Showing 3001 words to 6000 words out of 35486 words

Chapter 2 - ƘADDARA-CE_-By-Salma-Ahmad-Isah

05 Jul 2024

6340

ce ta dawo da shi zahiri. Ya dube su yana amsawa. Kafin suka bu?e masa gate ya fita da motarsa daga gidan. Sai da yafara biyawa ta gidan mahaifiyarsa Hajiya dake kusa da nasa gidan.

Ya gaisheta kafin ya wuce wurin aiki. Kasancewar akwai wani aiki na binciken mutuwar abokiyar aikinsu dake gabansu ya sa yana zuwa barrack bai nemi kowa ba sai Mu'az. Aboki, kuma abokin aikinsa.

_Share fi sabillilah??_

______________

Za ku iya karanta wannan littafin a ArewaBooks, da ma wasu litattafaina na baya @SalmaAhmad. Sai kuma Wattpad @Salma_Ahmad_Isah.

Saboda page ?in can za su fi na nan tsayi. And don't forget to follow, like, share and comment.

*Daga al?alamin Salma Ahmad Isah??.*
*CANDY CE??.*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*?ADDARA CE!*


*(c)SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY??*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_


*Paid book*


*02*

*No.53, off Justice Clara Ogunbiyi street, Asokoro, Abuja.*

MU'AZ POV.

Mutum biyar ne zaune a kan dinning table suna yin breakfast. Shi ka?ai ne a cikinsu yake cin abinci da hannunsa. Yayin da kowa yake ci da spoon. Mahaifiyarsu Hajiya Hauwa, wadda suke kira da Mummy ce ta dube shi.

Yanda ya dage yake cin abincinsa bil ha??i da gaskiya. Dan idan kana so ku sa?a da Mu'az a ?i ba shi abinci lokacin da yake jin yunwa. Idan kuma kana so ka burgeshi ka masa kyautar abinci ka ga ?auna. Shi da abinci 5 and 6 ne.

Shi ya sa kaf yaran gidan su biyar. Wanda suka ?unshi babbar yayarsu 'yar matar Daddynsu ta farko wadda Allah ya yi wa rasuwa. Me suna Farida. Sai shi da ya kasance ?an Mummy na farko, sai Mariya da take bi masa. Sanna Safiyya da ta ci sunan mahaifiyar Daddy, suna mata inkiya da Mima. Sai auta Na'im. Duk cikinsu ya fi kowa ?iba. Duk da shi ma ba wai ?ibar ya cika ba. Amma ya fi su jiki. Sai Mima da ita ma take da 'yar ?iba.

Kuma a duk cikin yaran Daddy su biyar, ya fi kowa farin fata. Dan shi farin Mummy ya biyo su kuma duk ba?in fatar Daddy suke biyowa. Hakan ya sa ya fita da ban a cikinsu. Idan ka ganshi ba lalle kace ?an gidan ba ne. Saboda yana da fari sosai, sa?anin sauran 'yan uwansa da suka kasance ba?a?e.

"Mu'az!"

Mummy ta kira. Hakan ya sa ya ?ago da fararen idanuwansa ya ?ora a kanta yana amsawa.

"Na'am Mummy"

Cikin tsare shi da ido Mummy tace.

"Me ka je ka aikata a gidan Hajiya Hadiza?... Jiya da daddare bayan ka dawo daga gidan ta kirani tana ta masifa!"

Maganar Mummy ta janyo hankalin kowa kansu. Shi kuma sai ya yi murmushi yana maida hankalinsa kan cin abincinsa. Dan ya tuno da tsiyar da yaje ya yi a wurin yarinyar aminiyar Mummy da tace masa ya je dan su daidaita juna.

"Ka san baka da gaskiya ke nan?"

Fa?in Mummy. Alhaji Jibrin Gimba Gashuwa ya kalli matarsa yana fa?in.

"Me ya yi kuma?"

Cike da jin haushin abin da ya aikatawa 'yar aminiyarta Mummy tace.

"Tsabar shi abin magana ba ya masa ka?an. Ya taka ya je har gidan aminiyata Hajiya Hadiza, dan ya ga 'yarta Rashida su daidaita. Tun da shi ya kasa za?awa kansa matar aure. Wai ya dubi Rashida ya ci mata mutunci, har da cewa wai ita ?azama ce. Kuma ta masa ka?an a matsayin matar aure!... Maganganu dai babu da?in ji!"

Daddy ya dubi Mu'az dake murmushi. Kafin ya kai ga cewa wani abu, Mu'az yace.

