Showing 1 words to 3000 words out of 35486 words

Chapter 1 - ƘADDARA-CE_-By-Salma-Ahmad-Isah

05 Jul 2024

6329

*?ADDARA CE!*

_(Destiny unfolds with a heavy heart)_

*(c)SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY??*

•••
Assalamu alaikum jama'a.

Barkan mu da wannan lokaci. Sannun mu da sake saduwa da ku a sabon littafina me taken ?ADDARA CE!.

To, kamar littafin HASKE, shi ma wannan paid book ne. A kan ?300 kacal. Amma kafin nan ina ?auke da free pages har guda 10.

To sai ku gyara zama, domin kar?ar wannan da zafinsa. Kamar dai yanda kuka saba kar?ar duk wani rubutu nawa.

*?? Ban yarda da wani/wata. Ya sarrafa min littafi ta ko wace hanya ba tare da izinina ba. Saboda yin hakan, babban kuskure ne. Da fatan za mu kiyaye, a bi doka a zauna lafiya.*

Na sadaukar da wannan littafin zuwa ga duk wata 'ya mace dake fama da cutar sickler...

•Gaisuwa zuwa ga Khadeeja Candy, Hadiza D Auta, Sadi Sakhna, Nainerh KD, Fatima Ahmad Isah da kuma Amina Ahmad Isah. Allah ya kare min ku a duk inda kuke.•

*SHIMFI?A...*

KADDARA!

Shin me cece ita?.

KADDARA na ?aya daga cikin hukuncin Allah da ya kan zartar a kan bayinsa tun yayin hallita.

KADDARA tamkar zagayen zobe take, wanda ?an adam ke rayuwa a tsakiyarsa.

Duk wani abu da ya samu bawa tun daga ranar haihuwarsa zuwa ga ranar da zai koma ga mahallicinsa sunansa KADDARA.

KADDARAr ko wani bawa na rubuce ne tun kafin ya iso zuwa duniya.

Kowa da ka ga yana rayuwa a doron duniya yana yin ta ne a doron KADDARA.

KADDARA na ?aya daga cikin manya manyan siffoffin Allah subhanahu wata'ala.

Domin duk abin da ya samu bawa a rayuwa mu?addari ne daga wurinsa. Wa lau me kyau, ko akasinsa.

??? ???? ?????? ??????

*01*

*Unguwar Fantai, Ha?ejia local government, Jigawa state.*

*Da misalin 08:20 na dare.*

Matashiyar yarinya ce tafe a gefen hanya. Hannunta na dama ri?e da farin bokitin fenti. Yanyin yanda doguwar rigar atamfar robar da take sanye da ita ke mannewa a jikinta zai sa ka fahimci cewa ana cikin yanayin hunturu ne.

A hankali take ?ingisa ?afarta ta hagu wadda daga gani bata da lafiya tun asali. A kallo ?aya da za ka mata za ka san cewa tana ?auke da ciwon sickler. Saboda kalar idonta da yake yalo. Da cikinta da ya tashi kamar na me jaririn ciki. Da kuma yanda yanayin jikinta yake nuna cewa tana da sickler.

Damuwa ce kwance a kan allon fuskarta dake nuna nau'in jinyar da take fama da ita. Kuma damuwar tata ta samo asali ne sakamakon wani da ya kar?i kunun ?ari biyu a wurinta ya sha. Ya tashi ya tafi ba tare da ya bata ku?i ba.

Ba wai wannan ne ya jefata cikin damuwa ba. Fargaba take na yanda za su kwashe da matar babanta Auwwa. Saboda kunun nata ne, ita ce take mata shi dan ta je ta siyar ta kawo mata ku?i. Kuma a kullum cikin garga?arta take kan kada ta kuskura ta bada bashi ko da kuwa kunun zai yi jangwa?o ne.

Jiki a sanyaye ta dakata a ?ofar gidansu na masu ?aramin ?arfi. Ta ?aga kai ta kalli gidan tana jin yanda iskar da ake a garin take shiga har cikin ?asusuwan jikinta da ba su da ?wari. Ga kuma yanda ?afarta ta hagu ke mata ciwo tun a safiyar yau da ta tashi. Kasancewar lokacin sanyi shi ne lokacin da ciwon sickler ya fi za?ar ya dinga tashi a-kai-a-kai.

Yawu ta ha?iye a sanda ta hasaso irin azabar dake jiranta a cikin gidan. Ko da rantsuwa za ta yi ba za ta yi kaffara ba kan cewar yau sai ta yabawa aya za?inta. Dan Auwwa ba ?yaleta za ta yi ba.

