Showing 6001 words to 9000 words out of 35486 words

Chapter 3 - ƘADDARA-CE_-By-Salma-Ahmad-Isah

05 Jul 2024

6338

Kasancewar ta sanar mata cewar nata sun ?are.

Basu rabu da Mummy ba sai da ta sai mata dafaffen ?wai. Dan ko ba'a fa?a ba ta san cewa Maimuna na bu?atar kayan ?arin jini. To kuma sai ?ADDARA ta sa ta taso a gidan da abincin da za ta sa a cikinta ma gagararta yake. Ballantana ta samu wanda zai ?ara mata jini. Haka Maimuna ta yi ta mata godiya har suka rabu ta dawo makarantar Famfo goma.

_Share fi sabillilah??_

_______________

_Ya kamata a fara biya tun daga yanzu fa!_

_If you want to subscribe pay ?300 to._

5487270431
Salma Isah
Monie point

*Daga al?alamin Salma Ahmad Isah??.*
*CANDY CE??.*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*?ADDARA CE!*


*(c)SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY??*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_


*03*

*No.42, Inuwa Wada crescent, Utako, Abuja.*

*12:55 na dare.*

MARIYA POV.

A dai-dai irin wannan lokacin da ya kasance duk wani abin hallita yake bacci domin samun hutu ita idonta biyu. Duk wani hankali da tunaninta ta tattara shi a kan agogon bangon dake manne a bangon ?akinta. Burinta bai wuce ta ga ?arfe sha biyu ta cika dai-dai ba. Ba dan komai ba sai dan ta tafi babban meeting ?in ?ungiyarsu da za'a gabatar a yau da ?arfe sha biyu na dare.

Cike da ?aguwa ta juya ta kalli Hilal dake kwance a kan bed ?inta yana bacci. Ta ja tsaki tana ?ara maida idonta kan agogon. Ganin mintuna biyu ne suke rage sha biyun ta cika ya sa ta mi?e tsaye. Ta sunkuya ?ar?ashin gadonta ta janyo wani akwati dake aje a wurin.

Zama ta yi a ?asa, sannan ta bu?e akwatin, komai dake cikin akwatin ja ne. Kuma abubuwan dake cikin akwatin ba su wuce hu?u ba. Daga wata jar doguwar riga, sai 'yar ?aramar ?warya da aka yiwa fentin ja. Sanna kuma a cikin ?waryar akwai wani jan ruwa me kauri.

Daga gani daskararren jini ne. Sai reza dake ?auke da busasshen jini a jiki, da kuma wasu zobunan ?arfe har da sar?o?i. Hannu ta kai ta ?auki rigar. Sannan ta mi?e tsaye, ta cire tufafin jikinta ta saka rigar. Har ?asan ?afafunta rigar ta sau?a, kuma hannun rigar dogo ne sosai.

Hannu ta kai ta cire ribbon ?in da ta ?aure gashin kanta da ba kitso. Ta barbaza shi a bayanta. Ta ?auki zobina masu ?auke da kan wata dabba mara fasali ta saka a yatsunta duka goma. Sannan ta saka sar?o?in dake cikin kayan. Ta ?auki kwaryar dake ?auke da daskararren jini ta ri?e a hannunta. Sannan ta juyawa gabar baya tana jiran cikar ?arfe 12.

A dai-dai lokacin da hannun agogon ?akin ya ka?a a kan ?arfe sha biyu dai-da. Mariya ta rintse idonta da ?arfi. Sannan pendant ?in ?aya daga cikin sar?o?in dake wuyanta ya kawo jan haske. A hankali cikin salihar muryarta ta furta.

"Mhish!"

A lokacin da fatar le?enta ta sama ta ha?u da 'yar uwarta ta ?asa wurin kaiwa karshen kalmar ta?ace bat a cikin ?akin.

*RED SHAITAAN'S SAVERNTS PALACE.*

Babban ?akin taro ne. Wanda ya ?unshi jerin kujeru sama da ?ari. Kuma duka kujerun suna kallon juna ne daga ko wani bango na ?akin. Kamar dai jerin kujerun majallisar sarakunan gargajiya.

Ko wace kujera a wurin ja ce, kuma kowacce tana ?auke da sunan me ita. Daga can kan stage ?in dake a tsakiyar ?akin taron daga can ?arshe kuma kujeru ne guda uku. Wadda ke tsakiya tafi kowacce kujera girma. Yayin da biyun da suke a gefe da gefenta kuma irinsu ?aya. Amma kuma su ma sun fi sauran kujerun dake ?akin girma.

