Showing 18001 words to 21000 words out of 35486 words
ta fito ita ka?ai ya sa Mu'az ya ?aga kai ya kalleta.
"Yana ina?"
Ta zauna a kan kujera tana fa?in.
"Wanka zai yi. Amma yace yana zuwa"
Mu'az ya gya?a kai, sannan yace.
"Me ya same shi wai?"
"Kwana ya yi da ciwon kai, shi yasa ya makara"
Ya kuma gya?a kansa yana ?aga Hilal. Suka ci gaba da wasa da Hilal ?in, har zuwa sanda Faruk ya sau?o sanye da kayan aikinsa, wato kakin sojoji. Kana ganinsa ka ga wanda ba ya cikin nutsuwa, ko kuma mara lafiya.
"Kaigama!"
Mu'az ya kira yana mi?ewa tsaye, yana ri?e da Hilal. Faruk ya ?an yi murmushi yana lumshe idonsa da kalarsa ta sauya. Sannan ya bu?e shi a kan Hilal.
"Idan kan naka bai daina ciwo ba za ka iya komawa ka huta"
Faruk ya girgiza kansa.
"A'a. Zan iya zuwa barrack. Mu je kawai"
"Kuma fita za ka yi ba tare da ka ci abinci ba?"
Mariya dake gefe ta fa?i. Hakan ya sa suka dubeta a tare.
"Yanzu na makara. Ki aje min abincin dare kawai"
Fa?in Faruk.
"A'a ka zauna ka ci abincika kawai"
Cewar Mu'az.
"Bana jin cin abincin ne. Mu je kawai, zan ci abincin a barrack"
Mu'az ya jijina kansa, sannan ya mi?awa Mariya Hilal. Suka mata sallama suka fita a motar Mu'az. Suna tafiya a hanya ?addara tasa Mu'az tsayawa a wani boutique me sunan 'UMMUL BANAT BOUTIQUE'. A sanda motar ta yi parking a harabar boutique ?in Faruk ya ?aga kansa ya karanta sunan boutique ?in. Sannan ya kalli Mu'az yana fa?in.
"MJ me za mu yi a nan?"
Mu'az na cire seat belt ya amsa da.
"Na'im ne yace na sai masa sweater"
"Okay mu je"
Ya fa?a yana bu?e ?ofar motar. A tare suka nufi ?ofar shiga boutique ?in. Boutique ?in da ?addarar Mu'az ke zaune a ciki. Boutique ?in da zuwansa cikinsa zai sauya rayuwarsa gaba ?aya.
Kamar yanda Na'im ya wassafa masa yanayin sweatern da yake so ita ya ?auko masa har guda biyu. Rigunan na ri?e a hannunsa suka nufi wurin cashier. Ya juya kansa yana yi wa Faruk magana. Ya ji ya ci karo da mutum. Kuma a lokaci guda abinda ke hannun mutumin da sukayi karon, wanda yake da tabbacin ya fishi tsayi ya zube a jikin rigarsa.
A lokaci guda zuciyarsa ta tafarfasa har ta fara shirin ?onewa. Hakan ya sa ba tare da ya duba da wa ya ci karo baya ?aga hannunsa da bai ri?e rigar da shi ba, ya sharara wa budurwar dake tsaye a gabansa mari.
Wata iriyar ?amewa ta yi. Ta saki kofin ruwan dake hannunta, wanda ruwan cikin ya zube a jikin rigarsa. Sannan ta ?ora hannunta na dama a kan kuncinta. A take hawaye suka soma zubowa daga raunannun idanuwanta. Da ?yar ta iya ?aga idonta ta saka su cikin nasa.
Kuma shi ma sai a lokacin ya samu damar kallonta. Wata farar matashiya ce, da a shekaru ba za ta ?ara Mima ba. Hawayen da suka wanke mata fuska ya sa ya ga fuskar tata har wani ?yalli take. Sanye take da farar Oxford shirt. Da kuma ba?ar straight skirt. Ta yafa ba?in veil a kanta. Kuma ya lura da kamar kayan su ne wanda masu aikin wurin suke sakawa.
?wayar idonta dake rawa a kan fuskarsa, da kuma hawayen da ya taru a cikin idonta da yake ?yalle saboda hasken fitilun wurin yasa ya ji kamar yana nitsewa cikin wani abu me kama da gajimare. Akwai rauni, ha?e da neman taimako a cikin idonta. Sannan ya ga fata da kuma sa rai a cikinsu. Yanayin yanda ta turo fatar bakinta ta ?asa zai sa ka san cewa shagwa??a??iya ce tun tana da ?arancin shekaru, ko kuma wadda gata ya yi wa yawa.
