Showing 66001 words to 69000 words out of 81157 words

Chapter 23 - BURI DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

08 Apr 2025

6620

cikin gyara babbar rigarsa dasai zashi babbar hidima yake sawa mal idi yashigo shima fes cikin babbar riga da hularsa sai faraa yakeyi.

Cikin girmamawa nadey tace"

Ina kwana baba????

Lafiya kalau Nadiya ya muka tashi?
Ya kwanan baqunci?

Murmushi kawai tayi tana cigaba da cin wainarta datake zaune gefen iya talatu.

Siririyar sallamar zakice ta sakasu juyowa yana sanye cikin wasu armless adidas masu tsadar na geaming daya gamo dukkanin qwandunansa da muscles dinsa masu nuni da qaqqarfan jikinsa a bayyane suke sbd Rashin hannun rigar sai hular rigar daya rufe kansa da ita asalin asalin jininsa na Igbo ya haskakawa a fatarsa.

Da ido ya kafeta Yana gaidasu kawun dasuka tsaya kallonsa baki a sake
Itadai iya talatu yi tayi kamar bataga me yake kalloba ta amsa gaisuwarsa tana tambayar zainab.

Ahankali ta Dan yamutsa fuska tace"

Good morning.

Bai amsaba ya dauke idanunwansa daga kanta Yana kallon kawu yace"

Kawu zan tambayeta wani abune.....

Ko amsa kawun Baibasa ba ya juya suka wuce sbd yagama gano dai dagashi har zakin Babu Wanda halinsa ya canzu idan ya biyesu wannan karon babbakesa zasuyi a wutar murhu ko yafada rijiya subar talatu da baqin cikin zaman takaba,
Saidai shikuma gskia bazai iya saka ido ace ko yaushe a gaban idonsa ake iya shege da 'yarsa ba.

Suna fita mal idi yace"

Dattiya gskia yaran nan zuwa zamuyi musake daura musu aure karfa azo ayi irin da kananan sake da baki kaji qaruwa ta samu.

Barni dasu idi duk wani Dan iskan America da shegenta daidai nake dasu baresu baqin haurenta inanan a dattiya Dina jira nake nagama sallamar masu damuna dinnan kafin naji dasu.

Daga bayansu sukaji yace"

Kawu kuje ga mukulli nan nabawa Nanu yakaiku duk inda zaku.

'dan so yayi ya washe baki saiya fasa ya nufi motar Nanu ya bude musu suka shiga zakin ya zuro Kai ya miqawa Nanu ATM dinsa yace"

Kabiya ka cire musu kudi kabasu idan zasuyi amfani dashi.

Duk yanda kawun yaso 'daurewa kasawa yayi ya saki wani murmushin jindadi yanajin wani girma na shigarsa musamman yau yasan a kasuwa saiyayita samun Yan fada.

Suna wucewa yadawo cikin gidan ya kalli iya talatu yace"

Ki shirya zaku fita yanzu JJ zaizo zai kaiku.

Kallonsa tayi da alamar tambaya tana wani daure fuska da basarwa.

Qin Bata amsa yayi ya juya ya fice waje gurin yaransa danshi haryanzu yanason zama acikinsu.

Qarfe goma JJ yazo ya daukesu suka fita zuwa gurin passport.

Sukuwa su kawu yawone Suka fitayi gashi kowannensu anabasa dubu hamsin hamsin ya zuba cikin babbar riga sukaje kasuwa rumfarsu suka ringa bankwana suna rabon kudi anata tayasu murnar yayansa dasuka dawo sunyi arziki dagashi har mal idi sun mayarda sunayensu alhaji da alhaji.


Daga kasuwa duk inda sukasan sunyi Sanaa Saida sukaje bankwana daganan Zaki yayiwa nanu waya yace yakaisu ayi musu passport daganan su samu su JJ a immigration office.

Aikuwa acan yakaisu inda akai musu passport da komai a Daren aka aikasu nemar musu visa din umra.

Jin hakan yasasu kusan kasa bacci musamman yau da kowannensu ya riqi dubu hamsin hamsin cikin aljihunsa tuni Suka raba dare suna firar.

