nufi kitchen. A lokacin Na'im ya sau?o daga sama. Kuma yana sau?owa ya yi kan Mu'az.
"Ya Mu'az ka siyo min sweatern?"
Na'im ya tambaya yana zaunawa kusa da shi. Maganar sweater ta tuno masa da yanda aka yi ya aje sweatern. Lokaci guda hoton ya taho ha?e da na fuskarta, da kuma na idanuwanta da ya fi kalla a fuskar tata. Maimakon yace wani abu sai ya dafe kansa yana fa?in.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Na'im ya ta?a shi.
"Baka da lafiya ne Ya Mu'az?"
Sai ya girgiza kansa yana ?agowa da shi. Sannan ya ?a?alo murmushi.
"Lafiyata ?alau. Na manta da siyan sweatern ne. Amma gobe inshallah zan siyo maka!"
Yana fa?in hakan ya mi?e tsaye, ya nufi hanyar fita daga falon. Mima da ta fito daga kitchen, hannunta ri?e da plate ?in abincinsa tace.
"Ya Mu'az ga abincin!"
Sai ya juyo ya kalleta. Ba tare da ya ce komai ba ya nufeta, sannan ya kar?i plate ?in. Ya juya ya fita daga part ?in Mummy ba tare da yacewa kowa komai ba. Har ya fice su Mima ba su daina mamakin abin da ya hana shi sukuni ba.
A falon part ?insa ya zauna, ya saka abincin da ya kar?a a wurin Mima a gaba yana kallo. Ya kasa ci, kuma ya rasa yanda zai yi da shi. Can kuma sai ya ja wani dogon tsaki.
Haba mana. Ya za ayi wata yarinya ta shigo tunaninsa ta takurawa rayuwarsa, ta hana shi sukuni haka kawai dan ya mareta?. Mutum nawa ya mara a kan sun masa laifi?. Sai ita da aka ?erata da gwal?. Za ta takurawa tunaninsa?. Idan har ta sake shigo masa tunani sai ya je har Ummul Banat boutique ?in ya hukuntata.
Da wannan maganar da zuciyarsa ta ra?a masa ya samu sukunin cin abinci. Har ya taso ya koma ?aki. Ya cire rigar jikinsa ya kwanta a kan gado. Ya kashe wuta da niyyar yin bacci. Amma sai baccin yace ai ba su yi yarjejeniya da shi kan zai ?auke shi a wannan lokacin ba. Tunaninta kuma ya ?ara dawo masa. Idanuwanta da suke ?yallin ?wallar da take zubarwa sun fi komai takura masa.
Hannu ya kai ya ?auki pillow ya danne kansa da shi, wai ko za ta fice masa a cikin tunani. Amma Wallahi ba ta fita ba. Daga ?arshe ma sai ya mi?e zaune a kan gadon, sannan ya dafe kansa yana fa?in.
"Ya isa Mu'az. Ya isa!"
Ya fa?awa kansa yana shafa saitin zuciyarsa. Sannan ya ?ara da.
"Babu abin da ya ha?a hanyarka da ta waccan yarinyar. But she's innocent!..."
Wani zancen ya shigo cikin wani. Sai ya rintse idonsa yana furta.
"Oh lord of mercy. Na shiga uku ni Mu'azzam!"
Ya bu?e idonsa. Sannan ya sau?a daga kan gadon. Ya shiga bayi, ya yi wani sabon wankan, wai ko zai samu yarinyar ta fita daga kansa. Ko da ya dawo ?akin ya kwanta ba ta sauya zani ba.
Daga ?arshe sai ya mi?e ya zauna a tsakiyar gadon ya shiga yin salatin annabi. Wata ?ila Allah ya dube shi ya kawo masa ?auki. A ranar bai yi bacci ba sai da ya sa a ransa cewar zai je ya bata ha?uri, kuma ya amin ce cewar ya aikata mata ba dai-dai ba.
Zuciyarsa ma sai da ta raya masa cewa wata ?ila ma mayya ce. Shi ya sa ta hana shi baccin dare. Amma dai ko ma aljana ce zai je ya bata ha?uri, in ya so ta ci kanta ta sha ba?in ruwa.
°°° °°° °°°
_Humm Humm Humm_
_Garin da?in kowa ya kama da wuta. In ji Malam Tsalha mijin me Koko.??._
_Da alama Halima da Kairat sun yi addu'a a bakin 'yan amin._
_Sir MJ dodon abinci ya kasa sukuni saboda kuskuren da ya aikata mata_
_Wai ni ina Maimuna ne?_
_To a yi dai mu gani_
_Share fi sabillilah??_
*Daga al?alamin Salma Ahmad Isah??.*
*CANDY CE??.*
--------------------
_Kada a manta da biyan ku?in littafi. Free pages sun kusa ?arewa. To subscribe pay ?300 to._
5487270431
Salma Isah
Monie point.
And send the evidence of payment via.
