Showing 33001 words to 35486 words out of 35486 words

Chapter 12 - ƘADDARA-CE_-By-Salma-Ahmad-Isah

05 Jul 2024

6330

sojoji, sai wani ba?in boot irin nasu na sojiji. Kuma yau ma kansa ba hula. Sai sweater guda biyu da yake ri?e da su. Ta sake kallon fuskarsa tana zare hannunta daga cikin nasa.

"To wai mi ye?"

Ta tambaya tana turo baki gaba. Mu'az ya yi murmushi kawai yana kallon wannan fuskar.

"Kaya na siya a boutique ?inku. Kuma ke nake so ki kai min mota!"

Sai ta ?ara turo baki gaba. Hawaye ko tun da ya ru?ota ta fara zubar da su.

"Ni lokacin tashi na ya yi"

"Okay. Bari in je na fa?awa oganku..."

Ya yi maganar yana shirin nufar office ?in manager. Duk dan ya tsoratata, kuma ta tsorata ?in, dan taku biyu kawai ya yi, ta yi saurin ri?o hannunsa ta dawo da shi baya. Ta ci gaba da ?ata fuska tana fa?in.

"To ai ba sai ka je ba... Ka je ka biya, zan kai maka motar"

Ta ?arashe tana ?auke kai gefe. Bai sake ce mata komai ba, ya yi murmushi ya je ya biya ku?in, sannan ya dawo ya sameta tsaye a inda ya barta, ya dan?a mata shopping bag ?in da aka saka masa sweatern a ciki. Sannan ya yi gaba ya barta a nan.

Halima ta ?aga jakar da ba wani nauyi gareta ba. Tsabar isa da gadara da take cin ransa, shi ya sa zai sa marainiyar Allah ta ?aukar masa. Ta ?arashe tana jan tsaki a ranta.

Sannan ta bi bayansa tana kumbure-kumbere, kamar kwa?on da ya ke shirin yin kuka. Kasancewar ta san motar tasa ya da kai tsaye ta nufi inda motar take. Ganin ?ofar driver seat a bu?e yabsa ta nufi wurin. Zaune ta gan shi a cikin motar. Amma kuma ?afafunsa na wajen motar. A gefe ta tsaya, sannan ta mi?a masa jakar.

"Ga shi"

Ta fa?i kamar me shirin fashewa da kuka. Mu'az da tun da ta fito yake binta da kallo ya sa hannu ya kar?i jakar. Tana shirin juyawa yace.

"Ba ki ji ba"

Cike da ?osawa Halima ta juyo, ta buga ?afarta a ?asa.

"Dan Allah ka ?yaleni ranka ya da?e. An tashi aiki, kuma gida nake son zuwa"

Sai kuma ta kai hannu ta share ?wallar da ta zubo mata. Ta juya masa baya, ta turo baki gaba tana har?e hannunta a ?irji. Mu'az ya yi murmushi. Sannan ya fito daga motar, hannunsa ri?e da bag ?in da Na'im ya saka masa chocolate da cookies a ciki. Ya zagaya ta gabanta, ya jingina a jikin motar yana ?arewa fuskarta kallo.

"Tambayarki zan yi"

Ta masa irin wannan kallon da yake sawa ya ji kamar ya tsaga ?irjinsa biyu, ya ciro zuciyarsa ya yar ya huta, saboda yanda bugunta yake hargitsewa.

"Ina ji"

Ta fa?a tana sau?ewa hannunta da ta rungume. Sannan ta goge hawayenta.

"Me nene sunanki?"

Sai ta dube shi.

"Ai ka sani"

Ya jinjina kai.

"Na san sunanki Halima. Cikakken sunanki nake nufi"

Sai ta ja hanci tana juya kanta gefe.

"Halima Auwal Ali Kaska"

Ya yi murmushi. Sannan ya ?auki chocolate ?aya ya mi?a mata. Ta kalli chocolate ?in. Sannan ta kalle shi.

"Ki kar?a"

Ta kai hannu ta kar?a, a sanda wata tambayar take biyowa baya.

"Ina ce unguwarku?"

Yanzu ma sai da ta masa kallon tsanaki. Sannan ta amsa.

"Da a Life Camp muke ni da iyayena. Bayan Allah ya musu rasuwa kuma sai na dawo wurin kawuna a Bwari!"

Ya kuma jinjina kansa. Sannan ya bata wata chocolate ?in. Ita ma ta kar?a tana kallonsa kawai.

"A halin yanzu kina karatu?"

Mu'az ya sake tambaya. Saboda yana so ya san wani abu da ya shafi rayuwarta, ?ila shi ne zai nuna masa hanyar da zai bi domin gano abin da idanuwanta ke fa?a masa a duk sanda nasa idon zai ha?u da nata.