"Iyaka abin da na ce kawai ta fa?a. Ba ta fa?a miki abin da ita 'yar tata ta min ba?"

"Me Rashidan ta maka?"

Daddy ya tambaya.

"Saboda Allah Daddy. Kamar ni Mu'azzam Jibrin Gimba za ta shanya a ?ofar gida ina jiranta. Wai tana kwalliya?. Ko me za ta yi wa kwalliyar?. Wannan mummunar ba?ar ?azar fuskar tata da bata rabo da majina sanda tana yarinya ko me?... Kuma da ma can fa ni ba ta min ba. Yarinyar ba class ?ina ba ce. And ta cika rawar kai da yawa!"

Cike da mamakin abin da yayanta ke fa?i a kan Rashida Mima ta ?aga kanta sama tana hango fuskar Rashidan. Ko ita da take mace Rashida na burgeta. Saboda iya wankanta da son gayu. Amma tsabar wula?anci irin na Mu'az cewa yake wai ?azama ce!.

"Ya Mu'az Rashidan ce ?az..."

Shiru ta yi saboda kallon da ya mata. Ta ha?iye maganar ta kora da miyau ?in bakinta. Mu'az ya harareta yana fa?in.

"?aramar mara kunya!..."

"Sannu shugaban marasa kunya!..."

Fa?in Mummy a ?ufule ita ma tana wurga masa harara.

"Mu'az"

"Na'am Daddy!"

Ya amsa a ladabce.

"Rashida ce ba ta maka ba ko wata ?abi'a ce gareta wadda baka so?"

Ya yamutsa fuska yana fa?in.

"Ta min ?an?anta da yawa. Sa'ar Mima ce fa Daddy. Kuma taba da rawar kai. Ga ta cika iyawa... Gaba ?ayanta ma bata min ba. I dislike her at all!..."

"Ka kyauta. Ka kyauta da ka zubar min da mutunci a idon aminiyata"

Mummy ta tari numfashinsa.

"Hauwa! Kin san ni me son abin da yarana suke so ne. Tun da har baya sonta babu yanda za ayi na aura masa ita. Da ace yana sonta kuma sai inda ?arfi na ya ?are wurin neman aurenta!"

"Shi ya sa nake sonka Daddy. You're the best!"

"Ban gama da kai ba ai... Dan baka son Rashida bai kamata ka ri?a kusheta ba. Hakan babban kuskure ne. Da fatan za ka kula nan gaba!"

Sai ya sunkuyar da kansa yana fa?in.

"To Daddy. Za a gyara!"

Wayarsa dake aje a gefen plate ?in da yake cin abinci ce ta shiga ringing. Hakan ya sa ya ?auka domin duba me kiran, ganin Faruk ne ya sa ya amsa.

"My Gee what's up?"

"Fine Wallahi. Ya ? Me ya sa ba ka zo barrack ba har yanzu?"

Mu'az ya mi?e tsaye wayar kare da kunnensa ya nufi sink domin wanke hannunsa da yaci abinci da shi. Saboda shi duk rintsi duk wuya ba ya cin abinci da spoon ko fork.

"Cin abinci na tsaya. Ka san aikin nawa ma ba zai iyu ba ba tare da na cika cikina ba!"

"Aikin ke nan ai. To sai ka yi sauri ka zo dan mu je mu ha?u da Muktar (?an sandan da yake bincike a kan case ?in mutuwar Munira) ?in. Tun da yace gobe zai yi tafiya"

Mu'az ya goge hannunsa da toilet paper yana fa?in.

"On my way"

Daga haka ya sau?e wayar ya dawo dinning area.

"Mummy ni zan tafi... An jima zan aiko driver ya zo ya kar?a min abinci!"

Mummy ta wurga masa harara tana fa?in.

"Saboda ga Mummy baiwarka ka aje za ta maka girki ko?"

Mu'az ya ?unshe daiyarsa.

"Oh lord of mercy!"

Ya fa?a, sannan ya kalli Mima.
"'Yar lukuta ki min girki zan aiko a kar?a min. Yau Mummy ta yi fushi da ni!"

Ba dan Mima ta so ba haka ta gya?a masa kai. Dan ita yau ta riga da ta tsara fita tare da ?awayenta. Kuma bata isa ta masa musu kan ba za ta yi ba. Ita a wa?. Yanzu sai ya hauta da bala'i. In ba sa'a ba ma ta kaisu ga duka.

"Oga tulele ka gama mu je na sau?eka?"

Ya fa?i yana kallon Na'im. Na'im ya ?auki bagpack ?insa yana fa?in.