Duk yanda Zaki yaso kebewa da ita qi tayi sai sake zamewa takeyi tana basar dashi,
Tun Yana hakuri harsaida yafadawa kawun
Kawun yayi shiru sbd ganin duk dai iya Reni sun rainasa Amma zaiyi mganninsu Dan yafi qarfin iskancin duk wani shegen America bare su na Nigeria.

Dad da kansa yazo Sukayi bankwana ranarda zasu wuce aka kaisu airport,
Ita,baby z,iya talatu,babanta,mal idi da matarsa sai Nanu.

Tunda Suka Isa take cikin tsaka Mai wuya sbd tsabar masifar babanta data mal idi sbd su komai saisun sanshi daki daki.

Babban tashin hankalinta shine tunda Suka tafi so biyu su baban na Bata sai ansaka nemansu shi baba idi ma har wata tsohuwar takari yaso maqalewa Wai zai aureta daqyar aka kashe zancen Suka maida hankali gun ibada.

Su kuwa suna nan ansaka gyaran gidan anroshesa gabaki daya ansaki kudi anfara aikin gidan tuquru sbd dattiya ya dage akan bayason tashi anguwar dole Suka sakarwa wasu kudi sosai Suka siye gidajensu aka hada dasu ana sabon gininda akeson kammalawa cikin qanqanin lokaci.


Yau da tashin hankali Suka tashi sbd mugun zawon da baba idin yatashi dashi akan kajinda tunda sukazo qasar dagashi har kawun basuda aiki saicin kajinsu da madarar Laban saigashi ta taba mal idin Suka dunguma zuwa asibiti inda qarahedai Saida aka jingina da Basu gado.
#MAMUH.
*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

*_Mamuhgee40_*
Tagumi ta rafka tareda sakin numfashi Mai sanyi lokacinda tasake shigowa dakinda aka kwantarda baba idin ta tarardasu babanta yasiyo musu gasashiyar kasar injin sunaci hankali kwance suna magana komawa gida dasuka kusa Yi.

Cikin dumuwa ta kalli Dr din cikin turanci tace Dan Allah ya sallamesu su koma gida sbd tagaji da abin kunyar dasuke saka mutane Dan musamman babanta dakebin duk ma'aikatan asibitin da kallon tausayi Yana cewa shifa gani yake kazarsu ta Nigeria tafi wainnan mutanen qwari.

Mota tasamu Suka dunguma Suka dawo masaukinsu ita lift tashiga su kuwa dama duk ubanda ya taru basa shiga lift tunda Suka shiga so daya Basu Kuma ba stairs sukabi duk tsawon building din sunfi ganewa hakan.

Dakinsu Suka shige itama tuni ta shige nata inda take itada baby z,sai iya talatu da shafa'atu matar idi Suma daki guda.

Da daddare ita tayo musu order na abinci sukaci taje dakinsu baban tayita bugawa Amma shiru qarshe reception takira akace Mata yanxu Basu Jima da fitaba.

Dafe goshinta tayi Tama fasa zuwa dakinsu iya talatun Takoma daki takwanta tareda Kiran JJ cikin damuwa tace"

Dady j wlh su baba haukatani zasuyi a qasar nan yanxu acikin Daren nan fa sun fita Kuma nasan wlh bazasu iya dawo da kansuba sai anje nemansu inaga gida zamu dawo direct bazamu biya Dubai dinba gskia.

Dariya yayi zaiyi mgn Zaki dake gefensa Yana aiki a laptop ya miqa masa hannu batareda ya juyoba ko cewa qala ba.

Miqa masa wayar yayi tareda miqewa Yana cewa,

Bari nayi magana da dad.

Jin shiru sosai ya ratso wayar yasa zuciyarba harbawa kadan tareda lumshe ido tana sakarwa pillow nauyinta sbd tasan waye ya karbi wayar.

Ahankali yace"

Nine nakira dazu kika qi daukar wayana sbd Kinga damata da yawa right????

