Showing 27001 words to 30000 words out of 81157 words

Chapter 10 - BURI DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

08 Apr 2025

6630

dakin zainab ta gudu.

Gashinta daya tarar zainab na gyara Mata ya kalla yaga yanda yakeda tsawo andaure Mata da band gashi sosai tayi wani irin haske na alamar tana jinya ya sake kallon dogon wuyanta zuwa qirjinta dake sama Yana qasa sbd numfashinta.

Dauke Kai ganin tanata wani mutsu nutsu alamar wani Abu ya gyara tsayuwa tareda zuba hannuwansa a aljihun wandonsa fuska ba sakewa yace"

Kinyi sallah???

Girgiza Kai tayi tana sunkuyar dakai.

Ya Dade shiru cikin takaicin zainab data tafi batareda ta tsaya yin abinda yakamata dinba gashi yanzu baisan uwarda zai musu ba.

Ganinsa kawai tayi a gabanta tayi saurin dagowa idanuwansu suka shiga na juna tayi saurin sunke idanuwanta tana matse hannuwanta.

Hannu ya miqa Mata batareda ya kalletaba Yana sake tamke fuskarsa.

Kallon hannun nasa tayi tareda dagowa da sauri ta kallesa taga ba alamar sauqi daga fuskarsa take taji jikinta na rawa sbd duk lokacinda jikinsu ya hadu jitake jikinta na vibration.

Ahankali ta dago hannunta Yana rawa ta Dora a nasan kusan atare Suka rintse idanuwansu Dan abinda yakeji idan jikinsu ya hadu kusan yafi wanda takejin.

Ahankali ta miqe Suka nufi toilet din dakin Yana riqeda ita tana dingisawa ahankali sbd qafar.

Suna kaiwa bakin qofar toilet din Suka tsaya shi ya sauke Kai Yana sake daure fuska ita Kuma tayi qasa dakai Dan kuwa zainab ce ke taimaka Mata gurin alwalar.

Daddafawa tayi tashiga bayin tareda turo qofa ahankali tana rintse ido.

Daqyar da dubara tayo alwalar Saidai duk ta jiqa bandage din qafar tana juyowa wani mugun santsi ya kwasheta ta bugu da madubin gurin atake ta zube agurin goshinta na fitarda jini.


Shiru shiru Bata fitoba tun Yana basarwa harya maida hankali kan qofar yaji yadainajin motsin ruwa daga ciki.

Yana zaunen zainab tashigo kusan tareda nurse da Dr sayyid dasuka Saba sosai dashi.

Atare Suka kallesa Dr na cewa"

Sarki Ina patient Dina ne bangantaba??

Zainab yayiwa wani kallo yace"

Jeki ciki ki dubota.

Toilet din ta nufa ta bude Kai tsaye zata rufo qofar ta hangota some tsakiyar bayin wani razanannen ihu tasaki tareda qarasawa da sauri tana kiran sunanta.

Da gudu Dr sayyid da nurse sukayo bayin cikin tashin hankali suna tambayar meye.

Ganinta kwance zainab nason dagota takasa yasa arikice Dr sayyid ya qaraso Yana cewa su matsa ya Kai hannuwa zai daukota yaji anriqe hannunsa riqewa irin wadda yasan ya riqu.

Da sauri ya dago abinda yagani a idon zakin yasashi matsawa gefe batareda ya furta ko kalma dayaba.

Hannu biyu zakin yasa ya daukota cak ya fito bayin da ita Suka biyosa zainab na Dan fidda sautin kuka ahankali sbd ganin yanayin zakin tasan Idan tayi hauka itace za'a bawa gado a dakin kusa dana nadiyar.

Cikin fada Dr ke dubata Yana cewa meyasa zasu barta tashiga toilet din ita kadai.

Fitowa yasa sukayi kafin yayi Mata dressing goshinta tareda Mata wasu allurorin Yana saka Mata wasu allurai a ruwa ta bude idanuwanta ahankali hawayen azaba suka gangaro Mata.

Sannu"Dr sayyid yace Mata cikeda tausayinta shidai Allah yasani yanajinta cikin zuciyarsa Kuma sosai ya lurada tana fama da maraici arayuwarta sbd Sam yanda Bata iya sakewa da danginta koyaushe cikin sanyi take kanta a sunkuye.

