Showing 69001 words to 72000 words out of 81157 words

Chapter 24 - BURI DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

08 Apr 2025

6624

ma a natse suke fes fes abinsu,Amma fa Lagos nada dadi kawai dai balainsu ne yafi qarfin dattiya Dole Zaki ya tsula tsiya Ashe ba abanza ya deboba,
Ruqayya tayi qoqarin zama anan.

Itadai nadey tanajinsu har suka iso jirginsu na sauka jj ne yazo daukarsu mota biyu shida nanu tun a mota yake tambayar maqwaftansa sbd so yake Koda zai Isa duk suna nan suyi masa barka da dawowa.

Suna isowa qofar tangamemen gate din gidansu guda biyu da akayi komai iri daya Suka fito da sauri harsuna rige rigen cewa"

Wato dai da gaske wani shegen saman ya mallake gidansu.


Dariya Nanu yayi tareda yin horn me gadi ya wangale gate Suka shige sai alokacin suka lurada su mal zailani dasukazo tarbonsu suna musu barka da isowa tareda murnar sabon gidan take Suka gano saisuka hau washe baki suna karba gaisuwarsu ana sake tambayar yaushe rabo.

Koda Suka shigo gidan sosai farin cikinsu yakasa boyuwa sukahau duba gidan suna aikin sakawasu zakin albarka da adduoi.

Qatoton palone da three bedroom sai wani palon me bedroom daya Wanda nan ne na kawun,
Sai boys quarter me Palo da daki sai toilet Wanda shikuma ba nanu ne sai dakin me gadi.

Sai wani babban part dake gefen nasu Kawun Wanda yake babban palone da bedrooms biyu sai kitchen da dining room shikuma shine na zakin JJ yace zai zauna da dad.


Komai iri dayane Dana alhaji idi Kuma anzuba musu furnitures da komai na buqata.
Iya talatu da shafa'atu duk bacin Rai dasuka dawo dashi tini suka aje Suka hau murnar sabuwar duniya baqi da Yan anguwa sai murna suke shigowa yi.


Daki daya ta zaba a Palo kusadana iya talatu anan ta baje itada baby z dayan dakin Kuma me aikin da aka daukoce.

Basu samu hutuba sai dare sosai mutane suka tsagaita.

Itakam da wuri tayi bacci iya talatu kuwa anacan anata baza sabon lissafin rayuwar daza'a fara.

Daqyar su alhaji dattiya Suka samu sauqin mutane suka shigo gidajensu amatuqar gajiye sai yanzu suke gane wani lokacin ba wulaqanci masu kudin keyiba kawai gajiyace da takura irinta mutane.

Abinci aka Kai masa Mai raida lafiya yaci yakoshi yashige daki yayi kwanciyarsa yana cewa"

Daban dawoba da yanzu talatu ce zataji wannan dadin ita kadai.

Hararar gefensa tayi tace"

Kaikuma baqin cikinka karnaci wannan arzikin nikadai.

Murmushi yayi tareda gyara kwanciya akan lafiyayyan gadonsa Yana cewa"

Ke yanxudai ki koyi daa ga miji dama can zafin talauci da rashine yasa nake dauka,yanzu hayaniyar mutane ma ta isheni.

Dariya abin yaso Bata saita gintse ta miqe ta kwanta itama.

Washe gari bayan ankai masa Kari yayi ya shirya cikin wata babbar shadda gezner fara qal sai daukan ido takeyi ya fito inda akace yanada baqi harabar gidan aka shimfida masu babban dadduma yafito ya zauna suna gaisawa cikin farin ciki baqinsu ne na kasuwa dasukai sana'ar lemo tare.
Alhaji idi ma cikin bulun shadda Mai qyalli ya qaraso Yana gyara babbar rigarsa ya qaraso ya zauna suna sake gaggaisawa.

Har yamma suna tarbon baqi idan lokacin sallah yayi masallaci suke shiga suyi sbd shima angyarasa sosai.

