Showing 42001 words to 45000 words out of 81157 words

Chapter 15 - BURI DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

08 Apr 2025

6623

dake daukar idon mutane sbd stones da Kuma kyawunta dake kashe musu ido.


Washe gari da qyar ta bude manyan idanuwanta dasukai laushi sbd bacci ta lalubo alarm dinda ke gefen gadonta Yana kuka ta kashe tana sake komawa cikin bargon.

Qarar wayarta yasata Jan qaramin tsaki tareda lalubo wayar ta dauka batareda ta duba ba tace"

Yes please.

Cikin yanayi na farin ciki JJ yace"

Nadey come downstairs now,you need to see this.

Bude idanuwanta tayi da sauri tana cewa"

Am coming.

Saukowa gadon tayi tareda zura bedroom slippers dinta na gashi masu tsananin laushi ta fito tana Kama gashinta bayan ta saka jacket saman kayan baccinta.

Palon ta qarasa saukowa tana kallon tvn dasuke kallo
Take zuciyarta tayi wani irin nauyi ta tsaya tana kallon yanda aketa baza labarai da sunanta ana nunota Saidai sunason ganin ainihin dad dinta Wanda bai taba Bari Yan press sunyi fira dashiba ko daukar hotunansa.

Karbar coffee dinda nanny Nancy takawo musu tayi tafara kurba tana kallon tvn yanda zancen ya baza duniya Yana sanyata nishadi sbd irin zallar dukiyarsu da ake fada tasan duk inda dillas suke yanxu ido rufe nemanta zasu fara Dan hada business da ita Wanda shine first target dama.

Murmushi tayi batareda ta dauke idonta daga tv ba tace"

Am Dilla I'm coming for you.

Aje cup din tayi tareda kallon JJ tana miqewa tace"

Bari naje Naga dad inason magana dashi.

Sun Jima sosai suna magana akan proposals dasuka samu da dama tsakanin jiya zuwa safiyar yau din Wanda Dole JJ ne zaiyi handling rabi ita zataji da sauran sbd dad din kwana biyu Yana fama da Dan nauyin jikin manyanci.

Cikin wata black BMW ta iso Noah's cikin wasu maroon pensil suit na Mata dasuka matuqar fiddo shape dinta sai wasu shegun heels black da black mk bag dinta tashigo companin tana waya da best friend dinta Annah Lauren.

Dukkanin ma'aikatan tasowa sukeyi suna Mata barka da zuwa su pa dinta da wasu ma'aikatan na biyeda ita har bakin office dinta inda aka rubuta CEO PA dinta ta bude Mata tashige.

Aiki tayi sosai tareda meeting harso biyu sbd yawan aikinma yasa sai dare tasamu damar dawowa gida lookacin baby zee tayi bacci Saidai kawai tayi wanka tasha fruits ta kwanta sbd batacin Abu Mai nauyi da daddare.

Washe gari ma a office ta wuni kusan yamma Annah tazo ta dauketa sukaje wani spa dagacan sai dare Suka dawo gida.

Ayyuka sunmata yawa sosai shiyasa gabaki daya she's busy ko lokacin zuwa yawon shaqatawa dasuke da Annah ta rage samu sosai.

Yauma JJ ne yaje ya daukota suka dawo gida.

Babban abinda yafara tunkarosu batareda sun samu proposal daga Dilla empire ba shine bullowar wani kamfani daya dame nasu akan dukiya da suna Wanda a iya bincikenta kamfanin duka duka baifi shekara uku da fitowa ba Amma Yana neman take nasu dayayi shekaru masu yawa.

Tension yayi Mata yawa sosai musamman safiyar yau dataga jaridar wani sati kamfanin zasuyi bikin bude kamfaninsu dake South Africa.

