Showing 51001 words to 54000 words out of 81157 words

Chapter 18 - BURI DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

08 Apr 2025

6616

Yana kallon kayansa cikin nuna takaici.

Kallonsa tayi da sauri tana sake kafesa da ido sbd tabbas tasan da gangan yayi sbd taga lokacinda yasa qafa gurin ya buge table din.

Mamakinsane tareda sabuwar fargabarsa tasake shigarta ta kalli kayan daya zubar din cikeda mamakin yin hakan zata dauke ido idanuwanta suka sauka kan id card dinta a qasa gurin bakin gado.


Atake taji idanuwanta sunyi jajir suna neman cikowa sbd tabbas tasan yau komai ya lalace Mata gashi police din ya hango id card din ya nufi gurin Yana cewa"

I think we found something here.

Kallon gurin haydar yayi yaga fuskarta baro baro akai,
Police din zai dauka yarigasa dauka fuskarsa ba wani sakewa yace"

It's mine,I think it felt dwn from my pocket while I was taking my phone out.

Sakawa alhijun suits dinsa yayi tareda nufar qofa Yana sake goge jikinsa da tissue.


Bayansa tabi da kallo yau Kam mamakinta da tsoronsa sunfi na jiya da yau a ranta,

Ta tabbarda da gangan ya zubarda abincin saidai Bata San meyasa yayi hakanba,
Id card dinta kuwa tasan nata ne yasan nata ne Kuma yaganta a jiki Kuma hakan ya nuna baro baro tana dakin kafin yanxu kenan Dole akwai saka hannunta Amma ya dauka ya Hana police su dauka,
Meyasa zai kareta ya boyeta ya Hana asirinta tonuwa????

Idan harya kareta ya Hana akamata akan ta cutatarda in-laws dinsa it means kenan shima yanada wani motive akansu....
Zatai bincike akansa Dole saitasan wayeshi, meyene motives dinsa akansu dillas dahar zaiga Wanda yayi musu abinda akai yau ya rufata,

He seems to be more clever and dangerous than her Dole zatai taka tsantsan tasan wayeshi batasan da wa take dealing ba,JJ zai binciko musu komai akansa cikin 3days.


Suma su dillas din fitowa sukayi nadeey na riqeda mum din Suma su am duk ransu a bace yake musamman am daya San wannan abin baqaramar mummunan illa zai musuba sbd business deals dinsu kusan yanxu duk ja Baya zaa dasu sbd sunansu ya baci a media.

Qoqarin shiga motoci sukeyi Amma Ina media ta rufesu sai tambayoyi suke musu Amma Babu Wanda zaikarbu sbd Muni da 'dacinsa shiyasa securities ke kakkaresu su samu shiga mota.

Daga can cikin yan press din wani yace"

Mrs Dilla ko Zaki iya sake bamu bayanin abinda kike nufi gameda cewar da kikayi Zaki kashe mayor da familynta???

Dukkaninsu cak Suka tsaya Jin wannan tambayar sbd fitarta media balaice atake am yayiwa wani securityn dad dinsa ido tareda nuna masa Wanda yayi tambayar.

Nadey data lura da hakan takuma San me zasuyi masa sai kawai ta fidda wayarta cikin style ta dauki hotonsa atake ta turawa JJ tareda masa text.

Aikuwa suna barin gurin shima Dan press din yafito ya hau abin Hawa Yana barin gurin sunyi nisa kadan aka taresu aka fiddosa cikin motar wasu masu mask ne Suka hau dukansa suna cewa waya basa izinin yiwa Mrs Dilla wannan tambayar gaban media.

Dukansa sukeyi sosai tareda yayyanka masa wuqa zasu sokesa daidai nan JJ daya Kira police suka qaraso sukuma Suka gudu.

Da sauri JJ yaqaraso gurinsa Yana cikin ransa Yana cewa"

Sorry nabarka sun dakeka sosai kafin mukawoma ceta munada buqatar hakan ne sbd zaimana amfani gaba.

Daukarsa akayi aka nufi asibiti dashi shikuma JJ yatura Mata massage ya rubuta"""done"""


Wani irin sahirtaccen murmushi tasaki tareda sake riqe hannun mum din tana fuskar tausayi cikin munafurci tace"

Mum please don't stress your self about this ok??? everything will be ok wen the cops finds out who is behind this.

Wani numfashin takaici tasaki zuciyarta na qara qonuwa ita Sam takasa yardama da wani banxan zancen cewa wani ne yayi musu hakan tun farko uban me sukeyi a hotel tare while they do all the business atare.

