Showing 75001 words to 78000 words out of 81157 words
ta shirya suje su siyo kayanta na sawa.
Cikin riga da skirt na red super Sheraton Mai golden kadan ajiki tasakata babbar kimono jallabiya akai tareda yin rolling gyalen jallabiyan kawai ta dauki handbag da key din motar Kai baby z school wata 'yar eclass3033 2019.
Fammah kuwa doguwar ash jallabiya tasaka sai qaramin gyalen jallabiyan Suka fito bayan sunyi bankwana da iya talatu akan saisun dawo.
Geaming yagamayi dagashi sai wasu riga da wando na Nike marasa hannu sai hularsu ya hada gumi sosai musamman sbd tsananin bacin Rai da tsananin kewarta daya kwana da ita yasa yakeyi yaqi tsayawa saiga Kiran JJ.
Dauka yayi tareda dakatawa ya miqe Yana cewa"
Saida kagama hadani da kawu kake kirana yanzu.
Dariya JJ yayi tareda cewa"
Gani Nan Nazo ai bawa kawun hkr da kaina.
Fitowa yayi harabar gidan daidai shigowar motar JJ ciki Suma daidai lokacin suka fito kowacce na ganinsu ta daure fuska.
Ita fammah hakanan taji Rashin Jin dadin abinda JJ yayi jiya a waya da akace itace tasan cewa yanajin haushinta da takaicintane sbd ita Dilla ce shiyasa ta dauke Kai tareda Dan kame fuskarta data gansa haydar ma Sam ko ganinsa batason yi yanzu sbd kallon datake masa a mijin nadey Wanda itama tata zuciyar haryanzu tana sonsa.
Nadey kuwa ganin Zaki yasata Dan daure fuskarta duk da tsorone fal aranta Dan taso su fice batareda yasan sun fitarba.
JJ na fitowa motar shima kallo daya tayiwa gefenda suke sbd fammah sai baisake kallonsu ba yace"
Nadey Ina zaku this early morning????
Mota ta nufa tana tsuke fuska zatai magana sukajisa yace"
She's goin no where.
Kallonsa fammah tayi ya kalleta shima fuska a daure take gabanta ya fadi tafara neman rikicewa Kai tsaye yace"
Ina zaku??
Kallon nadey data sake daure fuska cikin takaicinsa na yanda ya tsare fammah da ido gashi duk muscles dinsa a bayyane tace"
Dama she's taking me to....
To where????yafada cikin 'yar tsawa sbd ransa dashima yagama baci sbd kallo daya yayi Mata yaji zuciyarsa na quna da kishi.
Kayan sawa zata siyamin I don't have any clothes....
Wani mugun kallo ya watsawa nadeyn data fara saduda sbd ganin fushin dake kan fuskarsa ta dauke Kai da sauri tana Dan gyara tsayuwarta.
Kallon JJ yayi Kai tsaye yace"
JJ Kai fammah din asiyo Mata kayan wannan Kuma let me put some sense into her"""yafada tareda fizgo hannun nadiyar ya nufi part dinsa da ita.
JJ kuwa kasa motsi yayi Yana takaicin wannan yawon banzan dazai fitayi bayan shi gurin kawu yazo Dan yasan idan baizoba yau Babu abinda zai Hana kawun Isa can gidan.
Batareda ya kalleta ba ya nufi mota ta biyosa abaya jiki sanyaye sbd taga yanda qiri qiri Rashin Jin dadi ya bayyana a fuskarsa.
Jiki ba qwari tashiga motar yaja da speed yabar gidan.
Suna shiga palonsa ya saketa ya juyo da wani irin fushi zaiyi magana cikin tsananin bacin da sauri ta hanasa ta hanyar fadawa jikinsa ta qanqamesa sbd tsoron karya mammareta.
#MAMUH.
_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_
*08030811300*
*07067124863*
*_Mamuhgee45_*
Kasa wani dogon motsi yayi sbd yanda ta cukuikuye acikin jikinsa sbd tsoro da shakkarsa Daya bayyana atareda ita Tana sake cusa kanta cikin jikinsa hannuwanta na Dan rawa da qafafunta.