Abinci kuwa haka ake fitowa da kuloli daga gidajen biyu su mal zailani tuni Suka fara lasa arzikin Suma duk da Zaki kusan duk dattijan anguwan yabisu da jari ba laifi.


Yau kwanansu biyar da dawowa yaune Kuma jumaa dad da kansa yazo gidan suka Jima sunata magana.

Dukkaninsu hidima sukeyi sosai tsakanin gidajen biyu dadynta kuwa sai tambayarta metakeso yakeyi sai abin yabata mamaki tace"

Dad meke faruwane???

Aurenki zaa sake daurawa yau after juma'a.

Kallonsa tayi da sauri muryarta na rawa gabanta na faduwa tace"

Aure Kuma dad?
Dawa???

Nine na zabar Miki mijin kinji nadey karki damu.

Murmushi ta qaqalo tareda sunkuyar dakai sbd dad bazai taba magana tace aa ba.
#MAMUH.
*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

_*Mamuhgee41*_
Duk yanda taso daurewa kasawa tayi bayan fitar dad gurin iya talatu taje inda take kicin tareda matar dahiru da fadima me aikinta suna yanka fruits ta qaraso tanason tambayar iya din saita kasa tasake ficewa.

Tana fitowa tsakiyar palon wasu baqi su biyu Suka shigo farare tas dasu Saidai kammaninsu da dad yasa tasake kallonsu cikin Dan qaqalo murmushi tace musu welcome.

Dayar me Dan shekaru ce ta taso tareda rungumeta jikinta sosai cikin kulawa da qaunarta tace"

Hey nadey nice aunt din haydar qanwar dadinsa amby Sam Noah and this is our younger sister Sarah Sam Noah.

Murmushi ta qaqalo cikin farin cikin ganinsu ta sake rungume Sarah Suka sake gaisawa tace Bari takira mum dinta.

Kicin Takoma takirawo iya talatu Suka dawo palon Allah yasa sunajin hausa nan Suka gaggaisa dasu aka fara kawo musu drinks da cake dinda aka siyo na Leda nabawa baqi.

Fira sukeyi ahankali Suna tambayarta yanayin aiki da Shirin bikin tana Basu amsa a sake.

Saida aka tafi masallaci sallar juma'a kafin Suka fito sai alokacin Suka saka aka dinga shigo Mata da kayan akwatinanda haydar yasa sukazo dasu Suka wuce gidan dady.

Aikuwa kayane sosai set din wasu kyawawan maroon alnafyeel bags take iya talatu tasaka aka sanarwa gwaggo shafa'atu Suka shigo ganin kayan.

Itadai daki tashigewarta tana waya da  JJ daya kirata cikin sanyin murya da tayata farin ciki yace"

Andaura auren Mrs haydar Zaki Noah.

Wani lumshe ido tayi tareda sakin siririn numfashi tana sake gyara kwanciya kan gadon dakin tace"

Nagode dady j.
Allah yabaka matarda tafini komai na rayuwa da kyawawan halaye nagari.

Amin""yace tareda cewa"

Baby z na gida ko tabi su aunty?

Dama tun dazu tana gurin fadima Amma inaga Bata bisuba tana nan.

Tana Gama wayar ta miqe taje tayo alwala ta tayarda sallah cikin farin ciki da kwanciyar hankali.

Shiru shiru Babu Wanda yadawo har yamma sai kawai ta share itama taci gaba da hidimarta dama gwaggo shafa'atu takira wata madam eliqueen  Yar sudance Mai gyara tuni tasamu isowa tafara aikin gyaran jikinta duk da tace gskia tana buqatar sati iya talatu tace satin yayi yawa ayi Mata dai yau da gobe sai jibi sbd jikin nadiyar ma a gyare yake da santsin fata da laushi sbd tsadaddun products dinda take amfani dasu gurin wanka da shafa.

Saida aka fara kirayen magriba Suka kammala eliqueen ta wuce ita Kuma ta fada wanka da ruwan scent dinda tabata na rosallee florish purple sandal scent.

