Showing 27001 words to 30000 words out of 35486 words
aya Iya me Bara na bu?e bakinta.
"?warai kuwa yara. Na ga sanda ta wuce ta nan. Kuma ka ga can..."
Ta ?an yi fasali tana nuna musu ?ofar wani gida, Muktar da Ali suka juya suka kalli gidan, sannan suka sake kallonta a tare, sanda ta ci gaba da fa?in.
"... A ?ofar gidan can wata ba?ar mota ta tsaya. Wasu mutum biyu mace da na miji da ba?a?en kaya suka fito daga ciki, sannan suka ?auketa suka jefa cikin motar!... Ni kuma ganin hakan ya sa na tsorata, shi ya sa na yi gum da bakina ban ta?a fa?awa kowa ba"
"To iya shin kin iya ganin fuskokin wa?an da suka ?auketa?"
Muktar ya tambaya da sauri. Iya me bara ta girgiza kanta.
"A'a. Ban gani ba. Amma ranar da aka saceta akwai wani matashi ?an can gidan da shi ma ya ga sanda suka saceta, kuma har hoto me motsi ya ?auke su a wayarsa. Da yace zai fa?awa 'yan sanda, amma sai mahaifinsa ya hana shi!"
Muktar da Ali suka dubi juna. Sannan suka jinjina kai a tare.
"Iya me nene sunan matashin?"
"Audil"
Iya ta amsa. Yanda ta kira sunan Audil ?in instead of Abdul ya sa su yin dariya. Kafin Muktar ya ?ebo ku?i ya bata. Har suka bar wurin tana saka musu albarka. A ?ofar gidan da ta nuna musu suka tsaya. Ali ya yi sallama. Sannan suka tsaya jiran fitowar masu gidan.
Da farko mahaifin Abdul ?in ne ya fito. Sai da suka masa bayanin abin da ke tafe da su, sannan ya kira Abdul ?in. Ya saka su a gaba yana son ganin abin da zai faru. Dan ko sama da ?asa za su ha?e ba zai bari su tafi da ?ansa headquarter ba. Idan videon suke son kallo shi bai hana ya nuna musu ba. Za ma su iya turawa a nasu wayoyin, amma su tafi da ?ansa shi ne abin da ba zai lamunta ba.
"Abdul. Idan har ka san kana da videon nan a wayarka. Ka daure ka nuna mana. Saboda idan har ba ka nuna mana ba rayuwar sauran al'ummar gari tana cikin ha?ari!"
Abdul da ya sunkuyar da kansa ya ?ago ya kali babansa. Wanda ya har?e hannaye a ?irji yana kallon kowa cikinsu. Sannan ya kalle su.
"Idan da akwai a wayarka ka nuna musu. Ni ban hana ba, amma fa daga nan babu inda za ka ?ara ?aga ?afarka. Ba zan bari ka tafi ko ina ba Wallahi!"
Fa?in baban Abdul. Kuma kalamansa suka sa Abdul ya sa hannu a aljihun wandon jikinsa. Ya ?auko wayarsa ya cire password. Sannan ya nemo videon a inda ya ?oye. Ya kunna, ya mi?awa Muktar.
Muktar ya kar?i wayar da dukkan zumu?in duniya. A zatonsa zai ga abin da zai kawo ?arshen matsalar ne. Bai sani ba cewa yanzu ne ma matsalar za ta soma. Saboda tonuwar asirin makashin ba ya nufin zuwan ?arshen matsalar. Sai dai ma ya zama wani sabon mafarin tarin matsaloli.
Da farko da ya ga videon da fuskar macen dake cikinsu bai yarda ba. Sai da ya dawo da shi baya ya sake kalla, ya sake sakewa, wai dan ya tabbatar da abin da yake gani ko gaskiya ne. Duk da sau ?aya ya ta?a ganin matar Faruk ya ganeta. Saboda kwanaki da yake ta neman layin Faruk ?in ba ya samu ya sa ya tafi gidansa. Kuma a nan ya fara ganinta. Duk da ba wai ya tsaya ya ?are mata kallo ba ne a wancan lokacin ya ganeta a nan.
Kuma idan zai iya tunawa, Faruk ya sanar da shi cewar Mariya matarsa ?anwar Mu'azzam Gimba ce. Kuma ya san waye Alhaji Jibrin Gimba Gashuwa GG. Mutumin arzi?i me halin ?warai. Me dattaku da halin girmamawa ga na?asansa ba ma ga wanda ke samansa ba. Lalle akwai magana!.