08130172702
#Candy
#SalmaAhmadIsah
°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*?ADDARA CE!*
*(c)SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY??*
_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_
*08*
*Unguwar Fanisau, Ha?ejia local government, Jigawa state.*
"Maryam! Maryam! Maryam ke!"
Mummy dake cikin kitchen ta ?walawa Maryam dake zaune da Maimuna a falo kira.
"Na'am Mummy"
Maryam ta amsa tana nufar kitchen ?in. Ta tsaya a ?ofar kitchen ?in, sannan ta le?a kanta ciki.
"Mummy ga ni"
"Tsabar iskanci kina ji ana kirana amma ba za ki iya kawo min wayar ba?"
Maryam ta ?an yi dariya irin ta marasa gaskiya ta na sosa kai.
"Yanzu za ki je ki ?auko min wayar ne? Ko tsayuwa za ki ci gaba da yi a nan har Mahadi ya bayyana?"
Da sauri Maryam ta dawo falo, inda Maimuna ke zaune tana cin abinci. Ta ?auki wayar Mummu dake chargy. Sannan ta kai mata wayar ta dawo ta zauna a wurin Maimuna. Ganin mahaifiyarta ce mai kiran ya sa Mummy ta bi bayan kiran. Bugu uku Hajiya ta ?auki wayar da sallama.
"Hajiya Ina wuni?"
Mummy ta gaisheta cike da girmamawa.
"Lafiya ?alau Bara'atu!. Ya gida ya yaran?"
"Lafiyarsu ?alau. Alhamdullilah. Ya wurin su Faruk da matarsa, Dan Adam mun yi waya da shi ?azu"
"Faruk lafiya, amma ba lau ba Bara'atu!"
Jin hakan ya sa girar Mummy tatarewa wuri guda. Sannan tace.
"Me ya faru da shi?"
Hajiya ta girgiza kai.
"Matsalar Mariya ce ba komai ba. Duk da dai shi da kansa bai furta min hakan ba. Amma kuma ni na gane hakan tun ba yau ba!"
Mummy ta girgiza kanta.
"To ya za ayi Hajiya?. Tun da shi ba zai iya fa?ar matsalarsa ba ballantana a ba shi shawara sai a taya shi da addu'a!"
Hajiya ta sau?e numfashi.
"To... Haka ne... Allah ya dai-daita tsakani..."
Daga gaka suka ?an taba hira, kafin suka yi sallama. Ko da Mummy ta gama abin da take a kitchen ?in sai ta fito. Inda ta samu Maimuna da Maryam zaune a falo.
"Maimuna ya kamata ki tafi gida. Na ga lokaci ya ?ure. Kar Auwwa ta dakeki!"
Maimuna ta mi?e tsaye tana fa?in.
"To Mummy, bari na tafi!"
"Ga shi kuma yau Sadiq ba ya gari. Ballantana su raka ki shi da Maryam"
Maimuna ta girgiza kai tana fa?in.
"Ai ba komai Mummy. Zan iya tafiya Ni ka?ai"
Mummy ta jinjina kai.
"To mu kwana lafiya"
"Allah ya tashemu da alkairi"
"Amin"
Maimuna ta yi wa Maryam sallama, sannan ta fita. Tana tafiya a hanya tana tuna dalilin fitarta cikin wanna daren, kuma ba komai ya ja hakan ba face abinci da Auwwa ta hanata kamar yanda ta saba a wasu lokutan. Dan wani lokacin idan 'yan imanin na kusa ba ta hanata.
"Assalamu alaikum"
Ta yi sallama daga soron gidan. Sannan ta shiga. Gabanta ne ya soma fa?uwa tun da ta yi arba da Auwwa tsaye a tsakar gidan. Ta ?ame a gu ?aya. Hannunta kan ?ugu tana jijjiga kamar me shirin hawa bori. Tun da ta ga haka ta san cewa yau kam ta banu.
"Daga gidan ub*n wa kike?"
Auwwa ta tambaya. Maimuna ta ha?iye yawu jikinta na rawa. Sannan tace.
"Gi... Gi... Gidan su... Maryam na je!"
"Saboda ke gaki kwa?ayayyiya ko?... Su kuma ga su dangin waliyyai, masu zuciyar tausayi?... Shi ne kika ?auki ?afa kika tafi gidan..."
Ta dakata tana cafkowa hannunta. A take Maimuna ta fashe da kuka. Sannan ta soma ro?on Auwwa.
"Dan Allah Auwwa ki yi ha?uri! Dan Allah! Dan Allah!.."
Auwwa ta ?aga ?ayan hannunta da bata ri?eta da shi ba, ta doke mata baki har sai da jini ya fara fita daga bakin nata. Maimuna ta fashe da wani sabon kuka, a sanda ta ga Auwwa ta nufi gindin murhu da ita.
A gaban murhun ta dur?usar da ita, sannan ta sa wani cokali a cikin murgun, ta ?aiko garwashi, ta ?ora a kan