Cikin sadda?arwa da sallamawa rayuwa ta shiga gidan, bakinta ?auke da sallama. A tsakiyar gidan ta ci birki. Sakamakon arba da Auwwa da ta yi, zaune a tsakar gida tana firfita murhu. Wutar dake cikin murhun ta kalla. Sannan ta fa?awa kanta cewar sai an ?ana mata wannan wutar a fatar jikinta.

Saboda tsabar Auwwa muguwa ce. Ba ta hukuntata da komai sai da wuta. Hantar cikinta ce ta ka?a, a sanda hankalin Auwwan ya kai kanta. Wata uwar harara ta watsa mata tana fa?in.

"Kunu ya ?are yau?"

Cikin fargaba ta gya?a kanta tana aje bokitin hannunta a tsorace. Auwwa ta harerata tana fa?in.

"Mi?o min ku?in nan na lissafa shi."

A hankali ta matsa kusa da Auwwan tana jin ?amshin azabar da za'a mata na kusantota. Ta tsugguna a ?asa. Sannan ta sa hannu ta ciro cinikin da ta yi a cikin jaka. Ta mi?awa Auwwan tana jin ?wallar azabar da ba'a mata ba na cika idonta.

Auwwa ta kar?i ku?in. Sannan ta shiga lissafawa. Har zuwa lokacin matashiyar na tsugunne tana sauraron hukuncinta. Cike da masifa Auwwa tace.

"Ina kika kai ?ari biyu?"

Matashiryar da ?wallar idonta ta fara zubowa ta ?aga kai ta kalli Auwwa. Sannan ta girgiza kanta tana fa?in.

"Salisu osi ne ya kar?i kunun na ?ari biyu ya sha. Da zai tafi nace ya bani ku?in... Shi ne yace... Ya ce wai sai gobe zai bada, yanzu babu canji a wurinsa!..."

Ba ta kai ga rufe bakinta ba wani mari me ?arfi ya sau?a a kan kuncinta. Ta fashe da kuka tana dafe wurin. Cikin ?an?ace ido Auwwa tace.

"Maimuna sau nawa nake ja miki kunne kan bada kayana bashi?. Saboda irin wannan ya sa sai na auna kununa ko na nawa ne, sannan nake baki ki fita da shi... Amma sai da kika ha'ince ni. To ba ki sha ba!"

Auwwa ta kai ?arshe tana rarumar bakin wutar dake cikin murhu, sannan ta kamo hannun Maimuna ta ?ora mata shi a kan tafin hannunta. Haka ta dinga ?walla ihu tana kuka tana fa?in ba za ta sake ba. Amma Auwwa bata ?yaleta ba sai da ta tabbatar da ta ?auke mata fatar tsintsiyar hannun sannan ta saketa.

"Gobe ma ki sake bawa wani bashin kayana kin ji?... Kuma ki zo ki zauna ki ka?a min miya"

Cike da jin ra?a?in da hannunta yake mata. Maimuna ta gya?a kai. Tana jin yanda fatar wurin da Auwwa ta ?ora mata wuta ke tashi. Auwwa ta mi?e daga kan kujerar da take zaune. Sannan ta shige ?akinta.

Yayin da ita kuma Maimuna ta ja jikinta ta zauna a kan kujerar tana kukan da ya zama abokin rayuwarta tun tasowarta. Saboda a rayuwa ba ta jin tana haura sati ?aya ba tare da ta yi kuka ba tun da ta zo duniya kuwa.

Iyaye su ne bango kuma abin jinginar 'ya'yansu masu rauni. Ita bata ta so ta ga iyayenta a raye ba. A lokacin haihuwarta mahaifiyarta ta rasu. Kasancewar mahaifinta direban tirela ne ya sa lokacin da aka haifeta yana garin Lagos. Labarin samun ?aruwa tare da rashin da aka masa lokaci guda ya sa ya ?auko motarsa domin dawowa gida.

Sai dai kuma cikin nufin Allah sai ya gamu da ha?ari a hanyarsa ta Kano zuwa Ha?ejia. Hakan ya sa ta taso a wurin matar babanta ta farko wato Hauwa, wanda ake kira da Auwwa. Duk da kakarta ta wurin uba tama da rai, amma haka aka barta a wurin Auwwa tana gasa mata aya a hannu tun tana ?arama.

Da Allah ya so jarrabarta sai ya sa ta taso da cutar sickler wanda aka haifeta da ita. Ita kuma cutar sickler cuta ce da take bu?atar kulawa da kuma bin doka da ?a'idojin da cutar bata so. Amma sai ga shi ta taso a hannun matar da bata sonta, ballantana har ta bata wata kulawa da me cuta irin tata ke bu?ata.