Sake kallon jaridar tayi ta miqawa JJ tareda miqewa tana zuwa bakin glass wall din dake office din Bata tana kallon qasan harabar kamfanin cikin tsananin damuwa tace"

Idan muka rasa wainnan proposals din rugujewa zamuyi sbd dukkanin ribar shekaru muka zuba a wannan karon sbd kawai mukira attention din dillas da yawan proposals namu Amma out of no where wannan kamfanin yazo yasha gabanmu
who the hell is this *_HAYDAR'S BUILDINGS LMT_* ????

dafe goshinta tayi tana jinjina irin hasarar dazasuyi idan Basu samu open contract proposal ba Mai tsananin tsoka.

Qarasawo bayanta JJ yayi ya tsaya tareda zuba hannuwansa cikin wandon ash suit dinda ke jikinsa cikin taushin muryar lallashi yace"

Heyy don't stress your self akan Dan wannan issue din, we'll find a way bazamu taba Bari wannan company ya rusheba okk??? So please just calm down kinji?

Kallonsa tayi tareda Dan daga masa Kai batareda damuwar tasaketaba.

Kallonsa tayi tareda nufar kujerarta ta zauna tana rufe apple laptop dindake kunne gefen flatscreem APPL desktop din office din tana cewa"

Dole zanbi flight din chicago gobe Ina buqatar ganawa da wannan haydars buildings din Bari ma naje nafadawa dad akwai wani conference meeting dazanyi da wani sabon company dasuma haydars din zasuyi meeting dasu inason mu hade acan ina buqatar magana da CEO na wannan haydars buildings din kota yayane.
#MAMUH.
*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

*_Mamuhgee28_*

*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

*_Mamuhgee28_*
Zama tayi gaban mirror din bedroom dinta tareda qurawa fuskarta ido ta cikin mudubin Bata ko qyaftawa tsawon lokaci kafin ta lumshe idanuwanta hawayen ciki Suka gangaro Mata ahankali tasaki wani silent kuka tareda rintse ido.

Shekaru sunja da rasuwarsa Saidai har yau takasa raba kanta da kukan rabuwarsu kowane dare idan zata kwanta,

Shine farin cikinta,
Shine burinta,
Shine walwalarta,
Shine kadai zuciyarta ke bugawa kowace daqiqa da sonsa,
Har abada zuciyarta bazata taba son wani bayan Shiba,
Uban 'yarta Wanda shine sirrinta ciki da Bai dinta,

Meyasa Suka rabata dashi adaidai gabarda sonsa yagama shigewa gaban rayuwarta,
Meyasa Suka rabata dashi Suka maidata marainiyar bazawara itada 'yarta,
Sun rabata dashi,sun rabata da zainab  sun rabata da iyayenta tsawon shekaru,
Tanason ganin mahaifinta da mariqiyarta,
Tanason sanin wane halin suke ciki saidai bayyanarta hadarine ga rayuwarsu duk sbd suna 'daya _DILLAS_ .

Share hawayenta tayi ahankali tareda miqewa tsaye tana sake goge fuskarta ta nufi wayarta ta dauka Kai tsaye ta dannawa p.s dinta Kira tana dauka Kai tsaye cikin bada umarni tace"

I need two chicagos flight tickets by tomorrow.

Yes ma'am."""Jasmin din tafada cikeda girmamawa tareda kashe wayar take ta dauki iPad dinta tafara booking tickets din.

Closet din kayanta ta nufa ta bude tareda kallon inda kayan baccinta ke jere Babu kalar da Babu ta jawo wata white sleeping snowgown tasaka Mai tsananin laushi da 'dan tsawo zuwa cinyoyinta ta daure gashinta da band ta nufi mirror ta fesa calmScentsy jaguar miss tareda shafa body oil Mai qamshi ta nufi gadonta tana Shirin Hawa nanny Nancy tashigo Mata da Black coffee ta karba tana murna tace"

I love you nanny.
Zama tayi tana sake tambayar baby zee da Bata samun kulawarta sosai kamar da sbd wannan masifar ta loss datake ganin ta tunkarosu.

