Showing 39001 words to 42000 words out of 81157 words
masa cikin tsananin zafi da tafasarda zuciyarsa keyi masa na Rashin dansa qwaya daya tal a duniya batareda sun haduba ya danne bacin ransa sbd kar ayi biyu ya rasa dansa yazo ya rasa jikansa Kai tsaye yacewa driver suje gidan Dr sayyid din.
Cikin qanqanin lokaci suka Isa gidan Saidai sanin yabaro motarsa acan su am zasu iya ganowa su biyosa gidansa sai yafito motar da sauri ya shiga gidan yafara tattaro duk wani abin buqatar Mai mahimmanci tareda passport dinsa da takardunsa tareda magunguna da allurai ya fito da sauri Suka wuce.
Cikin motar jikinsa na rawa da sauri ya hada ruwan injections yayi Mata guda hudu sannan ya hada na JJ shima da sauri yayi masa Saidai shi Yana yimasa ya farfado Yana sakin wani gurnanin nishin azaba Yana qoqarin bude baki yana tambayar ya Nadiya.
Direct airport suka nufa cikin qanqanin lokaci akai cuku cuku sbd girma da kudinsa sukabi flight din tsakiyar Daren zuwa Lagos.
Bayan sallar asuba har gari yayi haske suka sauka Lagos wata qatuwar baqar jeeb tazo ta daukesu ta private exit inda Babu Wanda yagansu suka bar airport.
Wani qatoton mansion daya ninka na Dilla dasuka sani kusan so biyar Suka shiga Saida suka wuce gate uku kafin Suka Isa main harabar gidan Dana tun acan Sukayi ordering nurses guda uku Mata daga Primus private hospital atake cikin gaggawa aka shigada Nadiya sbd har lokacin Bata farko ba Saidai bleeding din ya tsaya gabaki daya.
JJ ma ciki akayi dashi duk da ya farfado Bai iya tsayawa miqe sbd gefen cikin nasa.
Securities ne suka budewa Mai gidan qofar mota sai alokacin yafito fuskarsa Babu annuri ko daya ya wuce Yana amsa gaisuwarsu da Kai yayi ciki.
Direct qaton bedroom din dake palon ya nufa inda aka Kai Nadiya saidai Bai shigaba ya tsaya tsaye tsakiyar palon Yana kaida kawo cikin wani irin tsananin bacin Rai na shekaru dayake zaburo masa,
Tabbas sbd kada dawowarsa ga dansa yazamo ha'dari ga rayuwar gidansu gabaki daya yasa ya boye kansa ya nesanta kansa da dansa dayasan haka zata faru tabbas daya fito sunyi gaba da gaba da dikko.....
Sir""
Sayyid yakira sunansa cikin sanyin murya kansa a Dan sunkuye cikeda ladabi ya dago ya kallesa murya cikin sanyi yace"
I'm really sorry sir,
Munshawo kan matsalar Nadiya the baby is safe now komai yayi normal insha Allah she just needs to rest Saidai a yanayinda take ciki gskia I can't assure the safety of the baby sbd her BP is very high.
Kallonsa yayi tsawon mintuna kafin ya juya yayi palonsa ya zauna cikin Dan 'dacin rai yace"
Jabeer fa???
Shima insha Allah namasa wani dinkin Nanda 48hrs zaiji sauqin zafin gurin sosai.
Sayyid tell me meyasa ka boyemin abinda ke faruwa???