Zama yayi kan kujera bayan yagama Yana rubutu cikin file dinta Yana cewa"

Nadiya please ki ringa kula kina kiyayewa da duk abinda zai tab lafiyarki.

Wasu sabbin hawaye ne Suka gangaro Mata ta juyarda kanta dayan gefen.

Shiru yayi Yana kallonta kafin ya miqe ya fice.

Zaki baisake shigowa dakinba ya wuce gida Dan Yana tsananin buqatar maganin ciwon qirjinsa kafin aga ya buga a gurin.

Zainab ce ta zauna tana Mata sannu cikin sanyin murya tana dafa goshinta dake nade da bandage cikin tausayin 'yar uwarta.

Kwana biyu tashin shima yayi sauqi tasake warwarewa Saidai wasu irin qaidojinda Dr sayyid ya shimfida akan lafiyarta kafin ya sallamesu Suka koma gida cikeda kewarsa sbd sosai yake bawa Nadiya kulawa Kuma sosai hakan yayi tasiri a zuciyar dukkaninsu musamman dattiya dahar wani sabo sukayi Dan duk zai koma gida idan yazo sai Dr yabasa dubu guda yace yahau acaba.

Iya talatu ma girman dayake Bata Wanda Sam Bata samuba daga yayanta daga Nadiya saishi yasa take jinsa matuqa.

Zainab kuwa dama tuni takamu Dan baqaramin burgeta Dr sayyid yagamayiba.

Zainab ce tayi musu gyaran dakinsu tashare ta goge komai tareda fesa turare takaiwa nadiyar ruwa har bayi taje tayo wanka.

Tana cikin shafa Mai yashigo dakin idanuwansa Suka sauka kan daurin qirjinta datake qoqarin saka hijabi da sauri har jikinta na rawa.

Qarasowa yayi ya nufi bakin wardrobe ya zare rigarsa ya dauki towel dinsa ya fice.

Miqewa tayi ta dauki rigarta ta bacci Mai tsantsi doguwa har qasa tasaka bayan ta fesa spray.
Har safar qafa tasaka sbd sanyi ta sanya baqar wula ta rufe kanta tareda cusa gashinta ciki Dan tunda zainab tasa Mata relaxer gashinta yayi tsayi sosai sbd miqewar dayayi.

Sallar ishai tayi tayi kwanciyarta agurin tareda qudundunewa cikin hijabinta sbd yau sanyi Sosai takeji sbd asibiti kullum dakin datake dumi  Dr sayyid ke saka masa shiyasa yanzu har cikin qashin bayanta takejin sanyin har gabobinta na fara Mata ciwo.

Yana shigowa dakin yaga yanda ta dunqule waje daya saiyaji kamar hankalinsa zai tashi Amma ya basar yayi duk abinda zaiyi yaje ya rufe gida  yashigo ya rufe dakin ya kashe wuta ya nufi katifa saiya kasa Hawa ya tsaya Yana jujjuyo zancen Dr sayyid akan sanyin daya kamata gashi yanda yake Jin fitar numfashinta yanxu yasan ciwon ne yakeson tashi tunda dr yace ko kadan daga yanxu kar abari sanyi na shigarta.

Shiru yayi kansa na daukar zafi haryaji tana fidda wani irin Nishi alamar dai ciwon ya dawo Mata.

Cikin duhun Kai tsaye ya sunkuceta gabaki dayanta ya kwantar kuryar katifar tareda zare Mata hijabinta ya kwanta tareda bude musu jibgegen bargonsa Mai laushi.

Rawa jikinta keyi sosai na sanyin dake ratsa qashin jikinta ganajinsa kusada ita sosai gashi dama baya kwana da riga ajikinsa.

Jin rawar jikin nata yayi yawa da nishinta yasa ya jawota cikin jikinsa ya rungume tareda zagayeta ya rufe a qaqqarfan jikinsa ga dumin bargo

Baa wani jimaba sanyin jikinta yafara raguwa 'dumi na shigarta sosai ahankali tafara dawowa normal Saidai yanayin yanda qirjinta ke manne da nasa yasa takasa motsi sbd kunya da tsoro ahaka bacci ya dauketa Dan dama akwai maganin bacci sosai acikin magunanta Dan harda hutu Dr sayyid yakeson tasamu.