Rintse idanu yayi ahankali yanajin dumin hannuwanta na kashe duk wani fushi da bacin ran daya shiga lokaci daya,
Ajiyar zuciya ya sake ahankali tareda kasa cewa qala sbd jikinsa dake neman saki ya saka hannuwansa biyu ya dagota ahankali yana kallon fuskarta cikin yanayi na nuna ikonsa yana basarda yanayinda sonta yagama jefasa ya kalleta da idanuwansa dake sake daga hankalinta cikin basarwa da iko yace"
This should be the last time dazaki sake gwada irin hakan,
Next if you try me again saina karya qafafuwanki da hannuwanki and I mean it kinajina ko???
Dan dagowa tayi da kanta ta kallesa Tana sauya fuska kamar zatayi kuka ta juya cikin haushi zata bar gurin ya fizgota saidata tsorata takallesa da sauri.
Cikin kallon cikin idanuwanta yace"
Ina mgn shine Zaki wuce kina fushi???
Hawayen datake riqewane ta bari Suka gangaro mata ta kallesa tareda sake barewa da hawaye tace"
Naji bazan sake futan ba shikenan Ina?
Yanda tayi yasa jikinsa yin sanyi yaji ransa na dacin yanda take tsiyayo hawaye.
Fuskarta ya quraw Ido yanajin dacin ransa na qaruwa.
Ahankali ya sake jawota jikinsa sosai yana riqo hanuwanta cikin nasa yace"
To this guntun hawaye da akeyi sbd a gasani ya Isa haka its killing me inside so please ya Isa Nima naji bazan sake fada haka sosaiba ok???
Wasu sabbin hawayen ta sake matsowa cikin son sake rikitasa tace"
Yafi shekara shida da kake cewa saika karyani nidai na.....
Hannu ya Dora kan bakinta yana kallon cikin qwayan idanuwanta ya dauke gira Daya yana sakin murmushinda bai Gama kama fuskansaba yakai bakinsa kunnenta ahankali yace"
Zan karyaki Amma ba irin wancan karyawanba wannan is very special karyawa irin na lokacin samun cikin baby z.....
Zaro Ido tayi da qarfi tareda turesa Tana sakin murmushi da gudu zata tsere ya damqota tareda dawo da ita yace"
Heyyy miss Noah aikin Riga kinshigo sashenki kenan keda shiga can Sai idan kinje gaidasu kawu Kuma sbd inason raba fadan kawu da dad akan baby z soon ta hanyar Basu kawo musu wani Sai araba gardama and this time Zan ringa ban ruwa ga shukatane Dan tayi kwari da kyau tasamu Ingantacciyar yalwa....
Cikin ihun kunya Tana qanqamesa tace"
Please stop mana ko nafadawa babana what your plans are na zaka lalata Masa 'ya.
Dariya yayi tareda dagata sama yana cewa"
Basaikin fadaba nida kaina Zan nuna Masa tunda ke kikeson a rikitasa yana zamansa.
Aa Allah kasan Kaine kakeson neman maganarsa idan baka dainaba mijin baby z zai ramawa babana wata Rana.
Cakularta yayi tayi zillo ta fado daidai kan gado Tana dariya Tana shafa gurin tace"
Mena Maka to ai gskia ne nafada daga bawan Allah yaji qan ka yabaka yarsa Sai neman rabasa da zaman lafiyarsa kake nidai daga yanzu bamai sake tabamin uba ya hanasa sukuni.
Rigar jikinsa ya zame yana cewa"
Hmmmn.
Jikinsa ta kalla ta Dan juyar da Kai Tana Jin gabanta na Dan faduwa kamar tsoro zai kamata.
Saukowa gadon tayi Tana zame kimonon saman kayanta tasaka closet Tana Dan Fara gyara dakin duk da baiyi komaiba Amma amatsayinta na matarsa gari ya waye ya tashi Dole ta gyara Masa shimfida.