"Eh na kammala mu je"

Suka yi wa Daddy sallama suka fita tare. Mummy ta yi ?wafa.

"Wai yanzu haka za'a zuba masa ido ya zauna babu aure?. Ga shi Mariya da take ?anwarsa har da yaro ?aya. Amma shi tsayuwa da 'yan matan ma ya ?i. Ballantana har a fara batun yin aurensa!"

Daddy ya yi murmushi yana sipping tea ?insa. Ya aje mug ?in yana fa?in.

"Hauwa ke nan!. Shi fa aure da mutuwa duk lokaci ne da su. Idan Allah ya nufa sai ki ga an yi nan kusa. Wata ?ila kuma shi nasa rabon a nesa yake"

"Hum-um. Ai bana jin Ya Mu'az zai yi aure kwana kusa Daddy. 'Yan mata nawa Mummy ta masa?. Amma duk cikinsu cewa yake babu wadda ta masa. Har da wadda yace warin baki take. Ai babu me iyawa wannan mutumin sai Allah. Ga zafin zuciya kamar garwa shi. Ga hancini!. Ga fa?ar ba?ar magana kamar jikan kutare!..."

"Duk zai daina with time. Har yanzu Allah bai ha?a shi da wadda za ta dace da shi ba ne..."

Daddy ya katseta. Mima ta ta?e bakinta tana ganin rashin iyuwar hakan. Dan a ganinta, babu budurwar da za ta iya zama da yayanta da halayensa. Su ma da suke 'yan uwansa wasu lokutan kasa ?aukan halin nasa suke ballantana wani da ban.

*Nigerian Army resources center, Mambilla Barrack, Asokoro, Abuja.*

"Hello! Sirikina ina kwana"

Fa?in Mu'az a lokacin da ya shiga office ?in Faruk dake jiransa. Dan bayan ya je ya aje Na'im a school kai tsaye ya wuto nan barrack ?in. Saboda daga gidansu zuwa Barrack ?in ba nisa.

Faruk dake tsaye a jikin shelf yana duba wani file ya jiyo ta kalli Mu'az ?in dake shigowa office ?in. Kamar kullum, sanye yake da wandon kakin sojoji, da kuma rigar da suke sakawa a ?asan rigar uniform ?in nasu me kama da T-shirt. Amma shi kam da ma abu ne me wuya ka gan shi sanye da complete uniform.

A cewarsa waccan ta saman takura shi take. Saboda shi da riga kamar ma?iya suke. Idan ka gan shi da complete uniform to meeting zai shiga, ko kuma akwai wani wurin da zai je ba barrack ba.

"Sannu da zuwa sir"

Fa?in Faruk yana sarawa Mu'az ?in. Kasancewar shi ne sama da shi. Mu'az ya cire glasses ?in idonsa yana fa?in.

"Karka sa na ji kunya mana sirikina. Ni ban san wannan abin. Ka share kawai"

Faruk ya sau?e hannunsa yana murmushi. Dan wannan ?in magana ce wadda ya haddaceta a cikin kansa.

"Ina ?ana?"

Mu'az ya tambaya.

"Lafiyarsa ?alau."

"An jima muna da meeting da general Haladu Mansur. Gwanda mu je mu ga Muktar kafin lokacin ya yi"

Ya fa?i yana maida glasses ?insa.

"Okay"

Daga haka suka fita zuwa FCID domin jin yanda binciken mutuwar abokiyar aikinsu ya kwana.

*FCID (Force Criminal Investigation Department), Moshood Abiola Road, Garki, Abuja.*

"A halin yanzu mun yi nasarar gano wuri na ?arshe da ta halarta kafin ta ?ata. Kuma abin da muke ta ?o?arin yia yanzu shi ne gano wanda ta ha?u da shi a wurin. Saboda mun gano wani sa?o a wayarta dake nuna cewa wani ne ya kirata zuwa wurin domin su ha?u. Daga zarar mun samu damar gane wanda ya aiko mata da sa?on za mu iya cewa mun kama me laifin. Saboda shi ne abin zargi na farko!"

Mu'az da Faruk suka dubi juna a tare. Kafin suka kalli Muktar ?in da ya gama zayyano musu bayanin.

"Lord have mercy!"

Fa?in Mu'az yana furzar da iska ta bakinsa. Yayin da Faruk da ya fi kowa shiga damuwa a kan case ?in ne ya shafa kansa cike da damuwa.

Saboda ?atan abokiyar aikin nasu me suna Munira tashi ?aya ya basu mamaki. Hakan ya sa suka bazama nemanta a ko ina. Bayan sati ?aya da ?atanta kuma suka samu labarin tsintar gawarta a wani layi. Babban abin tashin hankalin ma shi ne an tsinci gawar tata ne ba tare da wasu sassa na jikinta ba.