Fira sukeyi da nannyn sama sama tana aiki a laptop dinta tana sipping coffee din
Nanny ganin hankalinta baya gunta yasa tayi Mata Saida safe ta fice.

Hankalinta sosai taji yafara tashi da wainnan haydars buildings din sbd bincike takeyi sosai akansu Amma takasa ganin ainihin waye Mai kampanin sbd Sam Babu hotunansa a yanar gixon,
Abinda yafara daga Mata hankali da Bata tsoro shine money and power dinsu zasu iya rushe Noah's cikin lokaci qanqani.

Sake tsananta bincikenta tayi akansu Amma Bata samu abinda takesoba harzata kashe wani update na news ya sauka tayi saurin budewa ganin sunan Dilla's aciki.

_DILLAS EMPIRE TO PARTNERSHIP WITH THE HAYDARS BUILDINGS_

what"""tafada da Dan qarfi cikin tsananin tashin hankali da damuwa ta lalubo wayarta da sauri tana neman numbern JJ saiga kiransa yashigo tayi saurin dauka cikin nutsuwar lallashinta yarigata magana""

Hey hey baby relax.,
Relax okay????
Nariga Naga news din yanxunan aka sakesa acikin Daren nan,
Karki daga hankalinki please baby.

Cikin son danne damuwarta tace"

I don't know how to handle this situation, things are getting out of hands,
Da zaran wannan haydars buildings din sunyi amince da proposal din Dilla's shikenan bazan samu yanda nakesoba,
Alqawarin danayiwa dad bazai tashi a banzaba dady j we have to come up with another plan.
Plan B kenan.

Aje remote dinda ke hannunsa tayi tareda zama kan couch Yana daukan coffee dinda aka kawo masa harya fara hucewa yace"

Baby bazan taba Bari ki shiga familyn dillas ba karkima kawo wancan mgnar.

I have to,
Idan har munason cimma matsaya Dole zamubi wannan I promise you Babu abinda zai sameni.

Kashe wayarta tayi da sauri tareda kashewa gabaki daya bayan ta karanta saqon email din Jasmin flight dinsu gobe qarfe Tara na safe.

Washe gari tana tashi tafadawa nanny tafiya zatayi nan akahau shirya Mata Kaya cikin luggages dinta ita Kuma tana gurin baby zee yau itace takeyi Mata Shirin school da kanta.

Sama Suka hau gurin dad
Da gudu baby zee tayi gurinsa ta haye jikinsa tareda masa peck a kumatu tana cewa"

Gud morning grandpapa?

Hannu yabata Yana cewa"

Gud morning Miss zaynab Noah.

Kama hannunsa tayi tana cewa"

I love you grandpapa.

I love you too my sweet sweet miss Noah.

Murmushi nadey tayi tana qarasowa tace"

Sabaa'ul khaiir dad.

Kallonta yayi Yana amsawa yace"

Yau kece kika shirya miss zee kenan.

Yes Dad Nima yau zantafi Chicago zamu hadu da wasu companies din ne zan duba proposal nasu akanmu saikuma Ina son shigarda tamu proposal din a haydars buildings with 62% interest.

Jaridarsa ya dauka Yana karantawa yace"

Idan har dillas nada open proposal akansu zaiyi wuya su karbi tamu Saidai ki gwada kodan sbd High rate interest dinsu.

Breakfast Sukayi a babban dining room dinsu su uku Sukayi sbd JJ na territory acan ya kwana jiyan sbd wani urgent aikin dasukai.

Har mota takai baby zee tayi Mata kiss tana cewa"

I love you take care Mamma's princess.

I love you too mummy.

Bayan fitar motarsu baby zee din dawowa tayi ta nufi bedroom dinta ta tube Kai tsaye ta shige toilet tashiga cikin ruwan dumin data Tara harsun fara hucewa ta kwanta tareda rufe ido.