"Shekaru biyu da suka wuce na kammala FCT College of Nursing Sciences, Gwagwalada. Kuma a shekarar ne Allah ya yi wa iyayena rasuwa"

Ya kuma bata wata chocolate ?in.

"Me ya sa malamar asibiti take aiki a boutique?"

Yanzu kuma sai ta kasa amsa masa. Ta yi shiru tana kallonsa.

"Na gaji da amsa tambayoyin da ban san dalilinsu ba. Sai an jima"

Ta ?arashe tana shirin ra?a shi ta wuce. Amma sai ya ri?o damtsen hannunta a wannan karon, ya dawo da ita. Mamaki zane a kan fuskar Halima take kallonsa. Wai shi me yake damunsa ne?. Haka kawai sai ya yi ta ri?eta?. Shi bai san me take ji ba a duk sanda zai ri?eta?.

"Gida zan tafi"

Ta fa?a tana turo baki.

"Mu je na kaiki"

Yanzu ma kallonsa ta sake yi.

"Ni ban sanka ba fa Malam JJ ?an Iya!"

Sunan da ta kira shi da shi ya sa ya yi dariya ka?an.

"Ni kuma na sanki. Ki shiga mu je na kaiki"

Ta no?e kafa?a alamun ba za ta shiga ba. Lokaci guda Mu'az ya ha?e fuska.

"Get in, Idan ba haka ba zan mareki!. I'm running out of patience!. "

Lokaci guda cikinta ya mur?a. Saboda ta tuna yanda ya mareta last time. Dan haka ta yi saurin ja da baya za ta sa kuka.

"Leemat ba na son gardama. With due respect. Get into the car"

Ta turo baki. Sannan ta buga ?afa a ?asa. Ta juya ta zagaya ?ayan ?angaren, ta shiga gidan gaba tana hawaye. Shi ma motar ya shiga. Sannan ya mi?a mata jakar chocolate ?in hannunsa. Ta ?auka tana ta ?ata rai. Wanda suke hannunta ma a ciki ta sa. Ta kame kanta gefe, ta ?i yin magana sai hawayen da take.

Shi ma bai takura da sai ta yi maganar ba. Har sai da suka iso Bawri. Sannan ya tambayeta layin gidansu a Dutsen Alhaji. Sai a sannan ne ta yi magana. Kuma suna isa ?ofar gidan ta shiga ?o?arin bu?ewa ta fita.

"Baby girl!"

Cak ta tsaya daga shirin fitar da take. Saboda wani abu da ya fa?o a cikin kanta. A gaba ?ayan rayuwarta mahaifiyarta ce ka?ai ke kiranta da sunan. Hakan ya sa ta juyo ta kalle shi.

"Kukan na mi ye?"

Ta kai hannu ta goge ?walla tana ci gaba da tura baki.

"Ba kai ne ka min tsawa ba"

Kansa ya girgiza.

"Gardama kika yi. And i hate stubbornness. Amma ki yi ha?uri"

Ta ci gaba da tura baki tana kumbura shi.

"Ki ha?ura da wuri, saboda kar ki sake shigo min ciki tunani ki fitineni"

Ta kuma kallonsa.

"To na ha?ura. Kuma na gode"

Tana kaiwa nan ta fice daga motar. Zuciyarta cike taf da farin cikin wannan kyauta da ya mata ta chocolate da cookies. Saboda abu ne da ta da?e ba ta sa a ido ba, ballantana har ta kai ga sha. A ?aya ?angaren kuma tana cike da fargabar batun rage ma'aikata da za ayi a boutique ?insu. Shi ma wannan batu ya hana zuciyarta sukuni. Har ta shige gidan Mu'az na kallonta yana murmushi.

"Rigima Baby girl"

Ya fa?a yana shafa gajerar sumar kansa. Yana shirin tayar da motar kiran Faruk ya shigo wayarsa. Hakan ya sa ya fasa ya ?aga wayar.

"Kaigama what's up?"

Daga ?ayan bangaren Faruk yace.

"Yanzu Muktar ya kirani. Ya sanar min da cewa yana son ganinmu ni da kai da gaggawa!"

Mu'az ya ?an sosa kan hancinsa yana duba agogo.

"Okay a ina zan sameka?"

"Ina gida. Ka zo ka ?aukeni sai mu wuce headquartern"

"Okay"

Daga haka ya sau?e wayar. Sannan ya tayar da motar ya nufi gidan Faruk.


MUKTAR POV.

Zaune yake cikin office ?insa. Yayin da Faruk da Mu'az ke zaune a kan kujerun dake gaban teburinsa. Tun da suka zo headuatern, suka ritsa shi da tambayoyi na me ya same shi.