Aikuwa take toilet din ya gauraye da qamshinsa sosai har cikin dakinta
Ita kanta tana wanka tana lumshe ido sbd sanyin qamshin turaren.

Tana gamawa ta fito ta shirya cikin wata purple nolet gown Mara nauyi ko wani dogon hannu batada ta daure kanta daya Dan jiqe baki bakin tasaka hijab ta tayarda sallah.

Tana idarwa ta cire hijabin ta fito tana qwala Kiran z sbd tazo tayi sallar magrib.

Bata lurada mutum a palon ba Saida ta juyo zata sake qwala Kiran z idanuwansu suka hadu gabanta ya fadi sbd wani irin kwarjinin dayayi mata dakuma tsoronsa daya shigeta.

Sanye yake cikin farar shadda qal sai qyalli takeyi yacire babbar rigar tana riqe a hannunsa da alama tunda rana Bai sauyaba.


Ajiyar zuciya ya sauke ahankali tareda kallonta da idanuwansa dake cikeda gajiya sbd taron aurensu na yanzun yafi na farkon cika da jama'a sosai harda manyan abokanan huldarsa Dana dad dinsa gasu kawu Suma yanzu jama'a sun qarar musu,
Dattiya a gurin daurin auren dayaga maroqa sunata faman kirari suna roqo saiyaji abin nabasa kunya
Yaringa Jin kansa suka kalli juna da ido kowanne ransa wani iri kenan abin haka yake suna taqura jama'a suna wulaqanta kansu ba girma ba wani mutunci cikin mutane.

Idan kana roqo Wanda kafi qarfin arzikima wlh yafika girma cikin jama'a.

Da wannan tunanin kawu yacewa maroqan gurin su samesa gida bayan kwana biyu insha Allah zai Basu jari Kona sana'ar lemo ne yafi wannan yawon zubarda mutuncin.

Aikuwa nan Suka hau godia suna sake sakawa aure albarka da jero masa manya manyan adduoi.


Ba zato tajisa gabanta sosai harsaida tayi Dan Baya ya riqota a kasalance ya sake kallonta da idanuwansa dasuka sake rikita nutsuwarta yakai bakinsa kunnenta cikin kasala yace"

Yunwa nakeji sbd farin ciki yau ko ruwa banshaba tun safe please ki dubeni kar yunwa ta kashewa baby z uncle takashewa kawu Dan gaban sirikinsa.

Turesa tayi tareda harararsa tana yamutsa baki yasaki murmushi Mai kyau tareda juyawa bayan ya jefeta da wani kallonda yasan sirrin tasirinsa akanta tun a wancan lokacin dabatasan takamu da sonsaba bare yanzu datagama dulmiya cikin son nasa.

Aikuwa take duka gabobinta suka sake taji wani sanyi na shigarta
Boyayyan murmushi ya subuce Mata ta juya zuwa kitchen tana sake waiwayon qofar daya fice.


Yana zuwa part dinsa tubewa yayi yafada wanka sbd yau din amatuqar gajiye yake sosai.
Yana fitowa ya shirya cikin doguwar jallabiya baqa Mai laushi da tsantsi kasancewarsa fari saitayi Masa kyau matuqa ya tayarda sallar ishai da akayi Yana wanka yayi abarsa.

Yana gamawa ya dawo Palo ya zauna jiran takawo masa abincin bayan yakashe dukkanin wayoyinsa.

Agogo yasake dubawa yaga lokaci yatafi sosai shiru sai kawai ya miqe ya fito Yana 'dan dafe kansa dake ciwo kadan.

Tsayawa yayi daga balcony din part din nasa sbd hangota tafe daukeda tray fuskarta a daure sosai Wai ita karyaga damarta
Abin saiya basa dariya da mamaki yasaki murmushi kadan Yana juyawa kallon gate da aka bude mota tashigo yakumasan kawune ya dawo.

Kawu datun shigowarsu ya hangeta gabansa ya Dan tsinke Yana fitowa mota yace"

Kai waye agurin nan????