Zuuuu tayi da idanuwanta dake neman rufewa sbd yanda muryarsa ke tayar Mata da wata sabuwar kewarsa da tsananin sonsa.

Ahankali itama ta bude baki tace"

Banganibane.

Aje laptop din gabansa yayi tareda kallon wayar yasake tsuke fuska ransa na Dan baci baisan renin yakai hakaba Amma zai dawo da ita hayyacinta idanma hauka tafara zatasan Zaki nanan yanda yake.

'Daure murya yayi kai tsaye yace"

Bani 'yata.

Murmushi tayi Mara sauti tareda kallon baby z da bacci keson daukarta ta miqa Mata wayar tareda cewa"

Your uncle na magana.

Karba tayi cikin murna tana cewa Ina dadynta da granddaddy dinta.

Tanaji yayi fira da 'yarsa Yana gamawa ya kashe wayar baisake nemantaba.

Shiru tayi cikeda tunanin yanda zasuyi rayuwa idan Suka dawo sbd yanxukam Allah yagani tana buqatar mijinta atareda ita musamman yanxu dataga 'yan Mata masu kyau da burgewa na nuna zalamarsu a fili kansa,

Gefe daya Kuma tunanin fammah ne ke neman damunta sbd tanason sanin Yaya take tunda tasan suna cikin tsananin Rashi da buqata.

Wayarta ta dauka takira Annah Suka hau fira daga baya take fada Mata tanason sanin halinda dillas ke ciki.


Washe gari dasukaje masallaci acan Suka wuni bandasu baba dasukai wani aminin Wanda shima Dan juma ne da Dan jummai suka bazama yawon Shan shayi da maiqo har dare Basu dawoba
Sai washe gari tagansu shi dinma tana Jin motsinsu tayi saurin fitowa tun kafin tayi mgn iya talatu da itama take qule dasu ta fito ta watsa musu wani kallo cikin takaici tace"

Allah dai yasa kusan kun tsufa kudaina wannan yawon ta zubar din,
Harda qasardaba qasarku ba bazaku iya riqe qafafuwanku ba ku zauna guri daya wannan abin kunya har ina.

Cikin daure fuska dattiya yace"

Ke talatu ki fita idona banason Rashin mutunci da Rashin iya mgn,
Meye amfanin zuwan idan mutum Bai zaga yaga koina ba......

Cikin takaici ta katsesa da cewa"

Dan Allah dattiya kudaina wannan yawon kungafa gobe zamu koma Amma kun kasa tsay.....

Cikin kufula idi da dama yake cikeda ita tun wancan lokacin yace"

Talatu waike meyasa Allah bai zuba Miki dangana da iya Kama bakinkiba,
Bansan yaushe qiyayya tashiga tsakaninmu ba ranar har farin ciki kikeyi kika kirani sbd nazo Naga matattu da dagaske ne matattun ne wato nagansu zuciyata ta buga na mace agurin tunda dattiya baida kowa saini yanxu,
To dattiya kashiga tsakanina da talatu hakama ita tashige gaba tasa shafa daga hankalina a qasa Mai tsarki akan auren nan danayi niyya ta gashi nan nafasa auren Amma ba yanxu zankoma gidanba tukarin zamuyi muma.

Zaro ido nadey tayi cikeda faduwar gaba tace"

Baba wane irin tukari ana zaune qalau Dan Allah kuyi hkr yau tsakar dare jirginmu zai tashi.

Washe baki dattiya yayi yace"

Badamu zaku koma ba anan zamuyi takari alhaji garba zamu zauna agurinsa hanyoyin dogaro dakai gasunan birjik su zai koya Mana a qasar shekara daya mundawo gida.

Tagumi talatu ta rafka daga tsayen tanajin inama baazo dasuba wannan abin kunyar dasu dattiya zasu jawo musu.

Duk yanda Nadiya tayi dagewa Sukayi akan raayinsu batasan lokacinda tafashe da kuka ba tana sake roqonsu Amma Suka wucewarsu Suka barta iya talatu nabinsu da hararar baqin ciki da takaici.