Suna isa gida haka ta ringa lallaba mum din tana rarrashinta cikin munafurci sbd tasan ita daga yanxu anyi eliminating dinta cikin game din.

Ranar a gidan ko dinner Babu Wanda yayi komaima kashewa akayi na kallo sbd yanda aketa saka maimacin abin gidan television na labarai abin Babu ko shaawar nunawa,

A rayuwarsu Basu taba shiga irin wannan baqin ciki da kunyar ba sai yau shiyasa yau gidan tsit Babu ko wani dogon motsi.

Harta kwata taji wayarta na ringing ahankali ta bude ido ta lalubo wayar tana dubawa taga JJ da sauri tayi saurin tashi zaune tana kallon fammah dake bacci gefenta duk saitaji tabata tausayi sbd ita Babu ruwanta Amma zata dandana dacin abinda zai faru.

Toilet tashige tareda kunna shower sbd kar fammah ta farka by mistake ta jiyota.

Cikin wani irin yanayi na tashin hankali JJ yace"

Baby gamunan munxo dauke mayor da 'yarta Saidai muna iso wannan Mr haydar din ya daukesu a gabanmu ya tafi dasu mun bisu har airport munga yasasu wani private jet sun gudu and the biggest surprise din shine da kansa yaje gidan tareda wani yaronso they scattered the hole place in blood.

Zaro ido tayi jikinta na mugun daukar rawa da qyar ta iya cewa"

Mubari gobe zamuyi mgn Amma you'll have to be very careful with him,this haydars is something else.

Fitowa bayin tayi tana daga qafa daqyar zuciyarta fal tunanin zaiyi amfani da hakan ne against dillas ko kuwa.

Kwantawa tayi Saidai Sam takasa bacci sbd tunanin abinda ke Shirin faruwa Saidai ga dukkan alamu taga koma meyene plans din haydars akan Dilla's to su zai amfanesu.


Washe gari da safe qarfe Tara ta sauko shirye cikin Armani pep lom top milk da royal blue free Palazzo trouser sai scarf dinta blue Mai touch din black zimbwe heels dinta dasuka qarawa adonta kyau.

Qamshi take fitarwa ahankali ta nufo sitting room din inda dukkaninsu ke zaune cikin damuwa da ciwon ran jiyan sbd yau da safen business deals biyu aka turo musu anyi canceling sbd abinda yafaru jiyan.

Gaidasu tayi dukkaninsu cikin fuskar jimami zuciyarta cike fal da farin cikin ganinsu cikin hakan.

Ko zama batayiba suka dunguma zuwa table cin breakfast.

Zama kowa yayi Babu Mai wata doguwar walwala sbd tun cikin Daren babu kudinda am Bai fitarba Dan Hana abin yaduwa Amma Sam Babu dama media tafi qarfinsu.


Suna cikin cin breakfast din Mai aikinsu Lauren ta iso cikin tsananin girmamawa tace"

Ma'am police are here to see you.

Dukkaninsu kallonta Sukayi tareda aje spoons din hannuwansu suna kallon kallo kafin suka taso dukkaninsu Suka fito.

Police ne motaci uku Babu rahama a fuskarsu.

Nadey na ganin hakan tayi saurin yiwa JJ text tace yacewa amed paaris Dan press yayi saurin tattaro Yan press suzo Dilla mansion.

Kallon zeel babban cikin police din yayi tareda daga Mata cuffs yace"

Ma'am we are here to arrest you for the suspect murderer of mayor ambryam Marshalls.

What?????

Dukkaninsu Suka fada cikin tsananin tashin hankali da mamaki.

Nadey kuwa itama mamakin ya kamata so this is Mr haydars plan kenan.??

Duk wani son tsayawa bayani police basuyiba sukai arresting din zeel tana kuka tana komai suka tafi da ita am da Dilla kuwa kamar zasu buga sbd tsabar tashin hankali da baqin ciki Basu Gama fita wancan ba yanzu sunshiga wannan wanda yafi wanacan Muni.


Ana fitowa da ita Yan press Suka fara kokuwar dauka suna jefo tambayoyinsu akan maganar zeel din dinda tayi jiya akan zata kashe mayor itace ta aikata.

Tashin hankali Jin hakan yasa zeel fara ihun kuka tana neman qwacewa daga police Amma Suka dannata mota Suka tafi da ita.
#MAMUH.
*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*


*_Mamuhgee33_*
Fammah dake hawayen baqin ciki ta riqo cikin tausayinta da sigar lallashinta tace"

Karki damu fammah Allah na tare dake.