Gyara tsayuwa yayi cikin jimami da takaicin tsananin damuwar dayake hangowa ga mutuminda yazamo tamkar uba agaresa yace"
Sir dama koda nagama bincike Nagano Zaki shine Wanda muke nema nayi maka email na hotunansa da duk bayanai na yanayiwa dikko aiki to alokacin ne yazomin da buqatar nemawa Nadiya lafiya Kuma abinda yasa muka buqaci kudi daga garesa masu yawa sbd munyi tunanin hakan zaisa yaje ya nemi aikiyi da kansa Wanda nasan samun aikin zaisa yadainawa dikko aiki Saidai abinda bansaniba shine yanda yasamo kudin Kuma aranarda akayi aikin aranar koma menene yafaru yafaru lokacinda labari yafito ankamasa da yiwa qasa sata aranar naje Naga IG nabasa 1million akan case din sbd banasonma kaji hankalinka zai tashi Kuma hakan zaisa ka bayyana kanka Wanda lokacin daka tsara hakan baiyiba tunda akwai gabar da kake jira ka bayyana kanka,
To abinda yabani mamaki shine yanda wuta ya tashi a Daren Kuma babban abin mamaki da zargi shine IG yacemin a Daren dama sukai planning sakin zakin Saidai kafin su Isa wutarne takama and unfortunately......shiru yayi yakasa qarasawa ahankali ya furta"
Kayi hakuri Allah yaji qansa....
Miqewa yayi Bai tsaya sauraron sauran bayananba ya haye stairs Dan kuwa wata irin masiface dikko ya takalowa kansa shida familynsa Bai saniba.
Acikin Daren washe gari ta farka da wani irin tsananin ciwon Mara da zabure zabure Wanda ya tsorata nurses din da sauri Suka dauki waya suka Kira Dr sayyid hankali tashe ya qaraso nan suka hau dubata Yana addua da fatar shock dinda tashiga karyayi affecting babynta da lafiyarta sbd shock ne da high BP suka hadu lokaci daya.
Har asuba suna Abu daya daqyar yashawo kan matsalar yayi Mata allurai tayi bacci.
Dafe goshinsa yayi cikin tsananin tension yake kallonta kafin ya kalli nurse din yace"
Please after 30min give her antropespines.
Ok Dr ""tafada itama cikin tausayin Nadiyar.
Fita yayi yaje dakin JJ shima Saidai shi yaji sauqi sosai Saidai wani irin fushi da zafi dake cinsa Sam jijiyoyin jikinsa Dana kansa sun firfito Wanda har fushinsa ke bawa Dr sayyid tsoron irin burin fansar dayake hangowa a idanuwan JJ din.
Cikin nutsuwa da tsananin kwarjini Mai gidan ya shigo dakin JJ din Dr sayyid na bayansa tareda Mai aiki data shigoda abinci cikeda tray ta aje a bedside drawer ta juya ta fice.
Kallonsa JJ keyi Babu ko qyaftawa sbd ganin zallar kamanni da kwarjini irin na sarkinsu dake tattareda mutumin,
Baya tantama wannan shine mahaifin sarki sbd dama zakin baida tabbacin shin mahaifinsa mutuwa yayi kokuwa da gasken shi Dan fyade ne kamar yanda so dadama yake tsintar zancen gurin kawunsa,
Baitaba tambayar mahaifiyarsa ba waye babansa harta rasu sbd zaizamo tamkar cin fuskane agareta shiyasa yacire maganar aransa Koda shidin Dan halak ne ko sabanin hakan wannan tsakanin mahaifiyarsa ne da mahaliccinta.
Irin kallonta JJ ke masa yasa ya matso gabansa tareda miqa masa hannun ahankali ya furta"
*_ALHAJ ALEEYU NEYO NOAH_* Congress man starling city United States of America,Kuma nine mahaifin marigayi aliyu haidar Zaki.
Jajir idanuwan JJ sukai ya rintse ido suna qara yin ja jijjiga Kai Yana son daure kukansa Saidai Sam ya kasa durgushe qasa tareda sakin kukan mutuwar zakin dake hura wuta a jinin dake gudana cikin jikinsa tun Daren jiyan.
Ahankali jikinsu yayi sanyi cikin dauriya Dad din yace"
Fitar duka zakaji sauqi duk da nasan dikko yayi Mana gibi Mai girma a rayuwa da bazamu iya cikewaba tayin ajalin Zaki.
