Showing 45001 words to 48000 words out of 81157 words

Chapter 16 - BURI DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

08 Apr 2025

6617

ahankali yanajin duk qorafinsa na narkewa sbd yanayin yanda take maganar da muryarta dake rusa kuzarinsa ko yaushe.

Cikin wata irin murya data sata Dan kallon wayarta da mamaki yace"

Please baby don't do this again kinji yanda kika sani damuwan tafiyanki batareda munyi mgn ba
Nayi booking ticket samune banyiba da ayau din nan Saidai kawai ki ganni Chicago.

Murmushi tayi Mai sauti cikin zuciyarta qaunar JJ din da tausayinsa na sake shigarta sbd taji qaunarsa ne sbd zakinta na tsananin qaunarsa hakama tanajin tausayinsane sbd yayi Rashin Zaki dakuma soyayyarta dake taredashi Wanda yasani har abada Babu filin soyayyar kowa aranta bayan ta zakinta.

Cikin sanyi tace"

Dady j Dan allah ka kwantarda hankalinka komai na tafiya accordingly so please Just take care of the empire and my daddy.

Aje wayar tayi tareda sake rufe idanuwanta tana sake relaxing jikinta.

Qarfe takwas tagama sallar ishai tafara shiryawa itada Annah zasu
Ita Annah maison kwalliyace sosai so takira makeup artist akai Mata kwalliya tashirya cikin wata mini dinner gown daity blue Mai shegen daukan ido sai wasu black heels na laveeganxier sai pouch dinta tayi kyau sosai.

Tana gama kallon mirror ta juyo ta zubawa nadey ido data fito daga dressing room din dakin baki sake take cewa"

Holy Spirit,babe ure so damn hot I swear....

Gaban mirror nadeeyn ta iso ta tsaya tareda kallon kanta cikin wata fablic Italiano gown da stones dinta na rainbow ke rawa royal blue daidai jikinta wadda Bata kamataba Amma daidai jikintane sbd shape dinta daya fito sosai cikin tsari,

Blue vintage lious heels na a qafarta sai gashinta data daure cikin wata blue scarf qarami Mai adon tsones shima.
As usual brown lipstick ne a bakinta sai liner kadan da mascara da daliano pk powder.

Qamshin alexendral miss royalle ne ka tashi ajikinta saina oud kadan.

Diamond bracelet dinda ke hannunta da earrings dinta sai qyalli sukeyi ta sauke ajiyar zuciya ahankali tareda rintse idanuwanta takira sunayen Allah kafin ta bude tareda sakin murmushi cikin sanyi kafin ta dauki pouch dinta ta juyo takalli Annah dake kallonta tana murmushi tace"

Shall we???

Yes ma""tafada tana dariya suka fito.

Jasmin ma ta shirya tuni tafito su take jira Suka fito cikin wata baqar marceedes Benz 3600baymach2018 Suka fito Annah ce ke driving dinsu.

Hakanan takejin wani irin Rashin Jin dadi na shigarta,
Zuciyarta wani irin daci da qunci takeji
Da mijinta na raye da yanzu tanacan tana rayuwar aurenta hankali kwance kamar kowane ma'aurata,
Duk wannan dukiyar da daular datake ciki yanzu duk wannan murmushin nata da farin cikinta its all fake cikin zuciyarta qunci ne fal na Rashin mijinta da babanta Wanda take kwana dashi take tashi dashi aranta
tafison rayuwarta ta dah,
Tafison zama cikin rufin asiri inda mijinta da mahaifinta duk kuwa da Rashin jituwarsu.

Dafa hannunta Annah tayi ahankali tareda Kiran sunanta tana cewa"

Hey Nd are you ok?

Murmushi ta qaqalo tareda mayarda hawayenda Suka ciko Mata ido ta juyo ta kalli gurin sun qaraso.

Wani babban mansion ne Sukazo ta bude ta fito ahankali zuciyarta na harbawa ta juyo ta kalli sunan dake rubuce a locks na gidan daga gefe kan wani Dan madaidaicin block board dake jiki anrubuta _welcom to Dilla's_
Qurawa sunan ido tayi radadin rabuwa da mijinta na dawo Mata sabo hakama mutuwar 'yar uwarta qwaya daya tal da itace hasken rayuwarta.

Gyara tsayuwarsa tayi tareda kallonsu Annah tasaki murmushi tareda yin gaba itada Annah Jasmin na bayansu.

Securities Suka miqawa invitation dinsu aka bude musu qofa Suka shige tasake sakin wata ajiyar zuciya lokacinda tashigo cikin mansion din
Yau gata ga dillas Wainda Babu Wanda yasanta sai yanzune zasu dandani nata dafin dayafi nasu.