Saboda ganin raunukan da suke a jikinsa. Hannunsa na hagu da yake da tabbacin ya karye ya kuwa karye ?in. Dan yanzu haka sai da aka yi wa hannun ?ori a asibiti. Ban da sauran wuraren da suka raunatu a jikinsa.

Saboda jiya har ?arfe sha biyu suna asibiti shi da Walid da Ali. Kuma duk da yanda likitocin suka so ya zauna a asibitin ?i ya yi. Saboda ba ya jin zai bar abin da ya faru ya tafi a banza. Dole ne ya ?auki matakin gaggawa, a yanzu sun kuskure wurin halaka shi, wata ?ila nan gaba Allah zai iya basu nasara.

Ba mutuwarsa ce abar tsoro a wurinsa ba. Ya san cewa ko wani mai rai ?arshen rayuwarsa a duniya mutuwar ce. Kamar dai yanda mahaifinsa ya rasu ya bar su shi da ?aninsa da kuma mahaifiyarsu. Abin da zai fi ?ona masa rai shi ne da zai mutu ya bar Mariya da abokin aikata kisanta a raye, suna cutar Faruk da kuma sauran al'umma...

"Mukhy!"

Mu'az ya kirashi da ?an ?arfi, ganin kamar tunaninsa ya yi nisa da gangar jikinsa. Hakan ya sa ya dube shi da sauri yana amsawa.

"Na'am!"

"Ina ka tafi?"

Mu'az ya tambaya yana watsa hannu a iska. Muktar ya girgiza kansa yana ?ora hannunsa a kan table ?in dake gabansu. Ya furzar da huci ka?an. Sannan ya dubi Faruk, ya dawo ya dubi Mu'az.

"Kaigama!"

Faruk ya gyara zama yana fa?in.

"Na'am Mukhy!"

Muktar ya kalli Mu'az.

"MJ!"

"Umm!"

Shi ma ya amsa. Muktar ya jinjina kansa. Yana son sanin ta inda zai fara musu bayani a kan wata makusanciyarsu ita ce me laifin da suka da?e suna nema ruwa a jallo.

"Kaigama! MJ!. Ba na so na zama mutum na farko da zaisanar da ku wannan mummunan labarin!... Dan haka zai fi kyau ku kalla da idonku, kafin bayanina ya biyo baya!..."

Su dai kallonsa kawai suke da rashin fahimta. Kuma duk sun ?agu ya fa?a musu dalilinsa na yin kiransu. Ba su ce komai ba har ya juyo musu screen ?in laptop ?in dake kan teburin. Sannan ya na?e hannunsa yana kallon fuskokinsu.

A lokacin da videon ya kai ?arshe. Ba a ce a tsakanin Faruk da Mu'az wa ya fi wani shiga shock ba. Kallon juna kawai suka yi baki a sake. Kafin Mu'az ya yi ?arfin halin kai hannunsa ya sake kunnawa.

Tunaninsa, zuciyarsa, da duk wani abu me fa?a a ji a jikinsa na fa?in wannan ba ?anwarsa ba ce. Wannan ba Mariya ba ce. Wannan ba ?anwarsa da ta fi kowa acikin ?annensa soyiwa a ransa ba ce. Sam ba ita ba ce!... Ya ma za ayi ta kasance Mariya Jibrin Gimba?.

Shi dai Faruk ba irin wannan tunanin yake ba. A kallo ?aya da ya yi wa videon ya gane matarsa. Saboda ya santa, ya kuma san wacece ita. Amma abin da bai gane ba shi ne, me ya sa Mariya za ta sace Munira, har ta kai ga kasheta?.

Sannan wannan mutumin da suke tare da shi, waye shi?. Me zai sa matarsa da ba za ka yi tunanin idan ka sa mata hannu a baki ba za ta ciza ba ta yi kisan kai?... Yanzu har Mariya za ta iya kashe wani?. Me ya sa?. Me zai sa ta kashe Munira?. A tare suka sake kallon juna, sannan suka kalli Muktar da shi ma yake kallonsu.

"Na san kallon wannan videon zai sa tarin tambayoyi a cikin kawunanku... Tabbas wannan Mariya ce. Matarka Kaigama, ?anwarka MJ. Kuma..."

Bai kai ga ?arasawa ba. Mu'az ya mi?e tsaye, sannan ya sha?o wuyansa ya mi?ar da shi tsaye yana jin kamar ya kashe shi ya huta. Sai huci yake yana jin zuciyarsa na zafi.

"Yes, it is a good sentence! It's a clear and strong expression of defense and protection towards one's sister. The phrase "How dare you" is a powerful way to convey shock, anger, and disapproval. The sentence is well-structured and effectively conveys the speaker's emotions and stance.

Here are some similar sentences that convey a similar message:

"How dare you talk about my sister in that tone!?"