Wanka ya shiga yana sake gyara daurin towel dinsa.
Yana shiga ta saki ajiyar zuciya ta Dan kalli qofar bayin tareda sake ajiyar zuciya kafin taci gaba da aikin gyara dakin.
Tafiya sukeyi cikin motar Babu Mai cewa komai
ita dai fammah sbd a takuren datake ko wani qwaqwaran motsi batayi saima Jin datayi gabaki Daya fitar ta fita aranta gida kawai takeson komawa gashi batason ko mgn tayi Masa ganin fuskarsa a daure ya mayarda hankali yana tuqinsa.
Wani qaton mall kawai ya kaita batareda yace mata komaiba yayi paking ya kashe motar ya fito ya tsaya yana duba wayarsa fuskarsa a Dan sauyayyan yanayi ba laifi sbd ganin zasu shiga mutane.
Share siraran hawayenta tayi cikin tuno rayuwarta ta baya da irin gatanta Amma sauyin rayuwa yasa yau itace akewa alfarma wulaqantawa.
Fitowa motar tayi tadan saci kallansa tareda bude Baki cikin sanyin murya tace"
Ko zamu barshi mu koma gidane karna takuraka bansaniba ko kanada abinyi.
Juyowa yayi ahankali ya watsa Mata wani irin kallo dama itama din shitake kallo idanuwansu Suka shiga cikin na juna Suka qurawa juna Ido akaro na farko suke yiwa juna kallon tsaf.
Itace kunya tasata dauke idanuwanta tareda sauke Kai Tana kallon wani guri.
Shima juyarda Kai yayi cikin basarwa yayi gaba yana cewa"
Muje.
Ba laifi da kansa ya jidar Mata Kaya sbd ganin takasa sakewa shikuma ya gaji da wannan dolen komawa yakeson Yi shiyasa kawai yafara daukar Mata komai yasamu na buqata.
Dayazo gurin akwatina baiyi tunanin komaiba ya zabi wani simple set masu kyau da tsada masu guda hudu Kuma duk bawani girmane dasuba.
Aiko nan yacigaba da zabar komai dayazo kan undies ne ya fuske tareda tsuke kyakkyawar fuskarsa ya fidda wayarsa yana dubawa bai kalletaba yace"
Kiyi sauri kizaba inada gurin zuwa time yakusa.
Matsawa yayi daga gurin tabi bayansa da kallo Tana jinjinawa kanta da irin tunaninda zuciyarta ta jeho Mata najin inama tanada aure wainnan abubuwan Suka faru da rayuwarta Bata gantale hakaba,
Da koyayane Tana cikin rufin asiri bazata Zama Yar rabe rabe ba ko talakane dashine rufin asirinta take taji so da shaawar aure sun shigeta Amma waye zai sota ya amince ya aureta Tana Yar Wanda sunansa yagama baci a duniya sbd zalunci da kashe Rai ba bakin komaiba.
Kukane da batasan da zuwansaba ya kubce Mata jikinta na wata irin rawar tashin hankalin shikenan iyayensu sun Bata musu rayuwa suntafi sunbarsu da mummunan tabon rayuwa.
Da sauri ya juyo ya kalleta Jin kukanta yaga yanda jikinta ke rawa sbd sheshekar kukanta take yaji jikinsa yayi sanyi tausayinta ya kamasa sbd tabbas yasan iyayensu sun cutatardasu ta wani fannin.
Matsowa yayi bayan ya rintse idansa ya fitarda numfashi mai sanyi ya Dan kalleta tareda zaro handkerchief dinsa ya miqa Mata yana kallonta qasa qasa yace"
Meyasa zakiyi kuka cikin nutane sbd jawo kallo akankine kikeyi so please stop this right now and wipe this now"" yafada yana kallon hawayenta da cikin idanuwanta data dago ta kallesa tayi saurin janye idanuwanta sbd kasa hada Ido datayi dashi hawayenta na qaruwa.
Ganin takasa daina kukan sbd yariga yazo Mata yasa yabata key yace Takoma mota zai biya yazo.