Bai bacci ba shiru yayi da ita cikin jikinsa akaro na farko yakejin kamar rayuwarsa tasamu nutsuwar datake buqata,
Wani irin sanyin Hali yaji na shigarsa sbd yanda dukkanin gabobin jikinsa suke karbar baquntar jikinta a nasa.

Da asuba koda ya farka bacci takeyi sosai wannan karon hannuwanta zagaye suke da qugunsa hularta ta zame ya qurawa fuskarta ido sbd nepa daya farka yaga akwai.

Zameta yayi ahankali tareda gyara Mata bargon ya sauko ya nufi electronic cattle dinda ke dakin ya zuba pure water hudu ciki ya jona ya fice zuwa alwala.

Kusan tareda kawun Suka fito sallah sbd sallar asubar yanxu tashiga kawun batareda yasaniba ta hanyar saka idonsa akansu.

Harya dawo bacci takeyi ya juye ruwan a flask yasake zuba wasu yazo bakin katifar ya zauna tareda Dan buga pillow ahankali.

Cikin yanayin bacci dake cinta ta bude idanuwanta tareda mayarwa ta rufe
Saura kadan zuciyarsa ta fado da hakan datayi Dan kuwa har wani tari ya miqe Yanayi sbd sarqewar numfashi daya kamasa.

Kyaleta yayi ya hawo katifar ya kwanta tareda rufe rabin jikinsa kawai Yana 'dan qara gyara muryarsa kadan sbd yawun dasuka sarqesa sbd qafafuwansu dasuka hadu cikin bargon.

Lumshe idanuwansa yayi ya rufe yanajin yanda dumin numfashinta ke sauka a wuyansa yana dumama dukkanin jikinsa har numfashinsa na slow.

Kamar Wasa sai baccin dabai wani yiba cikin Daren ya daukesa ahakan.

Qarfe bakwai maganin yadan saketa ta bude idanuwanta ahankali tana sake gyara kwanciyarta cikin jikinsa.

Da sauri ta qarasa bude idanuwanta baccin na sakinta gabaki daya tayi saurin matsawa baya tana kallon fuskarsa datayi wani irin kyau dayana baccin,

Bakinsa dayayi wani Dan ja kadan ta kalla zuwa dogon hancinsa da gashin girarsa dake kwance kamar na mace,

Tabbas farine sosai dayake sirke da 'dan yellow na asalin mutan Igbon asali Saidai shi Sam baya wani tara sumar Kai saita gemu Wanda yake bana ustazanciba saina tsabar qwarewa a ta'addanci.

Karo na farko data saki murmushi bayan qare masa kallo.

Ahankali ta sauko tana qoqarin daukar hijab taji yace"

Ki juye ruwan cattle din kiyi amfani dasu idan kika taba ruwan sanyi wlh saina karya dogon wuyankin nan.

A matuqar tsorace da kunyace ta juyo ta kallesa taga har lokacin idanuwansa a rufe suke kenan duk Yana saneda abinda takeyi tun tashinta.

Cikin tsananin kunya da rawar jiki ta dauki cattle din ta fice tana rufe jikinta da hijib sbd sanyi.

Da ruwan zafi sosai tayo alwala tadawo sbd cikin gidanma tsit duk Basu fitoba sbd sanyi.
#MAMUH.
*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

*_Mamuhgee21_*
Tana komawa dakin ta nufi dardumar sallah saitaga wata sabuwar safa akai ajiye Mai tsananin kauri,

Dagowa tayi ahankali ta saci kallon gefensa taga alamar yatashi kenan shine ya ajiye Mata safar.

Dauka tayi tareda zama tasaka kafin tana miqe ta tayarda sallah.

Tana gamawa saitayi zuru da idanuwa tanason fita aiki Amma ganin yanda ya matuqar hade fuska sai tsoronsa ya taso Mata tafara kame Kamen son fita.