Ya fa?i a kausashe. Muktar bai ce komai ba, kuma bai yi yun?urin ?watar kansa ba. Saboda ya san ko shi aka zo aka samu da zancen cewa Walid ya yi kisan kai zai iya shiga cikin halin. Da ?yar Faruk ya cire hannun Mu'az a wuyan Muktar, ya ja shi baya ba tare da ya ce masa komai ba.

"I can't believe he thinks Mariya is responsible for Munira's death!... And... and!"

Ya kasa ?arasawa yana jin idonsa na cika da ?walla. Amma kuma ba ta zubo ba. Har ji yake numfashinsa na shirin ?aukewa. Ya yi shiru kawai, yana fitar da iska daga huhunsa da ?yar, kamar me ciwon zuciya.

"Get seated"

Fa?in Faruk yana zaunar da shi a kan kujera. Zaman ya yi yana dafe kansa da ya fara sarawa. Da ma shi haka yake, daga zarar ransa ya ?aci zai fita hayyacinsa gaba ?aya, idan bai yi sa'a ba ma sai ya kwanta jinya.

"Ina jinka Muktar"

Faruk ya ha?e kalaman yana ha?iyar yawu da ?yar. Saboda jin wani abu ya toshe masa ma?oshi. Shi bai fa?a cikinsa ba, kuma bai fito ta bakinsa ba. Muktar ya zauna, sannan ya ci gaba da fa?in.

"... Na samo wannan videon ne a unguwar da aka sace Munira. Na same shi ne daga wurin wani yaro da a lokacin da aka sace Munira ya yi recording videon... A lokacin da na samu vedion ban yi ?o?arin sanar da kowa ba face Ali mataimakina, wanda tare da shi muka je. Abin da ya ba ni mamaki shi ne a wannan ranar wani ya biyoni gida yana ?o?arin kasheni. Amma Allah ya taimakeni na tsira. Sai dai kuma a daren jiya Mariya da wannan mutumin na cikin videon ne suka zo har unguwar mu. Kuma na gansu, sannan su ne suka bigeni da mota. Har na samu wa?annan raunikan na jikina... Shi ya sa na ce ba zan yi ?asa a gwuiwa wurin sanar da ku wannan gaskiyar ba!"

Faruk ya dafe kansa. Tunanin abin da ya faru tsakaninsu jiya ya dawo masa. Ke nan jiya da daddare kashe Muktar ta tafi?. Innalillahi wa inna ialaihi raji'un. Ya furta yana murza goshinsa. Mu'az kuwa bai sake cewa uffan ba. Sai yatsun hannunsa da yake murzawa idonsa na sauya kala zuwa ja.

-------------------------------

_Wato a wasu lokutan. Abubuwan da ba mu yi zato ba su ne suka cika faruwa da mu._

_Irin haka ce ta faru ga Faruk da Mu'az._

_Shin! Wani dabi ne zai ?arke a ha?ejia, tsakanin Gambo da Maimuna da kuma Auwwa?._

_Shin, wani hali kuke tunanin Halima za ta shiga idan aka sallameta a aiki?._

_Me zai faru tsakanin Mariya da Faruk?._

_Sannan Mu'az, dan shi kam ya fi Faruk fusata._

_Yaya Mariya za ta yi domin wanke kanta a idon yayanta da kuma mijinta, da ma sauran jama'ar duniya da za su sani?._

_Shin, kuna ganin cewa, kisan Munira zai zama kisa na ?arshe da Mariya za ta aikata?. Ko za ta ci gaba da zama a ?ungiyarsu ta bayin Shai?an!?._

_Hummm!_

_Akwai magana. To, ga duk wanda yake son sanin amsoshin wa?annan tambayoyin, sai ya biya ?300. Tun kafin tafiyar nan ta wuce ku._

_Kun san daga ganin tafiyar nan ba ta wasa ba ce, dan har yanzu ba mu yi komai ba. Kuma ina me muku tabbacin ba za ku yi da na sanin siyan wanna littafi ba. Kun san al?alamin Candy akwai suger._

••• ••• •••

*Zan yi amfai da wannan damar, wurin gode muku, SALMANIANS. Kun san da cewa ku ne on top a ?albina. I love you like wujiga-wujiga. Ina sonku fiye da irin son da kuke min*

Ga duk wanda ya shirya dan ayi tafiyar nan da shi, zai ?300 kacal. Ta wannan account details ?in da zan rubuta. Idan kuma har ya zama complete document sai dai ku biya ?500.

5487270431
Salma Isah
Moniepoint

Shaidar biya kuma via.

08130172702.

Sai na ji ku SALMANIANS.

Best regards.
*SALMA AHMAD ISAH*
*(CANDY??)*

2024...

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login