Daga tsakiyar ?akin kuma wani katon rami ne dake ?auke da itatuwan dake ci da wuta. Ga kuma wasu kayan tsaface tsaface da baka ce ga sunayensu ba. A hankali suffar Mariya sanye cikin jan kaya ta bayyana a tsakiyar ?akin taron. Kuma sai da ta ji ?afafunta sun sau?a ?asa, sannan ta bu?e idonta a hankali. ?afarta ta cira ta fara tafiya a hankali. Har ta isa kujerar dake ?auke da sunanta a cikin ?ungiyar. Wato RAZOR!.

Sai da ta zauna sannan ta aje ?waryar dake hannunta a kan wani teburi. A hankali a hankali mutane suka ci gaba da bayyana a cikin ?akin. Kafin kace me har sun cika ?akin. Duk yawan wa?annan kujerun sai da suka cika su taf.

Mutane ne da ban-da ban, daga sassan duniya, wasu ba?a?en fata ne, wasu kuma fararen fata ne. Kuma ko wa a cikinsu na sanye da jan kaya. Yayin da wasu daga cikin bayin shai?an na wurin ke aikin ha?a wutar dake ci a ?akin taron.

Bayan shu?ewar wani lokaci wata ?ofa dake kusa da babbar kujerar dake ?akin taron ta bu?e. Sannan wani tsoho da ya tara farin gemu ya shigo sanye cikin jan kaya. Bayyanarsa a cikin ?akin taron ya sa sauran bayin shai?an ?in suka mi?e domin nuna girmamawarsu ga Shugaba!.

Tsohon ya tsaya a jikin kujerarsa da tafi ta kowa kyau da girma a ?akin taron, wadda ke nuna cewa ya fi kowa matsayi a wurin. Ya ?aga hannayensa duka biyu sama, sannan ya ha?esu wuri guda alamun bauta da jinjina.

"Jinjina zuwa ga bayin shai?an!"

Duka ?akin ya ?auka da muryoyin mutanen cikinsa, masu banbancin jinsi, al'ada da yare.

"Jinjina zuwa ga shugaban bayin shai?an!"

Tsohon ya yi murmushi, sannan ya musu alama da su zauna. Kowa ya zauna, sannan shina ya zauna. Sai da ya juya ya kalli ?aya daga cikin kujerun da suka saka tasa a tsakiya. Wadda wani ba'indiye ke zaune a kai, alamun dai shi ne na hannun hagunsa.

Kafin ya juya ya kalli ?angaren kujerar dake damansa, wadda babu kowa a kai. Sannan ya juya ya kalli sauran bayin shai?an ?in da suka yi shiru suna jiran jin abin da ya sa aka tara su a wurin.

"Kamar yanda muka saba gudanar da taron tattaunawa a ko wani mako. Yau ma haka ne. Sai dai ina so na sanar da ku cewar lokacin sadaukarwa ya kusa. Dan haka sai ku shirya domin sadaukar da ?aya daga cikin wa?an da kuke so ga shugabanku shai?an. Sannan kuma ku sani cewa duk wanda ya kuskura ya tsallake sharu?anmu to zai mutu, kamar dai yanda Kunda ya mutu. Duk wanda muka nuna cewa shai?an na so a cikin ahalinku, dole a sadaukar da jininsa. ?in amincewa da hakan na nufin barin mutum duniya. Dan za ku mutu ku je ku fa?a wuta tare da shai?an!"

(Wa'iyazubillah.!)

"Mun ji mun amince shugaban bayin shai?an!"

Suka amsa da babbar murya. Ciki har da RAZOR.

"Sai kuma batu a kan wanda zai maye kujerar Kunda!..."

Sai ya dakata yana kallon Razor da ta maida hankali kansa.

"Razor!"

Razor ta zabura ta mi?e tsaye, daga ciki ban da tsallen murna babu abin da zuciyarta ke yi. Dan da alama mafakin da ta ci burin cimmawa ne ya zamto gaske. Mafarkin da ya samu muhalli a cikin rayuwarta tun bayan mutuwar Kunda na hannun daman shugaban bayin shai?an. Wato maye kujerar Kunda ?in. Shugaban bayin shai?an me suna Wahash ya kalli sauran bayin shai?an, sannan ya nuna Razor da hannunsa yana fa?in.

"Razor ita ce wadda za ta maye wurin Kunda!"