Kuka sosai JJ yayi Amma Sam yakasa Jin abinda ya tokare masa ya fada ya dago da qyar yace"
Har abada abinda nakeji gameda mutuwar sarki bazai fadaba sai ranarda Naga qarshen zalinci da mummunan qarshen dillas gabaki dayansu.
Juyawa dad din yayi shima cikin danne nasa fushin yace"
Qarshensu na zuwa jabir karka damu,
Zan mayarda rayuwar dikko shafaffiya a tarihirin masu arziki,
Zan mayardashi mabaracinda ko suturar sawa baida ita ajikinsa insha Allah.
Miqewa JJ yayi yace"
Dikko,zeel,am nayi alqawarin ganin na mayarda asusun arzikinku daga zero me yawa zuwa zero daya tal.
Yanda kuka cutatardamu cikin zamba da aminci ta fuskar amintaka ahaka zan cutatar daku ta fuskar zamba da aminci.
Kallonsa dad yayi cikin jinjina Kai tareda qaunar JJ din sbd tabbas yaji dukkanin bayanin irin so da qaunarsa Zaki kewa JJ tamkar jininsu daya.
Ya rasa 'dansa Saidai dukkanin abinda dansa zai masa yasan magajinsa sai masa,
Yayi alqawarin saiya zubarda dikko ta hanya mafi ciwo da zafi Dan haka alqawarinsa na nan,
Shida JJ burunsu dayane.
Lokacinda Nadiya ta farka sosai hankalinsu ya tashi sbd dai a iya bincike da abinda Dr sayyid ya binciko shock din ya taba qwaqwalwarta Dole a mayarda ita asibiti.
Hankalin dad da JJ yayi matuqar tashi nan dad din yasa aka fara cuku cukun nemar musu visa Dan kaita asibiti anan is very risky dikko ya wuce duk inda ake tunaninsa zai iya ganonsu.
Cikin sati guda komai ya kammala Suka daga zuwa US a starling city Suka sauka nan akai asibiti da ita gashi abin yafara taba lafiyar cikinta Dole Suka tattara komai suka aje Dan ganin tasamu lafiya gashi dukkaninsu kowa Yana tsananin qaunar cikin basason abinda zai samesa.
Sannu ahankali likitocin qwawqwalwa suke ganinta ana Bata allurai da magani tun abin na hauka sosai saigashi tafara dawowa normal Saidai idan abin yatashi Babu sauqi hauka takeyi sosai tana ihu da Kiran sunan Zaki da zainab wani lokaci hardana babanta.
Ahaka dai Suka Mata transfer zuwa wata babbar asibitin psychiatrist dake Amsterdam inda Sukayi admitting nata ganinta sai wata wata.
Ba yanda suka iya su dad haka Suka hakura Suka barota Saidai kulawarta daban take ta musamman ce sbd cikinta da harya fara tsufa Dan lokacin Yana wata shida.
Sannu ahankali dad ya warwarewa JJ dukkanin sirrin dukiyarsa da rayuwarsa tareda dorasa akai duk da dai komai NASA yariga ya yanke shawarar sunan Nadiya da abinda ta Haifa zaa saka dukiyarsa kaf yace tasuce tunda sune Abu mafi soyuwa a rayuwar Zaki.
Sosai rayuwar JJ tafara canjawa musamman da dad din yasa aka ware masa wani program na classes dayake zuwa dauka na degree dakuma na aikin kakin soldier na shekaru biyu dazaiyi yagama.
Yawan geaming dinda yakeyi saiya fara bude jikinsa ahankali yafara zama wani qaqqarfan najimi gashi yanzu wani irin hutu da dukiya sun fara ratsashi musamman dayake dad din baiwani jin hausa sosai tunda asalinsa ga yanda yake Kuma yadawo nan din.
Duk wata tare suke zuwa dubo Nadiya Amsterdam suyi kamar kwana hudu kafin sudawo sbd dr sayyid tuni ya mayarda hankali kan fannin asibitoci da kamfunan magungunan NOAH.