Kallonta fammah tayi hawayenta na sake gudu cikin muryan kuka tace"

Meyake Shirin faruwa damune????tsakanin jiya zuwa yau komai na neman lalacewa,mun aikata wani Abu ne da muke ganin hakan?????

Girgiza Mata Kai nadey tayi tareda katseta da cewa"

Fammah kidaina fadan haka karki sabawa ubangijinki,
Wannan abin shi ake Kira da fitar haqqi.

Batareda ta wani fahimci maganar fammah dinba Suka dungumo cikin gida dama dad dinsu da am tuni suka dauki mota sukabi Police.

Cikin gidan ganin yanayin fammah yasa tadan nuna damuwarta akanta tana ta sake rarrashinta sbd tabbas fammah bazata iya handling abinda zai cigaba da zuwa ba musamman idan suka wayi gari sun koma zero account.


Acan police headquarter kuwa duk inda su am ke tunanin abin ya wuce nan sbd yanda yau waisu dillas ake qin saurara sai wani kwana kwana suke musu anmaqi Bari sugan zeel din tuni aka qargameta su saima anan suke ganin hotunan gidan mayor din da aka dauko jini ko Ina anyi kaca kaca da Kaya.

Abu kamar Wasa saigasu har kusan yamma anqi Bari suyi komai a kan case din gashi suna jiyo ihunta cikin tsananin azabar da ake Bata tafadi inda gawar mayor da 'yarta suke.

Jin bazasu iya daurewaba yasa Suka tattaro Suka dawo gida jiki amatuqar mace zuciya na matuqar daci.

Koda Suka dawo gidan fammah na ganinsu tasake fashewa da kuka sbd ganin Basu dawo da mum dinba dakuma yanayinsu dake nuna Babu wani sauqi.

Ranarma a Daren Babu Wanda yayi dinner sai nadey dataje kicin ta zauna akan kitchen island taci pancakes dinta da Apple ta koshi Tasha fresh milk da ruwa kadan Takoma sama daki ta tube tayi wanka da ruwan zafi sosai ta gasa jikinta tafito ta shirya cikin sleeping dress fara Mai Dan kauri ta daure kanta da band tazo ta kwanta gefen fammah da baccin wahala ya dauketa tun dazu.


Washe gari tunda safe dukkaninsu suka sake komawa headquarter wannan karon anbarsu su ganta aka kaisu dakinda zasu ganta Suka zazzauna jiran akawota.

Lokacinda aka shigo musu da ita dukkaninsu Saida Suka miqe tsaye cikin tsananin tashin hankali sbd irin mugun dukan dake jikinta gabaki daya ta sauya kamanni idonta daya ko gani bayayi ya rufe gabaki daya sbd kumburin jini hakama gefen bakinta ya kumbura harya juye gefe.

Daqyar take daga qafa tana ganinsu da idonta daya dake gani tafara wani irin kukan tashin hankali tana cewa su ceceta karsu barta cikin wannan halin.

Dukkaninsu jiinsu rawa yakeyi sbd tashin hankali,
Ita kanta nadey din Saida taji wani iri sbd yanayinda zeel din Takoma a kwana daya da yini.

Ko mintuna goma batayiba suka jata tana ihu tana Shure Shure Suka mayar da ita.

Hakan ya sake daga hankalin dillas musamman da anqi bayarda bail dinta kafin shiga court gashi kamar wani hadin baki ko Wainda aka saka azaba suke gana Mata akan ta fada inda gawar su mayor take.


Cikin kwana biyar gidan Babu Mai iya ko Shan ruwan kirku sunkoma kamar gidan mutuwa ko yaushe kowa na palonsa gashi mahaukatan kudi suke saki Amma Sam Babu wani alamar sauqi saisuka fara sakaran case din da saka hannun wasu manyan dasuka fisu sbd duk wata hanyar sauqi an toshe musu gashi Court za'a fara shiga washe gari.


Da daddare yunwa tasa fammah sulalewa ta fice daga gidan cikin motar fammah ta nufi gida tana waya da JJ akan fa haydar ya tsananta wannan alamarin sbd dillas anwayi gari ko abinci rabonda waninsu yaci anmanta Saidai ruwa.

Tana Isa gidan ta tararda Babu kowa daga mum har Annah basa nan tanada key harzatayi amfani dashi ta bude sai kawai ta fasa ta juya kota shiga bazataji dadin ci ita kadaiba batama da tabbacin ko akwai sunyi.

Wani restaurant ta nufa batareda tashigaba tana cikin mota ta bayarda order dinta ta cikin waya tana jiran su kawo mata.