Cike da farin cikin wannan batu na Wahash Razor ta zube ?asa, ta yi wa wutar shai?an sujjada tana masa godiya. Kafin ta mi?e tana yi wa Wahash godiya.

"Amma kafin faruwar hakan, dole ki sadaukar mana da ?anki Haruna Faruk Kaigama. Hilal nake nufi!"

Wahash ya fa?i abin da suke bu?ata a maimakon wannan kujera. Ba tare da tsoro, shakku, ko ?ar ba Razor ta amince cike da farin ciki.

Ta sadaukar da abubuwa da dama kafin ta kawo yanzu. Na farko sai da ta fita daga musulunci, dan sam a yanzu bata sallah ballantana azumi a watan ramadan, ko wata ibada da ta kasance wajib a kan ko wani musulmi na mai imani. Sannan ta sadaukar da mahaifarta bayan ta haifi Hilal. Ta kuma ?auracewa ha?a shimfi?a da mijinta tsawon shekara guda duka a kan wannan ?ungiya.

Abubuwan da ta sadaukar ba za su ?irgu ba. Dan haka ko da mahaifinta Alhaji Jibrin Gimba Gashuwa GG suka bu?ata za ta sadaukar da shi, ballantana Hilal ?aramin alhaki. Da wannan batun taron nasu ya waste. Amma kafin Razor ta tafi sai da suka yi tattaunawar sirri ita da Wahash.

"Razor!"

Ta kalle shi cikin girmamawa.

"Mun gano cewa mijinki da yayanki suna bincike a kan mutuwar Munira abokiyar aikinsu da kika kashe. Sakamakon ganinki da ta yi a lokacin da muka aikeku ku kashe Kunda a BB Paradise hotel!"

Nan take yanayin bugun da ?irjinta yake ya sauya salo. Daga na farin ciki zuwa na tashin hankali. Daga Mu'az har Faruk babu wanda ta yi wa ?aramin sani. Ta san halinsu kamar yunwar cikinta. Idan har suka gano gaskiyarta ba za su yi la'akari da ala?arta da su ba za su hukuntata. Ganin kamar ta tsorata ya sa Wahash fa?in.

"Babu bu?atar ki ?aga hankalinki. Domin mun yi wa tufkar hanci, ta hanyar goge duk wani CCTV footage na ranar da kuka ha?u da Munira a hotel ?in!"

Idonta ta lusmhe tana jin bugun zuciyarta na dai-daita. Sannan ta bu?e idon nata.

"Wahash yaushe zan sadaukar da Hilal ?in?!"

Ta tambayi abin da ya fiye mata muhummanci. Dan ita a yanzu babu abin da take bu?ata da ya wuce maye kujerar Kunda. Kuma ita ta ?agu ta sadaukar da Hilal ta huta. Tun da da ma shi da ubansa duka ba sa gabanta. Wahash ya goya hannayensa a bayansa yana murmushi.

"Me kike ci na baka na zuba Razor?. Ai daga zarar lokacin ya yi za mu sanar da ke. Yanzu dai abu ?aya nake bu?ata daga gareki. Shi ne gashin kansa, domin ba za mu sadaukar da jininsa ga shugabanmu shai?an ba ba tare da mun tsaface shi ba. Dan haka sai kin jira nan da wasu wattani!"

Duk da ba haka ta so ba ta ji da?i. Da wannan batu ta yi wa Wahash sallama, sannan ta dawo gidanta, cikin ?akinta. Kuma tana dira a ?akin Hilal ya zabura ya farka, lokaci guda ya canyara kuka. Amma ko ajikinta an mintsini kakkausa. Dan bathroom ma ta shiga.

Ta je ta yi wanka ta dawo ta sauya kaya ta kwanta a kan gadon tana kallon Hilal ?in dake kuka har zuwa lokacin. Kallonsa da ta yi ya motsa wani abu a cikin zuciyarta. Musamman ma da ta tuna cewa nan da wasu watanni za ta sadaukar da shi ga abin bautarta a yanzu, wato shai?an.

(Ya ilahi!)

Tausayinsa ta ji ya fara shiga zuciyarta, dan haka ta kai hannu za ta ta?a kansa. Amma sai wannan ba?in haya?in da ya saba rufe mata ido a duk sanda za ta tuna wani abu na soyyaya tsakaninta da Faruk ko ?ansa ya rufe idonta.