Lokacinda Nadiya tashiga 9month dinta alokacin ne Suka dawo Amsterdam dukkaninsu harda Dr sayyid Wanda bai wani Jima da dawowa daga Nigeria ba sbd dubo alqawarinda yayiwa Zaki tuntuni na kulada familynsa Saidai Bai fadawa kowa yajeba.
Two weeks after labour yazo Mata inda hankalin asibitin yayi mummunan tashi sbd tun Daren jiyan take fama da labor gashi sbd mental problem dinta yasa ihun azaba takeyi sosai Bata wani iya daurewa tunda batasan metake yiba.,
Ganin abin yafara fita out of their control yasa sukai transferring dinta to wani babban asibitin su dad Suka kwasa sukai can Babu Mai nutsuwa.
Da isarsu aka shiga labor theatre da ita sbd bazata iya haihuwa da kantaba gashi tayi weak sosai.
Lokacinda dad yasa hannu a takardar tiyatar Saida JJ yariqe hannunsa sbd yanda yake rawa cikin sanyi da dauriya yace"
Dad insha Allah lafiya zata fito.
Daga masa Kai dad din yayi Yana murmushin qarfin Hali da jarumta.
Har dare suna zaman jiran sai qarfe bakwai nurse biyu Suka fito cikin farin ciki dayar tace"
Congratulations Congressman.
Dayar ce ta karbe zancen da cewa"
It a baby girl sir.
Hamdala suka sake dukkaninsu tare cikin farin ciki dad yace"
Thank you for this wonderful news ladies.
Fitowar doctors ne yasa dad kallonsu Yana cewa"
Dr hw about the mother????
Kallonsa Dr Allen yayi ya jinjina masa Kai suka nufi office Yana sake karanto masa reports dinta dasuke saka ran tadawo normal daga mental issues dinta.
Lokacinda JJ yadauki babyn wani irin murmushin farin ciki tareda hawaye yakeyi yanajin tsananin qaunar yarinyar ya Dan shafi fuskarta dake yanayi data babanta ahankali Yana murmushi hawayensa na qaruwa.
Dan motsawa yarinyar tayi Hana 'dan turo harshe cikin tsananin farin ciki ya furta"
Zainab baby.
Dad dake bayansa sukaji yace"
Harkawa 'yarku huduba kenan.???
Qarasowa yayi ya karbi babyn shima yayi Mata addua Dr sayyid ma yayi nurse tazo ta karbeta ta mayarda ita gadonta dake kusadana mamanta da Bata farfadoba.
#MAMUH.
*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_
*08030811300*
*07067124863*
*_Mamuhgee27_*
Kwana biyu da haihuwarta taji sauqi sosai Saidai har lokacin Bata yiwa kowa magana sai shiru datakeyi hawaye na fita idanuwanta musamman da dad ya gabatar Mata da kansa dakuma matsayinsa na uba ga mijinta Kuma kakan 'yarta baby z.
Ranarda aka sallamosu Suka koma asibitinta na psychiatric Suma Suka gama nasu binciken Suka sallameta Suka dawo starling city anan Suka tararda Nanny's da qarin sabbin masu kulada gidan da ita kanta nadiyar.
Wani tangamemen hoton Zaki ne na zane dake facing duk Wanda yashigo makeken polon Wanda masu zanen Suka samoshi sosai kamar shi din ne aka dauka.
Tsayawa tayi cak tareda qurawa hoton ido tanason riqe kukan daya danne qirjinta tsawon watanni ta sakesa da qarfi tareda durqushewa gurin komai nasake dawo Mata sabo
Kunnuwanta na dauko Mata qarar sautin kuka da magiyar iyayenta tareda qarar bindigar Daren da abin yarafu dakuma qonanniyar gawar mutum mafi soyuwa a rayuwarta dake dawo Mata a ido.