Yanzu me zai sa matar soja. ?anwar soja, 'yar babban mutum kamar GG ta aikata garkuwa da ?an adam, da kuma kisan kai?. Gaba ?aya ya kasa ganewa. Idonsa ya ?aga ya kalli Abdul dake fa?in.
"Lokacin da suka tsayar da motarsu a ?ofar gidan nan na fito. Ganin suna shirin saceta ya sa na yi saurin komawa gida, na ?uya a bayan ?ofa na na?i wannan videon..."
Idonsa ya sake ?aukewa daga kan Abdul ?in. Sannan ya mayar da shi kan wayar ya na kallon bidiyon a karo na barkatai. Kansa ya jinjina yana mi?awa Ali wayar. Wai ko shi ma zai kalli videon dan ya tabbatar da fuskar wa cece a videon.
MARIYA POV.
Kamar yanda ta saba damawa Hilal custard haka yau ma shi ta dama masa. Sannan ta ha?a shi da shi. Wai ko ya yi shiru kunnuwanta su huta da kukan da yake mata tun safe. Tana saka masa baby bottle ?in a baki ya yi sarin saka hannunsa ya dafe ya fara sha.
Ta juya idonta cike da gajiyawa da halin yaron. Ita ba dan tana so ta sadaukar da shi ga shai?an ba ma da ta kasheshi rana ?aya kowa ma ya huta. Ba jimawa da fara shan custard ?in nasa tafara jin ?oyi. Hakan ke nuna mata cewar kashi ya yi.
Cike da jin haushi ta sa ?an yatsanta ta dungure masa kai tana hararsa kamar ta samu abokin fa?anta. Ai ko ka zauna da shi daga nan har zuwa sanda ub*nka zai dawo ya wanke maka. Dan ni bani da wannan lokacin.
Ta fa?i a zuciyarta tana tashi daga kan kujerar da take zaune. Ta haye sama ta barshi zaune a falo yana shan custard ?in. Juyawa ta yi ta saka sakata a ?ofar ?akinta bayan ta shiga ciki. Ta juyo tana baza idonta a cikin ?akin. Saboda jikinta ya bata cewar Lawan abokinta na ?ungiyar bayin shai?an na cikin ?akin. Kuma shi ne dalilin da ya sa ta kulle ?ofar ?akin.
"Gani a nan"
Ta juyo muryarsa a bayanta. Hakan ya sa ta juya. Tsaye ta ganshi a jikin ?ofar yana kallonta, fuskarsa ?auke da murmushi. Ita ma murmushin ta yi tana nufarsa.
"Sa?o ne daga fadar shugaban bayin shai?an!"
Jin hakan ya sa fara'ar dake fuskarta ta ?auke. Ta maida hankalinta duka kansa, domin jin sa?on da ya sa Wahash ya aiko shi gareta.
"A jiya Shugaban bayin Shai?an ya sa ?aya daga cikin bayin shai?an ya je ya kashe wannan ?an sandan. Amma kuma sai aka yi rashin sa'a ya sha. Kuma a yanzu haka yana da hujjar da take nuna cewa ke ce kika sace Munira, sanin cewa ke ce kika sace Munira na nufin ke ce wadda kika kasheta..."
Cike da razani Mariya ta zaro idonta. Ganin Lawan na murmushi ya sa tace.
"Amma Lawan me ya sa za ka na murmushi a cikin irin wannan yanayin?"
"Haba rezor. Ai abin bai kai mu tada hankalinmu ba. Kada ki manta da cewar shai?an na tare da mu. Da ?arfin tsafin da ya bamu ni da ke za mu iya kawowa ?arshen ?an sandan nan"
Idonta ta juya tana jin kwanciyar hankali ta fara nufo inda take.
"Yaushe za mu je gare shi ke nan?"
"Da zafi-zafi a kan daki ?arfe. Dan haka a daren yau zai ba?unci barzahu. Gobe da safe sai dai a samu labarin jana'izarsa!"
Mariya ta yi murmushi.
"Sai na jika zuwa an jima"
Lawan ya yi murmushi. Kuma ba tare da ya sake cewa komai ba ya ?ace daga ?akin. Mariya ta zauna a bakin gadonta. Abin da ya shiga tsakaninta da Munira a wacan ranar na yawo a cikin tunaninta.