Lokaci guda hannunta na dama da ta ?aga za ta ?ora a kan Hilal ya ?ame a saitin kan nasa. ?wayar idonta ta juye zuwa ja. Sannan lokaci guda fushi ya maye fuskarta. Sai ta yi saurin janye hannunta daga kansa.

Sannan ta juya masa baya tana huci kamar wadda aka ?atawa rai. Lokaci guda idonta ya soma zubar da hawayen jini. Ta rintse idonta gam tana karanto wata addua'a tasu ta bayin shai?an. Har ta samu ta yi bacci.

FARUK POV.

Da misalin ?arfe goma na dare ya fito daga ban?aki. Bayan ya watsa ruwa a jikinsa kasancewar bai jima da dawowa daga wurin aiki ba. Sanye yake da yellow plain T-shirt da ba?in sweat trouser, ?afafunsa duka na sanye cikin ba?in sliders ?insa.

A hankali ya kai hannu ta ta?a sumar kansa da take a ji?e, wadda kuma bata cika tsayi ba kasancewarsa soja ya sa ba ya tara gashi ko da ya so hakan. Shi yasa yake askin high fade tare da buzz cut.

Yana shirin kashe hasken dake ?akinsa, idonsa ya sau?a a kan wani hoto dake cikin kyakkyawan frame. Wanda ya ?unshi Mu'az da Munira da kuma shi kansa. Zama ya yi a gefen gadonsa. Ta inda hoton ke aje a kan side drawer.

Ya kai hannu ya ?auki hoton yana kallo. Gaba ?aya su ukun na sanye cikin korayen kaya ne na sojoji, kuma sai kayan dake jikin nasu ya tuno masa da lokacin da aka ?auki hoton. Wato ranar da suka yi passing out.

Domin NDA Kaduna (National Defense Academy Kaduna) suka fara ha?uwa da Munira a wurin training. ?wazonta da kuma nuna jarumtarta duk da kasancewarta mace 'yar arewa yasa suka ?ulla abota da ita. Ala?arsu da Mu'az kuma ta fara ne tun daga secondary school. Har suka kai ga tertiary school suna tare, kuma burin kowwane a cikinsu tun a wancan lokacin shi ne zama soja.

A sanda suka kammala karatu mahaifinsa Alhaji Haruna Aminu Kaigama yana da rai. Kuma shi ne wanda ya nema musu makarantar horar da sojojin ta NDA. Kasancewar Hajiya Batula mahaifiyarsa bata da matsala da aikin da yake son yi sai ya riga Mu'az tafiya.

Saboda shi Mu'az Mummynsu bata son ya yi aikin soja. Shi ya sa sai da aka kai ruwa rana kafin ta amince ya tafi. Amma duk da haka sai ya zo ya fisu mu?ami shi da Munira da suka fara zuwa a farko.

Wani abu da ya ?arawa abotarsu ?arfi shi ne lokacin da aka yi posting kowwane a cikinsu sai aka turasu gari ?aya. Da haka suka ci gaba da aiki tare har zuwa lokacin da ko wanne a cikinsu ya samu ?arin girma. Da kuma nasarorin rayuwa. Kafin komai ya tarwatse a lokaci guda.

Saurin aje frame ?in ya yi, saboda hoton gawar Munira da ya haska a cikin idonsa. A hankali ya kwanta a kan gadonsa. Ya yi rigingine. Yana kallon p.o.p ?in dake saman ?akin. Hannunsa na dama ya dun?ule, sannan ya ?ora tsintsiyar hannun nasa a bisa goshinsa yana tunani.

Can kuma sai yajuyar da kansa ya kalli makwancin Mariya a da. Kafin ta nemi raba ?aki da shi. Ya ?auke kansa yana tuna adadin lokutan da ya mata magana kan hakan. Amma sai tace masa ita bata da lafiya.

Tun yana ha?uri har ya gaji ya daina mata maganar. Kuma babban abin da yake damunsa da ita shi ne rashin kula da Hilal da take. Kamar ba ita ta haife shi ba. A ganinsa ko da ba ita ta haifi Hilal ba in dai ya kasance ?ansa bai kamata ta masa irin ru?on da take masa a yanzu ba. Cike da sa?e-sa?en goma da ashirin ?in da suka ha?e masa bacci ya ?auke shi. Amma bai kai ga barin Nigeria ba a duniyar baccin nasa kukan Hilal daga ?akin Mariya ya tasheshi.