Saidatayi relaxing tsawon mintuna ashirin kafin tafara wanka da royal Allie shower cream dinta da qamshinsa yacika toilet din tsawon mintuna goma Sha biyar kafin tagama ta fito daureda brown towel sau dan qarami daure a kanta.

Gaban mirror taje ta zame na kanta tafara goge jiki dashi kafin ta zauna tafara shafa Neutrogena pure laylns oil ajikinta dake fidda wani sirrin qamshin fresh Roselle Flower.

Bata cika wani make up ba Sam arayuwarta Saidai lips dinta dasukam akoyaushe 'dam sukeda hot daity brown mclipstick dake daukar hankalin mutane akanta.

Dogon Palazzo trouser tasa black Wanda saita tafiya zaka gane wando ne ba skirt ba sbd budewarsa.,

White brown free Prada top Mai yankakken hannu sai wasu heels a qafarta masu tsawo da wandonta ya rufe tsinin kawai kake gani sai wata scarf Mai stones datayiwa daurin gefe a kanta aka fito da luggages dinta tafito riqeda handbag dinta taje gurin dad Sukayi bankwana da kansa ya rakota har mota inda Jasmin da PA dinta daya suke jiranta tana shiga Suka nufi airport.

*****
Ahankali yashigo gidan Yana gyara babbar rigarsa zuciyarsa cike fal da bacin Rai da damuwa Yana masifa qasa qasa sbd yanxu ko dogon qarfin tashin hankali baidashi musamman qananan Yan iska dasuka cika anguwar yanxu.

Iya talatu dake zubawa aminatu sabuwar 'yar riqonta ruwa a geron datake wankewa ya kalla ya nufi tabarmar dake shimfide tsakar gidan ya zauna yana cewa"

Saidai hakuri talatu wlh shegun yaran nan sunyi qarmanje akan akuyar nan shima shegen Dan sandan da zanzaronsa me kamada talalar raqumi kamar zakaranda aka sawa wando yayi mirsisi yabi bayansu Ina gani Suka masa dubu daya.

Ajiyar zuciya iya talatun tayi tareda kallon matar dahiru dasuka dawo gidan data fito daki tace"

Zara'u Kama Mata wankin geron nan karta zubarda rabi a qasa.

Gurin dattiyan Takoma ta zauna kan kujerar zama tareda sake sauke wata ajiyar zuciyar cikeda damuwa tace"

Yanxu ko dabbobin gidan nan sunsan basuda gata sbd maraicin Rashin Zaki,

Duk tattalin arzikina na kaji da akuyoyina sun qare sbd sace sacen nan da akeyi haka kawai waiinan yayan banxar ke zuwa cikin anguwa suna damqewa mutane dabbobi suna sacewa bakada ikon mgn sbd mutuwar zuciyarda yansanda keda ita wani lokacin,

Kowa kukan rasuwar Zaki yakeyi anguwa da zagayenta sbd takai har 'yayan mutane suke matsewa yanxu ko ikon Aiken yaro da mangariba
Yanxu gashi shima dahiru kaduba kaga har cikin gidan nan fa aka shigo aka sace masa Dan babur dinsa.

Shidai dattiya shiru yayi Bai iya cewa komaiba sbd dama tuni hakan yafara zama dabiarsa tun rasuwar Zaki da batan Nadiya yakan zauna yayi shiru Yana tunani sbd duniya a rayuwarsa Babu abinda yake qauna kamar ruqayya tazo ta rasu tabarsa shikadai baida wani jininsa dazai kirada Dan uwansa sai 'danta data Bari,

Yana qaunar Zaki fiyeda ruqayyar Saidai halinsu ne baya jituwa da juna shiyasa Babu wani ragi tsakaninsu,

Sai nadiyarsa da allah ya fifita masa soyayyarta fiyeda sauran yayansa saigashi itama yau Babu ta,

Zainab da har yau itama yakasa cire rasuwarta a ransa sbd irin zalincin da akayi musu Kuma sunaji suna gani basuda ikon fadar yanda akayi sbd tsira da rayuwarsu da mutuncinsu,

Banda talatu da mal idi Suka tashi tsaye akansa da tuni ya zauce yafara tsince tsince lokacinda ya bude ido yaga gawar yarsa daya agabansa 'dayar Kuma suntafi da ita duk da Yana sawa ransa itama sun kasheta  Allah dai ya taqaita abin nan.