Gintse dariyarsa Zaki yayi tareda saukowa ya qaraso gaban nadiyar data tsaya cak jikinta na rawar kunya

Ya tsaya gefenta cikin cinnawa kawun tashin hankali yace"

Barka da dawowa kawu?
Nadey ce kawu ninace takowomin abinci naci.
Allah ya tashemu lafiya kawu.

Wucewa yayi gaba kawun yabisa da kallo idanunwansa kamar zaiyi kukan takaicin yanda Zaki Sam baisan kunyaba ya iya cinna masa hauka wato ga dattiyan mahaukata ko?
To wlh inanan a dattiya Dina kudi Basu canzaniba cikin masifa yace"

Wato Zaki nidai duk yanda naso shikenan mutanen Lagos sunci galaba akaina jininsu yafi na ruqayya qarfi akanka idona kake kallo kanacemin Allah yatashemu lafiya da 'yar tawa,

Ke Kuma ido tsakiyar Kai kinfito Lilo Lilo dake kamar gwaiwa Zaki kaiwa miji abinci wato dai ko yanzu bazaku Bari ace ku tareba to wlh Babu shegenda zai kaini yabaro kamar wancan karon so kukayi na Gama asarewa gurin zagayen kariyar mutuncina acikin gidana Ina daga kwance Kuna tsallakeni Kuna zuwa shaaninku...


Iya talatu da hayaniyarsa tasata fitowa ta tararda abinda ke faruwa ta qaraso cikin takaicin Halinda baya canzuwa kamar na dattiyan tace"

Haba Dan Allah Kai Wai yaushe zakasan ka girmane??
Karka manta yanzu fa jikokine dakai Kuma 'daya na cikin gidan nan idan taji irin diban albarka dakakewa iyayenta wlh ka zubar musu da mutunci a gurinta...

Ke Ni banason qabli da baadi,
Ni bakiga irin renin dasukai min bane Ina ubansu,
Shi wancan qaton mara kunyar dangin Lagos bakiji cemin yake Allah yatashemu lfy sbd tsabar raini to wlh daidai nake da gyarawa ko wane Mara kunya zama a cikin gidan nan sbd gida nawane baza'a rainani cikin gidanaba.

Dawowa Zaki yayi cikin yanayi na sake haukata kawun yace"

Kawu kayi hakuri zamu kiyaye insha Allah baza'a qaraba,
Baby kibawa kawu hkr.

Cikin tsananin mutuwar jiki ta bude baki murya na rawa zatai mgn kawun dake hararar Zaki baqin ciki yagama cinyesa agabansa Zaki ke Kiran 'yarsa da baby a hasale yace"

Kina bude baki agurin zan karya qafarki Mai kama da hayaqin tsintsinyar qamshi.

Tsit Sukayi dukkaninsu harda iya talatu dake boye tata dariyar tace"

To kaji sunbaka hkr dai yanzu muje daga ciki ke Kuma wuce kikai abincin.

Wucewa yayi Yana gyara babbar rigarsa haryayi gaba ya dawo yace"

Idan kinkai karki dawo rufe qofata zanyi Kuma naji kin kwankwasa Ina budewa kusani yau saikun barmin gidana.

Da sauri ta kallesa ta girgiza Kai cikin rawar murya tace"

Nafasa baba wlh Bari na......

Ba shiru taji zakin ya janyeta tana qwacewa tana masifa ya wuce da ita har part dinsa ya bude qofar palon suka shige ya rufe.

Kawu daya saki baki cikin tsananin mamaki da takaicin yanda surukinsa Kuma 'dansa yagama rainasa.

Qyaci yayi yace"

Zakusha mamakina acikin gidan nan Dan wlh bazaku batamin jika da wannan Rashin kunyar da Rashin mutuncin nakuba.

Yana shiga yasakawa qofar babban palonsu key Yana cewa talatu duk kika bude qofar nan kinfi kowa sanin abinda zanyi Dan wlh hanaki kowace irin Sanaa zanyi.
#MAMUH.
_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

*_Mamuhgee42_*
Suna Shiga palonsa ta qwace jikinta tareda ajiye abincin ta juyo a fusace zata fara masa masifa taji bakinsa cikin nata ta zaro ido da qarfi zata qwace yasake matseta jikinsa Yana kashe Mata ido daya Yana shafo gefen cikinta.