Ya bu?e idonsa da ?yar. Saboda bala'in baccin dake cin idonsa. Tun da ya fara aikin soja baya jin akwai ranar da ta zo ya rama tarin bashin baccin da ake binsa. Dan a ko da yaushe a gajiye yake dawowa gida. Idan kuma an tura shi wani aiki ne ma kwana yake idonsa biyu. Wani lokacin kuma sai ya samu baccin. Amma rashin baccin yana yawan damusa.

Jin kukan Hilal ?in ya ?i ?arewa ya sa ya mi?e zaune yana yin hailala. Ya saka takalmansa dake ?asan gadon. Sannan ya fita daga nasa ?akin ya shiga na Mariya. Ganin Hilal ?in kwance a gefen Mariya yana kuka bai bashi mamaki ba.

Dan ya ga abin da ya fi hakan ma. Shi dai a rayuwarsa bai san Mariya wata kala ba ce. Cikin ?akin ya ?arasa, sannan ya kai hannu ya ?auki yaron da yake ta kuka har da hawaye. Ganin yana gwagwiuyar hannunsa yasa ya fahimci cewa yunwa yake ji. Dan haka ya zagaya ta ?ayan ?angaren ya tashi Mariya a bacci. Duk da bata yi nisa a baccin ba amma da ?yar ta bu?e ido ta kalle shi.

"Mary Hilal yana ta kuka. Kuma da alama yunwa yake ji. Ki tashi ki shayar da shi."

Mariya ta mayar da idonta ta rufe, kamar ba za ta yi magana ba, can kuma sai tace.

"Ka duba kitchen akwai kayan abincinsa sai ka dama ka ba shi idan kukan nasa ya dameka!"

Cike da takaici Faruk ya girgiza kansa yana kallon yaronsa. ?acin rai ya sa bai sake cewa Mariya komai ba ya fice daga ?akin. Ya nufi kitchen da Hilal ?in a hannunsa, kuma har zuwa lokacin bai yi shiru ba.

Shi kuma sai faman jijjiga shi yake alamun rarrashi. Da Allah ya taimake shi sai ya samu bottle ?in Hilal ?in akwai damammen custard a ciki. Shi ya ?auka ya dawo ?akinsa da shi. Ya shiga ba shi yana masa kallon tausayi.

Dan yanda yake zu?ar bakin bottle ?in da ?arfi zai sa ka fahimci cewa yinwa yake ji. Hilal bai kai ga shanye custard ?in ba ya yi bacci. Cike da tausayin ?ansa Faruk ya kwantar da shi a kan gadonsa. Dan ba yau suka fara kwana tare ba. ?an karamin ?a da uwarsa a raye amma ya zama kamar maraya.

Sanyin AC ya rage. Sanna ya ?auki duvet ?an ?arami ya masa rufa. Kafin ya kwanta a gefensa yana kallonsa cike da so da kuma tausayi. Addu'a ya masa, shi ma ya yi, har Allah ya sa bacci ya sace shi.

MU'AZ POV.

"Mima ?ara min"

Ya fa?a yana mi?awa Mima dake serving kowa na gidan dake zaune a dinning table, kasancewar suna shirin yin karin kumallo ne. Mima ta kalli plate ?in da ya mi?o mata. Cike da mamaki ta kar?i plate ?in.

"Yanzu Ya Mu'az a ina zan ?ara maka wani abincin? Ji fa yanda plate ?in ya cika da abinci, baka ci ba amma ka na neman ?ari!..."

Wani kallo ya mata yana fa?in.

"Mi?o min na coolern duka. Tun da ke baki da dabarar sauya plate!"

Mima ta aje plate ?in tana ?ata rai. Mu'az ya mi?e ya zagaya ta inda take yana fa?in.

"Matsa ki bani wuri ko na sauya miki kammani yanzu!"

Mima ta turo baki gaba tana matsawa. Ta kalli Mummy da ke kallonsu, dan wannan fa?an nasu sun saba yinsa kullum a kan abinci. Tun ana saka musu baki har kowa ya ?yalesu da halinsu. Cikin ?un?uni Mima tace.

"Mutum sai ci kamar gara!"

Mu'az dake shirin zama a kan kujerar da ya mi?e ?azu, bayan ya sauya plate ya cika shi da abinci ya kalleta.

"Magana kika yi?"

Mima ta sosa wuyanta tana fa?in.

"A'a fa. Ni ban ce komai ba"

Ta fa?i ?wa?walwarta na fa?a mata amsar da zai bata. Dan tun ba yau ba sun saba, ta riga ya haddace kalmar kamar sunanta. Mu'az ya yi ?wafa yana jan kujerarsa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login