Hakan ya sa cutar ta kassarata sosai. Dan babu ta yanda za ayi ka ganta ka kasa sanin cewa tana da sickler. A hankali ta share ?wallar da ta gama ?ata mata fuska. Sannan ta kai hannunta na dama ta ?auki ledar kukar da ta siyo ?azu kafin ta tafi tallar kunu.

Ta yi amfani da hannunta na hagu da yake zugo ta kunce laidar. Sannan ta saka ludayi a cikin miyar, ta shiga ka?a miyar da ta san bata isa cinta ba a yau. Dan tun tana ?arama ta saba da horon yunwa. Shi ya sa kullum take ?arewa kamar tsinken kwakwa.

Sai da ta gama ha?a miyar, sannan ta sau?e tukunyar. Ta fa?awa Auwwa cewar ta gama ha?a miyar. Auwwa tace mata to ta kashe wutar, dan kada ta mata asarar ice. Duk da ita ta so ta zauna ta ?an ji ?umin wutar haka ta kashe. Sannan ta koma ?an ?aramin ?akin da yake a matsayin nata.

Ta ?auko ledar magungunanta da kawunta ?anin mahaifinta kan sai mata idan dama ta samu. Ta ?auki palludrine da folic acid. Magunguna biyu da sukafi sau?in ku?i na masu sickler. Ita palludrine aikinta shi ne sace sefar cikin me sickler.

Abinda ya kan kawowa masu ciwon sickler ?aton ciki shi ne kumburar sefa. Kuma ita ce takan jawowa masu sickler ciwon cikin ?ari guda. Sannan idan sefar me sickler ta kumbura ne zai sa ta janye jinin jikin me sickler, ta yanda sai an ?ara musu jini. Ita kuma folic acid amfaninta shi ne hana daskarewar ?argon me sickler.

Daskarewar ?argo shi kan haddasawa masu sickler ciwon jiki da kuma na ?afafu a wasu lokutan. Shi ya sa ake sanar da masu ciwon sickler su ri?a shan ta kullum sau ?aya a rana.

Bisa ga mamakinta sai ta ga folic asid ?in ta kare. Palludrine ?in ma saura ?aya. Zama ta yi ta ?auki palludrine ?in. Ta jefa a bakinta ta fara taunawa ba tare da ruwa ko wani abun da zai taimaka mata wurin ha?iye ?wayar ba.

Saboda irin wa?anan abubuwan ta saba musu. Har gwanda ma folic asid, wata tana da za?i, wata kuma bata da ?an?ano, amma palludrine tana da ?aci. Sai dai kuma ita sabo ya cire mata wannan abin.

Kwanciya ta yi hannunta na hagu na ci gaba da mata zugi, ga yanda sanyi yake ?ara ratsa ?ashin jikinta. Zanin atamfar da kakarta ta bata domin rufuwa ta ?auko ta lullu?a tana jiran ?aukewar ?afar mutanen gidan.

Tana nan kwance ta ji sanda Gambo yayanta, kuma tilon ?an Auwwa ya shigo gidan. Tana jin sanda ya ?auki abincinsa ya fita daga gidan, saboda shi ba ya kwana a gidan. Sannan tana jin sanda Auwwa ta gama cin nata abincin ta koma ?aki ta kwanta.

Sai da ta tabbatar da Auwwa ta wuce birnin sin a duniyar bacci, sannan ta saci ?afa ta fito daga ?akinta. Ta ?auki takalmanta ta fita daga gidan. Sai da ta yi nisa da layinsu ta saka takalmanta. Sannan ta ci gaba da ?ingisa ?afarta ta nufi unguwar Fanisau dake ha?e da unguwarsu.

Dan ba wani banbanci tsakanin unguwar Fantai da Fanisau ?in, kawai dai an raba unguwar ne. Kuma ita unguwar Fanisau ta fi unguwar Fantai kyawawan gidaje. Wani babban layi ta nufa. Inda ta tsaya a bakin gate ?in gidan da ya fi ko wanne girma a layin.

Tana hawayen famun ?unan hannunta da ta yi ta ?aga hannunta ta ?wan?wasa ?aramar ?ofar shiga gidan. Tana tsaye a wurin ta ji muryar ne gadin gidan daga ciki yana fa?in.

"Waye a nan?"

Ta goge hawayenta tana fa?in.

"Baba Habu Maimuna ce!"

"Ah-ah! Maimunatu? Me ya faru?"