Saboda tsabar yanda makashin ya bata wahala wurin kasheta ya sa su kansu ba su tabbatar da cewa gawarta ba ce sai da iyayenta suka zo suka tabbatar da cewa ita ce. Kuma tun bayan rasuwarta da Mu'az Faruk ba su huta a kan binciken wanda ya kasheta ba.

"Ka yi ha?uri Kaigama. Da yardar Allah za'a kama mai laifin"

Fa?in Mu'az a ?o?arinsa na kwantarwa da Faruk hankali. Ganin yanda suka fito daga headquartern duka a dame. Cike da damuwa Faruk ya dube shi yana fa?in.

"Har yanzu na kasa mantawa da hoton gawarta da na gani a idona MJ. Kuma hoton tashin hankalin da ahalinta suka shiga lokacin mutuwar ya kasa fita daga kaina. Ba na jin hankalina zai kwanta idan har ban kamo me laifin nan ba MJ!"

Mu'az ya dafa kafa?arsa.

"Insha'Allah za mu kamo shi!"

"Allah ya yarda"

MAIMUNA POV.

Kamar yanda ta saba farkawa sassafe haka ta farka a asubar yau ma. Abu na farko da ta fara yi shi ne alwalal sallahr asuba. Ta dawo ?akinta ta tada sallahr. Kuma bayan ta idar ta fita tsakar gidan ta fara aikinta na safiya kamar yanda ta saba.

Duk da yanda sanyin safiyar yake sau?a a kanta bata ha?ura da aikin ba. To da ta isa ma ta ha?ura da aikin?. Ita a wa?, Kare da gudun layya?. Sai da ta yi shara. Sannan ta wanke kwanukan da aka ?ata a daren jiya. Kafin ta zauna ta fara firar doyar da za ta dafa ta kuma soya domin kai wa makarantun safe dake kusa da su. A lokacin Auwwa ta fito daga ?akinta tana hamma.

Kanta ta ?aga ta kalli Auwwan. Sannan ta gaisheta a ?arare. A ranta take ?iyasta lokacin da Auwwan ta tashi. Dan ta san lokacin dai ?arfe bakwai za ta yi. Kuma ita ba ta isa ta tasheta a bacci ba. Saboda kyakkyawan warning ne daga Auwwan, kan kada ta kuskura ta tasheta idan tana bacci.

A kan idonta Auwwan ta ?auki buta ta yi alwala. Sannan ta shiga ?aki domin yin sallah. Sai da a kammala fere doyar sannan Gambo yayanta ya shigo gidan. Kallonsa ta yi tana gaishe shi. Ko kallon arzi?i bata samu daga gare shi ba. Ballantana har ta yi zaton zai amsa gaisuwar tata.

A tasowarta a gidan bata jin akwai rana ?aya da suka ta?a yin magana da ?an uwan nata ta minti biyar ta arzi?i. Ko kalo bata ishe shi ba ballantana har su samu damar yin hira. Kuma da ma shi ba zama yake a gidan ba. Kullum yana waje wurin abokansa masu hayar napep.

"Ke Maimuna!"

Auwwa ta ?wala mata kira daga cikin ?akinta bayan Gambo ya shiga ?akin.

"Na'am"

"Ki yi maza ki ?ora ?umamen tuwo yanzu. Gambo yace yunwa yake ji"

"Auwwa na ?ora tukunyar doya fa"

Tsautsayin shan zagi ya sa bakinta ya su?uta wurin fa?ar hakan. Ai ko an dan?aro mata zagin. Dan sai da Auwwa ta za?o wani zagi tun na zamanin maguzawa ta makawa uwarta dake cikin ?asa.

"...Gidana ko gidanki?. Da har zan ce ki yi abu ki kawo son ranki"

"Allah ya baki ha?uri"

Maimuna ta fa?i. Tana nadamar maganarta ta farko. Jiki na rawa ta sau?e ?atuwar tukunyar doyar da ta ?ora. Sannan ta ?ora ta ?umame.

"Kuma ki cire bayan tuwon da ya bushe"

Ta ji Auwwa ta sake fa?i daga cikin ?akin.

"To"

Ta amsa wani sashi na zuciyarta na farin ciki. Dan ta riga da ta san yau babu rabonta a ?umamen nan. Kuma tun da Auwwa tace ta ?are bayan tuwon tana nufin ta zubar bata so. To ita kuma da wannan damar take amfani wurin rage yunwar da take damun cikinta. Dan idan ta ?are bayan wankewa take, sai ta ?an saka yaji ta ci.