*Wata ?aya da ya wuce...*
*BB Paradise Hotel, Abuja.*
A gaggauce Munira ta fito daga cikin motarta, wadda ta faka a parking lot, bayan da ta shigo harabar hotel ?in. Kuma ba komai ya sa take saurin ba face sa?on gaggawa da tasamu daga wurin saurayinta Mubarak.
Da yake ya fa?a mata lambar ?akin da yake ciki sai bata sha wahalar neman lambar ?akin ba. Kai tsaye ta wuce zuwa ?akin. A bakin ?ofar ?akin da ya bata lambarsa ta tsaya. Sannan ta yi knocking. Ta ja baya tana jiran ya zo ya bu?e. Jim ka?an aka bu?e ?ofar daga ciki, idonta ya sau?a a kan Mubarak ?in da ya bu?e ?ofar. Murmushi ya mata, sannan ya bu?e ?ofar gaba ?aya tare da fa?in.
"Shigo mana My love"
Fuska ta ?aure. Dan da ma sun samu matsala kwanan baya, yanzu kuka da ya kirata yace yana son ganinta sai ta yi zaton yana cikin wani hali ne.
"Me ya sa zan shigo ciki?"
"Ke dai ki shigo. Magana nake so mu yi"
Kamar ba za ta amince ba. Can kuma sai ta gya?a kanta. Sannan ta ra?a shi ta wuce. Mubarak ya kulle ?ofar ?akin ya biyo bayanta. A tsakiyar ?akin ta tsaya ta fuskance shi.
"Wace magana za mu yi?"
Ta tambaya fuskar nan a ha?e. Duk da dama can haka yanayin fuskarta yake, kasancewarta soja. Mubarak ya yi murmushi.
"Sai kace ina korarki? Ko ba komai ai kya zauna mu tattauna ko?"
Ta sake ?ata rai.
"Mubarak! Ba na son wasa da hankali. Kawai ka fa?i abin da yake bakinka... Ina da abin yi a barrack!"
Mubakar ya sunkuyar da kansa.
"Shike nan tun da kin dage My love. Da ma, ina so in baki ha?uri ne, na gane cewa ni ne me laifi, da fatan za ki yafe min!"
Ta kalle shi na sakkani. Kafin ta ?auke kai tana har?e hannayenta a ?irji.
"Da ma ni ban ?ullaceka ba ai. Kawai dai na ji haushin abin da ka min ne!"
Mubarak ya yi murmushi ya na kamo hannayenta.
"To ki yi ha?uri. Ba zan sake ba"
Munira ta yi saurin janye hannunta da ya ri?e.
"Mubarak wai sau nawa zan ce maka ba na so ka na ri?e hannuna?. Ba na so ka na ta?ani irin haka, duk wanna abin kamata ya yi mu bari sai bayan aure."
Mubarak ya sake kamo hannunta.
"My love ya kamata ki fahimceni. Wai kwana nawa ya rage auren nan namu ne? Ki sani fa cewa baki da miji bayan ni."
Ta sake janye hannunta.
"Mubarak kar ka sake ta?ani. Ba na so"
Ta fa?a tana ja da baya. Ya nufota yana shirin rungumeta ta kauce. Sannan ta hanka?a shi baya ta fice daga ?akin da gudu. Kuma a sanda ta fita daga ?akin, ?addarar da za ta kawo ?arshen rayuwarta ta wanzu.
MARIYA POV.
Zaune suke a cikin motarsu da suka faka a harabar BB hotel ita da Lawan. Lawan ne zaune a driver seat. Yayin da ita kuma take zaune a ?ayar kujerar. Dukansu sanye da ba?a?en kaya. Ba?ar hand glove ta ?auka ta saka a hannunta. Sannan ta ?auki ba?ar p-cap ta saka a kanta. Ta ?ora hular hoodie ?in dake jikinta. Ta juyo ta kalli Lawan da yake rufe fuskarsa da glasses.
"Mu je Rezor"
Lawan ya fa?a yana bu?e ?ofar motar. A tare suka fita daga cikin motar. Suka nufi ?ofar shiga hotel ?in ta ?ofar baya. Kai tsaye ?akin da Vishal Kumar ya kama suka nufa. Saboda da ma shi ne target ?insu. Kuma Wahash ne ya aikosu domin su zo su kashe shi. Saboda ya sa?a dokar ?ungiyarsu. A dai-dai ?ofar ?aki me lamba 24 suka tsaya. Mariya ce a kan gaba, Lawan kuma na tsaye a bayanta.