Zama Sukayi dukkaninsu Suka rafka tagumi cikin baqin ciki da damuwa
Nadey datasha kuka harta gaji ta dauki waya takira haydar.

Yana kallo wayarsa nata ringin yaqi dauka Kuma yasan itace Amma yayi banxa da ita sbd zai banbanta Mata Aya da tsakuwa.

Qaruwa damuwarta tayi sbd tasan mulkinsane da izzarsa yasa yaqi daukar wayarta sai takira dad.

Cikin tsananin damuwa tafara fada masa abinda ke faruwa abin yabasa mamaki sosai sadai Kuma yasan dadine yasasu cewa bazasu dawonba takari zasuyi.

Cikin lallashi yace"

kwantar da hankalinki nadey nasan ya zan musu zasu dawo kafin kutashi tafiya.

To tace murya a sanyaye.
Ita su iya talatu nema ke Bata tausayi musamman shafa'atu da duk tafiyar ta fice aranta tun lokacinda mijinta ya ha'du da takari.

Dad nagama waya da Nadiya yakira layin wayar dattiya da aka siya musu kafin tafiyarsu wadda bayan Zaki da JJ Babu Wanda ya taba kiransu sai yanxu dayaji tana ringin cikin aljihun babbar rigarsa.

Da sauri yacirota Yana cewa"

Zaki ne ke Kira qila yaji bayanxu zamu dawoba bankwana zamuyi.

Dauka kawai yayi sbd koya tsaya duba sunan ba ganewa zaiyi sosaiba.

Jin muryar neyo yasashi sake washe baki Yana kurbar shayinsa na larabawa Mai shegen zafi yace"

Aliyu ya Nigeria??

Murmushi dad yayi tareda cewa"

Lfy klau alhmdllh yaya,
Yaya ibada da Kuma baqunci?

Lafiya kalau ibada baqunci Kuma ai munxama Yan qasa tuni.

'yan qasa Kuma yaya?
To dama Ni akan maganar gidankane kaida Yaya idi dazu aka kawo takardu Wai gidan mallakin wasu ne ba nakuba.......

Wata qatuwar ashar ya mulmulo Yana qonewa da ruwan shayin ya miqe yace"

Wane Mai rabon wahalar ne yace haka?
Gidan damuka gida da guminmu,
Ganinan tafe Nigeriar Inga wane Dan iskan kudun ne.

Alhaji idi da tuni ya dire kofinsa Yana jiran qarin bayani yace"

Meyasamu halalina???

Ciki ciki dattiya yayi da qananun idanuwansa ransa amatuqar bace yace"

Wani Dan baqin cikin dayakasa ganin munyi gaba ne Wai filin gidansa ne.

Miqewa idi yayi Yana cewa"

Dama yanxu magauta tako ina kunno Kai zasuyi Amma daidai nake dasu Dan Ni Dan iskan takari ma nafi qarfinsa bare na Nigeria muje.

Alhaji garba na musu maganar zamansu tuni sukace sun fasa yanxu Amma zasu dawo.

Yace"
to shagon damuka hada kudi muka Kama fa zamuyi sana'a??

Kai alhaji garba bakaji Wai hawun dake neman hawanmubane kake mgnar shagon Saida shayi da kaji.

Masaukinsu suka dawo lokacin har anyi sallar magriba suna zuwa ba kunya Suka hada kayansu tsaf Babu fuskarda kowa zai samu tambayarsu ya akayi dayake Suma sansan halin sai Basu ce musu qalaba har akai ishai Suka sake kakkamta kayansu mota tazo ta daukesu zuwa jidda suna Isa basuyi ko mintuna arbainba aka Kira jirginsu Suka miqe har lokacin su kawun fuskar nan a tsuke tam.

Suma haka Suka fecesu hardai iya talatu ita dama shafa'atu jira take akoma ta gyara masa zama.

Baby z ce kawai ke walwala a tsakaninsu sbd zuwa lokacin tasaba da kakanta sosai suke dasawa Saidai idan tayi Abu kadan turawa nashan zagi ba sauki.