Tattara kayan akayi guri daya aka Fara aikin hada kudinsu kusan minti arbain kafi aka Gama ya biya aka fiddo da kayan aka zuba bt da sit din baya sbd bt din bai dauke duka kayan.
Kasa tayarda motar yayi Saida taji shiru ta dago jajayen idanuwanta ta kallesa ya Dan ya mutsa fuska yace"
Kinsan bazan kaiki gida a wannan yanayinba nadey will feel bad seeing you like this.
Kallonsa tasakeyi da sauri jikinta na sakeyin sanyi,
Nadey taji Dadi tayi Sa'ar rayuwa kowa na sonta yanason farin cikinta.
Share hawayenta tayi ahankali ta furta"
sorry.
Ajiyar zuciya yasauke Jin yanda tace sorry din ya tayarda mota sukabar gidan.
Koda suka dawo shiru sukayi dukkansu cikin motar tsawon mintuna kafin ta Dan dago ta kalli gefensa vata kalli fuskarsa tace"
Thank you.
Daga Mata Kai yayi Shima batareda ya kalletaba.
Budewa tayi ta fito Shima fitowar yayi tareda bude boot ta dauki wasu kayan tayi gaba yabi bayanta da kallo yanda take tafiya kamar zata karye sbd sanyin jiki da damuwa
Bata ankaraba tayi tuntube zata Fadi taku biyu yayi ya tareta ta 'dan fado jikinsa.
Akaro na farko dayaji wani Abu a taba jikin mace sbd duk turawan dayake huldar aiki dasu yana shaking hands dasu wasuma har hugging Amma baitaba Jin komaiba Sai yau yaji wani irin shock da kasala lokaci guda.
Itama jitayi tasake loosing balance gabaki Daya jikinta yasake sakewa.
Kawu dake Shirin fita yana sanyo kai harabar gidan yayi sauri zaro idanu tareda sake fitowa Yana quresu da kallo daidai lokacin Suma su nadey sun fito Yana riqeda gefen qugunta suna dariya Yana sake riqota Yana Mata rada Tana kamo wuyansa dayayi Mata tsawo Yana sake dagata.
Juyowa kawu yayi gefensu Suma Yana kallonsu kamar zai rusa ihu
Yasake maida idanuwansa kansu JJ da kamarma sunfi su nadeyn shagala cikin masifa da daga murya yace"
Kowane shege ya tattara yazo yabarmin gidana.
Da sauri su nadey suka saki juna sbd sai alokacin suka Ankara dashi suka ga halinda jj da fammah din suke.
Nadey tayi saurin Isa ta riqo fammah din sai alokacin suka saki juna nadey ta riqeta zasu shiga ciki kawu yace"
Kudawo Nan kafin na karya qafafuwanku masu kama da takandar rage hardai ke me kama da jikar ifiritu Ashe kin koyawa fatimar rashin arzikinki gashinan su arana tsakiyama Kuma Dan tsabar anrainani ko aure Babu....
Cikin sauri jj yace"
Kawu bafa yanda kake tunani bane kayi hakur.....
Jabiru kadaisan a qule nake dakaiko?
To kayimin shiru agurin ko wlh na fusata na daura muku aure ayau saiku qarata can kaida ita
Kema Ina ganinki ta arziki Ashe kinkoyi rashin munyarsu..
Girgiza Kai fammah din tayi da sauri zatai mgn yace"
Zakimin shiru agurin kosaina fasa bakinki Mai kama da qofar kasuwa.
Zaro idanuwa famman tayi da qarfi tareda cewa"
Kasuwa????
Dariya suka danne sbd sukam sunsan halin kayansu tsaf itace sabuwa a abin.
Kayan menene nake gani harda akwatina???
Kallon kayan jj yayi yace"
Kayane aka siyo Mata.
Lefenka ne kenan ka hado Babu sanina sbd anrainani ban isaba kokuwa shi aliyun shine yabaka dama to ai ita fatiman a gidana take Dan haka a ikona take bazan bayarba.