"Mu'az!"
Faruk ya kira yana ta?a kafa?arta.
"Humm!"
Ya amsa kamar wanda ya dawo daga WATA DUNIYA. Ya kalli Faruk, sannan ya sake kallon budurwar dake tsaye a gabansa har zuwa lokacin. Tana dafe da kuncinta. Ga hawayen da take zubarwa, sannan bakinta da ta turo cikin shagwa?a yana rawa ka?an. 'Oh lord have mercy!' Ya fa?i a zuciyarsa.
"Wai me ya faru ne?"
Faruk ya tambaya. Amma sai Mu'az ya kasa magana. Ya ci gaba da kallonta. Har zuwa sanda wata murya ta kira sunan.
"Halima!"
Daga bayansa. Hakan ya sa ya juya, yayin da ita kuma budurwar me suna Halima ta kalli Kairat ?awarta da ta kirata. Dan haka sai ta sau?e hannunta daga kan fuskarta. Ta sunkuyar da kanta ?asa, ta ra?a Mu'az ta wuce wurin Kairat.
"MJ!"
Faruk ya kuma kira. Mu'az ya juyo ya kalle shi. Sai kuma ya kalli rigunan da yake ri?e da su, haka kawai ya aje rigunan a kan wasu kaya. Ya nufi hayar fita. Kai a kulle Faruk ya bi bayansa. Dan shi sam bai ga tahowar yarinyar ba, ballantana ya ga sanda suka yi karo da Mu'az ?in.
"Me ya faru wai?"
Kairat ta tambayi Halima da har zuwa lokacin bata daina hawaye ba. Sai ta juyo mata da ?arin fuskarta na dama. Inda shatin hannun mutumin da ya mareta ya fito har guda hu?u. Wurin har ya yi ja. Ya kuma kumbura.
"Na shiga uku? Wai wancan sojan ne ya mareki haka?"
Kairat ta tambaya tana zaro ido. Tare da kama gefen fuskar ?awarta tana ganin yanda wurin da aka mareta ya yi ja. Cike da shagwa?ar da ta zame mata jiki Halima ta gya?a kai tana goge ?walla. Sannan cikin murya me sanyi tace.
"Haka kawai bawan Allahn nan ya sharara min mari, wai dan na bige shi. Kuma fa sai da na kauce masa, shi ne bai kula ba!"
"To Allah ya saka miki. Ya hana masa sukuni saboda marainiyar Allah da ya cutar!"
Kamar an kunna famfo haka ta ci gaba da zubar da ?walla. Kuma da ma ita can haka take. Abu ka?an kan iya sakata kuka, ballantana yanzu da ta sha mari. Har zuciyarta ta jawa wannan azzalumin sojan Allah ya isa ta fi sau dubu.
MARIYA POV.
Kukan Hilal da ya cika ?akinta ne yada ta ja dogon tsaki. Sannan ta juyo ta kalle shi. Yanayin zaman da ya yi ka?ai ya sa ta gane cewa bayan gari ya yi a cikin diapers ?in dake jikinsa. Wani tsakin ta ja, sannan ta ci gaba da latsa wayarta hankali kwance. Kukan nasa da ya ci gaba da tashi ya sa ta kalle shi a hasalle, sannan ta daka masa tsawar da za ka dafa ?ur'an kan cewa ba ita ta yita ba.
"Ka rufe min bakinka a wurin!"
Amma bai yi shirun ba. Sai kukan nasa da ya ?arawa volume. Wani dogon tsakin ta kuma ja. Sannan ta mi?e tsaye ta fita daga ?akin, ta kulle ?ofar ?akin. In yaso ya je can ya yi ta yi shi ka?ai.
Tana taka stairs tattoo ?in dake bayan wuyanta ya soma haske. Hakan ya sa ta ?ame a wuri ?aya. Domin ta san kira ne daga shugaban bayin shia?an. Bata raba ?ayan biyu ba suffar Wahash ta bayyana a tsakiyar falo. Hakan yasa ta sau?a ?asa da gudu. Sannan ta yi saurin zubewa a ?asa, ta yi wa shugaban bayin shai?an sujjada.
"Giram gareka Wash. Duk wani shugaba da ba kai da shai?an ba ba a kan gaskiya yake ba!"
(A'uzubillah!)
Wahash ya sa hannu ya ?ago da ita, ya mi?ar da ita a kan ?afafunta. Amma kanta a ?asa cike da girmamawa irin tasu ta 'yan wahala a duniya.