Ita ta ?aga hannunta ta ?wan?wasa ?ofar. Suka tsaya suna jiran a bu?e. Suna jin alamun za'a bu?e ?ofar suka gyara takunsu. Vishal na bu?e ?ofar Mariya ta kai masa wani naushi a hanci. Hakan ya sa ya yi baya yana dafe hancinsa da ya fara zubar da jini.
Yayin da Mariya da Lawan suka shiga cikin ?akin ba tare da sun rufe ?ofar ba, dan sun san cewa ba jimawa za su yi ba. Vishal na ganin fuskokinsu ya zaro ido. Sannan ya sau?e hannunsa daga kan hancinsa. Ya yi kan Mariya zai daketa.
Amma yana zuwa daf da ita ta kama hannunsa da ya ?aga zai dake ta shi, ta mur?e hannun har sai da Vishal ya yi ?ara. Sannan ta sa ?afarta ta daki ?afarsa. Kafin ta sa hannunta ta ri?o gashin ?eyarsa, ta ?aga ?aga kansa sama yana kallonta.
A hankali ta kai hannunta da bata ri?e gashin kansa da shi ba, ta ?aga harshenta ka?an, ta ?auko wata sabuwar reza da har ?aukan ido take a cikin hasken ?akin. Ta ?aga sama, sannan ta yanka wuyan Vishal da ita.
A dai-dai lokacin Munira da ta fito daga ?akin Mubarak da gudu ta dakata a ?ofar ?akin. Ganin an yi kisan kai ya sa ta ?waka ihu. Ihun da ta ?wala ya sa Mariya da Lawan juyowa suka kalli bakin ?ofar. Ganin fuskar Mariya ya sa tsoro da tashin hankalin Munira ninkuwa.
Hannunta na rawa ta nuna Mariya da shi. Sannan ta kalli gawar Vishal dake ?asa. Ita ma Mariyan ta ganeta. Kuma ganetan da ta yi ya sa ta nufo bakin ?ofar ?akin da gudu. Ita ma Munira sai ta ranta a na kare.
Ta fita daga hotel ?in a ki?ime, ko motarta da ta zo da ita bata ?auka ba. Ganin ta fita ya sa Lawan da Mariya bin bayanta a mota. Amma saboda ta iya gudu sosai ya sa ta musu nisa. Dan har wayarta ta ?aga ta kira Faruk da ita. Sai dai kafin ta kai ga fa?a masa abin da ke bakinta tunaninta da komai nata ya tsaya cak. Har Mariya da Lawal suka ?auketa bata cikin hayyacinta...
~~~
Munira ce yashe a tsakiyar wani ?aki. Hannunta da ?afarta duka a ?aure. Sannan idonta a rufe. Idan ka kalleta ba ka ce tana numfashi ba...
Daga wajen ?akin aka turo ?ofar ?akin ciki, ?aran bu?ewar ?ofar ya sa ta motsa. A hankali kuma sai ta shiga bu?e idonta. Tun tana gani dishi-dishi har ganinta ya dawo dai-dai. Shiru ta yi tana kallon Mariya da ta shigo ?akin.
Da ?yar ta iya yin?urawa ta mi?e zaune, duk da ?afafuwanta da hannayenta a ?aure suke. A dai-dai lokacin kuma Mariya ta dur?usa a gabanta tana murmushi. Yayin da ita kuma Munira take zubar da hawayen tausayin abokanta. Saboda ita bata ta kanta. Dan ta san ba lalle ta tsira a hannunsu ba.
"Mariya me ya sa?. Me ya sa kike cutar da Faruk da kuma MJ? Me ya sa?"
Ta tambaya hawaye na ?ara zubo mata. Amma ita Mariyan ba ta yi magana ba. Sai murmushi da take. Duk da haka Munira ba ta ha?ura ba ta sake fa?in.
"Me zai sa ki kashe rai Mariya?. Mariya me zai sa ki za?i rayuwar da ba taki ba?..."
"Wa ye yace miki wannan rayuwar ba tawa ba ce?. Wannan rayuwata ce, rayuwa me da?i a ?ar?ashin gata da tallafin shai?an!"
Mariya ta katseta tana fa?a?a murmushinta. Munira ta yi shiru tana son gano inda zancen nata ya dosa.
"Mariya ke 'yar cult ce?"
Mariya ta lumshe idonta ta bu?e tana gya?a kai, hankalinta kwance.
"?warai kuwa Captain Munira Musa. Na bayar da ruhina ga shugaban mu shai?an. A yanzu ba ni da abin bauta sama da shai?an!..."