Miqewa tayi ta nufi bakin qofa tana qoqarin ficewa taji anfixgo hannunta tareda daga hannu zai sauke Mata lafiyayyan mari sai kawai ya kasa ya tsaya da hannu a sama ransa amatuqar 6ace.

Saurin rintse idanuwa tayi cikeda tsananin tsoron yanda Marin zai fasa bakinta saitaji tsit Marin bai saukaba.

Ahankali ta bude idanuwanta dasuka fara sauka Kam hannun dayake sama Amma baiyi marinba,

Kan fuskarsa take qoqarin mayarda kallonta ya rintse idanuwansa cikin bacin Rai tareda sakinta Yana fitarsa numfashi Mai zafi da takaicin abinda yasa yake biye Mata wani lokacin,

Cikin muryarda ta jima batajiba tasa ta tsantsan bacin Rai yace"

Daga yau bayan wanka da alwala kika Kuma fita dakin nan saina raba qafafunki biyu.

Sakin hannunta yayi yakoma ya kwanta tareda rufe idanuwansa kamar bashi yatashi yanxuba..Saidai kallo daya zakai masa kasan ransa amatuqar bace yake.

Sanyi jikinta yayi tadawo a sanyaye ta zauna kan daddumar sallah tareda dunqunqunewa cikin hijabinta.

Hakan sai kawai yaqara Bata ransa ya juya Mata baya tareda shigewa bargo ahaka bacci yasake daukarsa.


Qarfe goma ya farka yaganta kwance aqasa ta dunqule waje daya bacci ya dauketa.

Fuskarta ya qurawa ido daga idanuwanta har zuwa 'dan madaidaicin bakinta.

Nadiya ba fara bace sosai saidai Kuma ba baqa bace hakama ta 'dan Dara Wainda ake cewa chocolate haske danma yanayi na wahalar rayuwa da Rashin hutu yaqara canxa kalar fatarta,
Tanada dogon hanci sosai da fararen idanuwa masu Dan girma,

Sake kallon bakinta yayi tareda rintse ido ahankali ya dauke Kai tareda miqewa ya sauko.

Ahankali ya durqusa ya zare Mata hijab ya dauketa ta yanda bazata tashiba ya kwantarda ita kan katifa yana kallon fuskarta ta bude idanuwanta Suka qurawa juna ido akaro na farko kowannensu bai dauke ido ba.

Batareda tasaniba ta qanqame hannuwansa dake jikinta tanajin wani Abu Mai girma cikin zuciyarta dabatasan meyeba Saidai hawaye kawai dataji tanason zubarwa kozataji nauyinsa ya ragu,

Idanuwanta na cikin nasa hawaye Suka ringa gangarowa ta gefen idanun tana sake qanqamesa.

Hannunsa daya taji akan fuskarta yasa ta lumshe idanun da batasanma tanayin hakanba.

Bata bude idanuwantaba taji saukar hannun a wuyanta cikin wani irin sanyi
Batasan lokacin wani Nishi Mai qarfi ya qwace mataba Wanda yasa qirjinta yin sama ya mannu sosai da qirjinsa dake daf da nata gurin fitarsa Wanda hakan yasa qarfin jikinsa saki ya matseta jikinsa Yana sake cusa hannunsa cikin wuyanta zuwa bayanta.

Rufe idanuwanta tayi hawayen cikin nasake gangarowa tana Jin yanda hannuwansa suke zagaye da ita tanaji qarfin gabobin jikinsa na kashe 'dan qarfin nata gabobin dabasuyi ko kwatar nasaba.

Shiru sukayi ahaka ko motsi Babu Wanda yayi sbd duk sun dawo hayyacinsu daga Dan shagaltar dasukai Saidai har lokacin jikinsu a hade yake bai saketaba itakuma Bata motsaba tananan cikin jikinsa.

Dumin jikinsa Dana bargon yaqara sata Jin bacci bacci Saidai Rana tayi batason yi.

Sun Jima ahaka idanuwansa a lumshe bai budeba Saidai tasan ba bacci yakeba.

Harta fara lumshe ido zatai bacci taji ya zame ya sauka tana kallo ya dauki brush da toothpaste ya fice.

Ajiyar zuciya tasake sai alokacin tsananin kunyarsa tafara dawo Mata taji kamar tanason rasa kunya da control na kanta ne idan Yana tareda ita.