"Rezor!"
Wahash ya kira. Hakan ya sa ta ?aga idonta ta kalli fuskarsa.
"Mijinki da ?an uwanki, da kuma wani jami'in ?an sanda na shirin ha?a ramin binne kansu!"
Cike da rashin fahimta tace.
"Ban gane ba shugaban bayin shai?an!"
Wahash ya juya bayansa. Sannan ya yi taku biyu gaba. Ya ?an juyo ka?an ya kalleta.
"Duk da na sa a goge duk wata shida da za ta nuna cewar ke kika kashe Munira da kuma Danesh sai da suka yi ?o?arin za?ulo wani abin. Yanzu haka shi ?an sandan da suka ?ora a kan aikin yana ta binciken gano wanda ya kashe Danesh da Munira, domin kuwa duk sun gane cewa makasan nasu mutum ?aya ne ko biyu. Ko ma sama da haka, kuma da alama suna daf da cimma gano ki. Ganoki kuma yana nufin gane ?ungiyar jajayen bayin shai?an!..."
Mariya ta girgiza kanta da sauri, sannan ta tsaya avbayan Wahash tana fa?in.
"Yanzu wani mataki aka ?auka a kansu... Da ace asirin ?ungiya ya tonu tadalilina gwanda a kawar da mijina da kuma ?an uwana. Idan har asirin ?ungiya ya tonu ina zan saka kaina Wahash?!"
Wahash ya girgiza kansa, sannan ya juyo suka fuskanci juna.
"Mijinki da ?an uwanki ba su ya kamata mu kashe a yanzu ba. Shi wannan ?an sandan me sunan Muktar shi ne babban ha?arinmu a yanzu. Dan haka shi ne wanda za mu fara kawarwa a duniya"
Ba tare da ta nemi sanin waye ?an sandan ba tace.
"Ina fatan yin hakan ya kawo ?arshen wannan tsinannen binciken da aka fara. Da dukkan goyon bayana na amince da hakan Wahash!"
Wahash ya gya?a kansa. Sannan ya lumshe idonsa, cikin ?asa da sakanni ya ?ace a falon. Mariya ta ja dogon tsaki tana jin haushin Mu'az da Faruk a lokaci guda. Ta lura da kamar suna so su da?ile mata son kasancewarta ta hannun daman Wahash. Amma ba komai, idan har suka ci gaba da ?o?arin tono ramin za ta sa a binne su ciki.
_Share fi sabillilah??_
*Daga al?alamin Salma Ahmad Isah??.*
*CANDY CE??.*
--------------------
_Kada a manta da biyan ku?in littafi. Dan free pages sun kusa ?arewa. To subscribe pay ?300 to._
5487270431
Salma Isah
Monie point.
And send the evidence of payment via.
08130172702
#Candy
ーーーーーーーーーーーーーーーーーー
*?ADDARA CE!*
*(c)SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY??*
_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_
*07*
*Unguwar Dutsen Alhaji, Bwari, Abuja.*
*Da misalin 08:20 na dare.*
HALIMA POV.
Mai mashin ?in da ya ?aukota tun daga Ummul Banat boutique, wato wurin da take aiki ya tsaya a ?ofar gidan kawunta. ?anin mahaifinta, wanda take kira da Kawu Sani. Sau?a ta yi daga kan mashin ?in. Sannan ta ?auko ku?in mai mashin ?in ta ba shi.
Ta juyo ta kalli ?aramin gidan da ya fi ko wani gida nuna halin rashi a layin. Bakinta ?auke da sallama ta shiga gidan. A tsakiyar gidan ta taka birki. Ta shiga kallon jama'ar gidan dake kaikawo. Duk yawan mutanen gidan, an rasa wanda zai amsa mata sallama sai Mama Sadiya. Wato matar Kawu Sani ta farko.
Ba tare da tace ko ta yi komai ba ta wuce ?akin 'yan matan gidan. Su hu?u ta samu zazzaune a ?akin suna sabgarsu. Sallama kawai ta yi ta shiga cikin ?akin. Kai tsaye ta wuce wurin da take aje kayanta, wato kusa da katifarta ta kwana. Jakarta ta sau?e. Sannan ta zauna a bakin katifar tata tana jin yunwar dake cikinta na ?ara girmama.
"Halima!"
Zaliha 'yar Mama Sadiya ta farko ta kira sunanta. Hakan ya sa ta juyo ta kalleta.
"Me yake damunki?"
Ta shagwa?e fuska kamar yadda ta saba. Sannan ta nuna mata gefen fuskarta.