"Subhannallah! Subhannallah!. A'uzubillah! A'uzubillahi mina shai?anir-rajim!"
Wani duka da Mariya ta kaiwa bakinta ya sa ta fa?i gefe guda. Bakinta na zubar da jini. Mariya da fuskarta ta riki?a zuwa fushi ta sa hannu ta ta ri?o gaban rigar dake jikinta. Sannan ta janyota tana zare idonta a kanta.
"Idan kika kuskura kika sake bu?e bakinki kika fa?i wata ?azamar kalma ?aya a kan abin bautata shai?an sai na cinye namanki ?anye!"
Bakin Munira na fitar da jini, idonta na zubar da ?walla ta girgiza kai.
"Ba ke ba ce Mariya!. Wallahi ba ke ba ce. Kowa ya na yabon kyan hali irin naki, kina da nutsuwa da kamala. Kina da sanin ya kamata da ha?uri, me ya sa yanzu kika sauya? Me ya sa? Innalillahi wa inna ialaihi raji'un!..."
Mariya ta saki gaban rigar tata. Sannan ta mi?e ta fice daga ?akin a fusace. A wani ?aki ta je ta samu Wahash.
"Shugaba! Wani kalar hukunci ya kamata mu mata?"
Mariya ta tambaya tana huci. Saboda an ta?a abin bautarta. Wahash ya dubeta.
(Wahalallu??)
"Yanzu kun kashe Kunda (Vishal). Kuma za'a yi bincike a kai. Idan har aka kasheta ita ma zargi ne zai ?ara yawa. Dan haka dole mu jinkirta wurin kasheta!"
Mariya ta jinjina kai.
"Dole mutuwarta ta zama me tada hankali. Saboda ta ta?a abin bautarmu Wahash"
Wahash ya yi murmushi.
"Zamu ba ta irin mutuwar da hatta ahalinta ba lalle su ganeta ba"
Mariya ta jinjina kai. Kamar yanda suka tsara ba su kasheta a lokacin ba. Sun ajeta a masarautar shai?an na wasu satuka. Kuma a duk kwanan duniya da kalar azabar da ake ganawa Munira. Da haka har lokacin da za su sadaukar da jininta ga shia?an ya zo.
Sai da suka mata kisa irin na wula?anci. Kisan da duk wani me imani idan ya gani sai ya zubar da hawaye. Sun bata mutuwa irin wanda ko da fasi?in mutum ne ba'a so ya yi. Haka suka cillar da abin da ya yi saura na gawarta a wata unguwa. Hankalinsu kwance...
*Present Day...*
MUKTAR POV.
Kamar kullum. Yau ma haka Ali ya sau?e shi a unguwarsu. Sannan ya juya ya tafi da motar tasa. Saboda shi sam ba ya zama da motar a wurinsa. A ko da yaushe tana wurin Ali. Sai idan yana bu?atar zuwa wani wurin shi ka?ai zai sa Alin ya kawo masa ita.
Kamar jiya. Haka yau ma aka dalle shi da hasken fitilar mota, sa?anin jiya da ya kasance mashin. Cak ya tsaya da tafiyar da yake. Sannan a hankali ya juya bayansa ya kalli motar dake bayansa.
Duk da yanda aka haske shi da fitilar motar ya iya gane motar, har ma da mutum biyun dake cikin motar. Wannan motar ce da aka sace Munira a cikinta, sannan Mariya da crime partner ?inta da ba su san sunansa ba ne zaune a ciki.
Kamar yanda yake tsaye haka ma motar tasu take tsaye a wuri ?aya, duk da a kunne take. A hankali ya ja ?afarsa ?aya baya. Hakan ya bawa Lawan damar jan motar ma zuwa gaba ka?an. Ganin haka ya sa Muktar ya sake jan ?afarsa baya, Lawal ma ya ?ara jan motar gaba.
Muktar ya juya bayansa. Sannan ya ci gaba da tafiya a nutse, saboda ya ga abubuwan da suka ?ara wannan tayar da hankali. ?arewa har kan gadon baccinsa an zo an saka masa wu?a a wuya an yi barazanar kasheshi. To ai su su Mariya ?ananun 'yan iska ne.
Kamar yadda yake tafiya a hankali, haka ma motar ta ci gaba da binsa a hankali. Can kuma sai ya fara tafiya da sauri, hakan ya sa Lawan ma ?ara gudun motar. Ganin haka ya sa Muktar ya fara gudu. Lawan