Saurin qwacewa tayi da qarfi tana sauke numfashinta dake fita da sauri a boye ta zauna bakin sofa tana kasa dagowa ta kallesa.

Zama yayi hankali kwance kusada ita tareda yin balance yace"

Bani black tea din tukuna saiki bani veg din kadan shima.

Kasa motsi tayi sbd gabaki daya yagama hargitsa nutsuwarta hannuwanta har 'yar rawa sukeyi ta matsa kadan ta zuba masa black tea din ta miqa masa ya karba Yana kallon hannuwanta dake rawa ya hada dasu ya riqe tareda sakin ajiyar zuciya ya kalleta da idanuwansa masu sakata nutsuwa ahankali cikin kulawa yace"

Hey it's me,
Your husband,
Nine dai Yaya zakin dakika sani Babu wani qari ko ragi ok??

And I love you more than anything danake dashi arayuwa bazan taba cutatar dakeba,
Kawu duk wannan abin dakikaga yanayi yanayine sbd dabiarsace bawai haqiqanin abinda yake fadane acikin zuciyarsaba besides idan kawu ya daina wannan halayen nasa to ba lafiyaba sbd ciwone kawai zaisa ya daina Wanda bama fatan hakan,,,
So just chill my beautiful baby bride""yaqarasa fada Yana Mata wani siririn murmushi.

Miqewa tayi da sauri zatabar gurin ya riqo hannunta yadawo da ita kan cinyarsa Yana kallon fuskarta dake fidda annuri Yana Shan tea dinsa.

Harya Gama tanakan cinyarsa tana kallon yanda yakeyin komai nasa cikin izza da burgewa tun dacan haryanzu,
Haryanzu Bai wani iya sake fuska sosaiba Saidai murmushinsa da yanzu ya yawaita musamman agareta.

Murmushi tasaki Bata saniba tana kallon hannunsa inda tabon cizonsa yake a hannun haryanzu Wanda tasan da gangan yabar tabon Yana kallonsa bayan yana iya shafa magani tabon ya Bata.

Inda take kallo ya kalla ahankali take nutsuwar dayake Shiga duk lokacinda ya kalli tabon tashigesa sbd wannan moment din shine best moment a rayuwarsa sbd aranar yasan meye mace Kuma macenma wadda zuciyarsa da gangar jikinsa tafiso fiyeda komai.

Murmushi yasake ahankali tareda kallon nadeyn da kyau yana tuna yanda batai qwarin yanzuba a wancan lokacin taci wahala harda taumashi Amma Kuma yanzu tafi sanin ciwon jikinta musamman da hutu ya batata yanzu Amma zai banbance da kansa.

Matso da ita jikinsa yayi sosai tareda shafo cikinta murya qasa qasa yace"

Kinsan dai kawu yace bazaki Bata masa jikoki da Rashin kunyaba ko????

Murmushi tasaki tareda da kallonsa da idanuwanta dasuka mugun ta6asa Amma ya basar da shafo idanuwan Yana cewa"

Hmmmm kinason rabani da nustsuwatane?? That's not gonna happen.

Dauke gira daya tayi tana kallonsa da mamaki tace"

Really??

Hannunta ya matse cikin nasa Yana sake kallonta yace"

Hmmm.

Wani juyi tayi da ido tareda narkewa ajikin nasa tana lafewa tace"

Ok bacci ni nakeji gashi kasa babana ya koroni a Karo na biyu.

Murmushi yayi tareda safa wuyanta dake buso masa wani sirrin qamshi yace"

Kuma nasan yau bazai iya bacci ba Yana tunanin 'yarsa bazata iya daukar lalurar jarumin sarki kamataba....

Dukan qirjinsa tayi tana qoqarin miqewa yasake riqeta cikin jikinsa Yana Kiran sunanta cikin slow.