"Dubi ki ga abin da wani mugun soja ya min yau a boutique. Wai dan kawai mun yi karo fa shi ruwan da yake hannuna ya zube a jikinsa. Shi ne ya sharara min mari! Wallahi yanzu haka ma wurin ciwo yake min. Ji nake kamar ya karya min ?ashin fuska !"
Ta ?arashe ?wallar shagwa?a na zubo mata. Ta turo baki gaba. Tana jin kamar ta fashe da kuka. Da ace lokacin iyayenta na raye ne da yanzu wannan abin da ya mata ya sa ta kwanta jinya. Saboda a wancan lokacin ita 'yar gata ce. Shagwa?i?iyyar iyarta da babanta, saboda har suka koma ga mahaliccinsu ita ka?ai ce 'yarsu.
Mahaifinta Alhaji Auwal Kaska ?an kasuwa ne me arzi?i dai-dai gwargwado. Matarsa ?aya, haka kuma 'yarsa ?aya. Kasancewar tun bayan da aka haifi Halima ba su sake samun wani ?an ba sai suka shagwa?ata. Gata babu kalar wanda ba su yi mata ba. Shi ya sa ta taso a shagwa?e.
Domin ko me ta nema za ta samu. Ba ta san babu ba. Shi ya sa a sanda Allah ya yi wa iyayenta rasuwa a lokaci guda ta shiga halin ha'u'la'i. Ba'a samu kanta ba sai bayan kwana arba'in da rasuwarsu. Kuma daga lokacin ne ?alubalen rayuwarta ya fara. Saboda kaf cikin dangin mahaifiyarta babu wanda ya yi ?o?arin ?aukanta dan ya ri?eta. Kowa yana gudun wahala. A cikin dangin mahaifin nata ma da ?yar aka samu Kawu sani yace zai ri?eta.
Saboda a lokacin an raba gado, dan daga ita sai shi ne ka?ai suka ci gadon mahaifinta. A sanda ta dawo wurinsa ya lalla?ata da da?in baki ya ?wace duk wani abu da aka mallaka mata ya cinye. Sai da ku?a?e da kadarorinta na hannunsa suka ?are sannan ta fara fuskantar taskun rayuwa a gidansa. Dan gaba ?aya Kawu Sani riki?ewa ya yi ya sauya mata. A farkon zuwanta gidan ba ta cin abinci ?aya da sauran iyalansa.
Saboda ita ba ta saba da cin abinci mara kyau da da?i ba, shi kuma ta?onsa ya sa gidansa babu kyakkyawan abinci. Amma bayan ku?a?en sun ?are sai ita ma ta dawo tana cin abinci ?aya da na yaran gidan. Sai kuma tsangwamar da matar Kawu Sani ta farko wato Mama Zulai ke mata. Aikin wahala babu wanda ba ta sakata, kowa na gidan ya rainta. Shi ya sa gaba ?aya ta tsani rayuwar gidan. Idan ta tuna da yankan ?aunar da mutuwar iyayenta ta mata.
A rayuwar Kawu Sani, idan kana da ku?i kai ne mutum. Shi ya sa gaba ?aya 'ya'yansa mata suke fita domin nemo masa ku?i. Wasu ma ta hanyar da bata dace ba suke samowa ku?in. Amma shi bai damu ba, in har za'a kawo masa ku?i to su bi kowace hanya ma. To Halima bata shiga tara ba sai da Kawu Sani ya bijiro mata da zancen dole ta fara fita neman ku?i kamar sauran 'ya'yansa. A lokacin ta sha kuka sosai, duk da da ma can ita kuka ba ya mata wahala.
Sai dai ta riga tasa a ranta cewa ba za ta ta?a yin abin da su Jidda babbar 'yar Mama Zulai ke yi ba, na bin maza domin samun ku?i. Shi ya sa ta naimi taimakon Zaliha kan ta tayata naiman aiki. Shi ne har ta samu aiki a Ummul Banat boutique. To da wannan aikin ne take samun ku?in da take bawa kawu Sani, dan ta samu ta zauna a gidansa. Amma duk da haka ba ta da kwanciyar hankali, saboda masifar Mama Zulai ba ta barinta ta huta.
"Ayya. Sannu, kuma wurin ya yi ja sosai, bari in shafa miki man zafi!"
Fa?in Zaliha cikin tausayawa. Halima ta gya?a kai tana jin tausayin kanta, saboda yanzu haka ma kanta ciwo yake. Zaliha ta mi?e ta nufi jakarta ta kaya, ta ?auko man zafin. Sannan ta dawo ta zauna kusa da Halima, ta shafa mata a gefen fuskar tata da ya kumbura.