Open space party ne so a wani babban filin shaqatawa dake baya gurin swimming pool na gidan ake bikin anyi decorations masu kyau da tsada gurin sai wani haske da qyallin wuta ke tashi duk yawanci turawa ne Amma akwai baqaqen fata Saidai basukai turawan yawaba,

Duk Wanda ke gurin to tabbas babu Mai qaramin qarfi ga securities tako Ina anzubasu.

Cak ta tsaya tsakiyar filin ta qurawa inda suke ido suna nishadi cikin farin ciki sosai suke
Babu wata damuwa a rayuwarsu kamar Basu dauki rayukan mutane da damaba,
Sun saka mutane da dama kukan maraici Dana azaba,
Sun mayarda yara da yawa marayu,
Sun mayarda mataye da yawa zawarawa,
Sun saka iyaye da dama kuka da ciwon Rashin yayansu....yanxu lokacinsune dasuma zasu dandani wannan radadin da ciwo.

Dikko Dillan ne a tareda wasu turawa Wainda dagani manyane tasanma daya daga cikinsu mayor ne suna magana kowanne da glass din drink a hannunsa dukkaninsu cikin wasu irin tsadaddun designer kaftan suits,
Sai zeel dilla a gefensa itama taci ado white diamonds da wata Canadian tribe gown black tayi kyau sosai sbd kyakkyawa ce shiyasa daga am har fammah sukeda kyau Dan ita suke biyowa.
Am Dilla ne a gefen dad dinsa shima yayi kyau cikin wasu ash suit data fiddo kyawunsa da hutun dake tattaredashi dukkaninsu dariya sukeyi cikin kwanciyar hankali da nishadi.

Fammah ce dataci wani irin ado itama cikin doguwar English Morocco maroon gown Mara hannu tayi kyau matuqa musamman dayake ita farace sosai,
Hango shigowarsu nadeey tayi tasaki wani murmushin farin cikin ganinta tana kallon nadey din duk saitaji kamar zata Raina tata kwalliyar tabbas tasamu best friend dinda ta Jima tana nema Dan dama ita batada kwashe kwashen qawaye yanxune Kam zatayi qawarda hotunansu zasu ringa yawo a media da press.

Kallon iyayenta da brother dinta tareda ajiye glass din hannunta tana kallon nadeey tace"

Mum dad and am my special guest is here lets welcome her please.

Dukkaninsu atare Suka juyo inda fammah ke nuna musu.

Cikin wata irin tafiya ta daukar hankali dake nuna isarta tana sakin wani fitanannan murmushinda atake yagama tarwatsa zuciyar am da babansa ta nufo gurin tana juya jikinta kamar wata sarauniya.

Dukkaninsu baki ido Suka zuba Mata cikeda mamaki da farin cikin haduwa da ita Dan kuwa duk sun santa a media da harkar business sunkai proposal dinsu harso biyu wa kamfaninta Saidai Bai samu isaba saigashi yau itace agabansu cikin gidansu the queen of Noah empire
Tabbas ita din babbar special guest ce.,

Zeel kuwa necklace dinta da brcelet dinta na diamond take kallo tana qiyasta kudinsu kafin ta mayarda kallonta kan kyakkyawar fuskar miss Noah din tana qiyasa,kudi,kyau,gayu,burgewa,ilimi tareda wayewar nadey din duk abinda takeson matar am 'dinta ta hada harta zarta tabbas yau tasamu irin matar datakeson am da ita wadda dukiyarta tasa duniya ta sanda ita.

Mr Dilla kuwa gabaki daya miss Noah tagama basa mamakin haduwa da ita sbd ya Jima yanason shiga cikin business din Noah empire sbd tarin dukiyarsu da success dinsu tareda sunansu Saidai baisamu damaba yau ga dama ta samu tabbas bazai taba Bari haduwarsu ta tsaya iya nanba sun hadu kenan saisun shiga cikin dukiyarta sun mayarda duka dukiyarta tasu,duk wani kamfanin Noah saiya dawo Dilla.

Ahankali am ya ajiye glass din hannunsa Yana kasa dauke idanuwansa akanta zuciyarsa na wata irin harbawa,
Baitaba Jin son wani abuba lokaci daya kamar wannan
Love at first sight.

Tana qarasowa cikin wani irin murmushin Jan aji take kallonsu
Fammah takalli iyayenta cikin farin ciki tace"

Dad mum meet my friend Nadey.

Cikin Jin dadi da sakin fuska sosai Mr Dilla yace"

Nice meeting you mss Noah.