Baba Habu ya bu?e ?ofar yana fa?a. Hasken fitilun dake ?ofar gida suka haske masa fuskarta. Ya dubeta yana mamakin abin da ya fito da ita da wannan daren.

"Baba Auwwa ce ta ?onani. Shi ne na zo wurin Mummy!"

Ta fa?i tana nuna masa hannunta da ya ?one. Baba Habu ya kama baki cike da tausayawa marainiyar Allahn yace.

"Assha! Assha! An ya kuwa Auwwa tana so ta gama da duniya lafiya?"

Ita dai bata sake ce masa komai ba, sai zubar hawaye da take. Saboda ji take ma kamar yanzu ta yi raunin. Baba Habu ya bu?e mata ?ofar tare da fa?in.

"Shigo Maimunatu! Sannu!"

Ta shiga cikin katafaren gidan tana ?ingisa ?afarta ta hagu.

"Ita kuma ?afar me ya sameta?"

Baba Habu dake rufe ?ofa ya tambaya. Sai ta tsaya tana fa?in.

"Yau da safe na tashi tana min ciwo!"

"Sannu kin ji"

Sai ta gya?a kanta tana nufar cikin gidan. Da ?yar ta iya bu?e ?ofar falon shiga cikin gidan, sannan ta shiga da sallama. Mutum ukun dake cikin falon suka amsa sallamar suna dubanta. Matar gidan Mummy ce da yaranta biyu, Sadiq da Maryam.

"Mummy ina wuni"

Ta gaidata tana dur?usawa. Cike da mamaki Mummy ta aje wayarta a kan sofa tana kallon Maimuna ?awar 'yarta Maryam.

"Lafiya kalau Maimuna. Me ya faru da hannunki?"

Mummy ta tambaya tana duban hannunta na hagu da ta ri?e. Maimuna ta ja hanci tana fa?in.

"Auwwa ce ta ?ona min hannuna, saboda na bayar da kunu bashi!"

"Allah ya saka miki!"

Fa?in Maryam tana nufar ?awarta. Mummy kuma ta mi?e ta isa gaban Maimunan tana duban hannun nata, kasancewarta nurse a general hospital Ha?ejia.

"Mts ba zan iya treating wannan raunin naki ba Maimuna. Abin da za ayi gobe idan kin fita tallar safe, sai ki bawa wata daga cikin abokan tallar taki ta jire miki kayanki, ki je asibiti ki sameni a can!"

Maimuna ta jinjina kai tana fa?in.

"To Mummy. Na gode"

Mummy ta ci gaba da kallon yarinyar cike da tausayawa.

"Kin ci abinci?"

Mummy ta tambaya tana kallon idonta da ya yi ja alamun tana jin yunwa. Maimuna ta sunkuyar da kanta ?asa tana girgiza shi.

"Maryam ki je ki zubo mata abinci"

Mummy ta bawa Maryam dake dafe da kafa?un Maimuna umarnin tana zaunawa. Maryam ta gya?a kai tana jan hannun Maimuna zuwa jikin kujera.

"Zauna a nan na je na zubo miki"

Maimuna ta zauna. Kuma da ma haka aka saba. Tun bayan fara ?awancensu da Maryam ta fara zuwa gidan. Har ta kai ga ta saba da mahaifiyarsu da kuma yayan Maryam ?in wato Sadiq.

Kasancewar Mummy mace ce me tausayi ya sa take tallafawa Maimunan. Tun da ta fahimci cewa tana cikin matsatsin rayuwa. Hakan ya sa a duk sanda rayuwa za ta mata zafi babu inda take kai kukanta da ta wuce gidan su Maryam ?in. Kakarta Hajja wadda ta haifi mahaifinta kuwa ta tsufa sosai, idan tana zuwa mata da ?orafi a kan Auwwa zai iya sawa ciwon Hajja ta tashi ta hawan jini.

Kawunta ?anin mahaifinta kuwa ba sosai ta cika ganinsa ba. Dan idan ba gidan kakar tata dake unguwar Chadi nan kusa da Fantai ta yi ba, ba ganinsa take ba. A wasu lokutan ma sai ta yi sati tana zuwa gidan Hajjan ba tare da ta gan shi ba. Dan shi kullum yana gona ko kasuwa wurin aikinsa.

A wasu lokutan ma shi da kansa yakan zo domin ya dubata. Idan kasuwa ta yi kyau har kyautar ku?i yake mata, ko ya sai mata wasu daga cikin magungunan cutarta...

"?afar ma ciwo take?"