"Kin yi sallah?"
Zaliha ta tambaya. Halima ta gya?a mata kai a shagwa?e.
"To Mama ta kusa gama girki, idan ta gama sai na zubo mana mu ci"
Ta kuma gya?a kai, sanna ta kwanta tana jin kanta na ?ara mata ciwo. Idonta ta lumshe, fuskar wannan mugun sojan ta shigo cikin tunaninta, dan haka ta yi saurin bu?e idonta gabanta na fa?uwa. Dan haka kawai take ganinsa kamar wani dodo. ?wafa ta yi, sannan ta cije le?enta na kasa. Ta juya kwanciyarta tana ja masa Allah ya isa.
"Insha Allah ba za ka samu sukuni ba tun da ka ?aga hannunka ka mareni. Mugu me jar fuska kawai... Banza ?atoto!"
Ta fa?i a zahiri, zuciyata na zafi da abin da ya mata. Kamar daga sama ta ji Mama Zulai na ?wala mata kira.
"Ke Halima!. Halima!"
Idonta ta rintse. Ko wani ?an ?aniyar ne ya fa?awa wannan masiffafiyar matar ta dawo?. Mi?ewa ta yi zane, tana fa?awa zuciyarta cewa yanzu za'a ha?ata da wani aikin. Ba'a barta ta huta da gajiyar da ta kwaso a wurin aiki ba, an zo za'a ?ara mata da wani aikin.
Tana tura baki gaba tana shagwa?e fuska ta ?aga labulen ?akin da suke ciki, tana amsa kiran 'yan farautar da Mama Zulai ke mata. Tsaye ta hangeta a bakin rumfar da ake girki a gidan. Ta ha?e girar sama da ta ?asa, tana mata wani kallon tara saura kwata.
"Ub*n me kika shiga yi a ?akin?. Bayan kin san cewa yau girki na ne?"
'Aikin ?aniya na shiga yi a ?akin. Masifaffiya kawai! Ni na saki yin girkin dole?, Da za ki zo ki takurawa rayuwar marainiyar Allah?. Muguwa Azzaluma'
Ta yi maganar duka a zuciyarta. A fili kuma sai wani tsuke baki take tana rau-rau da ido. Tana wani karkata kai, wai duk dan a ji tausayinta. Amma ta san ba za'a ji tausayi nata ba. Tana yi ne kawai dan ya zame mata jiki.
"Ki fito ki zo ki ?arasa tu?a tuwon nan... Kuma in kin gama ki rabawa yara... Mtsuww!"
Mama Zulai ta ?arashe da tsaki. Sannan ta juya zuwa ?akinta. Jiki a sa?ule Halima ta fito daga ?akin. Tana tafe hawaye na mata zuba. Tana shirin zama a gaban murhun dake ?auke da tukunya lamba goma. Mama Sadiya ta fito daga ?akinta tana fa?in.
"A'a me sunana. Ta shi ki je ki kwanta ki huta. Ni zan tu?a tuwon!"
Halima ta girgiza kai. Sannan ta zauna a kan kujera tana fa?in.
"Ba komai Mama. Zan yi"
"Da dai kin kawo na tu?a"
"Ai ba yawa, yanzu zan tu?a"
Da haka ta ?auki doguwar muciyar tu?in tuwon da ta kusa kaiwa tsawonta. Sannan ta saka a cikin bu?a??iyar tukunyar. Ta fara ?iban garin dawar dake gefe tana zubawa a cikin tukunyar. Sai da ta gama tu?e tuwon, sannan ta shiga rabawa yaran gidan a tray. Ba ita ta koma ?aki ba sai da ta tabbatar da ta rabawa kowa nasa. Sannan ta koma ?aki ta kwanta. Tana hawayen da suka zame mata jiki tun shekaru uku baya.
"Halima tashi mu ci tuwo"
Fa?in Zaliha tana aje musu tray ?in tuwon da ta saka masa miyar kukar da Mama Zulai ta yi. Halima ta mi?e zaune, tana sharar ?walla. Ita fa a rayuwa ba ta san cewa mutane na cin dawa ba sai a gidan Kawu Sani. A rayuwarta ta baya ta ?auka cewa doki kawai ake bawa dawa.
Ashe ita ma za ta wayi gari ta girka tuwon dawa, har ma ta ci shi dan maganin yunwa. Kamar yanda ta saba cin ko wani abincin gidan dan kashe yunwa yau ma haka ta ci. Saboda da ace ita