Wayarta take amfani da ita tana turawa dad dinta saqon wasu files data sa akayo Mata forwarding daga Noah's tanason yasake duba matasu dakyau.

Dan dagowa tayi sai kawai ta hangosa tafe tayi saurin lafewa cikin motar batareda ya lurada itaba ya bude motarsa dake kusada tashi ya fada yabar gurin Bata tsaya komaiba ta buga tata tabisa sbd id card dinta datakeson karba.

Ahankali ya lurada motar na binsa sai yaqara dubawa yaga tabbas motar fammah ce yaja wani siririn tsaki tareda parkawa Yana fitowa itama tana kawowa saura kadan su hadu da juna tayi saurin yin baya daidai wata mota takawo aguje kan titin yayi saurin fizgota ta fado jikinsa ya Mata kyakkyawar runguma akaro na farko jikinsu ya hadu sosai.

Rawa jikinta yafara numfashinta na fita da mugun sauri jin jikinsa anata yasa hankalinta yasake tashi tafara girgiza kanta da qarfi tana cewa"

No no no ba jikinsa bane,
Wannan jikin ba nawa bane yanayin sukeyi,,,,no no I'm only imagining ne....
Qwacewa tayi da qarfi hawaye na ballewa daga idanuwanta sbd zuciyarta dake neman rudata dajin jikinsa kamar na zakinta,
Meyasa takejin kamar jikin zakintane komai da komai.


Juyawa tayi da gudu hawayenta na tsananta tafada mota da mugun gudu Wanda ya daga hankalinsa sbd yanayin yanda taja motar komai zai iya faruwa.

Bin bayanta yakeyi da gudun shima Saidai kasancewar ta roughrider ce sbd a college suna zuwa wasan race da motoci Wanda Annah ce keda son hakan sai itama abin yashigeta.

Tana zuwa gidan ta shige da motar da wani speed tayi parking ta wuce ciki da gudu har lokacin kuka takeyi.

Wani irin numfashi Mai zafi yasaki zuciyarsa na wani irin radadin zafi,
Ako wace safiya yatashi da ciwon zuciyar rashinta yake tashi dashi yake rayuwa,

Tsawon shekarun nan baitaba farin ciki Kona seconds neba sbd rashinta ataredashi Saidai dolene ya boyewa kowa kansa sbd samun zamansu safe har yagama Dora kowa a matsayin daya kamata.

Jan motar yayi da gudu shima ya wuce Yana Jin nauyin zuciyarsa yau Yana qaruwa.

Ya gaji Dole yagama komai cikin qanqanin lokaci yana buqatarta akusa dashi.



Ita kuwa kukan Rashin zakinta tayi sosai acikin Daren kafin tayo alwala tazo tayi sallar nafila tafara jero masa addua shida mahaifiyarta da ummansa.

Yau har wata sabuwar kewar babanta ta taso Mata
Tsananin qaunar ganinsa ta taso Mata takasa hkr ahankali ta lalubo wayarta ta Danna Kiran Dr sayyid.

Yana dauka ta tasaki ajiyar zuciya ahankali tace"

Babana Dr Ina yawan tunaninsa cikin kwanakin nan I hope canjin damuke buqata ansamesa I can't continue hiding Ina son ganinsa wlh.

Ki kwantarda hankalinki nadey babanki ansamu cigaban da akeso sbd yanxu yafara Sanaa Kuma ba laifi Naga ta karbesa sosai kayan fruits yake siyarwa ammafa wani lokacin shike zama yasha kayansa saiya qoshi.


Murmushin Dole ne ya subuce Mata Jin halin baban dai yana nan kawai dai qila kwantawa yayi sbd yanayin rayuwa.

Cikin Jin dadin babanta nanan da halinsa na ban dariya da takaici tace"

To Dr inaga tunda yasan amfani Sanaa yanxu zaka iya bashi kudinda kace Yaya Zaki yabaka.

Kinaga lokaci yayi kuwa?

Eh kabasu kawai aisun wahala ba laifi zasu tanada yanxu nasani.

Ok to insha Allah zanje nakai masa.

Harzai kashe murya cikin tsananin sanyi tace"

Dr idan zaka bashi ka dauko min fuskarsa inason ganin farin cikinsa Dan Allah.

Murmushi yayi yace""

Insha Allah.

Tana kashe wayar ta share hawayen tausayin babanta da iya kafin ta miqe ta kwanta a darare sbd gobe sunada zuwa court.


Washe gari dukkaninsu da sanyin jiki Suka tashi har itama din Saidai ita nata daban ne.

A mota daya suka isa court din am ne ke tuqi sai dad da fammah a baya ita agaba cikin wata baqar jeeb Mai daukan ido.