Qarfe goma na safe jirginsu ya sauka a Lagos sun fito Dan neman taxi zuwa masauki sai Jin tayi baby z ta kwace daga hannun babanta tana cewa"

Yeehhh my uncle.

Faduwa gabanta yayi ta dago da sauri ta kalli inda z din tayi tagansa sanye cikin wasu Armani wears normal size blueback sun masifar fitarda kyawun hasken fatarsa yasaki wani guntun murmushi tareda warewa 'yarsa hannu yadagata sama yana cewa"

My baby is back.

Kiss tai masa a kumatu tana dariya sosai tace"

I miss you so much uncle.

I love you so much my little miss Noah.

Su iya talatu ya qaraso Yana gaidawa fuskarsa a Dan sake kafin ya maida kallonsa kansu kawu da mal idi ya bude baki gabaki daya Yana kallon wata taquwar Mata data wuce da wani wando daya gama kamata kusan komai Bata ana gani sai wata riga Mara hannu da wani kalar gashi kalar Blue data saka akai.

Dattiya kuwa takalminta yake kallo Yana tafiya har yayi tuntube da jakar kayansu saura kadan ya kife talatu ta girgiza Kai tana cewa"

Karkaji ciwo alhaji kalli gabanka.

Fuskewa yayi Yana amsa gaisuwar zakin Yana sake kakkallon mutanen dake harkokinsu a airport din.

Allah yagani shikam bai taba ganin anbawa mahaukata damar kaida kawo hakaba sai anan.

Mota Suka dunguma dukkansu dama wata black BMW bus ce aka kawosa da ita ta daukesu duka suka nufi babban gidansa dake Victoria island.

Sosai ikon Allah yagama kamesu kawun tako Ina tun lokacin Suka dau hanyar zuwa gida Zaki yace"

Kawu kana cikin Lagos ne fa.

Kallo juna Sukayi da idi cikin ransa yace"

Ashe mutanen Lagos din sunfini iya tsula tsiya.

A boys quarter aka sauke su baban inda Suka hau baccin gajiya bayan sunyi sallah sunyi nis.

Bedroom biyune a palon qasa su iya talatu Suka shiga daya ta shige dayan.

Wanka tayi tai sallah ta kwanta sbd tana buqatan hutawa Dan tunda sukai tafiyar nan batada hutu haukacewama tasoyi sbd tsabar tension.

Bata fitoba sai yamma shima sbd yunwane.

Babu kowa a makeken palon sai hayaniyar z datake jiyowa a palon sama ta nufi qofar datake sakaran qila kicin ne tana budewa taga Babu komai ba kowa ta bude fridge shima drinks ne kawai sai apples ta dauki daya tanaci ta fito tana duba best restaurant a Lagos din ta wayarta sbd tayi order.

Wani kitchen crafts dake kusa tayi ordern chips source da white veg pasta sai coconut water mix tadawo palon ta zauna tana qoqarin Kiran dad taji qamshin possession royaltee man yashigo hancinta tareda sanyin aircon split dake daukeda qamshin airfresh na rosallee.

Lumshe idanuwanta tayi tareda budesu ta dago ta kalli direction din saman Suka hada ido take jikinta yasake mutuwa takasa Koda motsi harya sauko yazo ta gabanta ya wuce ya fice yabarta dabin bayansa da kallo jiki amace.

Koda aka kawo order dinta takarba tabiya kudin tadawo ta nufi dining taci.
Tana gamawa tasake komawa daki.


Da daddare semo da miyar kaji tareda gasashen kifin dayaji lemon yasa aka kawo gidan kowa yaci yaqoshi.

Saida yabari su kawu sun qoshi yace"

Kawu muje kuga gari.

Ba musu Suka kwasa Suka bishi tun Abu nabasu mamaki harsuka fara gigicewa da balain dasuke gani tuni dattiya yafara shafawa kansa lafiya da Yan iskan Lagos musamman wani gurin dayake gaisu sukasan da gayyane saiga su da salati suna ya maidasu gida.