Murmushi tasaki cikin Jin dadi tace"

No the pleasure is mine Mr Dilla.

Kallon mss zeel tayi tareda miqa Mata hannu fuska a sake sosai tace"

_ND NOAH_.

Maimakon ta Bata hannu cikin tsananin farin ciki da qaunar nadey din ta rungumeta tana cewa"

Welcome.

Tana boye mamakinta da farin cikinta dake bayyane ta rungumeta tana cewa"

Thank you mrs Dilla.

Juyowa tayi kan am da tuni dukkanin jikinsa yasaki kowane motsinta yagama burgesa da tafiya da imaninsa.

Ganin yanayinsa yasa tasake sakar masa wani shegen murmushin tana masa wani kallo dayasashi sakar Mata murmushi Yana gyara tie din wuyansa dayaji Yana shagesa ya kalleta Yana gyara tsayuwa da muryarsa mai dadi yace"

Am dilla and nice to meet you queen Noah.

Dariya tadanyi tareda cewa"

Thanks Mr am.

Gabatar musu da Annah tayi a matsayin friend dinta nan suka gaggaisa kowanne na qoqarin janta da fira sunayi harta Dan business Saida Sukayi kafin nan aka fara gabatarda partyn.

Duk inda tayi idon am na kanta iyayensa da qanwarsa tuni Suka ganosa mum dinsa kamar ta goyasa sbd dadi hakama dikko ji yayi kamarma su tara Yan press su sanar musu auren ND Noah da dansa am Dilla.

Fammah ma baqaramin dadi tajiba sbd hakanan tahi hankalinta na masifar tashi idan ta tuno haydar dinta da nadeeyn data gani a haydars buildings Saidai yanzu am ya taimaki fargabarta.

Duk abinda sukeyi tana luredasu saima sake sakar musu fuska datakeyi Suka qara shiga cikin qaunar alaqar.

Sosai Suka sake Sukayi enjoying partyn tareda juna duk wani abinda suke so akanta da am Babu wani kwana kwana sun fito sun nuna maitarsu.

Sosai Sukayi fira da am ta Dan sake masa Suka danyi magana
Bakin zeel gabaki daya yaqi rufuwa sbd farin ciki sai nunawa qawayenta takeyi tana wani dagawa danta yayi matar aure.

Da aka watse am din da kansa yadawo da ita gida da niyar gobe zaiso su fita.

Bayan ya ajeta bayan motarsa tabi da kallo tana jinjina irin wasan dazasu buga.

Tana shiga gidan Bata tsaya kula Annah dake tsokanarta ba ta wuce ta tube ta fada toilet tareda rufe idanuwanta hawaye Suka gangaro Mata.


Yana komawa gida mum dinsa ta taresa cikin zumudi tana cewa"

My am hope baku rabuba Saida kayi proposing?

Wani murmushin farin ciki yasaki tareda kallon dad dinsa dake kallonsu yana jiran Jin abinda am din zai fada yace"

Mum gobe zamuyi magana da ita.

Fammah data sauko daga stairs sanye da kayan bacci ta qaraso tana cewa"

Zanyi farin cikin nadey tazamo member ta cikin familyn nan gskia.

Kallonta mum tayi tana cewa"

Idan munason hakan yakamata kiyi convincing dinta tadawo nan gidan gurinki kafin ta tashi komawa Kinga by then am yagama sace zuciyarta I really want this to happen as early as possible gskia.

Kallonta fammah tayi zatayi magana am yayi saurin cewa"

Yes please fammah convince her.

Kallonsu tayi tareda miqewa tsaye tana cewa"" zan gwada nagani
saidai Nima inada baqo goben banso fita koinaba my haydars is coming sbd baisamu zuwa jiyaba.

Wani dadi yasake kashe zeel tana cewa"

Oh my God my children zasu kasheni da farin ciki.

Dilla kuwa shima wani shu'umin murmushin yasaki ganin zai Kama wuyan manyan business tycoons alokaci daya,lallai wannan karon dillas yakusa zama number one top billionaire sbd daga Noah empire har haydars buildings saiya tabbatarda komai nasu sundawo na dillas.
#MAMUH
*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

_mamuhgee30_
_Not edited_
Washe gari hakanan ta tashi da farin ciki tareda wata irin nutsuwa datake jinta aciki saita alaqanta hakan da burinsu daya dauko hanyar cikane akan abinda suke jira shekaru.