Tambayar Ya Sadiq ta dawo da ita zahiri. Hakan ya sa ta kalli ?afarta ta hagu sanna tace.

"Yau da safe na tashi tana min ciwo"

"Ai da ma da sanyi sai a hankali. Ita sickler ba ta son sanyi, ga shi ke kuma rabin rayuwarki a cikin sanyi take... Ki yi ta ha?uri kin ji Maimuna. KADDARA CE!. Kuma da yardar Allah za ki cinye wannan jarabawar!"

Fa?in Mummy.

"Kina shan folic acid ?inki?"

Ya Sadiq ya sake tambaya. Maimuna ta girgiza masa kai.

"Ban sha ba. Saboda aikin da ya min yawa yau ya sa ban sha tun safe ba. Kuma yanzu da na duba inda nake ajewa sai na ga ta ?are. Saura palludrine kawai!"

Mummy na latsa wayarta ta girgiza kai tana fa?in.

"Allah ya kyauta"

A lokacin Maryam ta fito daga kitchen ri?e da plate. Ta aje mata a gabanta tana fa?in ga shi Maimuna.

"Na gode"

Maimuna ta mata godiya kamar yanda ta saba. Da yake tana jin yunwa sosai. Sai ta cinye abincin da wuri. Maryam ta bata ruwa ta sha ta gode Allah. Sannan ta godewa Mummy. Da za ta tafi Maryam tace za ta rakata. Sai Mummy tace wa Ya Sadiq ya tashi ya rakasu. Sannan ta bawa Maimuna ku?in napep. Wanda za ta yi amfani da shi wurin zuwa asibitin.

Su uku suka fita daga gidan. Sai da suka raka Maimuna har layinsu. Sannan suka yi sallama suka juya. A sace Maimuna ta shiga gidan. Ta saka sakata. Sannan ta shiga ?akinta ta ?aura gidan sauro. Ta shiga ta kwanta tana jin yanda sauraye ke cizonta. Saboda net ?inta da yake a ?ule.

Ga kuma sanyi da ya dameta. Ita fa tun ba yau ba ma ta riga da ta san cewa ikon Allah ne ya sa take rayuwa har yanzu. Amma ba dan ikon Allahn ba bata jin me cuta irin tata zai kasance a halin da take ciki, kuma ya ci gaba da rayuwa.

*No.42, Inuwa Wada crescent, Utako, Abuja.*

FARUK POV.

A hankali ya tura ?ofar ?akinsa da ya fito daga ciki ya rufe. Sannan kai tsaye ya soma taka strais zuwa ?asa. Abu na farko da ya fara arba da shi a ?asan shi ne. Matarsa Mariya da kuma ?ansa Hilal.

"Babana"

Ya fa?i yana ?aukan ?ansa ?an wata goma sha ?aya da haihuwa. Kafin ya juya ya kalli matar tasa dake zaune a kan sofa.

"Mary!"

Ya kirata da sunan da shi ka?ai yake kiranta da shi. Mariya ta ?aga kai ta kalle shi. Kafin ta aje wayarta da take latsawa a kan sofa ta mi?e tsaye.

"Fita za ka yi?"

Ta tambaya ganinsa sanye da kayansa na aiki. Wato kakin sojoji. Kasancewarsa soja. Ya shafa kan yaronsa da ?ayan hannunsa yana fa?in.

"Eh zan fita"

"A dawo lafiya"

Kawai ta fa?i tana kar?ar Hilal ?in dake hannunsa. Sannan ta koma ta zauna tana aje yaron a gefenta. Faruk ya kalleta sanna ya girgiza kansa ya juya ya fita.

Shi har yanzu ya kasa gane abin da yake damun Mariya. Yanzu kusan shekaru uku da aurensu shi da ita. Amma har yanzu babu wata sha?uwa ta musamman irin wadda ake bu?ata tsakanin miji da mata a aurensu.

Bayan kuma auren soyyaya suka yi shi da ita. Kasancewar ita Mariyan ?anwa ce a wurin abokinsa Mu'az. Kuma ta hanyar Mu'az ?in ya fara ganinta. Har ta kai ga ya fara sonta. Kuma ba tare da ?oye-?oye ba ya furta mata cewar yana sonta.

Kuma ita ma ta nuna amincewarta kan hakan. Shi ya sa ba a da?e ba aka yi aurensu. A farkon aurensu ba zai ce babu soyyaya ba. Amma tun bayan da ta samun cikin Hilal komai ya sauya. Duk da da ma can ita ba mace ce me yawan magana ba.

Gaisuwar da sojoji biyun da suke gadin gidansa ke masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login