Sam yanxu Bai cika yawon maularsa ba sbd tafiya yaje Yana tunane tunane musamman idan sukaje aka wulaqanto su saiyaji jikinsa yaqara sanyi sbd Zaki dake wulaqanta duk Wanda ya wulaqantasa.

Hakan yasa sha'awar sana'a ta 'dan shigesa saiya yanke shawara shida mal idi suka fara sana'ar Saida lemu da ayaba shikuma mal idi doya Amma rumfarsu daya a layin Yan kayan marmari dake jikin babban roundabout ta babbar kasuwa.

Ganin yanayinsa yasa iya talatu Jin jikinta yaqara sanyi ahankali tace"

Allah ya mayar Mana da alheri yanxu shikenan Babu dabba ko daya a gidan nan dama wannan akuyar itace ta qarshe data rage duk sun sace.

Ganin har lokacin baisan metake fadaba cikin Dan daga murya takira sunansa.

Ya Dan motsa tareda dawowa hayyacinsa daidai shigowar abdulhakim 'dan dahiru Dan kimanin shekaru biyar Yana garo Taya baima wani iyaba
Ya qura masa ido wani irin rauni na ziyartar zuciyarsa da yanzu 'dan Zaki da nadiyarsa yakai shekarun Abdul inama ace kafin duk su rasu ko 'yaya sunbar masa Yana ganinsu.

Cikin dan daga murya da damuwa tace"

Dan allah nidai wannan tunanin ka ragesa kar wani ciwon ya kamata bansan ya zanyi da wannan rayuwarba idan wani abin ya sameka,
Ka rungumi qaddarar data samemu to meye amfanin tunanin.

Baice komaiba ya jinjina Mata Kai tareda miqewa ya dauki buta sbd Kiran magriba da ake qoqarin farawa.


*****
_CHICAGO_
Daga airport Annah ce tazo ta dauketa  itada ps dinta Jasmin.

Tun a hanya Suka fara maganar abinda yakawota Chicagon itada Annah inda Annah ke sake Bata informations akan abinda tasani gameda haydars buildings Saidai cikin wani irin yanayi annah tace"

Girl do you really think you can handle this haydars?

Batareda nadey takalletaba ta fitarda numfashi Mai qarfi tareda bude wayarta tana kallon wani kyakkyawan hoton AM DILLA cikin ranta tana cewa"

I'm not here for you am Dilla.

Suna isa mum din Annah da kanta ta fito Suka rungume juna da tana Mata sannu da zuwa tareda tambayarta Mr A Noah.

Direct dakin Annah aka Kai Mata luggages dinta Jasmin kuwa guest room aka kaita.

Wanka tayi tayi tayi sallah tayi relaxing a sofa tsawon mintuna talatin kafin ta fito sukai lunch a table dukansu.

Qarfe biyar na yamma tasake wanka ta shirya cikin wata Italiano gown Mai shape sosai da budadden wuya blue color sai wadges aelexendra shoes tafito tana tana fidda qamshin Barbie royalle da posses.

Kallonta Annah tayi tareda kallon lips dinta dasukaji daity Brown lipstick Wanda baida wani kala sosai ahankali tace"

You gatta be kidding me baby... I mean like seriously are you going for business or something else?????

Wani shu'umin murmushi nadey tayi tareda daukar handbag dinta tafito tana cewa"

See you.