Da sauri Zaki ya matso Yana cewa"
Yi hkr kawu dama Ina zaayi wani Abu bada izininkaba kawai kayan ne yasiyo tukuna.
Wani banxan kallo jj ya jefawa zakin Yana cewa"
Sarki karka sake hadabi da kawu mana,
Wlh kawu dama Babu wani wannan mgnar kayane na sawa batada aka siyo Mata thats it.
Kallonsa fammah tayi akaro na farko taji wani na rejecting dinta Kai tsaye duk da tasan he's right saidai yanda yayi mgnar cikin bayyana rashin sonta a fili.
Cikin wani irin yanayi ta bude Baki tace"
Baba Babu komai a tsakanina dashi ya taimakenine da suturar dazan saka ne kawai koba komai mezaiyi da 'yar da akewa kallo da laifin iyayenta,
Bashibama Babu Wanda zaiso aurena sbd karya auri 'yar mutanenda akewa kallon azzulimai,
Nasani Babu Wanda zai taba shaawar Sona bare aurena Dan haka kuyi hkr dukkaninku Nima ba laifina bane....
Kuka tasaki tareda juyawa ta shige ciki Tana toshe bakinta.
Sanyi dukkaninku jikinsu yayi musamman shi jj ya juya jiki ba qwari zai bar gurin kawu yakira sunansa.
Dawowa yayi ya tsaya yana sauke Kai.
Cikin nutsuwa kawun yace"
Jabiru idan nine zanmaka zabi da aure kamar yanda nayiwasu Zaki to haqiqa na zabar Maka Fatima sbd jahadi zakayi ka tallafi rayuwarta marainiyace zaka samu tarin lada da kwanciyar hankali insha Allah.
Baisoba har cikin ransa Amma ayanda kawun yake uba agaresu bazai iya musawaba,
Sarkima yayi Masa zabi ya daura Masa aure bai musaba bareshi.
Ajiyar zuciya ya saki a boye kafin ya dago ahankali yace"
Nagode kawu Allah yaqara girma da nisan kwana.
Dafasa Zaki yayi cikin basa qwarin gwiwa yace"
You won't regret this my magaji I promise,
Bakasan yanda auren dolen kawu yakeda Dadi bane zakazo yiwa kawu godia Ina Nan.
Wani kallon takaici kawun ya jefawa zakin zaiyi mgn jj yayi saurin cewa"
Yi hakuri kawu.
Jinjina Kai yayi zaiyi mgn saikuma ya fasa ya wuce Yana cewa"
Bazaa dauki lokaciba tunda baa buqatar wani abin inaga kufara Shirin Nanda wata Daya dai zanfadawa babanku.
#MAMUH.
*_Mamuhgee46_*
Kamar wani mugun labari haka ya dauki zancen auren Amma Kuma Daya tuna kawun ne yayi Masa zabin saiyaji zuciyarsa ta kwanta da alamarin saidai baisan ta Ina zaifara rayuwar iyali da fammah din ba.
Tareda Zaki suka fita zuwa ma'akatar dasuka bude gini guda sbd 'yan daba irinsu a da wadda aka budeta sbd su kawai Dan tallafi da yancinsu na bawa kowa jarin irin sanaarda zaka iya idan ka shiryo aka bude tsohon case dinka sune ke tsaya Maka da haka Allah yataimakesu abubuwan dabanci suka Fara ragewa yan ta'adda nata shiryiwa wasu Kuma ana tallafa musu suna komawa makaranta masu shaye shaye kuwa idan yayi tsamari gurin yan drugs suke muqasu da sharadin ba azaba Mai tsanani shekara gudane idan Allah ya taimakeka ka daina kenan har abada wasu ko shekarar basayi sun fito sun daina.
Cikin dakinsu kuwa nadey ce tafadawa fammah abinda baban yace ta Dora da cewa"
Kiyi hakuri nasan baba zai fahimta idan har bakyaso,
Zaiyi fada sosai amma daga baya zai hkr sbd bayada riqo ko fushi irin na wasu iyayen,
Baba haka halinsa yake saidai shi haka tasa qaunar take idan baya Miki fada to bayasonki sbd shi abinda yakesone kawai yake sawa gaba da fada komai kayi laifine.