Cikin nutsuwa tayi waya da dad dinta da JJ tafada musu komai shidai dad hankalinsa Bai wani kwantaba sbd sanin mummunar illar dikko da zuriarsa matuqar Koda Wasa Suka gano ita din wacece ba qaramar illa zasu Mata ba Sam bazaizo wani Abu yasametaba,

Cikin kulawa da damuwa jiki sanyaye yace"

Nadey please be very careful ok???
And please take care don't let them know anything daya shafeki tundaga past naki har yanzu dai komaima dangane da personal life dinki karki Bari su sani,
Ths people are very dangerous,they can kill without any hesitation stay alert.

Ok dad don't worry I will be extra careful and I promise you I will set everything right in a short time.

JJ kuwa irin kallon dayake matane yasa jikinta Dan yin sanyi sbd video call ne sukeyi
Ko magana yakasa Jin zancen am na sonta Kuma yagama ganin alamar kulasa zatayi Saidai Sam shi wannan plan din Bai masaba sbd sanin Dole zasu iya ganota idan batada backup Kuma wlh bazasuji shakkar kashetaba kamar yanda sukeyiwa kowa
Yayi aiki dasu yasan sirrinsu Dole tana buqatarsa ta wannan fannin.

Kallonta yayi cikin wani irin yanayi Kai tsaye yace"

Zuwa jibi zan tattara komai nayiwa director handling komai na Noah I will be coming to you
You are not safe alone acikin wainann dabbobin.

Zatayi magana ya datse Kiran tareda miqewa ko magana Bai tsayayi da dad ba ya fice zuciyarsa kamar zata qone sbd zafin kishi.


Itama dafe goshi tayi cikin damuwa tace"

Dady j Dan allah karka wahalarda rayuwarmu banason ganinka cikin wannan halin sbd bazan iya baka abinda kakeso you deserve someone better.

Fammah ranar tazo gidan anan ta wuni Saida yamma Suka fita sukaje spa dinta da akai partyn budewa sundan Jima acan suna dudduba abubuwa sai dare Suka dawo ta ajiyesu ta wuce gida sbd ranar gabaki daya she's Moody akaro ba adadi haydar yaqi zuwa.

Tun daga ranar kullum suna tareda fammah sbd tuni sukai shaquwa ta saki jiki sosai da fammah din harta Kai kusan ko yaushe suna tare.

Ta gefen am ma sosai tasake masa yasake matuwa a sonta kusan ko wace hour saiya Kira wani lokacin kuwa shike zuwa ya dauketa su fita yawo shiyasa hankalin zeel yasake kwanciya sbd zuwa lokacin ansanda maganar akwai soyayya da maganar aure a tsakanin Noah's da dillas.

JJ yazo Saidai ta boye suke haduwa suna magana akan wasu takardun bugi datasa yayo Mata zatayi wani amfani dasu.

Zeel baqaramin so da kulawa take nunawa nadey ba musamman takanas ta dauketa Suka fita wani magazine meeting Dan kawai ta nuna nadey dince matarda 'danta zai aura.


sanye da half sleeping dress dinta black ta fito sitting room ta tarardasu mum suna kallo dasu Annah ta qarasa cikinsu tana cewa"

Gud morning mum??

Morning sweetie""mum din tafada tana kalllonta.

Tana qoqarin zama suka miqe Suka hau table breakfast.

Suna gamawa ta wuce daki tashiga wanka kusan mintuna ashirin kafin tafito ta zauna tana qoqarin fara Shirin Annah tashigo tana sanarda ita zuwan fammah.

Mamaki tayi tareda kallon agogo qarfe goma Sha daya na safe ta dauke gira daya tareda Dan sakin murmushi ta miqe bayan tagama shiri ta bude closet ta dauko wata Ashape shaking gown Mai dogon hannu tasa ta fesa turare ta dauki wayarta tareda zuri slippers ta fito palon tana murmushi cikin wata irin yanga tana cewa"

Wow wat a pleasant visit fammah.

Tashi fammah tayi suka Dan rungume juna kafin Suka zauna cikin walwala fammah din tace"

Sorry I came without informing.

It's ok.

Fira sukeyi dukkaninsu harda Annah duk akan wani beauty parlor ne da Annah zata bude itama daganan sai fammah ta kalli mum din Annah dake zuwa tace"

Mum tun jiya brother na ya fita hayyacinsa akan 'yarki and please mum my fiance is coming I would like nadey to be there with me only for the weekend please.

Kallon nadey mum din tayi tace"

Nadey are you.....

It's ok mum I can go""" tayi saurin fada cikin basarwa Dan dama itama tanason zuwa gidan tashiga jikinsu Sosai.

Cikin farin ciki fammah takira am
Bayan two hours saigashi yazo daukarsu yaci ado cikin wasu designer mark$spencer.