Yau ?in ma haka aka yi. Tana ?arewa bayan tuwon shinkafar da ya bushe ta saka musu tuwon a cikin miyar dake kan wuta. Yayin da ta zube bayan tuwon da ya bushe a roba, ta wanke shi, tafaki ido ta zuba yaji a ciki. Ta koma gefe ta cinye.

Sannan ta wanke robar ta aje. Ta dawo ta sau?e tukunyar ?umamen. Ta sanar da Auwwa cewa ?umamen ya kammala. Kafin ta mayar da tukunyar doyar kan wuta. Tana zaune a wurin. Auwwa ta fito ta zuba ?umamen a kwanika biyu, ?aya nata ?aya kuma na Gambo.

Maimuna bata ta shi daga gindin murhun nan ba sai da ta gama dafa doyar, sannan ta soyeta da fulawa tas. Ta fa?awa Auwwa cewa ta gama. Auwwan ta zo ta zauna ta lissafa ku?in doyar. Sannan ta saka mata a cikin bokiti fallasa.

"Ta dubu uku da ?ari biyar ce. Saura kuma yau ma ki bada bashin"

Fa?in Auwwa tana hararta. Maimuna ta gya?a kai tana nufar randa.

"Ub*n me za ki yi kuma?"

Ta juyo a tsorace tana fa?in.

"Na ga hantsi ya fara ?agawa ne. Shi ne zan zuba ruwa a bokita na aje a rana. Kafin na dawo daga talla na san ya yi ?umi sai na ?an yi wanka da shi!"

Auwwa ta maka mata harara ha?i da jan tsaki. Sannan ta mi?e ta ja tulelen jikinta ta shiga ?aki. Maimuna ta zuba ruwa a bokita. Ta aje a rana. Sannan ta shiga ?akinta ta saka hijabina ta fito tana ?oye ku?in babur ?in da Mummy ta bata.

Ta ?auki bokitin doya da fulawar ta fita. Kasancewar yau ?afar tata bata ciwo ya sa ta isa makarantar Famfo goma da ta fi kusa da su da wuri. Dan a yankin unguwar tasu kusan makarantu shida ne. Kuma duk ciki babu wadda bata kaiwa tallahr doya da fulawa da safe.

Tana isa makarantar ta wuce sashin da 'yan tallah ke taruwa a babbar makarantar ta 'yan mata. Kasancewar government school ce ya sa masu kawowa tallar kayan suke taruwa da yawa. A kusa da wadda ta fi sani cikin 'yan tallar me suba Rahina ta aje bokitinta.

"Yau kin zo da wuri Maimuna. Dan sauraminti goma a fito tara"

Fa?in Rahina. Mamuna ta yi murmushi.

"Dan Allah Rahina so nake ki jire min kayana zan je asibiti a dubani!"

Rahina ta dubeta. Kasancewar ta san cewa su masu scikler ba'a raba su da jinya, ballantana kuma yanzu da ake cikin lokacin sanyi da cutar ta fi yawan tashi yasa tace.

"?afar ce ko bayanki ne yake ciwo?"

"A'a. Ai yau da na tashi ban ji ciwon ?afar ba. Auwwa ce ta ?ona ni jiya da dadare!"

Ta ?arashe tana nuna mata singalin hannunta na hagu da ya yi alamar ?una. Dan fatar wurin har ta tashi Cike da jin tausayinta Rahina ta kawar da kanta gefe tana kare fuska.

"Subhannallahi. Wallahi Maimuna Auwwa muguwa ce"

Maimuna ta sunkuyar da kanta tana gyara ledar dake kan murfin bokitinta. Sannan ta ?aga kai ta kalli Rahina dake kallonta.

"Bari na je"

"Amma kar ki da?e"

Maimuna ta gya?a kai tana mi?ewa. Kuma kai tsaye ta nufi bakin titi. Domin hawa napep, wadda za ta kaita Ha?ejia general hospital. Duk da asibitin bata da nisa da unguwar Fantai.

Da yake ta san sashin da Mummyn su Maryam take sai bata sha wahalar nemanta ba. Kai tsaye ta je ta sameta a inda suke zama. Kuma Mummy ita ta kaita aka ?aye fatar ?unan da ta tashi. Sannan aka saka mata magunguna.

Kuma a pharmacy ?in asibitin Mummy ta sai mata magungunan da aka rubuta mata, har ma da wanda ba'a rubuta ba. Wato magungunanta na cutar sickler.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login