Motarsu na tsayawa Yan media Suka zagayesu ko gurin fitowa Babu Saida securities sukazo suna tutture musu su suka samu fitowa ana karesu Suka samu shiga Court din.

Zamansu bada jimawa ba haydar ya iso kotun tareda securities dinsa biyu ya qaraso gurinsu ya miqawa dad din hannu Yana jajanta masa hakama am fammah kuwa narke masa tayi yadan saki fuska kadan Yana cemata karta damu komai zai daidaita kowa zaisamu abinda yayi deserving.

Satar kallonsa tayi Suka hada ido da ya zuba Mata idanuwansa take tafara kame kame tana hadiye yawu daqyar.

Ahankali ya mayarda idanuwansa kan 'dan space dindake tsakaninta da am wanda dashi gwara Babu.

Ya dauke kai Yana murmushin dashi kadai yasan mezaiyi.

Shigowa akayi da zeel data sauya kamanni gabaki daya cikin sati guda nan aka fara shariar Saidai Sam Babu haske ga dillas saima qara zurfafa zancen keyi ana bankado wasu asiransu Wanda yafara Basu tsoro da mamakin ya akai suke fitowa.

Ranar haka aka tashi court din Babu wani sauqi Suka nufo gida.

Kamar Wasa saiga shariar na tsawo ankasa samun wani taqamaimai dogon sanin inda zeel takai gawarsu meyo gashi dukkanin evidence suna nuna itace tayi kisar nan kotu kawai ta yanke hukuncin arufeta gidan yari tsawon shekarunda zata fadi Ina gawarsu take.

Ihu zeel keyi tana kuka tana Kiran dikko da am su taimaketa karsu Bari akaita prison wlh Bata kashesu mayor ba ita batama San gidantaba haka aka tafi da ita tana kuka tana riqe fammah dake kukan itama kamar ranta zai fita.

Am ma da dad din hawayene kawai basuyiba Amma dukkanin hankalinsu ya tashi idanuwansu duk sun Kade zuwa jajir ga uwar dukiyar dasuka zubar a wannan case din.

Nadey ce riqeta fammah harsuka nufo hanyar gida saigashi aka Kira daga office Kiran gaggawa.

Office din suka wuce gabaki dayansu inda suka tararda wani babban tashin hankalin Yan press ne cikeda gurin suna isowa sukayo gurinsu suna musu tambayoyi Wanda tambayar daya daga cikin Yan media din yake cewa"

Ance kun siyarda gabaki daya shares dinku na Dilla empire da kamfanin gabaki daya harda gidan dakuke ciki yanzu ga Wainda suka siya nan sunzo zasu karbe shin mezaku ce gameda hakan??????

Cak dukkaninsu Suka tsaya cikin mamaki da takaicin Jin abinda ake cewar,
A fusace am ya turesa tareda marinsa Yana cewa"

What rubbish.....

Hakan da yayi yasa Yan media harzuqa Suka ringa daukar abin suna qarfafa yadawa har marinda yayiwa Dan press din.

Basu yardaba Saida Suka Kai cikin building din Suka tararda lauyoyi da ma'aikatansu cirko cirko ga hukumar qasar cike suma ana jiran isowarsu.


Takarda lauya ya daga ya miqawa Dilla Yana cewa"

Ga takardar dake nuni da client Dina ya siya dukkanin shares dinku ga saka hannunku nan ga nasa ga namu lauyoyinsa na shedu ga Kuma stamp na Court so munxo karban ragamar kamfanin ne da komai.

Ko gama karantawa Dilla baiyiba ya baya zai zube am yayi saurin riqosa tareda fixge takardar ya karanta yayi wurgi da ita Yana cewa"

Qaryane Babu Wanda muka siyarwa komai mundaiyi investing kuma......

Katsesa dayan lawyern yayi da cewa"

Ba haka bane Mr am Dilla inaga tun farko idonka ya rufe baka karanta waincan takardunba dakayu Amma hakan shiyake a rubuce.

Kallon lawyern yayi tareda kallon takardar da sauri ya tuno ranarda ya karbo takardun zasuyi signing zai karanta nadey dinsa tashigo tace saiyazo sun fita da sauri yanda ta matsa masa tadau hankalinsa yasa Bai tsaya karantawaba yayi signing Yana fitowa yabawa dad shima yayi ya fita dasu daga gurin shaqatawarsu yaje yakai takardun kotu aka saka shedar kotu.

Dafe kansa yayi tareda durqushewa qasa Yana neman haukacewa...

Miqewa yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login