Cikin girmamawa ya gaisa da mum inda Suka Dan fira kafin su nadey Suka fito fammah na janye da 'yar luggage dinta.

Tunda Suka fito yakasa dauke idanuwansa akanta yanajin zuciyarsa na sake narkewa akan sonta,
Jiyake idan Bai sameta amatsayin tasaba zai iya rasa numfashinsa lokaci daya.

Ganin yanda yake kallonta yasa tacigaba da juya jikinta tana tahowa cikin yanga tana fuskarta ba wani a sakeba.

Fitowa Sukayi Suka wuce.

Wata irin tarba mum zeel tayi Mata cikin tsananin farin ciki sbd so take tayi yanda zatayi nadey ta gabatar musu da dad dinta Dan ayi maganar auren ita so take ayi cikin qanqanin lokaci.

Babban bedroom din fammah da ita kadaice a upstairs din sbd shi am part dinsa daban acikin gidan,
Anan Suka yada zango take aka shigarda kayanta closet Batai komaiba ita Saida tayi sallah sbd bataga alamar gidan suna sallah ba qila.


Kwananta biyu a gidan tagama karancesu da duk wani lungu da saqo na gidan tareda sawa harkar business dinsu ido sosai sbd bazasu taba iyawa dasuba tukuna sai sun fara rabasu da dukiyarsu.

Yau tana Gama waya da dad ta fito dukkaninsu Suka hadu a dining room Sukayi lunch inda suna gamawa sukazo Suka zauna itada dad din suna firar business ahankali tareda am din dake zaune kusada ita kamar wasu couples dadi sai sake Kama zeel yakeyi.

Suna cikin firar ne wayarta tayi ringing ahankali tace"

Excuse please""tareda daukar wayar tana miqewa ta koma gefe.

Wat????tafada cikin Dan bacin Rai kafin ta sake matsawa nesa dasu tana cewa"

Ya za'ayi suce abasu wannan proposal din akan 70% basuda hankaline?
Look Jasmin kusake meeting dasu idan sunason nayi musu hanya a Basu wannan deal din saisun yarda zasu zuba 80% Ni kamfanina na zuba 90% and cikin wata shida Suka dawo 150%
So idan zazu saka 80% kuyi magana idan babu kuwa tell them I'm backing out.

Ta jikin tangamemen agogon datake tsaye gabansa tagansu tsaye abayanta suna sauraron duk bayaninta tasaki wani murmushi tareda cewa"

Ok I'll talk to you later Amma yanzu zan turo miki information da details na investment company din saiki Basu.

Rubutu tayi ta turawa Jasmin text din ta juyo saita gansu zaune suna firarsu kamar Basu tashiba.

Tana zuwa ta ajiye wayarta gafen am tana cewa"

Baby I will just use a washroom and com back ok.

Cikin kulawa yace"

Ok.

Tana hayewa sama ta boye tana kallonsu taga am din ya dauki wayarta yayi forwarding din information da details din investment companyn zuwa email din kamfaninsu.

Ya goge ya ajiye wayar.

Kallonsa Dilla yayi tareda miqewa Yana cewa"

Ka tabbatarda ka riga kamfaninta neman wannan kamfanin ka shigar musu da percentage dinmu Mai yawa yanda zasu karbemu mune zamu samu wannan 150% din wannan karon.

Gyada Kai am yayi
Zeel kuwa cikin nutsuwa tace"

You better be very careful karta gano anmata zagon qasa a harkar business tazo tace tafasa aurenka.


Cikin murmushi tasauko tadawo kusadashi ta zauna tana cewa"

Baby nadawo na dauki wayana I'm little bit tired I will go and have some rest.

Tana zuwa daki ta rufe qofa ta nemi wayar JJ.

Yana dauka tace"

Be ready kowane lokaci zasu nemeka kace 70% share na dukiyarsu zasu saka within 3month zaku Basu 150%.

Harzata kashe yace"

Baby please be careful ok.

Ahankali tace"

You too please.

Kwantawa tayi tareda rufe idanuwanta ahankali tana neman relaxing.

Washe gari tunda safe Suka fice da fammah shopping sbd yaudai baqonta yace zaizo.

Daga can gidansu Annah ita ta sauka fammah din tadawo gida.


Zaune suke a office room dinsu dake cikin gidan am ya kalli dad din yace"

Dad munyi magana da wannan investment companyn gskia inaga akwai ha'dari fa musaka fiyeda rabin dukiyarmu aciki kar azo asamu matsala why not musaka kadan mugani.


Shiru Dilla yayi cikin nazari Saidai Kuma irin ribarda yaji nadey din tafada tasamu da tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login