Dan hugging mum din Annah tayi a Palo kafin suka fice itada Jasmin.

Ahankali ta zuro qafafuwanta daga cikin motar tana qurawa sunan kamfanin dake rubuce baro baro a saman building din Mai kusan Hawa biyar.

Drivern mum na ajesu komawa yayi Suka nufi cikin building din Jasmin na bayanta securities kuwa sai sannu da zuwa suke Mata sbd itama ba laifi kusan ansata a labarai da jaridu da televisions the queen of Noah empire ltd.

A reception ta tsaya gaban baturiyar dake gurin tana Mata barka da zuwa ta shigarda proposal nason ganin Mr haydars.

Cikin sakin fuska da 'yar damuwa tace"

I'm really sorry ma'am I can't give inn ur proposal, sir is going out of the country may be next time ma'am.

Thank you""tafada tareda tareda juyowa zata wuce sukai karo da wata kyakkyawar yarinya data fito daga wani office ranta amatuqar bace.

Baya Sukayi dukkaninsu kowacce na kallon daya daga sama zuwa qasa.

Sake kallonta nadey tayi da kyau akaro na uku ta dauke gira daya sbd sake tabbatarda _FAMMAH DILLA_ ce....

Wani boyayyan murmushi tasaki tana sake qarewa kyakkyawar fammah din kallo wadda dagani zasuyi shekaru daidai da wayewa daidai Saidai dukiya da kowa ke taqama da tasa
Cikin sauqi tasamu hanyar shiga Dilla's.

Dan gyara kanta tayi tareda Dan yamutsa fuska tana gyara rigarta tareda kallon fammah din cikin wata irin yanga zatayi mgn fammah din da nadey tagama burgeta musamman sanin ko ita din wacece sbd tana ganinta a media dakuma irin matsayinda take Kai da qananun shekarunta da Basu wuce shekarunta,

Nd Noah ta burgeta tako Ina dama da irinsu kawai yakamata ta riqa abota duk da ganinta kamfanin yasamata Jin kishinta kadan akan haydar dinta dataga mutuwa a sonsa Wanda zata iya komai akansa Saidai Kuma bataga alamar soyayyace takawo miss Noah dinba saidaima business.

Fuska tasaki sosai tareda miqawa nadiyar hannu cikin yanga itama tace"

Fammah Dilla.

Ba musu nadey ta miqa Mata hannu tareda sakin murmushinda ita kadai tasan ma'anarsa tace"

Nd Noah,CEO Noah empire.

Cikin Jin dadi fammah tace"

Wow nice to meet you miss Noah.

Zatayi magana aka Kira wayar fammah din ta daga wayar tareda kallon nadey cikin sakin fuska tace"

Sorry I gotta go.,
Zaro wani kyakkyawan Kati tayi ta miqawa nadey din tana cewa"

It's my opening party today 9pm I hope to see you there.

Karba nadey tayi tareda kallon Katin cikin murmushi tace,

Yes sure miss Dilla.

Juyawa tayi ta wuce tana kallon Katin sbd yau tasan zata hadu da duka dillas,,,,AM DILLA am coming for you.
#MAMUH.
*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

*_Mamuhgee29_*
Tana Isa gida Kaya kawai ta sauya zuwa wata half mini gown ta daure gashinta tareda amfani da wiper ta goge fuskarta da cleanser Mai sanyi ta kwanta Dan tayi relaxing jikin sbd fatarta tasake saki.

Kiran dad tayi tana daga kwancen Suka Jima suna waya kafin Suka gama takira nanny Nancy Suka dinga fira da baby zee da nannyn Saida Kiran JJ yashigo wayarta tasaki murmushin Jin dadin ganin number sa tayi sallama dasu nanny ta datse kiransu ta dauki nasa tana cewa"

Karkayi fada daddy j nakiraka kafin natafi but I couldn't reach you I'm sorry.

Ajiyar zuciya yasaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login