Saukowa tayi jiki a mace da kunya itama tadauki brush ta dauki flask ta fice.

Duk su iya talatu na tsakar gidan tai musu alamar gaisuwa tareda zuba ruwan zafin dake cikin flask ta sirka tayi brush tana gamawa ta nufi dakin zainab dake Shan waqa a wayarta tana gugar kayanta ta zauna gefen katifarta tana Mata alamar taje ta Dora abinda za'a karya dashi ita Yaya Zaki ya hanata daga yau.

Daqyar zainab tagane Mai take nufi sbd tun can dah Nadiya Bata damu da bayani ba shiyasa Sam bazaka gane Bata mgn ba idan Kai baqone sbd koyaushe Bata dogon zance bare tayi maka alama da hannu.

Wani ihu zainab tasaki tana cewa"

Iyye yarinyar nan kice mijinki ya hanaki aiki wahala sbd tsaro..?

Miqewa nadiyar tayi da sauri zata fice zainab ta riqota tana cewa"

Ke Yar bebiyar Yaya Zaki tsaya kiji to tunda yafara ji dake wlh kiyi sauri kisamu ciki kozamu qarasa samun yanci da Jin dadin duniya a gidan nan.

Zaro ido Nadiya tayi saikuma zancen yabata masifar kunya ta qwace tareda nufar qofa zainab takuma Shan gabanta tana riqo hannunta tace"

Ok let's be serious,wlh Nadiya yakamata kifara zagewa kiyi rayuwar auren,Ina nufin kifara aikinki kamar yanda kowace matar aure keyi a gidan mijinta,
Dukkaninmu Muna tsoron Yaya Zaki Amma yakamata ki rage tsoronsa ko kicire tsoron kwata kwata sbd ke matarsace Dole aringa ganin banbanci.

Zuba Mata ido Nadiya tayi cikeda mamaki da ganin wautar maganarta sbd Babu ranar dazata daina tsoronsa arayuwarta.

Riqo hannunta zainab tayi cikin wani irin yanayi tace"

Nadiya nikadaice 'yar uwarki Kuma tamkar qawa agareki
Ina fada Miki duk abinda yakamatane sbd zai iya yiyuwa wata Rana bananan bakida Mai fada Miki adaidai lokacinda yakamata ace kinada Mai fada mikin Wanda nasan alokacin zakiyi maraicina fiyeda kowa Nadiya,

Sanyi jikin nadiyar yayi ta kalli zainab din saitaga idanuwanta kamar sun ciko sai itama nata idanuwan Suka ciko ta riqo hannun zainab din tanajin kamar tsoron maganar zainab din nashigarta.

Murmushin qarfin Hali zainab tayi tace"
Nadiya Dan Allah kiyi amfani da matsayinki a gurin Yaya Zaki ki kawo sauyi a rayuwarmu gabaki daya muda iyayenmu sbd gyaran zai faro daga kansa ne to abin zaizo da sauqi,

Nadiya kimin alqawarin kulada iyayenmu karki Bari su mutu a kan turbar dasuke ayanxu.??

Rungumeta Nadiya tayi tana girgiza Mata Kai Dan jitake hankalinta na tashi tsoro na shigarta,

Batasan meyasa zainab ke Mata wannan zancenba Saidai tasan batason rabuwa da zainab itama,
Duk Wanda ke sonta takejin sanyi agurinsa tafiya sukeyi suna barinta wane irin baqin jini ne gareta?

Mamarta ta rasu Randa ta haifeta,
Umman Zaki dake tsananin qaunarta ta tafi tabarta,
JJ ma dayake matuqar qaunarta ya tafi,yanxu ga zainab na Mata wainnan zancen marasa dadi.

Sakin zainab din tayi zata miqe
Zainab ta saki dariya tana cewa"

Ke duk da Wasa nake Miki sbd kisaki jiki kiji da aurenki wlh Nadiya ke local ce kisaki jiki ki dinga haukata Yaya Zaki da shagwaba kiga yanda duk zai kwashe makamansa daga dakin nan yakaisu waje ya zubar.