Shiru Sukayi dukkaninsu kowanne idanuwansa arufe suna sauke numfashi ahankali cikin nutsuwa.


Sun Jima ahaka kafin ya miqe da ita ajikinsa ya nufi hanyar bedroom dinsa Yana kallon fuskarta data rufe idanuwanta.

Kan king-size bed dinsa ya kwantar da ita tareda juyawa ya nufi closet ya fiddo wasu ellecrux sleeping set na couples ya cire na mazan ya ajiye Mata na matan.

Jallabiyarsa ya zare ya nufi toilet yayo alwala Yana fitowa ya tararda tasaka Bata tayi saurin kwanta tareda lallubewa ya dauki nasa yasaka ya fesa Hugo boss spray dinsa ya kashe lights yazo gefen datake ya kwanta tareda shigewa jikinta sosai musamman sbd body contact dasuka samu na yanayin rigarta datafi Kama da Babu duk da taqi Bari yagani Amma yaji sbd Saida yasaka hannuwansa ahankali ya Gama lalabo yanda yanayin rigar yake ajikinta.

Akan cikinta ya ajiye hannuwansa Yana sauke Mata numfashi Mai dumi a wuyanta daya sata qanqamesa tana sake shigewa jikinsa da narkewa cikin jikin nasa.

Jin tagama hautsina duk wani tunaninsa yasa ta janye ahankali tareda sakin murmushin jindadi tana rufe ido cikin sanyin murya kaman zatayi kuka tace"

Bacci nakeji kaina da cikina harma da qafafuwana duk ciwo sukeyi.

Bede ido yayi da sauri cikin duhun ya kalleta saikuma yayi sanyi ya qyaleta tareda gyara musu kwanciya Yana lumshe ido.


Qarfe goma na safe ta fito daga part din ta nufi part dinsu baba tana Jin wata irin kunyar hada idanuwa dasu saitafijin kunyarsu ayanxu fiyeda dacan.

Da sallama tashiga palon
Baby z datun safe ta daga hankalin kawun akan Ina mummynta tanajin sallamarta ta taso da gudu tayi gurin nadeyn tana cewa"

Yehhhhh mummy your daddy said you left me hia and....

Shut up z""tafada tana Dan riqo hannunta.

Kawu dayake cikeda z din tunda ta ishesa da surutun neman uwarta yace"

Jaira me Kama da jikar ifiritu zakisan Dani kikeyi uwayenki bazasu maidani mutumin wofiba kema kizo da jajayen kunnuwanki na inyamurai ki rainani.

Dariya zancensa yabawa nadeyn da iya Amma Suka gimtse tana gaidasu ta wuce daki ta shirya cikin riga da skirt na gold atampa maroon ta fito ta nufi kitchen tahau hada masa breakfast sbd baban ya fita iyace kawai zaune a palon tana kallon African magic hausa.

Veg chips source tayi masa da no shuga black tea sai fresh lemon mix.

Saida takai Masa breakfast din tadawo tayiwa baby z wanka ta shiryata sbd dadynta daya Kira a shiryata zaizo ya dauketa harsu aunt su tafi.

Tana Gama fitowa Sukayi Dan zuwa part dinsa din itada z taji ana hayaniya bakin gate ta juya ahankali tana kallon gate din saitaji kamar hayaniyar na qara yawa ta Dan matsa.

Abinda tagani ne yayi mummunan daga hankalinta ta juya da sauri gabanta na bugawa da sauri
Yana ganinta ya ture me gadin da sauri yafado gidan ya riqeta tasaki wani irin ihun tashin hankali da tsoro ta turesa tareda daga hannu zata maresa saita fasa ta janye z baya jikinta na rawa tace"

Am bakada hankali ne?
Get out of here tun kana gane hanya da kanka....

Zubewa yayi gabanta cikin tsananin kuka abuge ya riqo qafafuwanta Yana cewa"

Dan Allah baby kidawo gareni wlh bazan iya rayuwa Babu keba,
Mutuwa zanyi nabi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login