Nanny Nancy ce tayi saurin riqota tana durqusawa gabanta cikeda tausayinta duk da batasan meye damuwarta ba Amma yanayinta ya nuna tsananin quncin da zuciyarta ke ciki.
Dad da JJ ma duk jikinsu sanyi yayi sbd ita yanzune data dawo daidai takejin komai yadawo Mata sabo musamman idan takalli maraicinda yarta zata taso dashi na Rashin uba.
Cikin sanyi dad yace nanny Nancy tayi ciki da ita.
Wani tangamemen dakin dayafi kowanne kayan qyale qyale da haduwa aka kaita inda aka zuba komai sabo na baby z Dana nadiyar tundaga situru da abubuwan buqata na gyara.
Bakin gado ta zaunar da ita tareda kwantar da baby z cikin gadonta ta fice.
Kuka takeyi sosai tanajin wani irin zafi da radadi na qona zuciyarta inda takejin wata irin tsana da qiyayyar familyn dikko Dilla musamman am datake gani a idonta lokacinda ya buge babanta yaja zainab cikin daki ya harbeta.
Cukuikuye jikinta tayi sbd tsananin abinda takeji na wutar tsanarsa dake ruruwa a jininta taci gaba da kuka.
Yini guda a dakin tayisa Bata fitoba tun shigarta gashi daga dad din har JJ Babu Wanda yayi yunqurin shiga dakinta Dan karsu takurata.
Su nanny da masu aikine keta hidimar kulada gidan da baby z sukuma su dad suna can sun maida hankali kan business dinsu.
Washe gari ma Bata fitoba a daki ta wuni kwance idanuwanta sunyi zuru zuru sbd Rashin bacci da tunani.
Sannu ahankali lokacin yafara tafiya har baby z tafara girma takai wata hudu cikin na biyar sosai nanny Nancy ke kulada ita musamman ta bangaren Bata madararta sbd nonon Sam baida wani ruwa sai kawai Suka maida himma gurin Bata Madara.
Duk yanda taso yakice abinda ke rura wutar qiyayyarta saitaji takasa sosai takejin batada sukunin zuciya Dana jiki akan irin kisarda akaiwa mijinta da 'yar uwarta tareda iyayenta,
Abu daya tasani shine bazata taba hutawaba saita biwa 'yar uwarta da mijinta haqqin ransu,
Dole za'a bawa matarda aka kashewa miji justice hakama uwar da aka kashewa ya agabanta.,
Babban abinda yafi azalzala wutar zuciyarta shine yanda ta haukace taso a maidata gurin iyayenta Amma dad ya Hana tareda fahimtar da ita matuqar tanason babanta tanason lafiyarsa ta nesanta kanta dasu yanxu sbd bayyanarta hadarine ga iyayenta dakuma 'yarta.
Akaro na farko dataji tana tsananin sha'awa da buqatar karatu Mai tsananin zurfi a rayuwarta sbd da shine kawai zata iya fuskantar Wanda yayi ajalin mijinta wato AM DILLA.
Sakin jikinta tafarayi ahankali tana koyan turanci sosai gurin nanny Nancy tareda wasu abubuwan.
Dad ma ganin tasaki jiki sosai lokaci guda sai abin yabasa mamaki Amma yaji dadi sosai musamman yanda tafara sakewa dashi Saidai yanayin zafinta yakan bawa JJ tsoro da mamaki sanin ita din Mai tsananin sanyi ce.
Dad da kansa yasa aka dauko Mata wani Dr Marshall Yana koyar da ita karatu da wasu hanyoyin business sbd shi arayuwarsa komai business ne,
Shi kansa babu abinda yakeso kamar nadiyar tazama independnt business woman dazata jagoranci _NOAH EMPIRE_ nan bada dadewaba.
Ahankali baby z tayi wayo zuwa lokacin Nadiya harta sauya sosai sbd yanda nanny Nancy take matuqar kulada cimarta sbd Sam tace Mata batason tayi jiki.