Ajiyar zuciya Nadiya ta sauki Jin Wasa zainab din takeyi ta miqe tareda hararar zainab din ta fice tana murmushi.

Tana shigowa tagansa zaune Yana waya tasan Kuma breakfast yake jira tunda taga ledar bread a gabansa dashi yashigo kenan.

Flask ta jawo tareda kayan tea ta ajiye gabansa ta zauna ahankali tareda hada masa tea din Mai kaurin gaske sbd Sam arayuwarsa bayashan sugar.

Miqa masa tayi tareda fara qoqarin miqewa yayi Mata wani kallon qasa qasa
Komawa tayi ta zauna tareda hada nata tea din kadan tafara Sha.

Kusan tare Suka gama ya miqa Mata magani ta karba ta shanye ta tattara kayan ta fitar ta dauki bread ta dibi kayan tea din taje takaiwa zainab Wanda zata hada musu itadasu baba tadawo dakin.

Gyaran dakin tahau Yi sbd yatafi wanka.
Shimfidar tafara gyarawa tsaf ta goge komai tayi shara ta fesa turare tana qoqarin tubewa yashigo da sauri ta mayarda rigarta tana kame kame.

Saidaya shirya ya fice tukuna ta tube taje tayo wanka tadawo ta shirya cikin doguwar riga Mara dogon hannu cikin Wainda ya siya Mata lokacin jinya ta fesa spray.

Abincin daza'a dafa ta Diba taje takaiwa zainab tadawo tana Jin jiri sbd maganin baccin dake cikin magunanta.

Bakin katifa ta zube take bacci yayi gaba da ita.

Bayan azahar sosai ta farka taje tayo alwala tayi sallah tana idarwa Yana shigowa hannunsa daukeda ledojin takeaways.

Ajewa yayi ya zare rigarsa ya fice waje Yana murza daurin qundarsa sbd wasu yara da aka kamo sun sassare yaronsa harya rasa hannunsa daya.

Yana fita qofar gidan gurin yayi mugun tsit bai tsaya komaiba ya dauki babbansu wani mahaukacin Marin dayasa hancinsa 6arewa da jini.

Goran hannun Nanu ya karba ya bugi qafafunsa atake ya zube qasa Yana roqansa da cewa"

Sarki Dan allah kayi hakuri kabarni da Raina wlh bansan yaronka bane da bazamu tabasaba muma ai yaranka ne wlh,
Dan allah sarki,
Dan allah sarki kayi hakuri
Kayi hakuri karka kasheni....

Wani bugu yayiwa bakinsa Saida haqoransa biyu Suka zubo qasa tareda jini da yawu...

Goran yasake dagawa ya bugi hannunsa,
Ihu yakeyi Yana neman afuwa da yafiya Amma dukan dayake masa bayan jini Babu abinda ke fita gashi guri yacika Babu Mai ikon cewa qala.

Dattiya daya dawo yaga guri yayi mugun cika yafara tambayar lafiya Yana ratso mutane Yana kawowa daidai Zaki ya daga Goran zai buga a tsakiyar kan wancan
Dattiya ya riqe goran

Ganin fushi da bacin ran dayake tareda zakin yasan yau antabosane a mugun wuri
Kai tsaye yace"

Bantaba shiga harkar ikonka ba a kan sarautarka sai ayau
Ayau dinma nashigane ba amatsayin kawunkaba sai amatsayin mahaifin matarka,
Ka kyalesa haka karkayi kisa sbd baka taba yiba idan kayi yanxu halinda 'yata zata shiga nake dubi.

Kallon kawun yayi cikin ido yaga tabbas yau ba kawunsa yake ganiba mahaifi uba yake gani Wanda keson Kare martabar auren 'yarsa.

Sakin gorar yayi akaro na farko da shima ya saurari maganar kawun shima baa matsayin kawunsaba Saidai amatsayin mahaifin matarsa.

Kallon Nanu yayi da jajayen idanuwansa yace"

Kasan abinda zakayi daganan sa Kai.

Da sauri Nanu yace"

Angama sarki.

Juyawa yayi yashige cikin gidan duk hannuwansa da jikinsa jini ya Dan batasu.

Akaro na farko dayaji bayason tagansa da jinin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login