Girgiza Mata Kai fammah tayi cikin yanayi na sanyi tace"
Akaro na farko a rayuwata da want yayi min abinda mahaifine kawai keyi,
Banda Mai tsayamin,
Banda Wanda zankira nawa saiku,
Baba yayimin abinda zaiyiwa 'yarsa konace abinda yayiwa 'yarsa Wanda Nima Ina yiwa kaina shaawar samun Ingantacciya,wadatacciya da kwanciyar hankalin rayuwan aure kamar naki to mezaisa naqi zabinda Wanda yadauki matsayin uba aguna?
Na amince da duk zabi da hukuncin baba akaina kowane irine.
Murmushi nadey tayi tareda tausayinta sbd Tana hango maraicin dake cin fammah din atareda ita sbd fammah din mutum ce Mai tsananin so da qaunar familynta.
Tasani kewar am haryanxu Tana cinta saidai tamayarda hankali gurin yimasa addua tareda nemawa iyayenta gafara.
Ahankali nadey itada iya talatu da fadime suka bude akwatinan suka zuzzuba kayan aciki komai Kuma ya shige abinda Babu daga baya nadeyn tace zataiwa jj din magana saiya qaro ko yabayarda kudi su siyo.
Ana Kiran magrib ta fito kitchen daukeda basket data jero semo dinda tayi Masa da fresh vegetables soup sai lemon mix da Babu sugar ko kadan aciki sai Zuma kadan itama.
Wanka tayo tareda alwala Tana fitowa sallah tafarayi kafin tafara shiri cikin wata doguwar royal blue straight D&G rubber fab gown.
Wani hot red lipstick tasaka na oriflame akan lips dinta sai powder kadan da eyeliners shima kadan baama ganewa ta sake gyara gashinta ta feshesa da hairspray ta dauresa tsakiyan Kai.
Bold hot red lipstick dinta shine yafi daukan hankali sbd yanda ya zauna.
Shape dinta da rigar tabi ta lafe fammah ta kalla Tana ayyanawa aranta itama saitayi haka zata samu zuciyar mijinta da kyau idan sukai aure sbd har cikin ranta ta karbi auren sbd ta tabbata jj zai inganta rayuwarta tabata kyakkyawar rayuwa so ita kam ta karbesa hannu bibbiyu tunda haydar yagama yimata nisa gwara ta rungumi abinda ya sawwaqa gareta sbd inganta rayuwarta karta tsaya hange rayuwar batada tabbas afterall Zama cikinsu shine rufin asirinta da farin cikinta,
Asalinsu basuda alaqar jini kusan dukkaninku zuriar gidan,
Aminci ne da amintaka tun dagakansu baban da amininsa hakama jj dasu Dr sayyid dasu nanu Amma sun riqi junansu tamkar jini daya,
Sun maida kansu zuria daya suna qaunar junansu fiyeda komai,
Iyayenta sune silar duk wani kuka da qincinsu Amma still sun karbeta acikinsu tazama tasu haka Dan uwanta sun basa damar gyara rayuwarsa.
Batada wasu dangi nata bayansu Wanda sai yanxu take sanin dadin qauna da tattalin juna tareda sakewa da juna Wanda basusamuba koyaushe iyayensu na hidimar neman kudi kota kyau kota sabanin hakan.
Murmushi yasauka a fuskanta ahankali ta tashi tazo ta rungume nadey data saka kimono da Vail saman kayan cikin farin ciki ta furta"
Thank you nadey dattiya Noah.
Murmushi nadey tasaki tareda rungumeta tace"
And wat are you thanking me for Mrs j.d Noah???
Murmushi fammah din tasake saki sbd Jin itama she'll soon be fammah D Noah.
Sake cewa tayi"
Thank you for giving me a wonderful life and family to call