Dattiya daya dawo harda hawayensa Yana cewa"

Lallai Ashe iskanci na Lagos shine yake cewa yafi Yan Lagos iya iskanci.
Allah yarabasa da iskanci irin na Lagos.

Dasuka dawo tuni kowa yayi bacci ya hayewarsa sama ya tube yayi wanka ya kwanta Yana danne abinda zuciyarsa keso.

Washe garima haka yasa aka dinga yawo dasu kawun a Lagos saigashi sun haukace da kallon ikon Allah da wani balain dayafi qarfin tsufansu.

Cikin saa kuwa suna wata anguwa lekki fada yatashi akahau sare sare da qona tayoyi take sukahau rawar jiki ba arziki Suka daga hankalin driver jikinsu Babu Wanda bai hada zufan balai ba harsuka dawo gida jikinsu rawa yakeyi mal idi ma Saida yahada dashiga bayi tun daga ranar harsukai kwana biyar basu sake marmarin fita koinaba.

Ranar dasuka cika sati aranar zasu koma gida har wani murna sukeyi sbd sunyi kewar gida matuqa musamman da duk tsorace suke sudai da Lagos din.

Airport Suka nufa kowa da ticket dinsa a hannunsa Banda Zaki sbd badashi zasu komaba Yana wani aiki ne.

Suna wucewa gaba ya kamo hannunta ya dawo da ita baya tareda matseta jikin mota Yana kallon cikin idonta da wani irin kallo dake kashe Mata jiki.

Hannu yasa ahankali ya shafo fuskarta tareda hura Mata iska ya daga Mata gira qasa qasa yace"

Babu ko bankwana Zaki tafi...???

Dan zamewa tayi yasake matseta tareda Kama hannunta yayi kissing yace"

Ki shirya Dana dawo zamu tafi.

Ahankali ta girgiza masa Kai batareda ta dagoba.

Yasaki wani siririn murmushinda yasake kashe Mata jiki yakai bakinsa kunnenta yace"

Okk nagane agaban kawu kikeson ki jere masa jikokinsa kenan ko????

Turesa tayi da sauri murmushi na kufce Mata tayi gaba tareda waiwayosa kadan Suka hada ido tasake juyawa da sauri ta wuce.

Dattiya da tuni yaketa masifa da baby z akan saita koma gurin uncle dinta ya danneta cikin takaici Yana cewa"

Ke banason taurin Kai irin na jajayen kunnuwan america,
Waincan uwayen naki basuda kunya ko kadan musamman ubanki daya Gama tarwatsamin tarbiyar 'ya tun bakizo duniyaba nake fama da Rashin arzikinsu dasunaji dasun daina Amma Ina..

Qwacewa tayi tana cewa"

Banaso sakeni.

Riqota iya talatu tayi cikin dubara tana cewa"

Kyalesu zainab ai yanzu mamanki zatazo.

Barta karma ta qyale kakkarya shegun qafafuwanta masu Kama Dana bebin roba zanyi kowama ya huta,
Iyayenta sun rainani itama ta rainani bazai yiyuba jaira Mai kama da baquwar aljana babbakewa da asarewa nawane banyiba kafin zuwanta duniya saikuma tazo Ina magana tanaimin turanci tunda ga dattiyan mahaukata,
To wlh ko mahaukatan lagos qarya suke bare na turai.

Isowar nadey ce tasa fadan yakoma kanta harsuka shiga jirgi fadan yakeyi idan yaga wani abin kallon saiya saurara ya kalla kafin yaci gaba.

Candai bayan yagama fira ta barke tsakaninsa da aminin Amana yace"

Kai alhaji idi wato su Lagos duk rabinsu mahaukatane.

Hmmm alhaji dattiya Ni wlh yanzu ko labarin Lagos naji anayi Aina daina shiga na zaqalqale,
Mutane ana kallo suna tafe a tsirara sbd lalurar hauka Amma duk ankasa masu taimako Kuma Amma dayake Naga basa duka ko ihu lafiya kalau suke tafiyarsu shinema saukin abin.

Dariya dattiya yayi yace"

Wato sbd girman lagos kana gani mahaukansu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login