Rashin fitarta yasa fatarta tayi mugun canzawa musamman dayake cikin masu musu aiki akwai Becca wadda Tai aiki wani babban beauty parlor ita ke sake kulada skin din nadiyar ta bangaren abubuwan datake amfani Wainda suka mugun karbar brown skin dinta.
Baby z nada shekara daya admission dinda dad ya nemarwa Nadiya a university of Toronto Canada yafito dayake duk a shirye suke Babu Bata lokaci ta wuce aka bar baby z agurin nanny Nancy da sabuwar nannyn da aka qaro Mata musulma daga qasar Libya sbd kulada bangaren tarbiyan addininta musamman dayake tafi sabawa da nnany nancy da dad said JJ datakewa kallon shine mahaifinta.
Babban Abu na farko da Nadiya ta mayarda hankali akansa bayan karatunta shine shiga harkar tsadaddiyar rayuwa sosai sbd tanason ta iya komai,komai ya zauna arayuwarta da jikinta tareda dabiarta sbd ta hakanne zata samu cikar burinsu daya zamo daya itada dad 'dinta da JJ.
Sosai take karatu musamman da rayuwarta ta sauya cikin shekara daya da fara karatun tuni ta sauya komai ta koma tamkar haihuwar turawa rayuwarsu ta shigeta ta bangare daya dad ma ya dage sosai yake sakata a harkar business tun Bata ganewa harya shigeta tana gane business sosai.
JJ ma yagama karatunsa yanzu yafi maida hankalinsa akan harkar training dinsa dakuma business din sosai sbd shine abinda dad yafison yashigesu.
So biyu kawai tazo starling city hutu tunda tadawo Canada din Saidai kusan kullum tana video call dasu nanny da baby z shi dad kusan Yana yawan zuwa kokuma idan yace tasamesa wata qasar Akan harkar business.,
Shikuwa JJ dama kusan duk yasamu time Yana hanyar zuwa Canada din gurinta.
N.D NOAH take amfani dashi a dukkanin takardunta da passports dinta tareda duk wani id card dinta ma'ana Nadiya dattiya Noah.
Yawanci friends dinta turawa sukan kirata da nadey Noah.
Ahankali karatunta yayi nisa harta kai shekarar qarshe Saidai zuwa gabaki daya rayuwarta da ita sunyi nisa da hannun riga da rayuwarta ta dah.
Bazaka taba kallon shape da zubin slimmy figure dinta kace ta taba daukan ciki bama bare haihuwa,
Skin dinta yatashi daga brown yakoma tamkar na half-caste ko black Americans sbd tsabar hutu da kyawun tareda tsadar products dinda take amfani dasu,
Sam ta manta when last ta zauna da wani tayi yarenta na hausa sbd dama dad ne shima Bai wani cika hausaba tunda dama ba tarensa bace,
Sai JJ shima turai tashigesa sosai Sam sai can suke hausa a tsakaninsu kokuma baby z dasukewa sbd ta 'dan iya.
Duk wani motsi da tarihin Dilla's suna sane dashi a tafin hannunsu yake yanzu zasu fara nasu wasan THE NOAH'S sbd shima JJ JABEER HAYDAR NOAH yake amfani dashi.
Shekara hudu cikin ta biyar cif ta Gama kammala first and second degree dinta a fannin business da harkar modeling fashion.
Ranarda ta sauka us a ranar cikin dare dad dinta ya hada wani gagarumin taron dinner inda ya bayyanarda ita a matsayin owner NOAH'S EMPIRE.
sosai Yan press Suka dinga daukarta hotuna suna Mata tambayoyi inda ta ringa Basu amsa cikin wani irin yanayin daya ringa rikita zuciyar manyan abokanan business din dad dinta da 'yayansu tun anan wasu Suka fara miqa business offer dinsu sbd duk wata suffar daukar hankalin 'da namiji tagama hadasu atare da ita musamman dinner gown dinta black Mai tsegen kyau